Karfe a wuta complete novel - Chapter 5
Karfe a wuta complete novel Chapter 5: Karfe a wuta complete novel Chapter 5. "Ba laifi na yi masa ba, haƙuri na je ba shi fa, amma ya kore ni a gaban mutane"
4,465 words
"Ba laifi na yi masa ba, haƙuri na je ba shi fa, amma ya kore ni a gaban mutane"
MD yayi murmushi ya ce "Ai ke ɗin ce ba kya ji, ya so ya koya miki aiki yadda yakamata, mussman yadda ki ke da faran-faran da mutane, amma ki ka ƙi ba kya so, idan ya saka ki aiki ki ƙi yi, dole ku din ga faɗa ai"
Nabila ta ce "Na daina fa, so nake na zama ƙwararriya a kan aikina, ko dan farincikin Abbana, ku yi haƙuri"
Ya jinjina kai ya ce "Shikenan, Allah ya sa, ki je ki bashi haƙuri"
Ya ce "Bayan ya kore ni, yauwwa sir dan Allah ka san barrister Naja'atu Bunkure?"
Ya jinjina kai ya ce "Yes, she's famous a tsakanin lauyoyi, har ma da jama'ar gari ma, ai sananniya ce sosai"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Wow ina yin matar nan sosai da sosai, yadda take gudanar da aikinta, ya ƙara jan hankalina a kan aiki, ai mun ganta kotu a lokacin da mu ka je kotu last, ni da barrister Bashir, ƴar gayu da ita"
"Nabila, ke dai ki na son harkar gayu, amma ba gayun ba, ki mayar da hankali sosai a kan aiki, ki yi ƙoƙari ki kamo ta, ko ma ki fi ta".
"In sha Allah, na yi maka wannan alƙawarin but i need your support"
Ya murmusa ya ce "Kin samu, ɗari bisa ɗari, ƴar gidan major"
"Yauwwa to ka bawa barrister Habib haƙuri, zan koma team ɗin sa dan Allah kar ya sake korata, mussaman a gaban mutane"
"To za a bashi in sha Allah"
Ta miƙe tsaye tare da faɗin "Godiya nake" ta fice ta bar office ɗin cikin nishaɗi.
"Bunkure na ki zai zo mini da sauƙi, saura kuma Aminu Viper"
*** Major ya ɗan tsurawa Uwargidan sa mama da ta tattare kwanukan da ya kammala cin abinci.
Ta ɗago su ka haɗa ido, ta ce "Ya dai?"
"Nasir"
"Me yayi?"
"Ki ja masa kunne, hawainiyarsa ta kiyayi ramata, na daɗe da gane in da ya dosa, amma tun da kin daƙile abun, to ya ƙara nesanta kansa da ƴa ta, kar ya kuskura in ji ko in ga wani abu da zai sosa zuciyata, kuma kar ya kuskura ya saka ta fara son shi, tun da ba ki amince ba, balle a jefa ta cikin yanayi mara daɗi".
Cikin rashin fahimta ta ce "Amma major, wani abun ya yi ne?"
"Bai yi komai ba,gugar zana dai nake yi, idan ma yana shirin yin, to ya shiga hankalinsa" cikin mamaki take bin sa da kallo, tabbas idan aka ji major yana magana da kurman baƙi, akwai abun da ya gani, kuma ko me za ayi, ba zai fito yayi bayanin abun da yake nufi ɗin ba.
**** Kamar ɓarawo haka yake zagaye tilon matsakaicin gidan, wanda can nesa da gidan, kamfanunnunka ne, sai gonaki.
Cikin ƙasaita yake tafiyar, yana yi yana duba ƙaramar wayarsa mai madannai.
Kamar korarre, haka wani matashi ya ƙaraso in da yake tsaye.
Ya ɗaga kai ya kalle shi ya ce "Menene labari, yaya aka yi ka fito?" Cak matashin ya tsaya, ya ce "Wai dama ba kai ne ka fito da ni ba?"
"Me zan tambaya idan na san komai?" Yayi maganar a ɗan hasale.
"Wallahi master....
Cikin wata irin razananiyar tsawa ya ce "Kar ka sake kirana da wannan sunan"
Cikin tsuma ya ce "Tuba nake oga, suɓutar baki ce, ban san waye ya fito da ni ba, kawai cewa aka yi na tafi"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Kuma ka tabattar da ka gaya musu sunana, cewar ni ne me kayan?"
"Wallahi na faɗa musu"
Ya jinjina kai ya ce "Shikenan"
Ya ɗaga rigarsa ya zaro wata sharɓeɓiyar wuƙa, ya danƙa masa ya ce "Maza ka fasa cikin gari, unguwarmu, su walid sun tafi yaran Madaki zaku farwa babu sani babu sabo, idan an yi ram da wani daga cikin ku, ku ambaci sunana, ku ce ni ne jagoran aika-aikar, amma ku kiyaye ƙa'idar aikina"
Ɗan mama ya risuna ya ce "Umarninka ne abun biyayya a gare ni, an gama za ayi yadda ka ce" ya soke wuƙar ya juya, ya tafi da sauri yana haɗa hanya..
Cikin ƙaramin gidan ya shiga, ya nufi ɗakin kwanansa, ya kunna fitilar wayarsa, ya kunna ƙwan solar, haske ya gauraye ɗakin.
Ya saka mukulli ya rufe ɗakin, sannan ya zauna yayi shiru tsawon mintuna, daga bisani kuma ya ɗaukko wiwi ya naɗa ta, ya kunna ya fara zuƙa.
Madadin ya ji ƙunci, da zafin da zuciyarsa ke yi masa, yana raguwa, sai ma wani irin baƙin ciki da matsananciyar damuwa da suka kawo masa ziyara.
Wani abu mai tsananin ɗaci yake ƙoƙarin haɗiyewa, amma abu ya gagara.
Ya ɗaga wiwin yana kallonta cike da baƙin ciki da takaici, yayi watsi da ita yana sauke numfashi.
Kamar mahaukaci ya zabura ya buɗe wata akwati, ya ɗaukko kwalaben allura, ya farfasa ya haɗa, ya yi wa kansa, ya nemi wuri ya kwanta.
Bai fi mintuna goma ba, kansa ya fara barazanar tsagewa, ya fara kakari yana rirriƙe kansa.
Duk yadda ya kai ga ƙara yawan doses ɗin abun da yake sha, ba sa ɗaukarsa, su mantar da shi damuwarsa, sai dai su wahalar da shi, shi a yanzu babban fatansa ya samu abun da zai yi amfani da shi, da zai goge masa komai na ƙwaƙwalwarsa ya yi bacci mai nisan gaske.
*** Nabila ce tsaye a kitchen tana ta ciye-ciye, tana yi wa magajiya surutu.
Baba magajiya ta ce "Dan Allah Arfa ki yi mini shiru na ji radiyona, wai ni ya aka yi, ki ka tashi da sassafen nan ma"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Baba magajiya kin gane mai muryar nan kuwa?"
Baba magajiya ta yi dariya ta ce "Sumayya ce mana"
"Ashe za ki gane ta"
"Ka ji ƴa, yau na sanku da ke da ita, da zan kasa gane muryarta"
"Ai in gaya miki baba magajiya, wata mata ce ta takura wa aminiyata, a wurin aiki, da iskanci kala-kala ga sumayya da son aiki, amma matar nan tayi ta taɗiyeta, ni kuwa na ce ta daina saurara mata wallahi,shi ne ma fa ake ba ta karanta rahotanni wasu lokutan, da experience ɗin ta da komai, wata sokuwa ta cuceta, ta hana ta cigaba"
Baba magajiya ta ce "Ohh Arfa, ai mahaƙurci mawadaci, yawan faɗa ba shi da amfani"
Nabila ta ce "A'a fa baba magajiya, ni ma ba faɗa ne da ni ba, wulaƙanci ne ba na so, duk wanda ya wulaƙanta ni, sai mun yi fito na fito da shi".
Baba magajiya ta ce "A dai din ga haƙuri, tun da.... ba ta gama magana ba, Nabila ta yi wani irin tsalle ta ɗauki radiyon, tayi waje da gudu.
Sashin mama ta faɗa, dan ta san tun da Nasir yana gari, lallai zai shiga sashen ta ya karya kafin ya fita.
Aikuwa a sashen ta tarar da shi, yana karyawa, su na hira da mama, da kuma sauda.
Ƙaro volume ɗin radiyon tayi, ta na yi masa nuni da ya saurara.
Rahoto ne a kan rikicin faɗan daba, da ya gudana a cikin ɗaya daga manyan unguwannin kano, wanda tun goma na dare ake rikicin, har ƙarfe sha biyu ana rigimar, ƴan sandan sun yi nasarar cafke wasu daga cikin matasan, in da ɗaya daga wanda aka kama, ya ce Aminu Viper ne ya aka su
Sai da suka kammala ji, Nabila cikin rawar jiki ta ce "Yaya Nasir, ba wannan ne wanda ka ke nema ba?"
Ya jinjina mata kai ya ce "Shi ne"
"Ka yi sauri ka tashi, ka je division ɗin da aka tsare ƴan daban, a baka su ka zurafafa bincike, gidan radiyon su sumayya ne, sai na biya can na sake samo rahoto".
"Ke!" Mama ta daka mata tsawa, har sai da ta ɗan razana.
"Tashi ki bani wuri, yaya ina magana da shi, ba sallama ba gaisuwa babu neman izini, kawai ki zauna ki na surutun banza" Nabila ta yi shiru ba ta ce komai ba.
Sauda ta ce "Dama mama yaushe za ta gaishe ki, tana abu kamar mahaukaciya"
Ta kalle su, ta kalli Nasir da yake wurin, ta haɗiye wani abu ta tashi, za ta fita.
Nasir ya riƙo hannun ta ya tashi ya tsaya, ya ce "Sorry barrister, na gode sosai da wannan gudunmawa, zan je division ɗin, ki samo mini bayani a wurin sumayyan".
Ya kalli mama ya ce "Haba mama, kin san tana gaishe ki, tsananin zumuɗin ta kawo mini labari ne fa ya sa ta manta, thank you Arfa ki shirya ki tafi aiki kar ki makara"
A ƙule mama ta ce "Wai kai har abada ba zaka yi hankali ba, dan ubanka ya zauna yana cewa in ja maka kunne, a kan shishshigin da ka ke yi mata, amma ina magana kana dizagani a gabanta" Nabila ta yi gaba ta fice a fusace, dan idan ta cigaba da tsayuwa, za ta iya aikata abun da zai hana kowa wuni cikin farin ciki.
Ya ce "Ni ɗin kuma mama?"
"Kai ɗin fa, ko ka shiga hankalinka, ko kuma duk abun da ya biyo baya kai ka so".
Sam sai ya ji maganar kamar maman ce, ta shirya kayarta dan ta saba, dan haka ya yi musu sallama ya fice.
A gurguje ta tsaya ta gaisa da Abba, ta fice cikin zumuɗi, gidan radiyon su sumayya ta fara tsayawa.
Sumayya ta yi mamakin ganinta, ta ce "Hajiya lafiya ki ka zo mana wurin aiki da sassafe? Talla ki ka kawo ko cigaya?"
"Ƙaniyarki na kawo" Nabila ta ba ta amsa.
Sumayya ta ce "Ai na san ke ungulu ce, ba kya jewar banza, ya aka yi uwar makara"
Nabila ta ce "Yau da safe kan na fito, na ji baba magajiya na jin program ɗin ku na labaran ƙarfe shida, bayan kin karanto naki, na ji wani rahoto na faɗan ƴan daba, jiya a kano"
Sumayya ta ce "Eh meyafaru?"
"Kin je wurin ne?"
Sumayya ta zaro ido ta ce "In je in yi me?"
"Na ji an ce wai yaran Aminu Viper ne"
Sumayya ta ce "Eh to, ni ma haka na ji"
"Dan Allah ki tashi mu je asibiti, an ce an kama wasu, wasu kuma da aka yi musu miyagun raunuka suna asibitin koyarwa na cikin gari"
Sumayya ta ce "To wai ke duk menene haɗinki da hakan?"
Kamar Nabila za ta yi kuka ta ce "Sumy ban gaya miki ba? Yaya Nasir ne incharge ɗin bincike a kan mutumin nan, kusan kullum sai an faɗi mugun aikinsa, ya tabattar mini da in dai na gano masa in da yake, ko na taimakasa ya gano zan yi suna sosai"
Cikin matsanancin takaici Sumayya ta ce "Tashi ki tafi ko na ɗura miki ashar, ƴar wahala, shi yaya Nasir ɗin ne ya gaya miki haka? Ƴar sanda ce ke? Su ma ya suka ƙarke da su balle ke ki na mace, wallahi ba zan kai kaina ga halaka ba"
"Sumy ki gane, this can all help our career ki zo mu je mana"
"Wallahi ba zan shiga shirgin ƴan daba su kashe ni ba, idan kin yi sunan uban me zai ƙara miki, za a binneki da shaharar ne idan kin mutu?"
Cikin ƙoƙarin son fahimtar da sumayya ta ce "Ba za a binne ni da shahara ba, amma atleast zan samu chances da zan iya fuskantar Naja bunkure"
Wata uwar ashar sumayya ta yi wa Nabila, ta tashi ta ce "Mahaukaciya, ai sai ki yi, ke da bunkuren ƴan wahala"
Nabila ta tashi a fusace, ta ɗauki jakarta ba tare da ta sake cewa sumayya komai ba, ta tashi.
Sumayya ta girgiza kai ta ce "Arfa Allah ya taro ki ya shirye ki, ya yaye miki baƙin taurin kai"
"Tun da kin ce ba zaki je ba, kar ki sake yi mini magana, kuma na gode"
"Eh ba zani ba, haka kurum a kashe ni a banza, mutanen da ba tsoron Allah ne da su ba, mutanen da suke shan ƙwaya tana gaya musu gaibu, su ɓantarani biyu a banza ba da ni ba"
Nabila ta yi mata shiru ta fice.
Nabila ba ta yi tunanin komai ba, ta garzaya asibitin koyarwa, na cikin gari.
Ba ta wani sha wahala ba, saboda tana zuwa, ta tarar jami'an tsaro sun kewaye sashen emergency, ba wanda yake shiga ko ya fita.
Zagaye harabar wurin ta fara yi,tana neman hanyar shiga, da son tabattar da abun da yake faruwa a wurin, ta samu wata cleaner, ko meyafaru a in da ƴan sandan suke.
Nan ta sanar mata da cewa, yaran da aka illata a wurin faɗan daba a daren jiya, aka kawo an hana kowa shiga ko fita.
Nabila ta yi mata godiya, ta yi mata alheri, ta nufi wurin da aka hana shigar da fita..
Ta ƙarasa ta samu ɗaya daga cikin jami'an tsaro suka gaisa, sannan ta nemi shiga, suka ce ba za ta shiga ba.
ID card ta nuna musu, amma ɗaya daga cikin su ya ce "Madam nan ba prison bane, kuma ba police station ba ne ba, nan Asibiti ne, ki bari idan aka kai su can, sai ki je ki yi aikin ki".
Ta kwantar da murya ta ce "Dan Allah yallaɓai, ku bar ni na shiga, Ma'aikaciya ce nima"
"Get out from here" yayi mata tsawa.
Aikuwa ta hasala ta ce "A beg, don't shout at me, aikinka ka ke yi, nima nawa nake son yi, a kan me za ka yi mini tsawa?" Hankalin mutane ya fara dawowa wurin.
Sake hayayyaƙowa Nabila yayi, amma cikin dakiya da taurin kai, take mayar masa da martani.
Da ƙyar aka rarrashi police ɗin, dan cewa yayi sai sun tafi da ita station, wataƙila ma ƴar ƙunar baƙin wake ce, ko ta na da alaƙa da masu laifin.
Nabila ta ce "Ni za ka yi wa sharri, ki in ƙunar baƙin waken zan kai, zan tsaya saurarku ne, da yanzu wani zancen ake ba wannan ba".
Ana ta ƙoƙarin sasanta magana, amma Nabila ta ƙi yin shiru.
Ta ciro wayarta, ta kira Nasir sai huci take yi.
Yana ɗagawa ta ce "Yaya, ya ake ciki ne? Akwai wani labari ne?"
Ya ce "No, wallahi arfa kin ganni, na zagaya station uku a yankin, duk ba a kai su ba, amma wata majiya ta tabattar mini da sakinsu aka yi, just recently"
"Sakin su kuma? Saboda me?"
"Ban sani ba, a kan abun da nake ƙoƙarin yin bincike kenan"
"Ka hanzarta ka taho asibitin cikin gari, akwai waɗanda aka kwantar, police sun hana shiga sun hana fita, an hana kowa shiga, ko da kuwa kusa da ɗakin. Har da ƴan jarida ma an hana su"
Cikin sauri ya ce "Ok shikenan, gani nan in sha Allah, hankalina bai kai kan in zo asibiti ba ma na duba ko akwai abun da zai taimaka mini, amma gani nan stay safe"
Ta amsa da "Ok"
Ta ajiye Wayar a jakarta, ta cigaba da kaiwa tana komowa, ƴan sandan suka saka mata ido, dan kar ta yi wani mummunan yinƙuri, dan ba su san manufarta na dagewa a kan son shiga wurin ba.
Babu tsammanni aka fito da matasan, wasu ɗauke da raunuka, wanda ba za su iya tafiya ba, an turo su a kan gado, an nufi hanyar barin emergency da su.
Nabila ta nufe su cikin sauri, amma ƴan sanda suka tare ta.
Ta kalli ɗaya ta ce "Yallaɓai ina za a kai su? Na ga wasu a mugun yanayi, ya za a bar asibiti da su?"
Babu wanda ya kula Nabila, aka saka matasan a cikin ambulance, har da iyayen wasu daga cikin matasan jami'an tsaron suka hana su bin su, suka rufe ambulance ɗin, su kuma su ka hau ta su motar ta ƴan sanda, suka bar harabar asibitin.
Ƴan jaridar da suka yi ƙoƙarin bin su ma, aka dakatar da su, aka hana su ƙarasawa ma in da motar take har suka tafi.
Tsayawa ta yi kamar wata shashasha, tana mamakin yadda abubuwa suke tafiya, kamar a film.
Motar DSP Nasir ce ta shigo cikin harabar asibitin, yayi parking ya fito, yana ƙoƙarin kiran Nabila a waya,ya tambayi tana ina.
Da sauri ta ƙarasa in da yake, tana kallonsa, amma ta kasa magana.
Ya ce "Yaya dai? A wane ɓangaren suke, kin samu ganin na su kuwa?"
Nan ta kwashe duk abun da ya faru, ta gaya masa.
Cikin asibitin ya shiga, tana biye da shi, ya tambayi office ɗin incharge na A&E ɗin, ya gabatar masa da kansa, tare da yi masa tambayoyi, a kan dalilin da ya sa, aka sallami mutane da raunuka a jikinsu. Amma ya tabbattar masa da cewa, babu wanda yayi musu wani cikakken bayani, kawai ƴan sanda sun kawo musu yaran jina-jina tun a daren jiya, sun ba su kulawar da ta dace, daga bisani ƴan sandan suka ce asibiti za su canza musu, aka tafi da su.
Nabila ta yi shiru, sannan ta ce "Akwai wata a ƙasa yaya Nasir, ko waye wannan Aminun, ya na da wanda su ke sponsiring ɗin sa. Shi an kasa kama shi, amma ya na saka yaran mutane ta'addanci, you need to put more effort, and i will hundred percent support you, everyone is equal before the law, dole a nemo shi a hukunta shi"
Ayshercool 08081012143 [8/29, 8:34 PM] Halimatu A/Rahman Sadeeya: *ƘARFE A WUTA*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
6
Nasir ya ce "Sannu da ƙoƙari arfanmu, amma ki daina saka kanki a risk kin ji ko? Zan cigaba da ƙoƙarina in sha Allah sai na yi sanadin kawo ƙarshen ta'addanci da harkar daba a garin nan, domin kuwa yana ci mini tuwo a ƙwarya nima, but for now mu je na kai ki wurin aikinki"
Nabila ta ce "DSP, dan Allah idan ka gano wani abu na rashin gaskiya, ko waye yake da hannu a ciki, ka tona masa asiri. Dan ina ga sumy zan yi wa magana, su faɗi abun da ya faru a gidan rediyo, an saki waɗanda aka kama, kuma wanda aka ji wa rauni ma, an hana kowa zuwa wurinsu, daga bisani kuma jami'an tsaro sun kwashe su daga asibiti, babu wanda ya san in da aka kai su, wannan wane irin abu ne?" tayi maganar cikin haƙiƙancewa.
Yayi murmushi ya ce "Kar ki soma, ki na wasa da hukuma arfa, yanzu sai ki kwana a ciki ke, yanzu dai mu je mota" haka ya tasa ta a gaba zuwa mota, suna tafe tana mita.
"Wallahi yaya na fara sarewa da lamarin ƙasar nan, anya kuwa gyaran ake so ayi da gaske, ta yaya za ace an gagara kama mutum ɗaya? Ana yekuwar ana nemansa, amma kuma ana kare laifukan da yake aikatawa, ni na kasa gane kan wannan lamarin. Ni fa muddin na gano wani abu na rashin gaskiya, sai na yi magana"
"No Arfa, ba huruminki bane ba, ba kuma aikinki ba ne ba, kar ki kuskura ki saka kanki a hatsari, ƴa mace ce ke lamarin ƙasar nan ya wuce tunaninki, ba abu ne mai sauƙi kamar yadda ki ke hangensa ba"
Ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ce "Yaya garin nan yana kan gaba a garuruwan da ake ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, duk al'ummar da matasanta suka lalace da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi ba ta da gobe mai kyau, matasanmu su ne tushen al'umma mai kyau"
Nasir ya ce "Na fuskanci abun da ki ke nufi, but is still not your field"
Tayi shiru ta mayar da hankalinta kan titi, tana ta tufka da warwara a zuciyarta.
Ko da ya kai ta wurin aiki, ta sauka suka yi sallama, ta shiga tana shiga office ɗin ta, sumayya ta fara kira.
Sumayya ta ɗaga ta ce "Kin gama fushin ne?"
"Ke ware ba wannan ba, matsoraciya da ba ki je ba ni na je, na samo labari, ina ga bayyana labarin ka iya janyo hankalin manya a cikin lamarin"
Sumayy ta gyara zama ta ce "Labarin me?" Nabila ta gaya mata komai, yadda yaran da aka kama suka yi ɓatan dabo, da yadda aka fice da na asibiti ba tare da sanin ina aka kai su ba.
Sumayya ta ce "Nabila lallai wannan magana ce babba, bari zan yi magana da MD na ji mai zai ce, gaskiya yakamata a zurfafa bincike a kan lamarin nan".
Cikin zaƙuwa ta ce "Dan Allah sumayya ki ƙoƙarta, ayi a sanar, a ji mai hukuma za ta ce a kan haka, ko kin san shi kansa Aminu Viper ana zargin ko dai guduwa yayi daga gidan yari, ko kuma sakinsa aka yi ba bisa ƙa'ida ba, shiyasa ake tsananta nemansa yanzu"
"Ke ya aka yi ki ka sani?"
"Yaya ne ya gaya mini, akwai lauje cikin naɗi a lamuran mutumin, mutum kamar wani sheɗani".
Sumayya ta yi shiru sannan ta ce "Bari, yadda mu ka yi da su zan gaya miki, amma maganar nan ta ɗauki hankalina sosai"
"To shikenan, ina saurarenki, yadda ake ciki, ki sanar mini" suka yi sallama.
Haka kurum zuciyar Nabila ta cigaba da azalzalar ta a kan lallai tana son sanin wanene wannan Aminun, akwai yiwuwar ta samu gagarumar nasara idan aka ce da saka hannunta wurin kama shi, shahararta ita zai ba ta damar yin gaba da gaba da Naja'atu Bunkure.
Sai kuma ta tambayi kanta, for the first place, laifin me ya yi aka kai shi prison, har ake tunanin ya fita ba bisa ƙa'ida ba?.
"Akwai ayar tambaya a kan abubuwa da dama" ta yi maganar a fili. *** Ƙurawa wayar gabansa ido yayi, yadda take ta vibration kamar ta tashi, a wannan karon ma private number ce, lambar da ko ta halin ƙaƙa yake fatan ganin ko waye mai ita ya bayyana a gare shi.
Ɗan mama da ke kusa da shi ne, ya ɗaga wayar ya sanyata a hansfree, ya tura masa gaban sa.
Daga cikin wayar aka ce "Manya gatan wasa, ko ka tsorata ne ya sanya ka gagara ɗaukar wayata?"
Yayi shiru bai ce komai ba.
"Idan za ka kwana dubu kana ɓarna, zan kwana dubu ina goge ta, ina ɓatar da sahunka. Ka na ta cigaba da aikata ɓarna, saboda kana son lallai sai ka san waye ni ko?"
"Wanene kai?" Yayi maganar a ɗan hasale.
Mutumin yayi murmushi ya ce "Mutum, mai zuciya cike da muradai kamar ka. Ƴan kwanakin nan ka fi mayar da hankali a kan sanin wanene ni, fiye da abun da yake damun zuciyarka. Ka bi a hankali kar garin kallon ruwa kwaɗo ya yi maka ƙafa, kar ka saki reshe ka kama ganye, ya kai wannan maciji mai hatsarin gaske"
Al-amin ya numfasa ya ce "Ni ba karen farauta bane ba, da za ka din ga wasa da ni, tamkar ɗan kwiwiyon da ka raina, ka yi a hankali da ni, ƙarfe nake cikin wuta, na fi ƙarfin ɗauka da hannu"
Ya sake murmusawa ya ce "Ka huta mutumina, ka samu abun da zai ɗebe maka kewa, ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, ba za su taɓa rabaka da damuwa ba, matuƙar ba ka yi abun da zuciyarka ke gaya maka ba, haryanzu ka na da sauran ƙuruciyarka, zaka iya amfanar da al'ummarka"
Kafin Aminu yayi magana, mutumin ya katse wayar.
"Amma Yallaɓai, kana ganin wannan abun da muke yi shi ne dai-dai? Akwai abubuwa da yawa da yakamata ace mun mayar da hankali a kai, ba bawa ɗan daba kariya ba"
Ya ajiye jaridar hannunsa ya ce "Kalle ni da kyau, ba na abun da babu manufa a kansa, dan haka kawai ka saka ido"
Waya ce ta fara ringing, ya ɗaga sannan ya miƙo masa.
Ya karɓi wayar tare da yin sallama.
"Wa'alaikum Salam, barka dai ya ƙoƙari?"
"Alhamdilillah sir, an yi clearing matsalar jiya, duk da an kusa samun akasi, yaron ba ya ji ko kaɗan, idan aka cigaba da tafiya a haka, kar asirinmu ya tonu fa, dan hakan tamkar yi wa doka karan tsaye ne, mu na saɓa ƙa'idar aiki"
Yayi murmushi ya ce "Kar ka damu, doka ce ta fara yi wa yaron karan tsaye, shiyasa nake amfani da dokar, wurin bi da komai"
"Haka ne sir, amma fa police suna neman shi ne ruwa a jallo, mu kuma muna kare shi, muna taka doka da yawa"
"ASC, ko sun kama Al'amin, ba zasu bari doka ta yi aiki a kansa yadda yakamata ba, za su bar shi da masu son zuciya ne, su yi abun da suka ga dama da shi, ba wai hukumar ce kawai take nemansa ba, akwai lauje cikin naɗi ne a neman da ake yi masa"
ASC ya numfasa ya ce "Shikenan, amma laifukansa sun yi yawa, duk wani ta'addanci da za'ayi a garin nan sai ka ji yaransa ne, slide mistake za'a iya kama shi, duk da wani abun kuma idan muka bincika, sai mu tarar ba shi ɗin ba ne ba"
"Haka ne, amma idan an kama shi ma, sunana na ko naka, babu wanda zai fito, haryanzu bai san ko ni waye ba, kuma ba zan bari ya sani ba, kuma yana aikata wasu laifuka ne dan ya tilasta na ƙyale shi, ko kuma na bayyana kai na a gare shi, amma ka rabu da shi, komai cikin tsari nake yin sa, ka bar police su cigaba da neman sa, hukumarka kuma ta cigaba da aikinta, kamar yadda na ce maka"
Ya amsa da "Shikenan sir, am always loyal to you, na gode"
"Yauwwa ASC, duk halin da ake ciki dai, ina buƙatar ka sanar da ni"
"No problem, sai an jima" bayan sun yi sallama, yayi wata irin dariya, da shikaɗai ya san ma'anarta ya ce "Wannan shi ne jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya" yayi maganar yana kallon yaronsa da yake tsaye yana kallon sa.
Ya ce "Lallai, amma zan so in ji wani irin shiri ne haka ka ke yi sir"
"Za ka gani a aikace, kai dai ka cigaba da biyayya ga abun da duk na umarce ka, nima zan yi amfani da ƙarfin iko da kujerata, na yi abun da ya dace".
"Ok sir, in sha Allah".
*** Misalin ƙarfe takwas na dare, wasu daga cikin manya na ƙungiyar ƙato da gora na unguwar suka tattaru suka zauna meeting a cikin ɗan madaidaicin office ɗin su. Duba da abun da ya faru, na faɗan daba da aka yi da yaran Aminu da na Madaki a waccan unguwa, sanin ya na shigowa unguwar lokaci zuwa lokaci, sannan kuma akwai yaransa a unguwar, ya sanya su zaman yin meeting, dan ƙara ƙarfafa tsaro a cikin unguwar su, kar su gama da can su dawo nan.
Suna tsaka da tattaunawar, wasu zaratan matasa suka yi sallama, suka amsa suna bin su da kallo.
Suka shiga cikin office ɗin, suka kewaye su, duk suka tsaya suna kallon su. A hankali ya sauke face mask ɗin fuskarsa, a take suka shaida shi.