Karfen kafa complete by fatty noor - Chapter 66
Karfen kafa complete by fatty noor Chapter 66: Karfen kafa complete by fatty noor Chapter 66. Rasheed ba Hausar kirki sai kame-kame yayinda ita kuma Ramlat…
3,332 words
Rasheed ba Hausar kirki sai kame-kame yayinda ita kuma Ramlat ba larabci don haka sai kawai suka juye harshe zuwa English suka ci gaba da hira. Abinci lafiyayye ta yi musu shi da abokinnasa, sai da ta ajiye komai kafin ta ba su wuri tana kauda kai daga kallon da Hussein ke jifanta da shi yana ji kamar ya haɗiyeta don kauna.
Ta kwanta rigingine saman gadon, kewar yaranta ta ke ji wannan ta sa ta kiran Hajiya. Bayan gaisuwa Hajiya ta haɗa ta da su. Hira sosai ta dinga yi da yaran, wannan na warce waya, wannan na sako baki yana magana kamar yanda ta fahimta. Dariya sosai suka dinga sanyata jin dagaske su dai so su ke ta dawo Kano ta dinga kai su makaranta a mota. Sai ma a lokacin ta tuna da motarta, yanzun ta san sai dai Hajiya ta ajiye su dinga amfani da shi koda wata matsalar za ta taso da waccan.
"Kinga gajen hakurin Yayanku ko? Sai da ya sauwakewa Bilkisu ya ji dadi."
Gabanta ya fadi jin abinda Hajiya ta ce.
"Kamar ya Hajiya? Me ya kuma haɗasu?"
"Uhm, wai gidan Amaryar ta je ta ja ta da fada har da kokarin dukanta, wannan ya fusata shi. Yanzu dai Kawunnanku sun ce tunda ya dauki zafi a kyaleshi kar a tursasa mishi sai ya maido ta, nan gaba itama watakila ta yi hankali. Yarannasa su na hannun Amarya."
Ramlat sam ba ta ji dadi ba, ko ya ya halin mutum ya ke, saki wani abu ne mai zafi. Cike da jimami ta ce.
"Allah Ya kyauta, Allah Ya daidaita lamuransu idan da alheri."
"Ameen."
Hajiya ta amsa, kamar koyaushe, nasiha mai ratsa jiki ta ƙara yi mata akan riƙe amanar miji da kuma kyautatamasa. Ta kara nusar da ita game da ibada musamman a watan Ramadan da ke ƙara kusantowa don bai fi saura wata guda da ƴan kwanaki ba.
"Allah Yay maku albarka, Ya ji ƙan Abbanku."
Ramlat ta amsa zuciyarta a raunane musamman tunanowa da Abbanta da ta yi, har suka yi sallama ba ta dawo daidai ba. A hankali kuma ta kwanta sosai ta juyawa ƙofa baya. Kewar Abbanta ta ke ji, ta tabbatar da ace yau yana raye zai yi matuƙar alfahari da aurenta na biyu, zai kuma ji dadi. Burinsa da kuma farin cikinsa bai wuce nata ba, ya ci alwashi a kanta a bayan aurenta da Aliyu wanda ya zamemata ƘARFEN ƘAFA, da kansa kuma ya janye sakamakon tsantsar kauna da tausayin da yake mata. Mutuwa ba ta barin wani don wani ya ji dadi. A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ba ta san hawaye ta ke ba sai da ta ji tattausan tafin hannun Hussein yana sharemata su. Da sauri ta juyo sai dai babu damar matsawa sakamakon hannunsa ɗaya da ke tokare a gefenta a saman gadon. Ido ya ƙuramata fuskarsa na nuna alamun ba dadi.
"Habibty, meke damunki har ki ke hawaye?"
Ta girgiza kai ta sunkuyar tana murmushi.
"Ba komai, waya muka yi da Hajiya, addu'ar da ta yimin ta sa na tuno Abbana. Shi ne kewarsa ta kama ni."
Ya kamo haɓarta ya ɗago suka kalli juna.
"Kiyi hakuri, dukkanmu muna da wannan tabon na rashin iyaye duk da cewa kaso kusan ɗari, mun samu kulawar da ta dace a wurin Dada wanda ko su ne sai haka. Haka Allah ke tsarinSa a rayuwa, dukkan mai rai mamaci. Allah Ya gafartamusu."
Ta amsa da amin tana mai jin karfin gwuiwa. Ya bita da wani irin kallo yana murmushi, ta yi azamar jan rigarta tana harararsa. Mikewa ya yi ya taɓe baki.
"Wane dare ne jemage bai gani ba?"
"Daren mutuwarsa."
Ta amsa, ya yi dariya, har ya dawo da baya sai kuma ya jinjina kai ya kama hanya yana fadin.
"Ki fito ku yi sallama zai wuce."
Jin haka ta mike ta maida hijab din da ta cire, fitowa ta yi har Rasheed din ya miƙe tsaye don haka suka yi sallama don ta san ba lallai su kara haɗuwa ba tunda a yau sha biyun dare zasu wuce Airport.
*** Bayan sallar isha'i ta shiga suka yi sallama da Hajiya Binta. Mata mai kirki, haka ta sanya ta a ɗaka ta ba ta shawarwarin da za su amfaneta a zamantakewa. Kafin ta yi mata kyautar miski mai kyau marar sirki. Ta yi godiya sosai. Koda ta fito ɗakin Hafsat ta faɗa jin yanda kwanaki biyu ba ta jin ɗuriyarta. A kwance ta isketa yatsarta na dama rike da Counter tana dannawa a hankali. Shigowar Ramlat bai sa ta ɗago ba balle ta san da wanzuwarta a ɗakin. Zama ta yi gefen gadon, hakan ya ankarar da ita, tausayinta ya kamata. Yanzun Dada ta gama faɗan sauyawarta, ta kuma san dalilin tunda Hussein ya faɗamata. Hafsat ta mike zaune da sauri tana goge hawayen saman fuskarta.
"Adda Amal, sannu da zuwa. Yanzu ki ka zo?"
Ramlat ta gyara zama sosai ta dubeta.
"Hafsat kar ki zama marar hakuri da juriya a lamarin soyayya. Ki zama mai hakuri. Kin san illar saɓawa iyaye kuwa? Na taɓa shiga makamancin halin da ki ka tsinci kanki ciki a baya. Na kuma san yanda ki ke ji, kina jin kamar ba za ki iya rayuwa babu Taheer ba, kina jin numfashinki zai iya ɗaukewa muddin ki ka rasa Taheer matsayin miji ko? Kamar su Dada da Yayyanki ba su yi maki adalci ba."
Hafsat ta kwantar da kai saman cinyar Ramlat, sai kawai ta fashe da kuka ta soma magana.
"Adda Amal wallahi hakane, na sani Mahaifinsa mai laifi ne a wurin su, amma shi me ya yi musu da za su yanke alaƙata da shi? Dada da bakinta ta yabeshi a ɗan zaman da ya yi tare da mu, ta fada ta ƙara, bai ɗauki halin mahaifinsa ba balle na mamansa, Hamma AlHassan ma haka. Hamma Hussein bai zauna da shi sosai ba da na tabbatar zai gamsu da kyawawan ɗabi'un Taheer. Adda Amal sanadin aurena da Taheer zai iya sanyawa su shirya. Babban damuwata Hamma Hussein ya kwace wayata, Rasheeda ta kirani ta wayar Dada tana kuka ta shaidamin yana asibiti kwance ba lafiya."
Hafsat na kaiwa nan ta mike zaune, ita Ramlat kallonta kawai ta ke tana fidda hawayen tuna baya, itama dama haka ta kafe? Amma ba za ta taɓa bari Hafsat ta yi irin nata ba.
"Adda Amal kimin alfarma ki ban wayarki, sau daya kawai zan kirashi, daga haka ba zan kara ba. Wallahi kawai gaisawa zamu yi na kuma roƙeshi mu ci gaba da addu'a. Har abada ba na fatan na bijirewa iyayena da yan uwana."
Ramlat ta yi jim, tana tunanin anya kuwa idan ta yi hakan ba matsala? Sai dai kuma irin magiya da nacin Hafsat ya sa ta miƙamata wayarta. Kasa fita ta yi daga dakin ta jira har Hafsat ta kammala wayar, Ramlat banda kallon ƙofa ba abinda ta ke yi. Tsoronta kar Dada ta faɗo ɗakin don ta san abu ne mai matsanancin wahala Hussein ko AlHassan su shigo ɗakin.
Da murmushi ta dubi Ramlat.
"Adda Amal."
Sai ta rungumeta don farin ciki can kuma ta saketa.
"Cemin ya yi za su zo nan da kwanaki kalilan har Babansa, zai zo neman gafarar Dada da su Hamma."
Sosai itama Ramlat ta ji dadin hakan. Ta rike hannunta.
"Toh kinga ni, don Allah ki saki ranki, kinga Dada kin jefa ta a damuwa. Ta ce ko ganin idon baƙuwarku ba kya yi, ba ki san ki danne zuciyarki da abinda ke cikinta ba. Jefa iyaye cikin damuwa masifa ce a garemu. Kuma ina mai ba ki shawara ki dage da nemawa kanki zaɓin Allah, ki rabu da biyewa son zuciya wurin dagewa akan zaɓinki."
Hafsat wacce tuni ranta ya yi fari sumul ta gyada kai.
"In sha Allah Addata. Ina godiya sosai. Sai dai Adda ba ki ban labarin da ki ka ce."
Ramlat ta murmusa.
"Kar ki damu, ai ana tare."
"Da'iman kuwa da yardar Allah." Fadin Hafsat, suka dara kafin Ramlat ta fice ita kuwa bandaki ta shiga ta wanke fuskarta. Ramlat na sallama da Dada sai ga Hafsat din, sosai ta yi mamakin walwalarta, ta karasa ta fda jikin Dadar tana neman gafararta cike da shagwaɓa. Murmushi Dada kawai ta yi gami da jinjinawa Ramlatun. Ta tabbatar aikinta ne.
*** A ɓangarenta kuwa, ganin fitilu a kashe ya ba ta mamaki matuƙa, ita dai ta san ba ta kashe ba. Haka ta ci gaba da tafiya a hankali har ta kai ga makunnin, kafin ta kunna ya riga ta. Ta juyo ta dubeshi, kafin ta kai duba ga cikin falon. Baki da hanci kawai ta saki tana dubansa ta kuma maida duba ga abinda idanunta ke gani.
I just published "BABI NA SITTIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1028701620?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=0Ip%2BQlXDoaoxyM7eqonDyl6cCNMjLR7b13cfWz0PO6rluIvQeUuu1jHeHigNXBE4IV%2Fm159PS%2BDsIeqGDHiIXMY5fTO3p4OINuf3vYe6Dx12trWJCYsK2knobbhhwa9y
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
64)
_*Assalamu alaikum yan uwa Barkanmu da wannan lokaci. Ku yi hakuri kun sha jira, da yardar Allah kiris*_
Wani ƙaton enlargement ne na ɗaya cikin hotunanta da ya ke da su, ta karkace kai tana murmushi har fararen haƙoranta sun fito, sai wani ƙaton kwali da ba za ta iya cewa ga abinda ke ciki ba sai kuwa akwatuna jere reras har guda sha biyu. Ta kai dubansa gareshi, murmushi ya ke sakarmata sosai. A hankali ya matso ya kama hannunta suka karasa cikin falon. Wani ƙaramin kati mai adon heart da fulawoyi ne ya soma daukar hankalinta don haka ta sa hannu ta ɗauka ta bude.
_*From the moment I first laid eyes on you, I knew you were a perfect match for me. I love everything about you Heart.*_
Ta juyo ta dubeshi, yana tsaye kawai hannuwansa cikin aljihun wando yana zubamata murmushi. Da ido ya mata nuni akan ta ci gaba da buɗewa. Ba musu ta kai durkusa ta kai hannu ta bude wani karamin gida na zobe, ai kuwa zoben ne mai matukar sheƙi, ya fi mata kama da na azurfa. Ya yi masifar burgeta, idanunta ya ƙara kaiwa saman wani kwalin karami da aka ɗaure bakinsa da igiya mai ƙyalli, ta bude, ganin mukullin mota kawai sai ta ɗago ta dubeshi, idanunta nan da nan suka cicciko da kwalla. Ta ajiye kafin ya taimaka mata da bude akwatinan, kaya ne maƙil, kowanne da set dinsa. Yanda dai ku ka san lefe irin na budurwar yarinya don wannan ma ya fi na budurwar kyau da tsari. Ko iyaka haka aka tsaya a na budurwa sai sam barka. Laces, atamfofi, mayafai, shadda, yadika, abayoyi da dukkan sauran kayayyakin shafa da sarƙoƙi ba abinda ba'a haɗa ba. Wannan ya bata tabbacin ba yau ya soma haɗawar ba. Bayan sun mayar da komai ta dubeshi, tuni hawayen da ta ke dannewa sun zubo. Ya kai hannu da sauri ya ɗaukemata su. Ba ta bar kallonsa ba ta soma magana.
"Allah Ya saka da dumbin alheri, na.."
Ya kai yatsa saman lebbanta.
"Shii...Ba kalar godiyarnan nake so, buƙatar fin haka nake. Kar ki manta kuma haƙƙi ne na maki sutura da ma duk abinda bai fi ƙarfina ba wanda zai farantamaki. Kin cancanci fiye da haka."
Ya ƙarashe gami da ɗagamata gira. Kunyar ta nema ta rasa, kawai sai ta juyo gaba ɗaya ta rungumeshi har bayansa na jingina da kujerar. Ya kuwa ba ta kyakkyawan mazauni a kirjinsa, kafin kuma kiɗa ya sauya salo.
*** KANO..
Wutar da ta tashi a wani gida dake unguwar ya sa mutane duk suka fito, cikin dare ne da misalin karfe biyu da mintoci. Banda salati da kokarin kashewa ba abinda ake yi. Da yawa suna aikin kashe ta amma fadi suke don kawa kar wutar ta haɗa da nsu gidajen ne amma banda haka dama sun gaji da Maigidan, bokancin da ya ke yi musu a unguwa yana tare matasa abin ya ɓaci.
Gora kuwa yana daga ciki banda ihu da neman agaji ba abinda ya ke yi, ya rasa ta inda aka yi wuta ta soma cin gidansa, babban abinda ya ƙara haukata shi neman jakar kudadensa da ya yi ya rasa, ga yaronsa ba ya nan. Wannan ya ɗan ankarar da shi cewa cin amanarsa ya yi. Nan fa ya haukace, tun akwai hanyar ficewa har ya zamana ya rasa ta inda zai bi ya tserar da rayuwarsa daga halaka. Haka dai kafin mutane su yi nasarar tsayar da wutarnan, Gora rai ya yi hali.
A ɓangaren yaronsa kuwa har da shi cikin masu kokarin kashe wuta kamar gaske, har ya tafi sai ya yi tunanin gwara ya tsaya ya tabbatar da mutuwar Gora kafin ya gudu, idan kuwa har aka yi rashin sa'a ya tsira, to ya tabbatar duk inda ya shiga a duniya ba zai tsira daga ta'addancin Gora ba. Ganin an fito da Gora a mace ya sanya ya ji wani sanyi a ruhinsa, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya hau mashin dinsa ya wuce can filin makaranta inda abokinsa Jabir da suke kira da Jabson ke jiransa su wuce. Yana zuwa suka cafke su na dariya. Nan ya ba shi labarin komai, ya dubeshi da kyau.
"Jakar fa?"
Jabson ya yi wani malalacin murmushi gami da mishi nuni da aji. Ya bubbuga kafadarsa suka dara kafin ya shige gaba zuwa ajin, sai dai shigar ya yi daidai da sokamishi wuƙa a baya ta ɓullo ta ciki, Jabson ne. Sai da ya tabbatar ya kashe shi har lahira sannan ya ɗauki jakar ya tsallakeshi. Mashin dinsa ya haye ya bar wurin a miliyan. Shi da garin Kano kuma sai nan da wasu shekaru.
Misalin ƙarfe sha biyu na rana, labarin ƙonewar Gora da tsintar gawar yaronsa ɗan aikensa Salmanu, ya karaɗe unguwar. Ko'ina maganarsu ake yi, ga Jabir abokin Salmanun da aka nema sama ko ƙasa aka rasa. Dama almajirai ne, wannan yasa aka shiga tunanin ko sace Jabir din aka yi bayan kashe Salmanu. Daidai sadda ake wannan hargitsin, motar Hajiya Zeenatu ta tsaya. Tun kafin su fito cikinsu ya ɗuri ruwa ganin yanda gidan Gora ya zama kango lokaci guda.
"Ke Zeenatu, anya gidan ne?"
Hajiya Zeenatu ta kasa amsawa Hajiya Batool, kokari ta yi kawai ta yi parking suka fito, yaran almajirai na ciki su na ta ɗage-ɗage ko za su yi tsintuwa. Daga ƙasan bishiya wasu samari suka hangosu. Ɗayan ya ce.
"Waɗannan su ne na goma sha takwas kenan, wannan mutumin fa yana wankar mata, yanzu haka ma wani mugun aikin su ka zo ya musu."
Wani ya mike.
"Bari mu je mu ji, idan ma shi suka zo nema mu ba su labari ko Allah zai sa su tsorata da lamarin rayuwa su shiryu."
Ganin haka sauran ma suka mara mishi baya don ba za'a yi babu su ba.
"Hajiya wurin Gora ku ka zo?"
Hajiya Batool da Zeenatu wadanda sun rasa ta ina za su soma, su ka dubi saurayin kusa a tare suka amsa da eh.
"Ayya, ai a daren jiya gobara ta cinye gidansa tas babu abinda ya tsira. Shima ya mutu ɗazunnan aka dawo daga binne abinda aka tsinta na gangar jikinsa. Shima dai yaronsa Salmanu an tsinci gawarsa a filin makarantar Firamare an kashe shi."
Hajiya Zeenatu sai da numfashinta ya bar motsi na wani lokaci kadan, ta kasa magana sai kawai ta ɗora hannu a kai ta fashe da kuka. Jiki na rawa Hajiya Batool ta ce.
"Shikenan Gora ya mutu dai ku ke nufi?"
Suka bisu da kallo kamar taɓaɓɓu, kusan ma duk kalar ruɗewar da sauran matan da suka zo suka yi, bai kai na wadannan Hajiyoyin ba. Mai magana ɗazu ya matso.
"Eh ya mutu. Duk wani mugun aiki da ya ke shukawa ya kare. Ya koma gidan gaskiya inda zai girbi abinda ya shuka din. Kuma ya kamata ku ji tsoron Allah ku tuba daga tafarkin shaidan tun kan lokacinku ya ƙure. Idan har ba so ku ke yi kuma ku zama tarihi ba, ku tafi a wofi."
Hajiya Batool ba ta ce uffan ba balle Hajiya Zeenatu da ke faman kuka, ashariya kawai ta ke narkawa Gora kamar ta mance da cewar ya mutu. Har dai dakyar Hajiya Batool ta maidata mazaunin kusa da direba ita kuma ta tuƙa motar suka bar layin, yara duk an cika ana binsu da kallo.
Haka suk isa gidan Hajiya Batool hankali a matukar tashe. Ita kanta Batool din dakiya kawai ta fi Zeenatu, amma ba ta ga laifinta ba don kuwa ta fi ta zazzage bakin aljihu a wannan harkar. Nutsuwa ta gagaresu, Hajiya Zeenatu kawai zama ta yi kamar kayan wanki a saman kujera tana ci gaba da surfa ruwan bala'i ga Gora da ya jima a gushewa.
"Yanzu shikenan Hussein da Ramlatu haka zan zuba ido ku cigaba da cin amanata?! Shikenan wai hakan na nufin sun yi nasara?! Wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na ga bayan Ramlatu da Uwarsa! Sai Hussein ya dawo karkashin ikona. Ba zan dauki wannan dumbin asarar ba! Batool nemomana Maryama a waya! Zuwa Nijar ya kama mu, ya zama dole mu kara gwada aikin Bokansu. Buzaye ne!Za mu yi nasara, za mu yi nasara."
Ta na maganar kamar wacce ta samu taɓin kwakwalwa. Itama Batool ta gane zuwannasu Nijar din kawai shi zai zame musu mafita don haka ba musu ta zaro waya ta dannawa Maryama kira lokaci guda kuma tana sharce gumi. Magana sosai suka yi, ba ta ɓoyemata duka asarorin da ya hau kansu ba. Maryama ta jajanta musu sosai karshe ta ce musu za ta yi musu booking na layin ganin Boka Buzu, kawai dai da zarar sun saka ranar zuwa su fadamata.
"Gobe ma zamu taso jibi mu iso."
Hajiya Batool ta katse ta da gaggawa, ƴar dariya Maryama ta yi kafin ta amsa da toh hadi da musu fatan zuwa lafiya.
Washegari kuwa da sassafe suka kama hanyar Nijar, direba ne ya kaisu. Yardaddan direban Hajiya Batool, Audu. Wannan karon ma sun tattara maƙudan kudade don ita Hajiya Zeenatu ba ta bi ta kan Manajanta ba, ta nemi manyan gwala-gwalanta har biyar ta shiha kasuwa ta siyar. Itama dai Hajiya Batool sai da ta haɗa da siyar da kadara, kowaccensu ta taho cike da burin samun abinda aka je nema. Idanunsu ya rufe, gani suke yi tamkar ga su ga burinsu har ya cika tsabar imanin da suka yi da abinda zai kai su.
Wuraren karfe sha biyun rana da mintoci suka iso Damagaran, anan suka kwana washegari da sassafe suka kama hanyar Niamey. Sun sha tafiya sosai kafin su isa Niamey, kai tsaye suka kira Maryama a waya. Da kwatance da tambaya suka iso katafaren gidanta wanda ya sha kayan alatu. Ta musu kyakkyawar tarba, ba kamar wancan lokacin ba, wannan karon gidanta ne na kanta ba na Maigidanta ba. Tun bayan rasuwar Mijinta ta siya gida inda ta ke harkar safarar yara zuwa Ƙasar faransa da ma wasu ƙasashen yawon bariki. A yanzun da su ke zaune a falon suna cin abinci bayan sun yi wanka, ba tare da kowaccensu ta damu da kallon gabas ba, ƴan mata ne ke safa da marwa cikin shiga mai ƙayatar da masu iri halinsu na bin maza. Babu wacce ba ta fito ta gaida baƙin Madame dinsu ba, a karshe Hajiya Zeenatu ta kora ruwan sanyin da aka ajiyemusu ta dubi Maryama.
"Kin tabbatar dai goben babu fashi a zuwanmu wurinsa ko?"
Wani murmushi Maryama ta yi ta dauki tuffa ta gutsira.
"Haba Hajjaju, zan maki ƙarya ne?"
Ganin haka Hajiya Zeenatu ta saki fuska.
"Ba haka nake nufi ba, kin dai ji komai ai daga bakin Batool, banda haka nan da kike ganina duk sadda zan runtse idanu ba abinda nake haskowa sai Mijina tare da waccan karamar karuwar. Gani nake duk kwana daya tamkar shekara ce."
"Ki sa ranki a inuwa, za ki sha mamakin yanda komai zai lalace. Mijinki ya dawo kamar kwai a hannunki sai yanda ki ka yi da shi."
Dariya suka yi har da cafkewa, nan da nan zuciyoyinsu suka ɗan waske sai dai ko ya ya suka tuna asarar da ta hau kansu na miliyoyi sai sun tsinewa Gora. Basu ma batun nemar masa gafara.