Kenza eBookz

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 20

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 20

Kida a ruwa book 2 complete Chapter 20: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 20. "Ke kuwa daga ina kike haka?". Ruky ta faɗa tana kallon Nimrah cike da…

4,494 words

"Ke kuwa daga ina kike haka?". Ruky ta faɗa tana kallon Nimrah cike da tuhuma. "Ina baya ne zaune kawai". Itama Nimrah ɗin ta bata amsa batare data kalleta ba. Gaba ɗaya sai Ruky taji wani abu mai nauyi ya tsaya mata a maƙoshi. Sai kawai ta ɗauke kanta bata sake mata magana ba. Sai ma kular abincinsu data tura mata. "Kinci ne?". "Uhmm". Ruky ta bata amsa a daƙile tana tashi tabar wajen. Sai kuma duk Nimrah taji babu daɗi. Riƙo hannun Ruky ɗin tai kawai da sauri ta rungumeta. Ruky zata kwace Nimrah tai saurin faɗin, "I am sorry my luv." "Wace luv ɗin. Kima daina yaudarar kanki Nimrah. Amma zan baki shawara ɗaya, koma mi kike ɓoyewa a kwanakin nan ki tabbatar ba abinda zai ƙona ki ko ruguza rayuwarki bane. Komi zakiyi ki dinga tunawa da UBANGIJI mai jinki mai ganinki. Bana zarginki da aikata komai mara ƙyau kona rashin ɗa'a, amma zuciyata na rawa da hangen-hangen abubuwa masu yawa." "Nagode da kikai min kyakkyawan zato, kuma ki cigaba da min, dan in sha ALLAHU har abada bazan taɓa aikata wani abu na saɓama UBANGIJI ba. Abinda kuma kike tunanin ina ɓoyewar ma nan gaba kaɗan zaki sani ba mummuna bane. Amma Please ki bar fushi dani. Fushi da juna na nufin sheɗan yaci galaba a kanmu, mun kuma yima kammu alƙawarin babu shaiɗan a tsakkiyarmu har abada duk tsanani". Sai da Ruky ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan ta ce, "Haka ne ki yafe min" daga haka ta rungume Nimrah, itama rungumeta tai suka shirya.......

>>>>>>>>✷⁠‿⁠✷<<<<<<<<< ★BAYAN WATA BIYU★

7:00am

"Mammah!!" "Mammah!!!". Muryar Bilal ya karaɗe gidan cikin sauti mai tada hankali yana sakkowa daga upstairs da steps bibbiyu. Ba Mammah kaɗai ba hatta su Ruky da gudu suka fito daga ɗakinsu, dan Nimrah ma daga bayi ta fito wanka, ALLAH ma ya sota bathrobe ce ba towel ba. Biebah ma wandon kayan barci ne kawai a jikinta sai best, sai dai ta yayimo hijjabin salla a hannu batare data saka ba. ALLAH sarki Mammah ita kam tana cikin ruturarta, dan har tayi wanka kasancewar ta mai wankan wuri. Dan tana idar da sallar asuba tai azkar wanka take fara yi kafin ta fito. A yanzu ma kammala shirinta kenan tana son fitowa tama su Nimrah magana su shirya su rakata gaishe da Baffa wannan kiran na Bilal yay mata amsa kuwwa. Jikinta har rawa yake wajen ƙoƙarin fitowa a ɗakin saboda tsabar jin tashin hankali. A ƙofa sukai karo da Bilal ɗin da waya a hannu. Rungumeta kawai ya fashe da kuka yana faɗin, "Mammah Dada! Dada Mammah shugaban ƙasa...." ya kasa ƙarasawa saboda kukan daya sarƙesa. Dai-dai nan kuma Ja'afar da Ma'aruff ma suka shigo suma a kiɗime. Sai ga Ammar da Mu'azz suma daga sama. Kuma kowa da waya a hannu Mammah kawai suke ƙwalama kira. Rikicewa Biebah da su Nimrah sukai, sai kawai Biebah ta koma ɗaki da ɗan gudu ta ɗakko wayarta. Yayinda Nimrah da Ruƙayya suka nufi Mu'azz suna tambayar abinda ke faruwa. Dan su Uncle Ma'aruff gaba ɗayansu sun rungume Mammah ne suma suna kuka. Hawaye Mu'azz ya share yana miƙa musu wayarsa, a tare suka amsa, rubutu kawai suka gani a X, kafin ma su sake tambaya cikin kuka Mu'azz ya ce, "Ku karanta".

