Kenza eBookz

Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 11

Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 11

Kurkukun kaddara book 1 Chapter 11: Kurkukun kaddara book 1 Chapter 11. Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, "Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne." Hannayenta…

3,370 words

Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, "Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne." Hannayenta ta sanya tare da zagayo da su ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa, "Daddy, to mu tashi daga mafarkin, Angel tsoro take ji." Tamkar ya fashe mata da kuka haka yake ji,

A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin davya fisgi ƙafarsa ba, ya ɗago da ita daga jikin ƙarfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan ƙafar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya ƙwammace ta mutu a cikin ruwan dacta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu ɗigon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su ƙona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin Angel sai kuka take yi, sautin motocin miyagun da suka biyo shi ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, Allah Sarki yana ji yana gani haka ya ɗaga Angel sama ya yi wurgi da ita, tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan mai zurfin gaske yana jiyo sautin kururuwarta.

Ba ƙaramin tashin hankali ba ne zai sa uba ya yi silar mutuwar ɗiyarsa.

Saboda tsabar kuka jikinsa har jijjiga yake yi, duk ya ji ya tsani kansa. Don tuni ya fitar da rai da rayuwa a cikin duniyar nan, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi, jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin wani irin jiri ne ya soma kwasar shi, nan take ya yanke jiki ya faɗi a mace.

A daidai lokacin suka ƙaraso da motocinsu, bayan sun yi parking sun kewaye shi, wasu gabza-gabzan samari ne suka fito, ƙirar Samudawa, baƙake wulik! Babu ɗigon imani a kan fuskokinsu, sun yi shigar bakaken kaya da alama bodyguards ne, a tare suka buɗe wa iyayen gidan nasu murfin motocin don su fito.

Abin ban mamaki, manyan mutanane dattawa, suna sanye cikin shiga ta mutunci wato shigar Hausawa, shadda har da malun-malun kai ka ce mutanen arziƙi ne. Koda fitowar su, ba su dora idonsu a kan komai ba sai a kan gawar Taj dake yashe cikin ciyayi.

Guntun tsaki ɗaya daga cikinsu ya ja, "Mala'ika ya riga mu ɗaukar ransa, ba haka na so ba."

Na gefensa ya ce, "Ban so ya yi salahar mutuwa irin wannan ba, amma duk da haka ba mu makaro ba, tun a nan za mu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun Munkar da Nakir."

Tuntsirewa suka yi da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma suka ɗaure fuskokinsu. Ɗaya daga cikin manyan mutanen ne ya juya tare da kallan ɗaya daga cikin miyagun da suka zo da su, cike da ba da umarni ya ce, "Miƙo mini galon ɗin fetur tare da lighter." A hanzarce wanda ya yi wa magana ya nufi motocinsu.

"Maganin masu kunnen kashi ke nan, an gaya musu shiga gonarmu abuvne mai sauƙi." Bai kai ƙarshen maganar ba, aka miƙo masa galon din fetur yasa hannu ya kar6a, cire murfin ya yi tare da zazzage masa fetur ɗin a jikin rigarsa, sharkaf suka wanke shi. Dalilin da yasa za mu ƙona shi, saboda gudun mu bar wata hujja da zai sa a zarge mu.

Ba su ƙyasta lighter ɗin ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin ƙanƙanin lokaci, wutar tacinye shi ƙurmus.

*To Jama'a Zaku ga nasanya Farkon labarin nayi hakan ne don in tariyo maku daga inda zamu tashi fatan an waye ni*

*waɗan da su ka shirya yin payment zasu iya farawa, 08103884440 cikin wata mai zuwa free pages book one zai ƙare, Ina yi ma kowa fatan alkhairi, sai mun haɗu a next page in Allah yakai mu da rai da lafiya*

*💋Boss Bature✍️💋*[9/22, 7:09 PM] +234 803 216 9283: *💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

_daga alƙalamin Boss Bature✍️_

*Dedicated To Aunty Kubra❤*

*E8*

Hasken rana ne ya haske fuskarta, sakamakon windown bedroom ɗinta da ta bari a buɗe, dogon numfashi ta ja tare da buɗe kumburarrun idanuwanta waɗanda suka yi luhu-luhu da su sun ƙanƙance saboda kukan da ta sha a daren Jiya. Kwance take a saman gadonsu, jikinta duk ya yi nauyi sam ta kasa motsawa, gefe da gefe na gadon ta kalla don ta ga ko Uzair ya dawo. Ras ta ji gabanta ya faɗi ganin still bai dawo gidan ba, hankali a tashe ta yunƙura ta miƙe zaune tare da wurga idanuwanta kan agogon bangon, ƙarfe tara na safe ko sallar Asubahi ba ta samu ta yi ba, saboda nauyin barcin da ya ɗauke ta.

Siraran hawaye ne suka gangaro daga cikin kwarmin idanuwanta har izuwa saman kuncinta, masu ɗumi, harshenta ta sanya ta ɗan lashi gefen bakinta inda ruwan hawayen ya gifta.

Daƙyar ta samu ta lalla6a ta sauko daga saman gadon, still riga da wandon jiya ne a jikinta, kanta babu mayafi, sumar kanta ce da ta zubo mata ta ko'ina ta yamutse.

A hankali take tafiya harta shige toilet, after some minutes ta fito daga cikin toilet ɗinta, da alama alwala ta yi, lemar ruwa ce a fuskarta da hannayenta.

Cikin wani irin yanayi na jin faduwar gaba, da tsinkewar zuciya, ta nufi closet ɗin kayan su, buɗewa ta yi tare da zura hannu ta ɗauki hijab ɗinta, ta sanya a jikinta.

Saman dardumar dake shimfiɗe ta tsaya, a tsanake ta kabbara sallah, cikin nutsuwa ta soma yin ibadarta.

Bayan ta kammala, zama tayi saman dardumar tare da ɗaga hannayenta Cikin harshen larabci ta soma yin addu'o'inta daga ƙarshe ta rushe da matsanancin kuka tana faɗin. "Ya Allah Ka dawo mun da mijina lafiya,Ya Allah ka karemun shi aduk inda yake! inaji araina kamar wani mummunan abu ne ya faru da shi, Uzair bai ta6a tafiya batare da sanina ba. Amma jiya ya tafi ya barni in the midnight without my knowledge," Sosai take yin kukan ta jima, kafin ta yanke shawarar zuwa Wurin taj donta tambaye shi idan Sunyi waya da Uzair."

Miƙewa tayi da sauri, ta fito daga Cikin bedroom ɗinta, ta nufi hanyar fita daga falon, a bakin gate ta samu maigadin gidanta zaune saman benci yana sauraron radio.

Tunda ya hango ta ya yi saurin ajiye radio ɗin saman bencin ya mike ya tunkare ta, "Barka da safiya hajiya, kun tashi lafiya."Ba ta amsa mashi sallamarshi ba, saboda ba ta acikin natsuwarta,

"Inaso zanje wurin taj ne, may be sunyi waya da uzair, wlh nadamu sosai nakasa samun natsuwa baba, inaji kamar wani abu ya faru da shi," Tana magana hawaye na fita daga cikin idanuwanta.

Tsananin tausayinta ya kama baba maigadi, tunda yake bai ta6a ganin hawayen Aneelerh ba, sai a daren jiya da kuma yau, ya lura da tashin hankalin dake akan fuskarta.

Cikin sanyin murya yace"Kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, in sha Allah uzair yana cikin ƙoshin lafiya, babu abin da zai faru da shi."

Gyaɗa mashi kai ta yi tare da wuce shi ta nufi gate ɗin, Hannu tasa ta buɗe ƙopar jikin shi ta fuce daga cikin gidan.

Girgiza kai maigadi ya yi ji yake da a ce yana da halin da zai iya taimakon Aneelerh a yau daya taimaketa, abin da ciwo ka ga mutumin daya saba kyautata maka a cikin wani ƙunci na rayuwa kuma baka da yadda za ka iya taimakon shi, komawa yayi jiki asanyaye ya zauna saman bencin.

Bayan fitar Aneelerh, kai tsaye ta nufi gidan Taj dake a jikin gidansu, tun abakin gate ta hango maigadin gidanshi a tsaye ya jingina bayan shi jikin gate ɗin, fuskar shi duk a harmutse da alamun damuwa atattare da shi, hakanan taji gabanta yayi wani irin mugun bugu ras!

Ƙarasawa inda yake tsaye tayi muryarta da fargaba atattare da ita ta ce, "Assalamu alaikum"

Tunkan takai ƙarshen maganar taga ya ɗan firgita, sai daya kalleta tukunna Yaɗan saki fuskarshi yace"wa'alaikum salam, malama Aneelerh, in ce ko lafiya?''

Hawaye ne suka sake wanke fuskarta, cikin shessheƙar kuka ta ce, "Har yanzu uzair bai dawo ba, yanzu ma zuwa nayi wurin taj, don inji idan ya kira shi awaya," Tana kai ƙarshen maganarta baba maigadi ya ce, "Innallahi Wa'inna Ilaihir raji'un!"

A ruɗe ta ce, "Baba lafiya?" Cikin tashin hankali ya ce, "ƴar nan tun jiya na gaza samun kwanciya hankali, ko runtsawa ban yi ba, saboda damuwa, jiya bayan kin zo neman Taj, kin tafi na shiga daga Cikin ɗakina na kwanta, har bacci na fara bacci sama sama, can cikin dare wuraren ƙarfe ɗaya da rabi, ina kwance na ji fitar mota daga cikin gidan nan. A firgice na farka na fito daga ɗakina, koda na fito naga gate a wangale, na leƙe banga komai ba, na dawo na duba naga babu motar taj da yake yawan fita da ita, a nan na gane cewa shine ya fita cikin motarshi."

Tunda ya soma magana Aneelerh ta dafe ƙirjinta da tafin hannunta, ta zazzare ido tana kallon shi,

"Na yi mamakin ina Taj ya tafi batare daya sanar dani ba! domin kuwa tunda nake aiki a ƙarkashin shi bai ta6a lekawa koda ƙofar gida batare da sanina ba, amma sai gashi jiya tsakar dare ya fuce, kuma abun da ya ɗaure mun kai, ba shi kaɗai ya tafi ba. Hada ANGEL!" A gigice Aneelerh ta shiga ambaton Innallahi Wa'inna Ilahir raji'in! Na shiga Uku! Wai meke faruwa ne? Wayyo Allahna!" Gabaɗaya ta bi ta ruɗe, shi kan shi baba maigadi da ya sanar mata, sai da yayi danasani ganin yadda ta daura hannayenta a saman kanta tana zabga salati.

Juyawa tayi da gudun gaske Ta koma Cikin gidanta, A lokacin malam Garba maigadinta Yana zaune saman bencin yaga shigowarta a guje, har yana tambayarta lafiya, amma bata saurare shi ba.

Hankalinshi ya ƙi kwanciya, Miƙewa ya yi da nufin yaje su yi magana da tajo,yana ƙokarin fita daga cikin gidan, baba maigadin gidan Tajo, ya tura kofar gate ɗin, suka yi kicibus da juna.

"Wai meke faruwane ɗan ladi"malam garbane yayi mashi tambayar fuskarshi a yamutse.

Baba maigadi ya ce, "Tun ɗazu naso in zo mu yi magana. Amma damuwa ta hana ni, lamarin dai babu daɗin ji." Nan ya kwashe duk abin da ya faru na tafiyar Tajo tsakar dare ya sanar da shi."

Malam Garba ya hauyin sallallami, hankalinshi duk ya tashi a rude ya ce, "Indai kuwa haka ne akwai matsala. Ya kamata a sanar ma Ƴan sanda don a san abin yi tun kafin lokaci ya ƙure mana"!!

Jinjina kai baba maigadi ya yi" ni ma abun da nake tunani kenan, amma mu ɗan ƙara jira kaɗan zuwa anjima"

"Shikenan zan koma bakin aikina, zuwa anjima idan ba wani labari game dasu sai muje police station ɗin" a cewar ɗan ladi, daga haka suka yi sallama da juna. Ya koma gidan da sauri don ya barshi a buɗe bakowa

Aneelerh kuwa bayan shigarta Cikin gidan. Afujajen ta nufi bedroom ɗinta ta shige, jikinta na kerma ta ɗauki wayarta dake ajiye saman bedside drawer,

Call logs ta shiga ta dannawa numbar da tayi saving da Abie kira,Tana fara Ringing, Aka ɗaga wayar, muryar babban mutuncine mai cike da kamala Ta karade kunnuwanta, "Assslamu Alaikum daughter..." Tun kafin ya kai ƙarshen maganar, Aneelerh ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita..."

Muryar Abie a ruɗe ya shiga kwala mata kira." Aneelerh lafiya kike kuka meya faru? Waya ta6a mun ke? ki buɗe baki ki yi mun magana!"

Sai da ta yi kukan mai isarta, sannan ta soma magana cikin shessheƙar kuka"a...Abie..Uzair da Taj.." katse ta ya yi da cewa."me ya faru dasu? Wani ya rasu ne' "A'a, tun daren jiya Uzair ya bar gida wuraren ƙarfe tara, shi kuma Taj ya bar gidansa karfe ɗaya da rabi na dare, kuma ya tafi tare da Angel. Babu wanda yasan meya faru dasu, kuma dukansu layinkan wayoyinsu akashe, Abie ina cikin matsanancin tashin hankali."

Lamarin ya girgiza abie sosai," Muryarshi cikin sigar lallashi ya ce, "ki kwantar da hankalin ki aneelerh, In sha Allah babu abun da ya faru da su, yanzu zan yi waya da uncle ɗinki, ki ɗan ƙara haƙuri." Cikin shessheƙar kuka ta ce"To Daddy, saina jika "ya ce" ki daure ki ci abinci, na san ba ki ci komai ba" Amsa mashi ta yi da to kafin suka yi sallama ta kashe wayar. Saman gado ta koma ta zauna zugudun cikin zullumi, salla kadai ke tada ta.

Wuraren ƙarfe huɗu na marece, tana kwance magashiyan fuskarta ta kumbura tayi suntum, tunda tayi sallar la'asar bata cire hijabin jikinta ba,

jiniyar motor ƴan sanda tajiyo daga waje Wii! wiii! ras! taji gabanta ya faɗi, fargabarta kada ace gawar Uzair kota taj suka kawo Cikin gidan,

A hanzarce ta miƙe, da gudu ta fito daga cikin bedroom tana sauko ƙafarta cikin falon, adai dai wannan Lokacin mahaifinta Alhaji Muhammad falgore ya doko sallama, Yana sanye Cikin shiga ta alfarma, Shaddace fara tass taji guga, tare da malun malun, kanshi Na sanye Cikin hula, Bayan shi kuma Ƴan sanda ne su huɗu sanye cikin kakin su, ɗaya daga Cikinsu Uncle dinta ne kaninta mahaifinta me ruƙe da muƙamin dco(Divisional Crime Officer),Atare dashi akwai Ic (inspector crime) sai kuma Ipo(Investigation Police Officers) Su biyu ne ɗaya mace ɗaya Namiji masu tsayi da jiki ba laifi a launin fata baƙake ne,

Zuba masu ido aneelerh tayi tana kallonsu batare da kiftawa ba, tasan aikin mahaifinta ne, mutunne mai ɗaukar abu da mahimmanci babu wasa a lamarinshi, Sam ba ta yi tsammanin zai yi report din case din wurin ƴan sanda ba, Sai gashi ɗungurugum ya taho dasu Gidan,

Ganin ta yi tsaye tana kallonsu yasa Shi yi mata gyaran murya yace"Daughter Kece kika koma haka"? jin haka yasa ta nufe shi da sauri, tunkafin ta ƙaraso ya buɗe mata hannayen shi ta faɗa a kirjin shi, ta fashe ma shi da kuka, duk jikinsu yayi sanyi, Hannu yasa yana shafa bayanta cikin sigar lallashi, kafin ya kalli uncle din nata yace dashi Bismillah su zauna"wuri suka samu kowa ya zauna saman sofa, Bayan ya raba jikinshi daga na aneelerh yace itama ta zauna, atare dashi suka zauna,

Uncle Bash ƙusa yace"Aneelerh Why tun daren jiya daya fita baki sanar damu ba"?

Cikin shessheƙar tace"Ae nayi tunanin zai dawo kafin da safe"

Jinjina kai yayi"okey, yanzu ki natsu ki faɗa mana taya akai yabar gidan without your knowledge"?

Ƙoƙarin buɗe baki tayi donta kora masu jawabi kamar yadda suka buƙata, nan take Wani irin yunƙurin amai yazo mata, da sauri ta miƙe daga saman sofa din ta watsa aguje zuwa bedroom ɗinta,

Dco ya kalli Ramlat Jami'ar binciken da suka zo da ita yace da ita tabi bayan aneelerh, amsa mashi tayi da Okey sir, Kafin ta miƙe ta bi bayan aneelerh cikin bedroom ɗinta,

Tana shiga tajiyo Sautin ƙaƙarin aman da aneelerh keyi acikin toilet, kaitsaye ta taka izuwa cikin toilet ɗin, Agaban Sink ta samu aneelerh tana ta kwara amai tamkar ƴar hanjin cikinta zasu fito waje,

Ƙarasawa tayi har zuwa bayanta, ta sanya hannunta tana ɗan bubbuga bayanta, Tana yi mata sannu,

Bayan ta kammala yin aman, Ramlat ta kunna mata fanfo, ta wanke bakinta tass, Takai hannu jikin tissue holder ta yago kaɗan ta miƙa ma aneelerh ta goge mouth ɗinta, daga haka ta ruƙo hannunta suka fito daga Cikin toilet ɗinta "Sorry dear ki kwantar da hankalinki, in sha Allah we will try our very best wurin ganin mun gano inda mijinki ya ke,"acewar Jami'ar binciken,

Aneelerh dake ta faman fitar da numfashi mai ɗumi tace"Bana jin daɗin jikina, tun jiya banci komai ba, kuma bana jin zan iya cin wani abu,"

Ramlat tace"Ki daure kici, lafiyar ki muke buƙata, domin kuwa idan ba lafiya atare dake taya zamu iya samun haɗin kanki wurin yin investigation ɗinmu"?

Takai ƙarshen maganar a lokacin sun dawo Cikin falon, Hankalin Dco da na sauran jami'an ya dawo kansu, mahaifinta kuwa jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba, ganin yadda ɗiyar shi ta rame, tamkar ba neelerh ɗinsa ba,

A gefen abie ta zauna tare da kwantar da kanta saman kafaɗar shi, Ramlat Ta kalli dco tace"Sir, bata da koshin lpy, kuma ta sanar dani cewa tun jiya bata Ci komai ba,"

Uncle bash yace"Idan har bata ci abinci ba, ba zamu iya samun bayanan da muke bukata ba awurinta," Yayi maganar eyes dinshi akan Abie, kafin ya mayar dasu kan Ramlat yace"ki duba frigde nasan baza a rasa abunsha ba, Ki ɗauko mata tare da ruwa me sanyi"Amsa mashi tayi"okey sir" kafin ta juya ta nufi fridge ɗin dake A falon"

Hanmu tasa ta buɗe frigde din, Lemuka ne a jere masu sanyi, hada fura da youghurt, fresh milk ta dauko mata tare da ruwa"ta ruƙo bottles din a hannunta ta dawo ta ɗaura su asaman C table din dake agaban sofa din da aneelerh take,

Uncle bash yace"Aneelerh ta shi kisha,"batare da musu ba, Aneelerh ta mike zaune, Takai hannu ta ɗauki milk ɗin ta buɗe ta kwafa abakinta, ta shiga ɗaɗɗakarta, makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat!!

Abie yace"Ki sha a hankali, kada ki shaƙe" janye bottle din tayi daga bakinta tana faman sauke ajiyar zuciya, lallai ba ƙaramar yunwa take ji ba, bayan ta ajiye milk din Abie ya dauki bottle water me sanyi ya mika mata, hannunta na kerma ta buɗe mufin ta kwafa abakinta, A hankali take shan ruwan harta kammala, Sai gashi ta ɗan samu natsuwa, Uncle bash yace"Aneelerh kiyi mana bayanin yadda komai ya faru a daren jiya, muna sauraronki"

Ganin yadda zufa ke keto mata, abie yace ta cire hijabinta"hannu tasa ta ɗebe hijabin, dama akwai Kallabin data ɗaure kanta da shi,

A tsanake ta soma Yi masu Bayani tiryan tiryan "Ji wuraren ƙarfe tara, nafarka ban samu uzair a saman gado ba, nayi tsammanin ko ya shiga toilet ne amma ko da na duba baya a ciki, na yanke shawarar zuwa na tambayi megadi,koda naje wurinshi yace mun Yaga lokacin da Uzair ya fita acikin motarshi, kuma har magana sunyi da shi kafin tafiyar shi, koda jin haka na dawo cikin gida na ɗauki wayata na kira layin uzair tana ringing amma uzair bai ɗaga ba, a ruɗe na ajiye wayar na fito na nufi gidan taj, ina zuwa na shiga gidan, A falo nayi mashi sallama, ya fito daga ɗakin shi, harma yayi shirin kwaciya, nake faɗa mashi Game da tafiyar uzair ƙarfe 9 na dare na farka banganshi ba, Nayi tunanin ko ya kirashi awaya, saboda kusancinsu dana sani, Uzair zai iya 6oye mun abun amma bazai iya 6oyema Taj ba, Shiyasa na tambaye shi,A wannan lokacin taj yace na jirashi ,Zaije room dinshi ya kira shi awaya, na tsaya ina jiranshi, koda ya dawo na tambaye shi ya kirashi,yace mun in kwantar da hankalina duk inda yake ayanzu yasan yana akan hanyar dawowa ne, ba don na yadda da kalamanshi ba, na dawo gida zuciyata duk a harmutse na kwanta, Ko a daren sai da taj ya kira layina, ya ƙara kwantar mun da hankalina, a wannan yanayin bacci yayi awon gaba dani,

Shiru ta ɗanyi tana mayar da numfashi, kafin taci gaba da cewa"da safe na farka wuraren ƙarfe tara, still uzair bai dawo ba, Nan ma hankalina ya ƙara tashi, Na yanke shawarar zuwa Wurin taj don inji idan sunyi waya da uzair, koda ace ya kirashi tsakar daren jiya, Ina fita daga gida na nufi gidan taj, tunkafin ma naƙarasa naga baba maigadin gidan atsaye ya jingina bayanshi jikin Gate din gidan fuskarshi da alamun damuwa atattare da ita..............."Komai daya faru saida aneelerh ta sanar dasu, lokacin da aneelerh ta kammala zayyana masu komai, Lamarin yayi matuƙar girgizasu, ipo Yace"akwai matsala, Uzair ya fita gida ƙarfe 9 na dare, Shi kuma taj ya fita tare da ƴarshi ƙarfe ɗaya da rabi nadare? tabbas wani Babban al'amarine ya afku"

Ramlat tace"Kuma dukansu atare da wayoyinsu suka fita"? Aneelerh tace"Shi uzair da wayarshi ya fita, Amma shi Taj banda masaniya akan hakan"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull