Kenza eBookz

Karfen kafa complete rufaida omar - Chapter 16

Karfen kafa complete rufaida omar - Chapter 16

Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 16: Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 16. ***

3,349 words

***

Motsin bude ƙyauren gidan ne ya farkar da ita daga azababben baccin da ya kwasheta ba tare da ta shirya ba. Rana tarr a saman kanta, Allah Ya taimaketa ma babu makaranta, Asabar ce. Ba laifi jikin da sauki sai dai ciwon kan bai sauka ba, bakinta babu ɗanɗanon komai. Wanka ta faɗa. Doguwar riga jallabiya kawai ta zura ta daure kanta da ɗankwalinsa.

Cikin faduwar gaba ta bude kofar falon, don bata da tabbacin fita ya yi ko shigowa. Ganin ba kowa sai wayarta da kaya a yashe saman kujera ya bata tabbacin shi ne ya maido su wurin. A hankali ta taka ta dauka ta kai daki, gaban madubi ta kara tsayawa tana kallon yanda goshi da bakinta suka kumbura suntum. Hawaye ta shiga fitarwa, ba ta isa ta je wa Abbanta da wani zancen ba akan Aliyu. Sai dai kuma shi kadai ne ke sauraron ta, banda shi ko waya ta kira su Zulaihat sama-sama suke amsawa.

Kicin ta koma ta dafa ruwan shayi da kayan kamshi kamar yanda Hajiyarta ke yi, ta zauna tana sha. Ba ta jin cin komai don haka ko kulolin tuwon da ta yi ba ta kalla ba balle ta iya ɗumamawa.

Babu abinda ta iya gyarawa a gidan, nan falon ta naɗe tana rawar sanyi, ciwon kai ya fi na baya. Ruwan shayin da ta sha shima haka ta amayar da shi. Bacci wahalalle ya kara daukarta, ba ta ji ƙarar shigowar mashin dinsa ba, sai jin hannunsa ta yi saman goshinta. A firgice ta farka, ganinsa ya sanya ta zabura za ta ruga ɗaki. Ya riketa gam a jikinsa, kawai sai ta fashe da kuka jiki na rawa.

"Don Allah ka yi hakuri ka rabu da ni, na tsaneka Aliyu, meyasa ka ɓoyemin munanan halinka? Wallahi ba zan iya ci gaba da rayuwa da kai ba."

Ya ɗago fuskarta yana mai riko haɓar.

"Baby wannan shi ne so? Don kin ganni a halin da ƙaddara ta jefani shi ne za ki gujeni? Baby maimakon ki ji tausayina ki tayani addu'a? Meyasa kika zo kusa da ni? Kalli yanda na ji miki ciwo? Baby baki da lafiya, jikinki zafi, muje ki sanya hijabi na kaiki asibiti. Kinji?"

Cikin karfin hali ta fincike jikinta ta faɗa saman kujera tana sheshsheka.

"Kar ka kara kirana da Baby. Wannan kuma ba ƙaddara ba ce, son zuciyarka ne! Kana saɓawa Allah kana kiran hakan kuma da suna ƙaddara? Wallahi sam ban yarda ba!"

Kalamanta sun soma yi mishi zafi sai kuma ya danne, lallaɓata kawai yake don ba ta jin dadi, don kuma wani abu da ya ƙudurta a ransa game da itan. Wannan tasa ya gane faɗa da zafi ba nashi bane. Ɗakinta kawai ya shiga ya fito da dogon hijabi ya taho da wayarta.

"Haba, ashe wayarki ba chaji shiyasa na yi ta kira bana samunki. Muje idan mun fita na bada chaji. Ki tayani addu'a, akwai wani ciniki da zan yi yau, idan ya faɗa har kaza zan siyomana, na kunna mana inji. Rashin wutar ya isheni."

Maimakon ta ji sanyin kalamansa, sai ta kasa jin hakan. Asalima baƙaƙen maganganun da ya jefeta da su a daren jiya har da zagin iyayenta sun fi komai tsayuwa a ƙahon zuciyarta. Ta haɗiye komai ta danne, ita kanta yanzun tana bukatar a duba lafiyarta, tana jin jikinta kamar babu jini balle ruwa, kamar ma a yau ɗin za ta mutu.

*** "Congratulations, kina da ciki wata biyu."

Kalaman da ke fitowa daga bakin likitiyar suka sanyata jin hanjin cikinta kamar zasu tarwatse.

"Ciki kuma? Dama haka ake cikin?"

Abinda ta fadi ya sanya daga Aliyun har Likitar dubanta, shi Aliyu ko fuskarsa kadai ka kalla za ka san yana murna da hakan duk da cewa yana auna yanda nauyi zai ƙara hawa kansa.

"Yes ciki, haka report ya nuna. Yaushe rabon da ki ga al'adarki?"

Tsabar rudewa ma ta mance da wani batun al'ada, ita tun zuwanta gidan Aliyu ba ta taɓa ganin jini ba. Shima Aliyun sai a sannan ya ankara da hakan. Maimakon ta yi murna, maimakon a ga tana dariya sai ta rike cikin tana kuka kamar wacce aka fadawa ranar da za ta mutu.

"Bana so, wallahi bana so! Dr ki zubar da shi."

Wani wawan mari Aliyu ya dauketa da shi. Ta rike ƙuncin a zabure ta mike tana dubansa cike da dumbin mamaki.

"Haba Malam, matarka ta sunnah? Ita za ka mara? Wane rashin hankali kenan? Koda ta yi kuskure ba ka ganin yarinya ce, bai kyautu ka lallaɓata ba? A ina aka taɓa marin mace, matar ma ta sunnah?"

Bai ko kalli Likitar ba wacce haushi da takaicinsa ya kamata. Ta zagayo ta kama hannun Ramlat da gaba daya ta gigice kukan ma ya tsaya cak. Ashe dai akwai marin da ya fi karfin kuka.

"Please get out. Ka bamu wuri."

Yana huci ya yi kwafa gami da hadata ita da Ramlat din ya watsamusu wani banzan kallo, har ya kai ƙofar ya juyo ya hau magana.

"Kika kuskura kika yi gangancin zubarmata da ciki, daga ke har ita sai na yi shari'a da ku!" Daga haka ya fice gami da banko ƙofar da ƙarfi har iskar na bugunsu. Dr Sadiya ta zauna kujerar da Aliyu ya mike, sannan ta maida Ramlat din mazauninta suna fuskantar juna.

'Ga ta a haka yarinya mai hankali da nutsuwa, sai dai da alama ba ta yi dacen miji ba.' Cewar Dr Sadiya a ƙasan ranta. Tausayin Ramlat ya kamata,ta danne ta soma yi mata nasiha.

"Ramlat ke fa musulma ce, cikinki koda shege ne ya haramta ki zubar balle kuma cikin sunnah. Ba ki yi kama da mutuniyar banza ba, ba kuma ki yi kama da mata ballagazazzu ba wadanda basu je makaranta ba. Ko mene ya yi zafi a rayuwarki, ki dinga tunawa da Allah. Shi ne Mai yaye dukkan wani azaba. Ki kwantar da hankalinki, idan ma haihuwa kike tsoro ki miƙa lamuranki ga Ubangiji, In sha Allah sai kiga kin haihu lafiya. Mutum nawa ne za ki ga su na neman haihuwar ba su samu ba? Wata ma da kudi za ki ga ta zo nan tana neman maganin da za ta sha ta samu ciki. Wata kuwa har kuka take yi tana faɗin yanda miji da danginsa ke wulaƙanta ta duk akan ba ta haihu ba. Ke kuma da Allah Ya ba wa cikin ma na sunnah ki ce bakya so? Kenan kina nunawa Ubangiji ba ki yi murna da kyautarSa ba?"

Ta girgiza kai tana share hawayen da sai a sannan suka zubo, so ta ke ta ce ba haka bane, so ta ke ta ce yaron ko yarinyar da ke cikinta, ba ta so su dauki ɗabi'un mahaifinsu, sai dai kuma ba za ta iyaba. Ko ba komai wannan sirrinsu ne.

Dr Sadiya ga ci gaba da lallaɓata da ba ta shawarwari har sai da Aliyu ya gaji ya dawo ofishin.

"Wai me ake yi? Ni fa zan iya barinki ki kwana anan idan ba ku kammala ba."

Ya yi maganar a fusace, Ramlat ta mike ta yiwa Dr Sadiya godiya, ita kuwa ta miƙa wa Aliyu file din suka fita. Tun a asibitin tana jinsa yana jan tsaki har dai suka siya magani suka fito yana mitar kudinsa sun kare.

"Wallahi injin ma na fasa kunnawa, kudin sun ƙare. Zan dai siyamaki kazar tunda na sakamaki rai."

Gyada kai ta yi kamar kadangaruwa, fuskarta duk ta kumbura saboda kuka. Bini bini sai ta shafi cikinta. Iskar mashin na neman yi mata yawa don haka sai ta dukunkule ta kwantar da kai kadan a gadon bayansa. Hakan da ta yi dukkansu sai suka ji wani sanyi da kaunar junansu yana kara ɗarsuwa a zuƙatansu.

"Ina sonka Sweet Aliyu, ba zan iya rabuwa da kai ba."

Ta furta a hankali, kalaman sun ratsashi. Ya yi murmushi gami da ɗan rage gudu.

"Baby wa ya ce miki zan iya rabuwa da ke? Ai mai rabamu sai mutuwa Baby. Don ina shaye-shaye addu'a za ki yimin har na daina, kin ji?"

Ya ji sadda ta gyada kai a jikinsa, kusan a tare suka yi murmushi. Murmushin tana yi hawaye na zuba, zuciyarta ta kasa tsanar Aliyun. Soyayyarsa da na abinda ke cikinta suka haɗarmata. Ta kuma daura ɗamarar faɗa wa Allah matsalarta akan Ya shiryamata mijinta.

Sai gashinan Gen din da yake cewa ba zai tayar ba, sai da ya siya mai rabin galan ya kunna suka ga haske. Ranar tattalinta ya dinga yi gami da fadamata karya da gaskiya duk don ta ji tausayinsa ta kuma yarda ba'a son ransa ya soma shaye-shaye ba. Ya kuwa ci galabar hakan.

**

🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

15)

Kallo ɗaya za ka yi mishi ka hango farin ciki tsantsa da walwala marar misaltuwa a saman fuskarsa. Sigari ya sanya a bakinsa yana zuƙa lokaci daya yana fesarwa. Ihu da kurantawa shi kawai ke tashi daga bakin maza da matan wurin.

"Cau cau Aliyu Angon Ramlat!"

Fadin G Baba. Hakan sai ya kara tunzura Aliyu har sai da ya zuƙe kara biyu cikin ƙanƙanin lokaci kafin ya kwantar da kai yana kallonsu ƙasa-ƙasa yana doka murmushi. Ko ba komai yau burinsa ya cika. Ko ba komai ya mallaki abinda ya jima yana dakonsa. Ya na a jingine da kujera cikin club ɗin, yana kallon yanda ake rawa da rausaya mata da maza. Duk ana yi don tayashi farin cikin samun cikar burinsa. Hannu ya zura a aljihu ya ciro bandir din dubu daya ya bude ya watsamusu. Aka hau kwasa ana ihu da kara korantashi. Abin na mishi dadi. Wayarsa dake saman tebur ya duba, kira ke shigowa ba kuma na kowa ba sai na Granny. Ya mike tsaye ya yi musu bankwana ya fice. Yau bai sha abin maye ba don ya fi son a yi komai cikin hayyacinsa ya gani.

Bai daga kiran ba har sai da ya bude sabuwar karamar motarsa Honda wanda Abulle ta sanya aka siyamishi ya shiga. Ya soma tuki a nutse kafin ya dauki waya ya kira Granny.

"Ina ka shiga wai? Ka zo mu tattauna game da lefen."

Ya yi murmushi gami da kara lumshe lumsassun idanunsa.

"Ina hanya Kakus, gani nan tafe."

Ya kashe kiran bayan ta mishi addu'ar zuwa lafiya. Ya kai duba ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa. Karfe tara da mintoci na dare. Buga sitayari ya yi gami da sakin ƴar ƙara da furta.

"Yes!!" Cike da nishadi ya kara gudun motar gami da ware kiɗa. Har ya isa gidan bai kashe kidan ba duk kuwa da hango iyayensa maza da ya yi zaune a saman tabarma ƙasan ƴar rumfa a farfajiyar gidan. Duk sadda irin hakan ta kasance, tattaunawa suke game da wani abun mai muhimmanci.

Kallonsa suke har ya kashe motar ya fito zai nufi cikin gida ba tare da tunanin gaishesu ba. Idan da sabo ya ci ma su saba.

Malam Abdussalam cike da takaicin halin ɗannasa ya sunkuyar da kai.

"Kai! Aliyu?!"

Fadin Kawu AbdulRashid wanda ke bi wa Malam Abdussalam a haihuwa. Aliyu ya maido akalar tafiyar garesu.

"Gani. Sannunku."

Yanda ya gaishesu kerere ya fi komai baƙanta ransu. Daƙuwa Justice ya wurga mishi.

"Ungo wannan! Yanzu kai tsabar iskanci da rashin kunya mu kake yiwa gaisuwa irin na ƴan iska?"

Nan ya gane kurensa, sai ya durkusa yana shafar suma. Dama ya riga yasan har gobe dattijon haushin sakin da ya yiwa ɗiyarsa yake. Yana cikin farin ciki yau, don haka bai shirya wani abun ya ɓata ransa ba.

"Ku yi hakuri." Ya ce kai tsaye cikin tausasa murya. Banda warin taba ba abinda ke tashi a jikinsa. Sun gaji da magana daya akansa. "Allah Ya shiryeka Aliyu, Yasa wataran ka sauya." Cewar Kawu AbdulRashid ransa na zafi.

Nan Justice ya shiga magana.

"Yarinyar nan mun ji labarin abinda ta aikata, kuma ta yi a bakin duniya duk don ta aureka. Ta yi laifi, ta yi kuskure. Mahaifinta ya damƙa amanarta gareka, da kunnenka ka ji kalamansa."

Aliyu ya gyada kai cikin son tuna abinda Abban ya furta gareshi ranar da ya karbi sadakin Ramlat a hannun magabatansa.

*"Ramlatu amana ce Allah Ya ba ni, yanzu kuma amanar za ta koma kanka. Ban ce lallai sai ka kyautata mata ba, ban kuma ce lallai sai ka yi mata adalci a rayuwa ba, duk wannan hakki ne da ya rataya a wuyanka ko ban faɗa ba. Ka ji tsoron Allah a lamuranka, kar ka manta zai tambayeka duk wani abu da ka aikata a rayuwa."*

Bai mantawa a lokacin murmushi ya yi kawai.

*'Ba dai haka ka so ba Abbanmu. Sai dai ba za ka hana abinda Allah Ya yi ba.'*

Nan take ya ce a cikin ransa.

"Don ubanka ina magana kake dariya? Wane raini kenan?"

Kalaman Justice suka katse tunaninsa, ya ankara da murmushin da yake zabgawa har haƙoransa na bayyana.

"Ayi hakuri." Ya kara fadi.

Kowanne ya tofa albarkacin bakinsa kan ya riƙe amanar yarinya, daga nan ya yi musu godiya ya mike da uzurin Abulle na nemansa. Mahaifinsa ya bishi da kallo gami da addu'ar shiriya. Yaran ka haifa ba ka isa ka saita halayyarsu ba.

Kiciɓus suka yi, ba haka ta so ba. So ta yi da sauri ta bar dakin Abulle kafin ya cimmata. Shigarta dakin Abulle don kai mata goron da ta dauko a dakin Daddynta. Jin Abulle na mitar Aliyun ya zaunar da ita zaman jiransa ya sa ta katse hirartasu ta yi mata sallama ta fito tana sauri ta bar bangarennata. Sai dai kuma ba yanda ta iya tunda gashinan gabanta. Ta daure ta haɗiye komai dake tasomata.

"Ina wuni Yaya Aliyu."

Bai san yana da kunya ba sai a yanzun, ya kauda kai daga kallonta.

"Lafiya. Ya kike?"

Ba tare da ta amsa ba ta wuce da sauri ta yi hanyar kofar sashinsu. Bayanta ya bi da kallo, Muhibbat kenan. Ya sa kai dakin Abulle.

Salati ta shiga yi kafin ta hau yi mishi fadan sigari da ya sha. Taɓe baki ya yi, ya mance da hakan shaf bai jefa alawa bakinsa ba, bai kuma fesa turare ya tsaye a waje na mintoci ba kafin ya hau mota ya tuƙo. Ya mance rabon da ya shigo gidan yana warin taba.

"Wai ni don Allah ki bar kunnena ya huta. Shikenan don kin ji warin abu a jikina sai ya kasance sha na yi? Ko a addini an hana irin wannan yanke hukuncin. Idan ina sha tsawon lokacin nan ba za ki sani ba sai yanzu? Mtsw, Abokina ne ya sha, shi na ziyarta shi ne ƙamshin ya biyoni."

Hakan da ya faɗa sai kuma ta gyara zama ta hau jijjiga kai.

"Kuma fa hakane. To ka kara kiyayewa dai. Raɓar abokai ɓata gari ba naka bane. Na soke abotar. Yanzu dai ya batun lefe? Mahaifinka cewa ya yi na farko an maka, na biyu kai za ka yi. Duk da haka Alƙali da sauran kawunnanka sun ɗan ba ka wani abin ka haɗa ka yi."

Murmushi ya yi.

"Lefen Baby ina son ya fi na kowa. Ina son a bude a kirashi da lefe. Masu yi mata habaici da zagi a kan aurena su daina. Don haka da kaina naji zan hada abina koda ace hakan na nufin karyewar jarina."

Baki sakaka Abulle ta saki tana kallonsa kafin ta magantu.

"Um um dai Zakina, ba za'a yi haka ba. Ƴar dangi ma ba ka ce hakan ba sai akan bare? Ina rabaka fa."

Ya yi dariya.

"Abulle tawa ni kadai, Baby ai ta isa na yi mata komai. Koda kuwa komai nawan zai ƙare a kanta."

Ta taɓe baki.

"Fadi dai sunanta na zahiri, shi zan fi fahimta. Ramlatu ko? To naji, ungo nan."

Ta daga filo ta fiddo damin kudi ta mikamasa. Ya karba ya zura a aljihu.

"Wai nikam me zai hana ka mayar da yarinyarnan ɗakinta ne? Naga dai tsiraicinka yafi rigar aro ta mutane."

Miƙewa ya yi tsam!

"Sai da safe Kakus. Kwanta ki yi bacci abinki. Nima na tafi nawa lissafin."

"Ai fa, ba dama a dauko magana sai ka kauce. Toh har gobe ban ga wata ɗiya da za ka kawo na ji ina sonta a raina ba irin Muhibba."

Daga kafada ya yi alamar ke ta shafa ba kuma tare da ya komai ba ya fice daga dakin. Ko a ransa bai ƙara tada zancen Muhibbat din ba.

*** "Kai Allah Ya rayamana mai sunan Abba."

Fadin Zulaihat kenan cikin waya tana murmushi ranta fari ƙal. Ramlat na daga kicin tana dahuwar indomie ta ji wannan kalamin. Anan ta fahimci sunan Abba ɗan Rafee'ah ya ci. Kwalla suka tarar mata, a yanzu ba ta rabo da hakan. Tunda aka daura aurenta da Aliyu, komai ya daina yi mata dadi. Ba kuma don ba ta sonsa ba, har gobe tana jinsa a ranta. Wuyarta ya kira wayarta ko kuma ta kirashi, za ka ganta cikin farin ciki da annashuwa. Kalamansa masu taushi da dadi, wanda ke nuni da nutsuwa da kuma cikar hankali, sun fi komai yi mata dadi a ranta. Sai dai ba ta nufin ta rabu da yan uwanta a dalilinsa, duk suna amsamata idan ta yi magana, sai dai irin amsawar da gwamma kar su yi. Babu fara'a babu sakin fuska. Sama-sama suke amsawa kamar ba sa so.

An kwaso kayanta kaf a gidan Hilal, a daren jiya ya zo har gidan ya riski Abba a falonsa. Sun jima suna magana sannan ya tafi. A hirar Zulaihat din da Hajiya ta ke jin cewa hakuri ya ba shi. Hakuri bisa sakin ƴarsa da ya yi.

"Ke wane rashin hankali ne za ki kunna gas har abu ya ƙone haka? Gobara kike son jazamana? Ko mu dinma kashemu za ki yi?"

Ta waiga ta dubi Zulaihat s'ilin da ta sanya hannu ta kashe gas din.

"Hajiya ta ce ki yiwa Mijinki magana za'a je a yi jere don Abba ya ce a satinnan za ki tare. Ya kawo muƙulli."

Tana kaiwa karshe ta fice a kicin din, kawai sai Ramlat ta fashe da kuka. Haka to za su ci gaba da yi mata?

Indo ta risketa tana kuka, ganin ta dage wurin rarrashinta duk kuwa da haushinta itama ta ke, ya sa ta daukar wayarta ta bar kicin din. Abincin da ba ta ci ba kenan.

*** Akwati takwas cif Aliyu ya shaƙe da kaya na gani na faɗa. Yakasai gidan su Hajja aka kai lefen kamar yanda Abba ya bada umarnin a yi.

"Anya Rabi'atu wannan yaron ba ya cin haram a aikinsa? Wannan wane irin kaya ne ya shaƙowa yarinyarnan?"

Hajja da mamaki ya kasheta a zaune ke wannan furucin cikin waya ga Hajiya. Hajiya ta yi murmushi mai ciwo.

"Ko ya ya dai Hajja ai ita yarinyar ta fi kowa sanin yanda aka haihu a ragaya. Tunda ya kawo lefe an karɓarmata shikenan. Ta je ta yi ta sakamishi."

"Kai Rabi, na rabaku da irin wannan fushin fa. Meyasa Khalid ya biyewa yarinyarnan bai yi bincike ba? Har da gwal a sarkokin."

"Hajja ina zuwa zan kiraki."

Hajiya na fadin hakan ta katse kiran. Ba wai don abin bai tayarmata da hankali ba, sosai hankalinta ya tashi. Yaron da aka ce a kasuwar ma ba wani mayar da hankalin a zo a gani yake ba. Ba ta son tunkarar mijinta da wannan batun, don ta lura yana cikin damuwar auren Ramlatun har lokacin. Wannan ta sa ta kira Munir. Kafin ma ta yi nisa ya katse zancen.

"Hajiya ke mahaifiyata ce. Don girman Allah kiyi hakuri ki bar min zancen Ramlat. Hajiya ki zubamata ido tunda kun mata abinda take so. Ku yi hakuri ku bi ta da addu'a idan da bukatar hakan. Ba ita kadai ku ka haifa ba, muna raye zamu share kukanku. Ki yi hakuri, ki sanya a ranki hakan ya zama alheri ba sharri ba."

Da wannan ya samu ya zame kansa daga abinda Hajiyar ta kawomishi, na bincike akan harkar Aliyu.

'Wane bincike bayan mai afkuwa ta afku? Komai ta fanjama fanjam!'

Ya fadi a kasan ransa.

*** "Ai yanzu kin girma, kin mallaki hankalin kanki, ba kya bukatar nasiha daga gareni. Duk abinda kika aikata ga rayuwarki daidai ne."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull