Karfe a wuta complete novel - Chapter 7
Karfe a wuta complete novel Chapter 7: Karfe a wuta complete novel Chapter 7. Madaki ya karta wuƙa a ƙasa, ya kalli tarin matasan da sun fi ashirin a…
4,467 words
Madaki ya karta wuƙa a ƙasa, ya kalli tarin matasan da sun fi ashirin a gabansa ya ce "Babu rangwame ko sassauci, babu mace babu namiji, ko babba yaro ko tsoho, duk wanda aka samu idan aka shiga operation ɗin nan a farmasa, ayi ɓarna ayi ta'adi a ɗauki fansar abun da Aminu yayi mana, jini ya din ga gudana ko ta ina, duk shagon wanda aka samu a fasa ku kwashi ganima, na yarje muku. Haka zalika duk wanda ya gano in da Viper yake, muddin ya kawo mini shi, a mace ko a raye, akwai tukuici mai tsoka"
Suka fara shewa cike da maye, ɗaya daga cikin su ya ce "Aminu fa ƙarfe ne a wuta, duk wannan shewar kama shi ba abu ne mai sauƙi ba, da mai sauƙi ne na san da ka riga mu kama shi"
Madaki ya ce "Rufe mini baki, ko na yi gunduwa-gunduwa da namanka, dole ne a kama shi, kai gobe duk wanda aka gani daga tsallaken unguwar su, ya shigo unguwar nan ma a sara mini shi kawai, a ɗauki fansa mafi muni na abun da ya yi mana, zan ga da ni da shi, waye zai sarara waye gaba da wani"
Cikin haɗa baki suka dinga faɗin "An gama oga, gobe akwai ƙaramin yaƙi"
misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe, a sannu take tafiya a cikin unguwar, tana duba kwatancen da barrister Habib ya tura mata.
Kasa ganewa tayi, ta tsaya a wurin wani mai kanti, ta sayi ruwa ta sha, kuma tambaye shi.
Tana tsaye tana duba wayarta a cikin shagon provision ɗin, wani matashi ya shigo, suka gaisa da mai kantin ya ce "Bani ƙulli biyu da ruwa uku"
Mai kantin ya ce "Amma ka san ina binka sauran kuɗi ko?"
"Zan biyaka, wannan yawa ne, ka bani na ware mana, caji zan yi kaina gaba ɗaya babu network,aljihuna kuma yayi gobara"
"Ba zan bayar ba" mai shagon yayi maganar yana miƙawa Nabila ruwan roba.
Nabila ta din ga satar kallon matashin, yadda bakinsa ya karkace saboda shaye-shaye take kallo, laɓɓansa duk sun zazzago.
Tayi gyaran murya ta ce "Ɗan uwa ka bashi mana, tun da ya haɗaka da Allah, in sha Allah zai kawo maka, tun da ya yi alƙawari"
"Rabu da shi, ba ya biyan bashi"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Nawa ne kuɗin nasa?"
Mai kantin ya ce "Dubu biyu nake bin sa"
Ta yi murmushi, tare da ciro kuɗi a jakarta ta ce "Dubu biyu ai babu yawa, Ga dubu uku, na biya masa kuɗin da ka ke bin sa, ka bashi wani bashin, ni kuma ka ɗauki kuɗin sayayyata"
Matashin ya kalleta ya ce "Sai kin yi babbar yaya, Allah ya ƙara arziki"
Ta amsa da "Amin ɗan uwa na gode sosai".
Wani abu ta ga an bashi a nannaɗe a leda, da ruwa ya sake yi mata godiya, ya fice. Yana fita ta ce "Malam dan Allah menene wannan ya saya?"
Mutumin yayi murmushi ya ce "Ƙanwata wiwi ce" waro ido ta yi ta ce "Wiwi kuma, ka ke sayarwa? Amma na ga kai kamar ba ka sha ko?"
"Ki yi ƙasa da muryarki mana, ya zamu yi sana'a ce, ni ba abun da nake sha. ga canjinki"
Cikin mamaki ta ce "Meyasa ka ke sayar da abun da ba ka sha?"
"Kar ki tsananta bincike malama" yayi maganar yana haɗe rai. Ta jinjina kai ta ce "To Allah ya taimaka"
Fitowa ta yi daga shagon, ta hangi matashin yayi nisa, ta rufa masa baya ta bishi da sauri.
"Bawan Allah ɗan tsaya dan Allah" ta ƙarasa tana haki.
Ya tsaya yana kallonta ya ce "Ya dai?"
"Abu zan tambaye ka, amma kafin nan ka san abun da ka saya ɗin nan, yana da illa ga lafiyarka?"
Tsayawa yayi yana kallon ta, tayi saurin cewa "Dan Allah taimako nake nema, wani gida nake nema, amma na kasa gane layin, ko zaka taimaka mini?"
"Ina ne?"
Ta gaya masa ya ce "Na san gidan, amma ba hanyar ki ka biyo ba nan"
"Dan Allah kwatanta mini"
"Mu je na kai ki bakin layin"
Ta ce "Yauwa ɗan uwa, dan Allah mu yi wata magana mana, ka san wani mutum Aminu Viper?" Wani irin burki ya ci yana kallonta.
"Yi haƙuri idan na ɓata maka rai, ɗan uwana ne shi, tun da Allah ya sa ya bar gidan yari, bamu sake ganinsa ba, kuma na ji an ce yaransa sun tayar da tarzoma a unguwar nan a satin nan, dan har asibitin da aka kai waɗanda aka yi wa rauni na je, na zaci zan ganshi, amma ban tarar da shi ba"
Ya ware mata jajayen idanunsa ya ce "Ki ka ce ɗan uwanki ne?"
Cikin ƙarfin hali ta ce "Eh, ina da alaƙa da shi"
Ya ce "Na san shi, na kuma san in da yake"
Da sauri ta ce "Dan Allah ka taimaka mini a ina zan ganshi?"
Ya ƙare mata kallo ya ce, idan kin tashi, ki tambayi ina ne layin iraƙi a unguwar nan, idan ki ka je akwai wata babbar bishiya zaki ga wasu a zazzaune a wurin, ki tambaye su, za su nuna miki shi.
Cikin tsananin farin ciki, ta din ga yi masa addu'a. Amma fa sai dai ta kasa tantance irin kallon da yake yi mata, hakan bai dame ta ba.
Har ƙofar gidan matar ya rakata, ta kuma yi masa godiya, ta ciro kuɗi ta bashi, sannan ta shiga gidan matar.
Matar ta karɓi Nabila hannu bibbiyu, bayan da Nabilan ta yi mata bayanin barrister Habib ne ya turo ta.
Ta bawa Nabila duk wani information da take buƙata, tana gama abun da take yi ta tashi ta ce tafiya za ta yi.
Babu yadda matar ba ta yi da ita ba, a kan ta zauna ta ci abinci ta yi salla, amma taƙi, ta tashi ta tafi.
Babu tunanin komai, tana fita, ta tambayi wasu yara, ina ne layin iraƙi?.
Duk sai da suka kalleta, ganin tana mace tana tambayar wannan layin da ƴan daba suka mayar mallakinsu, abunka da yara, babu tunanin komai suka sakata a hanya, ta yi musu godiya ta nufi kwatancen.
Tana ta addu'a Allah ya sanya ta dace, duk tana da burin cikar nata muardin, amma za ta yi farinciki sosai idan aka ce Nasir ne yayi nasarar kama Aminu, koba komai likkafarsa za ta sake ɗagawa, ta nufi layin ba tare da ta san idan ta ganshin me za ta ce masa ba.
Layin shiru babu kowa, babu gina-ginan kirki, sai kangwaye, sai da ta je tsakiyar layin, ta hango wata ƙatuwar bishiya, da mutane.
Kamar ba mace ba, babu razani ko fargaba ta tunkari bishiyar.
Gaba ɗaya suka zuba mata ido, har ta ƙaraso.
Wiwi kawai suke busawa, ta ɗan tsaya nesa kaɗan da su, saboda hayaƙi.
"Ina wuninku"
Suka amsa mata da lafiya ƙalau, suna mamakin ganin mace a wannan chamber.
"Dan Allah tambaya nake yi, wani nake nema, aka yi mini kwatancen nan aka ce zan sameshi".
Ɗaya daga cikin su ya ce "Waye shi?"
Ta ce "Amm, sunansa Al'amin, amma ana ce masa Aminu Viper, tun da ya fito daga prison ba mu sake ganinsa ba"
Ɗaya ne ya miƙe tsaye ya ce "Ke, ba ki da hankali, a dabar madaki ki ke naman wannan ɗan iskan? Kai kan taba, sako su mass su rakata, tun kan oga ya zo ya saka ayi gunduwa-gunduwa da namanta"
Sai yanzu ta fuskanci shigo-shigo babu zurfi wanda ya yi mata kwatancen ya yi mata.
Cikin sauri ɗaya ya ce "Meyasa za'a bari ta tafi? Bayan ka san yau zamu fasa ɗaukar fansa, ta kanta ya kamata mu fara" yayi maganar yana ƙoƙarin zare makami.
Sai dai tuni suka sako wa Nabila wasu irin murguza-murguzan karnuka, masu kama da zakuna.
Cikin ihu ta kwasa da gudun tsiya, tana kururwar neman agaji, saboda yadda take ganin kamar karnukan za su cinyeta ɗanya, sai dai gudun da suke yi ya wuce hankali, ga takalminta mai tsini ne sosai, dan haka suka kusa cimma ta.
Babu tsammani ta faɗi, saboda yadda numfashinta ya fara sama-sama. Ayshercool. 08081012143 [7/22, 1:49 PM] null: *ƘARFE A WUTA*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
P8
Ta saka hannu, ta kare kanta, tana jiran su hauta da cizo.
Wani irin fito ya yi wa karnukan, suka juya suka koma da gudu in da yake.
Matashin nan ne na ɗazu, da ta biyawa bashi, ya kalleta ya ce "Kin san meyasa na taimake ki?"
Bai jira amsar da za ta bashi ba ya ce "Ba na tunanin Aminu yana da wata ƴar uwa mace, dan haka ƙarya ki ke yi, akwai wata manufa a ranki da yasa ki ke nemansa. Sannan ya taɓa yi mini alfarma a lokacin da ya samu damar da zai kashe ni, kuma kin kyautata mini, alhalin baki sanni ba. Ɗan daba ba mahaukaci bane ba, shaye-shaye ne yake ruɗa mana tunani. Wannan shi ne kaɗan daga abun da ka iya samunki, idan ki ka cigaba da neman sa, ko bibiyarsa, wannan dabar babu abun da suke buri da fata, sama da su riga ƴan sanda kama aminu, mace ce ke ki kiyaye kanki, tashi maza ki tafi gasu can tahowa, idan suka cimmiki babu lallai na iya hana su illata ki"
Da ƙyar ta tashi, ta yi gaba da sauri, tana cigaba da haki, adaidaita sahu ta hau, ta yi masa kwatancen in da zai kai ta.
Kasancewar mai rabon shan duka, baya jin bari, suna tafe tana sauke numfashi, tana tunanin son sanin su kuma waɗan nan me yayi musu suke son su riga ƴan sanda kama shi, suna ƴan uwansa ƴan daba.
"Ko wani ya kashe musu?" Ta tambayi kanta.
"Yayi kisan kai, kuma a sake shi? Aikuwa sai na ga ƙwal uwar daka" ta furta a hankali.
Ta so ta gaya wa Nasir, abun da ya faru yau, amma ta san tsaf zai ce zai zaneta, saboda kasadar da ta yi, dan haka ta bar wa ranta cewa sai ta samu wata gagarumar nasara, sannan za ta sanar da shi.
Ko sumayya ma ba ta gaya wa ba, tayi shiru da bakinta, sai dai faɗuwar da tayi, duk ta goge gwiwa.
Haka kurum tausayi, da tunanin makomar rayuwar matasan da ta gani, a harkar daba da shaye-shayen nan, ya dami zuciyarta ta rasa abun da yake yi mata daɗi, tana matuƙar son sanin me suke ji a cikin kayan shaye-shaye? Tabbas da ita wata ce, sai ta taimakawa rayuwar su, ko a mutum goma, idan biyu suka shiryu ai an rage.
Kamar wadda ta sha kayan maye, haka yau tayi bacci da wuri, gudun da tayi jikinta duk ciwo yake yi mata, ga numfashi sai wahala yake ba ta.
A wani ɗaki ta ganta, mai duhu sai haske kaɗan a ciki, ga karnuka duk a cikin ɗakin, sai haushi suke yi mata, an ɗaure su da sarƙa. Ihu take yi tana neman agaji, amma babu wanda ya san tana yi.
Can sai ga wani mutum ya shigo, dogo sosai, mai cikar halitta, ba ta ganin fuskarsa saboda duhu, ya shigo ɗakin bai ce mata uffan ba, ya danƙo hannunta ya biyo tsakanin karnukan ya fito da ita daga ɗakin, ya ciro wuƙa zai caka mata a ciki.
Wani uban ihu ta saki, tana kiran sunan Allah, da na Abba da Nasir.
Tana buɗe ido, ta ga Abba a kanta, da Nasir, da su walida har da Anty da baba magajiya, ana ta tofa mata addu'a.
Kallonsu take yi ɗaya bayan ɗaya, ta ce "Abba ya na ganku a nan? Meyafaru?"
Nasir ya ce "Sannu"
Abba ya ce "Arfa ba kya addu'a ko?"
Ta girgiza kai ta ce "Ina yi Abba"
"A'a ba kya yi, da kina addu'a babu yadda za ayi, ki kwanta kina yi mana ihu da safiyar nan, shiyasa nake hanaki wannan shegen fentin da bulbula turare a jikinki, dole sheɗanu su yi ayari, su yi ta binki"
Nasir ya ce "Dan Abba ka yi haƙuri, haryanzu a tsorace take ma, a bari ta dawo hayyacinta gaba ɗaya, sannu Arfat, ki ɗauro alwala ki zo ki ɗauki Alqur'ani ki karanta".
Abba ya miƙe ya ce "Aishikenan, zan yi waya da Barrister, su baki day off, ki samu ki huta"
Nabila ta yi shiru tana rarraba ido, ta san lafiyarta ƙalau, tsabar tsorata ne da tayi. Tayi shiru ba ta faɗi abun da ya faru ba, suka din ga yi mata sannu.
*** YALOKO ƘARAMAR HUKUMAR UNGOGGO
Matashiyar yarinya ce, wadda dudu shekarunta ba su fi goma sha huɗu ba, take ta iza wuta a cikin murhu, gefe ga garin tuwo a cikin ƙwarya.
Yaro ne ya yi sallama, ta ɗaga kai ta amsa masa.
Ya kalleta ya ce "Ramma ki zo ana sallama"
Ta ɗan waro manyan idanunta ta ce "In ji wa? Ko Habu ne?"
"A'a, wani ne da mota"
Ta miƙe tsaye ta ce "To mota kuma, ina zuwa?"
Daga tsakar gidan ta ɗan ɗaga murya ta ce "Mama, wai ana nemana a waje, bari na duba waye, ruwan ya kusa tafasa"
Daga cikin ɗaki matar ta amsa mata da "To ramma, hanzarta ki dawo, ina son zan fita ne"
Ramma ta amsa da "to" ta ɗauki hijjabinta ta saka ta fice waje.
Mintuna goma sha biyu ta dawo, jiki a sanyaye.
Mamanta ta kalleta ta ce "Menene?"
"Mama daga Kano ne, wai Anty mai jidda ce gidan da nake aiki, ta yi waya wai azo a ɗauke ni a mayar da ni, a satin nan za su dawo"
Matar tayi sak ta ce "Da wuri haka, ba cewa aka yi sai bayan wata guda zaki koma ba?"
Ramma ta ja ta tsaya ta ce "Jikina duk yayi sanyi, wai yanzu-yanzu zamu tafi"
"To shikenan ai babu wani abu, ki yi haƙuri kin ji ramma, ni kaina ba a son raina ki ke barin gabana ba, da Allah ya sa mun tara kuɗin kayan gado, shikenan sai ki dawo ki yi auren ki. Maza mu je na tayaki haɗa kayan"
Cikin abun da bai fi mintuna arba'in ba, suka haɗa kayan, suka yi sallama ramma ta bi direba zuwa gidan aikinta da yake Kano.
Yana zaune ya zuba musu ido, suna haɗa masa tea, Walid ya zuba ƙwayoyi a cikin kofin, sannan ya zuba shayin.
"Ƙara wannan ba zasu ɗauke ni ba"
Walid ya ce "Amma boss, kai fa ka ke hanamu sha a baya, tayi yawa wallahi".
"Ka ƙara mini na ce" yayi maganar a hasale.
Ya ƙara masa ƙwayoyin yana kallonsa, saboda ƙwayar da suke yi wa laƙabi da raina kama, a baya sam baya shan irinta, saboda yadda take bugarwa, wasu lokutan rabi suke ɓallawa su sha, amma ya ce a saka masa kusan biyar yanzu.
Ya ɗauki kofin ya kai bakinsa zai fara sha, Walid ya ce "Yau fa madaki za su je ɗaukar fansa cikin unguwa, daga majiya mai ƙarfi na ji zancen, daga jiya zuwa yau ya ce idan ɗan arearmu ya shiga ta su, a aika shi kawai"
Ya cigaba da girgiza kofin ba tare da ya yi magana ba, ya sake yinƙunrin kai kofin bakinsa, walid ya sake cewa "Wata ta je nemanka a arear, aka kaita dabar madaki, Allah ne ya yi da kwananta a gaba, da kasheta za su yi"
Duk da cikinsa yayi wata ƙara, jin an ce mace ta na nemansa. Wace mai tsautsayin ce wannan? Me take nema a wurina?, amma ya maze ya ɗago jajayen idanunsa ya kalli walid ya ce "Ni kuma?"
Walid ya ce "Ba zan yi maka ƙarya ba, da gaske nake"
Wani dogon tsaki ya ja, ya dungurar da kofin shayin, ya tashi ya ce "Ku ɗebo yaran nan na cikin unguwa, da na can wajen gari, ku sake dira a dabar madaki, ina son ɓarnar da za ku yi ta fi waccan, kar ku basu damar cutar da kowa. Ko kun gaya wa jami'an tsaro ƙudurinsu, babu abun da za su yi musu, ku far musu kawai, ka shirya komai, a bawa yaran na shan sigari" bai jira amsar walid ba ya fice.
Walid ya yi ajiyar zuciya, ɗan mama ya kalle shi ya ce "Da gaske ka ke wata ta je nemansa, ko kuma ka faɗa ne, dan ka hana shi shan ƙwayar nan?"
Walid ya ce "Duka, kai da ya sha abun nan, zai iya mutuwa fa"
Ɗan mama ya ce "Ai rigimar da yake yi kwanan nan, ta ƙara yawa, sai an ƙara saka masa ido sosai, kashe kansa yake son yi wallahi, wasu lokutan bana son muke watsewa mu bar shi shikaɗai a gidan nan".
Walid ya girgiza kai ya ce "Ba zai kashe kansa ba".
"Ya aka yi ka san hakan?"
"Yana da abun da yake son cimma, kawai kayan ne gaba ɗaya ba sa ɗaukarsa gaba ɗaya yanzu, ka san yana cikin matsananciyar damuwa, duk kayan cajin nan kansa ba ya ɗauka kamar aljani, amma ina bincikawa, an yi mini alƙawarin wata zazzafar ƙwaya, daga kudu suke kawota. Yanzu dai wannan aikin da ya ce , maza-maza ka kira kwangila a waya, ya haɗa mana yara, a basu kayan caji, zamu fasa ƙofa, ai Madaki shi da ɗaukar wata fansa a kanmu, sai dai a lahira idan ana yi. Sai mun ga abun da ya turewa buzu naɗi. Ɗan mama ya miƙe ya ce "Ok, bari na hanzarta na fara haɗo su ta arear wajen garin nan".
Walid ya ce "Nima fitar zan yi, wurin liti zani, zan shiga karɓar balance". Suka fice gaba ɗaya.
Bayan tafiyar su Aminu ya koma cikin ɗakin, ya fara duba in da walid yake ajiye ƙwayoyi, amma ya dudduba bai gansu ba, ya zazzage ko ina, amma babu.
Wani irin takaici ya tokare masa ƙirji, ya ja dogon tsaki, ya ɗaga gefen katifarsa, allurar sa saura kwalba biyu kawai, kuma ya san ba ɗaukarsa za ta yi ba.
Haka ya zuƙe ta ya yi wa kansa, sai dai kamar kullum, yau ma ƙirjinsa ne ya fara da zafi, kansa yana juya masa.
Wuƙar da take gefensa yake ta kallo, zuciyarsa na raya masa abubuwa daban-daban.
Tun da Ramma ta suka isa cikin kano, gidan da take aikatau, kayanta kawai ta sauke a ɗakinta, ta hau aikace-aikace.
Duk da akwai wata mai aikin, wadda ta girmewa ramma, sosai da sosai, amma matar gidan ita ta yarjewa ta shiga sashenta, har uwar ɗaka da na maigidan ta gyara mata, a cewarta ramma ta fi nutsuwa, kuma ba ta taɓa ƴar aikin da ba ta yi mata sata ba, sai ita.
Matar gidan da ƴaƴanta gaba ɗaya sun tafi dubai hutu, shiyasa ta sallame ta, ta ce ta je gida ta huta, za su yi wata biyu kafin su dawo, kuma kwatsam yanzu sati biyu wai dawowa za su yi.
Tana falon matar gidan, tana ta uban aiki, ɗan kwanakin da aka yi ba a taɓa wurin ba, duk ya yi ƙura.
Ƙofar falon aka shigo, ta tashi da sauri, tana kallon mai shigowar, dan ba ta yi tsammanin ganin kowa a sashen ba, dai-dai wannan lokacin.
***
Nabila kuwa kusan kwanaki uku curr, ta kasa nutsuwa da kwanciyar hankali, da ta kwanta bacci, sai mafarkin karnuka, tayi ta ihu. Haka Anty da baba magajiya za su danneta, su yi ta shafa mata man gelo da miski, ta ja bakinta, ta yi shiru, ba ta gaya musu abun da ta aikata ba.
Yau kuwa gajiya ta yi da zaman gidan, dan baka cikin hijjabi ta shirya, ta ɗauki ƴar ƙaramar wayarta, ta fito falo.
Umma ta kalleta ta ce "Ke da baki da lafiya, ina zaki je kuma?"
Nabila ta ce "Wurin aiki, akwai buƙatar in je zan kai wani bayani ne mai muhimmanci"
"Amma kin gaya masa, kar ya dawo ya tarar kin fita, ya yi ta faɗa"
"Umma ba daɗewa zan yi ba"
Saudat ta ce "Mhmm, a ma faɗi gaskiya, ko yawon banza za aje".
Nabila har za ta yi shiru, ta ga idan tayi shiru, za ta cutu, dan haka ta ce "Idan fitsari banza ne, kaza ma tayi, idan yawon ma zan tafi, mai lasisi ne akwai riba, ke ki yi mana"
Umma ta kalli Sauda ta ce "Sauda dan Allah ki din ga jan girmanki, Nabila fa ba sa'arki ba ce ba".
"Na saka da ke ne?"
Umma ta girgiza kai ta ce "A'a baki saka da ni ba, Allah ya taimaka".
Sumayya tana ta aiki a news room, Nabila ta yi sallama ta shiga.
Sumayya ta kalleta ta ce "Ina aikin?"
"Ban je ba, ya aikin?"
"Lafiya ƙalau, meyasa ba ki je ba?"
Nabila ta ce "Ke ba wannan ba, yanzu na ga managern ku a waje muka gaisa"
Sumayya ta ce "Good, ya aka yi?"
"Rahotonki na last week, a kan case ɗin yarinyar nan da aka yi wa fyaɗe, na ji shiru baku sake cewa komai ba"
Sumayya ta ce "Eh ya aka yi?"
Nabila ta ce "ina da intrest a kai ne, ina son shiga lamarin, na ji shiru haryanzu babu wani update, na an ɗauki mataki"
Sumayya ta ce "Dalla ware, kamar wata lawyer kirki, you are not even serious about the job"
Nabila ta ce "Ke ban son wulaƙanci fa, am serious, na ji an ce wanda yayi laifin mai lasisi ne a garin nan, ina son sanin waye shi?"
Sumayya ta ce "Nima ban sani ba"
"Kamar yaya ba ki sani ba, am serious fa, da gaske nake sumayya ina son shiga case ɗin, free of charge na taimaka wa yarinyar, na ji tausayin su sosai da sosai, yadda uwar take kuka. Kuma daga ji ƴan karkara ne, masu ƙaramin ƙarfi".
Sumayya ta galla mata harara ta ce "Sannu ambulance uwar taimako, manyan lawyoyi sun riga sun shiga case ɗin tuni, sai ki ja gefe"
"Suwaye manyan lawyoyin? Kuma wai waye dan Allah, waye yayi fyaɗen?"
"Ke! Nifa a rubuce aka bani, karantawa kawai na yi, hatta recording ɗin da aka saka, na muryar uwar da ƴar, tararwa na yi an yi, ban ma gansu ba, ban ga suwaye ba, balle na samu wani bayani. Case ma fa lamarin ya kusa zama a gidan nan, saboda saka muryar matar da aka yi, murtala ne dama ya yi recording ɗin ya saka, sai da aka kusa korarsu"
Nabila ta ce "To fa, ina murtalan yake?"
Sumayya ta ce "Ba zan nuna ba, kin ganki Nabila"
"Ba wani abu zan yi ba, sonake kawai ya haɗani da matar da yarinyar".
"Babu fa abun da zaki iya yi a kai, shi ma bai san waye wanda yayi fyaɗen ba, yarinyar aiki take a gidan, baƙo ne daga zuwa yayi mata. Dan Allah ki haƙura da case ɗin nan"
A ɗan fusace ta ce "Saboda me?"
Sumayya ta yi murmushi ta ce "Na ji an ce mutuniyar ki da jama'arta sun shiga cikin case ɗin, shiyasa na ce ki haƙura"
Nabila ta ce "Wa kenan?"
"Naja bunkure mana, antynki mudubinki, a bar ƙaunarki" Sumayya ta yi maganar tana dariya.
A take annurin fuskar Nabila ya ɗauke, haka kurum jikinta ya bata babu gaskiya a lamarin nan.
"Uban mudubin nawa, in dai wannan mudubin ne, Allah ya fasa shi na huta, wallahi sumayya tun daga abun da matar nan ta yi mini, kawai nake ji a jikina fuska biyu ce da ita, wadda take kallon jama'a da ita, da kuma wadda take ɓoyewa"
"To ko ma dai yaya ne, sun shiga case ɗin, kin san kuma ba zasu tsaya su saurareki ba, mussaman da ta iya yi miki kallon ke ba komai ba ce ba"
Nabila ta ce "Haka ne, amma rai dai an cire wa fara kai, lokaci ne, yana nan zuwa da zan bawa duniya mamaki, sai na saka ƙafa na bi ta kanta ko da halin ƙaƙa"
"To ki bi a hankali, kar ke duniyar ta baki mamaki"
Nabila ta yi shiru tana tunani.
Sumayya ta ce "Ya dai?"
Tayi guntun tsaki ta ce "Sumy zaman gidanmu babu daɗi, kamar in gudu wallahi".
"Wai Nabila ba zaki daina wannan iƙirarin ba?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba zaki gane ba, faɗa muka yi da Siyama, har da Abba ayi mini faɗa, sauƙinta ɗaya ta ci duka da tukunya na din ga dukanta"
"Haba Nabila, wannan ai yawa ne, degree holder da dambe?"
"To yaya ki ke so in yi? In zuba mata ido ta yi mini duka? Ga uwarsu ta addabi rayuwata, ba ta san yadda ta tsane ni, nima haka na tsaneta ba, kawaici kawai nake yi mata ba. Duk uban ƴan matan gidan nan har da zaurawa, babu wanda duka sanyawa ido sai ni, da na motsa ayi ta janyo mini jafa'in karuwanci" ta ƙarasa maganar hawaye na cika mata ido.
Sumayya ta ce "No dear, dan Allah ki ƙara jurewa, lokaci ne da kin yi aure zai wuce"
"Yaushe zan yi auren? Dan Allah ni mummuna ce Sumy? Duk saurayin da ya zo, sai za a fara maganar aure, sai ya gudu kamar wata jaɓa"
"Nabila kina da matsala, Babu wata halittar Ubangiji mummuna. Ga ki fara, ga gayu da ilimin addini da na zamani, kina da kwarjinin da ki ke bawa maza tsoro ne, ai ke kalar manya ce tawan, ba duk kai ba"
Cikin takaici Nabila ta ce "Ba wasu manya, manyan da suka din ga yaudarata Allah ya isa da ba su aure ni ba suka ɓata mini lokaci, ni yanzu kowaye ma zan aura na bar musu gidan, ko ba na son shi. Idan ba haka ba wallahi wataran sai na gudu"
Sumayya ga tausayin Nabila ga dariya, tabbas Nabila akwai farijinin samari, masu kashe mata kuɗi ma kuwa, sai dai Nabila ta fiye zaɓe-zaɓe, kuma ba ta fiye ba wa masu sonta da gaskiya muhimmanci ba.
"Ki gudu ki je gidan uban wa? Gaki ga Abba nan maza ki gudu kar ki fasa"
Sai kuma ta koma rarrashinta, har bayan azahar suna tare, sai da sumayya ta tashi suka fito tare.
A reception suka tarar da wani mutum, ana ta yi masa fadanci, yana hura hanci cikin manyan kaya na alfarma, reception ɗin ko ina security.
Sumayya ta risuna ta gaishe shi ya amsa, amma Nabila ko kallonsa ba ta yi ba, ta sunkuyar da kai, kamar alla-alla take yi, ta yi ta bar reception ɗin.
Ɗan rikicewa yayi, ya ƙura mata ido, amma ta basar ba ta gaishe shi ba, sai so yake yi ta ɗago su haɗa ido, dan ya tabattar da abun da yake tunani, amma taƙi ta mayar da kanta gefe.
Mamaki ya shiga yi, yana tunanin ko dai gizo idonsa yake yi masa? Sai dai ya rasa abun yi kafin ya yi wani yinƙuri, sun bar reception ɗin.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan ya kalla ya ce "Wannan mai hijjabin ma'aikaciyar ku ce ita ma?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a sir, she's just a guest here"
Ya ce "She looks familiar to me, anyway shikenan dai" yayi gaba.