Kenza eBookz

Kayar ruwa part 1 complete novel - Chapter 8

Kayar ruwa part 1 complete novel - Chapter 8

Kayar ruwa part 1 complete novel Chapter 8: Kayar ruwa part 1 complete novel Chapter 8. shi dai yana tsaye kamar wani gunki kallona kawai yake yi, ya…

4,460 words

shi dai yana tsaye kamar wani gunki kallona kawai yake yi, ya shirya cikin manyan kaya riga da wando na yadi milk colour, yayi bala'in kyau kansa babu hula. kasa daina kallonsa nayi saboda masifar kyawun da yayi min, ba tare da shiryawa ba murmushi ya suɓuce min yayin kallonsa, kalmar kayi kyau na ke shirin faɗa masa, amma sai dai saƙon da ke a saman fuskarsa yasa na sunkuyar da kaina ƙasa na ce,"Ina kwana".

Maimakon amsa gaisuwar tawa sai ji nayi ya ce,"Kafin nan da awa guda ki tabbatar kin tattara kayan ki kin bar min gida, kije gidanku ki zauna har sai san da na neme ki".

a zabure na waro idanu waje har ban san lokacin da na sauko akan gadon ba saboda ruɗani, hannuna dafe da ƙirji idanunsa cikin nawa na ce,"Hubbi me ka ce?".

ransa a haɗe tamkar hadari ya ce,"Kinji ai ba kya buƙatar na maimata miki, ki tabbatar kafin na dawo kin bar gidan nan in ba haka ba za ki yi karo da abin da ba ki taɓa karo da shi ba, wallahi muddin na dawo na sameki sai na miki wulaƙancin da kare ma ba zai shinshina ba".

ya faɗa yana nuna ni da yatsa, kafin ya fita ya barni tsaye cikin maɗaukakin mamaki da tsantsar al'ajabi, haka na ƙame kamar gunki ƙofar kawai na ke kallo idona ko ƙiftawa ba yayi, tashin hankali da firgicin da su ke zuciyata kuwa tamkar zata faso ƙirjina ta fito.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un". na faɗa a bayyane ƙirjina yana harbawa hannayena har lokacin dafe da ƙirjina.

"lamarin har ya kai haka?, duk haƙurin da na ba shi?, wanne irin bala'i ne wannan?, in tafi gida fa har sai ya neme ni, me yay zafi har zai yanke tsatstsauran hukunci haka? akan dai iya abin da ya faru jiya ko kuma da wani laifin daban a gefe da ban san da shi ba? to ni kuwa in je in ce da su Abbaa me?".

a fili nayi maganar ina jan numfashi sama. daɓas na zauna kan gadon na kafe wuri ɗaya da kallo, cikin kaina na rasa tunanin me zan yi, na kuma rasa inda zan ɗora wannan al'amarin me girman gaske. ban san lokacin da hawaye ya shiga zarya a idanuna ba, lallai ina cikin jarabawa, kuma tabbas na yiwa kaina alƙawarin cinyeta, ba zan taɓa bari na faɗi ba in Allah ya yarda.

zuciyata ta fara bani umarnin gaggawar tashi in bar gidan karma ya dawo ya same ni yay min abin da zai zama sanadin bugawar zuciyata a yau, a karon farko naji bana son ganin ko da inuwarsa. haka na buɗe wadrobe ina ɗebo kayana, ina zubawa cikin akwatu ina magana tamkar zararriya.

"Me zan ce idan na koma gida? Na ce musu mijina ya ce in je gida sai ya neme ni?, bisa laifin me? da wanne ido zan kalle su in musu bayani? Hasbunallahu wani'imal wakil, Hubbi meyasa! Me na maka a rayuwa Hubbi?".

ina kuka sosai haka na gama haɗa kayana, na ɗauko hijabina zan saka wayata da ke kan madubi tayi ƙara, na rufe wardrobe ɗin na ƙarasa da sauri na ɗauki wayar don na shaida kiran Ummani daga ringtone ɗin da na saka mata na Uwa Uwa Mama me share min kukana.

sai da na saita kaina da danne yanayin da na ke ciki na ce,"Salamu alaikum Ummani, ina yini".

Daga can ɓangaren ta ce,"barkan ki dai Sa'ida, an yini lafiya, ya kike ke da mai gidan naki?."

na ce,"Lafiya lau Ummani, duk kuna lafiya?".

ta amsa,"lafiya lau, amma ya naji muryar taki kamar ba ki da lafiya."

na ce,"Ehh wallah Ummani na tashi da ciwon kai ne yau, yanzu na tashi a bacci ma shisa kika ji muryan nawa haka, dama ina cewa zuwa anjima zan kiraki".

na faɗi hakan ina dafe kaina yayin da sabbin hawaye masu zafin gaske ke zaryo min.

ta ce,"subhanallah to kin dai sha magani ko?".

na ce,"ehh na sha, shi ne ma naji daɗi ai".

ta ce,"to Allah ya sawwaƙe. daman maganar zuwa ƙauye zan miki na bikin ƴar gidan Kawu Musbahu, gobe ne tafiyar da safe in Allah ya kaimu, ga shi na ji ki babu lafiya sai dai ki haƙura kya je musu daga baya ko".

tamkar anyi min bushara da kujerar makka haka naji maganar Ummani, wani farin ciki ya lulluɓe ni har hakan na bayyana akan fuskata, cikin saurin maganar da ban taɓa yi ba na ce,"lahh ai ciwon kaine fa kawai Ummani, kuma na faɗa miki naji daɗi ma".

sautin murmushin manyancenta ya bayyana har ya taɓa zuciyata, ta ce"ke dai kawai za kiyi ƙarfin halin naki da kika saba, to Allah dai ya ƙara lafiya. sai ki faɗawa mijin naki, idan ya barki kin fito da sassafe to mu tafi tare, in bai barki ba kuma kya taho ke ɗaya tun da kuna da direba".

na ce,"ai kamar ma na sani muka yi maganar da shi ɗazu, da yake shima yana shirin tafiya za su koma dubai, kin san dama nayi miki magana an gama ginin ɗaya plaza ɗin da ya buɗe. sai na ke ce masa to daga biki kuma sai in ɗan yi kwanaki a gida ya ce babu matsala".

ta ce,"ah tou faɗuwa ma ta zo daidai da zama, shikenan to sai kin zo ɗin. kya ce masa ina masa Allah kiyaye".

da haka muka yi sallama ina mai farin ciki na samun damar da zan fake da ita ba tare da kowa ya san dalilin zaman da zanyi a gida ba bayan gama biki, wanda ina roƙon Allah yasa zuwa lokacin komai ya saisaita. sai dai kuma a gefe guda zuciyata cike fal da tarin fargaba da tsoro mara misaltuwa. *(10)* Cikin farin ciki na ci gaba da shirina, har da kayan da zan bayar a ƙauye duka na haɗa, ban san lokacin da zaman zai ɗauke ni ba tun da bai ce ga iyaka adadin kwanakin da ya bani ba, dalilin da yasa na tabbatar da na ɗauki duk abin da zan buƙata kenan. har wani ɓari na zuciyata ma na faɗa min wataƙila tafiyar da zanyi tafiya ce ba ta dawo ba, imma mutuwa ta ɗauke ni imma kuma sanadin zaman auren kenan. jikina naji ya mutu gaba ɗaya sai dai kuma ba wani jimawa naji wani ƙarfi ya ziyarci jikina na musamman, dan ma banda isassan lafiyar da ƙarfin zai tasiri sosai a jikina.

bayan duk na gama fitar da kayan can compound na dawo domin rufe ƙofar ɗakin, sai dai a lokacin da na ɗora hannu bisa hannun ƙofar zan jawo, idona ya maƙale akan cikin ɗakin na kasa ƙiftawa na wucewar mintuna uku. zuciyata ta matse, ƙirjina yay zafi, gabana yay mummunar faɗuwa, hankalina ya kai ƙololuwar tashi, ruwan hawayen da na tsayar na ce ba za su ƙara sauka ba a yau sai ga su tamkar an kunna famfo. cikin mutuwar jiki da fargaba na janyo ƙofar na rufe ina mai juya mata baya, yacca na ke sakkowa daga matakalen benen kamar marar lakka a jiki, kalamansa ne su ke maimaituwa cikin kaina na inje har sai randa ya neme ni, cikin raina sai na ke jin shikenan wannna tafiyar tafiya ce da ba zan ƙara waigowa na kalli wancan ɗakin a matsayin ɗakin aurena ba, sai na ke jin kamar ya furta min kalmomin saki ne kuma saki na har abadan ɗin da ba zamu ƙara rayuwa tare ba, na ke jin sai dai na fara amsa sunan tsohuwar matar Nazifi ba matar Nazifi ba.

sam bana wani gani da kyau na ƙarasa na ce da mai gadi ya tayani fidda kayan waje, idan an sami adaidata sahu ya taimaka ya taro min. kamar ya san abin da yake faruwa na ga jikinsa duk yay sanyi har ya gaza haƙurin furta min lafiya dai ko Hajiya?, na ɗaga masa kai ina riƙe yanayina da cewa,"ana biki ne a gida zanje in kwanaki".

anan bakin gate na tsaya ina jiran ya dawo daga samomin adaidaitar, shiru shiru babu labarinsa kawai na gaji na samu wasu yara na ce su ɗaukar min jakunkunan su kai min titi, muka dandale yanda zan biya su sannan su kai gaba ina biye da su a baya. sai bayan zuwana titi na tuna da babu fa ko sisi a hannuna, mafi kusa na samu shagon p.o.s na je na ciri kuɗi dubu huɗu, kuɗin da Abbaa ya turo min ne jiya da daddare, banda Allah yasa ya turo min da ban san ya zan yi da tafiyar ba, dole sai dai in tafi a ƙasa don ba zan dai je gidanmu in ce a bani kuɗi zan bawa me machine ba, ko a rayuwar baya ban yi haka ba balle yanzu, ba zan iya tonawa kaina da mijina asiri ba.

na sallami yaran na tsaya nan jiran samun mota, na mance gaba ɗaya ban saka niƙabi ba ga zafin rana sai dukan fuskata ya ke. na tsayar da masu adaidaita sahu sun fi shida babu wanda ya tsaya, duk wanda na cewa makwarari sai ya ce ba can yay ba, a taƙaice dai sai da na shafe mintuna kusan sha biyar tsaye kafin na samu wani ya tsaya, shima bayan na gama yi masa kwatancen in da zai kaini sai yace kai ba zai shiga ciki ba, har yay gaba kuma sai ga shi ya dawo yana cewa in shigo.

zan tsaya ciniki ya ce ba matsala abun biya ba zai gagara ba muje kawai, da kansa ya taimaka ya saka min kayan a ciki, wasu ƴan mintuna su ka kawomu ƙofar gidanmu don tun da muka taho bai yi tsaye tsaye ba, in an tsayar da shi ba ya tsayawa, har na ce masa ya ƙara samun passenger ya ce a'a babu matsala yafi so ya sauke ni tukunna. ya sakko min da kayana, Yaran da suke can ta gefen gidanmu na kira na roƙe su suka shigar min da kayan cikin gida, su ka barni ina ƙoƙarin baiwa mai adaidaita kuɗinsa, sai dai kafin ma na kai ga buɗe jakar naji ya tashi machine ɗin yana shirin tafiya.

dakatar da shi nayi da cewa,"ban baka kuɗin ba".

ya ɗan leƙo kai yana cewa,"Hajiya ai an biya".

"an biya?". na tambaya da mamaki. kafin na ƙara cewa,"kaman ya an biya Malam, ban baka kuɗi ba fa tun da muka taho kace ne in bari mu ƙaraso".

ya ce,"ehh tou Hajiya da kika tsayar da ni da farko nayi gaba, sai wani bawan Allah ya dakatar da ni ya ce in dawo na ɗauke ki, da ina ce masa ba zani ba gaskiya to kinga abin da ya bani shi ne dalilin dawowa na ɗauke ki, kuma daga sauke kin nan na tashi a aiki sai bayan kwana biyu kuma".

ya faɗa yana zaro farar envelop a aljihunsa ya buɗe ya nuna min ƴan dubu dubun da su ke ciki sabbi karrr masu yawa, daga ganinsu daga injin bugu sai hannun manajan da ya zuba su ciki, a iya ido adadin su kasan ba iya ƙirgen yatsun hannu ba ne sai an haɗa da na ƙafa. mamaki ƙarara ya bayyana a fuskata, ƙwayar idona kuma na kallonsa da ayoyin tambayoyi da son tuhumarsa.

"ai wallahi Hajiya ban taɓa taka sa'a a rayuwata ba irin yau, ni dai naji daɗin ɗaukarki wallahi. ban san waye ba amma idan rabonsa ce ke Allah ya haɗaku domin ya ce kar in ma yi kuskuren shaida miki shi".

rai na haɗe na ce,"kai Malam ni fa matar aure ce, ko da ka ganni daga gidan mijina na zo gidanmu. kai kawai kaga mutum baka san da ga ina ba ya kama baka kuɗi ka karɓa, to ni da kuɗina don haka ga hakkinka nan, babu ruwana da kuɗin da wani ya baka".

yay ƴar dariya da cewa,"ah ban ga kin yi kama da matar aure ba gaskiya, kuɗinki kuma ko na karɓa ma wallahi sadaƙa zan miki da su, gwara ki ɗauka ki rage zafi kafin Alhajin Allah ya bayyana a gareki ki huta da hawa abin haya".

ko kusa ko alama tunanin Nazifi a lokacin bai zo cikin kaina ba, idan ma tunanin nasa ya zo ba zan kawo shi ya biya ba dan babu ta yanda za'ai ya ɗau wannan uban kuɗin ya bayar kawai kuɗin motar da bai wuce ɗari shida ba, abu sai ka ce a film ko littafi, ai ba hauka ake ba, kuɗin ba tsigarsu yake yi ba. don haka tsaki naja dogo na wuce gida ina faman masifa akan irin ƴan rainin hankalin adaidaitar nan.

shi kuwa me adaidaita ya murɗa babur ɗinsa ya bar ƙofar gidan, tafe yake kawai idanunsa na haska masa hoton arniyar motar waccan mutumin, da shi kansa mutumin da kamarsa ta nuna tamkar sarki, ko ba sarki ba to ya ratsu cikin jinin sarauta, irin su ne zaka musu kallo ɗaya kasan da ba su taɓa sanin babu ba, haka ba su ƙyashin fiddawa su bayar. me ɗan sahu dai har ransa yaji mugun tausayin Sa'ida idan har mutumin yazo wajenta taƙi amince masa don yaga da gaske namijin aure ne.

ina shiga gida na tarar da Ummani a tsakar gida tana gyaran alayyawu, ta riƙe haɓa tana kallona ta ce, "Amma dai kuwa Allah ya shirye ki Sa'ida, haka sai da kika taho yanzu?."

yanayin fuskata kuma yasa ta ƙara cewa,"to ke da wa kuma daga zuwa sai ɓacin rai?".

dafe kai nayi ina zaunawa a kusa da ita na ce,"wani banzan me adaidaita sahu ne mara tunani da lissafi kawai".

ta ce da ni,"ai sai haƙuri, suyi haƙuri da mu muyi da su haka lamarin ya ke. sai ki saki ran naki haka kuma, ni ina zan wani farin ciki ina ganinki rai ɓace, ai sai kisa ni a damuwa".

jikinta na faɗa ina kwantar da kaina bisa kafaɗarta ina cewa,"Ummani nayi kewarki sosai wallahi, tun fa mutuwar Inna Talatu ko?". na faɗa ina shigewa jikinta kaman zan koma cikinta.

ta ce,"Kai jama'a, wai Sa'ida kam sai yaushe za ki girma ne ni kam, kita maƙalƙale ni kaman wacce bata bar shan nono ba? To ko dai cikin zan mayar da ke?"

ta faɗa cikin ƴar dariya tana mai tarairayo ni jikinta, yayin da farin cikin ganina ke lulluɓe da ita. murmushi nayi ina ƙara narkewa a jikinta ina jin wani irin tasirin natsuwa, so, ƙauna, salama, jin ƙai, na fitowa daga jikinta yana ratsa ilahirin nawa jikin.

na ƙara cewa,"Nayi kewar ki ne sosai Ummani, gaskiya mata muna ƙoƙari wallahi, in ba auren ba me zai nesantaka da ɗumin jikin mahaifiyarka har akai watanni da yawa".

Ummani ta ce,"to ya za'ai auren kenan, kuma ai ku godewa Allah ma da zamani ya canja, mu lokacin da akayi namu auren tsakaninmu da gida ai sai shekara shekara in dai ba da wani babban dalili ba".

na ɗago kai a jikinta ina zaro ido waje in ce,"shekara! tabɗijam, sai ka ce waɗanda aka kai kurkuku, duk haƙurina ba zan iya ba kam sai dai in haƙura da auren".

harara ta watsa min tana dungure min kai ta ce,"ke dai anyi autar gaske, Sa'ida aure sunnah ina ke ina cewa za ki haƙura da shi. hakan ma ki gode Allah mijinki ba mai tsananin kulle ba ne".

"Allah Ummani ko a haka ina jin rashin daɗi, shi ma ai kusan tsananin gare shi akan fita".

"eyy fa to ba laifi kam Nazifi shima ba ya son fita amma ai ba kamar wanda za ki ga sun wuce wata uku biyar babu in da suka leƙa, kuma ke fa duk wata hidima idan ta tashi ya barki kije. kuma ni fa daɗin hakan naji bacin haka Sa'ida in aka biye miki ai rana ɗai ɗai ne ba zaki zo gidan nan ba".

lafewa na ƙara yi a jikinta ina murmushi, ina jin tsantsar farin ciki da jin daɗin kasancewa da ita na ratsa zuciyata. idona a lumshe naji tana cewa,"mage sarkin son jiki sai ki tashi ai kije ki gaida mutanan gidan".

na zame a jikin nata ina cewa,"wai ina su Yasmin da aka barki ke ɗaya?". na faɗa ina ƙoƙarin karɓawar wuƙar hannunta ita kuma tana cewa,"waɗannan yaran yanzu ai sai Annabin yabo, kan in ƙyalla ido sai dai kiga na neme su na rasa. yanzu fa zancen da na ke miki ban san da fitar su ba kuma da suna zaune nan Walida na kafa min sharaɗan kar in musu miya me yaji".

nayi dariya ina cewa,"sai na fara make Walida in bata yi wasa ba, wato tsabar ta kai Babata ma take kafawa sharaɗi, lallai samun wurin zama, to kuwa rabon in kwasheta in mayar da ita wurin uwatta ne".

Ummani tayi dariya sosai ta ce,"ke da ubanta ai kun fi kusa. ni dai ƙyale ni da tayin aikin kije ki gaida mutan gidan tukunna". sai kuma ta ƙara cewa,"a'a sai yanzu ma abin yazo kaina, ina ƴaƴan na ki ba ku taho tare ba?".

allon ƙirjina naji ya girgiza, na tuna da yaran da nake jinsu yanzu har raina, na ce,"kin san da makaranta, musamman tasu da ba'a fashi, shiyasa na kai su wajen Iyam, amma suna ta rigimar za su biyoni su zo wurinki na ce su bari sai anyi hutu sa zo suyi kwanaki ma".

tana murmushi da ya nuna jin daɗin furucin nawa ta ce,"Allah sarki yaran albarka, wallahi Sa'ida sosai na ji daɗin kyautar nan da aka maki. zan samu lokaci in je har gida in yiwa Iyam ɗin godiya".

na yunƙura zan miƙe ta ce,"ke dakata me na ke gani a fuskarki haka? Na ganta a kumbure".

Gabana ya faɗi amma haka na ƙaƙalo guntuwar dariya na ce,"sharrin mura ne...shekaranjiya ta saka min azababben ciwon kai, muka je asibiti suka bani wani magani, shi ne ni kuma saboda tayi saurin tafiya na sha overdose ya juyar min da kai na koma kamar wata ƴar maye, garin sakkowa a bene layi ya ɗebe ni na ƙuma fuska a hannun bene".

ta kalle ni da kyau tana girgiza kai ta ce,"ke kam naga ranar da za kiyi hankali, ina ke ina shan maganin mura har over, ko da ya ke da aka samu ɗin ma kika sha".

fuskata ta ƙara washewa da gajeriyar dariya na ce,"Ai fa shima haka yayta faɗa".

"ai dole yayi miki faɗa, da kin gangaro daga saman fa?".

na datse maganar da cewa,"Allah ya taƙaita ai, Ummani ni fa yunwa na ke ji mura bata barni na ci komai ba yau, zumuɗin zuwa nan ne ma yasa na kasa tsayawa girki".

"naga alama ɗaukin zuwa ƙauye yay miki yawa. je ku gaisa ɗin kafin ki dawo miyar ta kammala, nima sauri na ke tayi kar uwar tawa ta dawo ta cinye ni ɗanya da mitar Kakanta yayi cefane da wuri ni kuma naƙi gama musu abinci".

ta faɗa tana tashi ta shiga madafa. dariya ta ban sosai da ta ce uwarta, Walida ce ƴar gidan Yaya Imam, ƴar nan ba dai tsufanta ba kamar aljana, tun da aka kawota Yaye shikenan ta zama ƴar gidan, tsakaninta da gidansu ziyara, har faɗa ma take ita fa Ummani ce Babarta ba Momi ba, ita da Daddynta Babansu ɗaya, duka Abba ne ya haife su. Gidanmu ba wani babba ba ne sosai, tsaka tsakiya ya ke, sai dai bai saka yawan mutanen da suke rayuwa cikinsa ba sun takura, dan zaka samu kowanne ɓangare akwai ɗakunan yara har biyu bayan na iyayensu, asalinsa ginin ƙasa ne daga baya aka sabunta shi da na bulo a hankali a hankali. gidan gado ne da iyayenmu su ka gada a wajen mahaifiyarsu, don haka ahalin mutum uku ne a gidan da su ka fito ciki ɗaya, tun bayan rasuwarta da aka raba musu gado sai suka yanke shawarar zama wuri ɗaya don babban burin mahaifiyar tasu kenan, mahaifinsu na raye shi kuma tun da ya samu karayar arziƙi har ta kai ga ya sayar da duk kadarorinsa hatta kuwa da gidansa da suke zaune saboda biyan basukan da ke kansa, shi ne ita Hajiya Umman tasa yaranta su ka gyara nan gidan nata da itama gadarsa tayi suka koma da rayuwa cikin rufin asirin ubangiji, dama ita ɗaya ce matarsa har ta mutu, don itama bata rasu ba sai da ta tsufa sosai.

ɓangarenmu ne a farkon shigowa gidan, idan ka shiga daga ciki ta tsakiya kuma ɓangaren Baba Tijjani da nasa iyalan, shi ne mai mata biyu da tarin ƴaƴa goma sha biyar. sai daga gefen hagu na ɓangaren nasa nan Baba Sabi'u ya ke, shima matansa uku amma sun rabu da ɗaya, ƴaƴansa takwas duk mata ne Allah ya ba shi. zaman gidan namu dai kadaran kadahan ne, waɗanda ba su son zaman lafiya Mamu da ƴaƴanta, ita ce fitinanniya a cikin matan iyayen namu, duk wani rikici da zai ɓarke a cikin gidan to zaka samu daga gareta ko ƴaƴanta ya soma, kuma da Allah ya tashi sai ya bata kishiya daidai da ita. Mamu da ƴaƴanta akwai baƙin cikin bala'i, ita babban tashin hankalinta taga cikin ƴaƴan gidan wani yafi nata, haka ta tsani taga facalolinta sun fita da wani abun, ko fita za su yi tare taga shigarsubtafi tata to tabbas ta haƙura, ƙiri ƙiri ta ke nuna hassadarta bata iya ɓoyewa, kuma ko da yaushe ita ɗin dai ita ce koma baya, shiyasa bama wani girmamata a dalilin abin da takewa iyayenmu da kuma raba tsakaninmu da ƴaƴanta da tayi.

mahaifiyata tana da haƙuri da kawaici, kuma tana cikin irin mutanen da ba su fiya son shiga hulɗar kowa ba, barsu da halinsu su kaɗai sai na jikinsu, bata ƙi ka mata abu ba taƙi ɗaga kai ta kalleka, Ummani ta ƙware a bawa iska a jiyar mutum. amma fa idan aka taɓa mata ƴaƴa to anan ake ƙure haƙurinta, anan ake gane bata da kyau ko kaɗan, sam sam bata kawaici ta wannan ɓangaren, bata iya bari ƴaƴanta su halaka saboda haƙurinta, haƙurinta ba yasa ta bari a shiga hakkin ƴaƴanta. dalilin da yasa Mamu ta shafa min lafiya kenan a yaran gidan, ko sharrinta ne ya tashi bata cika haɗawa da ni ba kam, don ta san bakin Ummani ba zai mutu ba akan haka, a cikin ruwan sanyi zata yaɓa mata maganar da zata hanata bacci. Ummansu Hindatu ce lakwaf lakwaf, shiyasa Mamun ke mata yanda ta so ita da ƴaƴanta duk da ba miji guda su ka haɗa ba, sau tari sai kishiyarta ce ke shigar mata idan tayi mata abu, ita Ummani babu ruwanta haka take cewa kowa tashi ta fishshe shi.

tun bayan da Yashaik yay aure aka bige ɗakinsa aka ƙara girman kitchen ɗinmu da tsakargida, sai duk tsakar gidanmu yafi na sauran girma, ga shi Yaya Imam da Yashaik suka haɗa kuɗi aka zuba mana fasashshen tayels, shikenan tun daga wannan gyaran fa Mamu ta ɗaura gaba da Ummani da ƴaƴanta, tsakaninta da mu harara da gyatsine, amma a hakan duk san da na zo Ummani sai ta tura ni ta ce inje in gaisheta duk da ta san ba zan samu tarbar arziƙi ba.

Ɓangaren Baba Tijjani na fara shiga, shi ne wanda Abbaana ke binsa. ina ta sallama daga tsakar gida babu wanda ya amsa min ga shi ina jiyo hirarsu a falon na su, sai da na ɗaga labule na leƙa falon tukunna. cikin yaran ba wanda yay min kallon arziƙi kamar yanda mahaifiyar tasu tayi min, don haka a tsaitsaye na gaisheta na fito na wuce ɓangaren Babanmu, shi kuma shi ne yake bin Abbaana Baba Sabi'u kenan, ƴaƴansa ke ce masa Babanmu duk sai muka ɗauka, na same shi yana nan muka gaggaisa har yana tambayar zuwan nawa na lafiya da rana tsaka haka, na ke shaida masa zancen zuwa ƙauye amma duk da haka sai ya kama min faɗa me yasa ban bari sai gobe da safe na taho ba, hakan ai rashin hankali da tunani ne, saura kuma idan an tafi bikin inga wajen zama in mance matar aure na ke.

mu ka fito tare da Hindatu tana min dariya, wacca na haɗe fuska tun ganinta ina aika mata harara saboda fushin da na ke yi da ita akan rashin zuwa gidana, zan iya cewa sau ɗaya taje sabon gidan nan namu, tsohon kuwa tsab zan ƙirga zuwanta shima. ko da yake mu haka iyayenmu suke, sai ka ce zaka je gidan ɗan uwanka a tsareka da tambayar me zaka je yi.

dawowata na iske Ummani har ta kammala girki, ta zuban abincin ta aje. sannu da aiki na mata sannan mu ka zauna ni da Hindatu, wacca ke faman tsokanar bai kamata a bani abinci ba ta san sai da na gama cin me maiƙo na taho. ban tanka mata na shiga cin abincina, loma biyar nayi naji abincin ya fita a kaina gaba ɗaya, ajiyar zuciya nayi yayin da zuciyata ke min ƙuna tunawa da abinda Nazifi yay min, nayi saurin mayar da ƙwallar da ta cika idona ina saurin miƙewa na je ga fanfo zan face majina.

Ummani ta bini da ido kafin ta ce,"kin ƙoshi ko me?".

"Ummani wannan murar ban san ya zan mata ba wllahi, ina son cin abinci amma sai in kasa ci".

"to Allah ya ba ki lafiya, ai da sauƙi ma tun da kina iya ci ko babu yawa".

sai sannan na ke tambayarta Kaka saboda na leƙa ɗakinsa ban gansa ba. ta shaida min Yaya Kamal da Yaya Al'ameen sun je kaishi wurin magani in da ake masa gashin ƙafa. jakunkunan kayana na kwashe na shiga da su cikin ɗan ƙaramin ɗakina, na bar guda ɗaya wadda na ajeta nan kan tabarmar da muke zaune ina cewa,"ga kaya nan Ummani za'a kai ƙauye".

Ummani ta jawo jakar tana duba kayan tace,"kai kai ai ko kin gwangwaje su, wannan kaya masu kyau haka, ai fa bari na ɗebewa amarya ma su kyan".

ta faɗa tana ɗaga wata abaya, ai ko Hindatu tayi saurin cafewa da magiya. "Ummani don Allah ki bar min wannan don Allah Ummani".

Ummani ta saki baki tana kallonta. "ke Hindatu me za ki da wannan rigar? duk uban kayan da kike da su saboda dai rashin godiyar me sama".

ta langaɓar da kai tana ci gaba da roƙon Ummani har sai da ta haƙura ta bar mata, kuma Ummani na tashi zuwa ta kai kayan abinci ɗakin Abbaa tayi sauri ta wawuri wasu kayan ta arce tana ce min ai batta ƙara fitowa sai gobe kuma. zaman da nayi ni ɗaya sabon zafin baƙin cikin gidan aurena ya shiga huda ƙirjina, sai dai haka nayi ta kokawa da kaina don ganin na dakatar da fallasa yanayin halin da na ke ciki akan fuskata, yanda na zo gida sam bana son abin da zai sa in ke tunawa da gidan Nazifi, a yau sunansa ma ciwo ya ke min mai raɗaɗi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull