Kawar zuciya Book 2 by takori - Chapter 8
Kawar zuciya Book 2 by takori Chapter 8: Kawar zuciya Book 2 by takori Chapter 8. Hatta kalmar gaisuwar makalewa ta yi a makoshin Azeezah Murtala, domin…
4,424 words
Hatta kalmar gaisuwar makalewa ta yi a makoshin Azeezah Murtala, domin sai yau ne tayi ma Zayyan Bello kallo na hakika don jiya ko kallon fuskarsa bata yi ba. Duk wata jijiyar da ke cikin jikinta sai da ta saki, ta karbi kwantaccen sakon da ke cikin idanunsa zuwa gare ta, kafafunta ma rawa suka hau yi, ta shiga gaishe shi da shakakkiyar murya da dimaucewa.
Baba Murtala ya kara bada ita da cewa,
“To shayin ma wato sai na sake cewa ki hada masa karo na uku ko Azeezah?”
Saura kadan Azeezah ta fashe da kuka, sabida bazata iya hada wannan shayin ba. Hannunta da jikinta duka rawa suke. Zayyan ya cece ta da cewa.
“Kyaleta ta je Baba, ni ko Safiyyah bata hada mun shayi, da kaina nake hadawa, kyaleta zan hada da kaina Baba”.
Tsaki Baba Murtala ya yi, yana ta korafi dai a kan halin sangartar diyar tasa, har yana cewa, yana jin tausayin duk mijin da zai kwashe ta. Domin kuwa ba haka uwarta take ba.
Murmushi Zayyan ya yi, beautiful serene smiles dinsa, wani tsadadden miskilin murmushi da ba koyaushe yake yin irinsa ba, ya ce.
“To Baba ni in rage maka dawainiya mana? Ni ina sonta a haka, ka ba ni ina so”.
Sakatoto da baki Baba Murtala ya yi yana kallon dan nasa, kafin ya ce, “Tau? Ubanka nake dai ba Kakanka ba, balle ka maida ni abokin wasan ka, ni ba sa’an wasanka ba ne Zayyan da za ka tsokane ni.
Barni in sha ‘tea’ dina cikin dadin rai, kada ka sa ya huce min da shiriritarku”. Ya daga kofin shayinsa ya kurba.
Zayyan ya dinga murmushi yana cewa, “In dai za ka ba ni Baba, ba zan yi maka wasa ko shiririta ba nima, ai babu irin wannan wasan tsakaninmu nida kai Baba. Uba ne da tilon Dan sa”.
Kawai sai ya ga Baba Murtala ya daddage ya fashe da kuka.
Jikin Zayyan ya yi sanyi, don ya dauka zafin maganarsa Baba Murtala ya ji, amma sai Baba ya kama hannunsa ya rike yana kallonsa da kauna ido fal hawaye.
Ya ce, “Bar ganin ina zubda hawaye, Bello na tuno. Ya taba cewa, ba don ka yi aure da wuri ba da zai fi so ka auri daya daga cikin ‘ya'yana mata don kara dankon zumuncinmu.
A lokacin sai na ce masa, kada ya kara irin wannan maganar kada mu taba tunanin yi muku auren hadi, wanda a karshe bata zumunci yake zama.
Yau da ka furta da bakinka cewa, kana son Azeezah, duk da yadda nake ta kushe ta a idanunka, tun zuwanka Zayyan ban yabi halin Azeezah ko daya a kunnenka ba, ko sau daya ban fadi alkhairi akanta ba, sai hakan ya tuna min da abinda Bello ya taba ce min a kanka.
Ya taba ce min, yana son baudaddiyar halayyarka, abin da kowa bai so ko ake ganin disadvantage dinsa, sau tari kai shi kake so. Abinda baya burge kowa kai shi yake burgeka.
Ya ce auren da ka yi shi kadai ya mara maka baya saboda daga Hajiya Fatu har ‘yan uwanka mata babu mai son auren saboda diyar Alaramma ce kuma stammerer.
Da wannan nake cewa, ni kuma na baka Azeezah, ka nemi yardarta, in Allah ya sa ta amince da zarar mun gama wannan project din, sai mu durfafi daurin aurenku”.
Shayin da basu sha ba kenan a yau, haka suka fita suka barshi a wurin ya huce.
Baba Murtala farin ciki ya hana shi sukuni, suna tafe a hanya direban Baban na sharara gudu da su a bayan Hyundai din Alhaji Murtala, sai ya ji Baba na waya da Azeezah din.
“Azeezah kina gida ne?”
“Mun fita ni da Mama Agege, amma muna hanyar komawa gida yanzu haka”.
Ya ce, “To ki shirya tarbar bako yau da daddare, wajen karfe takwas in na dawo gida”.
A dukunkune da fuska ta ajiye wayar don ta yi tsammanin ya dauko mata malamin da ya ce zai dauko ya dinga koya mata karatun addini a gida ne.
Ita a wurinta ta wuce zama gaban Malamin islamiyya yanzu. Baba Murtala kuma ya ce, ko izfi goma ya san bata hada ba.
Don haka ko da suka dawo gida ita da Mama, bata yi wani kyakkyawan minti goma a falo ba, ta gudu dakinta tasa sakata.
Zayyan sai goshin magriba suka dawo gidan shi da Baba, don haka masallaci suka wuce kai tsaye, wanda ke like da gidan Alhaji Murtala.
Can suka zauna suka bi jam'i har bayan da aka idar da sallar isha. Ko a masallacin Addu’a yake cikin ransa, idan nemansa da Azeezah alkhairi ne a gare su, shi da Safiyyah, Allah ya bashi kwarin gwiwar iya tsayawa a gaban wata macen da sunan neman soyayya ba Safiyyah Dandume ba.
Da suka fito daga masallaci Baba ya ce su wuce cikin gida su yi dinner, sai ya ce ma Baba yana zuwa.
Ya koma masaukinsa ya sake wanka, yau Zayyan kananun kaya ya saka, shirt da wandon jeans baki Tommy Hilfiger. Zai fesa turare kawai idanun Sophie suka fado cikin nashi idanun, sai ya fasa.
Don ji ya yi tamkar hakan ya zama cin fuska a gare ta.
“To na nawa kuma Malam Zayyan? Tunda gaka ka dauki wankan zuwa zance gun budurwa?”
Wata zuciyar ta tambaya ta kuma kara masa da ce masa, “You are no longer a trusted husband to Sophie, you are now a “man” like other men, who are guided by their heart desires and emotions”.
Ma'ana; kai yanzu ba dan amanar Safiyyah bane. Ba mijin da zata bugi kirji ta yarda dashi bane. A yanzun daya kake da sauran maza babu banbanci, wadanda ke tafiya akan muradin zuciyarsu da shaukin dake zukatansu".
Wannan tunanin ne ya sa jikinsa yin sanyi kalau, ya maida turaren muhallinsa ya ajiye. Ya fasa fesawa.
Amma sai wata zuciyar ta tabbatar masa da cewa, kara aure ba cin amana bane ga maza, ba kuma cin fuska ne ga Sophie ba. Karewa ma, yana ganin zai nemi wannan auren ne don ya samar mata maslaha a zama da shi, sannan ya nemo mata nutsuwa da kwanciyar hankalin data rasa a cikin rayuwarsu.
Muhimmi shine zai yi auren nan ne ma don ta samu Da daga gareshi. Wanda ya yi alkawarin nata ne da duk macen da ya haifa, kuma hakan maslahar ta ce a rayuwa da Mama, duk wata tsangwama, duk wani zargi na ta mallake shi zai kau daga idanun Mama yanzu.
Da wannan tunanin ya dan samu karsashin nufar cikin gida. Wai shi Zayyan ne yau zai je zance gun budurwa ba Safiyyah ba. Yana taku a hankali kamar ya fasa zuwa zancen, musamman da yake jin tamkar idanun Safiyyah na kallonsa.
Amma da ya tuno surar Azeezah da iya kwalliyarta sai nan da nan wata zuciyar ta ce,
"Zayyan kada ka bada maza mana, polygamy ba kanka farau ba".
Ya samu Baba yana waya, tuni an shirya musu abincin dare. Ya yafito shi da hannun damansa don ya zauna gefensa as usual.
Sai da ya gama wayar sannan suka fara cin abincin Baba na masa hira. Duk da Baba Murtala ya fahimci yau ya kasa sakin jikinsa da shi, shi ya sa ma yake kara jan hirar tasu don ba ya so surukuta ta shiga tsakaninsa da Dan nasa Zayyan tun yanzu. Yafiso su ci gabada gudanar da rayuwarsu normal ta uba da Da yadda suke yinta.
Sai da suka kammala Baba Murtala ya ce, ya shiga daga falon Hajiya Nana za ta turo masa Azeezah.
Bai jima da zama ba Hajiya Nana ta turo ta falon. Azeezah ta shigo fuska a turbune don ta dauka ko Malamin islamiyyar ne ya fara zuwa, don daga Mama har Alhajinsu ba wanda ya gaya mata cewa Zayyan ne. Don haka da ta ganshi a falon ta kusan sakin fitsari daga tsaye. Duk ta rude, domin kwarai Zayyan mijin Safiyyah ke da kwarjini a idanun ‘yammata.
Rasa me za ta ce ta yi, tunda dai ai ta san babu wata manufa da Baba zai turo mata shi in ba ta neman aure ko dalili makamancinsa ba.
“Zauna mana Azeezah”.
Zayyan ya fadi cikin tsare ta da idanunsa da suka kara ruda ta.
Haka ta dosana ta zauna a nesa da shi akan hannun kujera.
Ya gyara zama ya ce,
“Kun dawo kenan?”
Ta amsa da “Eh”. Tana wasa da ‘yan yatsunta.
Sai ya yi gyaran murya ya ce, “toh dai Azeezah, ba sai mun ja ta da nisa ba, tunda dukkanmu ba yau muka san juna ba. Kuma diyan Baba ne mu duka ba bakin juna bane.
Sannan ni ba yaro bane kamarki, na kusa shiga shekaru arba’in, kin ga kenan babu bukatar yin kwane-kwane ko bata wa junanmu lokaci.
Azeezah na ganki a gidanku, gaban iyayenki kuma na yaba, in short I admire you, zan so kara ki cikin iyalina idan kin amince.
Sunana Zayyan Bello, kamar yadda kika riga kika sani, ni dan marigayi aminin Baba ne. Ina da mace daya mai suna Safiyya, wadda tunda muka yi aure sama da shekaru goma ba mu taba samun matsalar da muka kasa warwarewa a tsakaninmu ba”.
Ya dan nisa kafin ya sassauta murya ya cigaba da cewa.
“Azeezah ni da matata muna da fahimtar juna, ina son kara aure ba don ta rage ni da komai ba, ina kuma barar shigowarki cikinmu, don kara dankon zumuncin gidanmu da gidanku. Idan har kin amince bana so abin ya dauki lokaci, don ni da ke babu bukatar sanin asalin juna, sai amincewarki kadai nake nema”.
Duk wata kalma guda daya da yake yi a kan matarshi kular da Azeezah ta ke yi, har ta ce a ranta, wai shi wannan a wurinsa haka ake zuwa neman soyayyar budurwa? Da alama farin shiga ne gun zuwa zance wajen budurwa ‘yar zamani kamarta.
Ba zai maida hankali wajen gaya mata irin kamun da soyayyarta ta yi masa ba, sai wani yan-yan-yan akan tsakaninsa da matarsa?
Kamar ta yi kuka saboda ba wannan take son ji ba, ta ce cikin gatse.
“Kuna da irin wannan fahimtar juna da soyayyar kai da matarka, to meye naka na son kara aure, kuma me ka zo nema a gare ni tunda ba so ba ne ya kawoka? In zumunci ne ai da abinku na ganku kaida Baba, so ko dani ko babu ni zaku cigaba da abinku yadda na riskeshi”.
Tana fadin hakan ta sha mur sosai, ta dora kafa daya kan daya, don ta tsani rainin hankali irinna maza.
Kwarai tambayar tata ta shammace shi, har ya rasa amsar da zai bata, hakan yasa ya baiwa kansa assignment na ‘yan sakanni. Don ya samu amsa kwakkwara da zai bata.
Yana ganinta yarinya, mai tarin wauta, ashe-ashe tasan abinda take yi? Meye dalilin son kara aurensa? In har yanada komai da yake bukata a gidansa? Shine assignment dinda shima ya baiwa kansa a yanzu.
Dalilai da yawa masu muhimmanci sun yi mujazar wannan son karin auren, domin yana ganin shine kadai maslaha a gare su shida Safiyyah, don yana sha’awar mace irin Azeezah a gidansa da rayuwarsa, yana son mace ‘yar gayu, mai wayewar kai, domin likely mace mai body shape dinta da irin dirarrun dugadugan kafar Azeezah itace daidai shi. Ustazancin Sophie yayi masa yawa, tsayin shekarun da sukayi tare da zata canza da tuni canza to ba’a sakewa mutum nature dinsa, wanda shi yake hana ta sakin jiki su yi irin soyayyar da shi yake so, for over a decade da aurenshi da Sophie yana ganin bai samu sakewarta da shi a gadon aurensu irin yadda yake so ya kai sau goma ba, saboda kunyarta da kawaicinta akan hakan, amma ba don bata sonshi ba.
Azeezah za ta yi bridging wannan gap din, ga dukkan alamu, duk da tarin negativities dinta da mahaifinta ke kuka dasu, shi ba zai zame masa matsala ba in dai zai samu yadda yake so da ita, yake kuma kwadayin samu a gidan aurensa, ko da kuwa Safiyyah ta haihu, hakan ba zai hana shi wannan auren ba.
Sannan idan Allah ya nufa ya samu haihuwa da Azeezah kafin Safiyyah dan ko ‘yar na farko da yardar ubangiji zai zamanto tukwicin kauna ta gaskiya ne da zai yiwa Safiyyah.
A takaice sexual dysfunction din Safiyyah da neman mata yaro daga gareshi, su ne dalili kuma silar son kara aurensa.
Azeezah ta kafe shi da idanunta tana jiran amsa, tana kuma ankare da yadda tambayarta ta jefa shi a gumi da tunani. Zayyan ya dago a hankali suka hada ido, sai ya yi mata murmushin da ya kara narka zuciyarta a kansa.
Ya ce, “kisa a ranki babu namijin da zai zo neman aure a inda babu burbushin soyayya a ransa. I like you Azeezah, amma don Allah kalmar SO dinnan ki yimin jinkirinta, har sai na tantance ta a raina, kada in fade ta a lokacin da bai dace ba.
Na yi miki alkawarin adalci da farin ciki a gidana, don ke kanwata ce da ba zan iya cutarwa ba, ina son aurenki bisa yarda da amincewarki”.
Maganganun nasa sun ki zauna mata daidai a kwanyarta, don jinsu ta ke tamkar rainin wayo. Amma me?
Zayyan din ya zo da karfin chemistry din da ya fizge zuciyarta nan da nan zuwa gare shi, har ta ke jin ba za ta iya ce masa dole sai ya takura kansa ya furta mata abin da ta ke son ji ba, tunda dai ya ce babu namijin da zai zo neman aure a inda babu burbushin soyayyar mace a ransa.
Zayyan ya katse mata tunanin da ya jefa ta da cewa,
“Can I go ahead Azeezah? Kin yarda iyaye su shigo cikin lamarinmu, in sanya ki cikin iyalina?”
Azeezah ta juyar da kai gefe, zuciyarta na bugawa da shigar SO farat daya, babu bata lokaci zuciyar tace itafa ta yi na’am da dan mutanen Rafindadi. Ko ma dai me yake nufi da cewa ta yi masa uzurin jinkirin kalmar soyayya zuwa wani lokaci za ta yi wannan uzurin, domin ta tabbata wuyarta a yi auren, tunda har ya kawo kansa ya yi confessing na neman amincewarta da bakinsa.
Tana wannan tunanin, ya sake maimaita tambayarsa na neman yardarta har ya ce,
“Kamar yadda ki ka gani ni ba yaro ba ne Azeezah, ba zan iya long dating dake ba, I truly admire you, ki ba ni yardarki”.
Sai ta samu kanta da gyada kai kawai, ta kuma tambaye shi ko yaransu nawa shi da maidakinsa Safiyyah?
Zayyan ya dan ciza lebensa cikin ‘yar damuwa kafin ya ce.
“Muna fatan Allah ya kawo su nan gaba. In kuma daga wajenki Allah ya bamu, ina neman alfarmar ki baiwa Safiyyah ko me ki ka haifa na farko. Na tabbatar miki za ta yi masa rikon da ko ke ba za ki yi masa ba tunda Da na ne. Za ta yi masa tarbiyyah irin wadda ko ke ba za ki yi masa ba. Za ki yi mana wannan alfarmar Azeezah?”
Wani abu a halin Azeezah shi ne, ba ta boye abin da ke ranta. Ita ma bata so a boye mata. Ko kuma tarin kuruciya ne ya debe ta a wancan lokacin? Har ta yi masa alkawarin yi masa wannan alfarmar.
Ta ce, “Allah da Ya halicce ni bai yi ni da son hidima da hayaniyar yara ba. Amma zan so in san kai da ita din waye mai matsalar haihuwa, don ka ce min kun yi kusan sama da shekaru goma tare?”
Wani abu da ba zai iya ba shi ne, yin zancen nan da wani, wanda ya kasance sirrinsu shi da Safiyyah, don haka ya ce da Azeezah, “We are all fit and healthy Azeezah, muna jiran hukuncin Ubangiji a kai. Now, tell me about your samari? Su nawa ne?”
Azeezah ta yi wata ‘yar shashashar dariya ta ce, “To me ye ruwanka da su "Dan Daddy?" (sunan da ta sa masa kenan, wato dan Babanta Alhaji Murtala, don Baban ma ce masa yake Dan wajena, tun ba su hadu ba ta sha jin yana ma mamansu Hajiya Nana zancensa), tunda dai kai Allah ya kashe ya baiwa Azeezar?”
Sai bayan ta fadi hakan cikin subutar baki sai ta ji kunya sosai, shi kuma Zayyan sai kansa ya kumbura. Abinka da namiji a hannun wayayyar yarinya, tuni Azeezah ta sa ya sake da ita, ta bashi labarin ita cikin masu sonta mutum daya ne soyayyarsu ta yi nisa a makaranta, wato wani mai suna Faris. Sun hadu ne a Cyprus.
Bayan dawowarsu daga karatu ya zo nan gidansu zance, Baba ya ganshi da wani (haircut), wanda bai masa ba. Tun daga ranar Baba ya saka masa karan-tsana, wai askin ‘yan iska ne akansa kada ya kara zuwar masa gida”.
Dariya sosai Zayyan ke yi, Azeezah ta dauki hankalinsa sosai da salon maganarta ta 'yan gayu, ga iya Hira, musamman yanayin yadda ta ke magana cikin rangwada da karya kai, har da yada hannuwa cikin salo mai daukar hankalin da namiji.
Ya ce, “What I want to know now (abinda nakeson sani yanzu?), ke kina son Faris din, ko kuwa Babana yayi miki kancal ne daya koreshi?”
Ta yi masa wata hararar love, ta ce, “In ma na so shi, to kafin in dora ido a kan Dan mutanen Rafindadi ne, shi kam sharp shooter ne, tuni ya sa na manta da kowa har ni da kaina ina mamaki”.
Zayyan ya mike ya iso inda ta ke zaune, ya dan tsugunna kadan saman kanta, ya dafa hannun kujerar da ta ke zaune yana murmushi.
Azeezah ta shaki ultraviolet dinsa sosai, wanda ya riga ya kama jikinsa da ya fesa ko bai fesa ba, har ta kusa shidewa a wurin don wata soyayyarsa mai dadi data kara kamata.
Ya ce, “Insha Allah ni kuma na yi miki alkawarin ba za ki yi nadamar zaben Dan Rafindadi a matsayin abokin rayuwarki ba. In dai za ki girmama min Sophie, za ki taya ni lallabata da martaba ta to in sha Allah zamu zauna lafiya.
Ina tabbatar miki za ki same ni fiye da yadda kike so, ko kike burin samun abokin rayuwarki”.
Tun daga ranar soyayyar shi da Azeezah ta kullu a gidan mahaifinta, kullum suka dawo aiki shi da Baba, to a falon da aka ware musu yake yada zango can Azeezah za ta kai mishi abincin ranar shi dana dare.
Tuni Hajiya Nana ta daina hada mishi kwano da Baba, har ranar Baba Murtala ke masa tsiya da cewa, Azeezah mai yankan kauna, haka kawai ta raba mishi kwano da dan wajensa.
Baba Murtala da Mama Fatu sun fi kowa farin cikin wannan al’amari, don kafin ya gama kwanakin aikinsa a Lagos Mama da Azeezah sun gaisa a waya a gabansa ya kai sau uku.
Hajiya Nana kam bata so ba, musamman jin Zayyan yana da mata, amma ganin yadda ‘yar da uban duk suka mika wuya, sai ta sallama musu. Amma kwarai ba ta son Azeezah da auren mai mata, don ita kadai ta rayu a gidan Alhaji Murtala tun daga kuruciya har girma. Kuma Azeezar nan ita kadai ta rage musu mace a gabansu.
Sai dai ta san Hajiya Fatu irin farin sani, a matsayinsu na matan abokan juna tun kuruciya, ta san Mama Fatu tun Architect Bello na raye, kuma a saninta ba ta da wata matsala da mijinta da al’umma, wannan ne ya yi convincing amincewar Hajiya Nana Aisha, don Mama ta kira ta officially ta ce ba jimawa za su kawo lefe.
Namiji kenan, duk inda yake sunansa namiji in dai a kan mace ne, ko idan ya so kara aure. Shi kansa yana mamakin wannan al’amari domin bai taba planning dinsa a kamus din rayuwarsa ba.
Rabonsa da ya kira Safiyya, ko ya saurari kiranta da sakonninta tun saukarsa a Lagos, da tozalinsa da ‘yar Babansa Alhaji Murtala.
Kullum da dare kusan kwana yake yana questioning kansa, yana mai kalubalantar kansa a kan wannan hukuncin da ya yanke. Amma ba ya bari tuhumar ta yi nisa yake kare kansa ta hanyar gaya wa kansa hakan shi ne kadai solution ga dukkan matsalolinsa da Sophie.
Allah sarki Safiyyah, tana can Abuja amma ruhinta yana Lagos, cikin damuwar canjin farat daya data samu daga Habiby dinta, wai yau Habiby ne ko wayarta ya daina dagawa kuma bai kara nemanta ba har kwana takwas da tafiyarshi, a kan laifin da a ganinta bai kai ya kawo ba.
Shin me ta yi masa haka ma da zafi ne? Ba yau ta soma rejecting dinsa a auratayya ba, amma bai taba daukar abin da zafi irin wannan karon ba.
Ba ta da masaniyar yana can Lagos yana banzar soyayya da diyar ubangidansa, wadda cikin dan kankanin lokaci ta kunce masa lissafi, ta sauke masa hadda.
Ba ya ko tunawa sosai da Sophie sai ya zo kwanciya bacci, to yanzun ma saboda wayar tsakar dare (midnight call) da suka tsiri yi shi da Azeezah ba ya ko samun lokacin da zai yi missing dinta cikin dare. Abun da ya sani shi ne, son Safiyyah a zuciyarsa daga Allah ne, babu mai maye gurbinta. Babu mai tumbuke matsayinta, amma ya rigada yazama attracted and highly infatuated ga son auren Azeezah.
Yadda Mama Fatu ta dauki zancen auren Azeezah da matukar muhimmanci kamar dama a jirace take bai kamata ya bashi mamaki ba, amma hakika ya bashin. Don kafin ma ya baro Lagos Mama da Zubaidah sun gama hada lefe na gani a bada labari kamar diyar gwamna za a kaiwa, akwatuna dozen, masu matukar matsayi, babu ce kurum babu a cikin lefen da Zubaidah ta hada.
Ana i-gobe zai baro Lagos, shida Azeezah ido ya raina fata, sukayi wata irin sallama ta soyayya saura kadan suyi runguma yayi maza ya fice, zuciyar sa na balli balli. Da kyar ya kwanci kansa daga zarce iyaka. Mama ta gayawa Hajiya Nana cewa suna so su kawo lefe washegarin dawowarsa gida.
Abin dai tamkar tatsuniya ko kuwa almara. Komai da komai ya faru tamkar kiftawar ido, neman auren da bayarwa da saka rana duk sun faru ne cikin abin da bai gaza sati uku ba.
Ranar da ya koma Abuja bai ko gayawa Sophie yana hanya ba, bai tashi jin kunyar kansa da kansa ba, sai da ya yi tozali da Safiyyah.
Damuwar da ya jefa ta a ciki ashe har kwantar da ita zazzabin sati guda ta yi, ta rame ta yi fiyat, kamar da ka bushe ta zata fadi, amma kyawun nan na Safiyya yana nan daram, duk da muguwar ramar da ta yi.
Ya ji kunya in ya ce kunya, yana nufin kunya ta karshe da bai taba ji a rayuwarsa ba, don Sophie ba ta ma san da dawowarsa a ranar ba.
Tana kitchen tana dafa ruwan ‘tea’ da za ta saka a hantar cikinta dake raurawa, ta ji motsin shigowarsa falon, ta hanyar amfani da nashi safayan makullin gidan.
Safiyya ta juyo da sauri jin motsin shigowarsa da kamshin turarensa. Suka hada ido, sai ya ji kunyar da bai taba ji ta diya mace ba ta lullube shi, hade da wani irin 'guilt'.
Fuskar Sophie kadaran-kadahan, wato ba yabo ba fallasa ta ce, “Sannu da zuwa”. Sannan ta juya tana ci gaba da juye ruwan zafin da ta kammala tafasawa a karamin ‘tea flask’. Tana kokarin hadiye hawayen da ke son gangaro mata.
Zayyan ya canza gabadaya har wata kuruciya da fresh fatar jikinsa ta kara, alamu ne na yana cikin mabayyanin kwanciyar hankali, hutu da jin dadin zamansa a Lagos, bai ma san halin da ya jefa ta ba. Ta sa dan yatsanta ta dauke hawayen da ya gangaro ta karshen idanunta.
Zayyan ya tako har inda take cikin shanye kunyar tasa, ya sanya hannayensa ya sakalo kugunta ya dora habarshi saman kafadunta yana sakale da waist dinta, ya ce cikin muryar rarrashi.
“Sophie I’m back, me ya faru da ke haka, irin wannan rama haka my Dear Safiyyah?”
Safiyyah ba ta taba hararar Zayyan bisa saninta ba sai yau, ta zabga masa harara ta zare hannayensa daga kugunta ta dau tea dinta da kofin mug ta bar wajen.
Haka ya biyo ta falon cikin karfin hali irin na Da namiji, ya ce.
“Laifuffukana ba za su lissafu ba gare ki Safiyyah, na sani. Amma ki gafarce ni yanzun ki fara ba ni abinci ba don halina ba, I terribly miss your cooking”.
Hawaye suka sulmiyo daga idon Safiyyah, wani weak point dinta kenan guda daya shima ya sani, ba ta iya barin Zayyan da yunwa, don haka shayin da bata sha ba kenan duk da itama yunwar take ji. Sai ta koma kitchen ta shiga hidimar girka masa abinci.
Shi kuma ya bi ta kitchen din ya zauna a kan granite yana ta baibaye ta da kalaman ban-hakuri da amsar laifi. Shi kansa ya rasa hujjarsa ta kin neman Safiyyah ko amsa wayarta har ya je Lagos ya dawo.
Gani ya rika yi yana daga wayarta ko tana jin muryarsa za ta gane ya fada komar wata macen ba ita ba, amma ba don laifin da ta yi masa a ranar da zai tafi ba.
Ta kammala dafa masa jallof din cous-cous da ya ji veggies da hanta sosai, ta zubo a faffadan tray ta kai masa kan dining din dake cikin kitchen din.
A nan ya zauna yana ci, yana yima girkin Sophie cin yaushe gamo da kewa mai yawa.
Ya yi- ya yi ta zauna su ci tare ta ki tsayawa don in ta ci gaba da tsayuwa a wurin rauninta bakidaya da take boyewa zai bayyana kansa. Ta ji ciwon abin da ya yi mata, domin ya zarta hukunci a kan laifinta, a ganinta ya koma zalunci kuma ya dauki hakkinta.
Tunda ta bar kitchen din shima ya ji ba zai iya ci gaba da cin abincin ba, tashi ya yi ya biyo bayanta zuwa dakinta.
Tana canza kayan jikinta, tana kokarin daura towell don shiga wanka Zayyan ya zagaye ta cikin hannayensa, ya kai mata sumba a wuya, ta goce da zafin nama. Ya sake kai mata a bakinta, nan ma ta kwace, amma Zayyan bai bata damar hakan ba domin tuni ya samo bakinta ya soma yi mishi tsotson yaushe gamo. As usual duk yadda ta so bijire ma Zayyan a wannan fannin da wuya ta ke samun nasara. Wuyarta ya soma kissing bakinta da nasa
Kuka ta saka masa, shi kuma ya soma lallashinta har da roko. Bai sakaya mata yadda bijirewarta gare shi ya saka shi sha’awar kara aure ba. Duk da bai fito fili ya fada mata har auren ya nema ba, an kuma bashi, amma kuma Safiyyah duk ta sha jinin jikinta.