Kida a ruwa book 2 complete - Chapter 32
Kida a ruwa book 2 complete Chapter 32: Kida a ruwa book 2 complete Chapter 32. Lokacin da suka fara aikin su kuma su Nabeeha hankalinsu nakan nasu aikin,…
4,364 words
Lokacin da suka fara aikin su kuma su Nabeeha hankalinsu nakan nasu aikin, shiyyasa babu wanda ya maida hankali akan wani, musamman daya kasance bata wannan bangon ɓangaren Nabeeha ɗin yake ba. Sun kammala suka koma sashen Mammah yin shiri, dan sabon ɗinkuna su Uncle Ja'afar suka musu har kala uku-uku na suna. Afrah na maƙale da Nimrah, dan haka ta fara shiryata ta mata wayon aikata wajen Mammah. Daga haka itama tahau shiri, su ma su Ruky nayin nasu. Sauri-sauri ta kammala nata shirin, ta idar da sallar la'asar sai ga wasu ƙawayen Bintu sun kira akan basu gane Street ɗin ba. Caraf Nimrah tace ta bata wayar tunda ita ta shirya zataje ta tarbosu. Basu kawo komai a ransu ba ta amshi wayar Bintu ta fito, dan suna da waya daga ita har Feedo. Lokacin da Nimrah ke fita a gate Sanda na cikin bayi, sai baba maigadi kawai. Shi kuma bai kawo komai a ransa ba jin tana waya tana yin kwatance alamar wasu zata tarbo. Hakama securitys ɗin dake waje, yanda ta tsaya tana waige-waige ga waya tanayi yasa suma basu maida hankali ba, gashi ma abinci da aka kawo musu suke ƙoƙarin fara ci. A wannan lokacin da gaske Nimrah ta fito ne da niyyar tarar baƙin Bintu, amma daga nan tana son tayi waya da Dagger ta sanar masa da anyi magriba ya fito su haɗu. Amma sai mi ta ɗan bar gate ɗinsu kaɗan sai ga su Adeel da Yohan da yake gidansa zaune. Nimrah bata san shi ba, kai ko Yohan ɗin bata sani ba, dan haka ko kallo ma basu isheta ba ta cigaba da tafiyarta tana tunkaro su. Cak Adeel ya tsaya kansa na wani irin tsuwwa da ganin Nimrah a bazata. Dan yau kwanansa biyu kenan da dawowa ƙasar amma ko mai kama da ita bai taɓa gani ba. Kai koda Ammar ma basu haɗu ba. Ganin kallon da yake mata Yohan ya fahimci akan ta ne kenan Adeel yazo anguwar ya tare, shi kansa yaran biyu suna birgeshi dan yana shan ganinsu idan za'a wuce dasu makaranta haka a mota. Ita dai Nimrah tazo ta gittasu a taƙaice tace musu "Good Afternoon". kawai, dan gaishe da na gaba da su koda basu sanshi ba wannan tarbiyyarsu ce. Da ƙyar Adeel ya iya controling kansa baibi bayanta ba, sai dai yace da Yohan su dakata a ƙofar gate ɗin su kira Ammar idan yana nan, dan yau bazai iya haƙuri ba sai ya shiga gidan nan duk da yaga anata shiga da fita alamar wata hidima sukeyi. Nimrah data gotasu kaɗan tana ƙoƙarin sake kiran su Teemerh dan har yanzu bataga wata alamarsu ba kuma ta fara gajiya gashi tayo nesa da gida kawai wata farar mota ta tsaya mata. Ganin motar ba wata babba bace sosai tayi tunanin su Teemerh ɗin ne, dan haka tabi ta da kallo tana ƙoƙarin kai wayar kunnenta kawai taji an fesa mata abu a fuska. A kiɗime ta ɗago numfashinta na fisga zatai magana kawai ta tafi gaba ɗaya, duhu ya mamaye mata cikin idanu, sautin motsin anguwar da ba wani mai yawa ba yay nesa da kunnenta. Daga haka bata sake sanin abinda ke faruwa ba...
Wani mai gadi dake ƙofar gate ɗin wani gida da yay facing inda Nimrah ta tsaya, sai dai motar tai blocking ɗinta dan har yana jin haushi saboda tunda Nimrah ta ɓullo suka zuba mata ido shi da abokin zamansa suna magana kawai sukaga motar tabar wajen a guje. Koda suka duba inda sukaga Nimrah kafin zuwan motar sai sukaga wayam babu komai. "Anya lafiya kuwa Zailani? Kalli fa yanda motar can ta bar wajen kuma babu yarinyar fa". Wanda aka kira Zailani ya miƙe cikin mamaki yana faɗin, "Ai ni nazata ko wanda ta sani ne. Amma gaskiyarka fa wannan gudun marasa gaskiya ne". Da wannan surutun suka tsallako titin zuwa inda Nimrah ta tsaya, sai ko ga wayar Bintu yashe a ƙasa, harda abin hannunta da mayafi alamar fita sukai. Wayar su Zailani suka ɗauka, dai-dai nan kira ya shigo. Bintu ce ta kira da wayar Feedo jin Nimrah shiru bata koma ba. Zailani na amsa wayar kafin ma yayi magana daga can Bintu ta ce, "Ninah wai har yanzu baki gansu ba ne?". Zailani yaja numfashi ya fesar, sannan cikin son fahimtar da ita yace, "Ba ita bace ba." "Kai! Waye to? Ina mai wayar? Ya akai tazo hannunka?". Kai tsaye ya bata amsa da, "Akwai fa matsala. Yanzu wata mota ta ɗauki mai wayar suka gudu da ita, shine suka yadda wayar, sai kiyi ƙoƙarin faɗa a gida azo a amshi wayar da mayafinta kuma...." Wani kalar razannanen ihu Bintu ta saka. Ihun daya dawo da hankalin kowa dake falon ɗakinsu Nimrah ɗin. Suma su Ruky dake ɗauri a gaban mirror tuni sunyi kan Bintu a hargitse. Dan sai kwarara ihu take tana faɗin, "Ninah! Ninah! Ninah". Ruƙayya ta fashe da kuka tana faɗin, "Ki gaya min miya samu Ninah ɗin dan ALLAH Bintu, wlhy zuciyata zata buga". Itama ta fashe da kuka jikinta na rawa. Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin ya cika, kowa Bintu yake tambaya dan ita keta faɗin, sunan Nimrah. Sai da Ummu tai mata tsawa da faɗin ta nutsu tai musu bayani sannan ya faɗa abinda wanda suka kira ya faɗa. Wayar Feedo aka amsa daga hannunta akai kiran layinta, kai tsaye nan ma Zailani ya amsa. Irin bayanin da yayma Bintu kuma yay musu. Hankali ya ƙara tashi, akace ya faɗi inda yake. Babu kwana-kwana ya sanar musu. Tsabar rikicewa wasu ma ko gyale babu akansu suka fito,........✍️
[12/27/2025, 12:52 PM] Zeenaran 😘: 79
........Mammah ma sai da aka biyota da takalma. Securitys ɗin wajen gate najin abinda ya faru suka watsar da plates ɗin abinci. Su Adeel sun bar wajen dan sun kira Ammar yace musu baya nan, kuma a gaban securitys ɗin nan akayi, ɗan sanin da sukaima Yohan dakan fito daga gida kullum motsa jiki ko idan zai wuce wajen aiki sukan gaisa yasa basu kawo komai a ransu ba. Kafin kace mi gayyar mutane sun zagaye su Zailani. Kamar yanda sukai bayani a waya haka suka maimaita. Jikin Mammah rawa yake sosai, dama tunda ta tashi yau gabanta ke faman faɗuwa. Sai ta barshi akan wannan taron ne maybe, da su Hajiya Hasiba sukazo kuma sai take ganin ko sunzo da wata fitina ne dan su ɓata mata taro, shiyyasa ta kwaɓi al'amarinsu cikin sauƙi tanata addu'a, ashe ga abinda ke shirin faruwa nan...
<<<<<。◕‿◕。>>>>>
A dai-dai wannan lokacin Imran da Dada na gidan Baffa ne. Tare da shi sukai sallar la'asar sukaci abincin rana. Sun sake dasa sabuwar hira da gaba ɗayanta akan al'amarin ƙasar ne sai ga Uncle Nasiru. Wannan ya ƙarama hirar armashi har lokacin la'asar da suka fita massalaci. Bayan sun dawo salla suna shirin daga nan suyi sallama da Hajjo da Baffah, sai dai da yake Baffa akwai son hira abinka da tsufa sai ya ƙara riƙesu da labarinsa. Da ƙyar ya sakesu suka fito suka barshi da Uncle Nasiru. Kai tsaye gidan nan na sirri da suka sakama suna UNIT ZERO suka nufa. A yanzu gida ne bana kai tsaye ba. Komai a cikinsa da tsari da tsaro. Suma kansu sai sunbi tsarin suke shigarsa musamman security na ƙofa da baya buɗewa sai da password. Kuma su biyu kacal suka sani. Imran ya saka Password ɗin ƙofar ta shige. Sun shiga kenan sun zauna Imran na ƙoƙarin buɗe laptop da faɗin, "Dabo ya tura min saƙo yanzu nan, idan ka basu izinin zasu ƙaraso shi da Yusuf". Kafin Dada ya bashi amsa motsin da wayarsa tayi ƙirar Samsung a karo na kusan uku kenan yasa shi jan ɗan siririn tsaki. Ajiye haɗaɗɗen pen ɗin hannunsa daya ɗauka shima saman takardar da zai yi rubutu yayi, sannan ya ɗago yana mai ɗaukar wayar. Ganin sunan Mu'azz ga miss calls ya jera masa kuma ya cigaba da kira ya sashi ɗaga wayar ya kai kunnensa a nutse, kafin ya motsa lips ɗinsa cikin dakakkiyar muryarsa dake a buɗe irin ta ainahin jaruman maza ya furta, "Kai ka iya damun mutane suna aiki ko?". Cike da girmamawa daga can muryar Mu'azz na rawa ya furta, "Dada. Dama Ninah ce ta fita wai tarar ƙawayen Bintu a waje wai wata mota ya ɗauket....." kuka ya sarƙe shi ya kasa ƙarasa faɗa. Wani irin duka zuciyar Dada keyi a cikin ƙirji. Ya dai daure cike da dakiya ya ce, "Ita kaɗai ta fita a gidan?". "Eh ita kaɗaice sai wayar Bintu......." nan ya bashi labarin duk yanda su Ruky sukai bayani akan fitar tata da abinda kuma masu gadin nan suka sanar musu. Kasa cewa komai yay, sai ya katse kiran gaba ɗaya yana furzar da iska mai nauyi. "Lafiya dai?". Imran daya maida hankali a kansa ya tambaya. Sai da ya ajiye file ɗin hannun nasa kafin ya furta, "Muje gida akwai matsala........." a taƙaice yay ma Imran bayani. Cikin ƙanƙanin lokaci Imran ya rikice. Tuni shima ya miƙe yana kashe laptop ɗin. Dada ma miƙewa yay yana sake kiran Mu'azz da saka wayar a hans free ya ajiyeta saman center table ɗin yana fara tattare takardun daya gama bazawa yanzu nan, sai dai kunnensa nakan wayar. "Dada naji ka katse ne!". "Kai kaɗai ne a gida?". "Eh, amma an kira su Uncle Ja'afar suma gasu nan tafe. Kaima tun ɗazun su Mammah ke gwada kiranka yaƙi shiga, shiyyasa hankalinmu ya ƙara tashi sosai." "Gani nan zuwa gidan". Ya faɗa yana nufar ƙofar fita. Imran yabi bayansa. Hankalisa a natuƙar tashe ya kallesa, "Haysam kodai a sanarma jami'ai ne?". "Imran karka ruɗa kanka, ko su wanene suna da dalili...." Ya faɗa dai-dai yana ƙoƙarin ficewa, dan haka shima Imran ya zabura. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan. Gaba ɗaya a compound suka same su, idan ka cire Mammah dake falo da su Ja'afar da suka ƙaraso. Amma sauran mutane da yawa ƴan suna duk suna compound, a hakama kasancewar yamma tayi mutane sun ragu sosai sai iya na jiki-jiki. Yanda ya ɓalle murfin motar ya fito. Ya isa ya sanar maka lallai kam shi ɗin tsayayyen mutum ne kuma jarumin sadaukin gaske da ko'a cikin sojojin ya isa a kirashi BARDE. Ga dai shekaru sun ja amma da alama har yanzu jinin jikin da ƙarfinsa yake gudana. Dan yanda yake taku ma kawai ya isa ka shaida asalin ZAKI ne, kuma tabbas a ƙuruciya an baza capacity iya capacity na manyan BARADA. Daga shi har Imran ɗin nasa a tsayensu suke. Badan da yawan wanda ke wajen sun san shi waye ba da sai suce kamar babu damuwa a tare da shi ma. Amma shi Imran yasan waye Zakinsa. Tarnaƙi baya bayyana kai a fuska sai a cikin zuciya da kwanji. Suna isowa wajen cike da girmamawa aka fara gaishe su, Imran ne kawai ke amsawa. Shi kam hannu kawai ya ɗaga musu ya wuce hanyar falo Agogon hannunsa ƙirar Maawad Company ya kalla, ganin lokacin sallah na sake matsowa. Tura ƙofar da shigarsa ya saka duk wanda ke a falon juyowa, sai kuma duk suka miƙe a kusan tare, banda Mammah da Gwaggo Khadijah. Kai tsaye Ja'afar da Ma'aruff suka nufosu suna musu sannu shi da Imran, shima idonsa a kansu dan haka ya jinjina musu kai. Ruƙayya dake jikin Mammah tana kuka ta taso da gudu ta shige jikinsa tana sake fashewa da kuka. "Dada Ninah ɗita, zasu cutar min da ita, dan ALLAH kuje kaida Daddy ku dawo da ita..." "Ya isa haka. Ki mata addu'a ALLAH zai kareta a duk inda take". Kai Ruky ke jinjina masa amma hawaye sun gagara tsayawa. Kama hannunta yay suka ƙarasa cikin falon sosai. Cike da girmamawa su Ammie dake falon suka shiga gaishe shi. Dan har sun gaisa da Imran ya zauna shi. Amsa musu yay batare da ya kallesu ba, sai kuma ya nufi inda Mammah take. Har ƙasa ya rissina yana gaisheta, ta amsa da kulawa da tsantsar damuwar dake shimfiɗe a fuskarta. Tashi yay ya koma a kujerar kusa da ita ya zauna, tare da riƙo hannunta cikin nashi, dai-dai nan Ammar da Bilal suma suka ƙaraso. Suma gaishe su suka yi. Imran ya amsa musu da kulawa, shi ko hankalinsa nakan Mammah yana mata magana ƙasa-ƙasa. Hawaye Mammah ta share tana jinjina masa kai. Imran ya katse shirun da faɗin, "Ya akai ta fita ita kaɗai?". Aunty Ummi ta share hawaye tana bama Imran ɗin amsa da, "Babu wanda yasan ta fita wlhy Yaya, gaba ɗayansu suke hidimar su can bayan sashen Dada, sai da aka kira la'asar suka shigo sukai wanka, dan ita tama sakko ta kawo Afrah wajen Mammah ta sake komawa, ni wlhy hankalina ya fara tashi, mi Ninah zataima wani da har zai yi kidnapping ɗinta, dole yana cikin gidan nan tun ɗazu tare da mu. Kuma ni gaskiya ina zargin......." Kallon Da Mammah ta mata ya hanata ƙarasawa. Imran daya lura da abinda Mammah tayi sai shima bai nema ƙarin bayani ba. Kallonsa ya maida kan Ruƙayya, cikin bada umarni ya ce, "Tashi zaune". Tashi tayi sosai ta zauna. Kafin ma ya tambayeta ta faɗa masa komai daya faru. Aka kira Bintu da Feedo suma. Wayar Bintu ɗin ya amsa. Yay ƴan bincike-bincikensa ya miƙa mata. Ya maida hankalin sa ga Dada dake kwance jikin kujera idanu a lumshe Mammah tai magana muryarta na nuna damuwa sosai, "Ni nama rasa wane irin tunani zanyi. Dan koma su waye suka aikata idanunsu na kanta ne shiyyasa har suka san fitar tata kamar yanda Ummi ta faɗa. Idan suka cutar min da yarinya bazan yafe musu ba, Imran kuje ku nemomin yarinyata kar ku barta ta kwana a wani waje dan ALLAH." Dada ya ƙara damƙe hannunta dake cikin nashi, sai kuma ya buɗe idanunsa dake rufe amma duk abinda ake yana saurarensu, cike da lallashi da kulawa, murya a tausashe ya ce, "Please Mammah calm down, in sha ALLAHU babu abinda zai faru..." "Muhamamd ta ina hankalina zai kwanta kuwa, kasan mi ake nufi da rashin budurwar yarinya kuwa?. Dan ALLAH kuje ku nemo min yarinyata". "In sha ALLAHU Mammah, bari muje muyi salla gata can ana kira. Kuma kuyi, kuyi mata addu'a ita tafi buƙata a yanzu kamar yanda Haysam ya faɗa". Kanta ta jinjina ma Daddy Imran mai maganar tana share hawayen da suka cika mata ido da hijjabin jikinta. Miƙewa su Ja'afar sukayi. Imran ya kalla Dada da bai motsa ba. Idan ka kallesa sai ka rantse bashi da wata damuwa, amma ya fisu jin tashin hankali, musamman ma furucin Mammah, kawai dai mazan maza ne shiyyasa ya shanye komai yanata nazarin abubuwa ne. Tare suka fita da ƙannen nasa da Imran masallaci.........✍️
[12/27/2025, 1:19 PM] Zeenaran 😘: 80
.......An idar da salla, koda suka fito a massalaci wajen su Zailani Mu'azz yay musu rakiya. Sun sameshi yana salla a ƙofar gate daga ciki, koda ya idar tasowa yay, dan yana ƙyautata zaton ƴan gidan su yarinyar nan ne da aketa masa zirga-zirga tun ɗazun, shiko bai gajiya da bada duk amsar tambayar da akai masa. Nutsuwa ya sake yi ganin masu zuwan yanzu. Ya rissina yana gaishe su dan bazai wuce sa'ar Ammar ba shi kam. Tambayoyi Imran yay masa, ya amsa kamar yanda yake amsawa kowa. Har suka gama Dada baice komai ba, sai daga ƙarshe ya tambayi kalar motar, sai kuma number ɗinta ko zai iya tunawa. "Wlhy ranka ya daɗe bazan iya cewa ga lambar jikin motar ba. Amma dai Camry ce fara mai baƙin gilashi. Da alama kuma wani abun suka hura mata ko shaƙa mata shiyyasa ko ihunta bamu ji ba sai da suka wuce, dan babu wani motsi da sukai da za'a iya zarginsu." "Ya isa". Ya faɗa a hankali yana kama hannun Mu'azz. Gida suka koma, Imran ya balbale sojojin dake gate da faɗa irin wanda basu taɓa sanin ya iya ba. Dan shi kansa Dada idanun kawai ya zuba masa, daka ƙarshe ma murmurshi ya nema suɓuce masa sai da ya zo ya kama hannunsa suka koma cikin compound. Cike da lallashi ya ce, "Relax Imran. Ko su waye irin wannan fusatar suke son gani daga garemu har mu kasa tunanin abinda ya dace. Gaskiyar Mammah kosu waye sunga fitar ta, sannan ba ɗaukarta ya kawosu ba, basu samu abinda suka shigo yi bane sai suka samu ita ta fita, shine sukai amfani da damar...." yay ɗan shiru, sai kuma ya maida hankali kan Imran daya zurfafa tunani. Iska ya ɗan furzar kaɗan. Cikin dakakkiyar muryarsa ya cigaba da faɗin, "Ina son ganin Dabo yanzun nan." Iska Imran ya ɗan furzar shima cike da gamsuwa da zantukan Dada, ya ce, "Amma mi Ummi ke son faɗa Mammah ta hana ta?". "Ina sane da batunta karka damu". Kai Imran ya jinjina, zai yi magana wayarsa ta fara vibration, dan haka yay shiru, sai kuma ya ciro wayar a aljihu yana ɗagawa ya kai kunnensa. Baiyi magana ba, dan ko tsayawa kallon lambar baiyi ba tsabar hankalinsa da tunaninsa basa jikinsa, a maimakon sallama da dariya ya fara cin karo. Hakan ya sashi janye wayar a kunensa ya danna recording sannan ya saka a hansfree har Dada yana saurare. Sai da aka gama dariyar cike da iskanci kafin a fara magana. "Imran Abbas!... Ko nace Yaron Zak-Shadow. Nasan kana kusa da shi a halin yanzu, dan haka ga saƙo zan isar kai tsaye a gareshi. Ashe shi matsoraci ne ban sani ba, irin wannan zubda girma haka, miye na ɓoye kai? TSORO NE?. Koda yake mubar ma wannan batun, awanni uku kacal da fara wasan har kun fara kai-kawo kuna cikama mutane kunne da ihu yannn!! Yannnn!!. Uhhmm! Koda yake banga laifinsa ba, dolene duk wani lafiyayyen namiji ya ruɗe akan wannan ƴar shilar matar tasa. Ƙyau iya ƙyau, ga jikin nata kuwa yay mata ɗas tamkar an zanata a takarda, kasan irin waɗan nan ƴan shilar da daɗi na musamm....." A tsawace Imran ya katse shi da faɗin, "Kai tsinanne, ka kiyayi wasa da GOBARAR JEJI, domin idan ta tashi zatai maka mummunar ƙuna ne da ko suffarka ta mutum mai halayyar dabbobi baza'a shaida ba!". Tamkar Imran ya karanta abinda ke zuciyar Dada ne dake jingine jikin mota ya wani lumshe idanunsa. Sai wani kalar kaɗa yatsun hannunsa na dama yake. Hakan kuma na nufin zuciyar mazan fama tana a maƙoshi... Shi kansa mutumin sai da yaji razani daga muryar Imran dama kalaman kansu, dan bai taɓa tunanin Imran nada zafi haka ba. Amma sai ya danne cike da raunin wayo ya ce, "Oh oh! Nayi shiru! Nayi shiru! Kawai nima naga ya dace ne na yaba halittar UBANGIJI ne. Amma shike nan! Shike nan chapter closed. To amma shi ubangidan naka tsoron magana yake ji daya kasa magana sai kai? Koda yake nasan ya zama ɗan wasan ɓuya ne, to ga saƙo a faɗa masa. Nasan yana son ganin GUDAN JININSA daya ɗauki tsawon shekaru yana nema ido rufe, na tabbatar kuma akan ƴar shilar tasa ya ɗora samun cikar wannan burin ko? Kaga ko zai so ta dawo garesa hankali kwance cikin ƙoshin lafiya. To komai mai sauƙi ne, buƙata ce ɗaya rak muke da ita sai mu samar da hakan mu kuma a gareku. Ka janye yaranka dake ƙofar yamma na awa ashirin da huɗu kacal. Mu da kammu zamu maido maku matar ubangidanka a inda muka ɗauketa....." "Kai ɗin banza..." Babu wanda bai zabura ba a wajen dan su Ma'aruff ma sun fito babu jimawa. Yanda ya faɗi (Kai ɗin banza...) ɗin da doka glass ɗin motar dake gefensu har sai da glass ɗin ya tsage. Da sauri Imran ya ajiye wayar ya riƙe hannun nasa da jini ya wanke yatsun alamar yaji ciwo. Daga ta cikin wayar da suka zata Imran ne yay maganar aka furta, "Okay! Ashe kuwa taurin kanka zai sake maimaita maka tarihin daya shuɗe a baya, tare da tukuycin rasa matar oganka da ƴarka dan itama gab take da zuwa hannun mu. Na kuma dawo naima waɗan nan zaratan samarin ƙannen nasa tsinci ɗai-ɗaya, na rufe tarihinku da waɗanan tsoffin guda huɗu. Awa ashirin da huɗu!!". Ya faɗa yana yanke wayar gaba ɗaya yana dariyar iskanci. Hannun Imran kawai Dada ya rimtse a cikin hannunsa da masifar ƙarfi, hakama idanunsa a rufe suke ruff. Sai da Imran ya dinga faɗin, "Haysam calm down, relax, relax please".
<<%>><<%>><<%>>
Da baya-da-baya Malam Buba ya dinga barin inda yake laɓe. Dan yau ya maƙale a gidan har akai magriba bai wuce ba. Duk da dai dama yakan kai hakan wani lokacin. Yau ɗin kuma rarumar rashin Nimrah ta zaunar da shi. Da farko hankalinsa a kwance yake da tunanin aikin Dagger ne. Sai dai yanzu kiran da akaima Imran ya sashi shan jinin jikinsa. Duk hatsabibancin Dagger yasan bazai kira Imran a waya ba. Musamman yasan Zak-Shadow na nan. Tashi wayar ya ciro bayan ya shiga bayin su yay kiran Dagger. Kamar yanda ya saba ya amsa masa, sai dai ko gaisuwa bai bari ma sunyi ba ya ce, "Oga Uwa na hannunka ne?". Dagger dake faman busa sigari saboda haushin Nimrah data raina masa hankali tun ɗazun yake jiran kiranta shiru yaja tsaki. "Mtsoww! Yaushe ma na ganta da har zata kasance a hannuna. Yarinyar nan fa ƴar rainin hankali ce, na fahimci akwai abinda take ƙullawa...." Cikin matuƙar kiɗimewa Mole yace, "Ban gane ba, oga anfa ɗauke uwa ɗazun da la'asar yanzu haka hankalin ƴan gidan duk a tashe yake. Nayi zaton kaine ka ɗauketa ma shiyyasa naketa nemanka wayar bai shiga ba. Sai yanzu da aka kira Imran naji mai maganar ba muryarka ba dan a amsa kuwwa suka saka, ni kuma ina laɓe a bayan mota. Sannan kalmar MATARSA da suka kira uwa da ita ya sake tabbatar min bakai ɗin bane, na kuma sake shiga ruɗani......" "MATARSA?!!". "Tabbas haka naji mai kiran wayar ya faɗa." Wata shegiyar ashariya Dagger ya lailayo ya dire yana miƙewa. "Eh lallai wannan mutumin mutuwa yake so da gaske. Shi tsohon nan ne zai ce Nimrah matarsa?". "Bafa shi ya faɗa ba, wanda ya kira waya ne ya faɗa....." "To shi ya musa zancen ne?". "A'a gaskiya, ni yanzu ba wannan kaɗai bane tashin hankalina. Sanin waye ya ɗauki min Uwa. Oga wlhy Naja'atu itace rayuwata." "Nima itace rayuwar tawa ai!!...." Dagger ya faɗa cikin ƙarajin da dole Malam Buba ya yanke wayar. Gaba ɗaya ji yake duniya na juya masa ma, kansa kuwa kamar ana buga masa ƙusoshi a ciki.....
★★★
Ba Malam Buba ne a ƙaulani kawai ba. Shima Sanda a cikin irin wannan yanayin yake. Dan shima dai kamar yanda Malam Buba yaji komai tunda a compound suke shima yaji. Jiki na rawa ya nufi bayan ɗakinsu jikin ɗakin Gen... Da Nimrah ke maƙalewa idan zatai waya shima ya shiga neman ogansa. Yana ɗagawa ya zayyane masa abinda ke faruwa. Kafin shima cikin tuhuma ya ce, "Ko kai ne ka ɗauke ta?". "Kamar ya ni? Wace magana kake haka? Ni a kanta nake wasana ko akan Haysam. Sannan ma wannan ƴar yarinyar ce MATARSA? Ina waccan to?". "Nima batun matar tasa da aka ce ya bani mamaki. Matarsa kuma naga ta dawo gidan yau, banama tunanin ya sani, ko kuma wannan al'amari ne ya kiɗima shi. Dan gaba ɗaya fa hankalin gidan a tashe yake. Kasan da yarinyar da Ruƙayyan nan sune zuciyar gidan. Kodai wanda take yawan waya da shi ne ya sace ta?". "Tabɗi jan yau naji abinda yafi ƙarfin kaina, amma sai na ci uban Almu kuwa. Ya akai bai taɓa kawo min wannan labarin ba? Wannan fa shine tirƙa-tirƙa". "Ta gasken gaske kuwa. Yanzu miye abinyi?......."
★★★
Acan bayan sashen su Bilal da babu kowa a ciki wata ce cikin irin wannan ruɗanin. Ita tana ta faman neman layin nata ogan amma yaƙi shiga. Ga labari tana son isar masa na abinda ke faruwa. Amma fin kira ɗari wayarsa na saka mata busy, daga ƙarshe dai ta yanke shawarar rubuta text message ta tura masa, a ranta tana addu'a da fatan ALLAH yasa ya gani da wuri. Dan wannan al'amari ya matuƙar rikita lissafinta. Musamman batun kasancewar Nimrah matar Dada. Bata taɓa jin maganar datai mata bazata ba a tsahon rayuwarta irin yau ɗin nan. Dan mutanen gidan basu taɓa yin zancen ba.....✍️
ALHAMDULLAHI.
BOOK 3 LOADING.......
ƘARSHEN WASA. ƘARSHEN YAƘI. TUSHEN SOYAYYA.
Su waye da wannan aika-aikar? Dan a wannan gaɓar kowa abin zargi ne.
Kungiyar duhu? First Lady da mijita?. Nabeeha da uwarta? Mole? Sanda? Shugaban dan sandan farin kaya? Shugabannin makaranta? Kai harma da wanda ban lissafo ba.
Ga Nabeeha ta dawo. Dada zai amsheta kuwa?
Batun aure ya fasu. Kokwanton Nimrah ya ƙare.
Karna cikaku da zance. BOOK 3 ya haɗa komai da kuke buƙata, harma fiye da... Dan anan komai zai baje kansa-da-kansa...🥰🥰🥰❤️🔥🤸. Kumuje zuwa kawai ba wasa🥱🏃🏼♀️🏃🏼♀️
Bilkisu Ibrahim Musa. (bilyn Abdull ce🥰🥰) C-27/12/2025.
Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa.
Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃
Akwai VIP Telegram 💃
(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)
Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇
(2k)
9032345899 Moniepoint MFB BILKISU MUSA IBRAHIM
KATI MTN (2k) 09032345899
Shaidar biya: 👇 Telegram Number 09032345899
Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇.
(1,500 CFA) +227 98 94 12 81 My NITA
Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram
Shaidar biya👇
Whatsapp number +227 98 94 12 81
AREWAPEN (Vvip) Chapters & Audio @BilynAbdull
Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂.
Whatsapp Number +234 805 568 7449
MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA
WhatsApp Number 👇 +234 805 568 7449 Telegram Number👇 +234 903 234 5899
TELEGRAM GROUP
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
WHATSAPP CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
TIKTOK
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