Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 44
Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 44: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 44. "Lokaci Yana ƙure maki, idan har kika…
3,023 words
"Lokaci Yana ƙure maki, idan har kika bari na juya na dogara sandata na koma Cikin ɗakina, To ku fidda rai da zan sake fitowa, wannan ce kaɗai damar da kuke da ita" tsohuwace tayi maganar, fuskarta ɗauke da shu'umin murmushi, mai nuna tsantsar farin Ciki, bata ta6a jin nishaɗi ba irin na yau, a hankali angel ta kawar da idonta daga kan fuskar tsohuwa ta mayar dasu kan fuskokinsu Javed da yasmin da hibba dake a zuƙunne saman gwiwowinsu, fuskarsu sharkaf da hawaye, gyaɗa kai kawai tayi Jiki ba kwari ta maida idonta ga tsohuwa, murya na kerma tace"zan roƙe ki ne bada son raina ba, dan haka kada ki yi tunanin kin ƙasƙantar dani ne, zanyi ne saboda waɗannan bayin Allahn, da kuma ƴar uwata dake acikin mawuyacin hali, Sannan kada ki yi tunanin kece zaki bata lafiya, Allah subhanahu wata'ala shine ya baki ikon yin hakan, domin kuwa saida yardar shi ne komai yake wakana" daƙyar takai karshen maganar ganin tsohuwa na ƙoƙarin juyawa ta koma Cikin ɗakinta, aikuwa da sauri angel ta ɗago ta zuƙunna saman gwiwowinta, Muryarta a disashe tace"Na roƙe ki dan Allah badan Ni ba, kije ki duba lafiyar Deeja" Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta fashe da ita, tamoji tamojin fuskarta har rawa suke yi, saboda tsabar yarda jikinta ke jijjiga, Angel kuwa wani irin ƙululun baƙin Cikine ya Turniƙe zuciyarta, har wani zazza6i taji ajikinta, Kusan atare su javed suka sauke ajiyar zuciya, saboda tsabar mugunta saida tsohuwa tasa angel ta maimaita maganar da tayi kusan sau uku tukunna tace"hakan ya yi mini, haƙiƙa yau na shaida irin ƙaunar da kike yi musu, ke ɗin uwace ta gari agare su, Ina ji araina cewa nan gaba har rayuwarki zaki Iya sadaukarwa akansu, don ba ƙaramin mamaki nayi ba ganin irin yadda kika sauke duk wani girman kai naki da kafiyarki wurin roƙo na akan lafiyar ƴarki deeja, Naji daɗi sosai Albarka zata tabbata akanki, ni kuma yau ta kasance ranar tarihi arayuwata, wato ranar da the most arrogant young lady in the world ta zuƙunna saman gwiwowinta domin ta roƙe ni......"Tsohuwa bata karasa maganarta ba, muryar angel Cikin fushi tace"Kinga surutun ya isa haka, tunda nayi maki abunda kike so, kema saiki biya ni" cike da shaƙiyanci tsohuwa tace"To gimbiya sarautar mata, Ai ko me kike so yau zanyi maki shi" Harara angel ta watsa mata kamar kwayar idanuwanta zasu faɗo kasa,
Juyawa tsohuwa tayi zata koma cikin ɗakinta, muryar javed ta katse ta"deeja fa? Naga zaki koma Cikin ɗaki" batare da ta juyo ta kalle shi ba tace"Ku jira ni yanzu zan fito," Tsayawa su kayi suna jiran ta, Badajimawa ba sai ga tsohuwa ta fito hannunta ɗaya ruƙe da gorar ruwa ta gargajiya, miƙa ma javed tayi"Ruƙe mun nan, Mu je ciki ka nuna mini ita" da sauri javed ya sanya hannu biyu ya kar6i gorar ruwan, Suka shiga gaba tabi bayansu, angel dai bata bi su ba, A nan ƙasa ta kwanta zuciyarta na tafarfasa, Ji take yau ta bata kanta, tun da harta durƙusawa tsohuwa,
Lokacin da suka shiga Cikin toilet ɗin, Tsohuwa ta basu umarnin su fita waje su jirata, haris dai bai yarda da ita ba, ya ƙyaleta ne kawai yaga iya gudun ruwanta, ɗaya bayan ɗaya suka fuce daga Cikin toilet ɗin, kafin javed ya fita sai da ya fara ajiye mata gorar ruwan a kasa, Tukunna yasa kai ya fuce, Cikin ɗakinsu suka koma Kowa zuciyarshi cike da zullumi, daga Cikin toilet ɗin suka soma Jin kukan deeja yadda kasan ana zare ranta, hankalinsu yai matuƙar tashi, gaba ɗaya suka gaza jurewa, Komawa su kayi Cikin sashen toilet, Koda suka je bakin ƙopar toilet ɗin a datse suka same shi, A dole suka zauna ƙasa zaman jiran fitowar tsohuwa, danish dai yana acikin ɗakinsu, bai bi bayansu ba, Saman gadonshi ya koma ya zauna, yana satar kallon angel dake kwance a ƙasa, Yana so yaje ya lallashe ta amma yana tsoron masifarta, don kuwa yau sai Allah, Taci ka ta batse, jira take kawai ta samu wanda zata huce haushinta akanshi,' wannan dalilin ne ya hana shi tunkararta, gudun kada yasha mari,
Yau fa babu bacci, Dare ya koma musu tamkar rana, azeeza ce kaɗai take gyangyaɗin bacci, tana atsakankanin Batool da naufal, ta ɗan ɗaura kanta saman kafadar batool, ga dukkan alamu bacci take so ta yi, Naufal ne ya lura da ita, ruƙo hannunta yayi acikin nashi yace"azeeza tashi muje in raka ki cikin ɗaki ki kwanta, kada ki yi bacci anan" maƙe mashi kafaɗa tayi muryarta adisashe tace"ba yanzu zan kwanta ba, sai na jira an fito da deeja" Haris dake sauraronsu yace"naufal, Kada ka biye mata, pls ka ɗauke ta, ka kaita cikin ɗaki," rigima ta sanya musu, akan ita bazata je ta kwanta ba, sai ta ga deeja" Naufal bai tsaya sauraronta ba, ya sanya hannayenshi biyu ya sa6e ta, kamar wata ƴar baby haka ya ruƙota ya nufi Cikin ɗakin da ita, A saman gadonta ya kwantar da ita, tare da janyo bargonta dake a nannaɗe ya lullu6e mata jikinta, sai gashi ta yi shiru alamar bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya naufal ya sauke sai da ya fara ɗagowa ya kalli danish dake kishingiɗe saman gadonshi, Ya kuma kallon angel dake kwance a ƙasa, Ya ɗan girgiza kai, kafin Ya juya ya nufi Cikin sashen toilet ɗin, Lokacin da naufal ya shiga Ciki, Ya yi dai dai da buɗe ƙopar toilet da tsohuwa ta yi, aikuwa Jikinsu har 6ari yake yi wurin miƙewa tsaye idon kowa akan Ta, fitowa tayi hannunta ruƙe da sanda, Ta ɗago ta kallesu tace"Ina babar taku take Ne"? Suka haɗa baki wurin cewa"Tana acikin ɗaki" tsohuwa tace"Ku je kuce mata ta ɗauko bargo tazo, ta ɗauki diyarta, " amsa mata suka Yi da toh, Batool ce taje cikin ɗakin ta isar da saƙon zuwa ga angel, atare suka dawo hannun angel ruƙe da bargo, fuskarta a kumbure take hararar tsohuwa,
Matsa mata Hanya tsohuwa tayi"Ki shiga Ki lullu6a mata shi ajikinta, ki fito da ita, " batare da ta amsa mata ba ta nufi ƙopar toilet ɗin ta shige Ciki, tsohuwa ta kalli javed tare da cewa"idan sun fito ka ɗauko mini gorar ruwan nan, ka biyo ni da ita" ya amsa mata da toh,'. Har ta fara tafiya ta dan juyo tana kallon fuskokinsu tace"Yakamata kuje ku kwanta, duk da ma naga kamar Lokacin ya ƙure garin ya waye" bata rufe baki ba, sai ga hasken ɗakin su Ya gauraye ko'ina, sun yi matuƙar yin mamaki, maganar tsohuwa ta tabbata, har gari ya waye basu sani ba, Atare suka haɗa baki wurin yi mata godiya, bata amsa musu ba sai cewa tayi"bani yakamata ku yi ma godiya ba, Babarku ce ta cancanci hakan," Fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar, tare da juyawa ta fuce daga cikin sashen toilet ɗin ta nufi dakinta,
Fitar tsohuwa keda wuya, Sai ga angel ta fito hannunta ɗaya talla6e da deeja, da alama hada wanka tsohuwa tayi mata, uniform dinta na sanye a jikinta, Daga sama kuma bargon da angel ta lullu6a mata ne," wani irin farin Ciki ne Ya lullu6esu, Ganin ƴar uwarsu ta wartsake har tana iya taka kafarta, Sai faman sauke ajiyar zuciya suke Yi, wuce wa gaba angel ta yi suka bi bayansu, a bakin gadon deeja suka tsaitsaya, angel ta taimaka mata ta kwantar da ita saman gadonta, muryar deeja na ɗan kerma tace"Sanyi nake ji, ku ƙara mun wasu bargunan akaina, Ko jikina ya yi ɗumi," Da sauri kowannan su ya nufi gadon shi suka ɗauko bargunansu suka lullu6a mata ajikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci bacci ya yi awon gaba da ita, duƙawa angel tayi agaban gadon deeja daga gefe, ta soma karanto addu'o'i tana tottofa mata, bayan ta kammala ta ɗago da idanuwanta ta kalli su Batool dake a kewaye da ita, tace dasu suyi mata addu'a suma, kowa ya ɗan zuƙunno da kanshi saitin gadon, suka karanta abun da taɗan koya musu suka tofa mata, daga bisani haris yace dasu, Su koma su kwanta, ganin jiya basu samu isasshen bacci ba, ba musu suka amsa mashi da toh, kowannan su Ya wuce saman gadon shi, suka kwakkwanta, Ya rage saura haris dake a tsaye sai angel dake zuƙunne agaban gadon deeja, wuri ya samu gefen gadon deeja ya zauna, ba laifi yanzu hankalin shi ya ɗan kwanta, kallon angel yae tare da cewa"Ke fa? Baki jin bacci"? daƙyar ta iya ɗago da ido ta kalle shi, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta, maganganun da deeja ta faɗa mata sune suke ta yi mata yawo a cikin kanta,
"Dake nake magana" muryar haris ce ta kuma katse ta, batare data amsa mashi ba, ta yunƙura ta miƙe ta nufi gadonta, tana isa ta haye sama ta kwanta, koda suka haɗa ido da danish dake kishingiɗe saman gadon shi, harara ta watsa mashi, kafin ta juya mashi baya, lumshe idanuwanshi yayi, zuciyarshi duk ba daɗi, saboda ya gane dalilin dayasa ta harare shi, dole taji haushin shi, saboda rashin ta6uka komai, shi kuma aganinshi indai baida maganin abu to baida amfani ya tsoma baki, shiyasa yake yin shiru, Amma har ga Allah yana matuƙar damuwa dasu, Yana jin tausayin ƴan uwanshi, Yana matuƙar ƙaunarsu fiye da kan shi,
Rabi da kwatarsu tuni bacci Ya yi awon gaba dasu, mutun uku ne suka rage, Haris da tuni ya jima da komawa saman gadonshi, damuwar halin da deeja ke aciki ce ta hana shi runtsawa, Sai kuma Parveen da Yunwa ta addabe ta, ta lafe kwance saman gadonta sai juyi take yi, bayan ita kuma sai Angel wadda babu alamun zata runtsa, ita fa babban abunda ke damunta, irin takurawa rayuwarsu da ake yi, da kuma cutar dasu da ake yi, tana matuƙar jin tsoran tarasa wani acikinsu, tabbas zata ji raɗaɗin da yafi wanda taji a lokacin da ƙaddara ta rabata da daddynta, a yanzu tafi jinsu acikin zuciyarta fiye da kowa ma nata, yanzu bakomai yafi tsaya mata arai ba, face mutun shiddan nan da Deeja ta faɗa mata cewa ta gansu akanta, Shin su wanene su? Uban me suka aikata mata? Kodai su duka suka afka mata a lokaci ɗaya suka lalata rayuwarta? Innallahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma Ajirni fil musibati...... wani irin ɗaci take ji acikin zuciyarta, idanuwanta suka cuccuko tab da ƙwalla, ta tausaya ma rayuwarsu, Idan har suka cigaba da kasancewa acikin kurkukun nan tabbas kuwa wata rana za'a nemi koda gawawwakinsu ne arasa, Ita dai bata fatan tarasa ranta acikinsa, kodan saboda ta gano su wanene suka assasa ƙungiyar da kuma waɗanda suka sadaukar dasu, Wannan alƙawarine ta ɗaukarwa kanta, sai sun ɗanɗani kuɗarsu, sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwarsu ta yi acikin duniyar nan!!! Acikin zancen zucin da take yi, kwata kwata bata sanya tsohuwa aciki ba, duk da itama taji haushin abunda tayi mata ayau, amma ta ajiyeta gefe ɗaya, saboda ba ita bace agabanta, masu ƙungiyar kurkukun ƙaddara sune agabanta, da kuma waɗanda suka yi sacrificing ɗinsu.
Lokacin da giants suka shigo kawo musu abinci, Mutun ɗaya ce ta Iya miƙewa, har zata tada su daga bacci, Haris yace ta ƙyalesu, taje ƙarƙashin gadon batool ta ɗauko kwandon da suke ajiye abinci, ta kwaso musu aciki, idan suka farka zasu Ci, ta amsa mashi da toh, Bayan ta ɗauko food basket ɗin taje gaban jerin farantan da giants suka sauke musu, Ta zuƙunna ta ajiye kwandon gefe, ta sanya hannu ta yaye jan ƙyallen dake akan farantin farko, Steak and onions ne, Yankan nama manya manya sunji albasa da kayan ƙamshi, Hannu tasa ta dinga ɗebowa tana zubawa cikin kwandon, duka ta kwashe, Ta kuma buɗe faranti na biyu dake ɗauke da Snacks tare da madaidaicin bowl Na kayan marmari ta kwashe komai ta ɗaura akan naman, Faranti na ƙarshe Bottles waters ne, Miƙewa tayi tare da sanya hannu biyu ta ɗauke kwandon, Yayi nauyi, A agaban gadonta ta ajiye shi, ta koma domin kwaso robobin ruwa, dake a jere saman faranti na ƙarshe, Ta ruƙo su a hannayenta, Bayan ta kammala giants dake a tsaye suka raƙwafa atare suka ɗauke farantan, Tare da kama hanya suka fuce daga Cikin ɗakin, Zama parveen tayi agaban gadonta, ta ɗago ta kalli haris dake kallonta tace"Ba yanzu zaka Ci ba? Yana daga kwance saman gadonshi, Yace mata"sai sun farka zai ci" tace"Nima in jira sai sun farka"? Ba don taso ba ta faɗi hakan, Girgiza mata kai yai alamar a'a kafin yace"zaki iya ci mana, kici iya cinki, sauran da kika rage sai muci, ae nasan duk haɗamarki ba zaki iya lamushe abincin duka ba, ko rabi ma ba zaki iya tadawa ba" murmushine ya bayyana akan fuskar Parveen, jin abunda yace, bata ƙara tanka mashi ba, takai hannu tana zakulo naman tana turawa abaki, Sai da taci iya cinta, ta haɗa da snacks ɗin duka, har saida cikinta yayi ƙato, tukunna ta dakata da ci tana faman shafa ciki, bottle water ta ɗauka ta buɗe tasha ruwan, Data kammala ta tura kwandon ƙarƙashin gadonta, Haris yace"Salon da anjima idan kinga muna cin namu, kice kema zaki ci," dariya ta ɗanyi har dimple ɗinta na saman chin ɗinta ya lotsa, komawa saman gadonta ta yi tare da hayewa, da niyar itama ta samu baccin ya ɗauke ta,
Basu suka tashi farkawa ba, sai da suka kwashe tsawon awanni suna bacci, daga bisani yunwa ta fara farkar dasu, ɗaya bayan ɗaya, kowa ya miƙe yana hamma, Haris yace suje su wanko bakinsu suzo suci abinci, Suka amsa mashi da toh, Kowa ya nufi toilet, bayan sun kammala wanke fuskokin suka zo suka zazzauna ya dauko musu kwandon abincin dake a karkashin gadon parveen, Ya ajiye musu atsakiyarsu, ba yadda baiyi da angel ba akan tazo taci abinci amma taƙiya saima ce mashi tayi ita bata jin yunwa su dai su ci, Komawa yayi bakin gadon danish a lokacin ya ɗan fara bacci, ya tada shi tare da cewa" ka taso mu ci abinci," danish yace"suje su ci baijin yunwa" lamarin yai mutuƙar ɗaurewa haris kai, su biyu sunce basu jin yunwa, Anya kuwa lafiya? Ko dai duk don saboda rashin lafiyar deeja ne yasa suka ƙi Cin abinci? A ƙarshe daya gaji dayi musu magana akan su taso sai ya ƙyale su, ya koma wurin dasu batool suke a zazzaune shima ya zauna, Suka tsoma hannayansu suna Cin abincin, Ba duka suka cinye ba, Sai da yace su rage ma Deeja idan ta farka, Sai kuma Angel da danish, Yankan nama shida shida suka ajiye ma kowannan su, Sai fruits, banda snacks duka suka cinye shi, Sun dai ajiye musu bottle water Biyu, bayan sun kammala suka ajiye musu nasu a karkashin gadon batool,
Wuraren marece, Deeja ta farka muryar ta a disashe take faɗin, Ruwa zata sha, ƙishi take ji, da sauri haris Yaje ya ɗauko robar ruwa cikin wanda suka ajiye musu, Ya koma gefen gadonta ya zauna yana kallonta a lokacin ta yaye bargunan da suka lullu6a mata, daƙyar ta yunƙura ta miƙe zaune ta ɗan jingina bayanta jikin bango, Yadda kasan fatalwa, tayi haske ga rama, ƙashin wuyanta duk ya fito 6aro 6aro jikin fatarta, Gashin kanta kuwa duk ya hargitse, Baiwar Allah daga gani ba ƙaramin Jiki taji ba.
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
"Sannu deeja ya jikin naki" ya yi maganar tare da buɗe murfin robar ruwan ya kwafa mata baki, Hannu bibbiyu tasa ta tallabe hannanyenshi dake a ruƙe da robar, saboda tsabar yadda take shan ruwa kana Iya jin sautin throat ɗinta kwat kwat! Har sai da yace mata tasha a hankali kada ta shaƙe, janye robar ta yi da hannunta alamar ta ƙoshi, Sai lokacin ta samu damar ƙare mashi kallo, su batool dake a zazzaune saman gadajensu suna yin fira, Ganin deeja ta farka yasa suka dawo bakin gadonta, wasu suka zauna wasu kuma suka tsaya atsaye, A hankali take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Ba ƙaramin daɗi taji ba, irin yadda suka nuna mata kulawa, sai dai a yayin da take kallonsu, wani irin tausayin kansu ne ya kamata, domin kuwa tasan ƙarshen su yana dab da zuwa, a yanzu bakowa tafi jimawa ba face waɗanda ba'a ta6a ɗauka acikinsu ba, musamman azeeza da tafi kowa rauni acikinsu, gata ƴar ƙarama duk da ba shekaru suka fita ba, amma babu alamun girma atattare da ita, saboda rashin tsawonta, idan suka miƙe tsaye ko kafaɗarsu bata kai ba, farat ɗaya ka kalleta sai ka yi hasashen shekararta Goma, saboda ƙarantar jikinta,
tana Cikin yin zancen zucin nan muryar batool ta katse ta da cewa"deeja me kike tunani muna ta yi maki magana tun ɗazu amma kin yi shiru baki ce komai ba, ina fata kina lapiya," ajiyar zuciya ta ɗan sauke, still idonta na akan azeeza data zauna gefen gadonta ita dasu Yasmin, haɗa baki suka yi wurin yi mata ya jiki ta amsa musu da cewa"Alhamdulillah Jiki da sauƙi, Naji daɗi sosai da irin kulawar da kuka bani, Ina matuƙar alfahari da ku ƴan uwana nakaina" Murmushi suka saki gaba ɗayansu, ta mayar da idonta kan haris dake kallonta, ta lura da irin damuwar da ya yi akanta,
"Lokacin da aka tafi dani, haris ya iya Cin abinci kuwa"? da zolaya tayi maganar, gaba ɗaya suka yi dariya, yasmin tace"ae tunda aka ɗauke ki, ya gaza samun natsuwa, idan ya kwanta saman gadonshi idanuwanshi na fuskantar ceilling sai ya ɗauki tsawon lokaci bai tashi ba, wata'ƙil hoton fuskarki yake gani" Harara haris ya watsa ma yasmin da tayi maganar,
Kafin yace "Abunda ta faɗa ba ƙarya bane, Na damu dake sosai, Ko bacci nake yi sai nayi mafarkin ki, Bani kaɗai ba Kowa ya damu dake" duƙar dakai deeja ta yi hawaye suka cicciko idanuwanta, muryar azeeza ce ta ratsa kunnan ta"Sister deeja pls don't cry, muna cikin farin cikin samun sauƙin ki, kada ki karya mana zuciyoyin mu," azeeza na rufe baki, deeja ta karasa kifa kanta saman gwiwowin ƙafarta, sosai ta fashe da kuka, Sai faman lallashinta suke yi, ita bakomai ne yafi damunta ba, face tuna cewa wata rana fa dole wani ya mutu a cikin su, gashi sun shaƙu da juna, Allah kaɗai yasan raɗaɗin da zasu ji aranar da suka rasa wani acikin su,