Karfen kafa complete rufaida omar - Chapter 18
Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 18: Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 18. Ya ƙarashe gami da watsawa G Baba harara. Shi kuwa G Baba ya…
3,355 words
Ya ƙarashe gami da watsawa G Baba harara. Shi kuwa G Baba ya kara yarda da irin son da Aliyu ke yiwa Ramlat. Ya tabbata shi ya shafi abinda ke cikinta. Aliyu kaifi daya ne idan ya ga dama, idan har ya yi irin tsaurinnan to ba mai juyamishi ra'ayi wannan ta sanya ya ja bakinsa ya wayance da yi mishi kirari hadi da fadin.
"Ko ba komai ai ma zo mu ƙarawa sama ado."
Suka cafke gami da wata irin dariya.
*** Ramlat zamanta ta yi a dakin bayan ta idar da sallar La'asar da ba ta yi kam lokaci ba. Tana jin yunwa, sai dai ba ta kaunar ganinsu. Kwantar da kai ta yi a saman hannunta jikin gado tana daga zaune saman darduma, tunani mai zurfi ta faɗa gami da riƙe cikinta. Har sannan tana kara jinjina lamarin, wai ciki ne da ita.
'Cikin mashayi.' Wani bangare na zuciyarta ya ayyana mata, ta jima anan zaune har wahalallen baccin da ba ta samu yinsa da safe ba ya soma fisgarta sai dai cikinta na ta ƙara saboda yunwa.
A hankali ta ji hannu saman fatar cikinta. Firgigit ta bude idanu, Aliyu ne durkushe ya daga rigar yana shafa cikin. Suka hada ido, murmushi ya sakarmata. Ita kuwa warin sigari ke tayarmata da zuciya don haka ta mike da sauri ya riko hannunta gami da miƙewar shima.
"Baby lafiya?"
Ta rufe baki da hancinta da hannu ta shiga tureshi tana girgiza kai.
"Don Allah ka fita, warin taba, zan yi amai wal..."
Yunkurin aman ya katseta, da sauri ta faɗa banɗaki shi kuwa ya fita daga dakin. Ba wani abin kirki ta amayar ba, ta wanke baki ta fito, ganin baya dakin yasa ta daukar turare mai sanyin kamshi a bakin madubi ta ɗan fesa a jikin wani dan handkerchief ta toshe hancin sannan ta bude winduna dakin.
Kiraye kirayen sallar Magriba ne ya sa ta mike ta zura hijabinta. Sai da ta yi sallah sannan ta mike ta nufi falon don Aliyun ya shigo har sau biyu kafin ta idar. Maimakon ƙamshin sigari, sai ta ji ƙamshin turaren wuta. Ba kowa a falon hakan ya bata tabbacin Aliyun ne ya kunna. Ta saba duk sadda ya gama busa hayaƙinsa za ta yi azamar daukar kaskonta ta kunna gawayi ta saka turare. Sai ta ji hakan da ya yi ya burgeta, kaso hamsin na damuwarta ya yaye. Sai a sannan ta ci dora abinci mai saukin dahuwa ta ci, ta shiga karatu.
*** Washegari da ɗokinta ta fita daga gidan. Aliyu ne ya kai ta saman mashin dinsa. Koda ta shiga Malami ya shigo basu sami damar gaisawa da Amrah ba sai dai wannan karon sun samu zama wuri guda. Ana tashi, kowa ya fice daga ajin suka yi zamansu.
"Mai ciki ba za ki ci komai ba? Rana fa ta yi." Fadin Amrah cikin murmushi. Harararta ta yi sannan ta ja guntun tsaki. "Ni har tsoron haihuwar ma nake."
"A gidan Aliyun ko kuwa me?"
Tasan Amrah da biyu ta yi tambayar, ba kuma ta so ta bada kofa yanzu Amrah ta san sirrin gidanta. Ta fi kaunar Amrah ta dawo da tausayi da kaunarta a zuciya kamar dai a baya.
"A'a, kada na mutu wurin haihuwa."
Dariya Amrah ta yi.
"Sai kuma aka fadamaki haihuwar ƙarar kwana ce? Addu'a za ki yi, In sha Allah za ki haihu lafiya. Af, ga saƙon Umma ma. Ta cemin ki dinga shan kayan marmari da abinci lafiyayye. Kar kuma ki yawaita daukar abu mai nauyi. Kuma wai ko nan gaba za ta aikomaki mene? Oho na manta. Ta ce dai na miki albishir tana nan zuwa."
Dadi, farin ciki da annashuwa suka cika zuciya da fuskar Ramlat. Daga washe haƙora tana dariya sai ga hawaye na fita. Hawayen tana da wata uwa da ba ita ta haifeta ba, amman ta tuna da ita. Tana kokarin ba ta kulawa irin ta uwa.
"Meye abin kukan?"
Fadin Amrah da ke jin zuciyarta itama na neman karyewa. Ta daure ta tattaro dauriyar wuri guda, ta shiga zolayarta.
"Oh, wa ya ga Ramsy da ɗa? Naga yanda za ki yi raino. Wai har ki shayar."
Ta ƙarashe gami da sanya dariya, itama ba ta san sadda ta dara ba ta hau share fuskarta.
"Kema ai kamar yau ne."
Taɓe baki Ramlat ta yi.
"Ni da aure sai na kammala karatu in Sha Allah."
Murmushi Ramlat ta yi kafin su taɓa hira, so take Amrah ta jefomata tambayar da ta shafi gidanta ko dangin mijinta, sai dai ta lura kokarin kaucewa hakan ma Amrah ke yi. Don haka itama sai ta kara rufe cikinta ba ta kaunar su sami wata matsalar.
*** Bayan sati biyu hankalin Ramlat a kwance, za ta yi waya da Abbanta da kuma Hajiya wacce a sannan ta ɗan sassauta kadan. Umman Amrah kuwa kiranta take sosai su yi hira ta yi ta kwantar mata da hankali. Ta dauketa kamar ƴar da ta haifa a cikinta. Bangaren Aliyu, ya rage zuwa ya yi mata shaye-shaye a gida kamar yanda ya daina shigomata a buge. Hakan ya kara kwantar da hankalinta ba kaɗan ba. Abinda ke yawan bata mamaki ya daure mata kai, banda Abulle babu wani ko wata a dangin Aliyu dake zuwa gidanta, zargin ba sa kaunarta ya kara tabbata a kansu. Don haka ta ja jikinta ta kama kanta. Hakan bai hana ta kira mahaifin Aliyun ta gaidashi, shi kam lafiya sumul yake amsamata.
A yammacin juma'a ta fito falon bayan ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando Pakistan. Tashinta daga bacci kenan bayan ta dawo daga makaranta. Kicin ta shiga ta hau kiciniyar yin tuwon semo da miyar kuka kasancewar hakanan ta ji tana sha'awarsa. Sai dai me? Babu gas.
"Ya Salam." Ta furta a fili. Jiki a sanyaye ta fito falon tana jan tsaki, waya ta dauka ta lalubo lambar Aliyu ta kira.
"Kamar ya babu gas? Har gas din gidan ya ƙare?"
Shi ne tambayar da ya jefomata bayan ya saurari bayaninta. Ta ciji leɓɓanta ta kasa cewa komai. Sai kuma ta ji ya ja tsaki kafin ya ce.
"Nidai wallahi banda kudi, kema kin sani kuma. Yanzu haka ganinan wani banza dan gin..."
Kiit, ta katse kiran, a duniya ta tsani ta ji yana ashariya. Abin na ƙona ranta.
"Allah Ka shirya." Ta firta a fili, ita kam yunwa ta ke ji don haka ta mike. Ta tuna da lemun da ta gani Aliyu ya ajiye a fridge da safiyarnan, sadda aka kawo wuta. Ta soma shiga kicin ta dauko ragowar bireda ta fiddo lemun. Tun kafin ta ƙaraso ta bude ta shiga kwankwada. Sosai ya yi mata dadi. Tana zama ta hau tauna biredin, idanunta na kan wayarta dake ƙara kuma sanin Aliyun ne ta ƙi ɗagawa. A hankali kuma ganinta ya soma zama dishi-dishi. A kokarinta na ajiye robar lemun saman Centretable sai ya zube a ƙasa.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Mene haka?"
Ta fadi cike da karfin hali. Ita ta san me take ji. Jirin na kwasarta, yana kokarin fitar da ita daga hayyacinta. A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ta danna. Cikin muryar ƴan maye ta soma magana.
"Aaaaaliiii."
Ba ta ji me yake cewa ba ta wurgar da wayar, ta mike ta na tafe tana rangaji da zagaye falon, ba ta yi aune ba ta ci uban tuntuɓe da takalminta ta bugi gefen mararta da tv stand ta zube anan. Duk da ba'a hayyacinta take ba sai da ta saki ƙara.
*** A hargitse ya banko kofar falon ya shigo. Kallo ɗaya ya yiwa robar lemun ya san abinda ke faruwa. Jijjigata ya soma.
"Baby! Baby! Ramlat!"
Ya rasa na kira, cak ya ɗagata ya fita. Ba kuma zai yiwu ya sanyata a mashin ba, dole ya dawo da ita ya fita ya taro ɗan sahu suka bar gidan zuwa asibiti.
*** "Ka yi hakuri, cikinta ya riga da ya zube."
Bayanin Dr Lamin kenan bayan ya gama faɗawa Aliyu cewa a jininta da aka auna an samu tabbacin ta sha kwaya mai ƙarfi, ya kuma yi faɗan meyasa ya bar ta yin shaye-shaye duk kuwa da sanin da ya yi tana da ciki. Ga mamakin shi kansa Aliyu ya kasa cewa komai, har Likitan ya yi faɗa ya kammala. Batun zubewar cikin ya fi komai ɗagamishi hankali. Idanunsa suka kaɗa.
'Ko mene laifinka ne ai! Da ba ka ajiye a gidan ba, ta ina za ta gani ta dauka tunda ba halinta ba ne!'
Faɗin wani sashi na zuciyarsa.
*** Awanni kaɗan bayan farfaɗowarta ya shiga. Ta ɗago idanu ta dubeshi sai ta soma hawaye. "Kaga abinda halinka ya jazamana ko?" Ya zaune gami da riko hannunta.
"Laifinki ne, meyasa ba ki ɗaga wayata ba ina ta kira? Tunawa nayi na ajiye a fridge shiyasa na so na gargaɗeki."
Ta kauda kanta kawai, cike da bakin ciki. Abin kunya sanadin shaye-shayen mijinta, cikinta ya zube.
"Kaicona." Ta furta a fili, sai kuka. Kewa, kewar iyayenta take. Don haka ta juyo ya dubeshi.
"Bani wayarka."
"Ki yi me?"
"Abbana zan kira."
Ya daure fuska.
"Ki ce mishi kin sha abin maye cikinki ya zube? Asirinmu za ki tona? Dama ya lafiyar giwa ballantana an jefeshi da kashi? Toh ki je ki gwada tona asirin namu. Naki ne zai fi wari, ni dama ba ganina suke da gashi ba."
Daga haka ya mike ya sa kai ya fice a zuciye. Ta bishi da kallo, wani malolon abu ta ji ya tsayamata a maƙogwaro. Tana jin haushin irin kalaman da Aliyu ke yi akan iyayenta. Ko ba komai iyayenta kuma su suka haifeta. Dole ta takawa abin burki.
'Kin manta ke kika bada ƙofa.' Cewar wani bangare na zuciyarta, hakan sai ya karyarmata da gwuiwa. Ta yi shiru ta soma hawaye. Tana jin haushi da tsanar kanta akan duk abinda ya faru tsakaninta da yan uwanta, a gefe guda kuma don Aliyu ya zama kamar bugun numfashinta wanda ba ta jin za ta iya rayuwa babu shi. Sai dai kuma hakan ba zai hana ta janyo ƴan uwanta jiki ba, ta dinga ziyartarsu koda ba su zo mata ba. Ta kudurta sauya takunta tun kan abu ya yi nisa.
*** Sai da ta yi kwanaki uku aka sallameta daga asibiti. Shi ne lokaci na farko da ta ga matan mahaifin Aliyu a gidanta da sunan dubiya. Ba su kadai ba, har su Abulle da Mamar Muhibbat sun zo. Kana ganin fuskokin za ka san dole akai musu.
"Ikon Allah, kema dai ina ce ba shi ya jawomaki ɓarewar cikin ba?"
Cewar matar Malam (mahaifin Aliyu) ta farko, Atine.
"Wane zancen banza ne haka ke Atine? Wa kike nufi da ɓarar da ciki? Au dama sharrin da za ku yiwa Zakina kenan?"
Fadin Abulle cikin masifa. Wannan yasa Atine fadin
"Allah Ya ba ki hakuri Baba."
Abulle ta yi kwafa. Ramlat dai tana zaune ta dukar da kai a saman kujera don Abulle ta hanata zama ƙasa.
Sun jima a gidan don har sai da Abulle ta saka yanmatan jikokinta su yiwa Ramlat girki a risho. Haka suka shiga suna kunkuni. Har gobe ba sa kallonta da gashi, Muhibbat ce tasu. A karshe kowa ya watse aka bar ta ita daya ta yi ta godiya kuwa.
Komawa ciki ta yi ta ga yanda suka yi kaca-kaca da kicin din, ta kuma sani da biyu suka yi hakan. Haka ta daure ta kimtsa ko'ina. Tana jin sadda Abulle ke cewa Zalihat diyar Atine ta zauna ta kwana biyu yarinyar ta yi kememe uwarta na turata ta fice ta shige mota. Murmushi ta yi mai ciwo. Ta dauki waya cike da so da kewar iyayenta ta dannawa Hajiya kira. Ringing uku ta ɗaga da sallama.
"Hajiya." Ta fadi a raunane zuciyarta a karye.
Daga dayan bangaren Hajiya ta ji gabanta ya fadi, ta daure. Kwanakinnan da tunanin Ramlat take kwana da tashi. Tun sadda aka ce ta yi ɓari ta kira Zulaihat da Rafee'ah akan su shirya su je. Yanzu kam sun amince zasu je bisa umarninta.
"Ramlatu, ya gida? Ya jikinnaki?"
Wani sanyin dadi ya saukarmata a zuciya. Yau ne karon farko da Hajiyar ta kira sunanta ta kuma bata kulawar da ta dace.
"Jikina da sauki Hajiya. Hajiya yaushe za ki zo? Ki yafemin don Allah Hajiyata."
Kukan da take riƙewa ta shiga yi.
"Hajiya kin yi shiru. Hajiya ki yafemin."
"Na yafemaki Ramlatu, na yafemaki duniya da lahira. Ki kwantar da hankalinki. Ki bi mijinki, Allah Ya yi maki albarka. Gobe yayyanki zasu zo."
Rasa kalar farin cikin da za ta yi ma ta yi. Sai ga ta nan tana dariya. Suka yi sallama da Hajiyar ranta fari sol. Ta ɗago kai kenan ta hada ido da Aliyu. Yana jingina kansa cikin bangon falon yana zuƙar taba da fesarwa. Ganin ta kammala wayar ya tako ya zauna gefenta.
"Su waye zasu zo?"
Ta mance da batun wani sigari ko warinsa, rungumeshi ta yi sosai cike da farin ciki ta amsa.
"Tayani murna, Hajiya ta yafemin, ga Anti Zulaihat da Anti Rafee'ah zasu kawomin ziyara gobe."
Ga mamakinta sai ta ji ya ja tsaki. Ta ɗago tana kallonsa.
"Da yake ba ki da zuciya ko? Duk irin rashin kaunar da suka nunamana akan wani banzan Hilal bai ishemu ba? Wane irin kalamai ne ita Zulai din ba ta ce a kaina ba? Ita kuwa Rafee'ah wato tsabar tsana har.."
"Ya isheka! Ya isheka!!" Ta tsinci muryarta da fada, bakinta da kakkarwa, jikinta da rawa. Ta miƙe tsaye kyam da ƙafafunta. Idanunta a rufe cike da masifa!
Kallonta kawai yake yana zuƙa da fesarwa, maimakon ɓacin rai, murmushi yake, murmushi sosai har da dora ƙafa daga saman Centre Table.
"Ƙarya nayi?"
Shi ne abinda ya furta.
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
19)
Dakin ya yi shiru, ba ka jin komai sai sheshshekar kukan Ramlat. Abba jikinsa ya yi sanyi jin abinda Aliyun ya aikata ga ɗiyarsa. Ga duka ga kuma kwatar dukiyar da ta ke mallakinta a yanzu.
"Wannan yaron anya zai zo?"
Fadin Dakta wanda ransa ya soma ɓaci da shirgasu da Aliyu ya yi. Abba shima nashi ran a ɓace yake.
"Ka rabu da shi Dakta, idan ma bai zo ba, za ta koma. Kawai dama so nake ya zo din don na gargadeshi akan duka, ba jaka ba ce."
Hajiya dai banda uhm ba abinda ta ce. Ita kuwa uwar gayyar yanzun ma kukan ya kasa fita, ta yi shiru kawai tana kallon kafet da kumburarrun idanunta.
Har aka kwashe awa daya, Dakta ya mike ya yi musu sallama zuwa wurin aikinsa. Shima Abba ya mike ya shirya ya fita.
"Duk abinda ke faruwa ke kika jazawa kanki Ramlatu! Gashinan tun ba'a je ko'ina ba kin fara girbar abinda kika shuka. Kin bude baki kin nunawa namiji ƴan uwanki ba sa sonsa, kin jawowa kanki da kuma iyayenki raini. Kin kafe akan ke lallai sai yaronnan, yanzu ai gashinan auren da ba'a shekara ba an soma jibgar Amarya. Ban kuma san me zan ce ba."
Hajiya ke maganar a zafafe, sai kuma ta miƙa ta bar falon ranta na ƙuna. Ramlat ta yi shiru tana tauna maganar Hajiyar. Tabbas ko me ya faru ita ce silarsa. Wani duka, zagi, cin mutunci da akai mata kafin aure, ba wanda ba ta faɗa wa Aliyu ba. Asalima shawararsa ta ke bi ta aikata duk abinda ta aikata.
'Shi yana zagin nasa ƴan uwan a gabanki banda iyayen Muhibbat da suka ɓata ransa?'
Faɗin wani bangare na zuciyarta, tabbas ta sani, ko batun ƴan uwansa za ta yi, zai ce ba ya so. Ta sharesu tunda shi za ta aura. Ba su damu da shi ba, amman shi kam bai yarda an wulakantasu ba. Sai ita ce wawuya ta saki baki har ya rainamata ƴan uwa?
Sai a sannan ta ji hawayenta sun zubo.
"Na yiwa kaina illa da kaina."
Ta furta a fili, dakyar ta mike ta shige tsohon dakinsu wanda yake mallakin A'isha a yanzu. Kwanciya ta yi tana tunane-tunanenta kafin wahalallen baccin ya kwasheta.
*** "Tana gidansu!" Ya fadi cike da tsawa ganin Abulle na neman takura mishi da tambaya. Ita kuwa gani ta yi daren jiya da kuma safiyar ranar duk a gurinta ya ci abinci.
"Idan ma abincin naki ne ba kya son na dinga zuwa ina ci ai shikenan, sai na zauna na mutu kowa ma ya huta. Komai Aliyu! Komai Aliyu! Ƴan uwannawa ma ba sona suke ba, da Ni mai arziki ne bibiyar da za'a dinga yimin ba kaɗan ba."
Abulle dai ta kama bakinta ta yi shiru jiki a sanyaye. Ta gane yau ran Zakinnata a ɓace yake. Sai da don kansa ya ci gaba da shan shayin da biredi da kwai sannan ta soma magana a nutse cike da rarrashi.
"Allah Ya huci zuciyar Gadanga ƙusar yaƙi. Haba Zakina, mene abin fushi don nayi tambaya? Abin bai kai nan ba ka ji, ba wanda ba ya sonka, halinka suke cewa sun tsana wannan ma nasan don ba su baka damar kun zauna tare ba ne. Ita kuwa Ramlatu me ya yi mata zafin da har ta tafi gidansu?"
Ransa ya ɗan sosu, idan yace bai yi kewar matarsa ba toh wannan karya ne. Yana son Ramlat, irin son da bai yiwa wata mace ba. Haushin da ta ba shi akan me ba za ta taimaka mishi lokacin babu ba. Yana sane ya ƙi zuwa gurin iyayenta, tsoro yake kar ace ya saketa, shi kuma ko sama da ƙasa za ta haɗe bai ga wani dan adam din da zai sa ya saki matarsa ba.
"Hutu na ba ta, za ta dawo."
Abinda ya cewa Abulle kenan, ganin za ta matsa ya mike ya mata sallama ya wuce.
A kofar gidan suka yi kiciɓus da Malam mahaifinsa.
"Kai zo nan."
Ya karasa ya ɗan russuna yana cin magani.
"Meke faruwa ne kai da iyalinka? Mahaifinta ya kirani akan yana son ganinka."
Ya kara tamke fuska.
"Ba abinda ya faru, anjima zan je."
Malam ya yi shiru yana dubansa, yana son yaron, halinsa ya tsana. Girgiza kai ya yi. Da alama shima da nashi kuskuren, ko kusa ya watsar da lamarin Aliyun ba ya ta tashi sam. Ya fi bada kulawarsa ga ƙannensa.
"Aliyu ka ji tsoron Allah a lamuranka. Wannan yarinya amana ce ta Allah a hannunka. Duk abinda ka yi mata ka sani Allah sai Ya tambayeka. Har sai yaushe za ka gyara halayyarnan taka ka zamo abin so da kauna ga kowa a dangi? Aliyu ba fa kai muka tsana ba, halayyarka ce ba ma so."
"Toh Malam don ba kwa so ai hannunka dai ba zai ruɓe ka yar ba. Addu'a za ku ci gaba da yi mini."
Takaicinsa ya kama Malam, haka yake. Ba dai a yi magana bai maida martani ba.
"Shikenan addu'a ko? Za mu ci gaba da yi, za kuma mu ɗora akan wanda muke yi. Yanzu dai don Allah ina rokonka, don yanzu ka fi karfin na umarceka, ka je ka taho da matarka. Ka dawo da ita ɗakinta. Duka-duka yaushe aka yi auren? Shikenan za'a soma ƙirgamaka aure?"
Ya shafi ƙeya, ko ba komai yau Malam din ya fadi kalamai masu nuni da sassauci da kuma kwantar da hankali a gareshi. Ba kamar yanda ya saba haduwa da ƴan uwansa su yi mishi caa ba. Sai ya tsinci zuciyarsa da yin sanyi kadan.
"Zan je anjima idan na tashi daga kasuwa."
Murmushi Malam ya yi.
"Ko kaifa, Allah Ya shiryeka. Ya yi maka albarka."
Ya amsa da amin, ya mike ya tafi. Ya manta rabon da maganar arziki ya shiga tsakaninsa da Malam din.
*** Tana daki ta yi jugum tana tunanin yanda ta yi fashin makaranta. A gefe guda Aliyu ne a ran, tunaninsa da kuma so da kauna su ke addabar zuciyarta. Ta yi kewarsa ba kaɗan ba. Don Aliyu wata jarrabawa ce daga Allah wanda ba za ta iya tsallakewa ba. Mutan gidan ba laifi sun sakarmata musamman Abba.
A ranar misalin biyar na yamma ta ji Abba na fadin Aliyu ya zo. Gabanta ya fadi. Ta koma cikin daki ta zauna bakin gado, can kuma sai ga A'isha ta shigo tana kallonta a fisge.
"Ki zo inji Abba."