Kayar ruwa part 1 complete novel - Chapter 6
Kayar ruwa part 1 complete novel Chapter 6: Kayar ruwa part 1 complete novel Chapter 6. A ɓangaren Rumana da Atika kuwa, zuwansu gidan ban da matsala da…
4,482 words
A ɓangaren Rumana da Atika kuwa, zuwansu gidan ban da matsala da nesanta tsakanina da mijina ba abin da ya haifar, yara su ka zamar min annoba, don zan iya cewa ta silar su ne hargitsi ya girmama a cikin gidan aurena, har akansu ina neman na kamu da ciwon zuciya. ya nesanta tsakanina da shi ya kusanta tsakaninsa da yaran fiye da tunani, da su ya ke shawarar duk abin da zai yi a gidan, ko magana zai min wacca ta kama dole sai dai ya faɗawa ɗaya daga cikinsu ta faɗa min, ga yaran sun raina ni, ba wacce na isa na mata magana sai ta min rashin kunya da fitsara, har kallon idona su ke su faɗa min ai Abbansu ba ya sona su ma don haka basa sona, ko abinci na ba su sai su ce ban iya girki ba ba zasu ci ba, idan ya dawo kuma su gilla masa ƙaryar ban ba su abinci ba, ba zan taɓa baƙi ba ƴaƴan nan su ga baƙona da ƙima su gaishe shi. ranar da na tsawatar musu akan ba su gaida Ya Imam ba, Hubbi na dawowa su ka ce ai na zazzagesu na ce zan koresu a gidan, alhalin kuma sun gaida Yayan nawa amsawa ne bai yi ba. ranar na yi kuka na gode Allah, don zagi na cin mutunci da ƙare dangi yay min a gaban yaran. wannan dalilin na cin zarafina da ya ke a gaban yaran sai ya ƙara ba su lasisin yi min duk abin da suka ga dama, ji na ke har gwara kishiya da su, don su idan su ka kunna wata wutar bala'in ba zaka taɓa cewa yara ba ne kuma ba zaka iya kasheta ba. ga sun iya kirsa abin kamar koya musu ake, a gabansa ladabin da su ke yi min kamar uwarsu, amma da zarar an ce bai gidan duk wacca ta ganni ma sai dai tayi min tsaki, ban isa ko ɗaga murya in yi musu ba nayi hakan na shiga uku ranar, idan suka ɓata wuri nasa su gyara sai yaci zarafina. na yi musu faɗa akan ƙin makarantar da su ke hakan sai ya zama tashin hankali har yana faɗin saboda ba ƴaƴana ba ne ba kuma ƴaƴan ƴan uwana ba ne, ina baƙin ciki yayyuna sun kasa sadaukar min da ɗansu ko guda, shi ne shi saboda an ba shi zan takurawa yaransa, to in cire idona daga sha'aninsu tun da ba ni ke ɗaukar nauyinsu ba.
ɓangaren ƴan uwansa kuwa sun taso ni gaba da gorin haihuwa, ba su tsaya iyaka nan ba har faɗi su ke wai me ake da auren ƴan talakawa, sam ba su ga abin da aurena ya tsinanawa ɗan uwansu ba, ban da ma tawaya da yaja masa, da sun san haka aurena zai zamarwa ahalinsu masifa da ba su bari ya aure ni ba. idan na shiga cikinsu tamkar mushe haka suke ja baya da ni suna habaici, a ke min gorin wai ai ko da aka auroni haka na zo babu kayan gara. ƙalilan cikinsu ne ma su tausaya min, sauran duk daga kyara sai hantara da nuna ƙyama, shi yasa na kama kaina na ja gefe domin wulaƙancin na su ya fara min yawa, har bana so abun zuwa cikinsu ya ta so, mugun haƙurina kawai ke sawa na sharesu bana bi ta kansu, idan na ce zan fanɗare ba su isa ma su min kallon banza ba, to bana son tashin hankalin iyayena da damuwarsu, sannan kuma ina tsoron abin da zai jawa igiyar aurena samun matsala.
duk matsaltsalun da ke ta faruwa da sanin surukata, tun ina zuba ido in ga ta tsawatar akan abubuwan da ƴaƴanta su ke min naji shiru, ga mamakina ma sai na ga tana goyon bayansu, itama ta hau kan layinsu, ƴaƴanta su min, ɗanta yay min, itama tayi min. gaba ɗaya na rasa ta ina ƙiyayyar ta samo asali, na rasa laifina. idan na bada haƙuri sai ya ƙara zama wani babban laifin, abin da na lura da shi ma ba akan rashin haihuwa kaɗai yasa su ka tsane ni su ke tsangwamata ba, akwai wani dalili na su a gefe wanda su ka barwa kansu sani. tabbas babu babban tashin hankali a gidan aure irin ace uwar miji ta sanyo ka gaba, ni a baya ban san wani matsalar uwar miji ba, idan naji ƙawayena suna ƙorafi akan uwar miji sai in ce ku ne dai baku iya zama da ita ba, ku sota tamkar mahaifiyarku sannan ku mata biyayya kamar taku mahaifiyar, to duk sanda na faɗi haka Hassana Tijjani ta kanyi murmushi kawai ta ce Sa'ida ba za ki gane ba, in uwar miji na sonki tana sonki kawai, in kuwa bata sonki to wallahi duk son da ɗanta ke miki zaman auren ba zai taɓa yi miki daɗi ba, in kuwa tana sonki to ko ɗanta bai sonki kya sami ƴar salama, ita uwar miji idan ta sako ki gaba duk wani kalar biyayya da za kiyi mata a banza ne, ashe hakan da su ke faɗa gaskiya ne domin kuwa ga shi ina ga ni, kallon banzanta gareni ya fi tsorata ni fiye da na ɗanta.
duk wannan tashin hankalin da na ke ciki iyayena da ƴan uwana babu wanda ya sani, ban taɓa faɗa ba kuma ban taɓa nunawa ba, sai dai kawai fa duk wanda yay min farin sani yana ganina zai ce ina cin matsala, hankalina ba'a kwance yake ba. domin kuwa lokaci guda na fita a hayyacina na ƙara yin wata muguwar rama, nayi duhu duk na sakwarkwace, na zama kamar mara lafiya ƙwaƙwalwa saboda kullum a firgice na ke, haka na ke jin duk rayuwar ta fita a raina, har so na ke dare yayi ɓarawon bacci ya ɗauke ni in sami ƴar salama, don bani da babban tashin hankali sama da wayewar gari, da zarar gari ya waye na shiga fargaba da taraddadi kenan.
uhmm so kenan, wallahi duk wannan tsananin da na ke ciki na gidan aurena har yanzu banji soyayyar mijina ta taɓu a raina ba, ban ji ina nadamar aurensa ba, ban taɓa jin ina ma ya sawwaƙe min in huta ba, sonsa na ke da dukkan raina, sam bana fushi da duk abin da yake min, uzuri na ke masa da kuma adu'a, tun bayan aurena da shi ban canja akalar adu'ata ba, kafin na yiwa kaina shi na ke yiwa, ni har na fi so ya zo yana min bambami akan ya shareni kwata kwata babu magana, kuma kullu yaumin bana fasa zuwa neman yafiyarsa da basa haƙuri a kowanne daren rana kafin kwanciyata, zan ta haƙuri ba zan karaya ba, Allah na zan ta faɗawa ya daidaita tsakaninmu, ya kuma bani ikon cinye jarabawar.
yau na tashi da matsanancin ciwon kai, hakan yasa na kasa fitowa gaba ɗaya, tun da nayi sallar asuba na durƙufa kan sallaya, bacci ma na ke so na koma amma na kasa saboda gabana da ke ta faɗuwa, ga shi ina so na tashi in je in tada yara su yi shirin makaranta sai dai in na tashi jiri sai ya mayar da ni. da ƙyar dai na lallaɓa na tashi a daddafe na fita, ɗakinsu na shiga, na shiga banɗaki na tara musu ruwan wanka, sannan na fito na tashe su kan suyi wanka. su ka tashi da ƙyar kowacce na faman ɓata rai, zama nayi ina lallashinsu da ba su haƙuri akan cewa watarana sai labari, yanzu ne su ke da dama da lokaci na yin karatu, idan basu yi ba nan gaba za su ciji yatsa.
na lallama su da ƙyar su ka sauko su ka wuce banɗakin, na jaddada musu da su yi sallah in sun shirya. ɗaki na koma saboda sanyin zazzaɓi da ya rufe ni, ina shiga na ƙudundune cikin bargo ina ta karkarwa, kaina jinsa na ke kamar zai faɗo, haka cikina ma wani bala'in ciwo ya ke min. ban ankara ba kawai naji amai, duk ƙoƙarina na kar in yi akan gadon hakan sai da ya faskara, amai nayi sosai mai wahalarwar gaske. gaba ɗaya jikina sai ya saki, da ƙyar na kimtsa wajen a wahalce na dawo na kwanta, hawaye kawai na ke zubarwa saboda ni ɗaya na san irin azabar ciwon da na ke ji a jikina. ina cikin wannan halin aka turo ƙofar ɗakin, Rumana naji tana cewa,"Anty mun gama shiryawa".
fito da fuskata nayi ta cikin bargon kaɗan, bana iya ko ganinsu da kyau, murya a wahalce na ce da su. "wayata na kan mudubi ƙarfe nawa?".
Atika ta duba tana cewa,"seven twenty".
idona na rufe, har ga Allah ban da wani ƙarfi da ƙwarin da zan tashi in dafa musu abinci. a hankali na ce da su,"Rumana ban da lafiya, ku yi haƙuri kuje kitchen akwai sauran abincin dare a flask ɗin Abbanku ku ci kun ji, na san bai huce ba. abincin makaranta kuma zan bayar a kawo muku".
su ka yi shiru ba su ce da ni komai ba duk su ka yi cirko cirko. tsoron abin da zai biyo baya yasa na miƙe zaune cikin tsananin azaba, cikin dauriyata na yunƙura zan sauko Rumana ta ce.
"Anty ki koma ki kwanta, a bamu kuɗin makaranta idan mu ka je sai mu siya snacks kafin a shiga class, ba zamu iya cin sauran abincin jiya ba".
na san yanzu Hubbi bai tashi ba, don haka nace da ita,"duba ƙasan littafin can akwai ɗari biyar ku ɗauka".
ɗari biyar ɗin kenan na ke ta ririta ko da wata buƙata ta ujila zata taso min. ta ɗauko tana faɗin babu canji, na ce suje da ita tun da ba su yi breakfast ba, magani nasa ta miƙo min ta fita ta ɗauko ruwa ta kawo min. nayi musu adu'a tare da a dawo lafiya su ka fita, Rumana ɗin ce dama me sauƙi sauƙin kai, don ko yanzu ita ce tayi min sannu tana Allah ya bani lafiya, amma Atika har su ka tafi fuska a murtuke tana ta ƙunƙuni.
ni dai zan iya cewa cikin awa guda na kusa shanye sacet ɗin paracetamol, amma duk da haka babu wani sauƙi da na ke ji a tare da ni, ciwon ma tamkar ƙara shi ake yi, hawaye masu zafi ne kawai ke sauka kan kuncina, idan nayi haka zan ɗau waya in kira shi sai in tuna kashedin da yay min, ba kuma na so in kira gidanmu nan ma ya zama fitina, haka dole na haƙura. adua na ke tayi, da kaɗan kaɗan kuma naji ciwon na ɗan raguwa tun da har ina iya buɗe idona, cikin baccin da ke son kwashe ni naji muryar Hubbi daga can nesa na kiran sunana da amon sautin da ya gigita ni ya firgita ni, zan iya cewa ban taɓa jin tsoro da firgici irin na kiran da yay min a yanzu ba, take kuwa na ambaci ƙalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un domin na san kiran bana lafiya ba ne, kafin na kai ga buɗe idanuwana ya banko ƙofar ɗakin, kana jin yanda ƙofar ta bada garam ka san a hasale ya ke.
"Sa'idaaa". ya ƙara kiran sunan a tsawa ce wanda hakan ya daɗa gigita ni musamman da na ke jiyo hucinsa kamar mayunwacin zaki.
ta cikin bargon da nake ƙudundune na amsa, sai dai bai ma jini ba, ya ƙaraso ciki ya yaye bargon yana sa hannu yay min wata muguwar fincikar da sai ganina nayi tsaye akan ƙafafuna, da sauri na runtse ido tare da dafe bango jin ina neman faɗuwa. na buɗe ido da ƙyar a ɗan runtse na dube shi na ce,"lafiya?, bana jin...".
ban ƙarasa furucina ba ya wanka min zazzafan marin da yasa ni zama daɓas babu shiri, a ruɗe na shiga girgiza kai ina kiran sunan Allah, tun da na ke da shi, tun da muke rayuwa gefen rigarsa bai taɓa sawa ya duke ni da ita ba, amma yau mari, marin ma a mawuyacin halin da na ke ciki, ban wartsake daga jin zafin ba ya shiga cewa.
"Wacce irin muguwa ce ke mara imani da tausayi, wannan ai tsagoron zalunci ne, banda rashin hankali da tunani irin naki ki bar yara su fita da sanyin safiya ba tare da kin basu abinci sun ci ba, haka babu abincin makaranta, Sa'ida haka aka yi miki da kina yarinya shi ne kike neman hucewa akan yarana?, wato saboda ba ƴaƴanki ba ne, ba ke kika haifa ba shi ne za ki azabtar da su da yunwa, wai me yaran nan su ka miki kika ɗora musu karan tsana?, kawai don ba ke kika haife su ba?, yunwa Sa'ida, kisa fa take yi, ko ke aka bari da yunwa ai an zalunce ki balle ƙananan yara, ba kya tunanin hakkinsu ya biki ya hanaki sukunin rayuwa, yaran nan fa yanzu ni ne mahaifinsu, ko darajata ai sa ci ki sassauta musu, amma saboda dai zuciyarki a mace take, tayi maƙil da baƙin ciki da zalunci shi ne za ki huce haushinki akan su, to Allah ya isansu, kuma ni bazan yafe miki ba...".
tun marin da yay min na nemi ciwon jikina na rasa, kallonsa na ke da mamaki ƙarara, idona tamkar an buɗe famfo haka hawaye ya ke sunturi saman fuskata, jujjuya kaina kawai na ke na rasa bakin magana. cikin kyarmar jiki na kamo hannunsa, na san zafin jikina da ya ratsa shi ne yasa shi ware ido akaina, ina kuka sosai na shiga ce masa.
"don Allah kayi haƙuri, wallahi ko kaɗan ba da gayya ko mugunta na bari su ka fita ba abinci ba, Hubbi ba ni da lafiya, ba ni da ƙarfin da zan iya tashi, ka tambayesu har kwatanta hakan na yi naji ba zan iya ba, kai kanka ka san in ba lalura ba babu abin da zai kwantar da ni a ɗaki har wa yanzu duk kuwa halin da muke ciki, amma na rantse da Allah ban bari sun fita ba su ci komai ba saboda mugunta ko rashin so ba, Hubbi ban tsani yaranka ba, ban taɓa jin ina ƙin su ba balle har in ƙuduri cutar da su, Allah shahidi shi ne shaidata yanda zan so ɗan cikina haka na ke sonsu, Hubbi ƴaƴan ƴan'uwanka ne fa, kai kuma ɗin nan ina sonka, mijina ne kai, Hubbi don me zan ƙi abin da aka baka?, don Allah ka sassauta fushinki ka ke daina faɗin duk abin da ya zo bakinka...".
buge hannuna yay daga jikinsa yana ƙara faɗin,"shashasha kawai, bagidajiya wadda bata san hakkin yaro ba. sai ki laifi da an miki faɗa ki fashe da kuka, a hakan kike sona?, idan kina sona ai ba za ki wulaƙanta ƴan uwana ba, ba zaki ƙi yarana ba. kuma ki sani wallahi tallahi yanda kika azabtar da su da yunwa haka kema zan hukuntaki, Sa'ida sai kin yi matuƙar danasanin abin da kika aikata a yau, wawiya mara aiki da iliminta".
fita yay daga ɗakin yana ta surfa masifa, na daskare wuri ɗaya ina bin bayansa da ido, ƙirjina naji ya matuƙar yin nauyi, me na yiwa Hubbi a wannan rayuwar ne?, wanne kuskure na aikata masa da ban cancanci yafiyarsa ba?, mijina me kyan hali da nagarta ne, ta ko'ina amfani da yake da tarin ilimin addininsa, amma me ya sauya shi?.
ban san lokacin da na zamo daga gefen gadon ba gwiwoyina su ka dire a ƙasa, na fashe da matsanancin kuka. me yasa aurena zai tashi daga rayuwar farinciki ya juye zuwa rayuwar baƙin ciki?, mun auri juna ne don muna son juna, mun fuskanci ƙalubale da yawa tun daga haɗuwarmu har aurenmu, duk tarin ƙalubalen da muka fuskanta bamu taɓa ji a ranmu cewa zamu haƙura da juna ba haka har muka yi nasara, amma me ya kawo canjin a lokaci farat ɗaya haka?, lokacin da ya kamata ace munji daɗin rayuwarmu, mun dulmiya cikin kwanciyar hankali da natsuwa.
Haihuwa!, kalmar ta motsa da zuciyata, kenan yau da zan haihu shikenan komai zai sauya?, kowa zai koma sona tamkar a baya?, za'a daina tsangwamata da tashin hankali?, idan kuma ban haihu ba shikenan haka za'a ci gaba da tafiya?. zuciyata ce ta fara jujjuya tunanika, wa ya kamata in kira in shaida masa halin da na ke ciki?, wa zan sanarwa da cewa rayuwar aurena ta juya cikin tsananin baƙin ciki da ƙuncin da ban taɓa tsammani ba, wa zan kira ya lallashe ni ya bani haƙuri da shawara?.
mahaifiyata ce ta zo cikin kaina, sai dai ba zan taɓa iya kiranta in sanar mata da matsalar nan ba, ba zan iya faɗa mata matsalar gidan aurena ba, na ƙwammaci in zauna a hakan ko zan mutu in mutu, har kullum farin cikin iyayena da kwanciyar hankalinsu na ke so, saboda haka ba zan taɓa bari su san halin da na ke ciki ba.
kai na kifa a gefen gadon, idona a rumtse yake kalaman cin mutuncin Hubbi nata yawo cikin kaina, lokaci guda kuma wani lokaci ya haska a cikin idanuna, yayin da wasu kalamai na lokacin su ka haska tarr a cikin kaina, jinsu na ke suna amsawa a ƙoƙon kaina tamkar yanzu yake faɗar su.
_"na yi miki alƙawarin zan tsaya a tare da ke a kowanne irin yanayi, nayi miki alƙawari cewa duk wata matsala ta hanyarki ni zata fara fuskanta, na yi miki alƙawari zan ba ki kariya ta kowanne gefe, na yi miki alƙawari ba zan taɓa bari idanunki su yi hawaye ba, na yi miki alƙawari a kowacce rana zan yi ƙoƙarin dacewa da ke, ba zan juya miki baya ba, ba zan taɓa canja miki ba, nayi miki alƙawarin cire ki daga duk wani baƙin ciki, nayi miki alƙawari Sa'ida! daga yau da kika zamto matata, dukkan soyayyata, amanata da rayuwata naki ne ke ɗaya, ina sonki Sa'ida, alƙawarin dawwamammen farin ciki Habibty"._
waɗannan sune kalaman da yay min a ranar ɗaurin aurenmu, bayan ɗaurin aure san da suka zo gidanmu gaisuwar surukai, na same shi a ɗakin Yashaik kafin a gama kimtsa cikin gidan su shiga. lokacin da na shiga na tsaya na kasa zama wurin da yake min nuni saboda kunya, wanda hakan yasa shi tasowa ya tsaya gabana tare da kamo hannayena duka biyun ya saka cikin nasa ya haɗe, kaina na ƙasa a wannan lokacin amma haka ya ɗago fuskata da dogon hancinsa, ya tilasta min saka ƙwayar idona a tasa kafin ya shiga karanta min waɗancan kalaman fuskarsa na me washewa da dukkan murmushin farin ciki da jin daɗi gami da alfahari.
sabbin hawaye ne masu zafi suka shiga zubo min, a raina ina tambayar duk ina wannan tarin alƙawarin da yay min?, shin mantawa yay ko kuma fatali yay da su?. doguwar ajiyar zuciya na sauke tunawa da farkon rayuwar aurenmu, sai kawai na saki murmushi me ciwo, ko ba komai ai nayi farin ciki tare da shi ko ya ya ne, ina alfahari da iyaka wannan ma. tsaida kukana na yi na miƙe na shiga banɗaki na wanko fuskata, na gyara jikina sannan na fita jiki a saɓule, tunanina me zan dafawa yaran cikin ƙanƙanen lokaci, amma me daɗi wanda zai gusar da rashin jin daɗinsu, abincin da su ke matuƙar so na tuna, wanda hakan yasa na sauka daga benen cikin karsashi, sai dai da zuwana ƙofar kitchen na murɗa handle naji ta a rufe, na zaga ta ɗaga ƙofar itama a rufe. *(8)* doguwar ajiyar zuciya na sauke, kenan da gaske ya ke akan furucinsa na zai hukunta ni akan barin ƴaƴansa da nayi da yunwa. yanda ban ba su sun ci na safe ba haka kenan nima yau zan wuni babu ci?, dama ana horo da yunwa?. kan kujera na koma na zauna na rafka tagumi, jefi jefi sai na sa hannu in goge hawayen da ke sakko min, tunani na ke yi daban daban, sai dai akan kowanne na rasa irin warwarar da zan masa. na kalli agogo naga ƙarfe goma da minti sha biyar, kuma kaɗawar lokacin ya haɗe da ƙugin da cikina yay saboda tsabagen yunwa, dama banci na daren jiya ba, lokaci guda dukkan tunanina ya tsaya cak, take kuma nauyin kaina ya dawo naji yay bala'in sara min, nayi saurin dafewa ina mai rumtse ido tare da jinginar da kaina jikin kujera, wucewar daƙiƙu uku na miƙe jiki babu ƙwari ina matuƙar jin jiri, a daddafe da bango na fita daga falon zuwa farfajiyar gidan.
can ta bayan gidan na nufa wajen da shuke shuken fulawoyi su ke, na nemi manyan duwatsu da busassun itatuwan fulawa da aka ciccire na haɗa murhu, na gangaro durum na kawo shi bakin tagar kicin. takawa nayi na zura hannu ciki, da dabara na samu na buɗe murfin durowar sama da ƙyar tukunna na lalubo ashana, dama tagar da ɗan faɗinta da haka nayi nasarar ciro ƙaramar tukunya. zuwa nayi na iza wuta na ɗora tukunyar, sannan na dawo na gangara durom ɗin zuwa tagar suto, shi dama ana iya shiga ta tagar don haka na shiga ta ciki na ɗebo macaronie da kayan sarrafata wajen girkawa, cikin sauri sauri na ke komai gudun kar mai gidan ya dawo.
a wurin me gadi na aro wuƙa da ce masa na nemi tawa na rasa, don haka yankan kayan miyan nayi tun da babu abin jajjage. nan da nan na tashi jalof ɗin macaronie, adu'a na ke tayi ta dahu da wuri har in samu na zuba akaiwa ƴan makaranta abinci tun da break biyu su ke fitowa dama, babu ƙaramin cooler da zan zuba musu abincin don haka ɗakina na koma dole na lalubo wani ƙaton flask me guda ɗaya, ashe da ranarsa da har ina cewa Kakarmu da ta bani bana so, a cikinsa na juye musu abincin na rage kaɗan wanda zan ci.
bayan na kammala haɗa musu komai ina sauri in fito in kaiwa Me gadi ya taimaka ya kai musu, isata bakin kofa in ɗaga labule na jiyo kamar tashin hayaniya daga compound, sai dai kafin nayi wani tunani akai aka cakumar min wuya. tsoro yasa na ambaci sunan ilahu da ƙarfi, sai dai idona na sauka kan wacce ke damƙe da wuyana abin ya bani girgiza ni. Anty Aysha ce sai huci take tana hararata, gaban rigata na ƙara kallo in da ta cukume da kyau, kafin nayi magana Anty Aysha ta riga ni da cewa, "don bura'ubanki wacece ke?, wanne kalar jahilci ne cikin kanki?, uban me kike gadara da shi a cikin gidan nan da kike ganin kin isa ki yi kowanne kalar iskanci ki zauna lafiya?, to koma me kike ji da shi yau zan banbance miki tsakanin aya da tsakuwa, zan sauke miki kowanne kalar buyagi Sa'ida, tabbas yau za ki ciji yatsa kina me nadamar abin da kika aikata don kutumar ubanki".
baki sake na ke kallonta da maɗaukakin mamaki, ba kalaman ba ne su ka shige ni, zagin shi ya girgiza ni. ko ban kasance matar ƙaninta ba ina ganin ai babu dacewa ta danƙara min zagi na rashin ɗa'a irin haka. sai dai kafin na kai ga wani motsi Yaya da ta iso ta ɗauke ni da gigitaccen marin da ya kai ni kifewa ƙasa, sai dai nayi jarumtar riƙe kaina a tsaye.
kuma kafin zafin marin ya sakeni ta ƙara min wani ta ɗaya ɓarin, wanda a ruɗe na ɗago ina ƙoƙarin ƙwace riƙon da Anty Aysha tayi min inyi ta kaina.
ganin hakan Yaya tace,"Au ƙoƙarin ƙwacewa ma kike?, guduwa za ki?, To bara nayi miki dukan tsiya sai naga da wanne ƙarfin za ki ƙwace ki gudu, Sa'ida ai yanda kika kwantar min da Yarinya a asibiti kema sai na illataki wallahi".
tana faɗin hakan ta fara dukana, duk inda hannunta ya kai a jikina nan take duka kamar wacce ta samu ganga, ni kuma duk wannan bala'in da na ke ciki tunanina ba ya ga in ƙwaci kaina ko in ɗau matakin cin zarafin, a'a hankalina da tunanina na kan furucinta na cewa na kwantar mata da ƴa a asibiti, wacce ƴar?, mene dalilin kwanciyar?, kar dai sharri yaran su ka haɗa min?, waɗannan su ne tarin tambayoyin da ke cikin kaina kuma amsarsu kawai na ke da buƙata.
sai da na farga daga hallakanin da suke shirin yi tukunna na fara kiciniyar ƙwatar kaina, amma ina sun riƙe ni gam sai dukana su ke babu ta yanda za'ai na iya ƙwacewa kun san ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi.
"Yaya ki daki cikin shegiya tunda babu uwar komai a ciki sai kashi".
Anty Aysha ta faɗa tana kallon Yaya. Ai kuwa kamar Yaya na jiran tuni akan hakan ta dunƙule hannu ta daki cikina da ƙarfi. "Wayyo Allah!". na faɗa da ƙarfi jin azaba wacce ban taɓa jin irinta ba a cikina.
cikani Anty Aysha tayi ta duƙa ta ɗaga ƙafata nayi baya na kifa ƙasa, ta saka ƙafa ta dakar min kwankwaso, a wahalace na runtse ido ina kuka amma hakan baisa sun daina dukana ba. da dukkan iyawata na tattaro ɗan ƙarfina na ture su daga jikina, naja baya da sauri ina ɓoye kaina. idonuna masu zubar da zazzafan hawaye ya tsaya cak akan Yaya wacce ke numfashin wahala tana girgiza, yanda take abin ba zaka taɓa sanyata cikin sahun manya mutane ba, ba ƙaramar mace ba ce, sai ƙwaƙwalwarta kawai da ke aiki da ƙarancin shekaru, zancen da na ke muku tana kan shekaru arba'in da ƴan kai ne.
"bagidajiya ƴar gidan ƙananun mutane, shashasha wacce bata ajiye komai ba. ke har kina da ikon hana ƴarmu abinci a cikin gidan ƙaninmu?, wawiya kawai, ba ki san da cewa ta fiki dajara da ƙima a idanun mai gidan ba?, ko mancewa ki kai da ana rabuwa da uwa a zauna da Ƴaƴa?...ko kuma ganin an zuba miki ido kina zaune ke kaɗai har yanzu cikin gidan nan shi ne kike son zuba iskancin da kike so. To ta ƙare wallahi, daga yau komai yazo ƙarshe, za ki gane kin hora ƴaƴanmu da yunwa, za ki tabbatar da bani da mutunci bani da kirki ko kaɗan. Kuma na rantse da Allah in kika sake wata cutar ta sami Atika sai na saka an ɓalla miki ƙafa dan ba zan kai ki police ba, sakawa zanyi kema a kashe ki dan uwarki da ubanki, azzaluma wacce bata san ciwon ƴaƴa ba".
Yaya ke wannan furucin da suke daidai da watsa ruwan zafi a jikina, kallo take min mai cike da tsana, yayin da ni kuma ke mata kallon da na kasa fassara shi. idona ya koma kan Anty Aisha da ke cewa,"saboda ba ki san darajar haihuwa ba, ba ki san zafin ɗaukar ciki ba, ba ki san wahalar laulayi ba dole ki bar mana yara babu abinci tun da abincin ubanki ne ya kawo. Mahaukaciya! jahila! juya! wacce da ita da namiji basu da banbanci, har gwara ma namiji zai yi ciki a ɗauka ke kuwa fa?, shekara takwas ba ɓatan wata balle ɓari"