Kayar ruwa part 1 complete novel - Chapter 20
Kayar ruwa part 1 complete novel Chapter 20: Kayar ruwa part 1 complete novel Chapter 20. "Daadee". ta faɗa da ɗan ƙarfi tana faɗawa jikinsa, ya kewaye…
1,951 words
"Daadee". ta faɗa da ɗan ƙarfi tana faɗawa jikinsa, ya kewaye matar tasa da dukkan hannayensa biyu cikin tsantsar so da kulawa yana faɗin,"Sorry Mon Cheri, calm down, calm down everything will be ok by God Grace". Bata iya cewa da shi komai ba sai sabon kuka da ta saki shi kuma yana ƙara rungumeta ya shiga shafa gadon bayanta ba tare da sunyi la'akari da mutanen da ke wajen ba.
Cikin kuka sosai take cewa da shi,"I am so scared Daadee". "Don worry relax and calmdown, i am here now, everthing will be oak, you stop crying please".
Ya ɗago kai ya kalli Samra yace da ita,"Iyayen yarinyar fa an samesu?".
Ta ɗaga masa kai,"Yes Daadee". ta faɗa tana yi masa nuni da kan wasu chairs inda iyayen Sa'ida su ke a zaune, tare da su kuma ƴan uwa ne kusan mutum goma a tsaye kowanne cikin jimami. sai yabi wajen da kallo yana ƙare musu kallo me tarin ma'anoni da yawa. Ya tattara hankalinsa da tunaninsa wajensu gaba ɗaya, sunyi tagumi kowannen su fuskarsa bayyane da bala'in tashin hankali da tsantsar damuwa, yanda yay nisa a kallonsu zai tabbatar maka da ya tafi cikin dogon nazari, kuma daga yanda yake faman yamutsa fuska sai kayi zaton ko ƙyanƙyamin kallon na su yake.
Samra da ke kallon mahaifin nasu ta fakaici idonsa a hankali kuma cikin dabara ta zura hannu cikin aljihun rigarsa ta zare kwalin sigaret ɗin da ke ciki. Da sauri ta bar wajen da nufin zuwa ta jefar, idan da abunda suka tsana a duniyarsu bai wuci shan sigari da mahaifinsu ya mayar tamkar abinci ba. Barinta wajen ƙarasowar Madam da Marfu'a, Daadee ya zame Maamee daga jikinsa yana yiwa mahaifiyarsa barka da isowa. Marfu'a kuma ta wuce da ƙaton basket na abinci taje suka gaisa da su Ummani kana ta dawo ta zauna kan kujerar da Samra ta tashi tana karɓar yaronta a hanun Nani.
"Saukar yaushe?". Madam ta ce da Dadee suna tafe zuwa wurin su Ummani ita da shi.
"Yanzun haka, don ina shigowa kuna zuwa".
Daadee ya ce da ita daidai da ƙarasowar tasu wajen dangin Sa'ida waɗanda suka kame kansu a gefe guda suna jiran tsammanin rai ko mutuwa na ƴarsu. Madam ta miƙa hannu ga Ummani tana cewa,"Bayin Allah sannunku, ya muka ji da wannan tashin hankali?".
Daadee shima ya miƙa hannu ga Abbaa da Kaka suka gaisa. Kafin nan ya shiga basu haƙurin hatsarin da ya afku yana kwantar musu da hankali akan da yardar Allah ƴarsu zata sami lafiya. Suka amsa da amin tare da godiya bisa karamcin tsayawa da aka yi akan ƴar tasu wannan kaɗai ma basu da bakin godiya sai dai su ce Allah saka da alkhairi, hatsari kuma ai afkuwa yake ba da gangan ba saboda haka babu buƙatar ake basu haƙuri ai an masu mutunci ma da aka ɗauke musu ɗawainiyar asibitin. Daadee ya kai ƙwayar idonsa ga hanyar shigowa wanda yay daidai da shigowar SJ kuma take annurin fuskar Daadee ya ɗauke, yay saurin ɗauke idonsa daga wajensa yana kawarwa gefe fuskarsa na nuna ɓacin rai, shima ɓangaren SJ ganin mahaifin nasa a wajen yasa shi dakatawa da tafiyarsa ya tsaya daga can nesa, haka kuma yanayinsa na sauyawa zuwa wani yanayi me wuyar fassaruwa, tabbas in ace ya san mahaifin nasa ya dawo to bai ga abin da zai kawo shi wajen nan ba, kamar yanda a ɓangaren mahaifinsa shima cikin zuciyarsa ke faɗin in da ya san SJ zai zo asibitin da babu abin da zai kawo shi a lokacin da zai zo.
Ahlan yaywa Maamee nuni da SJ, ta kai kallonta wurin suka haɗa ido da shi yana tsaye hannayensa sarƙe a ƙirji sai kallonta ya ke babu ƙiftawa, fuskarsa na nuni da rashin jin daɗin ganin Daadee da yay a wajen. Ta tashi ta ƙarasa gare shi don ta san ba zai ƙaraso ba kam, tayi mamakinsa ma da bai koma ba kamar yanda tayi mamakin Daadee shima bai fice a fusace ba, ita a duniyarta kam bata da wata damuwa bacin ta SJ da Daadee da basa jituwa ko na misƙala zarra kamar ba Uba da Ɗa ba.
Da isarta wajensa ya kama hannunta ya riƙe a nasa, tana kallonsa ta ce,"Me yasa ka baro aikinka?". Ta faɗa cikin harshen faransanci.
Yay shiru na ƴan sakanni kana shima cikin harshen na su ya ce da ita,"Maamee karon farko da naji sautin kukanki, kinga har yau zuciyata motsawa take da zafin kukan da naji kina yi".
Yay shiru yana rufe idanuwansa yana shafa hannun mahaifiyarsa da ke cikin nasa, bayan numfasawar minti guda ya ce,"Yarinyar fa?".
Kasa ba shi amsa tayi, ya buɗe ido tare da sanya hannu ya ɗago fuskarta ya ce,"Da ace kuɗi na siyan lafiya da ba'a kawo wannan lokacin ba, sai dai lafiya na wurin ubangiji bamu da yanda zamu yi, shi likita nasa taimakawa ne kawai. Don Allah Maamee ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki zata sami lafiya fa, Yanzu haka da na shigo sai da na fara zuwa wurin Dr yay min bayani kuma ya bani tabbacin zata farka lafiya lau wasu mintuna kawai ake jira, na dai jaddada masa suyi iyakacin iyawarsu wajen ganin Yarinyar tayi surviving and ba tare da zaman wani mummunan rauni a tare da ita ba".
Ya ƙarasa maganar yana sauke numfarfashi tamkar wanda yay tsaren gudu tsabagen doguwar magana nayi masa wahala. "Amma Bhai kana gani sama da 24hrs fa bata farka ba, kar ya zama na yi sanadin rai".
"Maameeeee".
Jin yanda ya ja sunan nata yasa tace,"To nayi shiru Allah ya tashi kafaɗunta". Hannunsa bisa fuskarta ya ce,"Marci".
"Ga mahaifanta can da ƴan uwanta muje ku gaisa ka tayani ba su haƙuri".
"Ok let's go". Yana riƙe da hannun mahaifiyar tasa suka nufa wurin. da zuwansu SJ ya duƙa har ƙasa ya gaida su da girmamawa tare da tambayar,"Ya mai jikin?". Sautin muryarsa ya fito da rashin ƙwarewar hausa a bakinsa.
Abbaa ya dinƙa kallonsa lokaci ɗaya sai yaji ya shiga ransa, saurayi mai kamala da natsuwa gami da girman kwarjini. Ya ce da shi,"To sauƙi yana wurin lillahi, tana can kwance dai har yanzu bata farka ba amma likitan ya ce wai zata farka duk da mun barwa Allah yay ikonsa".
Kan SJ sunkuye a ƙasa, cikin tausashshiyar murya ta son kwantarwa da mutun hankali ya ce,"Zata farka kuma cikin sauƙi in sha Allahu, likitoci za su yi iyakar bakin ƙoƙarinsu akan lafiyarta babu wani damuwa ku kwantar da hankalinku".
"To mun gode Allah ya saka da alkhairi". Ummani ta faɗa tana kallonsa. Ya miƙe yana yi musu sallama. Ummani ta kasa ɗauke idonta daga kansa, kallonsa kawai take yi tana so ta tattara yanayin da take ji akansa ta ɗora a ma'aunin lissafinta kana ta fassara shi, zuciyarta ta harba ɗaya, biyu, uku, tare da kalmar GARKUWA. Duk da halin jimamin da ake ciki hakan bai hana ahalin Sa'ida furta yabo da burgewa ba akan SJ da ahalinsa.
"Akwai buƙatuwar ki koma gida". "Bhai zan koma ne kawai idan naga farkawar ƴar mutane, sannan naga fitowar Muntaƙa daga station domin ƴan sanda sun riƙe shi sun ce yana tuƙi ba bisa ƙa'ida ba".
SJ ya kalla agogon damtsen hannunsa kana a hankali ya furta,"zata farka Maamee, zata farka ko don saboda samun natsuwar Mahaifiyata".
Ya faɗa yana tsayuwa gefen da Ya Imam ya jingina da jikin bango tare zuba hannayensa cikin aljihun wando gami da fuskantar ƙofar ɗakin da Sa'ida ke kwace rai hannun Allah, kuma fuskantarsa ƙofar ɗakin yay daidai da farkawar Sa'ida wacca ta ƙwallara wata muguwar ƙara da ta amsakuwa a cikin asibitin gaba ɗaya kafin furucin Abbaana ya biyo baya a bakinta. Ai fa kamin ƙiftawar ido cikin sauri kowa ya miƙe anyi cuncurundo a ƙofar ɗakin ana leƙenta ta farin gilashin jikin ƙofar, tana daga kwance tana faman jujjuya kai tana kiran sunan Abbaa. Dr ya ƙaraso wajen cikin hanzari shi da nurses suna a ba su hanya, sai dai sam babu ma wanda ya san suna yi. A hankali SJ ya sauke numfashi yana barin wajen da yake tsaye wanda shi ɗaya ne dama bai bar inda yake ba, ya ƙaraso kusa da Dr ya karɓi stethoscope ɗin hannunsa, sannu a hankali ya ratsa ta tsakanin mutanen da ke ta faɗin Alhamdulillahi yana jin kansa kamar zai bindiga saboda hayaniyarsu har ya kai bakin ƙofar yasa hannu ya buɗe room ɗin, Dr da Nurses su ka zo suka shiga ciki kana shima ya shiga ya rufo ƙofar.
Ba zuciyar Dr da Nurses kaɗai ba, hatta zuciyar SJ sai da tayi mugu mugun matsewa da tausayin critical condition ɗin da yaga Sa'ida, a hankali lumsassun idanuwansa ke kallon Finger pulse oximeter da aka sanya mata kafin ya sauke ƙarshen kallonsa kan Cervical Neck Collar da ya rufe har haɓar fuskarta. Ba ya jin a irin tausayin da yake da shi zai iya tsayawa kallon yanda likitoci ke gudanar da aikinsu akanta da kuma hawayen da yaga suna fitowa daga rufaffun idanuwanta suna sauka ta gefe. Takawar da zai yi ya juya ya fita yaji likita ya ɗaga murya wajen cewa da Nurses,"ku taimaka ku riƙe min ita".
Kuma kafin wani yunƙuri na Nurses SJ ya riga su isa gaban gadon yayma Sa'ida rumfa tare da danne hannayenta biyu don ganin ta daina jijjigar da take yi. "Désolé(Sorry)". Ya faɗa a hankali bugun zuciyarsa na ƙaruwa. ______________________________________ *_ALHAMDULILLAH! Nan muka kawo ƙarshen littafi na ɗaya, mu gauraya da ku cikin littafi na biyu da na uku domin jin yanda labarin zai ci gaba da kayawa. Na san akwai tarin tambayoyi a cikin kanku, haka akwai hasashen da kuke a game da ƙarshen labarin da kuma Mafarin labarin, sai dai fa ku sani Alƙamin Halima.hz a ko da yaushe saɓanin tunanin makaranta ne, duk da cewar a wannan karan na buɗe komai a labarin to amma still a wajena bai zama buɗaɗɗe a gareku ba. Ina da tabbaci gami da yaƙini akan littafin nan, babu danasanin siya balle nadamar karantawa, saboda haka na ke cewa kar da ku sake a barku da cizon yatsan rashin karantawa. Da ₦1K kacal za ku mallaki littafi na biyu da na uku, a shirye na ke tsab wajen faranta zuƙatanku....Mun dai san SO tamkar rayuwa ne, sai dai fa ba ko yaushe ya ke zamowa abu mai sauƙi ba haka kuma ba a ko da yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma menene ke yanke alaƙar soyayya cikin wata alaƙar soyayyar? Rabuwa ko yanke alaƙa na sanya rauni a jikin rayuwar wata halittar! Idan har akwai ƙaddara to akwai adu'a da ke canjata, kazalika idan akwai jinkiri to la shakka da alkhairi, tsananin haƙuri matakin nasarar cinye jarabawa...Takaicin ba kaɗan ba ne, Sadaukarwar me faɗi ce, haka ma butulcin ba kamar yanda sakayyar ke zamowa ba ne, yayin da aka ce akwai soyayya me tsuma zuciya ta sami mafaka a ruhi ɗaya cikin gangar jiki biyu ya tunaninku zai ba ku? Haƙuri ba ya yawa! Ƙunci ba ya dawwama in har da adu'a!...hallau dai ina ƙara nanata muku cigaban rayuwar auren gidan Nazifi da wakanar komai a ƙarshe zai zama saɓanin tunaninku ne tabbas sai dai akwai alƙawarin Happy Ending🥰.Kafin mu luntsuma cikin littafi na biyu zan so mu haɗe a comment section da ku domin bararraje abin da ke ranmu akan littafin ƘAYAR RUWA🔥...ku tura ₦1K via 2081611685,Kuda Bank,Haruna Zakariyya Saadiyya...shaidar biya kai tsaye ta👉🏻07018098175Allah ya horewa kowa kuɗin siya...Show me love masoyana abin sona😍ku girgiza akawunt ɗina da kuɗin littafin ƘAYAR RUWA na san ba zaku bani kunya ba😘...masu son magana da ni chartup via whatsapp 07018098175._* Siyan Na gari mai da kuɗi gida💃🏼tarin godiya ga waɗanda su ka zaɓi fitattu biyar😍son so sai kuyi magana a wannan lamba...Halima.hz(07018098175).*