Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 29
Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 29: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 29. Ruƙo hannayen aneelerh tayi acikin…
3,353 words
Ruƙo hannayen aneelerh tayi acikin nata"Aneelerh, kodai zaki ɗauki shawarar mahaifinki ne, ki koma abuja gidan Uncle ɗinki da zama? ina ganin kamar in kina acan zaki fi samun sauƙi acikin zuciyarki, amma zamanki anan sam babu cigaba," girgiza kai aneelerh tayi yi"Mami dan Allah kudaina yi mun maganar komawa gidan uncle da zama, ya kuke so nayi da rai na? A halin da nake Ciki, ku kaɗai nake gani inji sanyi acikin raina, indai nayi nesa da ku, bazan ta6a samun natsuwa ba" takai karshen maganar fuskarta a yamutse,
Mami ta fahimci halin da aneelerh take Ciki, dama tasan zaiyi wuya ta amince tayi nesa da su,
"Shikenan, bazan ƙara yi maki zancen komawa can ɗin ba, ina fata hakan yayi maki" jinjina kai aneelerh tayi alamar eh,
"Yanzu ki tashi ki shiga toilet ki wanke fuskarki sarkin kuka, Allah idan baki daina ba sai yaronki ya raina ki, ga shi nan yanzu shima ya fara zama irin ki, ko kallon banza mutun yayi mashi sai ya fara ta6e baki zaiyi ma mutane kuka," murmushi gefen fuska aneelerh ta saki, tare da juyawa tana kallon junaid dake kwance, har lokacin wuyanshi na sanye da cazbaharta daya sanya,
Dariya mami tayi don ita sai lokacin ta lura da cazbahar da ke sanye a wuyan junaid, "Wayaga ɗan Sarkin malamai," dariya sukayi atare, gwanin ban sha'awa,
Miƙewa mommy tayi"xan koma dining ki same ni acan ina jiranku,"
Amsa mata tayi da toh mami, kafin ta sauko daga saman gadon ta shige toilet, after some minutes ta fito tana gyara doguwar rigar material ɗin dake ajikinta,'
Har lokacin Junaid Bai farka ba, tasan dole yana jin yunwa, hannu takai tare da ɗauko shi, aikuwa kamar ta tsunkule shi, Yaita kuka yana fadin shi bai gaji da baccin ba, tana dariya tace"Am sorry My baby Boy, breakfast zamuyi da zarar mun kammala, Sai ka koma baccin ka, daƙyar ta samu ta shawo kanshi Ya daina kuka, Toilet ta shiga da shi, ta yi mashi wanka, ta fito dashi sa6e saman kafaɗarta, ta nado shi Cikin towel, Gyara mashi Jikin shi tayi kafin ta sanya mashi riga da wando, rungume dashi ta fito ta nufi dining table, Mami ta hango a zaune tana Shan tea, Kujera taja ta zauna suna fuskantar juna da mami tace"ɗazu ban gaishe ki ba, My first love, Ina kwana mamina, ina fata kin tashi cikin koshin lpy," fuskar mami dauke da murmushi ta amsa mata da cewa"Alhamdulillah, my lovely daughter, Ya grand son ɗin nawa naga yana ta tur6une fuska uwa alkubus, halan tashinsa ki kayi daga bacci"? Takai ƙarshen maganar idonta akan junaid, dake zaune saman cinyar mommynsa, sai shan mur yake yi, yana hura hanci, Shi an takura mashi,
"Mami saboda fa ya ci abinci na tada shi, amma da yake shi baisan abun arziki ba, shine yake ta hura mun hanci,"
Mami tace"kwantar da hankalin ki, ae da zarar yayi arba da noodles zai wartsake" hannu mami takai tare da ruƙo plate ɗin dake shaƙe da noodles ta tura ma aneelerh agabanta,
Hannunshi har kerma yake yi wurin kokarin tsoma shi Cikin taliyar, da sauri aneeleerh ta damƙi hannun nashi tare da cewa"Baka ga akwai zafi ba? So kake bakin ka ya ƙone"? ta6e baki ya soma yi alamar zaiyi kuka, lallashin shi ta shiga yi"haba my baby boy, Fushi ba naka bane bari na baka da hannu na" hannu ta sanya ta soma ɗibowa tana bashi abaki yana Ci,
"Mami Ina abie? Ko har sun tafi"? Jinjina kai mamie tayi"tun yaushe kuma, tun bayan sallar asuba yace mun bazai dawo gida ba, daga can zasu wuce, "
"Shi ne ko ya jira muyi sallama dashi" rai adan 6ace tayi maganar, mami tace"sauri yake yi ne, idan mun kammala cin abinci sai ki kira shi awaya ki yi mashi Allah ya kiyaye hanya," amsa mata tayi da toh, daga haka suka Cigaba da cin abincin su,
*south korea🌹*
Seoul City,
Hajiya adama ce zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, A cikin katafaren Palourn gidansu, jikinta na sanye da doguwar cord lace milk colour, idanuwanta na a manne da farin glass medicated, Ta natsuwa tana daddana laptop ɗinta dake asaman Table ɗin gabanta, da alama Komai ya daidaita don yanayinta bai nuna tana acikin damuwa ba,
Gaba ɗaya ta tattara kwandon hankalinta akan aikin da take yi acikin laptop ɗinta,
Sautin Dirar motoci ta juyo acikin Apartment din nasu, dakatawa ta ɗanyi da daddana laptop din ta ɗago tana kallon bakin kofar shigowa falon, duk da tasan ba lallai In baƙin su bane tun da basu kaɗai bane akwai sauran mutanan dake Haya Acikin Ginin,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Uncel abdallah ne Ya shigo Falon, Hannun shi ruƙe da key ɗin motarshi, Suit ne ajikin shi, Miƙe wa Hajiya adama tayi fuskarta asake tace "Welcome back dear, I heard the sound of cars Coming in ko munyi baƙi ne"? sai da ya samu wuri ya zauna tukunna ya kalle ta fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Ni ne baƙon ae, fatan na same ki lafiya, Yau naga walwala atattare dake, Ga shi kin ɗau wanka kinyi kyau abunki,"
Ta6e baki ta yi "Ae tun da kayi mun albishir game da komawarmu gida, Nake ta sakin fara'a ni kaɗai abuna, Yanzu haka ma da kaganni a zaune, Ina duba kayayyakin da zan siyane na tsaraba da zanyiwa mutanan gida," takai ƙarshen maganar tare da kama hanyar zuwa kitchen tace"Bari na kawo maka Ruwa mai sanyi kasha"
"Da kanki Hajiyata? Ina mai aikin gidan take ne"? A sukwane ta Juyo tana bin shi da kallon bansan rainin wayau,
"Oh kamanta irin Korar da kayi ma Ajumma daga gidan nan, Saboda laifin da ba nata ba, ƴar baiwar Allah, dama burinka kaga ina shiga kitchen da girmana, ae yanzu hankalin ka ya kwanta, Hajiya adama ta zama kukun mijinta" Dariya Uncle abdalla Yayi"Matar nan kina sani nishaɗi, Abun alfahari ne mace ta girka ma mijinta abinci da hannunta yaci ya sanya mata albarka, Ta samu lada, Ni ae naga Cigaba sosai, da na kori wannan tsohuwar matar, Tun barinta gidan, kika daina shan Soju, gashi yanzu kin samu natsuwa kin dawo Hajiya adamar dana sani,"
Hararar wasa ta jefa mashi daga inda take a tsaye" korar ajumma da kayi ba shi ne yasa na daina shaye shaye ba, Da naso zan fita inje in siyo da kaina ne, Allah ne yayi silar shiryuwata, dama ba halina bane, tsautsayine da ƙaddara, da kuma damuwar da na shiga na rashin mutun uku masu mahimmanci acikin rayuwata.........." muryarta a karye takai ƙarshen maganar, da sauri tajuya ta shige Cikin kitchen,
Jingina bayan shi Yayi a jikin Sofa ɗin da yake zaune, Har ga Allah Shi kanshi yana acikin matsanaciyar damuwa na rashin ya'yan shi da ya yi, Yaji raɗaɗi sosai, sai dai ba yadda zai yi, daure wa kawai ya ke yi, A duk lokacin daya tuna rashin Da yayi, Na ɗan uwansa, Kuma yayansa Malam zahiru, da mahafiyarsu deeja, Sai ya dinga Jin kanshi tamkar marayan da baida mafaɗi aduniya, Dama wake gaya mashi gaskiya idan yay badai dai ba? malam zahiru ne, tun yana yaro shi yake zaunar dashi yayi mashi nasiha game da rayuwar duniyar nan, kalmar da yafi faɗa mashi itace "ABDALLAH KAJI TSORON ALLAH, ' tuna wannan yasa shi kai hannu ya dafe goshinsa, Idanuwanshi suka Cicciko tab da kwalla, haƙika yaji mutuwarsu, Hatta yahana su Mahaifiyar Tajuddeen, Yaji mutuwarta sosai, Mutanan kirkiki, Mutane masu ƙima da daraja,
Ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe idanuwanshi, Bakomai yake tunawa ba face Tajudeen lokacin da zai raba shi da iyayenshi, Suna kuka yana kuka saboda basu son rabuwa da juna, Suna matuƙar ƙaunar ɗansu, Amma saboda son zuciya yabi ta ƙarfi da yaji don yana da arziƙi, ya ba mahaifiyarsu Cin hanci, aka damƙa mashi yaro, tun da yake bai ta6a danasanin raba tajudeen da iyayenshi ba, Sai bayan rasuwarsu, tsawon shekaru basu yi tozali da dansu ba, har sun koma ga mahaliccin su, Shi ma kuma ɗan nasu An neme shi ƙasa ko sama babu shi, Wannan wata irin ƙaddarar rayuwace? Yanzu idan Allah yasa aka ga su tajudden Taya zai Iya Sanar dashi game da mutuwar Iyayenshi!!? innallahi wa'inna ilaihirraji'un............
Tun ɗazu Hajiya adama ta fito daga cikin kitchen, hannunta ruƙe da plate mai ɗauke da glass cup na ruwa mai sanyi tare da snacks, ta jima a tsaye tana kallon Mijinta nata da ya yi zurfin Cikin tunani, Hawaye ta gani kwance a cikin idanuwanshi, Da alamun damuwa attare da shi ba kamar yadda ya shigo mata ba, A saman C table ta ɗaura plate ɗin dake hannunta,
Kwala mashi kira Tayi A firgice yakai idanuwanshi akanta yana kallonta
"wai lafiya dear, Ina ta kiran sunanka Amma hankalinka sam baya atare dakai, Meya faru ne? Yanzu fa nabarka fuskarka asake, amma kuma na dawo na taras dakai cikin damuwa" tayi maganar tare da kai hannu ta ɗauki Cup ɗin ruwan ta miƙa mashi,
Hannu yasa ya kar6a, tare da kaishi saitin bakinshi yana sha, Zama hajiya adama tayi tana fuskantar shi, Jira take yi ya gama sha yayi mata bayanin dalilin shiga damuwarshi,
A hankali ya sauke Cup ɗin saman table, ya zura hannu Cikin trouser pocket ɗinshi ya zaro hanky ya goge fuskarshi, sai da ya daidaita natsuwar shi tukunna ya kalle ta, gaba ɗaya hankalinta na akanshi, sam baison ya faɗa mata dalilin shiga damuwar tashi, don yasan halitta, Yanzu ta kama yi mashi kuka, shiyasa ko zancen su Taj bai cika son yi mata ba, Rauni ne da ita,
Gudun kada ta ƙara tambayar shi meke damunshi, yasa shi yin saurin canza zancen ta hanyar cewa"Yawwa, Yanzu wani shirye shirye yakamata muyi na komawa Ƙasar mu? Naji kince zaki yi siyayyar kayan tsaraba da zaki yi ma mutanan gida,"
Jinjina kai Hajiya adama tayi tare da cewa"eh, idan ya rage kamar saura 4 weeks Mu tafi, Inaso zamuje Shopping mall atare, Akwai kayayyakin da nake so Na Siyawa ƙanne na, kasan su mayun kallon korean drama ne, suna san suturarsu ba ƙaramin burgesu yake yi ba, inaso na siya masu, hada Jikana zan siyawa kayan wasan yara, da kayansu na al'ada suna burgeni, ita Fatima ma hada cewa in yi masu tsarabar abincinsu, In banda shiririyata, zan dai siya masu chocolates ɗinsu kalar wanda bamu dasu a gida, " magana take yi mashi amma hankalin shi gaba ɗaya baya akanta, har saida Tace"Kai fa? Me zaka yi tsaraba da shi Murmushin yaƙe ya yi mata, muryarshi a karye yace"Wa nake da shi da zanyi ma tsaraba? Dama ƴa'ƴana ne, yanzu kuma babu su, amma duk da haka zan siyawa Angel kalar suturarsu, a ƙiyashin da nayi yanzu takai 15years a duniya, Zan yi mata siyayya sosai in ajiye mata, hada bags and shoes da teddys, komai ma zan siya mata, duk ranar da Allah ya bayyanar dasu, sai in damƙa mata abunta,' yakai ƙarshen maganar, tare da duƙar da kanshi ƙasa, Shi kanshi baisan yayi waɗannan Zantuttukan ba, Saboda su ne aranshi shiyasa yayi maganar, Shessheƙar Kukan Hajiya adama yajiyo acikin kunnanshi, Kafin ya ɗago da kanshi tuni ta miƙe da sauri ta wuce zuwa bedroom ɗinsu, Binta yayi da kallo har saida ta 6ace ma ganinshi,
Girgiza kai kawai yayi, kafin ya miƙe ya nufi ɗakin, Don ya samu yayi wanka Ya canza kayan jikinshi,
*Back To Prison🥺*
Mutsu mutsun farkawa daga bacci ta ke yi, eye lashes ɗinta sun manne ma juna, daƙyar ta samu ta ware idanuwanta basu sauka akan kowa ba, sai akan fine face ɗin Danish dake ta sharar bacci, kasalalliyar ajiyar zuciya ta sauke a yayin da take kallon shi cikin natsuwa, kamar wani baby ya naɗe Jikinshi cikin bargo, fuskarshi kaɗai ce awaje, tun daga kan yadda yake fitar da numfashin shi, zaka shaida yana acikin kwanciyar hankali, baƙaramin daɗi taji ba, tana fatan Allah ya yaye mashi lalurar dake damunshi,
Almost 15 mins tana kallon shimfiɗarshi, kafin ta yunƙura ta miƙe zaune ta jingina bayanta a jikin bango, gadajensu batool tabi da kallo, Tayi mamakin ganin basu farka ba, Kamar wasu matattu sai sharar bacci suke yi, kowa ya kudundune jikinshi cikin bargo, sunyi matuƙar burgeta sai ta dinga jin inama ace Acikin Gidan Mahaifinta suke ba'a Cikin Gidan Kurkukun ba, da sun more rayuwarsu, tasan cewa Danginta zasu kar6esu hannu bibbiyu, musamman aunty aneelerh, da hajiya adama suna son yara sosai, taci alwashin idan Allah ya bata Ikon musuluntar dasu, Zata nema masu hanyar da zasu gudu daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara, Sai dai babban abunda take yi ma fargaba shine, Taya za'ae Su fita daga Cikin kurkukun da ransu da lafiyarsu? Idan Allah yasa sun samu ƙopar fita kenan, Bayan wannan abunda take matuƙar jimawa Anya kuwa GIDAN KURKUKUN ƘADDARA A cikin ƙasar Nigeria yake!? idan har ba'a Nigeria yake to kuwa dai suna acikin tsaka mai wuya! Fatanta Allah yasa ba awani ƙurmin dajin ginin yake ba, Don kuwa akan hanyar guduwa ma wata dabbatar na iya kai masu hari ta Cinye Naman Jikinsu......."
Tana Cikin yin wannan Zancen Zucin nata, Karaf idanuwanta suka sauka akan danish dake ƙoƙarin faɗowa daga saman gadonshi, Cikin magagin bacci, A hanzarce ta duro daga saman gadonta tayi gaggawar tarbe shi, ƙiris Ya rage ya tiƙo ƙasa, ba don Allah yasa tayi saurin zuwa ba, da kanshi yayi mugun buguwa,
Nannaɗeshi tayi tare da turashi saman gadon, Ya koma yadda yake, Ajiyar zuciya ta sauke yayin da take kallonshi, Soft red lips ɗinsa ta gani suna motsi, alamar yana sambatu, miƙewa tayi ta hau saman gadon, ta duƙar da kanta saitin la66ansa, ta natsu tana sauraron me yake cewa,
_the sounds is soothing me, I can't stop listening to ur voice, pls keep reading it in my ears, am really enjoying it_
Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, jin sambatun da danish yake yi, duk akan Karatun kur'anin da tayi mashi jiya ne, ta fahimci cewa ba ƙaramin daɗi yaji ba, shiyasa ma har yake sambatu acikin Baccinsa,
Whispering tayi mashi acikin ear ɗin nashi tace"Kana so In koya maka"? sam batayi tunanin zai amsa bata, sai ji tayi yace"yeah," da sauri ta kalle fuskarshi, Abun mamaki Bacci yake yi bai farka ba, amma yana magana, ƙumshe dariya tayi kafin ta ƙara cewa"Dame zaka biya ni idan na koya maka"? Tayi tambayar Tana sauraron amsar da zai bata,
Cikin muryar bacci yace"I ave nothing to pay you, but I can promise you myself if you want" Cikin nishaɗi angel take dariya, A maganar da yayi mata idan har zata fassarata a matsayinta na wadda tayi rayuwa awajen kurkuku, Tamkar kalaman soyayya ne, Amma shi awurin shi bakomai bane, ya faɗi mata hakan ne saboda baida abunda zai iya biyanta da shi, idan ba kan nashi ba,
"does that mean you will be my slave? If I give you an order, will you follow?" Amsa mata yayi"yeah" koda wankin Uniform ɗina ne? Tayi tambayar tana kallon fuskarshi, idanuwanshi na arufe gam, wannan karan bai bata amsar tambayarta ba, da alama ya kuma yin nisa Cikin baccin sa,
Ruƙo bargon shi ta yi tare da ƙara janshi ta rufe mashi har zuwa saman fuskarshi, Tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon danish, Ta ji yo motsin buɗe ƙopa, da alama giants ne suka ƙaraso, Yau Abinci ya riga masu Cin shi, ƙarasowa,
Ƙarasa saukowa tayi daga kan gadon nashi, ta tsaya a tsaye tana Jiran su ƙarasa shigowa Ciki, Takun tafiyarsu ta soma jiyowa, kafin su bayyana su ukun nan hannayensu a ruƙe da wooden trays, mai ɗauke da kayan Kalacinsu,
Akan idonta suka wuce zuwa saman dining carpet ɗinsu, Kowa ya sauke Farantin dake a hannunshi, Ja da baya su kayi atare suka ƙame kamar yadda suka saba, tunani ta shiga yi Kowanene acikinsu Ya damƙeta aranar nan har yayi wurgi da ita, bazata ta6a manta azabar da tasha ba, Ta tsani giants a rayuwarta, ko son ganinsu bata yi, Saboda basu da Imani, Ga ƙarfi kamar na dawakai, ta jima tana kokwanto akansu Anya kuwa Cikakkun mutanene? Kodai half jins ne?
Ta yi zurfi Acikin tunaninta, taji motsinsu, Ras taji gabanta ya faɗi ganin suna tattara kayan abincin da suka ajiye masu, aruɗe tace" ina zaku tafi da abincin mu? Bayan bamu Ci ba" babu alamun suna sauraronta,
"Magana fa nake Yi maku, idan saboda suna yin bacci ne yanzu zan tashe su, pls kada ku tafi" ko waiwaye wannan basuyi mata ba, Tana ji tana gani suka haura saman bene da abincin suka fuce daga Cikin ɗakin, Tana Jiyo sautin garkame ƙopa da su kayi,
"Ya salam" ta ambaci hakan tare da dafe kanta, muryar batool ce ta katse ta da cewa"Angel lafiya naji kina sambatu ke kaɗai"? Da sauri angel ta juya baya tana kallon batool dake kwance saman gadonta, farkawarta kenan daga bacci,
"Giants ne, Sun kawo abinci kuma sun tafi dashi bansan meyasa ba"?
Waro ido waje batool tayi fuskarta da alamun tashin hankali tace"mun shiga uku! Shikenan yau mun rasa abincin da zamu ci, angel meyasa baki tada mu daga bacci ba lokacin da suka zo"? Fuskarta a hargitse tayi maganar,
"Ina fa kokarin in tada ku daga bacci, sai naga suna tattara kayan abincin, kuma har roƙonsu nayi su tsaya amma basu saurare ni ba....." tunkan takai ƙarshen maganarta, suka soma Jin shessheƙar kukan Parveen, gaba ɗaya suka kai idanuwansu akanta, zaune take saman gadonta, ta wage baki tana ta kuka, Jin cewa Giants sun zo sun tafi da abincinsu,
Sautin Kukan Parveen ne ya farkar da sauran Ƴan uwan nasu, Hanna tana hamma tace"wai meke faruwa ne? Me akayi ma Parveen take kuka"
Javed yace"Yanzu haka rigimartace kawai, duk tabi ta tashi mutane daga bacci, saboda tsabar jarabarta,
Hannu danish ya sanya tare da zame bargon da ke lullu6e a jikin shi, idanuwanshi sun ƙanƙance daƙyar yake iya ware su, saboda baccin bai ishe shi ba,
Haris dake faman yin miƙa yace"kun yi shiru baku bamu amsa ba, Meyasa take kuka"?
Batool ce ta bashi amsa da cewa"Saboda giants sun kawo abinci, Angel bata samu damar tada mu daga bacci ba, har suka tafi da kayan abincin shine take ma kuka"
saboda tsabar tashin hankali Har suna haɗa baki wurin cewa"What? giants sunxo sun tafi da abincin mu"? Amatuƙar ruɗe kowannasu yake faman baza ido,
Dafe kai javed yayi"ae shikenan mun rasa abinci yau, Mu da ganinsu kuma sai gobe, kafin lokacin mun gama jigata,"
Yana rufe baki Rubina tace"Wlh bazan iya jurewa ba, da matsiyaciyar yunwa na farka yau...." mubeen yace"ae ba ke kaɗai ba, Cikina har wani kukan yunwa yake yi" yayi maganar yana shafa stomach ɗinshi,
"Yanzu ya zamu yi kenan"? Naufal ne yayi tambayar yana kallonsu,
Azeeza tace"Mu ci hakuri kawai, Idan munji ƙishi musha ruwa sai mu kwanta muyita bacci har gobe tayi, Harara Hibba ta jefa mata daga inda take zaune saman gadonta"Wannan fa ba abun wasa bane azeeza, magana ake ta babu abincin da zamuci yau, " azeeza tace"idan bamuyi haƙuri ba, to ya zamuyi" tayi maganar tana watsa hannayenta,
Da buɗar bakin deeja sai cewa tayi"bakowa bane ya jamana xama da yunwa ba face angel, meyasa da suka zo baki tashe mu daga bacci ba? Saboda tsabar mugunta,'
Shiru angel tayi don bazata biye mata su yi cece kuce ba, tun da ita halinta ne bata gajiya da shiga sabgar mutane,
"Kodai naje na faɗa ma tsohuwa, ta taimaka tayi magana, su giants su dawo mana da abincin mu," fuska amarairaice parveen tayi maganar, tagama shan kukan nata, taga babu mai lallashinta ta haƙura don kanta,
"Koda kinje babu abunda tsohuwa zata iya yi mana, kema kinsani" yasmin ce tayi maganar, fuskarta a hade, shi dai danish yayi lamo saman gadonshi yana bin bakunansu da kallo, sam baison hayaniyar da suke yi, don ba yadda ya iya ne daya dakatarsu,
Bakowa Angel tafi jima tausayi ba, Sai danish sanin cewa Jiya baici abincin shi ba, ya basu suka cinye, yanzu ga shi sun rasa abincin yau, dole yafi kowa jin yunwa bawan Allah,
Yau fa ba kanta, Duk jikinsu yayi laushi, Ko toilet babu wanda ya shiga don yin wanka ko wanke fuska, damuwarsu Yunwar da zasu kwasa yau, an sanyasu yin azumin dole batare da sunyi niya ba,