Karfen kafa complete by fatty noor - Chapter 9
Karfen kafa complete by fatty noor Chapter 9: Karfen kafa complete by fatty noor Chapter 9. Ta shiga istigfari a ƙasan ranta, shi kuwa tuni ya rude don…
3,301 words
Ta shiga istigfari a ƙasan ranta, shi kuwa tuni ya rude don dagaske ya yarda.
"Shi ne ba ki fadamin ba, ban ji dadi ba. Please yi hanzari ki je ki sha magani ki kwanta kinji? Zan kiraki anjima."
Ta gyada kai.
"Nagode. A gaida su Umma." Ta juya da sauri don dama jinta take kamar a kan ƙaya.
"Hey!" Dole ta dakata gami da juyowa. Yana rike da murfin mota yana bin ta da kallo kamar ya haɗiyeta.
"I so much love you!"
Maimakon ta amsa, sai ta bishi da murmushi da azama ta juya ta ci gaba da tafiya, a bangarensa ya fassara hakan da kunya. Wanda shi ke karamasa ƙaimi wurin sonta, duk kuwa da wani sashi na zuciyarsa bai gamsu da tarbar da ya samu ba.
'Na yi tunanin fiye da haka, zumuɗi, walwala, ɗoki.'
'Ka manta ba ta da lafiya? Ka yi mata uzuri. Ba ta da abin so idan ba kai ba.'
Da wannan tunanin ya ji karfin gwuiwa, hakan ya dawo da walwalarsa, burinsa yanzu ya haɗa dukkan takardun karatunsa ya bautawa ƙasarsa sannan ya kama aiki. Hankali da nutsuwarsa kacokan su dawo kan abar sonsa.
*** Tafiya na ta tafiya, rayuwa na zuwa na sauyi masu tarin yawa. Kama daga siffofin halittu har ya zuwa zuciyoyi da kuma nasarori ko akasinsa. Hakan ce ta faru da Ramlat sadda take cuku-cukun zana jarrabawar WAEC/NECO don hada kwalin Sakandire. Dukkan wata cika ta ƴa mace ta sameshi idan ka cire rama da ƙashin wuyar da ta yi sakamakon zullumin da ta jefa kanta ciki ganin na taso da shiri gadan-gadan na aurenta da Hilal da zai biyo baya nan da watanni hudu.
"Ke za ki soma shiga gidan aure a class din mu. Ina ji daga ke sai G smally."
Faɗin Amrah sadda take kokarin gutsirar eggroll da ta ke korawa da lemun Pepsi. Da gayya ta ƙi duban fuskar ƙawarta don tasan cikin dayan biyu ne, ko ta samu harara ko kuma..
"Mtsw, aikin banza!"
Murmushi Amrah ta yi ganin ta ƙarasamata tunanin da ba ta san tana yi ba.
"Mene abin tsaki? Ai gwara ki yi wani sabon abin, ba abinda zan fahimta. Tunda ke ba kya jin shawara har ta kai matakin da za ki karyar zuwa gidanmu don kawai Aliyu ya zo ku gaisa."
Kwarewa Ramlat ta kusan yi da lemun Mirinda da ta ke sha. Murmushi Amrah ta yi ta ci gaba da cin Eggroll dinta hankali kwance.
"Allah Ya isa, kina neman kasheni da rai. Toh wa kike faɗawa? Ke bari na fadamaki, yanzu ko kofar gidanmu Aliyu zai taka ba na fargaban komai. Ke dai ban sanki da tone-tone ba. Gwara ki ci gaba da ɓoyen wannan sirrin. Ni wannan yanzu bai fiye damuna ba. Damuwata wai Muhibbat tana da ciki. Kuma cikin Aliyu."
Ta ƙarashe tana mai jin kwalla na cika idanunta, baki sake Amrah ke dubanta. Karshe sai ta sanya salati kafin ta ɗora.
"Kin hadu da aiki, kin kuma hadu da wahala wallahi Ramlat. Shiga hurumin kuma da ba naki ba za ki fara? Amma dai ina fatan ba ki nuna bakin cikinki a gabansa ba? Tunda ke ba kya aiki da hankalinki yanzu."
Guntun tsaki ta ja gami da harararta wanda ya yi daidai da zubowar hawayen.
"Mene naki a ciki idan na nuna toh? Waye ba ya kishin abinda ba ya so? Ban gama sanin mene aure ba, amma naji a wurin wadanda suka yi cewar idan mace tana da ciki tana samun kulawa sosai a wurin miji, yana kuma son abinda ke cikinta. Hakanan kuma soyayyar zai koma kan abinda ta haifa, duk kuwa da 100% nasan Aliyuna ba ya son Muhibbat amma kishi halal ne."
"Kishi da matar aure? Matarsa ta sunnah? Ramlat kina tsoron Allah kuwa? Kar ki yarda ki zama mai irin wannan kishin na hauka, kar ki yarda ki haramta abinda Allah Ya halarta. Cin amanar Muhibbat da ku ke yi kuna waya har tsakar dare bai isheki ba sai abinda ke cikinta ya tsonemaki idanu? A'a Ramlat, kar ki kusa kuma kar ki yarda ki dora kanki a wannan turbar. Wallahi da ace akwai halin da za'a iya ciro zuciyar mutum a cire son wani a ransa, da tuni na ciro taki na wanketa tas na cire sunan Aliyu na maida gurbinsa da na Hilal. Ke da kanki kin fada da bakinki Hilal yana sonki, ya kuma gane cewar yanzun ba kya sonsa, kin ce ya sha kiranki ya ji call waiting, hakanan bai karaya ba kuma bai fasa batun aurenki ba. Wane so ne zai biyo bayan wannan? Yan uwansa da Mahaifiyarsa suna sonki, suna ganin girmanki, ji yanda Anti Bilki ke miki kamar kanwarta da ku ke ciki ɗaya. Akan wani can da ba ki da tabbacin aurensa kin sanya ƙafa kin ture duka wannan karramawar da Ubangiji Ya yi miki, kina kara cusa kai inda ba lallai ki yi kwarjini ba a idanun ƴan uwa da iyayensa. Kar ki manta, Muhibbat cousin sister ɗinsa Kuma matarsa ce, ina rabaki! Ina rabaki!"
Ko ba'a faɗa ba jikinta ya yi sanyi, sanyin da ya zama na fargaba. Ko ba komai kalaman Amrah sun dan taɓa zuciyarta amma hakan bai sa ta ji za ta iya hakura da muradinta ba. Don haka ta dubeta kurr.
"Kamar yanda ki ka ce Allah Ya karramani, kar ki manta Shi ke iko da zuciyata. Ba ni na sanya son wannan Bawan a raina ba, haka kawai na wayi gari da so da kaunarsa. Ba kuma zan iya hana kaina ba, batun shiga hakkin Muhibbat naji zan karbi hakan, zan daina. Amma ki sani, ba zan taba ganin kiran Aliyu na ƙi ɗagawa ba koda ace ina tsakiyar Teku ne ina kokarin nitsewa ba. Ba zan yi ba kuma ba zan fara ba. Zan kuma yi kokarin ɓoye kishina a kanta, saboda abu ne da idan aka yimin ba zan ji dadi ba, sai dai so hana ganin laifi. Ki bar sanya auren Hilal cikin ƙaddarata, babu shi, babu shi kwata-kwata a littafin rayuwata, kedai Allah Yasa mu kammala karatu lafiya. Duk wannan shirin da su Abba da Hajiya ke yi kallonsu nake, don zai tafi ne a gidana da Aliyu in Sha Allah."
Murmushin da take bugawa ya sa Amrah ƙara gasƙata zurfin soyayyarta ga wannan mutumin.
"Allah Ya kyauta, Ya hanemu mugun ji da gani." Abinda ta iya furtawa kenan kuma magana ta karshe tsakaninsu kafin su mike su shiga aji karfe uku don gabatar da lesson duk a cikin shirin zaman jarrabawa.