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida (RTD) ya fitar da sanarwa a shafinsa na X kamar haka.

★★Bayan cikakken nazari da sake duba shari'ar da ta shafi Haysam Abdul-Rasheed Shehu, wanda aka fi sani da Zak-Shadow, Gwamnatin Tarayya ta fahimci cewa an samu kura-kuran shari'a da suka shafi yadda aka gudanar da bincike da hukunci a wancan lokaci. Bisa ga ikon da Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar ƙasa ya bai wa Shugaban Ƙasa, tare da shawarwarin hukumomin shari'a da na tsaro, Shugaban Ƙasa ya amince da ba da cikakkiyar afuwa ga Haysam Abdul-Rasheed Shehu. Wannan mataki ba wai hujja ba ce ta cewa an warware dukkan tambayoyi da ke tattare da shari'ar, sai dai wani yunƙuri ne na tabbatar da adalci, kwanciyar hankali, da kuma mutunta haƙƙin ɗan Adam★★. A ƙarshe Gwamnatin Tarayya na kira ga al'ummar ƙasa da su zauna lafiya, su guji yaɗa jita-jita ko ɗaukar doka a hannu, yayin da hukumomi ke ci gaba da aikin su bisa doka da ƙa'ida. Wannan ƙasa ce mai doka da zaman lafiya, kuma babu wanda yafi ƙarfin doka. Kallon juna Ruƙayya da suma nasu jikin ke rawa a yanzu sukai. Tuni hawaye sun wanke fuskar Ruƙayya, ta rungume Nimrah da gaba ɗaya ita kukan yaƙi zuwa mata. Dan kuwa a wannan gaɓar hankalinta ya rabu gida biyu ne. Ba komai yasa hakan ba sai zancen mutumin can da tun randa suka haɗu bata sake bi takan al'amarinsa ba balle binciken da yace tayi, kenan da gaske yake Dada na prison ne ba ƙasar waje ba kamar yanda suka ji ƴan gidan na faɗa?. Tabbas a yau ta zama cikin ruɗani na kasa banbance waye mai gaskiya tsakanin shi da ƴan gidan to. Shin kukan murna zatai itama kamar kowa? Kona baƙin cikin sakin wanda bata da tabbacin shine ya kashe ahalinta ɗin ko ba shi bane?. Bata da mai bata amsa, hasalima hawayen sun gama wanke mata fuska batare data farga ba. Dan a duniya kukan Mammah yana jerin farko na karya lagonta. Matuƙar so takema tsohuwar nan a cikin jininta da ɓargon jiki. Bata jin kuma koda ta tabbata mutumin nan shine ya kashe mata iyaye hakan zai shafi soyayyar da take ma Mammah duk da mahaifiyarsa ce. Ta saka a ranta shi da laifinsa daban, alaƙarta da Mammah daban. Yanda laifinsa bazai hana alaƙarsu ba, soyayyar Mammah bazata hanata hukuntashi ba in har ta tabbata shi ɗin ne ya kashe mata zuri'a. Tuni ita da Ruƙayya da Biebah ma sunje sun rungume Mammah dake kuka sosai saboda karanto mata abinda suka karanta da Mu'azz yayi. Bayan tayi sujidar shukur ta ɗago harda Uncle's nasu suma. Hakama su Shariffa da suka shigo, sun haɗu sun zagayeta kowa na kukan farin ciki mara misalin ƙididdiga.........✍️

49

.........Ba gidan Mammah kawai ba a wannan safiya ƙasar ce gaba ɗaya data wayi gari da wannan batu ke neman rikicewa. Ya rabbi, kwatanta muku irin yanda ƙasar ta ɗauki al'amari bazatar nan da shugaban ƙasa yay ma kowa ɓata lokaci ne. Domin kuwa ƙura uku ce ta tashi a lokaci guda. Masoya masu farin ciki da godema UBANGIJI. Manyan azzalumai da hankalinsu ya tashi dan Janar ya mamaye su. Yara matasa irin su Nimrah da basu san miya faru ba. Dan haka suka fara neman bayanai akan dalilin rufe wannan gwarzon haziƙin soja da aka tashi a wannan safiya da zancensa tako wace manhajar social media. Dan gaba ɗaya media tamkar zata fashe ne da wannan batu da hotunan Zak-Shadow da aka rasa ma daga ina mutane ke samo su. Kafofin sada zumunta, gidajen rediyo, gidajen tv. Jama'ar gari, zaka rantse fitowar tasa ce kawai abu mafi muhimmanci a wannan satin a ƙasar... Babbar tsiyar da shugaban ƙasa ya tafka musu kuma ana fitar da sanarwar aka kuma sanar da barinsa ƙasar wani babban taro zuwa ƙasar waje da zai halarta na kwana uku. Wayyo ya rabbi, ai sai wutar ta ƙara sama. Saman data nema girgiza ƙasar gaba ɗaya. Musamman da aka samu bayanan shi kansa Zak-Shadow akwai ƙishin-ƙishin ɗin baya cikin prison. Gashi gidan gwamnati sunƙi sake cewa komai daga waccan sanarwar har zuwa yanzu da dare ya ratsa. Abu na ƙarshe zuba wani masifaffen tsaro daya bama kowa mamaki a anguwar su Mammah musamman ƙofar gidansu. Dan ko awa ɗaya ba'ai da sanarwar ba aka kawo sojoji anguwar suka zagaye gidansu. Hatta masu alaƙa da su irin su Uncle Nasiru da zasu shiga gidan sai da aka bincike su tsaf. Ko su Aunty Mommy da suka iso suma sai da akai musu hakan. Hakan ya sake tabbatar ma kowa abin da babbane, musamman ƴan media da tuni suka yoma anguwar tsinke na rediyo dana television harma dana social media dan son bin ƙwaƙwaf. Sai dai yanda suka samu gidan dole suka haƙura, sai kuma suka fara juya maganar akan Zak-Shadow baida isashiyar lafiya ne shiyyasa aka kaishi gida aka zuba tsaro kuma dan kar a ga halin da yake ciki. Wannan batu ya sake tada sabuwar magana. Ƴan ƙasa da ƴan siyasa da masu fashin baƙi suka fara kai-kawo da ka-ce-na-ce. Wasu suna sukar shugaban ƙasa, wasu suna yaba ma abinda yayi. Yan bani na iya na haɗa hotunan karya da videos a social media a zuwan Zak-Shadow ne aka fitar a prison magashiyan cikin raunuka da galabaita. Kai wani fa idan ya tsara maka batun ga abinda ya faru sai ka rantse a gabanshi akai komai ma......

÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷ ★JAMUS★

Yanayi ne mai armashi da ni'ima dake kaɗawa a irin wannan lokacin na yammaci a ko'ina ma kake a duniya. Koda lokaci ya banbanta ƙasashe irin wannan yanin a kowacce ƙasa yana da tasiri sosai saboda yakan zama abin so ga kowa, musamman mutane masu nutsuwa da rashin son hayaniya. Zaune a balcony ɗin ɗakin hotel ɗin nutsatstsen matashin dattijo ne cikin yanayi na ƙasaita da nutsuwa. Yanda ƙafafunsa ke harɗe a zama irin na izza zai tabbatar maka da kasancewarsa cikakken mutum. Sanye yake cikin ƙananan kaya da sukai masa ƙyau sosai kalar ruwan madara marasa nauyi. Hakan ya bayyana cikakken jikinsa dake a buɗe musamman daga sama, sam ba siriri bane, ba kuma yi da ƙiba mai yawa dan har yanzu ainahin jikinsa bai gama dawowa ba. Sai dai ko a haka ƙarfinsa a bayyane yake na ma'abota lafiya da cikar kamala. Gaba ɗaya hankalinsa yana akan littafin hannunsa ne da yake nazari, da ganin littafin kasan mai matuƙar amfani ne. Sosai hasken fatarsa ya sake washewa, ƙasumbar daya tara tun a prison na nan bai kwashe ta duka ba daga fuskarsa, sai dai yanda take kwance luff da style ɗin gyara na musamman zai baka tabbacin yana samun kulawa, dan harda wasu ƴan tsilli-tsillin gashi da sukai fari alamar furfura ta baiwar matsawar shekaru na cikar kamalar girma. Yanda siririn farin gilashin daya sanya ya zauna masa a kan nutsatstsiyar fuskar tasa ko kaine hasidin iza hasada dole ka furta masha ALLAH. Balle ga wani ƙamshinsa mai natsuwa daya cika wajen. Gefensa kaɗan ƙaramin coffee table ne da mug daketa turiri alamar coffee ɗin ne a cikinsa. A hankali yakai hannunsa da ƙumbar ke fes-fes batare da ya ɗauke idonsa daga kan book ɗin ba ya ɗauki kofin. Kan lips ɗinsa dake dai-dai da taswirar fuskarsa ya kaishi yana mai kurɓar coffee ɗin da alamu suka nuna dole zai yi zafi. Dai-dai nan aka buɗe ƙofar glass ɗin wajen data kasance mai bango guda. Duk da yaji an buɗe ɗin bai kalli wajen ba, bai kuma dakatar da kansa daga abinda yake ba har mai buɗe ƙofar ya bayyana. Ba kowa bane face Daddy Imran, shima dai sanye yake cikin ƙananun kayan tamkar Dadan. Hannunsa riƙe da tab... Da shima hankalinsa ke a kanta gaba ɗaya. A haka ya gyara kujerar gefen sa ya zauna yana faɗin, "Hummm wai kasan mike faruwa kuwa yau a gida Zak...?". A karo na farko Dada ya ɗan ɗaga ido ya kallesa, sai kuma ya maida kan book ɗinsa yana buɗe shafi na gaba. Sai a lokacin ne cikin golden voice ɗinsa dake fita a nutse ya furta, "Miyasa baka son hutar da kanka". Murmurshi Daddy Imran yayi da faɗin, "Ai ba abinda kake tunani bane. Takardar yi maka afuwa ce ta fita daga fadar shubagaban ƙasa a yau. Daga bakin mai magana da yawunsa a shafinsa na X." A yanzu kam sosai Dada ke kallonsa. Hakan yasa Imran miƙa masa tab... Ɗin. "Duba ka gani, dan ƙura ta tashi fa. Yanzun nan Faro ma yay kirana ya ƙara min bayani". Tab... Ɗin Dada ya amsa bayan ya kife book ɗinsa a saman cinyarsa, ya kai hannu ya ɗan gyara gilashin idonsa. Shi ke karatun amma Daddy Imran ke faman murmurshi, zuciyarsa na ƙara cika da jin ƙaunar Janar Yusuf Shu'aibu Tafida. A hankali Dada ya furzar da iska daga bakinsa yana ajiye tab... Ɗin a coffee table ɗin tsakkiyarsu. Sai kuma ya jingina bayansa da kujerar ta lumshe idanunsa yana sake furzar da iskar. Fin sakanni talatin yana a hakan Imran dai bai ce masa komai ba dan yasan akwai abinda yake nazari. Har sai da ya ɗago dan kansa yana mai sauke birkitattun idanunsa a kansa.... "Akwai matsala ne?". Imran ya katse shirun nasa da kallon da yake masa. Anan ma sai da yaja kamar minti ɗaya kafin ya girgiza kansa, sai kuma ya motsa lips kaɗan ya furta, "Imran, da nasan Janar zai yi hakan da na bashi shawarar kar yayi". "Mi yasa?". "Fitar da wannan afuwar tamkar zaburar da su ne a kansa." "Ni kuma sai nafi tsoron bats tashi zasuyi ba ta kai zasuyi. Dan Faro ya sanar min yanzu haka gidan soji ya ɗauki zafi da ƙananun magana. Suma ƴan siyasa nayin nasu". "Wannan dole zata faru ai, baka fahimceni bane. Shima Janar ya manta yanzu shi ɗan siyasa ne ba soja mai iya bada umarnin da za'abi ba koda ba'a so kuma dole ai shiru. Amma a siyasa koda a zahiri akwai shiru to a baɗini za'a samu matsin lamba ta cikin gida". Kai Imran ya shiga jinjinawa, dan ya fahimci abinda Dadan ke hangowa. Cikin sauke ajiyar zuciya ya ce, "Na fahimceka yanzu kam. To yanzu minene mafita? Dan shima ana sanar da afuwar yana barin ƙasar fa". Karo na farko Dada ya saki ƙaramin murmushi, sai kuma ya taɓe baki kaɗan yana shan coffee ɗinsa da kallon Imran. "Imran dole zamu koma gida a satin nan...." "Amma Janar yana so ka huta da ƙyau, idan son samu ne ma kamar wata biyar". "Bamu da wannan isasshen lokacin. Idan kuma mukai wannan sakacin za'a mamayemu a gaɓar daya kamata ace mune mukai mamaya. Ka kirashi yanzu...." daga haka ya miƙe. Imran ya bisa da kallo har ya ɓace masa. Kafin ya sauke ajiyar zuciya da furzar da iska mai nauyi yana zaro wayarsa a aljihu. Sai da ya fara nazartar time ɗin ƙasar da shugaban ƙasa yake a yanzu kafin ya rubuta text message ya tura masa. Daga haka ya miƙe shima yana ɗaukar tab... Ɗinsa da kofin coffee ɗin da Dada bai sha ko rabi ba ya koma ciki dan lokacin sallar magrib yayi.....

<<<<<<•>>>>>>>

Duk wani masoyi na gaskiya yau Mammah ta amsa wayarsa. Har sai da takai ta ma fara gajiya da amsa wayoyin su Aunty Ummi suka koma tayata. Wasu ma ko gane su basayi. Kai da ka ga mutanen gidan a yau kasan farin cikinsu ya canja matuƙa, canji kuma mai girman gaske. Dan bakin kowa yaƙi rufuwa. Mammah kam ta yini ne da tasbihi a baki na nuna godiya ga UBANGIJI, duk da hakan sabone a rayuwarta mace ce mai yawan ibada. Tuni Ja'afar da Ma'aruff sun fita gidajen abinci sunata saya suce a rabawa mutane. Sun kuma turama Uncle Jamilu kuɗi masu yawa sukace acan ma ayi dan mabuƙata sunfi tacan. Duk inda sukaje a fitarsu tare da sojoji ne, dan yau kowaye a cikinsu ya fita a gidan nan sai ya kasance da rakkiyar sojoji. Hatta su Nimrah da zasu tahfiz duk da ma sai da Uncle Nasiru ya korasu dan da sunce bazasu je ba suma dai sojoji suka musu rakiya, hasalima cikin sojojin ɗaya yay driving. Tsabar kuma yanda zaka fahimci shirin fa bana wasan yara bane har a ƙofar ajinsu sai da soja biyu suka tsaya, hakama ajin su Abees da su Afry. A wannan gaɓar Nimrah fa tana a cikin ruɗani ne. Amma tayi jarumtar shanyewa da danne komai a ƙasan zuciyarta ta barma isowar mutumin da duk ake wannan kai-kawo a kansa zuwa gida. Dan har yanzu dai basu ji komai akan batun zai zo gidan ba. Ba Nimrah ce kawai a ruɗani ba a wannan lokacin harda su Malam Buba driver, da Nabeeha dake can gidansu cikin matsanancin farin ciki, dan al'amarin yazo musu a matuƙar bazata kamar yanda yazo ma shugabanninsu. Gashi sai samun kira Malam Buba yake daga su Dagger, suna son jin ko Dada ya iso gida ne.........✍️

50

........A lokacin da zuriar alkairi ke farin ciki anan a ƙungiyar duhu dama wasu munafukan bayan fage cikin soji irinsu Garba a hargitse suke da tashin hankali. Dan shugaban ƙasa kam ya musu mamaya irin wadda ko'a mafarki basu taɓa kawoma zuciyarsu za'ayi ba. Tuni oga Jush yay kiranyen meeting na gaggawa, duk da shi bama ya ƙasar ya koma inda ya fito tunda dama lokaci-lokaci yake shigowa. Amma sai ya kira ta video call da akai connecting da ƙaton tvn meeting room ɗin nasu. Yau kam a zafafe yake, dan kai tsaye ya ƙalubalanci Mr Scythe dake matsayin ogan Janar, dan shine ya kawo sunansa matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa. Ya kuma nuna musu jawo Janar ɗin a jiki zai taimaka musu wajen sanin sirrin gidan soja fiye da sanin da suke da shi a yanzu. Sannan zasu sake karya zuciyar Zak-Shadow dan Janar ogansa ne. Su kuma ganin yanda Janar ke faman kwantar da kai da biyayya ga Scythe dama duk wani ɗan siyasa sai suka yarda da shi, batare da barinsa yasha wata wahala ba suka shiga suka fita ya samu kujerar ɗan majalisar tarayya, tenure ɗaya ya sake nuna musu sha'awar zama shugaban ƙasa, nan ma suka sake dagewa ya samu da babban shirin zasuyi amfani da shi wajen dawo da abubuwan da suka daina yi a baya dan ace da gaske da hannun Zak-Shadow a ciki tunda Janar ogansa ne. Sai kuma gashi tun kan aje ko ina reshe zai juye da mujiya. A satin da shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida ke ƙoƙarin cika kwanaki ɗari da samun mulki ya fitar da babban barazanarsu daga kurkuku. Lallai Janar bai nema zaman lafiya ba. Yau gaba ɗaya meeting ɗin bana daɗin rai bane ba. Dan haka baiyi wani armashi sosai ba suka watse akan kowa zaije yayi tunanin mafita daga nan zuwa sati ɗaya. Dan dole su bincika inda Zak-Shadow yake dan sun sami tabbacin asibiti aka wuce da shi ba gida ba. Dole ne su bincika asibitin kawai su kashe shi tun daga can sai dai gawarsa ta bayyana ma duniya. Shugaban ƙasa kuwa sai sun shayar da shi mamaki na gaske da sai ya gwammace shima kashe shi sukai. Kai hatta da ahalin Zak-Shadow a wannan karon bazasu tsira ba. Dole ne su shirya wasa na gaske mai sunan wasa a wannan gaɓar......

>>>>>>>>>>%<<<<<<<<< ★3-DAY LATER★

Kwanaki uku kenan al'amarin fitar afuwar shugaban ƙasa ga Dada na cigaba da trending a cikin ƙasar. Mutane ko gajiya ma basayi, sai ma wasu ƙungiyoyin matasa dake zanga-zangar lumana akan sufa ko sau ɗaya ne suna buƙatar ganin Zak-Shadow dan su samu kwanciyar hankalin yarda yana cikin ƙoshin lafiya kuma afuwar da akai masan ta gaske ce ba yaudarar ƴan siyasa ba. Dan ɓoyesa na saka musu jin kamar baya cikin ƙoshin lafiya ne ko wani abu ake son shiryawa da batun. A yanzu ma gwamnati batace uffan ba, sai ma batun dawowar shugaban ƙasa akeyi a yau ɗin daga taron kwanaki biyar da yaje. Dan washe gari yake cika kwanaki ɗari da samun mulki. Ga batun naɗe-naɗen mukamai da har yanzu yaƙi yi sai tsiraru da aka bamawa. Dan haka ita kanta jam'iyyar a wuya take da shugaban ƙasa, suna ganin raina musu hankali yake shirin yi da nuna mulkin mallaka irin na gidan soja daya saba a baya...

✨✨✨✨✨✨✨ .★JAMUS★.

A wannan lokacin daga ƙasar Jamus ma su Daddy Imran sun kammala shiri tsaff na isowa ƙasarsu ta haihuwa. Sai dai su akwai saɓani sai gobe idan ALLAH ya kaimu ne. Dan haka a karo na biyu Imran yay waya da Mammah. Dan randa aka sanar da takardar afuwar Dada sunyi waya suna taya juna murna, sai dai bai gaya mata yana tare da Dada ba ko'a lokacin. Ya dai tabbatar mata da yana nan dawowa gida a satin nan. Dan haka yanzu ma daya kira sunyi gaisuwa yanda suka saba irin ta mahaifiya da ɗa. Daga nan yake sanar mata a gyara ɗakin da babu kowa anan ɓangarenta. Yayi magana da wani kamfanin funichars za'azo a saka. Ɗan jimmm Mammah tayi na alamar tambaya, sai dai fahimtar kamar Imran bai son buɗe zancen yasa bata tambayi mi za'ai da ɗakin ba tace to kawai. Daga ƙarshe take sanar masa ya kira su Ma'aruff yay musu magana dan Uncle Tasi'u na son zuwa da yaransa yau da daddare amma tasan halinsu da shegen taurin kai. Bata son a samu matsala kuma, fatanta suyi haƙuri su barsa da halinsa su yafe masa komai ya wuce a cigaba da zumunci. A cewarta duka ma rayuwar nawa take. Murmurshi Imran yayi yana sake jinjina ƙyawawan hali irin na Mammah. Cikin lallashi yace mata karta damu, in sha ALLAHU zai musu magana. Daga haka sukai sallama. Duk wannan wayar da Daddy Imran keyi Dada na zaune a wajen. Sai dai hankalinsa na'a kan laptop zaka rantse baima san mi Imran ɗin keyi ba. Sai dai sarai yana fahimtar komai, dan ji yayi kamar ya kwaci wayar yayi magana da Mammah ɗin. Amma ya danne baiyi magana ba koda Imran ɗin ya kammala wayar ma. Sai ma wani zancen ya ɗakko masa akan aikin da yake yi a laptop ɗin. Kusa da shi Imran ya dawo ya zauna shima yana maida hankalinsa ga screen ɗin laptop ɗin......

<<<<<<<★>>>>>>>

Washe gari a gidan Mammah bisa umarnin Daddy Imran abubuwa biyu suka faru. Na farko isowar Companyn da zasu shirya ɗakin daya buƙata. Ba kuma wani ɗaki bane daban, ɗakin da Nimrah ta shiga ne tai kallon video kwanaki. Dama tun safe su Ammar suka fidda komai na cikinsa su Kulu suka sharo suka wanke bayin da ba'a taɓa amfani da shi ba. Lokacin da masu zuba kayan suka zo aikinsu kawai suka fara cike da ƙwarewa. Abu na biyu isowar Uncle Tasi'u gidan a karo na biyu, sai dai a wannan gaɓar harda yaransa uku. Biyu maza, ɗaya mace. Kamar kowa sai da sojojin nan suka musu bincike ciki da bai aka kuma tabbatar da sanin masu gidan suka zo kafin a barsu su shigo. A lokacin su Nimrah basa nan, suna makaranta iyayen gidan ne kawai sai su Aunty Ummi da kullum yanzu suna gidan sai dare suke komawa nasu gidajen. Shariffa ce kawai babu a falon dan yau ta tashi bata jin daɗi sosai kasancewar cikinta yafi na Lailah tsufa. Babban ɗansa yana kamanni da shi sosai da Mammah. Sai dai ko Ammar zai iya girmarsa da kusan shekara biyu. Sai mace itama budurwa, daka ganta kaga wayayya, gata fingai-fingai kamar kazar mayu. Itama dai Biebah zata iya girme mata kaɗan, dan bazai fi irin shekara ɗayan nan ba ta bata. Sai Auta namiji, shi kam zasu iya dai-dai da Mu'azz. Kai da ka gansu kasan rainon ƴan gayu ne, sai dai kuma da ganin inda suka zo ɗin yama fi gidansu komai suka kama kansu. Ga Mammah ta musu tarba ta mutuntawa da soyayya kamar zata haɗiyesu. Su Aunty Mimi ne ma dai sama-sama suka amshesu dan ma gargaɗin Yaya Imran ne. A haka su Nimrah suka dawo gidan suka samu baƙi, duk da dama a kwanakin nan kullum gidan bai rabo da baƙin. A gidan nan babu wanda yakai Nimrah da Ruky wulaƙanci idan mutum bai musu ba. Sun gaida Uncle Tasi'u da girmamawa matsayinsa na uba. Amma ƴaƴansa kallo ɗaya sukai musu suka watsar da su kamar sun ga kashi. Sun kuma yi musu haka ne saboda ganin yanda suketa wani jijji da kansu su a dole ga rainon turai. Kota kansu kuwa basu sake bi ba suka shige ɗakinsu, bakuma su sake fitowa ba ko abinci sakawa sukai masu aiki suka kai musu dan yau alhamis ne babu Islamiyya. Sai da Mu'azz ne ma ya dawo gidan yazo ya jajibesu suka haura sama ganin ɗakin da aka zubama kaya. Anan suka lalace sunata santi da hotuna da wayar Mu'azz ɗin. Dan ɗakin yayi ƙyau matuƙa. Haka suka fito suna damun Mammah da tambayar wazai zauna a ɗakin. Tace bata sani ba itama Daddynsu ne kawai yace a gyara....

★RANA BATA ƘARYA......★

Tabbas wannan batu haka yake. Dan kuwa washe garin juma'a kamar jiya yau ma Daddy Imran ya kira Mammah a waya yace su shirya za'azo a ɗaukesu bayan sallar juma'a zuwa wani waje. Kan Mammah ya fara ɗaurewa, amma sai nan ma bata tambaya ba saboda halin girma da dattako irin nata tace kawai to. Su Bilal ne ma data sanar mawa suka fara shan jinin jikinsu. Jiya an gyara ɗaki, yau ance su shirya anya kuwa?.. Kasancewar baƙin ido a gidan yasa basu ja maganar da nisa ba. Bayan sunyi shirin massalaci sun fita harda ƴaƴan Uncle Tasi'u Dayyan da Afeef, suma su Mammah dake gida suka hau shiri. Sai ga su Aunty Ummi sun fara isowa da tasu tawagar suma. Dan yaran basu sami sukunin zuwa gidan ba sai yau saboda makaranta. Shiyyasa yau juma'a kowa da ɗansa yazo. Nan fa aka sake kacamewa har wani baya jin zancen wani. Banda yara za'ai fitar, dan haka su Nimrah a gida akai shirin barinsu da yara amma suka shiga magiya da roƙon Mammah dole tace su shirya. Kasancewar harda Aunty Biebah da su Aunty Lailah su Nimrah sune ƙanana. Su yaran ma murna sukai da tafiyar tasu, dan a sanin da sukai musu basa ɗaukar raini, idan aka barsu da su dole su daku. Dan kaɗan daga aikin Damisa da Zakanya yaro yaci duka kafin uwarsa ta dawo.... Ba ƙaramin ƙyau sukai ba kuwa da kwalliyar tasu. Nimrah skirt da riga ne na atamfa da tai mugun zama mata a jiki, sanin ba barinta ake fita da ƙaramin gyale ba idan ta saka irin waɗan nan kayan yasa ta ɗora after dress a sama, ba ƙaramin ƙyau tayi ba ga fuska tsaff da kwalliya mai nutsuwa. Hakama aminiyar tata tana sanye da irin kayan nata sai dai ita kam gyale ta saka. Suka kawo turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. suka saka, gashi dama sunyi kabasa da shi a kaya.. Suna fitowa Ya Mu'azz ya fara tsokanarsu wai kamar ranar auren su. Ba raga masa suke ba, dan haka suka shiga ramawa ana dariya. Daga haka suka fito harabar gidan kowa ya shiga mota. Ninah da Ruky na tare da Mammah, Uncle Bilal ke tuƙi sai Mu'azz a gefensa. Ana buɗe gate suka fito motocin sojoji biyu dake jiransu suka take musu baya. Ɗaya a gaba ɗaya a baya. Wannan matakan tsaro na ba kowa mamaki a cikinsu, dan ko yanzu su Nimrah sai da sukai magana. Dan har a makaranta ma yanzu tare suke zuwa da sojojin da a yanzu suka zamewa kowa dogari a gidan batare da sun san dalilin yin hakan ba. Abinda kawai sojojin suka sanar musu tun a ranar farko da aka kawosu shine umarni suma kawai suke bi........✍️

[12/19/2025, 1:50 PM] Zeenaran 😘: 51

.........★AIRPORT★

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull