Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 26
Kida a ruwa book 2 complete Chapter 26: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 26. Ƙarar da Afeef ya fasa ta daki falon gaba ɗaya. Kowa ya zabura kamar an…
4,286 words
Ƙarar da Afeef ya fasa ta daki falon gaba ɗaya. Kowa ya zabura kamar an harba bindiga. Kofin shayin ya watse, ruwan ya zuba a kafet ɗin tsakkiyar falon, shi kuma yana mirgina a ƙasa yana riƙe ƙafarsa yana nishi. "Wayyo ALLAHA! Wayyo kaina, ƙafata". "Subhanallah!" "Innalillahi!" Muryoyin su Aunty Shariffa suka gauraye falon. Mammah ta miƙe da sauri tana nufarsa, Aunty Lailah ma ta biyo bayanta. Hakama Biebah da Ruky da har zata nufi kitchen ta dawo. Hanoon da Dayyan sun miƙe tsaye suma a firgice, hakama Mu'azz da sauran yaran su Aheel na tsaye kowa na kallon abin kamar fim. Dada ma ya tsaya cak, sai dai baiyi magana ba. Sai idanuwansa da suka sauka a wajen. Kallon farko ya tsaya ne kan Afeef dake kwance yana nishi. Kafin ya maida kan kafar daya riƙe da hannu biyu yana magowa alamar tana masa raɗaɗi. Slowly ya maida kan Nimrah ƙasa-ƙasa ta yanda babu wanda zai ce ita yake kallon. Tsaye take. Hannunta biyu riƙe da ƙugu. Fuskarta a haɗe, kamar bata fahimci me ya faru ba, ta wani zuba masa idanu kamar kowa. Idanun kuma darr babu alamar na mai laifi data firgita sakamakon ganin abinda ta aikata. Dada ya ɗan lumshe ido, ya sake buɗe su a hankali, ya maida kallonsa kan Afeef. Sai dai yanzun ma bai da alamar cewa komai. "Subahanallahi kaji ciwo ko ruwan zafin ne ya ƙona ka?" Mammah ta faɗa tana durƙusawa kusa da shi da kamo sa jikinta. "Zafi nake ji!. Kafa ta…" Afeef ya faɗa hawaye na ziraro masa a fuska. Biebah ta kalli shayin da ya zube. Cikin nuna mamaki ta ce, "Wai yaya ma haka ta faru? Naga babu komai a hanyar nan dai amma kamar wanda yaci tuntuɓe irin wannan muguwar faɗuwa haka". Afeef ya ɗaga kai, idanunsa na sauka kan Nimrah kai tsaye ya ce, "Ita ce. Ita ta saka min ƙafa." Falon ya ɗauke shiru na daƙiƙa ɗaya. Kafin Nimrah data zazzaro masa idanu ta ce, "Ni?!" ta faɗa cikin kamar ma mai mamaki irin na karya. Sai kuma ta shiga tafa hannaye "Kai! Amma kai mugun maƙaryaci ne. Ta ina zan iya kada ƙaton nan kamar ka to?!". Hanoon da ranta ya ɓaci sosai ta watsa mata harara, sai dai batace komai bata. Ruky data gama sanin wacece Trouble Queen ɗinta ta haɗiye dariyar dake son bayyana a fuskarta saboda Dada. Mu'azz ya taɓe baki yana ƙoƙarin danne dariya shima, dan tsaff ya gane aikin Ninah ɗin ne, haba shekara nawa ana haɗakar tsiyataku a tare. Aunty Lailah da Shariffa kam kallon su biyun kawai suke kamar ba su san dawa zasu yarda ba. "Nimrah… Mi ya faru?". Mammah ta kira sunanta a hankali, sai dai ta kafeta da idanu. Shagwaɓe fuska Nimrah tayi, kafin ya ce, "Ni Mammah sharri kawai yake mun. Kowa ai yana ganin tsifa nake ma Afrah. Yanzu nida ke can, yana nan ƙafar barewa ce da ni balle na iya zunguro shi?. Ƙilama ƙafafun nasa ne basu da kwari, dan gasu nan tsulai-tsulai kamar na talo-talo wlhy". Kafin kowa yace komai Afeef ya harare ta. "Wallahi ke kika saka min ƙafa!". Caraf Ruky ta ce, "Karya kake! Dan ina tsaye ta kusa da ku ni ban gani ba" A hasale Hanoon dake hararar Ruky ta karɓe da, "K dama ai bazaki faɗi gaskiya ba bakin ku ɗaya munafuka fitinannun yara! Kawai". "Ke ma fitinanniya! Dan ni da Buddy na albarka kullum Mammah ke saka mana da iyayenmu". Nimrah ta faɗa tana murguɗa ma Hanoon baki da nuna su Shariffa. Hanoon zata sake magana Mammah ta dakatar da su. "Ya isa haka. Mu'azz bani first aid kit" Mammah ta faɗa tana kama ƙafar Afeef da cigaba da faɗin. "Bari mu fara ganin kafar yafi wannan gardamar taku." Sai lokacin ta juya ta kalli Dada da tamkar baya ma a falon kamar tana neman taimako. Amma sai gani tayi hankalinsa ma akan wayarsa yake gaba ɗaya. Dole ta haƙura ta maida idanuwan nata ga Afeef. Abinda Mammah bata sani ba sarai Dada na lure da kallon datai masan, amma ya fiske. Sai ma mamaki da jinjina ƙarfin halin yarinyar nan da yake a ransa. Dan tsaff ta koma inda ta tashi abinta hankali kwance ta cigaba da ma Afrah tsifarta babu alamar tausayin yaron ko ɗigo. Murmurshi ne yay kamar zai kufce masa amma ya matse. Sai ma ya nufi ƙofa abinsa yana faɗin, "Mammah sai na dawo". Maganarsa ta saka hankalin su Shariffa dawowa kansa. Sai lokacin suka tuna ko gaishe shi basuyi ba. Aiko cikin sauri suka fara gaishe shin, dole ya dakata yana amsawa. Nimrah dake jin idanu masu kaifi a kanta tun ɗazun sai dai ta rasa wake kallon nata ta ɗan motsa kaɗan, zuciyarta na bugawa, amma fuska a tsuke kamar ba ruwanta. Nata idanun ta ɗan ɗago a karo na farko ta saci kallon Dada da kowa ke gaidawa. Cikin sa'a kuwa sai idanun nata suka faɗa cikin nasan. Cikin sauri ta janyesu ta sauke kanta ƙasa ƙirjinta na sake bugawa.. Dada da shima ya janye nasa cike da basarwa yana sake ɗaure fuska ya ɗan ja numfashi a hankali. Sannan ba tare da ya ɗaga murya ba ya furta "Sai na dawo". Muryar sa ba tai ƙarfi ba. Amma amonta da tasirinta ya ratsa kowa dake falon, musamman Nimrah. Dan kallon da ya sake yi mata kafin ya juya, ya sa zuciyarta ta buga sau biyu. Domin ta fahimci abu ɗaya. Dada ya gani. Kawai bai faɗa ba ne. Sannan bai nuna alamun yama san abinda akai ba. Bai ce Nimrah ba. Bai ce Afeef ba. Bai yi hukunci ba. Sai dai taji tasirin kallonsa na ƙarshe ɗin nan da idonta ya gani, dan bazata iya tantance na baya da bata san wanene ke mata shi ba.........✍️ [12/23/2025, 5:56 PM] Zeenaran 😘: 64
..........Babu wanda ya sake furta komai a ɗakin sai babbar jakar dake gefen oga Jush yay ma Mr Specter nuni da idanu. Mr Specter ya jinjina kai da tura jakar da ƙafa gaban Mole. "Ga wannan kaje da ita zamu nemeka idan buƙatar hakan tashi." Wani irin daɗi ne mai barazanar fasa zuciya ya daki zuciyar Mole. Duk da yaji damuwa da shirunsu bayan maganarsa ta ƙarshe, dan yaso ace sun tattauna fiye da haka domin su ƙara yarda da shi fiye da yanzu. Amma ko hakan ma ai tafiya tayi riba, dan ya tabbatar maƙudan kuɗi ne irin wanda aka saba bama Dagger yana tsakura musu yanda yaso, shima yau gasu an bashi matsayin nashi. Lokacin gina sabuwar rayuwa yayi, dan yana son sanda Nimrah zata dawo hannunsa tasan shi cikakken uba ne da zai mata gata....
Bayan sun sallami Mole ƙofar ɗakin ta maida kanta ta rufe. ɗakin ya sake komawa wani irin yanayi na shiru. Ba hayaniya. Ba motsi. Sai na ac. Shirun da kan gitta tamkar mutuwa ta ziyarci waje. Shirun da yake sa zuciya ta dinga tambaya kafin harshe. Oga Jush ne na farko da ya motsa. Ya gyara zama a kujerarsa a hankali, kamar wanda ke sauke nauyin wani tunani mai tsanani. Bai dubi kowa ba. Sai teburin dake gabansa. "Zak-Shadow…" Ya faɗa sunan cikin murya ƙasa-ƙasa. Black Spider ya ɗaga kai kaɗan ya kallesa, sai dai bai ce komai ba. "Na zata an gama da shi." Oga Jush ya ƙara faɗa, wannan karon muryarsa cike da ɗaci da zafin rai daya kasa dannewa. Iska mai kauri Viper ya furzar. Cikin nashi yanayin ɗacin ya furta, "Oga dama mutane irinsa nada taurin rai saboda taurin kansu. Gadararsu ta banza da wofi kansa su dinga jin ba su gama ba. Su kan ɓace ne kawai da maimaita kalmar zasu dawo koda da cika baki ne." Ƙwafa mai ƙarfi oga yayi, ƙwafar dake nuna babban ƙudirin dake tafasa zuciyarsa a wannan gaɓar. Sai kuma shiru ya sake ratsa ɗakin, kowa da irin tunanin da yake yi. Dan su sun ma fi oga Jush shiga cikin razani. Oga Jush ya sake katse shirun nasu. "Tambaya ya kamata muyi ma kammu yanzu, ba dawowarsa kawai ba." Ya ɗaga kai ya dubi kowan nen su a jere. Kafin ya cigaba da faɗin, "Tambayar ita ce… me ya dawo domin yi?" Tamkar ya dakesu a zukata ne da wannan kalma, dan babu wanda baiyi motsi irin na mai cizon cinnaka ba. Black Spider da ya jingina da bango, muryar sa na shaƙewa a naƙoshi ya amsa da, "Idan har ya sake kafa gida, to yana nufin yana da abin karewa." Viper ya ɗan yi murmushi mara daɗi. "Ko kuma ita ribar ƙafar ba, dan ina ji a raina riƙonta a garesa da manufa. Karfa ku manta yana da wayo, yana da target." Oga Jush ya lumshe ido na daƙiƙa kaɗan. Kafin a hankali ya ce, "Tabbas maganarka gaskiya ce. Musamman idan muka kalla Mole. Tana kusa da shi. Kuma ba ta san komai ba a kansa." Black Spider ya ɗan jinjina kai da furzar da numfashi mai nauyi. "Wannan ne mafi haɗari. Ku duba, mun bata video ɗin nan, amma babu wani motsi…" Shiru ya sake mamaye ɗakin kamar an kashe iska. Kowa ya nutsu cikin tunani, ba don rashin amsa ba, sai don girman barazanar da ke gabansu. Viper ya gyara zamansa da faɗin, "Idan har yarinya ta iya jure irin wannan barazanar, to tabbas tana da ƙarfin zuciya da dole sai mun sake nazartar ta… ko kuma tana cikin shakka da wasi-wasi. Kuma dole mu gaggauta......" Oga Jush ya ɗaga hannu da alamar yarda da zancen Viper ɗin. "Yarinyar ba matsala bace," Oga Jush ya furta yana zuƙar sigari, sai da ya fesar da hayaƙin da sake gyara zaman ƙasaitarsa yana kakkaɓe tokar sannan ya cigaba da faɗin, "Matsalar ita ce wanda ke kusa da ita. Ku sani Zak-Shadow bai dawo domin zama ba. Idan har ya sake takun zahiriyya, to lallai ya dawo ne domin ya gama abin da bai kammala ba a baɗini." "Kenan oga hakan na nufin idan yarinyar bata motsa ba, zamu tilasta mata ta motsa dole?." "A'a. Ba da gaggawa ba." Ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya saki wani murmushin mugunta mai armashi da ban tsoro. Sai kuma ya haɗe fuska da ƙarasawa da, "Amma daga yau… ta zama hanyar shiga." A tare suka bubbuga tebirin gabansu alama na amincewa. Babu dariya. Babu tambaya. Babu jayayya. Shirun da ya biyo bayan maganar ya fi kowace hukunci nauyi. Wannan shirun ya fi kowace tsawa firgita.....
>>>>>>>%<<<<<<<
Fitowarsa ya saya Imran dake tsaye jikin mota yana duba wayarsa kamar wanda ke jiran lokaci ɗagowa yana kallonsa. Shima kallon nasa yake, koda suka haɗa ido sai ya ɗauke nasa, kai kace baiga Imran ɗin ba ma. Dan kai tsaye gaban motar ya buɗe ta gefen mai zaman banza ya shiga abinsa. Imran dake binsa da kallo yay murmushi yana ɗan taɓe baki, kafin shima ya zagaya gefen driver ya shiga ya zauna.. Sai da ya tada motar ya ɗan kallesa da faɗin, "Ni harna fara tunanin binka ciki ma, jin shiru bayan kace gaka nan fitowa". Dada bai amsa ba. Ya daidaita zamansa ne kawai, ya jingina da kujerar, yana mai lumshe idanunsa. Sai da suka fice gaba ɗaya a gidan sannan Dada ya ɗan saki numfashi, tare da motsa lips kaɗan, cikin murya ƙasa-ƙasa ya furta, "Hmm.. yaranka basa ji." Imran ya ɗan juya kai ya kallesa, sai kuma ya saki murmushi da maida hankalinsa a titi sosai. "Oh, su ne suka tsaidaka kenan? Mi ya faru?" A nan ma shiru yay kamar bazaiyi magana ba. Irin shirun nan na manya, wanda baya nufin babu abin cewa, sai dai ana tattara abin faɗar ne saboda ɗabi'ar rashin son magana. Imran yasan halin kayansa, dan in kaji doguwar magana a bakin Zak... Ɗinsa ɗayan biyu ne. Kodai akan aiki, ko yana tare da Mammah ko da shi randa yaso hirar. Sun riga sun fice daga unguwar, har sun shiga babban titi, Imran na kallon hanya cike da natsuwa. "Wai bazaka gaya min ba, sai na sauke ka a hanyar nan?". Idanu Dada ya ɗan buɗe yana harararsa, Sai ya kauda kai gefe, kamar yana kallon wani abu a waje, ya ɗan taɓe baki, murmushi yana ƙoƙarin kufce masa amma ya haɗiye kayansa. "Kana son bani ciwon kai ne kawai kai da su Imran. Tsabar mugunta yaron nan kawai ta sama ƙafa ya kife a ƙasa shi da kofin tea. Ta kuma fiske abinta baka isa cewa ita ta aikata ba, harda kiransa mai ƙafar talo-talo". "ALLAH ya shirya min Ninah" Imran ya faɗa yana ƴar dariya. Dada ya juyo ya watsa masa harara. "Oh abin ma sugar yay maka kenan? Idan taji masa ciwo kuma fa?". "In banyi dariya ba kuka kake son nayi. Indai su Nimrah ne kaɗan daga aikin su ka gani." Shiru ya sake ratsa motar. Amma wannan karon shiru ne mai ɗauke da dariya a ciki. Dan Dada gintsewa kawai yake, amma yanda ta saka ƙafar yaron ya kife kifff kawai ke dawo masa cikin rai. Yana buɗe file ɗin daya ɗauka a gaban motar ya sake furta, "Na shaida hakan yau kam, dan ƙiri-ƙiri Ruƙayya ta bata kariya bayan yaron ya tabbatar ita ce ta kada shi, Mammah kuma ko faɗa bata musu ba fa." Imran ya saki dariya sosai har yana ɗan dukan sitiyari. Sai da yay mai isarsa, Dada da ya kallesa ya girgiza kai kawai. "To wai wanene aka kada? Nasan dai ba zasu ma Mu'azz ba". Dada ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin sanyin murya, "Cikin yaran mutum nan ne. Dama na fahimci ƴar tsama suke da su". "Kaji fitina, yaron da a tsaye ya fisu sau biyu!" Imran ya furta yana dariya. "Ba ku kuke ɗaure musu ƙugu ba, ba Mammah ɗin ba, ba kai ba balle Uncle's da Auntys ɗin nasu. Abinda suka aikato a school yau banji wani yace musu dan mi ba, ƙarshe ma Mammah na gayama su Ma'aruff dariya na jiyo sunayi Bilal harda musu kirari". Imran ya sake kallonsa, wannan karon da nishaɗi sosai. "Ba wani ɗaure musu ƙugu da muke. Dole akwai abinda ya aikata musu shima, dan duk ƙiriniyarsu basa faɗan rashin gaskiya. Ɗazu ma lawyer ɗin nasu ya kirani yana min bayani wai yaron ya farfaɗo, amma iyayen sun kawo lawyer suma, da farko da sun dage sai an sake maido su station ƴan sandan suka nuna masa basu cika 18years ba, basu da hurumin riƙesu anan." Dada ya ɗan yi ƙwafa kaɗan, murmushi na neman kufce masa. Ya dai juyo gefe yana ƙoƙarin ɓoye abinsa. Kamar baya so ya furta, "Yara ne. Amma ba ƙanana bane tunda har suna da wayon banbance abubuwa. Dan itama Ruƙayya aure zan mata" Cike da neman magana Daddy Imran ya ce cikin raha, "Hmm… yanzu ka fara ganewa kenan?" Dada ya kallesa. "Gane mi?" Imran ya ɗaga masa gira cike da tsokana da son ganin ya ƙure shi. "Cewa ɗiyata Nimrah ta girma." Nan ne Dada ya kasa danne kansa. Ya saki ɗan murmushi mai nauyi, ya kauda kai gaba ɗaya yana girgiza kai a hankali. "Kar ka fara". Ya faɗa cikin gimtsewa. Dariya Daddy Imran ya saki. "Wlhy dole in fara. Saboda kallon da ka mata yau a station… ai na san wannan kallo." Dada ya ɗaga kai yana harararsa da sake ɗaure fuska, sai dai murmushin dake makale a fuskarsa ya neman fallasa shi. "Imran!" Ya faɗa da gargaɗi. "Yi haƙuri Babban Yaya, wannan idanun bana son suna hararata." Sake hararar tasa kuwa Dadan yayi yana ɗauke kai. Imran ya murmusa da cigaba da faɗin, "Amma kai ka fi kowa sanin damuwar ka. Ka ƙi kace komai akan dawowar Nabeeha. Zak.. shekara takwas fa ba wata takwas bane. Lemon tsami, kanwa, azumin nan duk basa hana komai, kwantarwa ne kawai na lokaci. Ya kamata kayi abinda ya dace, bance Nimrah ba, dan tabbas tayi ƙanƙanta a shekaru, amma da wayonta. Sannan Nabeeha ba sakinta kai ba balle kace. Komai ya dai-daita, sai dai ka sani aiki bazai samu dukkan ƙarfinka ba, sai kaima ka Dai-daita. Wannan danne damuwar ta tsiya-tsiya bazata haifar da ɗa mai ido ba". Dada da ya ce, "Hummm" kawai ya yi shiru. Sai dai wannan shiru ba na ɓacin rai bane. Na tunani ne… da ɗan murmushi a zuciya. Dai-dai nan suka iso inda suka nufo. Ɓoyayyen guesthouse dan haɗuwar ta sirri ce da shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida...........✍️ [12/24/2025, 11:46 AM] Zeenaran 😘: 65
........A gidan Mammah kam bayan komai ya lafa, aka taimaka wa Afeef aka kai shi sama, ƴan uwansa Hanoon da Dayyan na tare da shi. Dan wata irin tsanar Nimrah da Ruƙayya suke ji na ƙara tasiri a zukatansu. Hatta ƴan gidan kowa ya basu haushi yau, yanda ko sau ɗaya ba'ama Nimrah faɗa ba balle cigaba da tuhumar gaskiya. Dan koda su Ma'aruff suka shigo kasancewar basa gidan su duka huɗun sunje duba wani makwafcinsu ne da baida lafiya da aka basu labari ko nuna zargin ma Nimrah basuyi ba su. Ƙarshe ma hira suka koma abinsu kamar komai bai faru ba. Hanoon ta kira Abbansu ta sanar masa komai, baya ƙasar dan tunda ya kawo su gidan yay tafiya. Shima ransa ya ɓaci har yana faɗin sai yayi maganin Nimrah idan ya dawo. Tunda yaga tsoronta suke ji a gidan. Shi yama rasa dangantakar su Adda A'isha da yaran duk da dai adadin jikokinta kawai ta sanar masa batai masa bayani ba bayan hakan. Shiyyasa yake tunanin jikokinta ne. Wayar yace a bama Afeef, ya lallasheshi da tabbatar masa zai dawo a cikin satin nan. Idan kuma zasu koma gida Lagos ne to ya saya musu ticket. Caraf Afeef yace shi bai yarda ba, yafi son Nan ɗin, dan wlhy bazai tafi ba sai ya rama.. Sallama yay musu da faɗin sai ya zo to. Daga haka aka yanke wayar Hanoon na cigaba da faɗin, sai ta koyama su Nimrah hankali a gidan nan. Shi ko Dayyan ƙudirinsa daban a cikin rai. Dan tunda yazo gidan hakanlinsa akan yaran nan biyu yake. Rashin mutuncin su ya saka shi haɗiye kwaɗayinsa. Sun jima a ɗakin kafin su fice su bar Afeef, dan abokin kwanan nashi Mu'azz bai shigo ba. A daren Afeef ya jima bai yi bacci ba yana ƙulla abinda zai ma Nimrah. Dan can cikin dare ma zaune ya tashi a kan gado kafarsa na masa masifar zogi, fuska a haɗe kamar ya ci lemon tsami. Waya ya ɗauka yana danne-danne, amma tunaninsa na kan ƙulle-ƙullensa. (Wallahi ba zan bari ba) Ya tuna murmurshin da Nimrah ta masa da gwalo bayan fitar Dada. Da yanda suka kalla juna da Ruky da munafukin nan Mu'azz sukai wani salo da yatsu suna gimtse dariya. Itama Ruƙayyan yana ganin yanda take kallonsa tana murmurshi. Harda gwada masa yanda shugaban ƴan iska ta saka masa ƙafa. Hakan na nufin itama ta gani amma da yake mufuka ce bakinsu ɗaya ne ta musanta harda bata kariya. "Yar iska… zanyi maganinki ta yanda ko takuna kika ji sai kin firgita " ya faɗa ƙasa-ƙasa. Sai kuma yay ƙwafa da sake faɗin, "Ba kince kina da wayo ba." Ya saki murmushi yana cizar lips da ƙara faɗin, "Zan tabbatar muku na fiku zama tantiri. Zaku san ni cikakken rainon yahudawa ne. Idan ba yau ba, gobe. Idan ba a falon ba, a wani wuri." Ya saki wata shegiyar dariyar data farkar da Mu'azz a barci. A fili ya sake faɗin, "Sai kin gane baku kaɗai bane jiƙaƙƙun tantiran ƴan iska a gidan nan". Sarai Mu'azz yaji furucin Afeef na ƙarshe. Sai dai bai ce komai ba, baima nuna masa ya farka ba. Amma ya fahimci akwai abinda yake shiryawa kuma akan Nimrah. Ji yay tausayin Afeef ɗin ma ya kama shi, dan wlhy ya tabbatar yace zai cigaba da shiga sabgar Ninah da Ruky a gidan nan to da wahala ba'a fita da shi a ambulance zuwa asibiti ba wataran. Dan yafi kowa sanin yaran nan, zaman lafiyarka da su kawai kada ka shiga sabgarsu. Anan kam zaka ga biyya, amma saɓanin hakan ALLAH ne kawai mai ƙwatarka saboda hanyoyin mugunta iri-iri sun santa kamar goyon iblis. Bari ya barsu da shi jikinsa zai gaya masa....
★A ɓangaren Nimrah tuni tama manta da wani batun Afeef. Dan koda suka shiga ɗakin su tsara yanda zasuyi yawo a weekend ɗin nan suke yi, suna fatan ALLAH ya ɗorasu akan Mammah kada ta hana su duk da suna hutun tahfiz ne. Sun jima kafin su kwanta sanin gobe akwai makaranta, duk da dai basu san ya zata kaya ba tunda sun bazar da ɗan shugaban ƙasa mai sauka a ƙasa. Nimrah ta kwanta amma bacci ya ƙi zuwa. Ruky ko tuni ta yi bacci tana sauke numfashi a hankali. Ita kam… ido biyu a rufe amma zuciya a buɗe. Haka kawai abinda ya faru ɗazu a falo kuma ya shiga dawo mata a rai. Ba kuma akan kowa ba sai kallon Dada ne yake dawowa mata a kai. Ba tsawa. Ba magana. Sai shiru da kallonsa mai kaɗa hanjin ciki.. "Tabbas ya gane ni na kada garan can fa…" Ta faɗa a ranta tana ɗan waro manyan idanunta cikin duhun ɗakin.. Ta ɗan matse bargon cikin hannunta. Ba tsoron abin da tayi take ji ba. Tsoron abin da ya gani take ji. "Me yasa bai ce komai ba?". Wannan ne ya fi tsaya mata a rai da zuciya. Idan ya yi tsawa… da sauƙi musamman in ta tuna yanda Small Mom ke basu labarin halinsa na rashin ɗaukar wargi. Kuma a ɗan dawowarsa sati gudan nan sun fara gane hakan suma duk da bawani zama yake cikin su ba. Magana ma sai idan da Mammah ne zaka ji yana yinta da tsayi. Bargo taja ta rufe har kanta tana faɗin, "Wayyo ni Nimrah ai gara ma ya yi hukunci zai fi sauƙi. Amma shiru irin nashi? Zai sa ka dinga tambayar kanka kamar wani mahaukaci". ta ƙare maganar tana bubbuga gadon kamar wadda ke swimming a cikin ruwa. Gaba ɗaya tunaninta ya cika da wani yanayi mai gauraye da ƙiriniya, ruɗani, ƙuruciya da wani al'amari da bata so ta saka suna ba. "Kar ma ki sake." Wani gefen zuciyarta ya faɗa cike da gargaɗi. Itama sai ta sake cukuykuye kan nata faɗin, "Nimrah kin mutu kawai gobe a gidan nan". Dama ga batun Zahir, yanda kowa yay musu shiru har Daddy, hakan na nufin an barsu da Dadan, shi kuma yaƙi ko sake tada batun. Ba ta gama tunanin ba. Bacci yay awon gaba da ita kasancewarsa gwanin iya sata......
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
Su Daddy Imran basu wuce mintuna biyar da isowa ba Motar dake ɗauke da shugaban ƙasa Tafida ta iso ba tare da hayaniya ba. Ba siren. Ba security. Ba wani alamar wani mai girma ne dan daga shi sai amintaccen dogarinsa. Kamar ba shugaban ƙasa bane a ciki. Sai dai duk mai huɗɗa da masu mulki yasan wannan ba komai bane daga yadda ake ɓadda kamar ɓoye iko a ganawa irin wannan ta sirri. Har yanzu su Imran suna cikin mota dama basu fita ba suma. Dan babu wani hasken fitilu mai yawa a ƙaramin compound ɗin gidan. A dai-dai inda motarsu take ta su Janar ma ta tsaya. Dogarinsa dake tuƙin ya fito da sauri yana buɗe masa murfi, dan yana zaune ne a baya. Dai-dai nan Daddy Imran da Dada suma suka fito. Shugaban ƙasa Tafida ya ɗan zuba musu ido, sai kuma ya saki gajeren murmurshi ransa fal farin cikin ganin yanda Dada ya dawo Zak-Shadow ɗinsa. Banbancin kawai gashin saje daya ajiye yanzu akan kyakkyawar kamilar fuskarsa mai bayyana kwarjinin ibada. Amma kasancewar shekaru sun ƙaru sai Janar ya ga kimar da kamewar haɗe da cikar haiba da nutsuwar kamar sun ma fi na Zak-Shadow ɗin shekaru takwas ɗin baya. Dan wannan na yanzu kai da ka hangosa koda daga nesa ne kasan ba ZAKIN wasan yara bane. Nagartaccen mutum ne da UBANGIJI yay ma baiwar abubuwa da yawa da sai mai hankali ke iya kallonsu tun daga zahiri.... Dada daya tabbatar da idanun Janar dake yawo a kansa sai ya kauda fuska. Yanda yay ɗin sai ya bama Janar dariya. Amma bai dara ɗin ba ya dai ɗan murmusa da maida kallonsa kan Imran. A tare Dada da Daddy Imran suka ma Janar barka da isowa. Daga haka suka wuce ciki ba tare da gaisuwa mai tsawo ba. Gida ne mai ƙyawu sosai da yaji kayan alatu irin na manya. Dan shiryayyun kujerun kansu abin kallo ne. Tuni an shirya abubuwan ciye-ciye a Centre table ɗin tsakkiyar kujerun. Hakan yasa ƙanshin abubuwan dana room fresheners da aka sanya suka haɗu suna bada ƙamshi mai armashi. Ga sanyin ac da ke fita kaɗan-kaɗan. Ba'a cika ba, ba ai ƙwauro ba. Television ma na'a kunne, sai dai ba ƙara sosai dan ko maganar da ake a ciki ba'aji. Daga Imran har Dada babu wanda ya tambayi waye yay wannan aikin, sai ma zama da sukai bayan Janar ya fara zama saboda girmamawa a garesa matsayin ogansu, babban yaya, idan ma sun kira shi uba basuyi laifi ba, sannan shugaban kasa. Sunyi gaisuwa fiye data waje, Janar yay addu'ar godiya ga UBANGIJI da komai yazo da sauƙi fiye da yanda akai zaton sa. Dan tun suna Jamus Imran na sanar masa duk abinda doctors sukace game da lafiyar Dada. Dai-dai lokacin dogarinsa ya kammala zuba coffee a kofuna masu shegen ƙyau na zallar farin gilashi mai garai-garai daga haɗaɗɗen coffee maker dake saman Centre table ɗin. Gaban kowa ya kai ya ajiye. Kafin cikin girmamawa ya nema izinin tafiya. Kai Janar ya jinjina masa alamar bashi dama. Sai ya sake risinawa sannan ya fice ya maida ƙofar ya rufe musu, bayan ya ƙara rage hasken falon ya bar blue ɗin wuta mara ƙarfi kamar waɗanda ke cikin club.........✍️ [12/24/2025, 12:12 PM] Zeenaran 😘: 66