*** Juyi yake yana kara tunanin zantukan da ya yi da Ramlat game da shirin aurenta da aka fara, gaba daya kansa ya kulle don ji yake muddin ya rasata ba shi da sauran nutsuwa balle kwanciyar hankali, ya kai duba ga inda Muhibbat ke kwance tana bacci sannan ya mike ya dauki wayarsa ya fice daga dakin. https://my.w.tt/At99ZcOeF9
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
10)
Tarr ta bude idanunta jin motsin bude kofar. A hankali ta kai hannu saman dirowa ta dauko wayarta gami da duba lokaci, karfe uku saura mintuna, mayarwa ta yi ta ajiye kirjinta na wani irin zugi tana cin ɗaci a maƙogwaro. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar falon, kunnuwanta ba zasu iya juriyar sauraron hirarsu ba don haka ta dawo dakin. Banɗaki ta shiga ta kama ruwa gami da ɗauro alwala, nafila ta yi raka'a biyu, ta jima cikin sujjada tana zubar hawaye gami da kai wa Allah kukanta kafin ta ɗago ta sallame. Nan ma Alkur'ani ta jawo ta karanta a karshe ta yi addu'a ta shafa.
Shi kuwa Aliyu tun da ya kira ya soma zazzaga ruwan kalamai ga Ramlat mai nuni da kewa da kuma damuwar halin da za su shiga idan wani abin ya afku.
"Na kasa bacci, na kasa samun nutsuwar yi, kin kuma san ke ce. Ina tsoron na rasaki Baby."
Ya ji motsin rufe kofa, ya waiwaya sannan ya kara kishingida ya ci gaba da wayarsa hankali kwance.
Daga ɓangaren Ramlat ta kara cusa kai cikin bargo yanda A'isha ba za ta motsa ba.
"Na fi ka shiga wannan zulumin, Sweet Aliy babu ta yanda zan rasaka in sha Allahu. Ka kwantar da hankalinka."
Murmushi ya yi mai sauti. Nan kuma suka shantake suka shiga hira har da kyakyacewa.
Muhibbat zaune saman darduma ta zurfafa cikin tunani, ta ji labarin kaddarorin aure da dama, sai dai irin nata ya bambanta da kowanne. Ta yi sanadin sauyawar lamura da dama. Ta rugurguza farin ciki da dukkan tanadin da ta yi a zamantakewar aurenta. Shigowarsa dakin ya katse tunaninta, ya kai duba ga inda take, sai kuma ya dauke kai ya koma saman gadon ya kwanta gami da juyamata baya. Ta tsayar da idanunta ga kallon bayannasa, a duniya ba namijin da take so irin mijinnata, dama so na rikiɗewa har haka? Da me wannan baiwar Allahn ta fi ta? Meyasa yake ƙuntatamata saboda ita? Meyasa ta kasa samun zaman lafiya a rayuwar aurenta duk a dalilinta? Ta dauka duk mace mace ce!
Wasu hawaye masu ɗumi suka zubomata ganin halin ko in kular da yake nunamata aduk sadda irin hakan ta faru. Bacci har da sakin munshari ta tsinceshi yana yi. Ta kai hannu ta shafi cikinta ɗan watanni biyu kacal, a hankali ta lumshe ido tana addu'ar neman sassauci da kalar rayuwar mijinta.
*** Hajiya ta yi mata ƙuri da ido.
"Kwanakin nan kin fiye yawo, kin je gidan Amrah ya fi a kirga, yau kuma Muniru ki ka tuna? Yaushe sabo mai karfi ya shigeku har haka?"
Ta turo baki kadan.
"Dan uwana ne fa Hajiya."
Abba dake karanta jarida ya ɗago kai yana dariya.
"To kinji amsarki ai. Kwana nawa ne za ta tattara ta bar miki gidan ke da autarki? Ki bar ta ta sada zumunci, ta samu lada biyu. Na juma'a da kuma zumuncin."
Ramlat ta sauke ajiyar zuciya, dama tana sane ta tambaya a gaban Abban don tasan zai goyi bayanta. Tun safe Hajiyar ke cin magani tana mitar wai ta sauya daga Ramlatun da ta sani akan ta shigo tana waya ta yi shiru har ta fita daga dakin. Wannan ne kuma ya tabbatar da zargin Hajiyar cewa akwai saurayin da ke huremata kunne a yanzu. Koda Hilal bai ce komai ba, ita ta lura ɗiyar ta bar rawar kafa a kansa da komai ma.
"Ban wayarki. Idan kin dawo kya karɓa."
Maganar Hajiyar ya daskarar da ruwan jikinta, ta bude baki za ta yi magana sai dai tuni miyan bakinta ya daskare jin muryar Abba na magana cikin nuni da goyon baya.
"Ba ta idan har za ki tafin. Tunda gidan Yayanki ne ai ba damuwa. Zuwan dai ake kokarin hanaki."
Ba haka ta so ba don dama da biyu take son fitar, Aliyu na son ganinta ko ta wane hali don su tattauna su samarwa kansu mafita sai dai kuma da alama karyarsu ta kare muddin wayarta ta shiga hannun Hajiya. Ba ta da zaɓin da ya wuce ta fiddo wayar daga jaka ta miƙa wa Hajiyar.
_Idan lokacin bayyana soyayyarmu bai yi ba har yanzu, sai yaushe? Sai yaushe ne za'a san abinda muke ta ɓoyansa? A soyayya ba'a shakka balle tsoro. Idan aka yi hakan ba'a yi mata adalci ba, ba'a fitar da hakkinta ba._
Wadannan kalaman Aliyu ne, nan take ta ji wani kwarin gwuiwa. Ƙarƙari Hajiya ta bincika wayarta ta kuma bibiya shiga da ficen kiranta. To me ta aikata? Ai ba haramtacciyar soyayya ba ce.
'Nema cikin nema?'
Ta ture tunanin ta hanyar yi musu sallama ta fita, Abba ya bita da kyakkyawar addu'a yayinda hankalin Hajiya ya koma ga wayar ta yi mishi ƙuri kamar mai jiran amsa daga cikinta.
"Menene wai Rabi'atul Adawiyya? Meke damarmin ke da zuciyarki? Kwanakin nan ina lura da tsaurin da kike ƙara yi game da yarinyar nan. Ta yi wani abu ne?"
Hajiya ta yi shiru tana dan kallonsa, ta fi kowa sanin halin mijinta, yana da sauki amma idan ranshi ya ɓaci babu kyau. Bai fiye zargi ba kamar yanda bai fiye daukar magana ba idan har ba shi ya ganewa idanunsa ba ko kuma yana da hujja. Tasan idan ta furta wani abin bisa zargin zai iya yiwuwa nata ne zai yi wari don haka ta ɗan murmusa.
"Ba komai Abban yara, tunaninka ne kawai ya ba ka hakan. Ramar da take yi ne kawai bana so, a kanta aka fara aure?"
Ya riko hannun Hajiya yana murmushi.
"Kar ki damu, ko kin manta ban da auren shirin zana jarrabawa ta ke? Na dan lokaci ne In Sha Allah. Ko kin manta kalar naki zullumin dab da aurenmu?"
Da sigar wasa ta harareshi suka yi dariya gami da yiwa Ramlat din kyakkyawar addu'a.
*** Cike da fara'a Anti Bilkisu ta tarbeta.
"Lale marhabin da Amaryarmu. Yau an tuna da ni?"
Ramlat ta kama hannun Maama babbar ƴar Yaya Munir suka zauna saman kujera. Tana dariya
"Kai Anti, ko wata fa ban yi ba rabona da gidannan."
Taɓe baki Anti Bilkisu ta yi tana dan murmushi.
"Ai shikenan, nasan da mutuniyata ce har da kayan kwananta zan ganta. Kin dai wanke kanki tunda kin zo. Yau na huta da shiga kicin."
Dariya ta yi kawai sanin halinta, wato dai tana nufin A'isha don sun fi ɗasawa, dama murnar da take na zuwannata kusan da biyu ne. Wata irin mace ce mai son jiki da ba ta son aiki, burinta kawai a yi mata, wasu lokutan akwai ta da shan ƙamshi da kuma sakarwa mutum hidima duk sadda ya kai mata ziyara, wannan ta sa ba ta fiye zuwan ba. Da ace ta san ma dalilin zuwannata da sai ta ji kamar ta shaƙeta.
"Mutuminki kuwa jiya kusan wuni ya yi a gidannan, kinsan fa ni ya damƙawa haɗa lefe don haka ki min biyayya idan kina son ganin tsala-tsalan kaya."
Tsaki ta yi wanda ba ta san ma ya fito fili ba, da mamaki Bilkisu ta dubeta.
"Tsaki ki ka yi?"
Sai ta ɗan basar.
"Wayata na tuna na bari a gida, kuma ina son yin waya. Don Allah ban aron ta ki."
"Au, toh ki gama wayar a karshe ki ce ya turon kati don nasan ƙararwa za ku yi."
Ta ƙarashe tana mai sanya kai ta fice daga falon zuwa ɗaki. Da sauri Ramlat ta mike ta nufi kicin, lambobin da suka riga suka zama tamkar lazimi a wurinta shi ta shiga rubutawa kafin ta danna kira. Sai safa da marwa take yi a kicin din har kiran ya shiga.
"Assalamu alaikum."
Ta tsinci muryar mace, muryar da ba ta yi kama da ta Muhibbat ba don akwai sadda ta taɓa kiran Aliyun, ta daga ta ce ba ya kusa. Ranar ta tabbatar sun kusa yin kaca-kaca da Aliyu don har rantsuwa ya yi mata a kan idan tana so ma zai sauwakewa Muhibbat duk a dalilin kishin da ta motsamata.
"Hello."
Aka kara fada daga can bangaren sai dai ta kasa magana. Tana shirin katse kiran cike da faduwar gaba ta tsinci muryar macen.
"Kanwarsa ce Habiba, Yaya Aliyun yana ciki wurin likita su na magana."
Da wani irin matsanancin tsoro ta watsamata tambaya kamar a tsawance.
"Meya sameshi?! Wane asibitin ne?"
Habiba sai da ta ɗan yi shiru kafin ta yi magana cikin rashin wayo.
"Anti Muhibbat ce ta yi ɓari, ya bar wayar a dakin ne, idan ya dawo zan fadamasa kin kira."
Da sauri ta katse kiran ta kuma goge lambar daga wayar. Tasan ba ta son Muhibbat, ba kuma tsana ba, a'a, kishinta take. Sai dai fitar cikin ya zo mata a bazata, ba ta san sadda ta shiga fitar da hawaye ba, ta ajiye wayar a gefe ta hau fiddo kayan girki jikinta a sanyaye. Ba ta taɓa jin tausayin Muhibbat din ba sai a wannan rana.
Tana cikin gyara kayan miya ta tuna ba ta ma tambayi Antin abinda za'a dora ba, tana niyyar fita ne kuma ta ji wayar ta dauki ƙara, jiki a sanyaye ta karasa ta daga, lambar Aliyun ne.
"Ki yi hakuri, waccan ƴar rawar kan ce ta ɗaga. Ta fadamaki muna asibiti ko? Kar ki damu fa zan zo din. A ina za mu hadu?"
Ita kuwa wane irin rashin adalci ne wannan da zai sa ta nemi ganinsa a yau duk da tashin hankalin da matarsa ke ciki yanzu? Ko ba komai a yau Muhibbat ta cancanci duk wata alfarma. Don haka ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta shiga girgiza kai kamar yana gabanta.
"Ka yi hakuri, nima ce maka zan yi Hajiya ta karɓi wayata har sai na koma gida sannan za ta maidomin. Yanzu haka ina gidan Yaya Munir, wannan wayar Anti Bilkisu ce."
"Kenan ba zamu hadu ba?"
"Ka yi hakuri don Allah Sweet Aliy, a yau Muhibbat na bukatar kulawarka. Ka ce ina mata sannu. Zuwa gobe zan san yanda za'a yi mu hadu ko bayan tashi daga makaranta ne."
"Yau ita ta samu wannan alfarmar a wurin sarauniyar masu kishi?"
Ya fadi cike da zolaya yana ƴar dariya. Murmushi kawai ta yi mai sauti.
"Ai ina tunanin gida zasu wuce da ita har sai ta samu lafiya. Naga yayyunnata sai wani kallo suke watsamin kamar ni na janyo zubewar cikin. Mtsw, ita kanta In-law ba don darajar Granny ba sai na fadamata maganar da za ta hanata bacci."
Ta gane In Law din da yake nufi, wato Mama mahaifiyar Muhibbat, a duniya ya sha fadamata ya tsani matar saboda ko kallo bai isheta ba har gobe. Idan ma ya gaidata amsawar kamar mai taunar maɗaci haka ake yinta.
"Allah Ya bata lafiya."
Ta furta cike da tausayi.
"Ke na yi wani karambanin. Wayarki na soma kira kafin wannan. Har kuma saƙo na aika da ban ji kin ɗauka ba."
Ta fiddo ido waje game da riƙe kirji.
"Dagaske?"
"Yes, amma ya naji kamar kin razana? Mene a ciki? Mene don Hajiya ta san da zamana? Ko kina tunanin lokaci bai ba da zamu bayyana abinda ke zukatanmu? Saboda Allah na gaji da wannan ɓoyon!"
Ta ɗan sauke ajiyar zuciya.
"Me ka rubuta a sauƙon toh?"
"Idan kin koma gidan kya gani. Sai anjima." Ya katse kiran, nan da nan hankalinta ya tashi har garin saurin ta kirashi, kiran Yaya Munir ya shigo ta katse. Sai da ya kusan katsewa sannan ya daga.
"Me za ki cemin kuma?"
Ta marairaice.
"Ka yi hakuri. Wallahi nima yanzu bana tsoron kwan ya fashe kowa ya ji. Kawai dai na tambaya don na sani, amma ka yi hakuri."
Sai da ta kwashi mintuna uku tana bada hakuri, karshe ya hakura ya shiga karfafamata gwuiwa akan kar ta kusa ta ji shakkar komai akan abinda yake ƴancinta. Ya na kara nunamata muddin ta bari ta auri mijin da ba ta so za ta tafka kuskure. Ita kuwa ƙara hawa take gami da hango gaskiyar hakan. Tana ji kira na faman shigowa ta ƙi maida hankali a kai, sai da aka soma warning na karewar kati sannan ta tuna ita ta kira suka yi sallama bayan ya dorata kan hanyar da za ta bi ta fidda abinda ke ranta idan Hajiya ta mata zancensa. Ba tare da ɓata lokaci ba ta goge dukkan shiga da fitar da lambarsa ta yi a wayar. Hamdala ta yi kafin ta fita ta kaiwa Antin wayar.
"Me zan dafa?" Ta katse Anti Bilkisun dake kokarin daga wayar mijinta, cikin maida hankali ga wayar a gaggauce ta amsamata.
"Duk abinda kike so ki dafa kawai. Hello."
Ta ƙarashe da daga wayar Munir. Cikin sauri Ramlat ta yi gaba tana ji Anti Bilkin na ba shi hakuri da cewa ba ita ke amfani da wayar ba, can kuma ta ji tsakinta da masifa. Taɓe baki Ramlat ta yi don ta san kaɗan daga aikinta kenan. Ko a jikinta don tana da tabbacin zai wahala Yaya Munir ya isketa cikin gidan.