Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 26
Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 26: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 26. "Nima ina neman yafiyarki angel, duk…
3,362 words
"Nima ina neman yafiyarki angel, duk da bana ɗaya daga cikin masu ƙuntata maki" raba jikinsu su ka yi daga cikin na juna, kowannansu idanuwanshi ya kaɗa yayi ja saboda kukan da suka sha, still hawayen basu daina sintiri saman faces ɗinsu ba,
Kallon javed su ka yi dake a tsaye, Shima da alamun nadama atattare da shi, cikin sanyin murya angel tace"basai kun nemi yafiya ta ba, saboda ba laifinku bane, nayi maku uziri tuntuni'
Ƙarasa shigowa Cikin toilet area ɗin yayi ya tsaya a kusa da su, sannan yace"Angel, muna so mu tabbatar da gaskiya, a tsakanin ki da tsohuwa, sai dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da zamu shaida hakan," yakai ƙarshen maganar idon shi akan fuskarta,
"Ku bani lokaci, bi'iznillahi Zan kawo maku ƙwaƙƙwarar hujjar da zan wanke kaina, ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA BA GIDAN MARAYU BANE, SANNAN ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA AKWAI ALLAH WANDA YA HALICCE KU, BA DAGA SAMA KUKA FAƊO BA,"
Baƙaramin daɗin maganarta su ka ji ba, batool ta ruƙo hannayen angel biyu acikin nata, cikin natsuwa ta soma magana"Ina yi maki fatan nasara Angel, muna atare dake,"
Angel tace"Bana so ku nuna mun shirya agaban tsohuwa, Ku cigaba da pretending cewa Kuna goyan bayanta baku atare dani, ta hakanne zan samu damar bayyanar maku da gaskiya,'
Atare suka haɗa baki wurin amsa mata da toh, Kallon azeeza ta yi wadda ke atsaye tana jinsu amma bata iya ganinsu,
"Mu koma Ciki mu kwanta, Azeeza ta gaji da tsayuwa" ta ruƙo hannun azeeza, Batool da javed su ka yi gaba a cikin ɗakin suka yi ma juna sallama, Kowa ya wuce gadonshi, sai da tafara kai azeeza saman gadonta ta kwanta ta lullu6eta da bargo, kafin Ta koma nata gadon, daga ƙasa ta ajiye fitilar hannunta, ta haye saman mattress ɗin taja bargo ta lullu6e jikinta zuwa saitin neck ɗinta, kasa runtsawa tayi, ɗan juyawa ta ɗanyi tare dakai idanuwanta saman shimfiɗar Danish, why Har yanzu ba a dawo da shi ba? Allah yasa dai ba jikin nashi bane yayi tsauri sosai ba, duk da babu sabo a tsakanin mu, naji na yi kewarsa sosai, inaso na sake ganin danish, Fatana Allah yasa adawo dashi, kada maganar batool ta tabbata na cewa duk wanda aka ɗauka ba'a dawowa da shi ya tafi kenan har abada! To wai ina ake kai su? Idan suna araye meyasa ba a ta6a dawo da su ba? Ni dai a iya sanina mutuwa ce kaɗai idan akayi ta ba'a dawowa!!!!!
Ɗaura hannunta na dama tayi asaman goshin ta zagoyo da shi, idanuwanta na fuskantar ceilling,
"Menene ma'anar Gidan Kurkukun ƙaddara? A iya sanina Gidan Kurkuku Yana nufin Gidan Gyara hali, Amma wannan kurkukun meyasa last name ɗinshi Ya ƙare da ƙaddara! Dole ya kasance ɗaya Cikin biyu, Kodai kyakkyawar ƙaddara ko kuma mummuna, ' lumshe idanuwanta ta yi a hankali ta ware su, Zuciyarta Cike fal da tunani, Tun lokacin da daddynta ya gudo da ita daga Gidansu, Take lissafin kwanaki, bata ta6a bari lissafi ya kwace mata ba, ko babu calender tana iya hasashen Yau nawa ga wata, ku ma ta canka dai dai,
Tana Cikin Yin tufka da warwara, Tajiyo Takun Tafiyar Mutun, Tunkafin ma takai idonta kan wanda ya shigo ɗakin nasu, Ta yi hasashen tsohuwa ce, daga kwance ta wurga eye balls dinta kan tsohuwa dake shigowa Cikin ɗakin, Sanye cikin shigarta, ta gado jar doguwar riga me hula, hannunta ruƙe da kaskon turaren wuta, zagaye ɗakin ta soma Yi tana kora hayaƙin ta ko'ina, murmushin takaici angel ta saki, yau ta ƙudiri aniyar sai tayi mata magana ga da ga, batare da jin tsoro ba, ta mike tare da saukowa daga saman gadonta, Cikin sanɗa take tafiya har ta ƙaraso bayan tsohuwa ta Cigaba da binta suna tafiya atare, batare da tsohuwa ta ankara ba, kasa kunne angel tayi tana sauraran ɗalasiman da take karantawa, kai daga jin yadda take Karanto su zaka shaida cewa ba abun arziƙi bane, wani mugun abunne take ƙulla masu,
"ƴar nan Kina tunanin bansan Kina bin bayana bane"? Tsohuwace tayi maganar, batare da ta juyo ta kalli bayanta,
Koda angel taji maganarta, bata ji wani fargaba ba, saima ƙwarin gwiwa da ta samu na cewa" nasan kinsan ina bin bayanki mana, Taya ki aiki nake yi, naga kina ta wahala ke kaɗai, Me zai hana yau Ki bani Kaskon turaren wutar In rage maki aiki"? juyowa tsohuwa tayi suka fuskanci juna ita da angel, Wani irin balagaggen murmushi ne ɗauke akan fuskarta tsohuwa,
Ɗaure fuska angel tayi tamau ba fara'a ko misƙala zarratin,
"Bibiyata kike Yi kenan? Da alama har yanzu baki daddara ba, Ina mai baki shawarar Ki ajiye makaman yaƙin ki, Ki yi rayuwarki tamkar salihar dabba, ki ajiye wannan Girman kan naki, da taurin kan nan da kafiya, Muyi rayuwa Cikin salama,' takai ƙarshen maganar tana washe wawulan bakinta,
Still angel bata tanka mata ba, Jira take ta kammala Suratan nata marasa kan gado,
"Ƴata faɗa da aljani ba riba, Ko har yanzu Kina tunanin zaki Ci galaba akaina ne eye? Tsabar takaici Ji take kamar ta shaƙo wuyan matar, mummunar banxa kawai, ta ambaci hakan acikim zuciyarta, a fili kuma tace"tun yaushe kuma? Cin galaba akanki tuni na fara, bari na faɗa maki abunda kike tunanin bansani ba,' ƙura mata kwarkwararrun idanuwanta tsohuwa tayi tana jiran jin me zata ce, "Kafin na faɗa maki irin nasarar dana fara samu akanki, zan fara faɗa maki babban kuskuran da kuka tabka," fuskarta ɗauke da murmushi takai ƙarshen maganar, Tsohuwa dai tayi kasaƙe tana kallonta,
A tsanake angel taci gaba da cewa"Kuskuren kuwa shine, ɗauko ni da ku kayi zuwa Cikin gidan Kurkukun nan, ganganci ne mutun ya ɗauko ajalinsa ya raine shi da hannunsa, ada ina tunanin meyasa na kasance acikin gidan kurkukun ƙaddara? Amma yanzu na samu amsar tambayata, inaji araina Ba hakanan Allah ya ƙaddara mun rayuwa acikin gidan kurkukun nan ba, babu shakka Nice zanyi silar tarwatsewar........" bata kai ƙarshen maganar ba, Sakamakon wata ƴar iskar dariya da tsohuwa ta fashe da ita, Ta wage wawake bakinta, Haƙoran nan jawur dasu, kasancewar angel na a kusa da ita, Da sauri ta kawar da kanta gefe Jin ƙarnin Jini na fita daga cikin bakin tsohuwa, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai zuciyarta ta shiga ruɗani, gaba ɗaya ta rikice tana zare ido, fuskarta ɗauke da tsantsar mamaki da aljabi ta ɗago tana kallon tsohuwa a lokacin ta dakata da yin dariyar,
Da shaƙaƙƙiyar Miryarta ta tsoffi tace"Your dream will neva come true angel, Wasiƙar jaki ce kike saƙawa aranki, wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, har yanzu akwai sauran kuruciya atattare dake, shiyasa nake yi maki uziri, bakisan komai game da gidan kurkukun ƙaddara ba, ki kalli ginin da kyau, Tsohon ginine wanda tun kafin zuwana duniya aka ƙirƙire shi,"
Angel fa ta shiga ruɗani, Idanuwanta azazzare take kallon tsohuwa, sama sama take fahimtar zancenta, wata irin narkakkiyar zufa ce ta shiga tsastsafo mata ta ko'ina ajikinta, saman goshinta duk ya jiƙe da zufa, bakomai ya tsara mata arai ba, face wannan ƙarnin Jinin da taji abakin tsohuwa,
"Gidan Kurkukun ƙaddara, Baida ƙopa a lokacin da aka Ginasa, Kurman ginine, Ke Ko mutuwa bata isa ta fidda gawar mutun daga Cikinsa ba idan har ya shiga Cikinsa, Duk wanda muka ƙaddara ma rayuwa acikinsa, Anan zai rayu Anan kuma zai mutu, Ƴar nan ta ina kike tunanin zaki iya tarwatsa Gidan kurkukun ƙaddara? Ta yi mata tambayar tana sakin shu'umin murmushi,
Tuntsirewa Angel tayi da dariyar yaƙe, tana girgiza kai, hada dafe Ciki, tsohuwa ta zuba mata ido Itama da murmushi akan fuskarta,
"Halan wani shaƙiyancin ne zaki yi mun shine kike dariya" ? Tayi tambayar tana kallon angel,
Dakatawa tayi da yin dariyar, Tare da sanya hannu tana kore hayaƙin kaskon turaren wutar dake a hannun tsohuwa daya takura mata,
Sai da ta daidaita natsuwarta tukunna tace"Ubangijin mu Allah subhanahu wata'ala, mamallakin Komai da kowa, mahaliccin Maginin gidan kurkukun ƙaddara da kuma tsohuwa ita kanta dake agabana, da iznin shi komai ke wakana, wanda idan yaso a yanzu haka da muke atsaye sai ki fadi ki mace shikenan, An shafe babinki rayuwarki, duk wani ƙarfin iko da kike taƙama dashi kinga ya qare, Zaki je ki fuskanci reality, Allah kenan da shi na dogara, Kuma shi zai bani Ikon tarwatsa ku, wai ke har kina da bakin cewa duk wanda kuka kaddara ma rayuwa acikinsa Bai isa ya fita ba? Anan zaiyi rayuwa anan zai mutu? Ke wacece? Kin manta ta ƙofar da kika bi kika zo duniya? Kin manta yadda aka halicce ki tun daga ɗigon maniya har zuwa gudan jini? Ke kanki fa baiwace ta Allah ƙasƙantacciya butulu, waɗanda ma suka fiki hatsabibanci irinsu fir'auna Yanzu suna Ina?
Jin wannan tambayar ta angel yasa Walwalar dake akan fuskar tsohuwa ta gushe zuwa tsananin fushi da 6acin rai,
"Dama nasan bazaki bani amsa ba, ƙarya ta ƙare, Idan Allah yaso arana ɗaya dake da kurkukun duka zai shafe babinku, Shi kaɗai yake da iko akan komai, Bansan A ina kika samu kwarin gwiwar Yin magana a gadarance ba, akwai fa ranar da wannan sihirin naki bazai ta6a taimakon ki ba,
Zaro ido tsohuwa ta yi tana kallonta, Cike da mamakin Jin ta ambaci cewa tana da sihiri taya akai tasan hakan? Bata kai karshen zancen zucin nata ba Angel tace"Kina mamaki ne? Ta yi tambayar fuskarta ɗauke da murmushi, Kafin taci gaba da cewa"Ɗaya daga Cikin nasarorin da na fara samu kenan, Kina amfani da sihiri wurin sarrafa Tunanin waɗannan bayin Allah, Kun Hana ayi ibada acikin gidan kurkukun ƙaddara saboda Itace Lagwanku, wannan dalilin yasa Duk wani prisoner dake rayuwa acikinsa, kuka hana shi yin addini, Hakan na nufin ku kanku Kuna tsoron Allah saboda kunsan cewa shi kaɗaine zai Iya kawo ƙarshen ku, shiyasa kuke gudun dun wani abu daya shafi addini musulunci, sai dai kunyi abanza, domin kuwa kome kuke Yi Allah yana kallonku, dama ce na ɗan lokaci ƙanƙani, "
Ajiyar zuciya ta sauke kafin taci gaba da cewa"Ke kanki kin fara Jin shakkata, dalilin dayasa kuwa nace haka, Saboda kinga addu'ar da nake Yi masu tafara tasiri ajikinsu, Har sun fara gaddama dake, Wannan dalilin ne yasa Kika Koma Yi masu hayaƙin sihiri domin juye tunaninsu, sai dai kash aduk Lokacin da ki ka turara masu hayaƙin sihiri ni kuma ina bin kowani gado In tottofe su da addu'a, wannan yasa kike jin haushina saboda ina ruguza maki shiri, sabo tsabar makirci kikayi ƙokarin cusa masu tsanata acikin zuciyoyinsu, duk don saboda kisa in karaya, shima kinyi abanza,"
yadda take magana babu tsoro tamkar zata shaƙo wuyan tsohuwa, daurewa kawai take yi tana yin magana da ita, saboda munin fuskar matar, Ƙyamarta take Ji, fuska duk ta lalace ta ta6ar6are,
"I ave alot to say, Amma bazan Iya jure Yin magana mai tsayi dake ba, saboda 6ata lokacine yin magana da matacciyar zuciya," fuskar tsohuwa babu annuri take kallon angel, Kaskon turaren wutar dake a hannunta tuni garwashin ya mutu, hayaƙin ya daina wanzuwa
Dogon tsoki Angel taja, tare da juyawa zata je ta kwanta, har ta kusa kaiwa bakin gadonta, ta ɗan dakata da yin tafiyar ta waiwayo ta kalli tsohuwa dake a tsaye ƙiƙam uwa saƙago, ta kafe ta da waɗannan kwartayen idanuwan nata,
"A'uzubillahi minasshaiɗanirra'jim, Aniyarki ta biki, Kuma ina nan ina zuba ido, Gobe adawo mana da ɗan uwan mu danish, idan ba haka ba komai zan iya aikatawa wlh, zan nuna maki hatsabibanci na, zan addabi rayuwarki,
"takai ƙarshen maganar tare da jefa mata harara ta murguɗa mata baki, gyaɗa kai tsohuwa tayi Batare da ta furta wata kalma ba, ta dogara sandarta zuwa kopar ɗakinta, ta buɗe ta shige tare da jan ƙopa, tafiyarta keda wuya angel tabi kowani sashe na ɗakin ta tottofe shi da addu'o'in neman tsari kamar yadda ta saba, ta kuma bi kowani gado tun daga kan gadon su Hanna duk ta wanke su da addu'a, bayan ta kammata ta koma saman gadonta, A tsakiyar gadon ta zauna tare da ɗaga hannayenta tana addu'a, akan Allah yabata Ikon yin nasara akan miyagun mutanan nan, Allah kuma Ya tsare mata daddynta aduk inda yake, idan kuma Ya mutu Allah ya kai rahama ƙabarinshi, Hatta danish sai da ta yi ma shi addu'a, Ta kuma roƙi Allah daya kawo masu ɗaukin fita daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara, Ta jima tana yin addu'o'i kafin daga ƙarshen ta janyo bargonta, ta lullu6a ma Jikinta,
Cikin ƙanƙanin Lokaci Bacci Yayi awon gaba da ita, can cikin dare wata irin zufa ta soma wanke fuskarta, wani irin matsanancin zafi ta ko'ina ajikinta, mutsu mutsu ta dinga yi tana matse idanuwanta, yayin da ta dunƙule hannayenta, tamkar ƴar dabbe, duk ta hargitsa shimfiɗarta, da alama mafarki take yi, ciccije la66anta tayi har sai da ta fasa su, ƙasa ƙasa take karanta duk wata addu'a da tazo mata a cikin kanta, a daren ranar bata yi bacci mai daɗi ba,
Tun daga saman gado Ta mirgino ta ƙundumo ƙasa ta daki floor ɗin sosai, har cikin kanta taji zafin buguwar da ta yi, Lokaci ɗaya ta farka kamar wadda Aka tsakura ta ware manyan gray eyes ɗinta tana kallon ceilling, Sai faman haki take yi kamar wadda ta yi gudun famfalaƙi,
Ƙoƙarin tariyo abunda tayi mafarki akanshi tayi, A cikin mafarkinta wasu baƙaƙen Maguna Guda uku sun farmake ta asaman gadonta, Faɗa ya kaure a tsakaninsu, Ta dinga yakushinsu tana kai masu cizo suma suna kokarin yakushinta sai dai Allah bai basu nasara ba, a ƙarshen itace taci galaba akansu ta yi masu jina jina sukai ta kuka, har suka sauko daga saman gadonta suka watsa aguje,
Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, lokaci ɗaya ta saki murmushi har dimples ɗinta suka lotsa, da alama taji daɗin damben da tayi acikin mafarkinta, bata motsa daga kwancen da take a ƙasa ba, hada bargonta da pillow ɗinta duka suna rungume a hannuwanta, Suma hadasu akayi artabun,
"Gidan kurkukun ƙaddara Ba gidan marayu bane Gidan Matsafa ne" yanzu ta ƙara tabbatar da zarginta akan cewa Gidan Mallakin Matsafa ne, Sai dai batasan wasu kalar matsafa bane, masu shan Jini, ko kuwa masu Cin naman mutun, akwai sauran rina akaba, dole sai ta bi asannu tukunna zata gano ainihin me waɗannan matsafan suke aiwatarwa da mutane ,
Ta yi zurfin acikin tunaninta muryar batool ta katse ta"Sister lafiya? Me kike yi a ƙasa"? Wurga idonta tayi akan batool dake A zuƙunne gabanta, ba tasan Lokacin da tazo wurinta ba,
"Sai faman sakin murmushi kike Yi kamar wadda akayiwa albishir da mukullin fita daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara" fashewa angel tayi da dariya Jin abunda batool tace, haƙiƙa maganarta ba ƙaramin daɗi tayi mata ba, wannan babban albishiri ne kuwa mutun ya mallaki mukullin fita daga kurkukun ƙaddara, Har tafara ayyana irin shagalin da zatayi aranar da tabar gidan kurkukun nan, zatayi farin Cikin da bazata Iya misalta shi ba,
"Faɗamun me kike ma dariya? Wata'ƙil nima ya sanya ni farin Ciki"acewar batool fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar,
Mikewa zaune angel tayi still pillown ta na rungume a hannunta, sumar kanta duk ta tarwatse saman bayanta, hada side by side na fuskarta, hannu batool takai tare da ruƙo gashin kanta tana fadin"yakamata In rage maki sumar kannan naki, idan ba haka ba nan gaba idan kina tafiya sumar zata dinga taɗiyo ƙafarki ne," dariya suka saki atare,
Angel tace"baki lura gashin ki yafi nawa yawa ba? Kalli Fa yadda sumar kanki ta Cika ko'ina kamar kin kifa kwando asaman kan naki, Gashin duk ya nannaɗe kamar taliyar indomie,"
Ta6e Baki batool tayi ta ɗan kai idonta kan sumar kannata, ita kanta tsoron kallon yawan sumar ta take Yi, saboda yadda take ha66aka,
"Kwanan nan zan samu abunda zan datse ta, Don ni banga amfani gashin kaina ba," acewar batool,
Angel tace"da ace a waje kike rayuwa da baki faɗi hakan ba, saboda gashi abun ado ne ga ƴa mace, yana ƙara ƙawata kyan mace sosai, kuma yana jan hankali mutane, idan Allah yasa muna da rabon fita daga Cikin kurkukun nan, ke da kanki zaki shaida abunda nake faɗa maki, mutane ma rububinki zasu dinga yi saboda kyanki,"
Duk wannan maganganun da angel ke yi batool fa bata fahimtarta, domin kuwa batasan Ya kyan fuskarta ya ke ba, tun da Allah ya halicce ta Bata ta6a kallon madubi ba, tadai san kyau a fuskar danish da kuma fuskokin su Azeeza, Amma Ita batasan Ya kamanninta suke ba, kamar yarda suma su Azeezan basu ta6a kallon madubi ba, Basusan Ya suffarsu take ba, Sai an kwatanta masu,
"Angel nifa bansan Ya ake ganin kyau na ba, Saboda bansan ta wace hanya zan ga fuska ta ba," tayi maganar tana kallon angel,
Tuntsirewa angel tayi da dariya Hada dafe Ciki, Batool ta daure fuska"stop laughing at me bana son wasa fa " daƙyar angel ta samu ta dakata da yin dariyar, A tsanake Ta kalli batool tana zayyana mata kyawun fuskarta,
"Farko dai ke doguwace, fara sol son kowa ƙin wanda ya rasa, idanuwanki Dara dara dasu manya farare ƙyal launin su brown colour, ga dogon hanci, tausasan la66anki brownish colour ne yadda kasan yankan tumatur saboda tsabar kyansu, ke fa ɗin kyakkyawa ce ajin farko, tun da angel ta soma magana batool ta saki baki galala tana kallonta, Tsabar farin Ciki ya hana ta furta komai, Daɗi take Ji ana zayyana mata irin kyanta,
Wani abu da angel bata sani ba, tun lokacin da Ta soma zayyana kyan fuskar Batool, Gaba ɗaya su Hanna dasu azeeza, rubina Hibba, eve, yasmin, da deeja da parveen Kaf ɗinsu Suna a zuƙunna kewaye dasu, Jira suke ta kammala Zayyana ma Batool kyawun fuskarta suma ta faɗa masu Ya nasu Kyan yake, Tofa angel ta zama Mirror,
Baƙaramin wahalar da ita su ka yi ba, Sai da tagama da matan sai ga Javed da mubeen, hada naufal suma suka tasa ta gaba sai ta faɗa masu Ya kyawun fuskarsu yake, har wani jiri take gani acikin idanuwanta saboda tsabar gajiya, Ga gunwa tana ji sunƙi bari ko toilet ta shiga ta watsa ruwa ajikinta, sai daɗi suke ji an faɗa masu cewa su kyawawane, Sai da ta kammala Javed Yace"Yanzu ki faɗa mana waye yafi kowa kyau acikin mu"? Suka tsareta da ido suna jira su ji amsar da zata basu, Kowa sai gyara sumar kanshi yake yi don ta ce shine yafi kyau,
"Zan fada maku tsakani da Allah, wanda yafi kowa kyau acikin ku, Baya atare daku yanzu haka," gaba ɗaya taga sun kwashe da dariya, Da mamaki akan fuskarta tace"meya baku dariya" Mubeen yace"saboda Kin canka dai dai, Wannan wanda baya atare damu shine yafi kowa kyau acikin mu,"
Murmushin gefen fuska angel tasaki tare da ɗaura idonta kan batool tace"Amma duk da kyanshi, Batool itace zata zo na ɗaya saboda Ita macace, bayan batool kuma sai Azeeza kodan saboda wannan kyakkyawan murmushin nata, Daga azeeza kuma sai Javed...." duk wanda ta ambaci sunanshi sai taga yanata washe baki
"To ki faɗa mana wanene Yafi kowa muni Acikin mu"?
Batare data yanke shawara da zuciyarta ta basu amsa da cewa"Haris ne, Cikin mata Kuma deeja ce"
Deeja dake atsaye Ta ruƙe qugu tuni ta tur6une fuska, jin an kirata da mummuna, dama a ƙule take da angel ganin yadda sauran Ƴan uwanta duk suka Saki jiki da ita, bayan irin Ƙarairakin da tayi masu, ita kanta angel tayi mamakin zuwan da su ka yi wurinta, bayan Irin juya mata bayan da su kayi amma yau sai gashi sun sake da ita, duk da tasan Zaiyi wuya ayanzu su yarda da ita, kamar yadda suka yarda da ita a lokacin Baya,
Duk wannan abun dake faruwa Haris Baya acikin ɗakin bai jima da farkawa ba, Ya wuce Toilet, baisan wainar da suke toyawa ba,
"Kowa ya ta shi yaje ya shiga wanka, ya tsarkake jikin shi, kafin giants su kawo mana breakfast ɗin mu," batool ce tayi masu magana, ɗaya bayan ɗaya kowa ya mike Ya nufi Toilet,
Lokacin da suka kammala Yin wanka, bada jimawa ba, Giants Suka kawo masu Abinci, Yau Hada Chocolate Cake aka kawo masu Kowa ɗaya, ba ƙaramin dadi suka ji ba, Saboda suna matuƙar son cake,