Kenza eBookz

Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 24

Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 24

Kurkukun kaddara book 1 Chapter 24: Kurkukun kaddara book 1 Chapter 24. Cikin shessheƙar kuka tace"Idan ka ta shi ka kashe ni dan Allah, kada ka barni da…

3,362 words

Cikin shessheƙar kuka tace"Idan ka ta shi ka kashe ni dan Allah, kada ka barni da rai na, meyasa zai ce na ɗauki wuƙa? Ina ruwan shi? Idan har bai shiga hurumina ba ni zan shiga nashi ne"? Ta yi tambayar a ƙule, Batool tace"ban goyi bayan wani a cikin ku ba, Amma laifin danish nafi gani, meyasa za ka tona mata asiri don ta ɗauki wuƙa? Menene naka aciki? Juyawa ta yi kan angel'ke kuma angel baki kyauta ba, kalli yadda kika raunta shi, sai kace ba ɗan uwanki ba...."tunkafin takai ƙarshen maganar angel tace"danish bazai ta6a zama ɗan uwana ba, bana son shi bana ƙaunar ganin shi," Jinjina kai batool ta yi"its okey, daga yanzu zan shiga tsakanin ku, kada wanda ya ƙara shiga hurumin wani ina fata hakan ya yi," Javed yace"idan ma suka ƙara ni da kaina zan sanar ma tsohuwa a ɗauki mataki akansu," daga haka Haris da su mubeen suka kama hannun danish su kayi mashi jagora zuwa saman gadonshi, kwanciya saman gadon ya yi bawan Allah har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi, shifa bakomai yasa ya tona ma angel a sirin ta ɗauki wuƙa ba, face sanin irin tsanar da tayi mashi, tsoron shi kada ace shi zata yanka da wuƙar wannan dalilin ne yasa shi tona mata asiri, ashe da rabon yaci na jaki a hannunta, Miƙa mata hannu azeeza ta yi"ki tashi muke ki kwanta, ki huta" sai da ta ɗanyi jim kafin ta ruƙo hannun azeeza ta miƙe, saman gado ta koma ta zauna, hawaye sha6a sha6a akan fuskarta, danish ya tarwatsa mata plan ɗinta, taji takaici kamar ta sanya pillow ta taushe ma shi fuska haka take ji, "Angel me zaki yi da wuƙa"? batool ce ta yi mata tambayar, ɗagowa angel ta yi tare da kallonta, tana a tsaye gefen gadonta, Girgiza kai ta ɗanyi"babu komai, kawai inaso na mallake ta ne," ɗan zaro ido batool ta yi"karfa ace wani kike harin kashewa a cikin mu" cikin zolaya ta yi mata maganar, Cikin sanyin murya angel tace"a'a batool bazan iya kisan kai ba, ni kawai naso ace na mallaki wuƙar," "Da ace kina shiri da danish, da ya aro maki wuƙar shi," da mamaki angel ta kalle ta tare da cewa"yana da wuƙa"? Jinjina mata kai ta yi eh, akwai wata ƙaramar wuƙa da yake amfani da ita wurin datse gashin kan shi, tsohuwa ce ta bashi wuƙar lokacin da ya ta6a tambayarta yana so ya rage tsayin sumar kanshi, shi ne ta ba shi wuƙar to bai mayar mata da ita ba, har yau tana nan a wurin shi," Dafe kai angel ta yi tare da satar kallon danish dake a kwance saman gadonshi, da alama bacci ya yi awon gaba dashi, yadai sha wahala, "Ga samu ga rashi" ta ambaci hakan acikin azuciyarta, tasan koda me take yawo danish bazai ta6a ara mata wuƙar shi ba Kallon batool ta yi"kinsan inda yake 6oye wuƙar" kallon sama batool ta ɗanyi da alama tunani take yi, can tace"a ƙarƙashin katifar gadonshi naga yana 6oye ta, Angel tace"ki taimaka kice ya ara maki ita a matsayin ke zakiyi amfani da ita, Ɗan zaro ido batool ta yi"ae bai yadda ya fiddo da wuƙar nan, kaifi ne da ita tana da haɗarin gaske, kona tambaye shi bazai bani ba, saboda yasan ba abun da zan yi da ita," Jinjina kai angel ta yi"shikenan na haƙura" daga haka bata kuma cewa komai ba, ta koma ta kwanta amma fa bawai ta haƙura bane, a can cikin zuciyarta tana shirya yadda zata sace wuƙar danish batare da sanin shi ba, da wannan tunanin ta yini da shi kuma ta kwana,

A daren yau ta kammala shirya yadda zata ɗauke wuƙar, kowa ya yi bacci saman gadonshi, duk sun lullu6e da bargunansu, angel ce kaɗai idonta biyu tana kwance idonta na fuskantar ceilling duk da duhu babu wadataccen haske saina fitilun ɗakinsu da suka kunna,

"Lokaci ya yi da zan tashi inje saman gadon danish in ɗauke wuƙar sa," acikin zuciyarta ta yi maganar, tana ƙoƙarin miƙewa tajiyo takun tafiyar mutun acikin ɗakin nasu, da sauri ta koma ta kwanta cike da fargabar wanene a dai dai wannan lokacin ya faɗo masu ɗaki, Ƙyalla ido ta yi daga kwancen da take tana satar kallon inda take jiyo sautin tafiyar, kaskon turaren wuta ta hango a hannun mutumin dake zarya cikin ɗakin nasu, wani irin baƙin hayaki ke tashi daga cikin kaskon, kamar ana turara turaren wuta, Mutumin dake ruƙe da kaskon turaren wutar, jikin shi na a sanye cikin doguwar riga me hula launin ja, rigar har ja take ƙasa, Kasa kunne angel tayi tana sauraron muryar mutumin dake magana, kamar muryar tsohuwa sai dai bata iya tantance da wani yare ake magana ba, wani irin gu6ataccem yare mara daɗin ji, Nan fa hankalin angel ya ɗan tashi, xufa ta wanke fuskarta, duk ta sha jinin jikinta, tsoro take ji kada ace wani mugun ne yazo cutar da su, Bata kai ƙarshen zancem zucin nata ba, ta hango mutun yana tafiya a bakin gadajen su Hannah, yana tafiya yana hura masu hayaƙin zuwa saman jikin su, Da sauri angel taja bargo ta lullu6e fuskarta, acikin zuciyarta tana ambaton la'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalamin," lokacin da mutumin yazo saitin gadonta, da sauri ta sanya tafin hannayenta duka biyun ta toshe bakinta da hancinta, duk don saboda kada hayaƙin ya samu damar shiga jikin ta, Tana jiyo takun tafiyar mutumin yadda kasan takun tafiyar jaki, Lokaci ɗaya tadaina jin takun tafiyar da kuma surutan da mutumin ya ke yi, da sauri ta ya ye bargonta, tabi ko'ina da kallo bata ga kowa ba, alamar mutumin ya tafi, sai dai hayaƙin daya turara masu har yanzu bai gushe ba, Saukowa angel tayi daga saman gadonta, Zuciyarta cike da ruɗani, ko wanene mutun nan daya zo masu a tsakiyar dare, sanye da jajayen kaya? Turaren menene yake hayaƙa masu a cikin ɗakinsu da kuma saman jikin su? sam bata yadda da hayaƙin nan ba, tafi tunanin wani mugun abunne aka turara masu, Tunawa ta yi da surori da kuma addu'o'in da malaminsu na makatantar islamiyya ya ta6a koya masu yace su yawaita karansu domin neman kariya daga sharrin mutun sharrin aljan da duk wani abun cutarwa, "Zan tai taimaka masu, saboda basu da maiyi masu addu'a, a kullum in na kwanta ina bacci, daddyna yana yi mun addu'a, su kuwa basu da iyayen da zasu yi masu addu'a" acikin ranta tayi maganar Kamar yadda mutumin nan yabi ko'ina na ɗakin yana turara Masu baƙin hayaƙin nan, itama haka ta soma bin kowace kusurwa ta ɗakin nasu tana karanta Ayatul kursiyyu, da amanar rasuli, Suratul mulk, Suratul kafiroon, Suratul ikhlas, falaqi da nasi, duk in ta karanta kowannan su Saita maimaita, daga bisani tabi kowani gado tana tottofa masu addu'oin saman bargunan da suka lullu6a da shi, daga kan gadon hanna ta faro xuwa gadon mubeen har zuwa gadajen su batool, tana zuwa kan gadon danish taja guntun tsoki zata wuce, sai kuma taji aranta kamar bata kyauta ba, don me zata yi ma kowannan su addu'a amma shi ta kasa yi ma shi saboda me? Lafin me ya yi mata? shiru ta yi tana tunani, menene ribar ta idan taƙi yi mashi addu'a,

Har ta kusa wuce gadon shi taja da baya ta koma tare da shiga daga gefen gadon, ranƙwafawa ta ɗanyi saitin fuskarshi ta soma karanto addu'o'in bayan ta kamalla ta tottofa mashi saman fuskarshi, kamar daga sama taji an damƙi hannunta, a razane ta kalle shi ashe ya farka, muryar shi a disashe yace"tsanar takai har ki zo kan gadona kina tofa mun miyau asaman fuskata"? Zuba ma shi ido angel ta yi batare da tace Furta komai ba, tama rasa bakin magana, yadda ya yi mata maganar ita kanta ta yi mamaki sai kace ba wannan mai jin shakkartata ba, bakomai yake jima tsoro ba, face wannan kalmar da take faɗi na cewa zata tofa ma mutun charman dudu Cikin shi ya kumbura, tuna wannan yasa shi ƙara tsorata, shi kanshi baisan yana da ƙwarin gwiwar yi mata magana irin haka ba, tsawa ya ɗanyi mata tare da cewa"Ba ki ji ina magana ba"? Still ta yi ma shi shiru saboda bata jin zata iya faɗa mashi cewa addu'a take yi mashi, don ma kada yaji kamar tana ƙaunarsa ne, Ganin ta yi mashi shiru ya ƙara har zuƙa, A tsananin tsorace Ya damƙo ƙasan rigarta da ƙarfi da niyar ya goge abunda ta tofa ma shi asaman fuskar shi, Cikin rashin sa'a ya janyota gaba ɗaya ta faɗa saman jikin shi..................🥱

(Nasha wahala wurin haɗa page ɗin nan, Jiki duk ba lafiya, To jama'a Mu haɗu Next page on monday in Allah yakaimu da rai da lafiya) Game neman ƙarin bayani 08103884440) Boss Bature ce✍️[9/22, 7:10 PM] +234 803 216 9283: *💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*Daga alƙalamin Boss Bature✍️*

*Dedicated to Aunty kubra❤*

*Gargarɗi!!!*

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!_

E16-17

💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* 📦

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano* *Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki* *Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida* *Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso* *Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano* *Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* http://wa.me/+2347069711327

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*

dukkan ilahirin jikin shi rawa yake yi, kusan suman kwance ya yi saboda tsabar tsoratar da ya yi jin Angel saman jikin shi ɗungurugum, zuciyarta har wani tafarfasa take yi saboda tsabar fusata, a rayuwarta ta tsani jikinta ya haɗu dana ɗa namijin da ba daddynta ba, kamar ta haɗiyi zuciya take ji, tayi Niyar idan ta ɗago ta kwashe shi da zazzafan mari, Sai dai wani yanayi da ta tsinkaye shi a ciki ya yi silar dakatar da ita, lokacin da jikinta ya haɗe da nashi wani irin zafi taji rau tamkar hucin garwashin wuta, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai, ta fahimci cewa baida ƙoshin lafiya, da alamun zazza6i attare dashi numfashinsa kanshi da hucin zafi yake fita, gaba ɗaya jikin nashi a raunace yake, Ga fargabar angel dake a kwance saman shi, yasha jinin jikinshi a tsorace yake da tsiwatarwa, baiso ta tayar mashi da lalurarshi

daddagewa tayi tare da yunƙurawa ta ɗago daga jikin shi, tarwatsastsiyar sumar kanta ta sauka har saman wuyan shi, a raunace ta kalli kyakkyawar fuskarshi, sama sama yake numfashi ya lumshe sexy eyes ɗin shi bai kai ga datse su ba, shima ɗin ita yake kallo, farar fatar wuyan shi tabi da kallo, ta ko'ina Jan tabon yakushin da ta yi ma shi ne,

Sun ɗauki tsawon lokaci A saman gadon Batare da wani ya furta wata kalma ba, idanuwansu acikin na juna, Jira yake ya ga wani Irin hukunci zata yanke mashi don yasan ba ƙyale shi za ta yi ba, tana iya cewa xata karanta mashi charman dudu, Cikin shi ya kumbura,

saukowa ta yi daga saman gadon nashi jikin ta duk ba daɗi, Sai yanzu ta lura da irin illar da ta yi ma shi, tana zargin kanta da alhakin Ciwon nashi, Ji take kamar taje ta faɗa ma tsohuwa cewa baida lafiya, amma ta kasa sam ba ta so yasan ta damu dashi, kuma ba ta son taje wurin tsohuwa saboda tsanar matar da ta yi,

zuciyarta a karaye ta koma saman gadonta ta kwanta, Ita kanta tasan bazata Iya runtsawa ba, Saboda zullumin rashin lafiyar danish, gani take kamar idon ta rufe idanuwanta zata farka ta taras da gawarshi ne, tana da hanyoyin da zata iya taimaka mashi sai dai bazata iya ba, saboda batason Raini ya fara shiga a tsakaninsu,

"I don't know why I'm worried about him," ta ambaci hakan acikin zuciyarta tare da juyawa don ta saci kallon shi, a kwance yake kanshi saman fillow, idon shi biyu ya yi lamo yana kallonta,

Gyara kwanciya tayi Ita ma ta fuskance shi, don yau taci alwashin bazata bari ya runtsa ba, kodan kada yayi bacci daga nan ya zarce zuwa barzahu, zullumin da take yi kenan,

Ganin yaƙi daina kallonta yasa ta ɗan ɗaure mashi fuska tare da cije lower lip ɗinta, ƙasa ƙasa da murya tace"Stop looking at me or else i will poke ur eyes" ta yi maganar tana kwatanta mashi yadda zata zungure ma shi idonshi da yatsan hannunta, har wani lumshe ido ya yi, tamkar yaji saukar yatsan nata acikinsu,

Slowly ya kuma ware manyan idanuwan nashi akan fuskarta,

Ƙura ma juna ido su kayi kallo na ƙurulla, ta jima tana mamakin wani abu atattare da prisoners ɗin da take atare dasu, gaba ɗayansu babu mummuna acikinsu, sam ba su yi kama da ƴa'ƴan malam shehu ba, sunfi kama da rainon madara, ƴan gidan Mommy da daddy, Expecially danish da Batool da Azeeza Hasken fatarsu sam bana baƙar fata bane, Kamar dai ita da take half cast, Launin fatar Su Hanna da su javed Dukansu irin na ya'yan Hutun nan ne, Ko'ina Aka samu kyawawan yaran nan? Zaiyi wuya su kasance ya'yan talakawa ne , Sai dai irin ƴa'ƴan hamshaƙan masu kuɗin nan, wannan ɗan shilan da take kallo, Yanayin shi tamkar akwai jinin sarauta atattare da shi, Baisan magana baisan hayaniya, kullum yana naɗe saman gado yadda kasan ɗan wani basarake, idan ka kalli soft skin ɗinshi ko tabo babu, fari ne sol, ga kyan ido ga kuma kyan sumar kai, Anya wannan ba ɗan wani shegen bane, ta yi tambayar acikin zuciyarta,

Bawan Allah, duk ya tsargu da irin kallon da angel ke yi mashi, Ga bacci yana ji amma yaƙi yarda baccin ya ɗauke shi saboda gudun kada ta yi ma shi wani abu, yasan dole ta hukunta shi,

kallon juna suka cigaba da yi da zarar taga ya fara lumshe ido zai yi bacci sai ta Ambaci kalmar charman dudu, a firgice yake ware idanuwanshi , ta hana shi runtsawa gashi in bai samu isasshen bacci ba, yana samun matsala, kusan raba dare su ka yi ita da danish, sai da Allah ya taimake shi bacci ya fara ɗaukarta tukunna ya samu shima ya runtsa_

In the morning🌹

Mutsu mutsun farkawa daga bacci ta soma yi, a cikin zuciyarta tana karanto addu'ar ta shi daga bacci, tunawa da danish yasa tayi hanzarin buɗe idanuwanta A hanzarce ta yi wuff ta miƙe zaune tana kallon shimfiɗarshi, babu kowa asaman mattaress ɗin sai Bargonsa da pillow dinsa, hankalin ta ya yi matuƙar tashi, ta shiga tambayar kanta Ina danish ya shiga? Meyasa kowa yana a kwance saman gadon shi, sai shi kaɗai ke babu? Ko dai ya shiga toilet ne?

Ta ƙarasa zancen zucin a lokacin da take sauko daga saman gadonta, cikin takun sauri ta nufi ƙofar shige toilets ɗinsu, hannu tasa ta tura ƙofar ta shiga daga Ciki, sai da tabi kowani toilet ta bincika amma babu danish,

Dawowa tayi da sauri taje gaban gadon batool,

Bubbuga ƙafarta tayi tare da Kiran sunanta"Batool! Sister!" saboda tsiwar muryar angel hatta su Azeeza sai da su ka farka,

"Meya faru sister" muryar batool a disasashe tayi mata maganar, tashin ta kenan daga bacci, idanuwanta sun ɗanyi ja saboda bacci,

"Na duba ko'ina banga danish ba, Jiya ya kwana da zazza6i yanzu kuma na farka ban same shi ba,"

"What? Danish bai da lafiya"? Haris ne ya yi maganar tashin shi kenan shima daga bacci, Fuskarshi da alamun ruɗi don ba ƙaramin Jin danish yake ba acikin zuciyarshi,

Jinjina kai angel tayi alamar eh kafin tace"Bansan inda ya shiga ba, tun ɗazu nake neman shi" Ta shi xaune batool ta yi, idonta akan angel tace"meya faru da danish ɗin mu"? Ina ya shiga"? Ta yi tambayar tana faman yin hamma,

Javed yace"Ni dama tun jiya na lura bai da ƙoshin lafiya, kunsan halin shi idan baya da lafiya yana da juriya baya bari mu sani kodan kada mu tashi hankalin mu akanshi, Amma nasan yanzu duk inda yake yana a tare da GIANTS, zai iya yiyuwa sune suka so su ka ɗauke shi"

Batool tace"taya zamu iya tabbatar da hakan"?

Hibba tace"Idan mu ka tambayi tsohuwa zata faɗa mana inda ɗan uwan mu yake, Bari naje na sanar mata," Ta karasa maganar tare da saukowa daga saman gadon nata, da azama ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa,

Kowa yayi zugudum yana jiran tsammani, Knocking ƙopar Hibba ta yi, Almost 3 times, suka soma jin mutsu mutsun buɗe ƙopa ta cikin ɗakin,

Fitowa tsohuwa ta yi hannunta ruƙe da sanda kamar kullum dai Cikin shigar nan tata, ta gado, wato doguwar riga launin Ja,

Haɗa ido su ka yi da hibba, Cikin girmamawa hibba ta gaishe da ita, ta amsa mata gaisuwar ta ta, tare da cewa"Zan iya sanin meke faru"?

"Dama danish ne, Angel tace jiya taji zazza6i a jikin shi, yanzu kuma mun farka bamu ga ɗan uwan mu acikin mu ba, bamu san inda ya tafi ba" Hibba ce ke magana amma idon tsohuwa yana akan angel dake daga can cikin ɗakin tsaye ta ruƙe qugu a bakin gadon batool, wani irin kallo take yi mata, murguɗa mata baki angel tayi tare da galla mata harara,

Ƙayataccen murmushi tsohuwa ta saki wanda bai kai zuci ba, ta ɗauke idonta daga kan angel ta mayar dasu kan Hibba,

"Giant ne yazo ya ɗauke shi, yanzu haka danish yana a treatment room, da zarar yaji sauƙi za'a dawo maku da ɗan uwanku," tana kai ƙarshen maganarta, ta juyawa ta koma cikin ɗakin nata, taja ƙopa ta rufe,

Kowa ya ji Amsar da tsohuwa ta ba hibba, hankalin su duk bai kwanta ba, Mamaki ƙarara akan fuskar angel tace"dama har treatment room ke akwai a Cikin prison ɗin nan"

Batool ce ta bata amsa da cewa"Eh, amma bakowa ne idan baida lafiya, ake kai shi can ba, Tsohuwa ce take duba lafiyar jikin mu,'

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull