Kenza eBookz

Karfen kafa complete rufaida omar - Chapter 48

Karfen kafa complete rufaida omar - Chapter 48

Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 48: Karfen kafa complete rufaida omar Chapter 48. Lokacin tana gida ta hargitse tana jiran shigowar Hussein don…

3,366 words

Lokacin tana gida ta hargitse tana jiran shigowar Hussein don su bar garin zuwa wata Jahar kafin lamura su kwaɓe. Ga dai tana ta kiransa ya ƙi ɗagawa. Lokacin ne kuma kiran Chairman ya shigo, kamar ba za ta ɗaga ba a farko, sai dai ta ɗaga.

"Nikam Zeenat, mijinki Hassan da Husseini ne?"

Ta saki rigar Hussein da ta ke shirin sanya wa a akwati. Gaskiyar Gora kenan da yace su na tare?

"Lafiya? Kin yi shiru?"

"A ina ka gan su?"

Daga amsar ya fahimci ruɗewarta. Kai tsaye ya ce.

"A asibiti na je duba Amaryata Ramlatu, kinsan harbinta aka yi. Shi ne na tadda su a ɗakin. Sai wani hararata yake yi kamar na kashemasa wani. Na yarda da zarginki, son yarinyarnan yake kuma kwalalensa."

Tusa Hajiya Zeenatu ta saki wanda ya tahomata da guntun kashi. Ta sharce gumi ta hau safa da marwa.

"Yanzu a can ka baro su? Wane asibitin?"

"Zan miki ƙarya ne? Nawa za ki ban idan na miki ƙaryar? Idan kina son ganewa idanunki ki taka ki je."

Ya sanarmata asibitin, ba ta jira komai ba ta katse wayar. Banɗaki ta shiga ta sauke nauyin cikinta, ta kimtsa jiki sannan ta fito. Sun rabu da Hajiya Batool akan zasu haɗu su je wani ƙauye domin a yi musu aiki maikyau. Sai dai ba ta jin za ta jure wanzuwar Ramlat a doron ƙasa, za ta sa a karo na biyu a kashemata ita. Duk abinda zai faru sai dai ya faru.

Ta fice daga gidan gaba ɗaya.

*** Chairman da tun bayan kammala wayarsu da Zeenatu ya yi shiru yana tunani.

"Ina maka rantsuwa da Allah zan sa a kashe Ramlatu idan ni ban kashe ta da hannuna ba muddin ta yi kuskuren shiga rayuwata da mijina."

"Dakata!" Ya ba direba umarni, ganin haka direban ya ja ya yi parking a gefe.

Chairman ya fidda waya ya ƙara kiran Hajiya Zeenatu, yana ta ringing ba ta ɗaga ba. Haka ya yi ta dialing shiru, don haka ya yi saurin cewa direban ya mishi magana da daya daga cikin abokan tafiyarsa. Da sauri direban ya fita zuwa ɗayar motarya kira.

"Sir."

Chairman ya dube shi.

"Ku juya ku koma asibitinnan, ku tabbatar kun kula da marar lafiyarnan. Ina zuwa."

Ya hau lalube cikin hotunansa har ya fiddo hoton Hajiya Zeenatu a wajen wani taron biki da suka hadu. Koda wasa ban yarda ku bar wannan matar ta shiga dakin ba."

Ya jinjina kai cike da girmamawa ya karbi odar ya koma motarsa. Motar Chairman ya wuce su kuma suka juya zuwa asibitin.

*** Hussein ya yi shiru kawai yana kallon Halima wacce har sannan ta ƙi faɗar gaskiya. Sai ka rantse hankalin a kanta yake, amma ina! Zuciyarsa na wani ɓangaren, sai hura hanci ya ke yana ƙara cin magani. Garin Kanon ta fita ransa, so yake su juya tare da ɗan uwansa kawai. Sai dai kafin nan yana son nunawa Hajiya Zeenatu kurenta. Yana son maka ta a kotu yanda za ta fuskanci fushin hukuma, duniya kuma ta san da abinda ta aikata.

Wayar AlHassan ta yi ringing, gani Dada sai ya yi murmushi ya fita daga station din. Hisham ya ɗan daki kafaɗar Hussein kaɗan, dubansa ya yi kawai ya watsamasa harara ya kauda kai.

Dariya sosai Hisham ya yi.

"Ikon Allah, to ni kuma me na yi? Nasan fa me ke cin ranka"

Hussein ya gyara tsayuwa gami da ɗan lumshe idanu bai ce uffan ba.

"Kar ka yiwa kanka saki na dafe, tun kafin lokaci ya ƙuremaka gwara ka faɗamata abinda ke ranka."

Ya dubi Hisham.

"Me kake nufi? Kuma wa kake nufi?"

Hisham ya bude baki zai magana ya ɗaga mishi hannu.

"Malam bana son shirme, yimin shiru. Kai a komai sai ka sanya wasa da zolaya. To ka fita idona."

Dariya sosai ya ba Hisham. Daidai sadda AlHassan ya dawo ya dubesu yana dariya.

"Lafiya dai? Tom and Jerry?"

Murmushi kawai Hussein ya yi.

"Dada ce?" Ya tambaya. Gyada kai AlHassan ya yi yana murmushin shima.

"Yes, ita ce. Sai dai ban fadamata komai ba, na dai ce ina tafe da wani babban albishir."

Jinjina kai Hussein ya yi.

"When? Nima na ƙagu na gan ta."

"Very soon in sha Allah."

"Maiduguri fa?" Cewar Hussein kamar zai yi kuka.

Dariya AlHassan ya yi.

"Duk za mu je da yardar Allah. Saboda rashinka na ɗauke ƙafa, ganina yana sa Hajjo kukan tunawa da kai. Wannan ta sa tsakaninmu sai waya."

"Ina son hukunta ta." Hussein ya fadi zuciyarsa na zafi, fuskar Hajiya Zeenatu ya ke haskowa da kuma cuɗanya iri-iri da ya yi tare da ita.

"Muje daga waje please. Nan ba wurin tattauna wannan zancen ba ne."

Suka dubi Hisham mai magana, su ka maida hankali ga Halima da ta yi musu ƙuri da kumburarrun idanunta. Duk hirar da ake yi tana ji, kalaman Hussein na ƙarshe ya sa tsoro ya ƙara kamata. Kada dai ita yake nufin a hukunta? Ita kam ta shiga uku. Ba ta mance shawarar da kaninta ya ba ta ba da ya zo.

"Idan kinsan ba da gaske kike ba Yaya Halima, ki fito ki fadi gaskiya kafin lokaci ya ƙuremaki. Nidai gaskiya ban yarda da abinda kika faɗamin ba."

Ta share hawaye tana ci gaba da kokwanto a ƙasan ranta. Ta faɗa ko kuma ta yi shiru? Ita kanta ta rasa wanne za ta zaɓa. Har suka fice tana kallonsu. Ta bi wurin kwananta da kallo, ta ja majina. Anya Hajiya Zeenatu dagaske ta ke za ta cire ta a wannan taskun? Shiru ta yi, karshe ta yanke shawara ta aika ƙaninta wurin Hajiya Zeenatu ya yi mata bayanin halin da take ciki.

*** Ramlat ta yi shiru, ita kadai a dakin, su Rafee'ah sun wuce, sai Hajiya dake bandaki ɗauro alwalar sallar Azahar. Nos Khadija ta kwankwasa ta shigo tana jan kayan dressing din ciwo a ɗan keke. Suka yiwa juna murmushi. Ɗan zaman da ta yi a asibitin sun saba, mace ce mai kirki.

"Su kuma waɗannan ƴan sandan da aka zubamana a bakin ƙofa fa? Da alama dai Angonnaki na baki kulawar da ta dace."

Wannan ne karon farko da ta ji haushin Nos Khadija, sam ba ta son abinda za'a haɗa ta da Chairman. Tun kafin su Munir su tafi, suka zoda zummar tsareta bisa umarnin ubangidansu. Har ta soma faɗa Munir ya ce ta rabu da shi kawai. Shi ya sani. Taɓe baki ta yi ba ta ce komai ba. Daidai sadda Hajiya ta fito, suka gaisa da Nos Khadija gami da yin ƴar raha don mace ce mai tsokana da kuma ja da wasa. Tana cire Bandage din kafadar suna ta hira abinsu, bayan ta goge ta ƙara rufewa sannan ya dubi Ramlat jin Hajiya na faɗan ba ta son cin abinci.

"Ki dinga cin abinci don Allah Ramlat, haba yar uwa, ina yabonki? Ki ci yanda idan na ba ki magani ba zai sanyaki jiri ba. Yanzu zan dawo."

Ta gyada kai ba don ta so ba, ita kawai komai ma ba dadi ya ke mata.

*** Hajiya Zeenatu tunda ta doshi barandar ɗakin da Ramlatu ta ke ta hangi wasu masu kayan ma'aikata tsaye a bakin ƙofar ta yi turus. Wuƙar da ke cikin jakarta yasa ta kasa ƙarasawa, juyawa ta yi tana tunanin ina mafita? Ta ya za ta cimma burinta? Yanzun ta tabbatar Hussein ba zai kara yi mata kallon mace mai daraja da ƙima ba a idanunsa, amma tabbas idan ta bar Ramlat na yawo a doron ƙasa tofa shakka babu, wataran za ta ji batun aurensu. Abinda ba za ta taɓa ɗauka ba har abada. A kan idanunta, Nos Khadija ta shiga, hakanan a kan idanunta ta fito. Wata dabara ta faɗomata don haka koda Nos Khadija ta zo wucewa ta wurinta ta saki fuska sosai suka gaisa.

"Nace don Allah idan babu damuwa, ina son ganinki."

Nos Khadija ta bita da kallo, a shekaru ta girme mata sosai hakanan kuma ba ta yi mata kama da wacce ta fito daga ƙaramin gida ba.

"Shikenan, ba ni minti biyu."

Hajiya Zeenatu na murmushi ta gyada kai. Ba jimawa Khadija ta dawo suka ɗan fita waje.

Shiru Khadija ta yi tana jin bayanan Hajiya Zeenatu. Kirjinta ya shiga dukan uku-uku.

"Ki sani, wallahi-wallahi duk wani jin dadi na rayuwa kin sameshi kin gama matukar kika yimin aikin da na sanyaki. Zan ba ki duniya iyakar ƙarfina. Za ki taka duk ƙasar da kike so, za kuma ki shiga duk inda kike so a faɗin garinnan ba wanda ya isa ya ce maki don me?"

Jikin Khadija ya ɗauki wani irin rawa. Tunda take a duniya, tunda ta ke, ba ta taɓa jin lamari irin haka ba. Wani irin tsoron da ba za ta iya misaltawa ba ya shige ta. Daga yanayinta Hajiya Zeenatu ta gane babu nasara don haka ta bude jaka ta fiddo bandiran kudi ƴan dari biyar guda biyu ta miƙamata, Allah Ya taimaka babu jama'a a wurin, ta ɗago mata lafiyayyar wuƙa sabuwa fil ta nunamata.

"Ki zaɓi ɗaya Hajiya Khadija, idan ba haka ba ni da kike gani don na kasheki ba komai ba ne a wurina. Sai na ɓatar da ke da ma ƴan gidanku. Don haka zaɓi ya rage naki, na baki nan da awanni biyu, duk abinda kika yanke ki kira ki sanarmin. Kar ki manta rayuwarki a tafin hannuna yake."

'Ƙarya kike, Allah ne Mai iko da rayuwakanmu.' Nos Khadija ta fadi a fili don ba ta jin tana da kwarin gwuiwar faɗa a zahiri. Ta gyada kai kawai a fili, ta karɓi kudin ba don ta so ba ta zura a aljihun wandonta.

"Ina tsumayenki. Ga lambar wayata." Hajiya Zeenatu ta fadi karo na biyu tana miƙamata karamin complimentary card mai dauke da numbobin wayoyinta a jiki. Nan ma Khadija gyada kai ta yi.

"Je ki." Ta ba ta umarni, ta juya da sauri ta shige ciki har tana cin karo da wata mai tsohon ciki.

"Yi hakuri don Allah." Matar ta bita da kallo kawai gami da jan tsaki irin na masifaffun masu ciki. Haka ta wuce ta a mita.

Koda ta karasa dakin Nurses, ba ta tarar da kowa ba don haka da sauri ta ciro kudaden hannu na rawa ta cusa a jaka ta zuge zif. Bandaki ta shige ta soma watsawa fuskarta ruwa tana salati a ƙasan ranta. Yau da wane rashin sa'a ta fito daga gida? Kawai sai ta shiga hawaye, nutsastsiyar fuskar Ramlatu da kuma na Hajiya mai cike da dattako da kamala take tunawa. Ta ya ya? Ta wace hanyar za ta iya kashe wannan baiwar Allahn? Duk da dai idan ta so abu ne mafi sauki a aikinta, za ta iya kasheta irin kisar da zai yi wuya kafin a gane ita ce silarsa. Amma ina! Ba'a ba ta wannan tarbiyyar ba kuma ita ba haɗamammiya ba ce akan abin duniya. Kaɗan ma da ta ke samu ya wadatar da ita.

Sai da aka kwankwasa ƙofar sannan ta fito. Karo suka yi da Nos Jamila. Ta bita da kallo.

"Dije, lafiya?"

Murmushin yaƙe ta yi ta hau murza idanu.

"Ba komai, abu ne ya faɗa idanuna."

"Aa Dije, faɗamin gaskiya."

Girgiza kai ta yi, ba za ta iya ba, tana tsoron abinda zai sanadin rayuwarta.

"Ko haihuwar ki ka karɓa, don nasan halinki na tausayi."

Dariya ta ba ta.

"Oh na tuna, ashe fa ba duty naki bane yau." Cewar Nos Jamila karo na biyu.

Ita dai Khadija ta sulale ta fice daga ɗakin. Maganin ma kasa komawa ta ba Ramlat ta yi sai wata ta aika.

*** Hussein da AlHassan zaune a falon gidan Hisham suna cin lafiyayyen girkin Aisha. Gogan ci yake kamar an mishi dole.

"Wai Hussein lafiya? Ko kaima jinyar kake taya Ramlat?"

AlHassan ya fadi yana murmushi don tuni ya ɗago shi.

"Mene haɗina da ita? Kawai dai na damu da harbin ne, na kuma rasa waye zai yi ƙarya da ni ya harbe ta. Shiyasa na kasa fahimtar mai laifin, me ya sani tsakanina da ita da ya zaɓi hanyar kasheta ta amfani da ni."

"Da mamaki kam, amma ko ma mene in sha Allah nan ba da jimawa ba zai bayyana. Har wanda ake ɓoyemana."

Hisham ya furta yana kashe mishi io ɗaya, AlHassan ya yi kamar bai gansu ba ya ci gaba da kai loma yana murmushi. A yau jinsa yake kamar a duniyar gajimare tsabar murnar ganinsa zaune tare da ɗan uwansa.

Hussein din ma banda harara bai cewa Hisham uffan ba, saboda gudun zargin sai ya saki jiki ya ci abinci. Bayan sun kammala ya mike.

"Ina zuwa?"

Fadin AlHassan don ba ya son ya ji Hussein din ya matsa daga gareshi. Murmushi Hussein ya yi.

"Gidan Hajiya Zeenatu."

"Aa, bai kamata ka je kai kaɗai ba. Muje tare."

Jinjina kai Hussein ya yi cikin amincewa da zancen dan uwannasa. Suka ɗunguma suka fita, Hisham ya takamusu har ƙofa kafin ya dawo ciki. Kusan shima yau dai jinsa yake sak. Babu sauran damuwa.

*** RAMIN ƘARYA.... [3/16, 1:55 PM] +234 703 629 0938: I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/IRx4QB4kMcb

🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

48)

Kallonsa yake yi sosai kirjinsa na bugawa da sauri. Ramlat ta runtse idanu tana mai addu'ar komai ya tafi daidai.

Da wani irin sassarfa AlHassan ya tako ya rungume Hussein kawai sai ya soma kuka.

"Hussein." Ya ƙara kiran sunansa karo na biyu, Hussein ya yi ɗif sai hawaye da ke zuba saman fuskarsa. Ji ya yi kamar ana saramasa guduma a tsakiyar kansa, a hankali ya soma ganin dishi-dishi, lokaci guda idanunsa suka juye yayinda baƙin kwayar idanun ta ɓace ɓat. Hisham da ke tsaye a baya shi ya lura da sauri ya karasa ya rike Hussein. Jikinsa wani irin kakkarwa ya ke yi.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"

Cewa Hisham yana rike hannun Hussein, jin haka AlHassan ya ɗago wanda saura kiris Hussein din ya zube don kuwa da jikinsa ya samu madafa.

"Riƙe shi sosai." Cewar Hisham, suka taimaka suka fitar da shi sai wurin likita. Ramlat tuni ta miƙe tsaye. Su kansu su Hajiya sun rude. Ganin tana kokarin ficewa yasa Rafee'ah riƙo ta.

"Ina za ki je? Ba ki ganin halin da ki ke ciki? Idan kin je lafiya za ki ba shi?"

Ta girgiza kai tana hawaye, ta bude baki sai dai ta rasa me za ta ce don haka ta koma ta zauna. Hajiya ce ya fidda waya don ta kira Malam ta sanarmasa halin da ake ciki. Nan take ya ce maza ta aiko a karɓi ruwan da ya haɗa da ganyen magarya ya yi addu'o'in karyewar sihiri. Ba shiri ta yiwa direbanta waya ta ce ya biya Yakasai ya karɓo mata saƙo.

*** Duk iyakar awon da likitocin su ka yi ba su gano komai game da ciwon Hussein ba. Don haka koda suka samu ya bar jijjigar, idanun suka dawo daidai sai Likitan da ya karɓi Hussein ya fito wurin su AlHassan. Suka tarbe shi da gaggawa.

"Ku yi hakuri.."

"Mutuwa ya yi?" Faɗin AlHassan a gigice, girgiza kai Likitan ya yi yana mai riƙe hannunsa.

"Ko kusa ba haka ba ne, asalima yanzu mun samu komai ya daidaita. Sai dai hakikanin gaskiya ba za mu ce ga abinda ya jawomasa hakan ba, yanzu dai halin da ake ciki, dole zamu yi mishi tests don mu gano ainahin inda matsalar take."

Suka jinjina kai.

"Ba damuwa Dakta. Allah Ya ba shi lafiya." Cewar Hisham da hankalinsa ya ɗan kwanta.

Bayan wucewar Dakta ya dafa kafaɗar AlHassan wanda ya cire hular kansa tsabar gumin da fargaba ta haifarmasa.

"Kada ka damu ɗan uwa, na fadamaka dama duk sadda maganar dangi ko ƴan uwa ta haɗa mu da Hussein ya kan shiga wani irin hali, ina kuma ga yau ya yi ido huɗu da ɗan uwansa?"

"Hakane, sai nake ganin kamar ba na asibiti ba ne."

AlHassan ya faɗi bayan kai karshen nazarinsa.

"Hisham, ya jikinnasa?"

Suka juya, Rafee'ah ce. Ta karaso suka yi mata bayani.

"Allah Ya ba shi lafiya. Kada ku damu, Hajiya ta aika a karɓo ruwan ganyen magarya mai addu'o'in karya sihiri, da yardar Allah komai zai daidaita."

AlHassan ya sauke ajiyar zuciya yana ɗan murmushin jin dadi da wani irin kaunar zuri'ar da ke kara mamaye zuciyarsa.

"Na gode kwarai, Allah Ya sakamaku da alheri. Allah Ya bar zumunci."

Ta yi dariya kadan.

"Ameen. Ai yiwa kai ne. Bari na koma, dama Hajiya ce ta ce na sanarmaku sannan na gano halin da yake ciki don marar lafiyarmu ta tashi hankalinta sai kuka ta ke yi."

Murmushi AlHassan ya yi yana mai hasashen wani abu da tun a jiya ya yi zaman dirshan a kwakwalwarsa.

*** TA FARU TA ƘARE...

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Halimar aka kama?!"

Hajiya Zeenatu ta faɗi tana tsaye a bakin ƙofar gidan Kakar Halima wacce ke rike da ita. Ƙanin Halima uwa daya uba ɗaya wanda daga ita sai shi, su uku iyayensu suka haifa kafin rasuwarsu, dayayar Halima, Halima sai Yusufa. Kakarsu ta karɓi riƙo. Yusufan ya share hawaye yana duban Hajiya Zeenatu.

"Wallahi ranki ya daɗe, ɗazu aka yi mana waya, naje har ofishin ƴan sandan na sami Aunty Halima, wai dumu-dumu aka kama ta da bindiga za ta yi kisa. Wannan abu ne da ko a mafarki ba mu zaci faruwarsa ba. Su biyu aka kama, shi ɗayan ko Gwaska ko wa? Yana asibiti. Yanzu Kaka na kwance ba lafiya tun da ta ji halin da ake ciki."

Hajiya Zeenatu wacce ta yi mutuwar tsaye, ta yi sauri ta dawo hayyacinta. Baki na rawa ta ce.

"Ta..ta..faɗi wadanda suka sanya ta?"

Kallon da Yusufa ya yi mata na nazari sai da ya sa ta sakin ƙaramar tusa mai haɗe da fitsari ba shiri. Ya girgiza kai.

"Abin kunya ne ace saboda ɗa namiji za ta aikata hakan. Kishi ne kawai don uban gidansu na aiki zai auri abokiyar aikinta Ramlat. Haka ta sanarmin."

Ya karashe da wani irin jin kunya. Ajiyar zuciya Hajiya Zeenatu ta sauke ta juya za ta shige mota.

"Amm..Hajiya, na ce sai dai ban sanki ba. Kema wurin aikinta ki ke ne?"

Ta juyo.

"Eh, tare muke aiki." Tana kaiwa nan ta juya da sauri ta faɗa mota, ta ja. Kiyayewar Ubangiji ce kawai ta isar da ita gidan Hajiya Batool. Itama nan ta iske ta su na dambe da surukarta. Dakyar ta raba su. Ɗan Hajiya Batool ba ya nan ya yi tafiya Dubai, shi ne surikar ta zo gidan kwana.

"Haba Hajiya, me ya yi maki zafi za ki tsaya dambe da suruka? Ke kuma don ba ki da kunya wannan ba uwar mijinki ba ce?"

Fareeda wacce ke tsaye tana huci ta narkawa Hajiya Zeenatu uwar harara kafin ta saki dariya gami da tafa hannu.

"Ahayye! Ai fa da yake daga ke har ita jirgi ɗaya ya kwaso ku dole ne ki ga laifina! Tsoffin banza da ba su riƙe girmansu ba ai ba zan ji kunyar taka su son rai ba. Kin tauye hakkin yaro kin danne kina zaune da shi! Ko an fadamaki bani da labarin mijinki? Kina kai min uwar miji yawon bin bokaye don mijina ya ƙara aure ko? To wallahi karyar ku domin tun kan a haifi uwar mai sabulu balbela ke da farin kai. Don haka idan ku na son na lulluɓe dukkan sirrikanku to ku tabbatar an fasa batun auren Mijina da kowace shegiyar kucaka. Idan kunne ya ji..." Ta ƙarashe da rike kunne kafin ta wuce tana dariya ta bar su baki galala. Bayan shigewarta ɗaki Batool ta yi gaba ta haye sama, Hajiya Zeenatu ta bi ta a baya. Su na shiga ɗaki suka sa mukulli.

"Batool akwai matsala!"

Hajiya Batool da ta zauna rike da ƙugu tana ambaton wash sakamakon cizon da ta sha a wurin Fareeda. Ta amsa wa Hajiya Zeenatu kamar za ta yi kuka.

"Matsala nima cikinsa kika tarar da ni Zeenatu. Kamar Gora yaudararmu ya ke yi yana cin dukiya a ɓagas. Ni na rasa kan wadannan lamuran."

Hajiya Zeenatu ta yarfar da jaka da mayafi, da sauri ta faɗa banɗaki. Can kuma ta fito ta zauna tana sharce gumi. Ta kora dukkan bayani ga Hajiya Batool gaba dayanta a rude.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull