Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature - Chapter 66
Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 66: Kurkukun ƙaddara takun farko by by boss bature Chapter 66. Maƙe mashi kafaɗa tai tare da cewa"ae…
3,310 words
Maƙe mashi kafaɗa tai tare da cewa"ae babu kyau, bazan goge maka ba, sai mun yi aure" maimaita kalmar aure yai"what does that mean"? Jujjuya eye balls ɗinta ta yi, tare da sauke su kan fuskar shi tace"Zan faɗa maka amma ba yanzu ba, sai mun fita daga cikin kurkukun nan," ta ƙarasa maganar tare da fashewa da dariya, tabi ta gefen shi, ta fuce daga cikin toilet ɗin, bin bayanta da kallo yai har ta 6ace ma ganin shi, ta tafi tabar shi da aikin maimaita kalmar Aure, tunawa da Gabriel dake acikin ɗakin, yasa shi yin saurin bin bayanta.
Tana shiga ɗakin ta samu su azeeza zazzaune saman dining carpet ɗinsu kamar masu cin abinci, Alhalin nan kuwa fira suke yi a tsakanin su, gwanin ban sha'awa, Gabriel Na ganin ta yae saurin yunƙurawa zai miƙe daga zaunan da yake a gefen gadon shi, suna haɗa ido da ita, Sai ga Danish Ya faɗo ɗakin, da sauri Gabriel Ya koma ya zauna fuskarshi babu walwala, bai ta6a ganin ɗan takura irin Danish ba.
A bayan angel ya tsaya tare da yi mata magana"muje ki kwanta" ba tare da ta kalle shi ba tace"bacci a yanzu? A'a gaskiya, Ni sai dare yayi zan kwanta, Zanje wurin su hanna mu yi fira ne, " yace mata"Okey, my eyes on u," yana faɗin hakan ya nufi akwatin kayan su, ya buɗe ya ajiye rigarshi, ya ɗauko red vest ɗinsa ya zura ta a jikin shi.
Su hanna na ganin Angel, suka soma sakar mata murmushi suna faɗin Ga Masoyiya angel nan, Ku bata wuri ta zauna, mayar musu da martanin murmushin ta yi, taji daɗin sunan da suka kira ta dashi Masoyiya Angel.
A tsakankanin Jamima da azeeza ta zauna, tana fuskantar Hanna da parveen, kowannansu yai zaman cin tuwo kamar ɗaliban makaranta allo.
"Ku fada min akan me ku ke tattaunawa ne"? Tai tambayar tana kallon fuskar kowannan su, Sarah ce ta fara magana"Labari su ke bamu akan abubuwan da ki ke koya musu, Lokacin da bamu nan" Parveen tace"Namanta ban faɗa maki ba, lokacin da ki na yin bacci kamar jiya ne, Gabriel ya tambaye mu, wai mu bashi labarin ki sannan mu faɗa mashi abubuwan da kika koya mana, kuma duk mun faɗa mashi" a tsanake ta ke sauraron su, yayin da idanuwanta ke a kan la66an masu yin maganar.
"Yau har training ɗin rawa ya bamu, duk mun gaji, shiyasa muka zauna muna ɗan zantawa" acewar Hannah.
"Pls Angel, ki koya mana abunda ki ka koya musu muna so" Jamimah ce tai maganar, Hibba tace"damuwa tasa kin daina koya mana karatu," numfasawa tayi kafin ta soma magana
"In sha Allah zamu cigaba da yin karatu, nima ban ji dadi ba, dana daina koya ma ku, yanzu dai kowa ya faɗi abunda yake so mu dinga yi, don mu sanya junan mu farin ciki"
Duk wani a bu da suke tattaunawa akan kunnan Danish, da ke a zaune saman gadon shi, nan ya zauna bayan ya sanya vest dinsa, idon shi akan la66an Angel da ke cikin yin magana tana kora masu parveen jawabi akan abubuwan da zasu dinga kullum.
Ko ƙyaftawa baiyi, Gabriel kam Idon shi na akan Danish, lamarin ya ɗaure mashi kai, ganin irin kallon ƙurullan da ya ke yi ma Angel, kamar zai lashe ta,
Firgit! ya yi jin saukar hannun mutun saman kafaɗar shi, da sauri yakai idonshi kan wanda ya ta6a shi, Haris ne ya zauna gefen shi.
"Da alama ka manta da ɗan uwan ka, na lura kwanakin nan hankalin ka gaba ɗaya yana akan Angel tun da ku ka shirya da ita, wai menene a tsakanin ku ne? Tell me ɗazu ma mu na kallon ku ni da Deeja, Angel ta shiga toilet ka bi bayanta, tsawon lokaci ba ku fito ba, sai daga bisani mu ka ga ta fito, kai ma ka biyo bayanta kamar ma wanka ka yi" tun da haris ya soma magana Danish Ya baza kunnuwanshi yana sauraron shi, sai dai har yanzu bai janye idanuwanshi daga kan fuskar Angel ba saboda tsabar jaraba.
Da mamaki akan fuskar Haris yace"kai magana fa nake maka? Ko kallo ban ishe ka ba kenan," motsi yae da la66ansa wurin furta mashi"Am all ears," haris yace"ae nasan kana ji, saboda ka maidani shashasha ina magana idon ka na akan Angel, wai me ka ke kallon akan fuskarta ne"? Yai tambayar yana leƙen fuskarshi, da buɗar bakin Danish sai cewa yai"kyau nake kallo, ko ba ka gani ba" sakin baki haris yai,"Dama kyau yana kallon kyau"? ɗaga mashi kai ya yi alamar Eh.
"Bari na tashi na baka wuri, ka gama kallon kyan, don na lura gaba ɗaya bata ni ka ke ba," kafin haris ya miƙe Danish yai saurin ruƙe hannun shi yace"Hankalina akan yake, idanuwana ne kawai basu atare da kai, amma ina sauraronka" Guntun toki haris yaja"dalla ni sakar min hannu na, ɗan rainin wayau," Ƙin sakin hannun nashi yai, ya damƙe shi acikin nashi, su naufal dake zaune saman beds ɗinsu, gaba ɗaya hankalinsu na akan Danish da haris, Mubeen yace"ku tashi muje wurin su mu ma muyi fira, tun da suma matan sun haɗa kansu" Kamar dama jira su ke yi yai maganar, kowannan su ya sauko daga saman nashi gadon su ka nufi Danish, gefe da gefen mattress ɗin suka zazzauna.
Javed yace"me kuke tattaunawa ne? Shi ne baza a kira mu ayi zantawar damu ba," Haris yace"kun ga alamun muna tattaunawa ne? tun da nazo na zauna gefen shi, bai juyo ya kalle ni ba, idanuwanshi na akan Angel, na rasa gane me yake kallo akan face ɗinta, ya dai ce min kyau yake kallo" dariya su ka saki gaba ɗayan su, naufal yace"abun mamaki, kyau na kallon kyau," Ba tare da Danish ya kawar da idanuwanshi daga kan fuskar Angel ba ya bashi amsa da cewa"ba abun mamaki ba ne, ni nasan me nake kallo" mubeen yace"ban yarda ba, sai dai wani abun na daban, idan kyau ka ke son kallo, ka ɗauki mirror ka kalli fuskarka mana," shiru bai tanka mashi ba, don ba ƙaramin takura shi su ka yi ba, Gabriel da ke zaune gefen gadon shi, a takure, yaso ace angel tana fuskantar inda yake ne don ya ji daɗin faɗa mata inda ya ajiye mata wasiƙar, sai dai ta juya mashi baya.
"Tun da baka son mu zauna a kusa da kai, ku tashi mu je wurin ƴan uwan mu mata, su yi firar tare da mu," haris na faɗin hakan kowannan su ya miƙe su ka nufi Dining carpet ɗin su, inda su Angel su ke zazzaune kowannan su Ya samu wuri ya zauna, cikin sa'a Naufal ya zuƙunna bayan Hannah da ke fuskantar Angel, da ya ke dogo ne shima tubar kalla, gaba ɗaya ya kare ma Danish Fuskar Angel, baya iya ganinta da kyau, takaicin duniya ya ishe shi, sai ya mayar da kallon shi ga Gabriel, su ka haɗa ido da juna, Jira ya ke yaga in gabriel zai miƙe da niyar yaje wurin su, kamar Gabriel yasan me ya ke ayyanawa acikin zuciyar shi, da gangan ya miƙe zai nufi wurinsu, a hanzarce Danish ya miƙe, komawa Gabriel yai ya zauna gefen gadon shi, sai gashi shima Danish ɗin ya koma nashi gadon ya zauna, Ikon Allah.
Su biyu ne basu je wurin ƴan uwan nasu da ke yin fira ba, hatta Majnun yana a tsakankanin Deeja da Rubina, Ya natsu kamar mutumin arziƙi, duk wanda yai magana acikinsu haka zai ƙurawa la66ansa ido har sai ya gama magana, wani lokacin sai ya tintsire da dariya, ko ba abun dariya aka faɗi ba.
"Tun da yanzu mun ƙara yawa, A faɗa mana waya fi kyau a cikin mu"? Acewar Yasmin, hibbe tace"wa zai faɗi? Sai dai ko Angel,' girgiza kai angel tai " a'a, a samu wanda yafi kowa hankali a cikin mu ya faɗa mana wanda yafi kyau,' ta yi maganar tana nuna musu majnun da idonta, dariya su ka saki gaba ɗayan su, Deeja tace da shi"Chinonso faɗa mana waya fi kowa kyau a cikin mu, yau zamu tabbatar da idan kana da cikakken hankali"
murmushi suka ga ya saki yana murmura idanuwanshi, hada ƙoƙarin miƙewa tsaye yana kallon fuskokin su, tsawon lokaci sun kasa kunne suna sauraron shi, yadda kasan me nazarin wani abu, har wani leƙa fuskarsu yake yi, a ƙarshe yace"Haris" shiru su ka yi, haris ko sai tiƙar dariya yake yi, itama Deeja murmushi ta saki,
Jamima tace"Ƙarya kake yi, ba haris bane yafi kyau, ba ka ga shi baƙi bane,"
Harara chinonso ya watsa mata, tare da ruƙe qugunshi, ya turo ciki gaba yana faɗin"ke ne kike ƙarya, harisu ba baƙi bane, Fari ne fat," waro ido su kai gaba ɗayan su suna kallon shi, Angel tace"Anya kuwa Majnun Ƙwaƙwalwarka tana aiki dai dai? Haris ɗin ne yafi kowa kyau kuma fari ne" jinjina mata kai yai fuskarshi a ɗaure yace"Eh mana, yafi kowa haske aciki ku, shi ne yafi kowa kyau" Mubeen na murmishi yace"anya haris ba wani abu ka yi mishi ba? Ko dai ka yi mishi ƙyafcen ido ne"? Haris na dariya ya ce"Ka tambaye shi mana sai ka ji idan ni ne nasa shi ya faɗi hakan"
Miƙewa mubeen yai tare da komawa gefen chinonso da ke a tsaye, ya duƙo yadda tsawon su zai dai dai ta"faɗa min wata irin barazana haris yai maka"? Ta6e baki majnun yai, ni bai min komai ba, gaskiya na faɗi yafi kowa kyau acikin ku, shine fari" fuskarshi a ɗaure yai maganar babu alamun wasa don shi har ga Allah gaskiyar shi ya ke gaya musu.
"Yau naga ikon Allah, wai dole sai ya ƙaryata abunda ya faɗi? Nifa na sani dama, haris yafi kowa kyau a cikin ku"! acewar Deeja, haris ya kar6e da cewa faɗa mu su dai, Ni ɗin kyakkyawa ne, da alama kishi su ke yi dani, '
ruƙo hannun Majnun mubeen yai tare da jan shi zuwa gaban Danish da ke zaune gefen gadonsa, Yace"yanzu faɗa min tsakanin haris da Danish wanene fari"? Jin muryarsu yasa Danish kawar da idon shi daga kan fuskar Angel, ya dawo da dubanshi akan fuskar chinonso daya ƙura mishi ido, har wani kashe ido ɗaya yake yi.
"Idan har ya kasa banbance waye fari acikin su, to kuwa dole mu zubda chinonsu Cikin Kwandon shara, don banga amfanin shi acikin mu ba, abincin da yake ci ma ya tashi abanza," parveen ce tai maganar, kowannan su ya saki murmushi, Angel tace"da alama ƙarya ta ƙare, Ya tasa Danish gaba sai kallon shi ya ke yi, yaƙi magana"
"Kai muke jira" acewar mubeen, girgiza kai chinonsu yai fuskarshi a hargitsa ya kalli mubeen'"to..ae na kasa ganewa, shima haris ɗin ya dawo gefen shi ya zauna, sai in banbance" Miƙewa haris yai tare da komawa gefen Danish ya zauna, Suka tasa chinonso gaba Akan saiya gano musu wanene fari acikin su, shifa bilhaƙƙi Haris fari ne, Ya dai ce musu Danish yafi kyau, matsalar shi ɗaya Baƙi ne wulik, Shiyasa Haris yafi shi kyau, wannan maganar ba ƙaramar dariya ta basu ba, Ga dukkan alamu bayan ta6in hankali da yake dashi Chinonso yana fama da matsalar Gani, yau sun tabbatar da hakan, tun da gashi ya tabbatar musu da cewa Danish yafi kyau, sai dai baƙi ne, har tambayarshi su ka yi shi fa wani kala ne, yace musu shima baƙi ne
Mutumin da ya ke albino, hasken ma ya wuce na lafiya, Amma yana kiran kan shi da baƙi, kusan mutun uku fararen Cikin su, su ka tambaye shi ya faɗa musu wani kala ne su, yace musu duk baƙaƙe ne. Ba ƙaramin nishaɗi su ka yi ba a ranar, Lokacin da dare yai, Kowannansu Ya canza kayan shi zuwa tsoffinsu, Wanda suka maida na bacci, Kafin suka haura saman gadajensu suka kakkwanta.
Gabriel ya kasa runtsawa Yana zaune tsakiyar gadon shi, Sarai Angel ta lura dashi, hakan yasa itama taƙi kwantawa tayi baccin, Haka zalika, Danishi yaƙi runtse idanuwanshi, Ga bacci yana ji amma yaƙi bari ya ɗauke shi, Saukowa tai daga saman gadonta, zumbur Danish Ya mike zauna, tare da kallon ta yace
"Angel where're u going, ba zaki bacci ba" yatsina fuska ta ɗanyi tare da kallon shi" Addu'a nake so inyi maku kafin in kwanta...." tunkan ta ƙarasa maganar taga ya sauko daga saman gadon shi, Ya ruƙo hannunta acikin nashi tare da cewa"Nima zan ta ya ki, mu yi musu addu'ar a tare" dariyar yaƙe ta sakar mashi"kai da baka iya ba, taya zaka iya taya ni mu yi musu addu'ar?
"Ni dai muje," duk yadda taso ta yi mashi wayau don ya koma ya kwanta ita kuma ta samu damar zantawa da Gabriel Ya hana hakan faruwa, Atare su ka bi gadajen su Hannu tana karanta musu addu'o'i tana tottofa musu saman bargunan su, hatta sarah da ke a kwance ƙasa sai da ta zuƙunna ta yi mata addu'a, kafin ta miƙe bayan ta kammala, ta tsaya a Tsaye tana satar kallon Gabriel da ya hana idon shi bacci tasan duk don saboda ita ne, Ganin tana kallon shi yasa Danish damƙar hannunta yaja ta har zuwa saman gadonta, fuskarshi a ɗaure yace"ki kwanta ki yi bacci," ba tare da ta yi mishi musu ba, ta hau saman mattress ɗin ta kwanta, tare da ɗaura kanta saman pillow, ' ta yi tsammanin zai haura nashi gadon ya kwanta amma sai taga ya zauna gefen gadonta, Ya tsareta da waɗannan kyawawan idanuwanshi nashi
"Why danish? What's going on? Why don't you go to bed? You're bothering me." A hasale tai maganar tana jifar shi da harara, cikin sanyin murya yace"idan kina so in yi bacci to ki fara yi, if not sai dai mu kwana idon mu biyu," muryarta a takure tace"hakan ma bazata faru ba," runtse idanuwanta ta yi, zuciyarta nata saƙa mata yarda zata yi mashi wayau, yayin da shi kuma Man ɗin Ya jingina bayanshi da bango idonshi akan Gabriel, Dake zaune tsakiyar bed nasa.
A hankali ta ɗan buɗe idanuwanta, ta saci kallon fuskar Danish, miƙewa tayi zaune, Jin motsinta yasa shi kallon ta
Yamutsa fuska ta ɗanyi tare da cewa"Zan shiga toilet ne," ruƙo hannunta yai acikin nashi"muje in raka ki" fusge hannunta tai fuskarta a ɗaure tace"Banaso, Ka zauna anan inje in dawo," bai damu ba, tun da yasan ita kaɗai zata shiga, zai zauna ne ya tsare Gabriel kada ya motsa, Saukowa tai daga saman gadonta ta nufi sashen toilet ɗinsu, tana jiyo muryar Shi yana bata umarnin kada ta daɗe acikin toilet ɗin, idan ba haka ba zai biyo bayanta.
ta amsa mashi da toh, tana shiga ƙopar sashen toilet ɗin, ta juyo tana leƙen Gabriel, Dama abunda ya kai ta kenan, tun kafin ta shiga ran shi ya bashi cewar ba wani abu zatai acikin toilet ɗin ba, za ta je ne don ta samu damar yin magana dashi, Satar kallon Danish yai, ganin ya ɗan lumshe idanuwanshi yasa shi yin saurin kallon ƙopar shiga sashen toilet ɗin, cikin sa'a ya hango angel tana ɗaga mashi hannu, A hankali ya janyo pillow ɗinsa da ya jingina bayanshi da shi, Ya rungume shi a ƙirjinshi, Ya sanya hannu yana ta6a zip ɗin jikin shi, ta ɗauki tsawon lokacin kafin ta fahimci abinda ya ke son nuna mata, buɗe ido Danish yai tare da saukowa daga saman gadon shi, Ya nufi sashen toilet ɗin, da sauri Gabriel yai mata alamar gashi nan zuwa, kamar walkiya ta buɗe toilet ta shige, Yana shigowa wurin, ya soma kiran sunanta"Angel! Angel!" buɗe ƙopar tai tare da fitowa tana yarfa hannunta data wanko shi da ruwa, Kallon shi tai aranta tace"Jarababbe kawai" a fili kuma tace"lafiya"?
"Na jira ne baki fito ba, shine nazo in duba ki" harara ta wurga mashi, kafin taja hannun shi, suka koma ɗakin, tace mashi"ka hau gadon ka, ka kwanta nima in kwanta a nawa, in yaso sai mu fuskanci juna" Ya amsa mata da toh, bayan kowannan su ya haura saman gadonshi, suka ci gaba da kallon juna, tun yana ganinta biji biji, har ya kai ga rufe eyes ɗinshi, tsawon mintuna ta fahimci cewa bacci ne yai awon gaba dashi.
Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali ta miƙe ta ɗauki pillow ɗinta, ta zuge zip ɗin ta curo ƴar takardar da Gabriel ya ajiye mata, ta buɗe ta cike da fargabar kada Ya farka, Saukowa tai daga saman gadonta ta nufi tsakiyar ɗakin nasu tana karanta wasiƙar, yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi, wani irin ruɗani ne ya bayyana akan fuskarta, Takasa yarda da abunda Gabriel ya rubuta mata, Shin dagaske ne ya haura tagar nan ya shiga cikin prison ba tare da wani abu ya same shi ba? To ya akai ita ta kasa shiga? Can kuma ta koma tunanin yarinyar da ya ce mata ya gani tana neman taimakon shi, Anya kuwa Gabriel ba ƙarya ya ke faɗa mata ba? Sai dai kuma abunda zai sa ta iya yarda da maganar da ya rubuta mata, na farko bai yi kama da maƙaryaci ba, sa'annan idan har dagaske ƙarya yake yi mata to taya akai yasan da Tagar da aka cire glass ɗinta, nannaɗe takardar tayi tare da ɗagowa ta kalli shimfiɗar Gabriel, Har yanzu bai kwanta ba idanuwanshi na akanta, sai da ta fara juyawa ta kalli Danish da ke bacci, taga bai motsa ba, kafin ta maida dubanta ga Gabriel, Saukowa yai daga saman gadon shi ya tunkareta, hannunta ya ruƙo acikin nashi, Yaja ta suka shiga sashen toilet ɗin su, saboda su samu damar tattaunawa da juna ba tare da Danish Ya farka ba.
Ba acikin toilet su ka shiga ba, acikin sashen suka tsaya, muryarta da alamun mamaki tace"Abun da na karanta acikin wasiƙar nan taka dagaske ne? Jinjina mata kai yai"tabbas dagaske ne angel, naso tun time dana haura tagar na dawo ciki in sanar da ke amma Danish ya hanani yin hakan, Nasan ke kaɗai ce zaki iya taimaka min wurin nemo ƴar uwata tun da kema kina nema taki ƴar uwar, kuma naji awurin ƴan uwanki cewa, kina da burin fita daga Cikin kurkukun nan, shiyasa na ƙara samin ƙwarin gwiwar tunkarar ki in faɗa maki,' Tun da ya soma magana Angel ta ke binshi da kallo mai tattare da tsantsar mamaki da al'ajabi, Shi dai gashi ba musulmi ba, amma wani iko na Allah, ya samu damar shiga prison ba tare daya fuskanci irin matsalar daga fuskanta ba, a lokacin da ta dira tagar, ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin daɗi taji ba, atlease ta samu wani mai ra'ayin son guduwa daga prison, idan su ka haɗa hannu dashi zasu iya sama ma kansu mafita.
"Angel kin yi shiru bai kamata muna 6ata lokaci ba, wannan ce damar da mu ke da ita, ta taimakon yarinyar nan, ita ka ɗai sai garari take yi acikin prison" fuskarshi da alamun damuwa yai mata maganar.
"Gabriel, ina kokwanto fa, zai yi wuya ace mutunce ita, may be barazana aka yi maka da ita don a tsorata ka, Nima time dana fita an tsoratar dani ta hanyar nuna min daddyna wasu haluttu munana suna cin naman jikin shi, aranar nasha wahala, ba don Allah yasa Danish yaje ya ɗauko ni ba, da shikenan tawa ta ƙare" girgiza mata kai Gabriel yai"Bana tunanin cewa anyi min barazana da itane, mutunce ita Angel I saw her from the top of the third floor. She was running, looking for help. fara ce kamar ke, tana da yawan sumar kai kalar naki, itama nata, Nannaɗaɗɗe ne harma yaso yafi naki yawa da nannaɗewa.......'
Tun da ya suffanta mata matashiyar yarinyar, Hankalinta yai matuƙar tashi, Ta zazzaro idanuwanta waje, La66anta na kerma ta furta sunan"BATOOL" domin kuwa a bayanin da ya yi mata kaf irin suffar batul ne,
"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Wlh inaji araina ƴar uwatace batul," tuni hawaye sun wanke mata fuskarta, jikinta ya kama kerma.