Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 47
Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 47: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 47. "A ina zamu ɗibar musu abincin mu kai…
3,346 words
"A ina zamu ɗibar musu abincin mu kai musu"? hibba ce tai maganar, hannah tace"ku daina magana kada Giants su ji mu, abunda za'ae mu ɗauko kwandon batool mu ɗibi abinci, sai mu ajiye, bayan sun tafi sai muje mu kai musu acikin toilet ɗin," haris yace"kin kawo shawara mai kyau," batare da 6ata lokaci ba, hanna ta miƙe taje ta ɗauko kwandon daga ƙarƙashin gadon batool ta dawo ta zuƙunna gaban farantan, ta yaye jan ƙyallan da aka rufe faranti na farko dashi, fried fishes ne aka kawo musu, manya manya sun soyu sai maiƙo suke Yi, a ƙalla kowa zai samu ɗaya, Kifin akwai tsoka jikinshi sosai, A hankali take kai hannu tana ɗaukar kifin tana ajiyewa acikin kwandon, ganin ta ɗauki uku, yasa haris yace"Ki ƙara ɗaya kodan saboda danish" duk da fushi da yake yi dashi hakan bai hana shi jin damuwa dashi ba, Hanna tace toh, tasa hannu ta ƙara ɗaukar ɗaya ta ajiye, Ta ɗibar musu fruits tare da robar ruwa guda uku ta ɗauka, miƙewa tayi hannunta ruƙe da kwandon taje bakin gadon batool ta ajiye shi ta dawo ta zauna, a tsanake suke Cin nasu fried fish ɗin, Suna ci suna satar kallon giants dake atsaye sun goya hannayen su saman ƙirjinsu yadda kasan Gumaka, ko gajiya da tsayuwa basa yi,
A 6angaren su angel dake acikin toilet, Tuni bacci yai awon gaba da azeeza da batool, duk suna akwance saman jikinta, itama angel ɗin wani irin bacci take ji ga yunwa dake addabarta, sai faman lumshe idanuwanta take yi,
Daga wajen ƙopar toilet ɗin ta soma Jin ana yi musu knocking ras taji gabanta ya faɗi, hatta su azeeza dake baccin jin bugun ƙopar yasa suka farka a firgice suna faman zazzare idanuwan su,
Muryar hanna suka jiyo tana faɗin"Ni ce angel, ku buɗe mini kopa, breakfast ne na kawo maku" Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, duk sunyi tsammanin ko Giants ɗin ne suka zo tafiya dasu,
"Ku jira na amso mana abincin" tai maganar tare da zame jikinta daga nasu ta miƙe ta nufi ƙopar, ta cire jam lock ɗin, ta janyo ƙopar tare da leƙo da kanta waje,
Hanna ta gani atsaye ita da haris, kwandon Yana a hannun hanna ta ruƙo shi,
"Angel Giants sun zo kuma sun tafi, Ni ina ganin kamar ɗigon jinin nan ba jini bane. Tunda da ace shine, Giants zasu tafi da su azeeza ne, Amma kinga har sun kawo mana abinci sun tafi" shiru angel ta ɗanyi tana nazarin maganar Hanna. Ita gani take kamar jini fa ne, kawai dai bai kai ga zuwa bane gaba daya shiyasa basu zo sun ɗauke su ba
Muryar haris ce ta dawo da ita daga zancen zucin da take yi,
"Nima ina tunanin ba jini bane gaskiya, tun da ga shi har zunzo sun tafi batare da sun buƙaci tafiya dasu ba" abunda za'ae yanzu ku fito mu koma cikin ɗakin ku zauna ku yi breakfast ɗinku" Gyaɗa kai angel tayi badan taso ba tace"Allah yasa abunda muke hasashe ya zama gaskiya, bari nayi musu magana su fito mu koma daki amma kafin nan, zan taimaka musu su wanke fuskokinsu," haris ya amsa mata da toh .kafin ya kalli hanna yace"Mu jira su acikin ɗaki" juyawa suka yi atare suka koma ɗaki,
Badajimawa ba, Sai ga angel ta fito hannayenta ruƙe da nasu azeeza, Bayin Allah har faɗa wa sun ɗan yi saboda damuwa, Ƴan uwansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba, da su kayi tozali dasu,
A saman dining carpet suka zauna su uku, Hanna ta ajiye musu kwandon. Angel da azeeza suka ɗauki fried fish ɗinsu A hankali suke Ci, Sauran ƴan uwansu duk suna a kewaye dasu suna kallonsu, ganin batool ta kasa ci ne yasa haris yi mata magana yace"batool meyasa baki ci? Muryarta na ɗan kerma tace"Hannuna Zafi yake yi mini" sai lokacin suka tuna da cizon da azeeza ta gartsa mata, Zuƙunnawa haris yai agabansu, ya kai hannu cikin kwandon ya gutsiri tsokar kifin ya mika mata abaki, ta ɗan buɗe shi tana Ci, sai ƙara kwantar musu da hankali ƴan uwan nasu suke Yi, bayan sun kammala Ci, suka sha fruit ɗinsu, tare da ruwa,
Angel tace yakamata suje suyi wanka, jikinsu duk zufa, suka amsa mata da toh, har tana cewa idan bazasu iya yin wankan ba zata taimaka musu suyi, batool tace ita zata Iya, azeeza kuma tace tafi son angel tayi mata wankan, hannun su aruke dana juna suka nufi toilet, bayan tafiyarsu, Haris ya ɗauki kwandon yana kallon sauran Fried fish din daya rage na danish tare da Rabin gwanda, Ta6e baki ya ɗanyi kafin ya nufi gadon danish, Ya ajiye mishi kwandon daga gefen shi yace"Idan kaga dama ka ɗauka ka ci, breakfast ɗin ka ne" ko motsi danish bai yi ba, ya runtse idanuwanshi, kuma ga dukkan alamu idonshi biyu ba bacci yake yi ba,
Watsa hannu haris yai alamar bai damu ba, Ya wuce abunshi, bayan wani lokaci, angel tafito daga Cikin toilet tare dasu azeeza, Wani irin sanyi suke Ji, asaman gadajensu suka kwanta, angel ta lullu6esu da bargunansu, Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yai awon gaba dasu,
Ajiyar zuciya kowannan su ya sauke, yanzu sun ƙara tabbatar da cewa ba jinin gaske bane suka gani acikin toilet tunda har marece ya doso amma ba'a zo an ɗauki wani daga Cikin su ba,
Ita dai angel ta kasa samun natsuwa acikin zuciyarta, abu biyu ne ya dameta, na farko Jinin batool da danish yasha da niyar ya taimaka mata wurin dakatar da bleeding ɗin da yake yi, amma wani abun mamaki bai zubda jinin ba sai ya shanye shi, hankalinta bai kwanta da hakan ba, abu na biyu daya tsaya mata arai shi ne wannan ɗigon jinin dake acikin toilet na wanene? Dole akwai wanda ya zubar dashi,
Zuciyarta cike fal da tunani ta ɗan kishingiɗa saman gadonta, da niyar ta samu ta runtsa, juyawa ta ɗanyi tana satar kallon danish dake kwance saman gadonshi, yatsun hannunshi dana ƙafarshi sai kerma suke Yi, hakan ya tabbatar mata da cewa idonshi biyu, ta6a baki ta ɗanyi aranta tace"Haka zaka ƙare, mutun sam baya gajiya da hawan gado, mai matacciyar zuciya kawai" takarasa xancen zucin tana mai jan tsoki, ta ɗauke idanuwanta daga kan jikin shi, ta mayar dasu kan kwandon da haris ya ajiye mashi daga gefen gadonshi, yau kuma kowa zai lallashe shi yaci abincin shi? murmushin takaici ta dan saki, wani lokacin in yana abu kamar ƙaramin yaro, har mamaki yake Ba ta
*after some hours💔*
Kafin marece ya yi sai da kowan nan su ya yi wanka, Suka koma saman gadajensu suka kwanta, har lokacin danish bai motsa ba, Yana ayadda yake lafe saman gado,
Angel tana ƙoƙarin nutsawa cikin baccinta, ta soma jin motsin mutun a jikinta, aɗan firgice ta ware manyan idanuwanta akan fuskar wanda ke zaune saman gadonta, Tayi mamakin ganin batool, fuskarta duk a yamutse. Idanuwanta sun ƙanƙance, tunkafin ma batool tayi mata magana taji wani irin faɗuwar gaba,
Muryarta na ɗan rawa tace"Lafiya? Batool meke damunki"? Cikin sanyin murya ta soma magana"Bana jin ɗaɗin jikina angel, gaba na sai faɗuwa yake yi, na gaza jurewa, shiyasa nazo wurinki, don kiyi mini addu'a, ko na samu naji sanyi araina" ajiyar zuciya angel ta sauke a yayin da take yunƙurin mikewa xaune tace"Wlh har gabana ya faɗi dana ganki nayi tunanin ko jinin ne kika gani yazo miki ashe bashi bane" jinjina kai batool ta ɗanyi alamar eh, tace"Bashi bane, bana jin daɗi ne kawai"
"Tun da nake dake batool ban ta6a ganin ki cikin damuwa ba, irin na yau, kin canza sosai, duk sai naji ba daɗi jikina," daƙyar batool ta ɗan ƙaƙalo murmushin dole akan fuskarta tace"kada ki damu sister, zan dawo dai dai ne, just fargabar abunda ya faru ɗazu ce tasa duk na canza, Amma yanzu da ɗan sauki"
Ido cikin ido suke kallon juna. angel ta ruƙo hannayenta acikin nata tare da cewa
"Zanyi maki addu'a, amma nafi so naji ki ajiki na, don naji daɗin kwantar miki da hankali kamar yadda kika saba yi mini" murmushi suka sakar ma juna atare,
A saman chest din angel batool ta kwantar da kanta, tare da sanya hannayenta, ta zagayo dasu ta bayanta, sosai tayi tighting ɗinta, wani irin tsananin ƙaunarta take ji, suna matuƙar son junansu fiye da tunanin mai tunani, addu'o'i angel ta soma karantowa tana tottofa mata asaman kanta, har cikin zuciyarta take jin wani irin daɗi yana ratsata, har tana fadin"sister kada ki daina yi mini addu'ar nan, ki cigaba, ina jin wani irin sanyi acikin raina," murmushi angel tasaki, tare da ɗaura hannayenta saman sumar kan batool dake a dumbuje babu gyara, ta shiga shafata tana faɗin"indai akanki ne, zan iya kwana batare dana runtsa ba, wurin yi miki addu'a, ina matuƙar ƙaunarki my batool, " muryarta asanyaye ta karasa maganar,
"Mu kwanta mu yi bacci, mu ma, " acewar batool, a manne da juna suka kwanta saman mattress ɗin, angel taci gaba da yi mata addu'a har sai da bacci ya ɗauke su gaba ɗayansu,"
To jama'a, ɗaki fa ya yi shiru baka jin hayaniyar komai, hankalinsu kwance sai sharar baccinsu suke yi, kamar waɗanda aka yanka mutuwa agabansu,
Lokacin da marece Ya nutsa, deeja tafarka daga bacci ta miƙe ta zauna saman gadonta, hannunta rungume da pillow, ɗaya bayan ɗaya take bin gadajensu da kallo, kafin ta tsayar da idonta akan shimfidar haris, ta jima tana kallon shi, kafin ta ɗauke idanuwanta, hakanan taji tana ra'ayin tabi kowani gado ta kalli fuskokin ƴan uwanta,
Don haka ta sauko daga saman gadonta, Still jikinta ba ƙwari sosai, kamar ɗiyar roba hake take yin tafiya, tun daga kan gadon su hanna taso ma bi tana kallonsu har zuwa gadon azeeza, Ta ɗan dakata da tafiya tana kallonta, wani abu daya ɗaure mata kai bacci take yi amma sai firgita take Yi, numfashinta kuma a hargitse take fitarshi, matsawa ta ɗanyi tare da samun wuri gefen gadon azeeza ta zauna, hannunta ta ɗan ɗaura bayanta ta ɗan bubbugata, aikuwa a firgice azeeza ta farka tana faman zazzare idanuwanta, lokaci ɗaya kuma ta dafe kanta da hannu ɗaya tana faman sauke ajiyar zuciya ganin deeja ce,
"Azeeza lafiya kike ta firgita kina bacci? Ko dai baki da lafiya ne"? Tayi mata tambayar cikin nuna damuwarta,
Muryar azeeza adisashe tace"Hankalina ba a kwance yake ba, deeja bana jin daɗi, baccin nan da kika ga ya ɗauke ni har mafarkin Giants sai da nayi" idanuwanta acike tab da kwalla takai ƙarshen maganar,
Janyota deeja tayi zuwa jikinta ta dan rungumeta da hannu ɗaya, tana lallashinta,
"Ki kwantar da hankalin ki My little sis, muna atare dake, babu abunda zai faru daku,"
Azeeza tace ina jin ƙishin ruwa," da sauri deeja ta raba azeeza daga jikinta, ta sauko daga saman gadon ta nufi gadon batool ta zuƙunna ta tura hannu ƙarƙashi ta ɗauko robar ruwa, Ta miƙe ta koma gadon azeeza, ta zauna tare da cire murfin ta kwafa mata ita abaki, sosai ta shiga shan ruwan,
A wani irin firgice Azeeza Ta jefar da robar ruwan dake ahannun deeja. Ta zabura ta yunƙura ta duro daga saman gadonta ta faɗo ƙasa, Ta shige ƙarƙashin gadonta, Jikinta sai kerma yake yi, Lamarin yae matuƙar ɗagawa deeja hankali, muryarta da alamun ruɗu take kwala ma azeeza kira tana tambayarta lafiya? Meyasa ta jefar da ruwan! Kafin deeja tayi yunƙurin saukowa daga saman gadon azeeza da niyar ta duƙa ƙarƙashin gadon ta janyota, kwatsam ba zato ba tsammani taji motsin buɗe ƙopar ɗakin su hankalinta a matukar tashe ta ɗago tana kallon Benan, Ba ita ba hatta masu bacci sai da suka farka jin sautin buɗe ƙopar, wani gabjejen Giant na ya faɗo Cikin ɗakin, mai faffaɗan ƙirji bayyanar shi tamkar baiyanar mutuwa ne agaresu, Wani abun ɗaure kai ma Giant ɗin daya shigo yasha banban da waɗanda suka saba zuwa kawo musu abinci, domin kuwa shi hada Star ɗaya a jikin baƙar rigar jikinshi daga gefen hannun hagu, sai lokacin deeja ta gane dalilin dayasa azeeza ta gudu ta 6oye ƙarƙashin gado, Wata irin faɗuwa gaba ce tazo ma deeja, lokaci ɗaya ta fasa ƙara mai matuƙar firgitarwa muryarta na rawa take ambaton"Innallahi wa'inna ilaihirraji'un! wayyo Allahna mun shiga uku! Mun bani!' wannan maganar da deeja tayi ce tasa duk wani mai bacci ya ƙarasa wartsakewa, Hankalin angel da batool yai matuƙar tashi, a matuƙar ruɗe angel ta ruƙo hannun batool suka sauko daga saman gadonta, da gudun gaske taja ta suka faɗa cikin sashen toilet ɗinsu, Suna shiga ɗaya daga cikin makewayin, Angel ta zura jam lock ta datse ƙopar, tana juyowa batool ta faɗa jikinta tana kuka take faɗin"Angel tafiya za'ayi dani, naji ajikina nice aka zo ɗauka, shikenan za'a raba ni da farin Ciki na ina ji ina gani, za'a ɗauke ni a tafi dani inda za'a cutar da rayuwata, Ba lallaima ne a dawo dani Cikin ku ba" Fashewa da kuka angel tayi Cikin shessheƙa tace" wlh bazaiyiyu ba, haƙurina ya ƙare, komai xai faru sai dai ya faru amma wlh bazan bari atafi dake ba, duk runtsi duk wuya ina atare dake, Sai dai su kashe ni" gaba ɗaya sun shiga matsanancin tashin hankali, su biyu acikin toilet sun ƙanƙame juna
A hankali giant ɗin yake saukowa daga saman staircases ɗin, haris yai matuƙar harzuƙa, Su rubina duk sun zazzare idanuwansu, damuwace ƙarara kwance akan fuskokinsu. Wasu har sun fara kuka, tun kafin ma a ɗauki ƴan uwan nasu, Duk wannan budurin da akeyi danish bai motsa ba, haka zalika Azeeza bata fito daga inda ta 6oye ba, domin kuwa tuni ta jima da sumewa,
Yadda kasan zaki Haka giant ɗin nan Ya tunkaro wurin gadajensu, Yana zuwa tsakiyar ɗakin Yaja burki ya tsaya ga dukkan alamu kamar kallonsu yake yi duk da basu Iya gane hakan. Tunda jikinsu gaba ɗaya a lullu6e yake da baƙaƙen kaya, hatta idanuwansu
Ƙasa ƙasa da murya haris yace"ku ƙyale shege kada ku faɗa mishi inda suke muga ya zaiyi, Na rantse yau sai dai ayi duk wacce za'ae amma bazan Bari wannan ƙaton Ya ɗauki ɗaya daga Cikin mu ba"
Muryar Hanna Cikin shessheƙar kuka take take roƙon giant ɗin tana faɗin"Dan Allah kada ku raba mu da ƴan uwanmu, Idan ma ɗaukar ta zama dole to ni ku ɗauke ni ku tafi dani amma na roƙe ka ka ƙyalesu, sun tsorata sosai zasu Iya rasa ransu, "
hannah na rufe baki, sauran matan suka fashe da kuka suna roƙonshi, bayin Allah hada ƙoƙarin saukowa daga saman gadajensu suna yi mashi magiya akan ya ƙyale musu ƴan uwansu, su sun amince ya ɗauke su amma kada ya ta6a musu Azeeza da batool, tabɗijancan Iska na wahalar da me kayan kara, sufa duk atunaninsu zai ji tausayinsu Ya ƙyalesu, Sai dai abunda basu sani ba, Zuciyar giant tamkar dutse take. basu da tausayi ko misƙala zarratin, babu ɗigon Imani akansu, Su fa kawai Umarni suke bi daga sama, haris da ranshi ke a6ace yace"Ku daina wahalar da kanku, babu alamun zai saurareku, tun da ba tausayi ne dasu ba, Ae mun riga da mun 6oye su, kuma babu wanda zai nuna mishi inda suke idan yaga dama yai ta tsayuwa daga yau har jibi, idan ya gaji ya kama hanya ya koma," haris fa ya ɗauko ta da zafi,
Tunda suka fara magana, gabjejen giant ɗin nan baiko motsa ba, Kamar yana sauraron me suke tattaunawa,
Da mamaki su ke kallon Giant ɗin, ganin ya ɗaga hannayen shi biyu yai clapping ɗinsu, Cikin rashin fahimtar me yake nufi yasa suka zazzare ido suna kallon Juna,
Danish ne ya fara motsawa daga saman gadonshi, Ya miƙe ya sauko da ƙafafuwanshi ƙasa, ya ɗan ɗago ya kalli giant ɗin dake a tsaye na wani lokaci kafin ya ƙarasa saukowa daga saman gadon, Yaje gaban giant ɗin ya sara mashi, a matuƙar ruɗe suke kallon danish, abun mamaki abun al'ajabi
Daga bisa ni, su ka ga danish ya juya Ya nufi sashen toilet ɗinsu, gaba ɗaya suka bi shi da ido, Batare da wani ya motsa ba, Zuciyoyinsu cike da fargabar me danish zaije yi acikin sashen toilet ɗinsu,
A lokacin batool da angel suna a zuƙunne jikin bangon toilet, sun ƙanƙame juna, Unexpected Angel tajiyo motsin buɗe kopa, tashin hankalin da ba'a sama shi date, Ƙopar dake a rufe kafin su shigo ta ciki ta sanya jamlock ta garkame ta, A matuƙar ruɗe take kallon Jikin ƙopar ganin jam lock ɗin yana motsi da kanshi ya zame kanshi, ƙopar ta buɗe, saboda tsabar tsoron da taji tuni zufa ta wanke fuskarta, batool kuwa tuni jikinta ya ɗauki wani irin zafi na fitar hayyaci,
Duk a tunaninsu giant ne zai shigo wani abun al'ajabi sai ganin danish su ka yi ya faɗo Cikin toilet din, yana ƙarasa shigowa, Ya miƙa ma Batool hannu yace ta taso su tafi, wani irin kallon tashin hankali angel da batool suke binshi dashi, Ganin taƙi miƙa mashi hannunta yasa shi yin saurin damƙo damtsen hannunta ya janyota ta ƙarfi ya fiddo da ita daga Cikin toilet ɗin, da gudu angel tabiyo bayanshi, ta cafko hannun batool tana ƙoƙarin ƙwato ta, amma abun ya faskara domin kuwa ba ruƙon wasa yai mata ba, Adai dai lokacin da danish ya fado Cikin ɗakin, su haris suka ga ya ruƙo batool, zuciyarsu tai matuƙar karaya, lamarin yai matuƙar girgixasu, tsabar ruɗanin da suka shiga yasa suka gaza ta6uka komai,
Kafin su yi wani yunƙuri, Danish Ya ƙarasa gaban Giant ɗin tare da batool Ya damƙa mashi ita, Giant ɗin ya sanya hannu biyu ya ɗauki batool saman kafaɗar shi batare da 6ata lokaci ba. ya juya ya nufi hanyar fita daga ɗakin, Al'ajabi ya hana su motsa, Suna ji suna gani giant ya tafi da batool tana ta kuka tamkar ranta zai fita,
Nan take angel ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume, kamar jira suke Yi giant ɗin Ya fita, Haris yai wani irin kukan kura ya duro daga saman gadonshi, Ya kai ma Danish farmaki, kwalar rigarshi ya damƙa ya jijjiga shi, Hawaye na fita Cikin idanuwanshi yace"Ka kashe mu danish! Ashe dama baka da hankali? Kai wani irin wawan mutun ne sakarai soko maloho, wanda baisan Ciwon kanshi ba, wlh ka karya mini zuciyata ko a mafarki ban ta6a tunanin zaka Iya ruƙo hannun batool ka damƙa ma giant ita, don aje acutar da rayuwarta, ashe na yaudari kaina bansani ba, mugu azzalumi, wawa daƙiƙi...." Kafin haris ya ƙarasa maganar shi, Gaba ɗaya sauran ƴan uwan nasu suka tarar ma danish, bugu ta ko'ina suka shiga kai mashi, Kamar sun samu jaki, Hada matan duka suka nannaɗe hannayen rigunansu suka dunga bugunshi, amma ko gizau baiyi ba. Har saida suka fasa mishi hancin shi da bakin shi jini ya soma zuba, tukunna suka sake shi, anan ƙasa ya kife idanuwanshi sunyi jawur tamkar garwashin wuta, wani irin jiri yake gani, ya rasa meke yi mishi daɗi, ta ko'ina ga6o6in jikinshi raɗaɗi suke yi mishi domin kuwa ba ƙaramin bugu suka yi mashi ba, sun haɗa mishi Jini da majina sun xautar dashi,
Kowa sai faman haki yake yi, Kuma babu wanda yaji tausayin shi, suna a tsaitsaye cirko cirko suna kallonshi, sai faman juyi yake yi, tun da suke dashi basu ta6a jin tsanar danish ba sai yau daya nuna musu true colour dinshi, mugun zargin shi suke yi, tabbas shima yana atare da giant shiyasa yake goya musu bayan duk abunda suke yi. Ɗan jakar uba,
Haƙiƙa Danish ya yi breaking heart dinsu, hawaye ta ko'ina akan fuskokinsu, Ji suke kamar su tattake shi ya mutu su huta, tun da baida amfani acikinsu, tare da shi ake haɗa baki a cutar da ƴan uwansu,
"Daga rana irin ta yau kada ka ƙara kiran mu da sunan ƴan uwanka, mugu azzalumi" Javed ne yai maganar, deeja tace"dama tun jiya da aka dawo dani, naga sauyi atare dashi, ko sannu baiyi mini ba, ashe hada shi ake haɗa baki a cutar damu,"
Mubeen yace"ae ni banso muka barshi da rai ba, wlh da mun sani mun karkarya ƙasusuwan Jikin shi, " yana magana yana cije le6e,