Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 99
Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 99: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 99. ***** Bunkure ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda rashin…
4,490 words
***** Bunkure ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda rashin sanin abin yi, dan tun bayan da Nabila ta damƙa mata kundin ƙorafe-ƙorafen da zata kai ma'aikatar Shari'a a kanta, ta rasa yadda zata yi. Gashi ma'aikatar shari'ar duk waɗanda ta sani yanzu ba sa nan, an yi musu canjin wurin aiki, tana ta kasa kunne ta ji ta ina za a nemeta. Tsananin damuwa ya sanya ko baccin kirki ba ta iya yi, sai ta sha tayi mankas tukuna. Duk da abokan aikinta, na ta ƙarfafa mata gwiwa, da nuna mata cewa za ta iya fuskantar ƙalubalen da yake gabanta. Ga mutane duk sun dawo daga rakiyar Foundation ɗin ta, kuɗaɗen da suke tallafawa ƙungiyar domin taimakon mutane, duk sun daina saboda sun gano cewa cuta ce. A dalilin Nabila, mutane da yawa suka samu 'yancin yin magana, tare da sanarwa duniya tallafin da aka nema da sunansu, ko aka basu, ana dawowa a karɓa, wasu kuma ma ba a basu. Sosai social media da gidajen rediyo, maganar bunkure ta yamutsa hazo, ko ina zancen ake yi.
**** Washegari aka sallami Abbu daga asibiti, suka koma gida. Shahida na ɗakinta, tana kwance tana karatun Alqur'ani, Viper ya ƙwanƙwasa mata ƙofa, ta yi masa iznin shiga, ya shiga ya zauna, ya dube ta ya ce "Kin gama idda ko?"
Ta jinjina masa kai, ba tare da ta ɗago ba.
"Magana nake son mu yi, shawara ce, ba dole zan yi miki ba, zaki iya cewa a'a idan abin bai yi miki ba"
Ta jinjina masa kai.
"Na san zaki ji abin wani banbarakwai, amma ba zan yi miki zaɓen tumun dare ba, kuma ba dole zan yi miki ba, ina son Abbu ya haɗa aurenki da Muhsin ne, abokina Walid. Na san zaki yi mamaki, ko ki ji babu daɗi, saboda duba da yanayin mummunar rayuwar da muka yi a baya. Dama kowane mutum tara yake bai cika goma ba, duk wani halin kirki na mutum, sai an tarar da shi da wani hali da ba a so, kuma yanzu muna ta ƙoƙarin gyara ɓarnar da muka yi ne a baya. Ina baki tabbacin Muhsin mutumin kirki ne, kuma zaki ji daɗin zama da shi, ya fi ni nagarta da halacci, da zunzurutun haƙuri. Kema kuma na san mutuniyar kirki ce, a dalilinki ina fatan ya ƙara shiryuwa, amma ina baki tabbacin zaki iya dukan ƙirji a gaba, ki ce kin yi dacen mijin aure. Amma ba dole nake yi miki ba, na tuntuɓe ki ne dai da maganar, kafin nayi masa, idan kuma ba kya son sa babu wani abu shikenan shawara ce".
Sai da Shahida ta ji dummm, tabbas Walid ma tsohon ɗan sara suka ne, kuma bata san shi da wata sana'a ba, amma kwana biyun nan da take zuwa asibiti, suka ɗan zauna tare, akwai nutsuwa da dattaku a tattare da shi, kuma karo na farko kenan, da Al'amin ya yi ƙoƙarin yin wani abu a kan rayuwarta, ta san ba zai cutar da ita ba, dan haka ta numfasa ta ce "To yaya duk yadda ka yi dai-dai ne, in dai ka amince, nima na yarda".
"A'a kar ki yi mini haka, ki gaya mini abin da yake zuciyarki, ko kuma dai na fara turo shi ya nemi yardar ki da kansa, amma magana ta domin Allah bamu iya soyayya irin wadda ku ke so ba, sai dai ki koya masa, kin san mazaje we are always serious" yayi maganar yana ɗan murmushi.
Ita ma murmushin ta yi tana sunkuyar da kai.
Nan ya cigaba da koɗa mata nagartar Walid, da ƙoƙarin da ya din ga yi wa rayuwarsa.
Za ta iya cewa, ba ta taɓa zama sun yi hirar kirki mai tsawo da yayan nata ba sai yau.
Da daddare ya bar gidan, ya tafi can gidan da suke zama, Walid suna ta faɗa da liti, a kan liti yayi musu wanki, ya ce ba zai yi ba, ya saka Viper ya dawo da ɗan mama yayi, tun da ya fi jin maganar sa, dama ɗan mama ne yake yi musu.
Viper ya ce "Rabu da shi mai laya, kai ka kusa shiga daga ciki, a din ga haɗa kayan ka masu datti a bayar wanki, ka bar Liti"
"Wace zata aure shi, bai iya komai ba sai saka aiki, daga kai har shi?"
Viper ya ce "Seriously, Walid Abbu zai baka auren Shahida, abin da ya rage maka kawai ka nemi yardarta" waro ido Walid yayi ya ce "Wane Walid ɗin?"
Liti ya yi shewa ya ce "Sai dai kai maigida, Allah ya ja zamaninka ka daɗe ka yi ƙarko irin na dabino, Allah dai ya saka da alkhairi"
Walid ya ce "Kai fa mahaukaci ne wasu lokutan, uban waye zai bamu aure a haka? Mai zamani ka daina wannan wasan"
Viper ya kwanta ya ce "Ba wasa nake yi ba, da gaske nake, ka nemi soyayyarta kawai, aure zan yi muku, Abbu ma ya san zancen. Kai kuma liti sai dai ka nemo da kanka, tun da na san kai ba gwaninta ake yi maka ba"
Walid ya ce "Dan Allah a daina wannan wasan, wai waye ma zai bani wani aure? Dan Allah ka bari ta samu mutumin kirki ta aura"
Viper ya tashi zaune, ya dafa kafaɗar Walid ya ce "Kai ma mutumin kirki ne, shiyasa ba zan so wata ta samu ba, alhalin ga ƙanwata, ku daidaita kawai sai da safe" yana gama maganar ya kwanta.
Walid ya zauna kamar soko yana rarraba ido, Liti kuwa dariya ya din ga tuntsirawa, saboda har gara Viper ma da Walid, dan shi kamar ma tsoron mata yake ji, shi ko da wasa bai taɓa tare budurwa ba.
Liti ya din ga tsokanarsa, yayi masa banza ya kwanta, hango Shahida yake yi, yarinya nutsatsiya yar gayu, wai kuma ta aure shi shi dai abin bai yi masa tsari ba.
Washegari za su je duba Abbu da yamma, kamar ya fasa zuwa, saboda gaba ɗaya kunya ce ta kama shi.
Kasancewar Viper ya riga su tafiya, ya sanar wa Shahida, su Walid za su zo duba Abbu, dan haka ta shirya, za su yi magana ita da Walid ɗin.
Duk abin nan, rahila ba ta san me ake shiryawa ba.
Sai bayan la'asar, su Walid suka zo, duk yadda yake ɗan sakin jiki da Abbu su yi hira kasa yayi, ya din ga mutsu-mutsu, kamar ya nutse a ƙasa, liti yana ankare da shi, kamar ya yi dariya. Liti ya ce zai je ya dawo, ya fita ya yi nasa wuri, bayan sun yi wa Abbu sallama, a ƙofar gida Viper ya ce "Na yi mata magana, za ta fito ku yi magana, mu haɗe a jungle"
"Dan Allah Viper ka ce da wasa ka ke yi, ni wallahi ban san me zan ce mata ba, wallahi kunya nake ji"
"Malam yakamata ka girma, ka yi mata tatsuniya if you like" zai sake magana, suka yi ido huɗu da Shahida, ta fito cikin doguwar rigar abaya maroon.
Viper ya yi gaba yana murmushi, Walid ya ɗan diririce.
Ta ƙaraso tayi masa sallama ya amsa, ta saci kallonsa, dogo ne shi ma, sai dai bai kai Viper jiki da tsawo ba, kuma yana da haske sosai, sai dai laɓɓansa baƙi ƙirin, idanunsa kuma jajaye, yana da dogon hanci da gemu kaɗan ba mai yawa ba.
"Sannu ya jikin Abbu?"
"Da sauƙi Alhamdilillah"
"Amm na san wataƙila mai zamani ne ya takura miki, idan ba kya so na, ki rabu da shi kawai, Allah ya zaɓa miki miji nagari, rigimarsa ce kawai ta saka ya ce wai zai aura mini ke" yadda duk yake a rikice ne ya sanyata murmushi ta ce "Yaya Muhsin, mu yi addu'a mana, bamu san me Allah ya ɓoye ba, mu nemi zaɓin Allah, in dai nima zaka kula da ni, ka din ga lallaɓa ni kamar yadda ka ke yi masa ai ba wani abu" sunkuyar da kai ya yi yana murmushi, sai dai kamar ya zuba da gudu dan kunya. Bai fi mintuna goma ba, yayi mata sallama.
Da ya koma can gidan da suke, kamar wanda ya aikata zunubi, liti ya saka shi a gaba, ko murmushi yayi, sai ya ce tunanin Shahida yake yi, ya hana shi sakat.
Da daddare Shahida ta kira Viper, ta tambaye shi ya suka je gida. Maimakon ya bata amsa, sai ya miƙa wa Walid wayar.
Tayi masa ya yaje gida, sannan ya ce zai ɗauki lambarta a wurin Viper.
Washegari da sassafe, Viper ya shirya ya fice ya bar su, dan yai zai koma wurin likitan ƙwaƙwalwa, kuma yana son ya ga Nabila.
*** Ƙarfe tara na safe, Nabila ta fito falon madam Halima, hannunta riƙe da jakarta, da court ɗin ta, kawai ta ga Viper a falo, suna magana da Madam.
"Mummy good morning"
"Morning sweetheart, kin fito?"
"Eh, Good morning" tayi maganar tana kallon in da Viper yake, bai amsa ba, ya ci gaba da magana da Madam.
Kitchen ta nufa, kusan mintuna biyar, madam ta tashi ta shiga ɗakinta, Viper ya bi bayan Nabila.
Sai da ta tsorata da ganinsa unexpected.
Wuri-wuri ta yi da ido tana kallonsa.
Ya sauke ajiyar zuciya ya yi ya ce "Abin da ki ka yi mana kina ganin kin kyauta ko? Nayi tafiya mai hatsari, ya na je ya na dawo, bai dame ki ba? Kin yi mini laifi amma ba ki iya bani haƙuri ba, yau zamu koma asibiti you don't even care to call me. And a gabana ki ka bi kankarofi, duk dan ki tura mini takaici".
Tayi shiru ta ɗan kalle shi ta ce "Ba faɗa ka ke yi mini ba, komai ka yi ta hantarata"
Ya ce "Ke ki ke yin abin da zan hantarekin ai. Akwai muhimman batutuwa da yakamata muyi discussing, kawai kina wani fushi mara dalili. Ana ta matsa mini lamba, za ayi posting ɗina wurin aiki, da zarar na kammala aikin da nake yi a kan Indabo, ina son ayi aurenmu dai-dai lokacin da zan tafi aiki"
"Kai da wa?"
"Ni da waye a nan wurin?" Yayi maganar yana tsareta da idanunsa.
"Allah ya baka madadin matarka da ka rasa, ba zan iya aurenka ba Vi, i fulfill my work on you, amma mu bar wannan maganar Please"
Sai da ya nazarceta sannan ya ce "Ƙarya ki ke yi mini da ki ka ce ki na so na kenan?"
Ta ɗan ja da baya, saboda tsoron yadda idanunsa suka fara sauyawa ta ce "Ko ma ya ne, kai ka fara discouraging ɗina, a lokacin da ka yi fatali da tayina, ka ce mini ba wannan maganar, bayan jauhar baka kallon kowace mace. Nima kuma na gamsu da hakan ba zan iya auren mijin 'yar uwata ba. Amma Alhamdilillah na cimma burina a kanka, tun da ka dawo yadda take fata kafin ta mutu".
"Ba kya so na kenan? Ba zaki aure ni ba?" Ta jinjina masa kai, tana kawar da kanta gefe alamar eh.
Juyawa ya yi, ya fara takawa, wayarsa ta fara ringing, ya cirota ya saka a kunnensa ya ce "Na'am"
A razane ya ce "What Walid ɗin? How?"
Ayshercool 08081012143
100 Cike da gigicewa ya ce "Gani nan, kar ka sanar da kowa"
Saboda rikicewa, sai ma ya rasa ina ne hanyar fita, sai daga baya.
Nabila ta ce "Vi menene? Meyafaru?" Bai kulata ba, yana ƙoƙarin fita, Madam Halima ta ce "Au nan ka biyota, na zata tafiya ka yi ai" sai dai yanayin fuskarsa ya nuna mata akwai damuwa.
"Viper menene? Meyake faruwa ne?"
"Walid, gayen nan da muke zuwa da shi, na baro su a gida, ya fita yin refiiling, shi ne bai koma ba, Abdallah ya bi hanya ya tarar da cylinder gas ɗin a gefen hanya, da takalmansa da agogonsa, that means ɗauke shi aka yi" tuni kamanin Viper suka canza, saboda tashin hankali.
Yana ƙoƙarin fita, madam ya ce "Wait Viper, tattara hankalinka ka nutsu, tunani al'amarin nan yake buƙata da nutsuwa, ba gaggawa ba. Yanzu na san Joseph ya ƙaraso, zai fita da Nabila, ya kai ka ku je a tabattar da abin da yake faruwa, sannan ka kira Oga ka sanar masa da halin da ake ciki" ya jinjina kai ya wuce cikin hanzari ƙirjinsa na bugawa da sauri.
Da sauri Nabila ta ce "Bari na bi shi Mummy, kar ya je yayi wani abun, kin san shi da zuciya da wutar ciki"
"Kya ma gama gulmarki ne daughter, Allah ya bayyana shi cikin aminci" ta amsa da Amin.
Kafin ta ƙarasa har ya riga ya shiga mota, sai da ta haɗa da sauri, sannan ta ƙarasa ta shiga baya, kasancewar gaban motar ya shiga.
Tana shiga ta ji Viper yana waya "Liti kar ka matsa daga wurin, gani nan zuwa, kuma kar ka gaya wa kowa, ka kira wayarsa ne?"
"A gida fa ya manta ta a kan window ya fita"
"Shikenan gani nan zuwa"
"Nabila na ta son tayi masa magana, amma ta san a ƙule yake da ita, dan haka ta ja bakinta ta tsuke"
A haka suka isa dai-dai wurin da liti yake, yana ta buge-bugen waya.
Yana zuwa ya tarar da Liti a hanyar shiga rukunin kamfanunnukan da a bayan su gidan nasu yake, bai taɓa komai ba, yadda ya tarar da takalman walid, da cylinder gas da agogonsa a yashe.
Viper ya yi shiru, yana nazartar wurin, Joseph ma fitowa ya yi, suna dudduba wurin, ya kalli Viper cikin broken English ya ce "Oga, da alama sai da aka yi kokowa da shi kafin a tafi da shi"
Su na nan tsaye Viper yana duba wayarsa, sai ga motar Civil defense sun zo wurin, su ka yi wa Liti tambayoyin da yakamata, suka yi investigation a wurin. Su ka yi ta bawa Viper haƙuri, da ƙoƙarin kwantar masa da hankali.
Jiki a sanyaye Nabila ta ce "Ka yi haƙuri, in sha Allah yana cikin ƙoshin lafiya, bari na tafi"
"Ki shiga mota, mu ajiye ki, zan bi bayan civil defense ɗin nan, na ji me ake ciki"
Ta jinjina masa kai, ta shiga mota suka tafi suka ajiyeta a wurin aiki.
"Idan kin kammala, ko za ki je wani wurin, ki kira ni kar ki fita, i don't think you are safe".
Nabila ta ce "Ok shikenan na gode"
Abu kamar wasa, aka shafe kwana biyu, babu Walid babu ɗuriyarsa, hakan ya ƙara ɗaga hankalin Viper fiye da tunani, tun yana ɓoye-ɓoye, har maganar ta fita, sai da ya sanar da Abbu. Duk da ba wata shaƙuwa tsakanin ta da Walid, amma ta san shi da yayanta, kuma yana nuna damuwa da abin da ya shafe su. Sosai hankalinta ya tashi, Abbu kansa da shi ake ta zarya. Alhaji mu'azzam ma sai kwantarwa da Viper hankali yake yi, liti ya fi kowa shiga damuwa, dan kuwa har wata irin muguwar rama yayi, a ƙa'ida shi ne yakamata yaje yayi refiiling ɗin, ya tsaya jan jiki, Walid ya zuciya ya tafi ya yo, tsautsayin ya faɗa masa. Duk in da ake tunanin samun Walid, an duba ba a same shi ba, Liti har wata irin rama yayi. Duk ƙaunar Viper da Abinci, baya gabansa, ba ya iya ci, saboda damuwa da tashin hankali. Gashi yana ta gargaɗin Nabila a kan yawo anyhow, dan ya san tun da aka farmaki Walid, a kowane lokaci za a iya sake kai ma wani na kusa da shi hari.
Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare, yana zaune ya kasa bacci, yana ta tasbihi, yana fatan Allah ya kuɓutar masa da Walid, wayarsa ta fara ringing.
Cikin azama ya ɗaga, ya saka a kunnensa ya yi shiru.
"Ban yi mamakin jin idonka biyu ba, saboda sai da na duba, na duba na tabattar da wanda na kama, shi ne na kusa da zuciyarka, da taɓa shi zai tabattar maka da ina sane da kai, ban manta da kai ba".
"Ina ka kai Walid, kar ka bari sabgar nan ta juye zuwa wani abu daban, ka fito da shi, duk in da ka kai shi"
"Ta daɗe ba ta juye ba, ka manta tare ku ka din ga yi mini aiki a baya, ai ina ganin kamar shi haryanzu ba shi da wani muhimmin tabo, da bangar siyasa tayi masa kamar kai. Ai talaka ba shi da wani amfani, ban da ku yi mana hidima, amma kun dage zaku kai ni ƙasa, zan saki Walid ne, a lokacin da wa'adin zaman Abdul yasar ya ƙare a gidan yari. Sannan zan sake duba abu mai muhimmanci a gareka, na yi masa ɗaurin talala, yana raye amma kamar matacce, kamar yadda ka saka aka ɗaure mini ɗa a ƙasashen waje. Na samu labarin kana aiki a kaina, sai ka ga bayana, gani gaka, ɗan halak ka fasa".
Viper ya ce "Wannan shi ne kuskure na biyu mafi muni da ka aikata Indabo. Ni da kai muke harƙalar nan, kuma batun ɗanka, hukunci aka yi masa dai-dai da abin da yayi. Ina mai gargaɗinka da kakkausar murya ka saki Walid, idan ba haka ba zan razana duniyarka da abin da baka taɓa zata ba, awanni arba'in da takwas kawai ka ke da su, kuma ka fara ƙirgawa daga yanzu" yana gama maganar ya kashe wayar, ya dafe kansa, cike da wata irin nadama da danasanin biye wa Indabo ya din ga aikata ɓarna.
Wato a duniya idan amfaninka ya ƙare kai ba a bakin komai ka ke ba, meyasa zai ɗauki Walid maimakon ya ɗauke shi, tun da da shi yake yi, ba Walid ba.
Da sassafe Viper ya tafi barrack, saboda Nabila, yana tsoron ita ce next target na indabo, tun da tare suke yin komai da ita, sai dai tayi noticing rama da kuma damuwa a tattare da shi.
Tana ta shiri, yana falon madam yana jiranta, gani yane da ya kawar da kai, komai na iya samunta.
"Vi" ya ji ta kira sunansa.
"Ka karya sai mu fita" ya girgiza mata kai bai ce komai ba.
Ta fuskanci damuwa na ƙara saka shi miskilanci da rashin magana.
Nabila ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah ka ci ko kaɗan ne, duk ka yi wani iri"
"In ci Abinci ban san halin da ɗan uwana yake ciki ba? Shi ya ci? Duk a dalilina, shikenan duk wanda ya raɓe ni a haka rayuwarsa za ta ƙare a wahala da tashin hankali, menene laifin Walid ne?"
Cikin rauni ta ce "Na sani, na kuma fahimce ka, amma hakan babu abin da zai canza. Addu'a da ci gaba da jajircewa ce kawai za ta kawo mafita, ka yi haƙuri dan Allah Vi ka saka wani abu a cikinka" ya ƙura mata ido na wani ɗan lokaci, kawai ya tashi tsaye ya ce "Idan kin gama ki same ni a mota" sosai tausayin sa ya mamaye mata zuciya.
Jiki a sanyaye ba tare da ta samu ta yi breakfast ɗin ba, ta bi bayansa.
Da suka kai ta wurin aikin ma, har ta shiga ta ji kamar ana bin ta, ta waiwaya ta ga shi ne ya biyota. Ba ta ce masa komai ba, ta shiga office ɗin ta ya bi bayanta.
Kujerar cikin office ɗin ya samu ya zauna, bai kulata ba, ita ma ba ta ce masa komai ba, ta ci gaba da aikinta, gani yake yi yana kawar da kai, wani abun zai sameta ita ma.
Har ta gama aikinta na ranar yana zaune, sannan Liti ma ya saka an mayar da shi cikin barrack.
Duk yadda ya bi wayar Indabo abu ya gagara, sai taƙi shiga, gashi gani yake yi kamar babu wani ƙoƙari da ake yi a kan neman Walid ɗin.
Kwatsam Nabila na shirye-shiryen tafiya, ya sake jarraba wayar Indabo, cikin sa'a ta shiga kuma ya ɗaga, Viper ya miƙe cikin zafin rai ya ce "A karo na ƙarshe, ina Walid yake?"
"Babu wata barazana da zaka yi mini Viper, sharuɗɗa zan saka maka, wanda dole sai ka bi su. Na farko ka saka wannan yarinyar ta janye ƙorafin da ta shigar a kan Bunkure a ma'aikatar Shari'a, sannan ka tattaro duk wani bincike da ka yi a kaina, na yinƙurin tona mini asiri, da wannan wayar da ka ke amfani da ita ka bani, sai a saki Walid, idan ba haka ba wannan banzar yarinyar ita ce next target ɗina a kanka, sai na saka an wulaƙanta ta, wulaƙanci mafi muni na tagayyara rayuwarta, fiye da yadda ka ke tunani" Viper ya ɗaga kai ya kalli Nabila da take kallonsa, amma ba ta san me ake cewa ba.
Viper ya ce "Saboda abin da nake shiryawa a kanka ne ya sanya ka kashe P.A?"
Indabo ya ce "Eh, ban damu da a in da ka samu labarin hakan ba, iyaka na san ba ka da wata cikakkiyar shaida a kan ni ne kashe shi, duk wanda ya ci amanata, sai na kawar da shi. P.A ya ci amanata ya haɗa kai da kai, domin yana ganin ya zame ya bar ni shi ne zai sanya ka ƙyale shi".
Viper ya sauke numfashi mai zafi, cike da dana sanin, sanin Indabo a rayuwarsa ya ce "Idan kuma ina da shaidar kisan kan da ka yi wa P.A da hannunka fa?"
"Gwargwadon yadda ka ci gaba da zurafafawa, gwargwadon yadda zan ci gaba da hura wutar da ka ke ciki, ba dai kana yi wa kanka iƙirarin ƙarfen cikin wuta ba, idan ba zaka ɗakku da hannu ba, zan ci gaba da iza wutar da ka ke ciki, sai ta kai matakin da zata narka ka"
Viper ya datse laɓɓansa na ƙasa, ya fesar da wani zazzafan numfashi, ya ce "A ina zan kawo maka abin da ka buƙata?"
"Zan turo maka adireshin wurin, kuma ba kana bayarwa za a sake shi ba, sai na ba wa ƙwararru sun tabattar da ingancin abin da ka bayar, kuma a yau ba gobe ba, yarinyar nan ta janye maganar Bunkure"
"Na ji, zan yi abin da ka ce, amma yarjejeniya ɗaya idan ka saɓa, wutar da kake ƙoƙarin narkani da ita, kai zata ƙona" Indabo ya katse kiran.
Viper ya kalli Nabila, ta ce "Vi wai lafiya?"
"Zamu je ma'aikatar shari'a, ki janye ƙorafin da ki ka shigar a kan Naja'atu Bunkure"
A razane Nabila ta ce "Saboda me?"
"Saboda haka na ce" yayi maganar a fusace.
Nabila ta ce "Akwai dalili dole, ka gaya mini, idan ba haka ba zan iya janyewa ba gaskiya, gaba ɗaya wahalata a kan lamarin matar nan na ɓata lokacina, kawai kuma sai na janye?"
"Sai kin janyeta, babu wani bayani da zan yi miki, dolenki ki janye" yayi maganar yana kallon Nabila, yana hasko cikin bala'i da tashin hankalin da zai shiga, idan aka taɓa ta.
****
Goye yake da Jaka a bayansa, a dajin Allah shikaɗai, sai waige-waige yake yi. A kan babura da manyan bindigu, wasu mutane suka ɓullo, suka zagaye shi. "Ka ajiye jakar, ka ɗaga hannayenka sama" wani yayi masa umarni.
Ya ajiye jakar, ya ɗaga hannayensa, ɗaya ya karɓi jakar, ya zazzage, ya dudduba ya ce "Kayan ne"
Wani daga cikinsu ya ce "Za a aika shi ne?"
"A'a kai ba a ce ba, jami'i ne, asirinmu zai iya tonuwa, mu ware kawai".
Suka ja baburansu, suka yi gaba, suna tafiya aka turo masa saƙo.
"Ke je dutsen da yake in da kuke, ka ɗauki gawarsa" kamar mahaukaci, haka Viper ya sake gigicewa, daga in da aka saka shi kai kayan, bai isa in da Walid yake ba, sai bayan awanni uku.
Yana zuwa ya lura da ba a lokacin aka yar da shi a wurin ba, kamar ya kwana a wurin, an ɗaure masa hannu da ƙafafuwa, an tura masa tsumma a baki, an ɗaure wuyansa da wayar cable, ga jikinsa ko ina a farfashe saboda duka. Fuskarsa ta kumbura suntum, duk jini, ƙanan ƙwari sai bin sa suke yi.
Kamar yaro ƙarami, Viper ya fashe da kuka yana kwance Walid, ya kwance wayar da take wuyansa, ya ɗaga shi yana kuka, yana kiran sunansa.
Ya ƙanƙame shi a jikinsa, kawai ya ji zuciyarsa na bugawa, a hankali.
Zumbur ya miƙe, yana ambaton Allah, ya goya shi a bayansa, gani yayi idan ya tsaya buge-bugen waya, zuciyarsa zata daina bugawa, haka ya kwashi tafiya, har rukunin kamfanunnukan nan, ya ce su taimaka masa su kai Walid Asibiti.
Kai tsaye barrack ya tafi da shi, ya kai shi asibitin cikin bariki, babu wani jinkiri aka rufu a kansa, yana da rai bai mutu ba, sai dai babu tabbacin ya tashi.
Duk da Nabila tana cike da ɓacin rai da damuwar sakata janye ƙorafi da yayi, ba tare da ya yi mata bayanin komai ba, amma tana ganin saƙonsa na yana Asibitin cikin barrack tare da Walid, ta tashi tana tsuma, ta saka hijjabi ta fita.
Yanayin da ta ganshi ne ya karya mata gwiwa. Ta ce "Vi ya ake ciki?"
"Yana ciki sai dai babu ya rayu" yayi maganar yana zubar da hawaye.
"Kayi haƙuri vi, ka kwantar da hankalinka, in sha Allah Walid zai tashi da ikon Allah"
Sai ita ta kira su Alhaji mu'azzam, da Liti ta sanar musu an ga Walid.
Babu jimawa wurin ya ɗinke da jama'a.
Hatta Abbu yana wurin, Shahida ma kasa zama tayi, sai da ta biyo Abbun.
Abbu sai shi ya kama hannun liti, yana ta rarrashin sa, gaba ɗaya ya firgice, an tuɓe Walid daga shi sai gajeren wando, duk jikinsa shaidar duka, aka yi dressing ɗin raunukan jikinsa, aka ɗebi jininsa ana ta gwaje-gwaje. Duk wani abu da za a buƙata wurin bincike, sai da suka ɗauka, kafin a taɓa shi.
Ɗaya daga cikin likitocin ya fito, ya ce "Ku kwantar da hankulanku, Alhamdilillah. He's responding to treatment. Vitals ɗin sun dawo normal, in sha Allah muna saka ran ya farka a kowane lokaci. Idan ya farka zamu tura shi sauran gwaje-gwaje.
Sai a lokacin suka ɗan samu nutsuwa.
Cikin dare aka kira Viper wurin ogansa, Ya sha faɗa a kan abin da ya yi ba tare da ya sanar musu ba. Shi dai yayi shiru, dan a halin da yake ciki, babu umarnin wanda zai iya tsayawa saurara, ya sha faɗa duk da yayi bayanin abin da ya faru a yanzu.
Ya numfasa ya ce "Jami'anmu sun tafi, za su dawo da wayar, duk wanda aka kama da wayar ɓatar da shi zamu yi, cin amanar ƙasa da ƙoƙarin tonon asiri ne, duk wanda aka kama da wayar ba jami'inmu ba" Viper dai yayi shiru, domin an ce ya saurari punishment ɗin da za ayi masa.
****
Sai da Walid ya kwana a Asibiti, ya wayi gari, sannan ya motsa ya farka.
Liti ne ya ga ya motsa hannunsa, ya tashi da sauri, ya nufe shi yana zazzare ido yana kiran sunansa.
Walid ya buɗe ido ya kalli Liti, ya yinƙura zai tashi Liti ya ce "Kai kar ka tashi, a asibiti kake"
Ya ɗaga kai yana kallon ɗakin, Viper ya ƙaraso, yana cewa "Mai laya, kalleni ka gane ni?"
Murmushi ya yi ya ce "Na kiyayi mai zamani"