Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 91
Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 91: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 91. Ta ce "Good, meyasa kai ba ka yi masa, duk da na san ka fi…
4,479 words
Ta ce "Good, meyasa kai ba ka yi masa, duk da na san ka fi Viper morar mahaifinka, kai ya kai ka waje ka yi karatu shi kuma ya bashi ƙwaya da makami, ya bar shi a sake a cikin al'umma? Ko kuma shi ba shi da ƙwaƙwalwar dai idan an biya masa kuɗin karatu, ba zai iya ba?"
Abdul ya yi shiru.
"Mahaifinka ya yi wa Viper laifukan da su su ka zama kanwa uwar gamin ruruta wutar ƙiyayyar da yake yi wa mahaifinka ce ta gangaro zuwa kanka. Na san ka san meyafaru da Nura guduma zuwa yanzu, duk da ba abu ne mai daɗin da zan ta nanata shi ba, hakazalika ban sani ba ko ka san abin da mahaifinka ya yi wa Viper. A kan case ɗin Nura ya aika a kashe Viper, amma aka ɓuge da kashe matarsa, wadda take twin sister ɗina, kuma aka rufe shi shekara biyar da zargin shi ne ya kasheta" cikin tashin hankali da mamaki yake bin Nabila da kallo.
"Ta yaya ka ke tunanin Viper zai iya yafe wannan tozarci da aka yi masa, Ramma ƙanwace a wurinsa, ya na da dangantaka da ita ta ɓangaren uwa, shikaɗai ne yake tsaye a kansu, yake taimaka musu. Ya na ɗora alhakin mutuwar Nura a kansa, dan haka ya na jin dole yayi duk mai yiwuwa ya yi supporting ɗin su. Ni ya damƙawa ragamar shari'ar rahama, kamar yadda ragamar ta sa shari'ar ma take hannuna. Da zafina har cikin zuciyata nake son na ga an hukuntaka, saboda abin da ka aikata ya tsaye mini. Ga rape, ga tozarta uwar yarinya, ka sace mata 'ya, ka yi amfani da dukiya wurin aurenta ta ƙarfin tsiya. Aka kama wani daban aka ɗora masa laifin, ƙarshe ma aka kashe shi, duk dan a kare ka. Banda waccan azzalumar matar mai rufe kura da fatar akuya da take zaluntar mutane, Naja bunkure wadda na yi wa kaina alƙawarin tona mata asiri. Sai dai abin da na gani ya bani mamaki, daga gareka da kuma rahama, na bibiyi wasu abubuwan da su ka faru babu saka hannunka. Amma dagiyar da muke yi, kowa da gaskiyar sa, twins sister na ban taɓa ganinta ba, duk da wani labari ne daban, amma ko ba komai, na shigo cikin labarin nima. Yanzu abin da nake so da kai, gaskiya ni na karaya, ka tattauna da lauyoyinka, mu yi zama na musamman a kai mu shari'a law, saboda ka samu sassauci ko yaya a hukunta ka dai hankalinsu ya kwanta, ina tunanin makomar Rahama da abin da yake cikinta, they really need you. Ka cire girman kai da duk wani abu, ka roƙi alfarmar Viper da mahaifiyar rahama, ita dan ta rahama a ƙyaleka ba sai an hukuntaka ba. Ta na ta yi mini magiyar a sassauta maka. Amma ya ka gani"
Abdul ya ɗan yi shiru, ƙarshen ƙasƙanci dai ace ya durƙusawa Viper, yaron mahaifinsa da ba sa ga maciji ƙasƙantaccen ɗan daba, amma ba shi da wani zaɓi sama da hakan.
Ya numfasa ya ce "Na amince da hakan"
Ta ce "To Alhamdilillah, ba amincewarka ba kawai, ka tattauna da lauyoyinka. Ni kuma zan san yadda zan shawo kansa, a yi zaman tattaunawar ka san murɗaɗen mutum ne, da ba ya sarrafuwa cikin sauƙi, amma dai ka yi shawara"
Ya amsa da "Shikenan, na gode sosai da sosai, da ƙoƙarin da ki ke yi mana, dan Allah ki gaida mini da rahama, ki ce na ce dan Allah ta kula mini da lafiyar su, ta daure ta din ga cin abinci "
Nabila ta yi murmushi ta ce "In sha Allah"
*** Aka shafe sati guda, Nabila da Viper ba su haɗu ba, ta koma gidan major ta yi zamanta, mutanen gidan babu mai iya tanka mata. Viper ya sha mamakin yadda Nabila ta watsar da shi gaba ɗaya, idan ya ɗaga waya kamar ya kirata sai ya fasa ya ga kamar ya faɗo. Ita kanta daurewa kawai take yi, ba ƙaramin azalzalarta zuciyarta take yi, a kan ta kira Viper ba, ko ta je in da yake ba, amma ta dake.
Lauyan Abdul ya kira Nabila a waya, ya sanar mata da sun amince ayi zaman sulhun.
Nabila ta na zaune a office ɗin ta, ta na tunanin yadda za ta shawo kan Viper a kan lamarin ramma.
Ta cire kayan jacket ɗin ta, daga ita sak dogon wando da shirt, ta ɗora ƙafafuwanta a kan tebur, ta ajiye popcorn a wata container, ta na ci kaɗan kaɗan ta na tunani.
Buɗe ƙofar ya yi ya shigo, tare da yin sallama ƙasa-ƙasa.
Ita ma a cikin ta amsa masa, ta ɗauke idanunta daga kansa, ta maze.
Har ya ƙarasa gaban teburinta, ba ta motsa ba.
Ya daddaki teburin, ta ɗago, ya kalli ƙafafuwanta ya kalleta.
So ta yi tayi burus da shi, sai dai ya yi mata kwarjini, ta sauke ƙafafuwanta, ta na yamutsa fuska.
Ya matso kanta ya tsaya, ya yi gyaran murya ya ce "Kin koma asibiti wurin yaron indabo, me ki ka je yi? Next week idan Allah ya kaimu cigaban shari'ata, ya ake ciki?"
Ta kalleshi ta ce "Ya ka ke bibiyata kamar wata ɓarauniya ne? Na je wurin Abdul, za mu sake zama da su na musamman, kafin mu shiga kotu. Shri'arka kuma normal ne, ban karɓi cin hanci daga wurin kowa ba, na tanadi duk abin da yakamata".
Sarai ya gane magana take gaya masa, da take nuni da abin da ya sanya ta fushi, amma ya basar ya ce "Zaman me kuma za a kuma yi a kan shari'ar ta, ba kotu kawai za a kai mu ba, me ake jira ko wani abin dai ki ke kuma shiryawa ban sani ba. Sannan ki na kasada da rayuwarki yadda ki ka ga dama, ba ki san ta ina za a iya kawo miki hari ba amma ki na yawo yadda ku ka ga dama a gari"
Tashi ta yi tsaye ta ce "Allah zai kare ni, ramma kuma idan ka na kokwanto a kai na, ka canza mata lauya, ka daina zargina babu dalili, ka na yi mini masifa" tayi maganar ta na nufar hanyar fita.
Kamar ya riƙo kyanwa, ya janyo ta ta baya, ta dawo gabansa su na fuskantar juna.
Hakan ya bata damar shaƙar warin sigarin da yake yi, wanda daga nesa ba aji, saboda turaren da ya saka.
Ya ɗago mata jacket ɗin ta, da take shirin fita babu ita, ya na ci gaba da tsareta da idanunsa.
Da idonsa kawai ta gane meyake nufi, amma in da yake kallo a jikin nata ya ƙara razanata, jikinta ya hau rawa.
Ya ɗora mata rigar a kafaɗarta, ya ja da baya, wata irin kunya ta mamayeta, dan kai tsaye ƙirjinta ya zuba wa ido.
Da ƙyar ta aro jarumtar da ta ce "Vi wiwi ka sha ko?"
Ya waiwayo ya tsura mata ido, ta ɗauke kanta ta ce "Kar ka mayar mana da aiki baya"
Ta yi maganar ta na ƙoƙarin buɗe ƙofar office ɗin ta fita hannunta riƙe da rigar.
"Idan ki ka fita ba ki rufe jikinki ba, ranki zai yi mummunan ɓaci".
Ta waiwayo ta ce "Malam know your limit, ka daina ba ni umarni yadda ka ke so" tayi maganar tana hararsa.
Ayshercool 08081012143 92 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.
90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Ba ƙaramin haushi ne ya kama Viper ba, ba fitsarar da Nabila ta yi masa ce ta baƙanta masa rai ba, yadda ya kasa sarrafa kansa, har ya shagala da kallon abin da ba halalinsa ba ne ya fi komai ɓata masa rai.
Sai dai wani irin matsanancin kishi ya taso mata, ganin da gaske a hakan ta fita, bin hanyar ya yi ya fita, ya tarar da ita a reception ta saka rigar, su na magana da Barrister Habib.
Barrister Habib ya na ganinsa ya yi murmushi ya ce "Yau ziyara ka kawo mana, barka da wannan lokaci" yayi maganar yana miƙa masa hannu.
Nabila ba ta saka ran zai kula Barrister Habib ba, amma ta ga ya miƙa masa hannu, su ka gaisa Viper ya bi hanyar fita ya fice.
Nabila kuwa murmushi ta yi, ganin yadda ta kunna shi, ko ba komai ita ma ta rama.
****
Alhaji mu'azzam tun da ya sake haɗuwa da hafsa bayan rabuwar su, kawai ya ji ya na matuƙar jin tausayinta, har ga Allah ya na son Nabila ma, sai dai ya san Viper ba zai taɓa barin sa ya aureta ba, ko da zai samu aurenta sai an kai ruwa rana, amma matuƙa tausayin hafsa yake ji. Ya na ta bibiyar unguwar ko zai samu ya ganta.
Ranar da ya sake zuwa wurin Baba kuwa, Allah ya taimake shi, ya ganta ta dawo daga islamiyya, dan kuwa islamiyya ta koma, idan ta je makaranta ta na samun sassauci daga damuwar da take damunta.
"Baba na dawo"
"Sannu da zuwa" Baba yayi maganar ya na kallonta.
Ta saka kai za ta wuce, duk da yadda Alhaji mu'azzam yake ta kallonta.
Baba ya ce "Hafsatu ba ki ganni da baƙo ba ne?"
"Na ganshi"
"To ba zaki gaishe shi ba?"
Ta kalleshi ta zumɓura baki ta ce "Ina kwana?"
Baba ya ce "Kwana kuma da yammacin nan?"
Alhaji mu'azzam ya ce "Hakan ma na gode, lafiya ƙalau ya makaranta?" Ba ta amsa ba ta shiga cikin gidan.
Ya na so ya yi wa baba maganar hafsa, mussaman da ya samu labarin, ta samu matsalar ƙwaƙwalwa, amma ya kasa.
Bayan baba ya shiga gida ya hau ta da faɗan abin da ta yi kawai ta fashe masa da kuka ta ce "Baba ni ko son ganinsa ba na yi ne, amma ai na gaishe shi, ni na tsane shi ne"
Baba ya waro ido ya ce "Hafsatu, ba a cewa an tsani mutum, ko ba komai auratayya ta taɓa haɗaku, ba ki san mai zai faru gaba ba, ki daina haka"
But Zakiyya ta fito ta ce "Baban saifu, Alhaji mu'azzam ɗin ne ya zo, ko bikonta ya zo yi?"
Hararta Baba ya yi, kawai ya wuce turakarsa, daga ita har Babbar su saifu ya watsar da su, ko turakarsa su ka je korarsu yake yi. Da yaransa kawai yake harkokinsa, shi ma kuma ba dukkansu ba, saifu ne sai Hafsa, mussaman hafsa da yake jin tausayinta.
Zakiyya ta saka Hafsa a ɗaki, a kan yadda za su lallaɓa a sasanta ta koma gidan Alhaji mu'azzam, A take ta ce Allah kar ta ko shi ne autan maza ba za ta koma gidansa ba, ita yanzu islamiyya za ta yi ta zuwa, ta zama malama ta din ga yi wa addini hidima har ta mutu.
"Wallahi baki isa ba hafsa, ka ji baƙar muguwar yarinya, yi wa addinin hidima ba sai ki yi a ɗakin mijinki ba, wallahi sai kin koma, ba zaki yi mini baƙin ciki ba"
"Wallahi ba zan koma na ci gaba da zaman boranci ba, ai tun farko dama ba so na yake yi ba, ki ka saka dole ya aure ni, wallahi ba zan koma ba"
Zakiyya ta rasa yadda za ta yi da ranta, ta shirya ta tafi gidan su Viper, wurin ƙawar cin mushenta rahila, dan lambar wayarta ba ya shiga, rabonta da ita, tun ta na Asibiti bayan Abba ya daketa.
Sai dai ta tarar da ita cikin damuwa da tashin hankali ita ma, shahida ta kashe aure, Amira an sake gwaji babu HIV sai ciki, ta zubar da cikin ta gudu, ga Abbu ya kori Abba daga gidansa, Naziru kuwa tun da ya tafi kudu ba ta sake ganinsa ba, sai labari da aka kawo mata ya zama riƙaƙƙen ɗan iska a kudun.
"Rahila yanzu ina zamu saka ranmu, maigidanmu fa duk ya yi watsi da mu, yanzu ya gano ɗaya yar ta sa hankalinsa ya na kanta, soyake ya lallaɓa ta dawo hannunsa, gashi daga gani ba ta da kunya. Ba na son Alhaji mu'azzam ya san da ita ya ce ita ma so yake yi, hafsa ta kasa komawa ɗakinta, ta ɓangaren ki babu wani zazzafan malamin ne?"
"Zakiyya da alama ruwa ya ƙare wa ɗan kada. Dan yanzu asirin ba cin mazajen yake yi ba, har su ma yaran. Gaba ɗaya yarana sun ɗaiɗai ce sun tsiyace babu wani mai ɗan dama-dama sai shahida, Abba ya ɓaci da shaye-shaye tuburan"
Zakiyya ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan shaye-shayen ya zama bala'i. Ni fa da depression da shaye-shayen ne su ka haɗu su ka saka hafsa hauka" nan su ka ci gaba da jajanta wa juna.
*** Da daddare Nabila na shirin kwanciyar, take kallon wayarta, ji take yi tamkar ta kira Viper, dan ta san ta gama ƙular da shi, amma ta dake taƙi kiransa.
Washegari da safe ta tura masa message da "Mu haɗu a CID da ƙarfe goma, saura ka ƙi zuwa, wani abin ya biyo baya ka ce an bani cin hanci"
Jujjuya wayarsa ya din ga yi ya na kallon saƙon nata.
Gaba ɗaya su ka haɗu kusan lokaci guda, daga ita har Viper kamar ba su san juna ba, sai basar da juna suke yi.
Babar Abdul sai cika take ta na batsewa, kamar ita aka yi wa laifi, ta na kallon ramma da take ta rufe cikinta kallon banza.
Abdul kuwa satar kallon matarsa yake yi, kallo ɗaya ya yi mata ya tabattar da maganar Nabila na ƙarancin jini da kuma damuwa a tattare da Rahama, gashi duk ta rame ga pimples ƙanana sun feso mata saboda ciki. Tausayinta da ƙaunarta su ka mamaye shi, ya ji ina ma su na tare, ya ciyar da ita da ingantattun abinci masu gina jiki, da kulawa ta musamman.
Ɗaya daga cikin lauyoyin Abdul ya sake gabatar da kansa sannan ya ce "Mu na godiya da amincewa da ku ka yi ku sake zama da mu, domin a duba a ga abin da zai yiwu na mafita da kuma masalaha a kan wannan case".
Mahaifiyar Abdul ta ce "Go direct to the point. Su faɗi ko nawa su ke so, idan ma kuɗin da ya ba su bai ishe su ba, zamu ba su kuɗi, su ƙyale mini ɗa a nema masa lafiya. Dan na gaji da wannan sintirin ba yau babu gobe ana wulaƙanta ni da ni da yarona saboda wata ba ƙauyuyiyar yarinyar"
Cikin ƙunar rai babar ramma ta ce "Uwa uwa ce, babu banbanci tsakanin abin da ki ke ji a kan ɗanki da wanda nake ji a kan 'ya ta. Da mazajenku sun sauke hakkin da Allah ya ɗora musu na al'umma, mussaman na karakara da babu yadda za ayi yaranmu su fito birni aikatau dan nema mana abin da zamu rufa wa kanmu asiri, balle yaranku marasa kirki da tarbiyya su keta musu haddi. Da sai dai can su haɗu da watsatsu irin su su lalace, ba dai da yaranmu ba. Ba komai kuɗi zai iya saya ba, an riga an cuceni, ko a hukunta ɗanki ko ba a hukunta ɗanki ba, ya riga ya cuce ni, ubansa ya kashe mini ɗa, ɗanki ya keta wa ya ta haddi, ya dawo ya nemi nima ya keta mini haddi, ya jaddada mini shi ya yi wa 'ya ta fyaɗe na yi abin da zan yi ya ɗauke ta ya tafi da ita. Ubansa kuma ya ci gaba da bibiyar mu da yinƙurin sakawa a kashe ni, dan na nemi hakkin 'ya ta, uwa ce fa ni sukenan yaran uku, uba ya salwanta mini rayuwar ɗa, ɗanki kuma ya kassara rayuwar 'ya ta, kuma ki na gaya mini nawa zaki bani, ki je can da tsiyarki, ɗa ne na ji ɗan sunna ne, za ta haife shi a kawo muku tsiyarku, amma ba zan bar wurin nan ba sai ya sakar mini 'ya" ɗif kowa ya yi yadda maman ramma take kuka mai ƙarfi, wanda yake fallasa asirin zunzurutun baƙin ciki da takaicin da yake cikin zuciyarta.
Ramma ta ƙanƙame mama, ta na jin tamkar ba ta yi wa kanta adalci ba, ba ta yi wa mahaifiyarta ba.
Nabila ma gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, a hankali Abdul ya saukko daga kan kujerar da yake, ya je gaban babar ramma ya durƙusa a kan gwiwoyinsa sai dai ya kasa ɗaga kansa, kuma ya kasa magana.
A hankali kuma ya ce "Tabbas ahalina sun zama tamkar wata muguwar kibiya, da ta rusa miki dukkanin ginin rayuwarki da ta yaranki. Idan rahama za ta iya tunawa kwanki kaɗan su ka rage na nemeta na rasa, ta farka ta ganni ina kuka cikin dare. Na yi kuka ganin abin da mahaifina ya aikata, abin ya bani tsoro. Sai dai ina neman afuwarku, dan Allah kar a hukunta ni da laifin da babana ya aikata, a hukunta ni da iya wanda na yi, ba zan iya ɗaukar hukuncin laifukansa ba. Dan girman Allah mama ki yi haƙuri, yadda ki ke iƙirarin ke ma uwa ce, ko sau ɗaya ki kalle ni a matsayin ɗanki, idan ya tsinci kansa a halin da nake ciki, ya tuba yayi nadama, watsar da shi za ki yi, ko kuma rungumarsa za ki yi ki ci gaba da yi masa addu'a da fatan shiriya?. Na cutar da ku, kuma na san jarrabawa ce, Allah ya jarabce ni da matsanancin son rahama. Ina nan a kan bakana, a hukunta ni, zan karɓi hukuncin da duk aka yi mini, amma dan Allah kar ku ce na saki rahama wallahi ba zan iya ba. Sannan dan Allah mama kar ki tsani abin da rahama za ta haifa, wallahi ɗan halala ne, kar laifina ya shafe shi, shi ma ya zama lalatacce".
Ya kalli in da Viper ya ke ya sunkuyar da kai ya ce "Duk da ina ganinka tare da mahaifina, ban san iya girman alaƙar da take tsakaninku ba, ban san laifukan da ya aikata maka ba, babu sanya hannuna, ban sani ba. Amma duk da haka kai ma ina baka haƙuri, dan Allah kar ka hukunta ni da laifukansa, dan Allah kar ka ce na saki rahama. Ka san me nake ji, tun da ka taɓa tsintar kanka a makamancin halin da nake ciki, ba ƙarya nake yi ba da nake nanata muku, ina son rahama, dan Allah ku daina cewa na rabu da ita, ko in saketa, idan ciwon na bai kashe ni ba, tsana da tsangwamar da ku ke yi mini zai iya halaka ni"
"Amma Abdul ka yi asara ka bani kunya, yanzu duk a kan mace ka ke wannan abin? Yanzu halin da mahaifinka yake ciki da ɗan uwanka bai sanya ka yi kuka ka kira wa kanka mutuwa ba sai a kan mace?" "Mummy waye silar shigata wannan halin, laifukan waye su ka ƙara yi wa rayuwata ƙawanya, daddy mahaifina ne, ya yi iya ƙoƙarin sa a kaina, amma laifukan da ya aikata sun shafe kimarsa, babu abin da zan iya yi a kan abin da ya aikata face na yi masa addu'a, kuma ya saduda ya nemi yafiyar waɗanda ya zalunta"
Shiru Viper ya yi ya juya ya fice, haushi ne ya kama Nabila, wace irin zuciya da Viper hake ne.
Maman ramma ma shirun tayi, ya riƙe hijjabin rahama, cikin marairaicewa ya ce "Dan Allah ki saka baki rahama, ki ce su yafe mini, kar su rabani da ke ba zan iya ba"
Ban da uban tsaki, babu abin da take yi.
Nabila Viper ta bayan Viper ta biyo ta na mita.
"Haba Vi, abin da ka ke yi ba ka kyautawa, haba dan Allah, ai atleast ko ba zaka amince ba ka tofa wani abun ko" shiru ya yi bai yi magana ba, bai kuma waiwayo ba.
Nabila ta zagaya, sai ta ga ya na share hawaye da handkerchief, ta fuskanci duk lokacin da za ayi maganar abin da ya shafi jauhar, ƙarara yake karaya, wasu lokutan sai ya zubar da hawaye. A kullum ta na jinjina girman ƙaunar da yake yi mata.
"Vi menene kuma? Kukan me ka ke yi"
"Leave me" ya faɗa ya na kawar da kansa gefe.
"Amma atleast yakamata ka ce wani abu ai"
"I say you should leave me, muddin ina kallonsa ina tuna Indabo ne mahaifinsa, ba zan taɓa aminta ayi duk wani abu da zai sanya ya samu sassauci ba. Sai dai ya yi gaskiya na san abin da yake ji, dan har gara shi da ni, ni abin da nake so ɗin ubansa ya yi mini silar rasa shi, ba na fatan ya shiga mawuyacin halin da ni na shiga a silar rashin abin da yake so. Ba kuma zan iya watsa wa mahaifiyar rahama ƙasa a ido ba, dan haka ba zan sake cewa komai ba, abin da mahaufiyarta ta yanke shikenan"
Jikin Nabila ya yi sanyi, hakan ya na nufin ya saukko, ya sassauta abin da ya ƙudurta a kan Abdul, sai dai ba kowa zai gane hakan ba, sai wanda ya san shi ya saba zama da shi.
A hankali ta koma ofishin, ta tarar still maman ramma ba ta ce komai ba, sai kuka da take ta yi.
Nabila ta ce "Ina ga, yakamata a bamu ko 3days ne, mu yanke shawarar ƙarshe"
A haka su ka watse, Abdul ya so yayi magana da ramma amma sai haƙura ya yi.
Bayan Viper ya koma gida, ya din ga tunani, sosai ya ga tsantsar nadama da damuwa a idon Abdul, wanda da mutane mai izza da jin kansa, ga gayu da hutu, amma shi ne duk ya koma haka saboda soyayya. Ɗan mama kuwa an sako shi, kawai sai ganinsu su ka yi ya dawo, liti ya saka shi a gaba, ya na tambayarsa waye ya sako shi?.
Ɗan mama ya ce "Dama ni ai ba laifin komai na yi ba, kawai shaida ne ni dan mugunta aka garƙame ni".
"Ɗan mama ka ji tsoron Allah, ko waɗanda ka ke kai wa munafuncin ne su ka karɓo ka"
"A'a sakina kawai aka yi"
Nabila kuwa Alhaji mu'azzam kankarofi ta kira, ta gaya masa halin da ake ciki a kan lamarin ramma.
Ya ce "To ke ya ki ke gani barrister?"
"Sonake ka yi wa Viper da maman ramma magana, su yadda aje shari'a court kawai, tun da ya yi nadama, ko dan ɗan da yake cikin ramma"
Kankarofi ya ce "Ni a su wa zan yi wa Viper magana, taɓ babar rahaman dai wannan gayen ai sai dai ke ɗin, haka kurum ya din ga yi mini kallon banza ba zai yiwu ba"
"Na sani ya na da zafi, amma mutum ne mai sauƙin kai"
"A'a ban ga alama ba, ke dai ki ji da shi, zan yi wa mahaifiyar rahama magana" suka yi sallama a kan haka.
Alhaji mu'azzam da kansa ya je gida, ya din ga rarrashin maman ramma ya ce "Na san an yi miki laifi, amma yanzu sai mun so za a cigaba da yayata abin da ya sameta. Wasu lokutan sai an jarrabaka ka ke samun ni'ima. Ba dan abin da ya faru ba da babu lallai na sanku, balle na taimaka muku. Da babu lallai garinku su samu albarkacin rahama, ta na son mijinta, idan har ki na son farincikin rahama, ki daure ki yi haƙuri, an san duk wanda aka ce wa ya yi haƙuri an cuce shi ne. Amma abin da zai sanya namiji ya yi wa mace fyaɗe ta dawo ta na sonsa ba ƙarami bane ba, su suka zauna da juna, Allah kaɗai ya san irin zaman da su ka yi ta fara son abin ta. Ki yi haƙuri, ki yi haƙuri ki yafe masa kamar yadda ya nema, yayi nadama na je na ganshi ai, saboda na taimaka muku, matata ƙanwar ubansa yanzu ta bar mini gida, wai na tozarta ɗan uwanta, kuma rahama mai aikinta ce, ba irin bautar da ba ta yi mata ba, kuma ban tsaya muku dan ina son ɗaukar fansa a kan ubansa ba, na tsaya muku ne a matsayina na uba, wanda na haifa nima, ba zan so ayi mini haka ba, amma ki yi haƙuri, ba kuma dole zan yi miki ba ba a yafiya dole, amma ba ki san me Allah zai yi miki ba albarkacin yafiyar ba. Abin alfahari ne a sanadin rahama Allah ya shiryi Abdul" ya daɗe ya na yi mata nasiha mai ratsa zuciya.
Ta amince da a kai ƙarar shari'a Court, dan Abdul ya samu sassauci.
Amma hakan bai yi wa babar Abdul daɗi ba, a gaban Alƙali aka karantawa Abdul laifinsa, a chamber alƙali a ka yi shari'ar, domin privacy ɗin rahama da identity ɗin shi kansa Abdul ɗin.
Ana karanta masa laifin, Abdul ya amsa, Alƙali ya ce a kai masa shi prison, bayan sati uku a dawo ya ci gaba da saurarar ƙarar.
Waro ido Rahama ta yi, ta san Abdul ba zai iya zaman prison ba, babu yadda lauyoyin Abdul ba su yi ba, a kan a bayar da belin Abdul, amma Alƙalin nan ya murtuke ya ce babu wannan.
Babarsa ta ce "Shi ya janyo wa kansa, dama haɗa baki aka yi, aka zo shari'a court, dan a kulle shi a tozarta shi"
Aka taso ƙeyar Abdul, Rahma ta kasa damuwarta da ruɗewa, ya kalli maman ramma ya risunar da kansa.
Ta bakin lauyoyin sa, suka yi wa su Viper godiya, bisa alfarmar da aka yi musu, aka gabatar da shari'ar kotun addinin Muslunci.
***
Nabila na office ɗin ta a zaune, Sumayya ta turo ƙofar ta ce "Suprise"
Nabila ta ce "Ko ma ki yi mini sallama malama"
Sumayya ta ce "Ba zan yi ba"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Ki ci kanki"
Sumayya ta ce "Nabila ana ƙoƙarin hana gudanar da recall election, an kuma sake ɗagawa ba ki ji raina ba"
Nabila ta kwaɓe baki ta ce "Mhmm, ai na san a rina, sai dai idan ba a ƙasar nan muke ba, na ji ana maganar EFCC za su sake shi, amma haryanzu babu wani tartibin bayani a kan laifukan da ake tuhumarsa da shi"
Sumayya ta ce "Za kuwa mu yi raising alarm a social media, lallai ayi mana bayanin meyake gudana ina kuɗin al'umma suke?"
Nabila ta kwashe da dariya ta ce "Ɗansa ya wawushe fiye da rabi, ya yi wa matarsa hidima, Ai Allah ba azzalumin sarki bane, kuma wani ikon Allah yaƙi faɗar ɗansa ne ya wawushi kuɗin"
"Ya za ayi ya faɗa, dama fa ware su aka yi dan yayi campaign, shi kuwa yayi campaign a in da ya dace. Wai ina mutuniyar ki Naja'atu Bunkure ne?"
"Oho mata na daina jin ɗuriyarta, ina nan ina tattara ƙorafe-ƙorafe a kanta, zan kai ma'aikatar Shari'a, she's not suppose to practice law at all, her licensed must be seazed in sha Allah"
Sumayya ta duba wayarta ta ce "Ke ni fa tare nake da baƙo, bari na yi masa magana ya shigo".