Kenza eBookz

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 4

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 4

Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 4: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 4. Tun yana lallashinta ta buɗe ma shi…

3,353 words

Tun yana lallashinta ta buɗe ma shi ƙopa har yakai ga danƙara mata zagi kamar mai yin magana da babban mutun, Ya zazzageta Da masifa duk wannan baisa ta buɗe mashi ƙopa ba, har saida ya kira Uzair A waya ya sanar dashi cewa Angel Ta rufe shi a ɗaki, ya kawo mashi taimakon gaggawa batare da 6ata lokaci ba sai ga uzair Yazo gidan, A zaune Ya same ta saman Sofa tana kallo, aikuwa ya kar6e key din a hannunta Ya je ya buɗe ma shi ƙofa, koda ya fito baibi ta kanta ba Ya fuce daga falon yana huci, Uzair dai yaci dariya, shi ya ruƙo hannunta adole suka tafi da ita wurin aikin nasu,

Saboda bala'in angel Saida yakai ga kullum sai Taj Ya zubar mata da hawaye don ta dinga Jin tausayin shi, bawan Allah duk yayi duhu ya rame, ita kuwa Babyn tashi har kumatu ta yi saboda rayuwar Jin daɗi, yarinya fa kamar rainon turai fara sol da ita, gashi duk wanda yaji Labarin Halayyarta bai yarda, saboda kowa Mamakin shekarunta ya ke yi Just 5 years fa,

Duk irin ɗawainiyar da yake Yi mata sam bata Gani Shine girka mata abinci Yayi mata wanka ya wanke mata gashi Yayi mata kitson kalaba, har ƙunshi na jan lalle yake ƙunsa mata da kanshi, Amma yarinyar nan Idonta sun makance idan kana son Ganin Dariyar ta to ka tabbata ta ƙuntata ma Mahaifinta ne,

Lokacin da takai Shekara 7 a duniya, Ranar wata friday Ya shiryata zasu fita Gidan ɗaya daga Cikin abokanan aikinshi, mai suna Muhsin lokacin da suka je ba ƙaramin farin Ciki muhsin da matarshi sukayi ba, musamman da yazo masu da angel, yarinyar da kowa yake kwaɗayin Yin tozali da ita saboda kyanta, Allah yayita da farin Jini,

Tunda suka je gidan aka kawo masu kayan makwalashe, Taƙi ci da suka tambaye ta meyasa baza ta ci ba sai cewa tayi Daddynta ne Ya hanata cin abincin gidan mutane, a lokacim kasa magana taj yayi saboda baisan amsar da zai basu ba, ƙiri ƙiri ta yi mashi ƙarya, Muhsin ya roke shi akan yayi mata magana taci abincin, Sai taj ya sanya baki yana lallashinta akan taci, da buɗar bakin ta sai cewa tayi "Ai ko yace inci idan muka je gida buguna yake yi,"

Gaba ɗaya Angel ta kashe mashi baki, Muhsin kuwa ya nuna rashin jin daɗin shi akan maganar angel, har suka ta shi tafiya Bata Ci komai ba, tun lokacin yaci alwashin saiya yi mata fada in suka je gida, Ashe da zasu Baro gidan, Ta sace warin Takalmin matar gidan mai tsadar gaske, Babu wanda Ya lura sai bayan Da sukayi nisa da tafiya saman titi, Ta ɗago takalmin tana nuna mashi Wai yakai amayar mata dasu Na yara, Sun burgeta, hankali atashe Yayi parking ɗin motar, dama a ƙule Yake da ita wuyanta Ya shaƙo Ya jijjigata Ya hauta da masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, a karshe yace"Bana sonki kin fita araina, Ke ni ba mahaifin ki bane, bansanki ba ki fita arayuwata" Yayi waɗannan kalaman ne Cikin fushi, buɗe motar yayi tare da fitar da ita waje"Kije ki nemi wani uban"

Yayi tunanin zata saduda ta bashi haƙuri, Amma sai yaga ta watsa da gudu Ta nufi Cikin wata ƴar kasuwa mai tarin jama'a, fitowa yayi daga Cikin motar yabi bayanta, yana faman ƙwala mata kira Koda Ta lura yana binta saita Ƙwala Ihu tana faɗin "Wayyo Allah taimako wani mutun zai sace ta, ɗan yankar kaine ataimaka A mayar da ita wurin iyayenta, kafin kace me Tuni mutane sunyi dandazo akansu, Ganin mutane sun taru hada ƴan ƙato da gora, Aikuwa Ta fashe da kuka ta faki idon mutane ta sanya hannu ta daki hancinta batare da kowa Ya ankara ba, Ya soma bleeding duk don mutane su ɗauki abun serious sosai tadinga kuka tana Faɗa masu cewa"Ba mahaifinta bane sace ta ya yi yana gana mata azaba, Yanzu ma gudowa tayi tana neman iyayenta, dan Allah Hukuma su dauki mataki akanshi, Jin wannan maganar yasa ran mutane Ya 6aci, Musamman ƴan ƙato da gorar nan sun fusata sosai, Kamar jira su ke yi dama a harzuƙe suke, Gaba ɗaya suka rufar mashi da bugu kamar sun samu jaki ita kuwa ko ajikinta, har rantsuwa ya dinga yi masu akan cewa Ƴarsa ce ba satarta yayi ba, Amma suka ƙi yadda saboda bata yi masu kama da jinsin baƙar fata ba, tafi kama da ƴa'yan larabawa da turawa, shi kuma yana da ɗan duhun fata ga kuma Launin idonta ba kalar nashi ba

Ba don Allah yasa an samu wani bawan Allah ya kira ƴan sanda ba, da tuni ƴan ƙato da goran nan sun jima da halaka Tajuddeen, daƙyar suka ƙwace shi a hannunsu, Sunyi ma shi jina jina, rashin sani yafi dare duhu dayawa mutanan da suka rufar mashi da bugu sun san shi, saboda sanannan Ɗan jaridane a garin, babbar matsalar da aka samu, mafi akasarin su Fuskarshice dayawa basu sani ba muryar shi kawai suka sani, A wannan lokacin kuma ba wanda ya an kara kuma ba su ba shi damar da zai yi masu bayani ba.

Police station suka wuce dashi, A cikin Cell suka tura shi, tare da garƙame shi, Sam baya acikin hayyacinshi, Ya galabaita sosai,

A Yayin da Taj ke acikin Cell kulle cikin mawuyacin Hali, Angel tana Office ɗin Dpo tana shan A.c ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, Ganin yarinyar tana da wayau yasa dpo ya soma tambayarta Ya sunanta, Tace mashi sunanta Angel, ya kuma tambayarta ko zata Iya tuna wani abu game da mai satar Yaran da aka kama ya sace ta? da budar bakinta sai cewa tayi ae bashi kaɗai bane mai satar Yaran ba, Akwai abokin aikin shi Uzairu, atare suke sace ya'yan mutane,

A lokacin taj ya dawo hayyacinshi, Suna magana da wani inspector Ya nemi alfarmar su taimaka su ba shi waya Ya kira aminin shi da matar sa zasu bada shaida akan shi,Babu musu inspector ɗin ya bashi damar Yin waya, Nan ya kira uzair Ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar mashi,

Bawan Allah uzair ashe da rabon Yaci na jaki, Saboda tsabar sauri Ko aneelerh bai jira ba, yaja mota Ya nufi station din da taj ya yi mashi kwatance.

Bayan yayi parking ɗin motar, Ya fito ya shiga Ciki da azama, Kamar jira suke Uzairu Ya ƙaraso suka Tallabi ƙeyar shi zuwa cell ɗin da aka rufe Taj, Suka Hankaɗa shi ciki Lokacin daya Kalli tajuddeen dake ta faman Nishi Fuskar shi duk Sahun naushin mutane, bakinshi da hancinshi duk sun fashe, baisan Lokacin daya fashe da kuka ba kamar ƙaramin yaro, rungumeshi yayi ajikinshi, sosai, Gwanin ban tausayi,

Har kiran Angel a kayi daga office din Dpo, Aka nuna mata uzair suka tambayeta shi ne, Tace Eh shi ne.

Sun sha wahala a hannun ƴan sandan, Yinin ranar har dare ya yi ana Bincike a kan su, Daƙyar suka samu a kayi masu alfarmar su kira wani da zai bada shaida akansu, Anan ne Uzair Ya kira Aneelerh, Ya bata address ɗin Ps din da zata same su,

Ba'a ɗauki Lokaci ba Motar Aneelerh Ta ƙaraso Cikin harabar station ɗin, hankalin ta duk Yabi ya tashi Jin suna a hannun police, bayan Tayi parking ɗin motar, Ta fito sanye Cikin doguwar riga ta yafa mayafi akanta a hanzar ce ta nufi cikin station ɗin, Lokacin da ta shiga Ciki, ƴan sandan suka Yi mata jagwaro zuwa cell din da aka rufe su, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba Ganin Yadda aka raunata Taj, duk ya fita hayyacin shi kamar wanda yayi hatsarin mota, Saboda jigatar da yayi.

Cikin shessheƙar Kuka Ta kalli ƴan sandan tana faɗin "Why why!why pls? Laifin me suka aika ta da za ku yanke masu irin wannan ɗanyen hukuncin," Copral ne Ya bata amsa da cewa"Ana zargin su da sace Ƴa'ƴan mutane suna amfani da su" Waro ido waje aneelerh Tayi tana kallon su, har bata san lokacin da tace "Amma baka da hankali Officer, Ka iya bakin ka, Shin kuna da hujja akan a bunda kuke zargin su ne? waye ke baisan Taj da uzair ba....."bata kai ƙarshen maganarta ba muryar dpo ta katse ta"Muke da ƙwaƙƙwara Hujja akansu," Idanuwanta jawur ta ɗago tana kallon Dpo ɗin, Cikin sanyin murya ta furta"where's the evidence"?

Kafin dpo ya bata amsa sai ga Angel tana fitowa daga Office ɗin shi

A ruɗe Aneelerh take kallonta Cike da son Jin ƙarin bayani,

Da kulkin hannunshi Ya nuna Angel, itace ƙwaƙƙwarar Hujjar da muke da ita, Wannan yarinyar An same ta cikin kasuwa tana gudu tana kuka a kan Wannan bawan Allahn daya sace ta, Ya raba ta da iyayen ta don baƙin zalunci," yakai ƙarshen maganar Yana nuna Tajuddeen,

Hankali amatuƙar tashe Aneelerh ta daura hannu akai tana sallallami"You ave made a big mistake officer wannan fa Ƴarshi ce," muryarta a disashe takai ƙarshen maganar,

"Amma ae ita Yarinyar da kanta ta faɗa mana cewa shi ɗin ba mahaifinta bane satarta Yayi," acewar dpo,

Tuni hawaye sun kuma wanke fuskar aneelerh, Girgiza kai tashi ga yi tana kallon angel, "Wlh officer Ƴarshi ce sharri take yi mashi, Yarinyar bata da cikakken hankali ne," Da buɗe bakin angel sai cewa"Ni ƙarya take yi mun officer itama hada ita suke yi ae"

Curo handcuff Inspector yayi tare da cewa"You are under arrest" ya ambaci hakan yana ƙoƙarin sanya mata ankwa Ganin dagaske Kamata za su yi ne yasa tayi saurin cewa"Ku dakata kada kuyi abunda zakuyi danasani Officer, akwai hotunan yarinyar da videos ɗinta a wayar Mahaifinta zaku Iya bincika wayar shi ku gani. Girgiza kai Dpo yayi"Wannan ba hujja bace duk shirin ku ne" Jinjina kai tayi to shikenan me zai hana Muje asibiti ayi masu DNA test, this is the Only solution" Jinjina kai dpo "Good idea Copral"Dpo ne ya kira sunan shi "Yes sir" ya amsa mashi. "Ku tafi da Mutumin da yarinyar a yi masu gwajin DNA, ku tabbatar anyi komai agaban ku," "Consider it done sir" Ya ambaci hakan tare da sara ma shi,Kafin Ya fiddo dasu Taj daga Cell ɗin, Bawan Allah kamar lagwanin fitila duk ya rasa ƙwarin Jikinshi, sai da uzair Ya taimaka mashi tukunna ya iya tafiya da ƙafafun shi, wani abun mamaki ko kadan Angel bata ji tausayin shi ba, ko son kallon shi ma ba ta yi,

A cikin mota suka sanya su, Aneelerh kuma Ta shiga motarta tare da angel,

Bayan zuwan su asibiti, Akan idon Police men ɗin akayi komai, Bayan Bincike da likita Yayi result Ya nuna cewa Jininshi ce ita,

Hankalin ƴan sandan ba ƙaramin tashi yayi ba, Lokacin da suka kalli result ɗin da likita ya basu Sun sha mamaki, Lamarin Yayi matuƙar girgizasu, Tun anan Inspector Ya kira Dpo ya sanar dashi sakamakon Gwajin da akayi masu, dpo yafi kowa girgiza, har sai da ya tako yazo asibitin Don Ya basu taj haƙurin akan zargin su da suka yi Anan aka kwantar da Tajuddeen, Sam ya fita hayyacin shi,hada drip suka sanya mashi,

Atare ƴan sandan suka ba su Aneelerh da Uzair hakuri akan kuskuren da su ka yi na ɗaukar mataki batare da sun fara Bincikar ainihin tsakanin shi da yarinyar ba, A ƙarshe dpo ya ba aneelarh shawarar a haɗa ta da manyan malamai su cire shaiɗanun dake ajikinta, ko kuma a kaita Psychiatric Hospital koda tana da matsalar kwakwalwa ne,

Bin shi da kallo kawai aneelerh tayi don ita tasan Wacece Angel, Lafiyarta ƙalou itace aljanar kanta da kanta, yarinyar da ana yi mata ruƙiya tana cewa malamin Yadaina wahalar da kanshi Lafiyarta qalou "

Kwananshi uku a gadon asibitin saboda jikin shi da yaƙi sauƙi, cikin kwanakin Aneerlerh ce da Uzair suke ɗawainiya da shi Ko uncle abdalla basu Sanar mashi da halin da ake ciki ba, da yake suna waya dashi kusan kullum ne sai sun kira su kosu su kirasu, A ƙarshe suka koma gida da yin jinya, Har hutu Aka ba Taj wurin aikinsu jin Abunda ya faru da shi, Uzair ne ya sanar dasu amma bai fada masu ainihin abunda Ya faru ba, kawai ya sanar dasu cewa Sun yi hatsarin motane, ya yi hakan ne saboda sanin halin su na ƴan jarida, yanzu ka ji labari a social media,

Bawan Allah Taj kullum yana kwance saman gado, Wanka da sallah ne kaɗai suke tada shi Wani sa'in yana ɗangya shi haka zai samu ya lalla6a Ya shige toilet, Ko sannu angel bata ta6a furta mashi ba sai in tana jin yunwa ne zata addabe shi wai ya tashi yayi masu girki, in ba haka ba zata je ta daura da kanta,

In ta gaya mashi hakan Jiki na rawa Yake kiran Uzair a waya Ya sanar dashi, dama Cikin ƴan kwanakin nan mai aikin su Uzair hada Su taj take girka ma abinci duk in za ta yi, bisa umarnin Uzair ɗin,

Ana haka Yau kwana Biyar kenan bai zuwa ko'ina Yana gida, Wuraren ƙarfe biyar na marece, ya fitowa daga wanka jikin shi sanye da short baƙi, saman Gado ya haye bacci mai daɗi ya ɗauke shi Yayi nisa acikin Baccin shi, Yadinga Jin Hayaniya acikin gidan jiki a mace Ya miƙe daga saman gadon ya nufi ƙopar ɗakin, Leƙawa yayi don yaga su wanene

Waro ido waje ya yi ganin mutane maƙil Cike da falon, Kasa kunne ya yi yana sauraran me suke cewa "Allah ya jiƙan shi, Taj mutumin kirki halinshi na gari Ya bishi," Can kuma yaji wani yace"A ina ne za'ayi jana'izar ta shi"? Wani ya ba shi amsa da cewa"Mu jira Mutanan gidan su fito sai muji," Shiru yayi la6e bakin ƙopar Ya kasa fitowa, Jikin shi duk yayi sanyi, tunani ya shiga yi wai wanene Ya mutu? dama akwai wani taj ne bayan shi"? sam bai da mu da rashin ganin angel ba yasan bata wuce Gidan su Uzair.

Komawa Cikin ɗakin yayi Jikin shi duk ya mutu, Wayarshi Ya ɗauka da ke a jiye saman gadon Yana kunnata Ya shiga call logs, Nan yaga missed Calls sunyi ɗari uku na mutune, abun ya ɗaure mashi kai,

Number uzair yayi dialing Ya danna mashi kira, Tana fara ringing uzair Ya ɗaga, "Assalamu alaikum" batare daya amsa sallamar ba Yayi saurin cewa"Uzair kana ina ne"? On the other hand Uzair yace"Gida mana" Cike da damuwa yace"Uzair na shiga Uku, Yanzu kawai na farka daga bacci Naga dandazon mutane a falon gidana, Na kuma taras da missed calls a wayata Ya yi ɗari uku na mutane wai meke faruwa ne"?

Muryar uzair da ɗan ruɗi yace"Kodai angel tayi wani abu ne? bata jima da shigowa Gidan mu ba, Take sanar dani cewa Ta ɗauki wayarka kana bacci, Ta sanya yatsan ka ta buɗe ta "tunkafin Uzair yakai ƙarshen maganar ta shi, Taj Yayi rejecting call ɗin, Ya shiga laluban wayar shi, Sai ga Notification na facebook on the top of the screen yayi appearing, Likes ya dinga gani na mutane da kuma Comment da ake tayi, A hanzarce Ya shiga facebook dinshi, a nan Yaga hoton shi dana angel ta ɗauka yana bacci tayi share ɗinshi a facebook, a ƙasa ta rubuta RIJF, Su kuma Mutane da suka Ga posting din dayawan su sunyi tunanin ko matarshi ce Tayi amfani da wayar shi donta sanar masu mutuwar shi, Shine suka kwaso ƙafafuwansu zuwa Gidan don a yi jana'ixa da su.

jiri ne Ya soma ƙoƙarin kwasar shi, lalla6awa ya yi tare da samu wuri gefen gadon ya zauna yana ambaton Allahumma Ajirni fil musibati wa aklifli khairan Minha, Na jima ina tunanin Ranar mutuwa ta, da kuma abunda zai yi silar bari na duniya ashe ƴar Cikina ce, Laifin me nayi mata ne da ta tsane ni? sai ka ce ba mahaifin ta ba,ƴar ƙarama da ita sai Iya mugunta wayyo Allah na,

sai daga bisani Ya tuna inda tasan kalmar RIJF, a tv ne wani ya rasu ana sanar da ta'aziyar shi, daga ƙasan hoton shi aka Sanya RIJF, Rest In jannatul firdaus, shine take tambayar shi wai me yake nufi, da yake ta iya tambaya kamar yar jarida, Bai yi tunanin komai ba ya sanar da ita ma'anar hakan, Shine tayi mashi aika aika.

Kiran Uzair Ne ya shigo wayar shi, A sukwane ya ɗaga Kiran a nan yake sanar da shi abunda ta aikata mashi, Uzair yasha ruwan mamaki

A ƙarshe dai,Uzair da aneerlerh ne suka shigo gidan suna bama mutune hakuri akan cewa Taj bai mutu ba, Yana a raye mistake aka samu wurin Yin posting din, ƙin tafiya sukayi Har sai da suka ga Taj da ƙafafun shi tukunna suka bar gidan suna yi mashi Allah ya kyauta, A falo suka zauna gaba ɗayan su, Uzair da Aneelerh suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Taj kuma yana zaune a saman 2 seater,fuskarshi duk a hautsine, "Yanzu menene mafita"? taj ne ya yi maganar yana kallonsu, "Lamarin Angel Yafi ƙarfin mutun sai dai Allah, ae ni tun ranar da aka kira malami yayi mata ruƙiya ta sace takalman shi, tun daga nan Jikina Yayi sanyi," acewar Uxair, "Benazir ta tafi tabarmun bala'e" tamkar taj zai fashe da kuka Yayi maganar,. "Me zai hana ka jaraba Bugunta"? a ɗan firgice ya kalli Aneelerh da tayi maganar, Cigaba da magana tayi"Idan har ba za ka iya bugunta ba shawarar da zan bada shine, Kasan mafi a kasarin ƙananun yara akwai abunda suke tsoro, Ni ina ganin a jaraba samo Mage ko kare ko kuma ƙadangare, Idan aka samu wanda take tsoro acikinsu, Sai adinga Yi mata Baraza na da shi, Koya kuka Gani"? tayi tambayar tana kallon Taj, wanda ya yi zugudum yana kallonta, yarinyar da take kallon Zombie tsakar dare, Taya zata Ji tsoron waɗannan halittun, Acikin zuciyarshi ne yayi maganar, Jinjina kai Uxair yayi"Good idea idan na fita Yanzu xansa Almajirai su ɗauko mun ƙadangare a fara jarabata dashi, inyaso gobe sai a kawo karen Nasan dole asamu wanda take matuƙar tsoro acikinsu," "Allah yasa dana fi kowa Farin Ciki" acewar Taj,

Sun jima suna tattaunawa kafin Su ka yi ma shi Sallama, Atare suka bar gidan,

Duk dabbobin da aka kawo gidan don angel ta tsorata amma abun ya ba su mamaki bata tsoron su, illa ma ita dabbar da aka kawo taji tsoronta, yarinyar ta zarce tunanin mai tunanin ga karfi Allah Ya yi mata, Ranar da taj yasa aka kawo mage agidan Sai da ya yi dana sani, A lokacin Yana kwance yana bacci Ya barta a falo ita da magen da ta sanya ma suna Chu chu, suka soma kokawa tana kiciniyar kamata, magen ta watsa aguje tana kuka, tabi bayanta da gudu suka shiga zagaye palourn, Sune har cikin kitchen, Magen ta haye saman Dish racks, inda Jerin Plates na tangaran suke, Angel takai hannu da niyar ta cafkota aikuwa gaba ɗaya Ta 6aro da Kwanukan tangaran din, Suka tarwatse kasa duk suka faffashe, Tsalle magen tayi ta ruƙo jikin Cupboard wasu hadaddun Glass Cups ne dana tangaran, Ruƙo ƙafar magen Angel ta yi, Gaba ɗaya Cups din suka Rikito ƙasa duk suka tarwatse, Kubce mata magen tayi da gudu ta sauko ta nufi Store da kopar shigar shi ke anan cikin kitchen ɗin, Aguje angel tabi bayanta, Suka shiga yin yar tseral, Wasu jerin Crates din kwai Ne Magen Ta hau saman su, A ƙalla sunyi crates goma sha biyu, Gaba ɗaya suka kife kasa eggs ɗin suka faffashe, hayewa sama magen ta yi inda aka jera Sunƙi sunƙin bready, Ganin tsawonta bai kaiwa yasa ta janyo jarkar Manja, Ta haye samanta Ta cakumo wuyan magen, jarkar da ta hau saman kanta ce ta Karkace da ita da magen Da jarkar man, Da Ledojin breadin sunkutukum Suka Kife ƙasa, Nan take murfin jarkar ya buɗe Manjan Ya shiga gangarowa ƙasa, bari in takaice maku zance sai da Angel ta canzama Kitchen din halittarshi, tamkar Bola, uk Ta hargitsa komai ba,

Da ta ga Ta yi 6arna sosai, saita Saki Cucu, Ta ruga da gudu ta nufi gate, A lokacin baba mai gadi Yana Cikin yin alwalar sallar magrib, Ya hangota ta nufo shi,

Readers Also Read