Kenza eBookz

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 23

Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 23

Kida a ruwa book 2 complete Chapter 23: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 23. ..........8:30am suka fito cikin shirin tahfiz, Mammah ce kawai a falon…

4,262 words

..........8:30am suka fito cikin shirin tahfiz, Mammah ce kawai a falon zaune tana shan shayi. Su Kulu sun gyara ko'ina tsaff sai ƙamshi ke tashi kamar me, dan zuwa yanzu ƙamshin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Sun gama kama gidan tako ina. yanda Nimrah da Ruky ke faman tuttura baki gaba yasa Mammah faɗin, "Oh oh mi akama Autaras ɗin Mammah? Kuzo naji". Inda take duk suka nufa, yayinda Biebah ke faɗin, "Yo Mammah miza'ai musu, halin ne ya motsa makarantar ce basa son zuwa". Rungumesu Mammah tayi tana faɗin, "Su dai basu ce ba Biebah, zasuje makarantar su ko?". Tai maganar tana taɓa wuyan Nimrah. "Kinga babu ma zazzaɓin". Sake langaɓe mata sukai suna shagwaɓar su, dai-dai nan Mu'azz da Ammar da suka fara sakkowa daga stairscase, cike da neman tsokana Mu'azz ya kalli su Nimrah da suka tashi daga jikin Mammah zasu je dinning ke faɗin. "Tunda kaga Zakanya da Damisa na kumbura yau akwai ɗaukar magana a makaranta kenan." Ammar dake dariya ya ce, "Kada ka musu sharri". "Hummm ALLAH Uncle baku fahimce su bane, duk randa yaran nan basa son zuwa makaranta ka kula sai sun ɗakko magana. Kuma zaka ce nina faɗa maka. Kai dai kabar wayarka a kusa da kai kawai, dan nasan za'a kiraka, bare ma kwana biyu basu tafka ta'asar ba". Hararasa kawai su Nimrah sukai basu ce komai ba, Mammah dake hararar Mu'azz itama ta ce, "Kar ku kulashi kunji ƴan albarka. Maza kuje ku karya kar ku makara." Gwalo suka masa suna matsawa suka gaida Uncle Ammar dake musu dariya. Dai-dai nan suma su Ayyan suka shigo da gudu cikin nasu shirin. Afrah ta faɗa jikin Nimrah. Sosai bakin Nimrah ya washe da farin ciki, ta ɗauketa suka wuce Dinning dan Biebah da Mu'azz har sun ƙarasa. Yanda suka cika falon da uban surutun su sai ka ɗauka wata gayya ce guda. Mammah da Ammar na daga falo suna tasu hirar. A haka su Yaya Ja'afar suka shigo falon tare da su Shariffa. Cikin girmamawa duk suka gaida Mammah, ta amsa musu da kulawa tana tambayar ya jiki-jiki. Su duka kunya ta hana su amsawa sai murmushi da sukai suna duƙar da kawuna. Sai ga Bilal shima ya sakko, yanda yake ɓata fuska yasa Yaya Ma'aruff tambayarsa lafiya?. Sashen Dining ya harara da faɗin, "Wlhy yaran nan sun hana ni barci Yaya". Shima su Nimrah dake kwasar dariyar abinda Ayyan yake yi ya kalla. Sai kuma ya dawo da kallonsa kan Bilal ɗin yana faɗin, "Ai kai ke ɗaure musu ƙugu dama idan sana wani abun. Sai ka bari su tafi ka koma? Dada fa?". "Inaga yana barci shi ma, tunda muka dawo massalaci ya sake shigewa. Yauwa Mammah yaran nan fa kwana biyun nan basa fita sallar asuba wlhy. Dan yanzu haka Dayyan baiyi ko salla ba". Tsaki Ammar yayi, cikin takaici ya ce, "Shiyyasa na baro masa ɗakin, nafa tada shi yafi sau uku amma yaƙi tashi. Sai kace wanda yasha wani abu. Ni dai Mammah yau kisa a gyara musu ɗakin baƙi su koma gaskiya". Caraf Biebah dake isowa wajen ta ce, "ALLAH nima ƙorafina kenan Yaya. Ita waccan sai latse-latsen wayar banza, ta dameni da charting da dare da dariya." Ja'afar da sai yanzu yay magana cikin takaici ya kalla Mammah shima. "To wai tunda sun gaishe mu su koma gida mana? Idan shi Babban ya gama makaranta su kananun fa?". Rasa ma abin cewa Mammah tayi, dan gani take taron dangi suke neman yi mata ita kam. Cikin sa'a takun sakkowar Dada ta saka wani bai sake magana ba, sai ma maida hankali sukayi ga stairscase ɗin. Su ko su Nimrah da hankalinsu ba nan ma yake ba sun cigaba da surutun su ne. Dan kusan yana step ɗin ƙarshe Ruky ta taso da gudu da abu a hannu, Nimrah na binta alamar koma miye nata ne Rukyn ta ɗauka. Tsabar kuma basu da man kai ta wajen stairscase ɗin suka yi. Ai ko kaɗan ya rage Ruky taci karo da shi, yay gyaran muryar data ratsa kunnuwansu. Ai ko cak ta tsaya tana zaro idanu, haka ma Nimrah dake bayanta sai da taji zuciyarta ta buga. Lokaci ɗaya falon yin tsitt, dan har su Abees sai da suka nutsu..... Sosai ya zuba musu idanunsa da suka saka su duƙar da kawuna ƙasa. Cikin ƙarfin hali Ruky ta ce, "Dada mun tuba, ALLAH bamu san ka taho ba ne". Maimakon tankawa kallonsu kawai yake. Duk sai suka sake firgicewa, Nimrah ta sake ɓoyewa a bayan Ruky kamar wata munafuka. Sai da yaja fin minti ɗaya idanunsa na ladabtar da su kafin ya furta, "Dama ya dace mata suna guje-guje?". Kawuna suka shiga girgizawa da sauri. Yanda suke yi ɗin ya bama kowa dariya, sai dai babu mai zarrar yinta a fili inba Mammah ba. Ita kuma murmushi kawai tayi ta ɗauke kanta. Ƙasa-ƙasa Ammar ya furta, "Aiki gamai ƙareka. A kallo kawai Ninah da Ruky sun nutsu dole nayi sadaka idan na fita". Mintsininsa Bilal yayi, ya rufe baki yana buge masa hannu. Ya Ma'aruff kam gefe ya kauda ido yana murmurshi bayan sun kalla juna da Twinyn sa Ja'afar. Shima bai sake ce musu komai ba ya ƙaraso falon, hakan ya saka su Lailah sake nutsuwa kawunansu a ƙasa na girmamawa. Zaune ya kai a kujerar kusa data Mammah, sai kuma ya kalla su Aheel da sukai tsuru-tsuru, to iyayen daba sun nutsu bare su. Hannu ya miƙa musu, babu musu kuwa suka nufe shi su duka ukun. A mamakin kowa kansu ya shiga shafawa fuskarsa na sassautawa duk da ba murmurshi yake ba. Suma yaran sai suka fara gaida shi, duk da ganin jiya kawai sukai masa da alama kamaninsa da iyayensu da yake ya tasirantu a zukatansu. Ya gaisa da su Ma'aruff duka bayan sun dawo sallar asuba. Amma hakan bai hana su sake gaishes hi ba a yanzu. Suma su Shariffa suka gaishe shi da Biebah. Sai lokacin su Nimrah suka ƙaraso suma suka gaida shi. Biebah yay ma umarnin kawo masa coffee, ta amsa tana nufar kitchen. Bata wani jima ba ta dawo, table taja gabansa tana ajiye masa ƙaramin tray ɗin data ɗora cup ɗin, dai-dai su Nimrah sun kammala tattare kwanikan dining suma. Sun dawo falon da nufin ficewa Mammah ta dawo da batun da su sun ma manta sun fara, dan tasan halinsu zasu iya zagayewa su gayama Dadan nasu. "Ina roƙonku ku bisu a hankali, kuyi haƙuri kuma da su, kofa ba komai ƴan uwanku ne, da wannan ƙorafin ai inaga kuyi jihadin gyara musu ɗabi'un nasu na banza cikin hikima zai fi ko". Kamar Biebah zatai kuka ta ce, "Wlhy Mammah ko mazan zasu canja banda macen. Bata da mutunci fa, da nai mata magana jiya da daddare zatai live da kayan barci catai min wai bata son takura naji da matsalolin gaba na. Shiyyasa na bar mata ɗakin na koma ɗakin su Ninah na kwana". Caraf Nimrah ta ce, "Lah Small Mom dama kece? Nifa na zata ita finga fiyau ɗin ce ta shigo mana. ALLAH kaɗan ya rage ban faɗo da ke ba a gadon, kuma da har na ayyana haka a raina naga ban gama fita daga kamun UBANGIJI ba ina zazzaɓi sai na wuce ɗakin Mammah abina acan na kwana nima." Dariya su Bilal sukayi saboda (Finga fiyau data kira Hanoon). Yayinda Dada ya kusa ƙone lips da coffee jin taɓargazar da tsuntsuwar yarinyar nan ke neman yi masa, tunda in kowa bai san a ɗakin Mammah ya kwana ba ai ita Mammah ta sani. Sarai Mammah taji mi Nimrah ta faɗa, amma ta basar dan koda ta ɗan kalli Dada ta gefen ido ta lura sai da ya ɗago nasa idanun ya kalla Nimrah ɗin, kafin itama ya saci kallonta. Ke Biebah da baki san miya faru ba ta amshe zancen Nimrah da faɗin, "Haba naso inyi magana da kika shigo da asuba kina ƙanshin turaren daban sani ba, sai kuma na tuna sanda muka tashi baƙya nan. Kice kaɗan ya rage nasha ƙasa. Ina arziƙi an jeho uwa, dole na fara kwana da fitila indai na shiga ɗakin ku kuwa". Ammar da Mu'azz da su Lailah na dariya ƙasa-ƙasa, Dada na ayyana dole ya sallama turaren daya saka a daren jiya kuwa a gidan nan. To Biebah taji ƙamshi ai bashi ba sake saka wannan turare balle ta fahimci daga shi yake. Ja'afar ne ya katse zancen da faɗin, "Mammah a bar zancen sai an jima. Ku kuma kuwuce kada ku makara". Mammah ma ta fahimci dole zancen ya tsaya iya nan kada a kama wani layin, sai dai a ranta tana jinjina hukun UBANGIJI, dan ikonsa ne ya haɗa waccan haɗuwar ta daren jiya a ɗakinta..........✍️

Gaskiya ya kamata a ƙara gasama Nimrah baki karta ɓaro aiki wataran da shegen surutun nan nata😂🤣

[12/22/2025, 5:46 PM] Zeenaran 😘: 57

........."Aunty! Aunty Nabeeha! Aunty please ki tashi". Da ƙyar Nabeeha ta iya buɗe idanunta da sukai mata nauyi saboda barci. Dan ko sallar asuba da ƙyar ta tashi tayi ta wajen ƙarfe shida ta sake komawa gado. Yanzu kuma ga Ismat tazo tana tashinta. Akan Ismat ɗin ta sauke su, sai kuma ta sake lumshewa da buɗewar dai. "K kuma daga ina da safiyar nan?". "Daga gida mana. Ina su Momy naji gidan shiru". Cikin yamutse fuska Nabeeha tai hamma tana tashi zaune da ƙyar, sai da taja wayarta ta duba agogo. Ganin goma harta wuce ta maida ta ajiye tana bama Ismat amsa. "Momy tayi tafiya, suna Chaina ita da Aunty Amo." "Uhmm ita Momy ai bata gajiya da yawo a jirgi kamar ƴar sama jannati. Taita biye ma matar nan, sun sauka a mulkin ma bazata ƙyaleta ta huta ba. Su Amima fa?". Baki Nabeeha ta taɓe alamar amsa zancen farko kenan, kafin ta amsa na ƙarshe da faɗin, "A club suka kwana. Ina ƙyautata zaton kuma yau Momy zata dawo ma. Ke dai da gaske kin bar gidan nan ko? Ko takaicin zama da wannan shegiyar matar ta Daddy baƙya yi". "Hummm wlhy Aunty Ummu nada kirki, kawai dai bamu fahimceta bane. Yanzu fa ki duba, badan tayi tsayin daka ba Daddy bazai barni na zauna a gidan nan ba, amma wlhy har faɗa saida sukayi a kaina saboda ƙin sauraren Aunty Jiddah da yayi a farko. Ni bama wannan ba, labari na kawo miki mai daɗi, sai dai ban tabbatar da ingancinsa ba." Koƙarin sauka Nabeeha tayi a gadon cikin halin ko'in kula tana faɗin, "Labarin mi? Uwar kwashe-kwashe". "Hummm Aunty Nabeeha wannan kwasha-kwashan fa indai ya tabbata gaskiya wlhy har ƙyauta zaki bani. Wani ƙishin-ƙishin fa naji a wajen Imam kamar Dada ya dawo gida". Cak Nabeeha dake ƙoƙarin shiga bayi ta tsaya, sai kuma ta juyo da sauri tana kallon Ismat dake murmushi. Gira ta ɗaga mata da faɗin, "Bani fa da tabbas, shiyyasa nazo sanar miki ma dan ki bincika. Nayi tunanin su Imam zasuje gidan ne ma sai naga sun wuce tahfiz, Ummu kuma banga tana wani shirin fita ba balle nace zan bita na sami tabbaci. Dan abinda ma ya faru waccan ranar yasa wlhy tsoron zuwa nake ji. Nimrah ɗin nan ba kunya ce da ita ba ita da Ruƙayya" Nabeeha daba wani saurarenta take ba a yanzu tuni ta dawo bakin gadon ta zauna. Kamar wadda ta ruɗe ta kalli Ismat ɗin da faɗin, "Ismat kar ki saka naji kamar zan haukace dan ALLAH da gaske?". "Aunty shiyyasa nace miki ban tabbatar ba ai. Amma mu bincika dai"......

<<<<<<<<%>>>>>>>>

A gidan Mammah kusan ƙarfe uku na rana Daddy Imran ya iso gidan. Su aunty Ummi duk suna nan, dan su Ja'afar ma yau basu je kasuwa ba. Dama su Bilal ma'aikata ne yau ranar hutu. Suna zagaye da Mammah da Dadansu cike da nishaɗi mara misali. Ga Uncle Nasiru yazo gidan shima kusan tare suka yini. Uncle Jamilu ma da su Gwaggo Khadijah sun tabbatar da suna tafe in sha ALLAHU. Dan yau ɗin ma duk sunyi magana da Dadan ta waya. Itama dai Ammie matar Daddy Imran tun ɗazun tana gidan, sai dai ita kaɗaice yara sun wuce islamiyya. Rashin yaran ya saka gidan zama babu hayaniya dan baby Nawal ce kawai data kasance ana goyo. Duk da Dada bamai jimirin hira bane bai ji ya ƙosa da wannan zaman ba. Dan ma su Lailah sun kasa sakewa saboda kunyarsa, shiyyasa ko hirar basa iya saka baki sosai sai jefi-jefi. Sai da ma suka ɗan shiga yin girki kitchen da su aunty Mommy sannan. Sanda suke kammalawa su Dadan suka tafi sallar azhar. Wannan fita salla ita ta saka Dada da su maigadi yin kiciɓus na farko, dan da asuba dukansu kaucewa sukayi dan ma shi Malam Buba ba gidan yake kwana ba. Yanzu kam babu wannan damar. Koda yake sun fito ne a bazata daga sashen Mammah ɗin, shi Malam Buba daya fara hangoshi har ya miƙe zai gudu cikin bayi sai akai rashin sa'a Ammar ya tsaida shi ta hanyar ƙwala masa kira. So yake ya bashi aikar amso masa saƙo wajen wani abokinsa. Daburcewa Malam Buba yayi, sai dai ganin da sun riga sun ƙure masa ya aro jarumtar dole. Haka ya iso inda suke da sassarfa yana kaucema idanun Dada, dan yasan a waccan haɗuwar tasu ta shekarun baya babu daɗi. Shi Dada ma hankalinsa ba kansu yake ba, waya yake yi da Imran ne daya kira shi. Har yayi kamar zai wuce su dan Ammar daya tsaya na bama Malam Buba saƙon ne. Sai dai me, kamar gilmawar inuwa a cikin ƙwaƙwalwa ya lura da malam Buba dake cikin yanayi na tsarguwa. Karo na farko ya ɗan zuba masa ido, dai-dai Malam Buba na gaishesu su duka. Sai akai sa'a kuma a lokacin Bilal ya furta, "Kun shigo kun gaida baƙo kaida su Malam Almu kuwa?". Malam Buba da ya runtse ido irin na naga takaina ɗin nan yay murmurshin ƙarafafa kai da faɗin, "A'a Alhaji, ai bamu san akwai wani baƙo ba, mun zata Alhaji Imrana ne ya dawo daga tafiya. A gafarce mu. Alhaji barka da zuwa ina yini". Dada dake kallonsa cike da nazari hannu kawai ya ɗaga masa. Sai kuma yay wucewarsa yana cigaba da wayarsa hankali kwance kai kace babu wani abu daya ma lura da shi. Dada mutum ne mai taku. Shiyyasa ko a gidan soja suke faɗin suna tsoron shirunsa. Dan ko kai waye baka isa a tashi guda ya maka magana ko nuna maka wani yanayi akan wani abu naka ba. Idan ma kana da ƙaracin tunani saika ɗauka bai san dakai ba a waje, a wannan silen yanayin nasa yake ma mutane da yawa illa batare da sun farga ba. Dan shi yanda kasan iskar dake gurɓata yanayin ƙasa haka yake shiga jiki a hankali batare da an ɗauki al'amarin da girma ba a zahiri.. Ganin abinda Dadan yayi ya bama Malam Buba nutsuwa da tunanin ai bai ganeshi bane, to taya ma zai gane shi a wannan yanayin ɓadda kamar tasa. Amma duk da haka dole ne yaje wajen Malaminsa ai masa aiki akan mutumin nan, dan lokaci yayi da za'ai wasa mai ƙyau da shima yake ganin zai zama wani abu a wajen manyansu, ba wai cigaba da zama ƙarƙashin Dagger ba kullum yana sammusu daga uwar dukiyar da ake basu. Ya tabbatar Dagger ya jima yana cutar su, kawai dai suna ƙyalesa ne tunda shine yasan manyan arnan, ta hannunsa suke samun umarninsu. Bayan sun dawo sallar ya sake iske Malam Buba ya ɗakko su Afrah daga makaranta, ya kaima su Nimrah abinci kuma. Anan ma ta gefen ido ya gama ƙare masa kallo dan ya kawo saƙon Ammar ne daya amso. Falon suka sake zama aka cigaba da ƴar hira, duk da dai shi ba wani magana yake mai tsaho ba ko da yawa. Hasali ma ya gaji da surutun amma bazai iya tashi ba saboda farin cikin ƴan uwansa dake zagaye da shi da yake ciki. Balle ga su Ayyan da aka ɗakko daga Islamiyya sun zagaye shi da labarinsu da a magana ɗaya biyu sai ance Aunty Ninah, aunty Ruky. Tun baya fahimtar wacece suke kira Ninah ɗin har ya gane. Dan tun jiya yake jin sunan a bakunan ƴan gidan bai tantance dawa ake ba sai yanzu. Kusan 2:30 ya tashi ya haura sama.

★Mintuna kusan talatin da shigowar tasa yana zaune kawai a sofa da laptop akan ƙafafunsa daya miƙe saman table, aiki sosai yake, sun fara shiri da yawa, shiyyasa yake jin bashi da wani lokacin hutu. Dan a nan kusa yake son ganawa da su Faro da sukai waya ɗazun ya sanar masa baya babban birni yaje wata jiha aikin gaggawa. Goran ruwa ne daya sha fin rabi a kusa da ƙafafun nasa, sai takardu daya baza a kusa da shi saman sofa ɗin da jikinsa. Koda akai knocking ƙofar bai ɗago ba balle dakatawa da abinda yake yi a haka ya bada iznin shigowa... Daddy Imran ya turo akwatin hannunsa Ammar da Bilal na biye da shi da wasu akwatinan suman. Sallamarsu da ƙarar tayoyin akwatinan ya saka Dadan a karo na farko ya ɗan kallesu. Sannu da aiki Bilal da Ammar sukai masa, ya jinjina musu kai kawai idonsa dai akan akwatinan da suke ajiye wa. Sai da suka juya zasu fita ya jefa musu tambayar da ta sakasu dakatawa... "Ma'aikata nawa ne a gidan nan?". Batare da tunanin komai ba Ammar ya ce, "Su biyar ne Dada, sai mata biyu dake aikin cikin gida. Kulu da Asabe, maigadi Malam Almu. Sai driver malam Buba. Akwai mai sharar tsakar gida da bama flowers ruwa sunansa Sanda ƙanin Malam Almu ne mai gadi. Sai kuma can ɓangaren su Yaya Ma'aruff, akwai maigadi ta gate ɗin can ma, da mai kula da flowers". Dada dake ɗan jinjina kai ya lumshe idanu yana sake buɗe su. Da hannu kawai yay musu alamar suje kafin ya maida idanunsa ga laptop ɗin. Sai da suka tura ƙofar batare da ya ɗago ba ya furta, "Malam ka dameni da kallo". Murmushi Daddy Imran dake tsaye ya riƙe ƙugu yayi, sai kuma ya zauna a bakin gadon yana faɗin, "Ba dole na kalleka ba. Kwana ɗaya ko gama hutawa bakai ba ka fara tambayar ma'aikatan gida. Anya kuwa Zak... Baka da aljanu?". "Tsamiya ce da kuka ba aljanu ba". Fashewa da dariya Imran yayi sosai.........✍️ [12/22/2025, 6:16 PM] Zeenaran 😘: 58

........"Daga ina ka fito da wannan kayan, kamar mai shirin kai lefen aure?". Dada ya katse dariyar tasa. Cikin shanye dariyar Daddy Imran ya ce, "Kayan lefen Nimrah ne dan gara ta tar......" Ai bai ma kai ƙarshe ba Dada yay wata kalar ɗagowa ya watso masa firgitattun idanunsa. Ai ko Imran ya sake fashewa da dariya harda kwanciya. Sai da yay mai isarsa ya tsaigata da faɗin, "Haba Zaki irin wannan kallon ai saika gigita ni, maida wuƙar wasa nake maka. Nima ba kare ya cizan ba da zan baka yarinyata tun yanzu ka halaka min ita yanda ka shekara takwas ɗin nan kana mafarke-mafarke." Kai kawai Dada ya girgiza batare da ya tanka zancen ba... Imran yasan iyakar amsar kenan. Shima sai ya saki zancen dan dama tsokanarsa yake ya fara masa bayani akan kayan cewar nasa ne da aka ɗinka. Sai takalma da dai duk wani abin buƙatarsa daya saba na yau da kullum.... Dada yasan wannan kaɗan daga aikin Imran ɗinsa ne, sai kawai ya zuba masa ido yama kasa magana. Cikin ƴar Harara shima Imran ya ce, "Malam nima daina kallo na." Dada ya ɗan murmusa kawai yana maida idonsa ga screen ɗin laptop ɗin sa......

★←★→★←★→★

"Mole miyasa kake nemana da gaggawa haka?". "Oga akwai matsala ne, duk yanda nai tunanin ajiyewa har na san gaskiya hakan ya gagara. Akwai fa baƙo da akayi a gidan nan shekaran jiya, kuma sam zuciyata ta kasa nutsuwa da shi saboda tare da Imran suka zo". "Baƙo! Tare da Imran?". Dagger ya faɗa yana tsatstsare Mole da idanu. "Tabbas, yanda kuma ƴan gidan suke masa ya saka na ɗora ayar tambaya a kansa". "Mole ina buƙatar ganin Nimrah yanzun nan". Yanzu kam sosai Mole ke kallonsa kafin ya girgiza kai". "A yanzu haka kaima kasan bazai yiwu ba, duk da makaranta zani ɗaukarsu, amma kasan ba ita kaɗai bace. Ga yarinyar nan murɗaɗɗiyar kanta ce, idan ba ita taso abu ba akwai daru." Iska mai zafi Dagger ya furzar yana kaina sitiyari duka, dan yasan gaskiya Mole ya faɗa akan Nimrah. Duba da tunda suka haɗu sau ɗayan nan yarinyar nan bata sake nemansa ba. A duk videon da masu bibiyarta kuma ke kawo masa babu ko ɗaya daya ganta a damuwa. Ya rasa wace irin sheɗaniyar yarinya ce ita. Cikin ɗan zafi-zafi ya kalla Mole da faɗin, "Amma ai kasan Zak-Shadow, taya zaka gagara ganesa a yanzu?". "Oga! Idan na gagara ganesa fa banyi laifi ba. Karka manta sanin da nai masa wancan karon sani ne na sama-sama. Yanzu kuma wannan baƙon harda ƙasumba a fuskarsa". "Mtsoww! Mole dolene naga Nimrah, dan na fara fahimtar kai wawa ne a wasu lokutan. Kayi duk yanda ma zakayi gobe mu haɗu." ya ƙare maganar yana jawo jotter da pen a cikin drower ɗin motar, rubutu yayi mara tsayi ya miƙa masa. "Ka bata wannan yau, a yanzu kuma". Komai Mole bai sake ce masa ba ya amsa takardar, dan kalmar Wawa daya kira shi da ita ta ƙona masa rai, dama ga Mole da shegen zuciyar tsiya. Shima Dagger cikin takaici ya sake faɗin, "Fita min a mota". Kallonsa Mole ya juyo yayi cikin ido, sai dai nan ma baice komai ba ya buɗe motar ya fita. Ta gidan su Nimrah da zai je ɗaukarsu ya koma. Sai da ya bar wajen sannan ya buɗe takardar da Dagger ya bashi.... (Ki gaggauta haɗuwarmu daga gobe zuwa jibi, dan akwai magana mai muhimmanci. Jinkirin ki zai iya zame miki dana sani da kukan rashin Ruƙayya ko Mamanku). Laɓɓa Mole ya cije tare da yin ƙwafa. Saboda irin wannan dama ya nutsu ya koya karatu da rubutu a wajen Dagger ɗin, gashi kuwa amfanisa ya fara zuwa masa a gaɓar data dace. A baki ya saka takardar ya taune ta, sai da ya tabbatar ta narke ya tofar a titi ya cigaba da tafiyarsa zuwa makarantar tahfiz ɗin su Nimrah......

★Idanu sosai Malam Buba ya zubama Nimrah da suke fitowa ita da Ruky, yanda suke dariya zaka tabbatar wata hirar farin cikin suke yi. Mu'azz ya ƙaraso inda suke yana miƙa musu leda, hannunsa da ince na leda yana sha alamar shine a ledar da suma ya basu. Wani murmushi ya saki a karo na farko. Zuciyarsa na ayyana masa lokaci fa yayi da shima zai ci arziƙin wannan wahalar tasa. Dole ne yay ma Dagger juyin mulki ko su zama sarakuna biyu a fada guda. A yanzu fa ƴar nan tasa itace IGIYAR FITO da kowa zai buƙata wajen samun nasarar kaiwa GAƁAR ruwan kodan ceton rai ba DUKIYAR da aketa kai-kawo a kanta kawai ba. Domin kuwa shi shaida ne, mutumin nan da gaske shi ne DODON mutanen nan duk ƙarfin su da damar da suke da ita a hannu. Gashi kuma a salon daya dawo zai iya zame musu KIƊA A RUWA... kenan washi dama ce a yanzu da zai murza kambunsa fiye da kowa, ta yanda gaba ɗaya manyan ƙungiyar ma zasu koma tafin hannunsa sai abinda ya faɗa musu, dan yana da abubuwa fiye da Dagger da suke ganin shi kaɗai ne shegen su. Kai-kai shi kam yau sai yaji ma yana alfahari da abinda Hassatu tai masa na bada Nimrah ga Zak-Shadow... Karo na farko a rayuwarsa ya ayyana (ALLAH ya jiƙan ki Hassu na. Kin haifa min ƴar gudalliya ta zame min alkairin tsanin yin kuɗi da zan fantama a rayuwa ni da ita.....) Isowar su Nimrah ya katse masa tunani, duk suka gaisheshi kamar ya da suka saba sannan suka shiga mota. Mu'azz na gaba suna baya. Duk sun cika motar da hirar su har suka iso gida....

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

"Wai nikam yau lafiya? Sai nake ga kamar kanata ɓoye-ɓoye. Musamman idan ka kimanci lokacin fita massalaci. Sai yanzu kuma nake ganin kamar kana yin haka ne saboda baƙon nan na jiya." Wata shegiyar harara Sanda ya zabgama Malam Almu da faɗin, "Oh ido ka saka min kenan ban sani ba?". "A'a wlhy taya zan saka maka ido ni kuwa. Kawai dai ina ganin ya kamata idan da wani abu ne ka sanar min nima sai na kiyaye gudun kwaɓa aiki. Bana son nayi wani kuskure da ƴar uwata zata cutu a dalilin sakaci na shiyyasa. Saboda ni kaina dai da jiya kawai na fara ganin baƙon nan sai na jini kamar a tsorace. Dan daga ganinsa kaga BARDEN NAMIJI da baya buƙatar wargi. Irin waɗan nan kuma yana da ƙyau kasan su wanene su kodan ka kiyaye musu". "Mtsowww! Malam Almu tashi ka bani waje kafin na canja maka kamanni, ka cika min kunne da shegen surutunka fa mara amfani". "ALLAH ya baka haƙuri, ya huci zuciyar ka. In dai nine kaga tafiya ta". Maigadi ya faɗa yana fita a ɗakin yabar Sanda dake binsa da kallon harara. Fitar tasa ce kuma tai dai-dai da isowar Malam Buba ɗauke da su Nimrah. Dan haka ya buɗe masa gate al'amarin Sanda na cigaba da masa kai-kawo.......

______________★

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull