Karfen kafa complete by fatty noor - Chapter 4
Karfen kafa complete by fatty noor Chapter 4: Karfen kafa complete by fatty noor Chapter 4. Ya ƙarashe cike da barkwanci. An zo gaɓar da ba ta so, wannan…
3,368 words
Ya ƙarashe cike da barkwanci. An zo gaɓar da ba ta so, wannan ya tilasta mata miƙewa tana duba agogon dake manne a bangon falon.
"Nidai bari mu wuce, Hajiya ba ta kaunar tuƙin dare."
"Ahaf, ai daga an dauko batun aure sai ta sauya akalar, toh ma ga iya gudun ruwanki. Ba inda za ki je."
Fadin Zulaihat. Ita dai ba ta tanka ba sai kallon da ta watsawa A'isha dake dariya sannan ta yi gaba tana yi musu sai da safe.
Har bakin motar Zulaihat da yaranta biyar suka musu rakiya. Ta rankwafo saitin Ramlat.
"Malama akwai muhimmiyar maganar da zamu yi. Idan ma ba ki samu shigowa ba Ni zan shigo gidan."
Ta dan dubeta fuska a yamutse.
"Allah Yasa zancen gizo wannan karon ta bambanta da ta ƙoƙi."
Harararta ta yi.
"Idan ma ta zama daya ya zama dole ki bi, ba ki da zaɓi. Ko ma mene idan muka tashi yinta za ki ji. Sai da safe ku gaidamin tsohuwata."
Daga haka ta kama hannun yaranta suka koma ciki, twins na kuka akan a bar musu su yaran su kwana. Su kansu ba da son ransu ba sai dai makaranta ta share dukkan son ransu.https://my.w.tt/ub8deMQ0g9
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
04)
*** *ADAMAWA*
_*ALHASSAN AMINU*_
Ya kai tsawon mintuna uku tsaye a falon sai dai nisan da ta yi a tunani bai sa ta hankalta ba. Dattijuwa ce da za ta yi kimanin shekaru sittin a duniya. Ya daure ya kara maimaita sallamar, sai a sannan ta ɗan yi firgigit ta dubeshi da amsa tana kokari kauda kai da share fuska.
"A'a, Biyu? Yaushe ka shigo? Sannu."
Ta furta duk a lokaci guda, ya karasa bayan ya cire bakaken silifas din ƙafarsa ya durkusa gabanta gami da riko hannunta.
"Ya isa, ya isa haka don Allah Dada. Har yaushe za ki ci gaba da damuwa akan abinda ba'a hannunnu yake ba? Addu'armu ita ya fi buƙata. Kiyi hakuri, akwai ciwo, sai dai mun yi imanin komai yana da lokaci."
Ta dubeshi, ta girgiza kwarai ganin yanda ruwan hawaye suka ɓata ɗan farin gilashinsa har suka biyo saman fuskarsa. Hannunta ta zare ta cire mishi gilashin gami da dauke hawayen da tafin hannunta.
"Sau da yawa wasu abubuwan fin ƙarfin zuciyoyinmu suke. Rauninmu ya sa bamu da karfin aiwatar da abubuwa da dama. Nauyinmu yakan rataya a wuyanku. Na daina, na daina Biyu, kar ka kara. Ganin kukanka damuwa zai ƙaramin. Allah Ya magance mana, Ya karkato da hankalin ɗan uwanka gida a duk inda yake rayuwa."
Da murmushi ya amsa da Amin a hankali. Shi yana ji a jikinsa kamar da wuya ace dan uwannasa na raye duk tsawon wannan lokacin. Idan ma yana raye to ya manta da wanzuwarsu a doron ƙasa.
"Ya su Fatima?" Ta tambaya cikin harshen fulatanci, ya maida mata amsa fuska sake, cikin son kawar da duk wannan damuwar.
"Tana nan, gobe zan kawomaki ita ta yi miki sati ma."
Nan da nan kuwa ta washe haƙora.
"Allah Ya kaimu."
Ya amsa da Amin sadda yake kokarin maida gilashinsa.
"Ina waccan ƴar ƙauyen?"
Murmushi Dada ta yi.
"Ba ta jima da ficewa ba, ta raka Addarku gidan ƙunshi."
Gyada kai ya yi, ya kawar da zancen da batun tafiyar da ta zo mishi zuwa Kano, ya kara da fadin.
"Darakta ya ce na wakilceshi a wani meeting da za'a gudanar."
Ta fadada fara'arta.
"Sai ka karasa ka gaisarmin da Modibbo."
Jin ta ambaci Modibbo ya sanya annurin fuskarsa raguwa.
"Me hakan ke nufi?"
Ya dubeta, shi take duba da son jin abinda zai fito daga bakinsa. Gane hakan ya sanyashi murmushin yaƙe.
"Zan je in Sha Allah Dada."
Ta yi murmushin itama
"Allah Ya yi maku albarka. Ya yayemana damuwarmu."
Ya amsa da Amin cike da tausayinta. Ta sanya rai a abinda har abada ba ya zaton za su ƙara ji ko gani daga gareshi. Fatansa Allah Ya ƙarawa Dadarsu hakuri da dangana.
Washegari kuwa sai da ya biyo ya saukemata Fatima sannan suka kara sallama ta kara jaddada mishi ziyartar Modibbo ya amsa da toh kawai sannan ya kama hanyar Kano.
*** *KANO*
_*Lamiɗo Crescent*_
Wata hamshaƙiyar mace ce mai kimanin shekaru arba'in da ɗoriya zaune saman ɗaya daga cikin kujerar dinning, an jera kayan maƙulashe kala-kala a gabanta. Waya take tana zabga murmushi ga dukkan alamu tana jin dadin tattaunawar. Hajiya Zeenatu kenan.
Hankalinta ya kai ga mijinnata wanda ke saukowa daga matattakala sannu-sannu kamar mai ciwo a tafin ƙafa. Kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kai. Daidai sadda ya ƙaraso ta cire wayar a kunne bayan sun yi sallama da abokiyar wayarta ta.
Ta dubeshi kamar ta haɗiye sa'ilin da yake zama saman kujerar dake fuskantarta. Kallo take ƙarewa matashin mijinnata wanda da ace ta yi aure da wuri da kuma ƙuruciya, da ta haifi sa'ansa ko wanda da kaɗan ya rage ya kai shi a girma. Hannunta ta ɗora saman haɓa ta zubamishi idanu shi kuwa banda danna waya ba abinda yake. Yana sanye da wata shadda da aka fi kira da Commisioner fara ƙal, an mishi dinki ba mai hayaniya ba kuma na zamani irin na matasan da ke ji da gayu da kuma kudi. Baƙin agogon fatar da ya ɗora a tsintsiyar hannunsa na hagu shi ya ƙara taimakawa wurin haskaka fatarsa mai cike da gargasa a idanunta. Ta kara kallon halittar ƙira da kuma fuskarsa wanda ke ƙara sanyawa ta ji shi ɗin nata ne ita kaɗai a duniya, don ita aka halittoshi. Har abada babu wata da za ta raɓarmata wannan inuwa da ta ke ganin don ita kaɗai aka ƙagi ni'imarsa. A yanzun da ya zauna nesa da ita, gani take kamar an jonamata mayen ƙarfen da ba zai rayu ba tare da ya kusanci ƙarfen da ke hakilonsa ba. Wannan ya sa ta miƙewa gami da nufar kujerar dake gefensa ta zauna bayan ta ja shi sosai zuwa jikinsa. Wayar hannunsa ta karɓa, wannan yasa shi ɗago kai gami da dubanta, duk da irin saƙon da ta karɓa bai sa ta girgiza ba. A ganinta wannan ba komai bane idan har ita din mace ce mai jarin juyawa, to ko birnin Sin ne za ta iya takawa ta je don cimma kowace manufa.
"Lafiya?" Ya furta yana ɗan lumshe idanu wanda hakan halittarsa ce, halittar da ta bambanta shi da halittu irinsa. Wanda da kallo ɗaya za ka bambancesu. Hajiya Zeenatu ta sauke wani ajiyar zuciya don jin so da kaunar matashin mijinnata na ƙara yin amai a cikin zuciyarta.
"Komai ma anyi Ranka Ya Daɗe, ni wannan fushin ba zai wuce bane? Daga radda aka yi ai ya ci a ce ya wuce kuma an rufe babinsa. Na ba ka hakuri tun a ranar, me zan maka bayan wannan don Allah, uhum?"
Ta ƙarashe cikin sigar jan hankali irin na gogaggun matan boko kuma ƴan shagwaɓa. Nan da nan ya ji tsikar jikinsa ta tashi, kwanakin nan kawai dannewa yake sai dai zuciyarsa na tsananin kaunar su shirya, yanda yake kwana da wuni da tunaninta haka ita kuma ta ɗaure fuska ta sauya mishi akan laifin da ba shi ya gayyato ba.
"Ya wuce."
Ya furta dakyar bayan ya tattaro nutsuwarsa. Ta ɗago hannunta wanda ya sha adon awarwaro da zobuna na gwal ta ɗora gefen fuskarsa da saje ya zagaye.
"Ka tabbata?"
Murmushi ya yi ya kalleta gami da dauke kai, bai c komai ba. Dama ta san ba lallai ya ce din ba, mafi yawan lokuta shirun ne amsarsa. Da rawar jiki ta shiga serving dinsa tana jan sa da hira, nan da nan ya sake suka ci abincin suka haura sama sai turaka.
Tana gefen gado zaune tana waya ya fito daga wanka. Ganin yanda take tsuma ya sanyashi maida hankali gareta. "Su a banza a wofi!! Ko sun manta mu ne gwamnatin?! Bar ni da su!" Kiit! Ta kashe wayar.
"Ofishin haraji zamu je." Abinda kawai ta iya ce mishi kenan itama ta faɗa banɗaki.
*🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem
05)
Safiyar talata da misalin karfe tara da mintuna, ta shiga ma'aikatar Revenue wurin aikinsu. Kai tsaye ofis dinsu ta wuce bayan ta gaisa da idon sani. Nan da nan ta haɗe fuska ganin wanda ke zaune tare da abokan aikinta suna hira. Mutumin nema yake ya takuramata, sallamarta ya sa duk aka amsa, ya kuwa zubamata ido kamar ya haɗiyeta.
"Kai kam Oga Ahmad ka taki sa'a ga dukkan alamu. Ga wata ga zara."
Ba ta san sadda ta watsawa Halima mai wannan furucin kallo ba, itama Halimar ta yi don zolaya, hakan yasa ta basar da hararar gami da dariya ciki-ciki.
"Ai kuwa dai Halima. Gwara da Allah Yasa na yi sammako. Ganin na Ramla wuya yake."
Ba ta tankawa kowa ba ta zauna saman kujerarta ta maida hankali ga Rabi suna gaisawa. Jin maganar mutum ta yi a gefenta yana fadin.
"Haba Gimbiya Ramla, wannan ɗaurewar fa? Ina fatan dai ba daga ni bane?"
Ko kallo bai isheta ba, to girman ne ya zube warwas! Ya riga ya tureshi tun radda ya bayyana fitsararsa ƙarara. Ya gama bambamin surutunsa ya fice.
"Ba ki da wayo Ramla, da ni ce da damarki, za ki yi mamaki."
Ta maida duba sosai ga Halima,
"Idan wannan shi ake kira da rashin wayo Halima, to ki jera Ramla a sahun farko. Kema ina roƙamaki shiriya."
Daga haka ta maida kai ga aikinta ba ta saka baki cikin caa da abokan aikin maza da mata suka yi ga Halima ba wacce ranta ke susa da maganganun Ramla. Ta kuma ci alwashin sai ta rama ko ba jima ko ba daɗe.
*** Suka yi parking ɓangaren da aka ware don ajiye ababen hawa. Kusan a tare suka fito. Kai tsaye Hajiya Zeenatu ta fiddo waya ta dannawa Chairman kira. Suka ɗan yi magana sannan suka kashe. Da kwatancensa suka nufi ofishin, ba tare da wani jinkiri ba aka yi musu iso zuwa ciki.
Aliyu Dikko matashin da zai shekara arba'in da ɗoriya ya dubeta fuska a washe.
"Manya gatan wasa, ganinki sai da dalili."
Ta yi dariya tana mai zama sa'ilin da suka zauna.
"Ai ku ne gwamnati, shiyasa dole ku za'a bi ko an ƙi. Ba don wankin hula na neman kai ni dare ba ai ba ka ganni ba."
Ya ƙyaƙyace da dariya gami da maida hankali da matashin da tun gaisuwar da suka yi bai ɗago ba balle ya shiga maganarsu, asalima waya yake sarrafawa.
"Ah lallai kam. Wannan ƙaninmu ne?"
Tambayar ta sa ya ɗago kai ya watsamasa wani irin kallo kafin ya dubeta fuska a murtuƙe.
"Please mu yi abinda ya kawomu."
Ganin haka ta shiga nutsuwarta ba shiri.
"Chairman jama'arka sun min laifi duk da dai da nawa laifin. An ƙullemin shago saboda kuɗin haraji. Wannan abu ba ƙaramin tozarci ne a gareni ba don haka na zo nayi clearing komai."
Ya jinjina kai, zai so ya san wane saurayin da har ya iya jan Hajiya Zeenatu kamar raƙumi da akala sai dai kuma ba fuska. Waya ya ɗauka ya danna kira kai tsaye ga department ɗin da ke kula da wannan ɓangare. Mintuna kaɗan shugaban department din ya hallara. Cike da girmamawa ya gaida Chairman. Ya saurari dukkan jawabinsu kafin su mike su bi bayansa don aiwatar da abinda ya dace.
"Bismillah ku zauna."
Oga Ɗalhatu ya umarcesu bayan sun isa ofishinsa. Ya kira abokiyar aikinsa da ya ke da tabbacin takardun Hajiya Zeenatu a hannunta suke.
Ramla na zaune ta dukufa shigar da wasu bayanai kwamfuta, tana yi tana hamma da duban lokaci. Sa'arta ɗaya ba ita ke da alhakin ɗauko yara ba a'a ranakun Litinin zuwa Alhamis bisa yanayin aikinta wanda sau da dama sai huɗu suke tashi. Sai dai a yau ɗin gani take ta gaji ba kaɗan ba, kamar ba za ta iya kai wannan lokacin ba, haka kawai ba ta jin dadin jikinta. Kiran da Oga Ɗalhatu ya yi mata ne ya katse komai da take yunƙurin yi, ta miƙe ɗauke da file din Hajiya Zeenatu har wani abokin aikinta Salihu na faɗin Hajiya ta ji wuta ta kawo kanta suna dariya.
Da sallama ta shiga ciki bayan an amsa mata. Gaba ɗaya sun bata baya, sai Oga Ɗalhatu dake fuskantar ta.
"Yauwa ƙaraso Ramlatu."
Ta shigo sosai, ido hudu ta yi da Hajiya Zeenatu, hakan yasa ta gaisheta da ɗan murmushi. Ita kuwa ta amsa ciki-ciki tana kauda kai. Ba ta ga dalilin da za ta sakarwa kowace ɗiya mace fuska ba muddin tana tare da Mijinnata. Tana kishinsa, kishi mai tsanani. Ramla ta kauda kai da mamakin hali irin nata, sam ba ta ko kalli mutumin da suke tare ba balle ta maida hankali gurin gaidashi.
Bayanin Oganta take sauraro kafin ta karkata ga Hajiya Zeenatu ta fara yi mata bayanin duk abinda ya dace ta yi kuma ta biya cikin kwarewa da sanin makamar aiki.
Ya ɗago kadan ya kalleta, aka ci sa'a itama idonta ya sauka a kansa sadda ta ɗan rausaya ido duk cikin bayani. Kirjinta ya harba, ina za ta mance fuskar da tun kallon farko ya kasa ɓacemata? Shi ne, shi dai da ta yiwa ɓarnar dubunnai ya yi mata afuwa. Ya haɗe cikin maroon voyel sai hula da ta hau da kayan. Ɓata lokaci ne ka tsaya siffanta tsatsar kyan da Allah Ya mishi. Gareshi kuwa, kallo ɗaya kwaƙƙwara ya mata sai ya ɗauke kai.
"Aikinki za ki yi ko kuwa kallon mazan wasu?!"
Ta ji kalaman Hajiya Zeenatu tsakar kanta, sai sannan ta ankara da tafiyar tsutsar da kalamanta suka soma yayin furtawa sakamakon kallon sanin da ƙurillar da take yiwa abinda bai shafeta ba. Sai dai zafin kalaman Hajiyar ya sa ta ɗaure fuska. Har aka kammala komai suka tafi ba ta ko ƙara kallonsa ba, balle shi kuma da ba ta gabansa.
"Kinsan Allah mijinta ne, makwaftan wata ƴar uwata ce. Wallahi a ranar farko da na gansu tare sun fito daga gidansu ban yarda ba don har ina cewa ta samarmin lambarsa, ƙarshe na yarda don akan na gaidashi a bakin ƙofa, matarnan har ɗaga hannu ta yi da zummar marina ya riƙe hannun sannan ya ja hannunta suka koma ciki. Tun daga ranar ban ƙara wannan gangancin ba."
Hirar Najaatu da Halima ta tsinkayo daga nasu mazaunin, tsalam ta ji Salihu ya sa baki.
"Ke Hali dubu! Yanzu wannan mijinta ne?"
Tana ji Halima ta hau rantsuwa da fadin kwarai kuwa.
Nan da nan aka hau yin caftarsu, daga mai cewa kuɗi ya gani ya yi wuf da ita sai mai fadin bai yarda ba saboda sam saurayin bai yi kalar babu ba.
Uffan ba ta ce musu ba har lokacin tashi ya yi, ta haɗa tarkacenta ta yiwa kowa sallama ta fice.
Tuƙi take sai dai hirar da akai akan matashin da Hajiyar da aka kira da matarsa ya tsayamata a ƙahon zuciya.
'Me ya kai shi? Da ƙuruciyarsa da komai? Kyakkyawa kuma ɗan gayu irin wanda babu macen da za ta ganshi ba ta ji sonsa ba? Me ya kai shi auren wacce ko ba ta yi sa'ar mahaifiyarsa ba, za ta zo a babbar yayarsa?'
Nan da nan zuciyar ta warwaremata zaren da ta ƙulla ba tare da shan wahala ba.
'So! So ne! Ba abinda ba ya sa wa, kamar yanda ya sa na aikata abinda bansan zan iya ba.'
Ta haɗiyi miyau tunanowa da ranar da ko daga bacci ta farka za ta bada labarinsa.
*** _*SANADI*_
Bini-bini sai ta kalleta ta ci gaba da tafiya tana murmushi. Ƙarshe Ramla ta gaji ta kai mata duka a baya tana dariya.
"Wai ko ke aka sanyawa ranarnan sai haka!"
Dariyar suka yi gaba ɗaya.
"Wallahi ba ki ji yanda nake murna ba. Ba don na gama tsallena cikin gida ba da yanzun ƙarawa zan yi."
Tsaki da dariya ta yi kawai ba ta ce uffan ba. Sai da suka ƙarasa har titi Ramla ta samu ɗan sahu kafin su yi sallama ta soma ƙoƙarin tsallakawa hannun da zai mayarta gida.
"Ƴan mata bamu chanji mana." Ta juya inda maganar ke fitowa, adaidaita ce ta yi parking a gabanta, sai da ta ji ba za ta iya yafewa kanta ba sa'ilin da idanunsu suka haɗu, da ba ta kalleshi ba, abubuwa da dama ba zasu chanja daga zuciya zuwa gangar jikinta ba. Sai dai kuma nan take ta ƙaryata. Shima da yake daga cikin ɗan sahun watsi ya yi da nashi a kwandon shara ya maida kai zuwa cikin abin hawar.
"Babu kenan." Ta ji muryar ɗan sahun sa'ilin da yake sauka yana nufar abokin aikinsa da zummar karɓar chanji. Bisa kuskure idanunsu ya ƙara sarƙewa, ta yi saurin janye kwayar idanunta shi kuwa an zo gaɓar da ya yi amannar hakurinsa ya ƙare.
Ta gifta napep din har ta samu nasarar tsallakawa. Haka kawai take zuba sauri don ta isa gida, ba ta yi aune ba ta ji muryar mutum a bayanta.
"To ni kuma da ba ɗan unguwa ba kina wannan saurin idan na ɓata fa? Kar ki kaini gidan ƴan yankan kai."
Cak ta tsaya gami da juyowa, bata san sadda ta yi suɓutar baki ba.
"Biyoni ka yi?"
Duk yanda ta so kar ta ƙarasa faɗi bayan ta ankara da suɓutarsa hakan ya faskara. Murmushi ya yi ya ɗan tako kaɗan. Kusan a gigice take duban layin, fatanta kada koda wasa Yaya Munir ya ganta tsaye anan. Wannan yasa ta juyawa da zummar soma tafiya.
"Don Annabin Rahma ki tsaya."
"Sallallahu alaihi Wa sallam." Ta furta a hankali sannan ta dubeshi.
"Malam wallahi an sakamin rana yau ɗin nan ma, don Allah ka yi hakuri ka daina bina. Matsala za ka jawomin a gida."
Ta furta rai a haɗe sannan ta soma tafiya kirjinta na harbawa. Fatanta Allah Yasa ya dakata.
"Ni duk ba wannan ba, nima inada matar aure. Kwatance za ki min."
Ba ta fasa tafiyar ba, bai fasa bibiyarta yana magana ba. Dole ta tsaya ganin an kusa shan kwanar layinsu. Ta dubeshi da idanunta masu firgita maza. Ya kuwa lumshe nashi ƙananan idanun masu kama da na mai jin bacci ya bude, shirunta na nufin tana jinsa kenan
"Wani gida nake nema, bansan kalarsa ba. Ba zan ce ga girmansa ba, kuma da ace ma da hali naga gidan ban ƙi ya zama mallakina ba na har abada. Amma kinsan me? Matar gidan ta nunan ba ni da wurin zama cikin gidanta. Ni ne da nacin tsiya na kasa haƙura. Idan na kasa mallakar gidannan, bana jin akwai gidan da zai ƙara burgeni koda kuwa ace wanda nake da shi yanzu ne! Ki tausayamin don Allah."
Ya ƙasashe cikin karaya, rabin hankalinta na ga kallon hanya rabin wajensa, ko kusa ba ta gane wannan tatsuniyar ba don haka kai tsaye ta ce.
"Wallahi ban gane komai ba Malam, ka rufamin asiri ka tambayi wani ko wata sai anjima."
"Saƙo na ƙarshe don Allah, nima daga nan zan juya na tafi kar na sha wahala."
Dole ta ja tunga ta juyo tana dubansa, shima ƙara narkar da idanunsa ya yi cikin nata gami da jingina kansa jikin bishiyar darbejiyar dake bayansa. Ta kauda kai tana ƙara yiwa kanta tunin wannan ba HILAL bane tsaye.
"Bana yiwa mace kallon da ya wuce biyu, amma kin janyomin sauka a unguwar da kusan bani da kowa, ban taɓa bin mace a baya ba, don wannan ba ya cikin sabgar ALIYU, kin sanya na biyoki. Bansan gaskiyar sanyamaki rana ba duk da cewa fuskarki ba ta maƙaryata bace, sai dai ki taya kaina da kuma ke addu'ar kada mu kasa cika alƙawarin waɗanda muka ɗauka matsayin abokan rayuwarmu. Fatan alheri MATAR GIDA."
Daga nan ya juya bai ƙara waiwaye ba, duk da dukan da kalaman suka yiwa zuciyarta, bai sa ta fasa ci gaba da tafiyar ba. Sai dai fa tana tafe tana yiwa kalaman filla-filla, sannu-sannu kuma take haddarsu. Ta kasa fahimtar manufar, ba kuma ta marmarin ta fahimta ɗin don a ganinta bai da amfanin komai, wannan ta sa ta yin watsi da shi. Sai dai daga lokacin Aliyu ya yiwa mafarkanta illar da har ta soma tunanin ba mutum bane!
Hilal ya zo suka yi sallama sadda zai wuce Malaysia, kowannensu wata irin kewa yake ji, Ramla kuwa kasa jurewa tayi ta shiga hawaye.