Kenza eBookz

Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 28

Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 28

Kurkukun kaddara book 1 Chapter 28: Kurkukun kaddara book 1 Chapter 28. Saboda Jin daɗin maganar Batool batasan Lokacin da ta fashe da wani sabon kukan ba,…

3,321 words

Saboda Jin daɗin maganar Batool batasan Lokacin da ta fashe da wani sabon kukan ba, Matsawa batool tayi inda suke Ta janyo Angel ajikinta ta rungumeta sosai, Ta mika hannu ta ruƙo azeeza itama ta rungumota, atare suka cigaba da yin kukan,

*Nima dai na matse ƴar kwallata🥺🤣 Mu haɗu next page don jin yadda zata kaya, Idan Allah yakai mu da rai da lafiya, shin meyasa tsohuwa take Yi masu ƙarya ne? Meye manufarta akansu? Ya batun danish da har yanzu shiru ba'a dawo masu da shi ba, tsawon kwana biyar? Shin dagaske Gidan Kurkukun Ƙaddara Yana da Prisoners sama da mutun ɗari huɗu kamar yadda batool tace? Kuna tunanin Angel zata samu damar rotsa gilashin windon nan don taje yi masu lekan asiri? Tambayoyin suna da yawa sai dai mun nutsa Cikin labarin, har yanzu dai muna a takun farko, bamu je takun tsakiya ba balle kuma takun ƙarshe🤣*

*Mutane sun fara yi mun magana kan abu biyu, Na farko meyasa suke jin turanci bayan basu je makaranta ba? Ae ba dole sai wanda yaje makaranta ba yake jin turanci, sun taso suna jin yaren da ake yi masu magana dasu, shi yaro ae da yaren da ake mashi magana da shi zai taso koda kuwa harshe uku ne, zai taso yana jinsu, a gidan kurkukun ƙaddara Suna yin hausa kuma suna yin turanci, abun daga waɗanda suka raine su ne, fatan an fahimce ni,Na biyu kuma meyasa angel bata yin sallah? shin baku karanta inda aka ce ta sha jaraba yin sallah ba wani mummunan abu na faru wa da ita ba wanda ya ke affecting din brain ɗinta? nasan me nake yi, faɗarkawa nake yi ba zan rubuta abunda bai da dalili ba, idan ku kayi haƙuri a sannu zan fayyace maku komai😊idan har mutun nada tambaya game da littafina pls ni zai tuntu6a ashirye nake dana amsa tambayoyinku, its better akan mutun yayi magana ta ta bayan idona, sannan masu tambayata ina da aure, bani da shi, matashiyar budurwace mai jini ajika,🤣, adaina tambayata ya yara ya mai gida, nauyin abun nake ji🤣*

Much luv My novel's fans, Allh yabar xumunci a tsakaninmu, Keep sharing my novel✍️

Domin neman ƙarin bayani 08103884440, Text on whatsapp only banda phone calls,

share fisabilillah👌 [9/22, 7:10 PM] +234 803 216 9283: *💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

Daga alƙalamin Boss Bature✍️

Dedicated to Aunty kubra❤

E20-21

💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* 📦

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano* *Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki* *Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida* *Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso* *Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano* *Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* http://wa.me/+2347069711327

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*

Muryar Javed su ka ji yo daga bayansu

"Nima ina neman yafiyarki angel, duk da bana ɗaya daga cikin masu ƙuntata maki" raba jikinsu su ka yi daga cikin na juna, kowannansu idanuwanshi ya kaɗa yayi ja saboda kukan da suka sha, still hawayen basu daina sintiri saman faces ɗinsu ba,

Kallon javed su ka yi dake a tsaye, Shima da alamun nadama atattare da shi, cikin sanyin murya angel tace"basai kun nemi yafiya ta ba, saboda ba laifinku bane, nayi maku uziri tuntuni'

Ƙarasa shigowa Cikin toilet area ɗin yayi ya tsaya a kusa da su, sannan yace"Angel, muna so mu tabbatar da gaskiya, a tsakanin ki da tsohuwa, sai dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da zamu shaida hakan," yakai ƙarshen maganar idon shi akan fuskarta,

"Ku bani lokaci, bi'iznillahi Zan kawo maku ƙwaƙƙwarar hujjar da zan wanke kaina, ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA BA GIDAN MARAYU BANE, SANNAN ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA AKWAI ALLAH WANDA YA HALICCE KU, BA DAGA SAMA KUKA FAƊO BA,"

Baƙaramin daɗin maganarta su ka ji ba, batool ta ruƙo hannayen angel biyu acikin nata, cikin natsuwa ta soma magana"Ina yi maki fatan nasara Angel, muna atare dake,"

Angel tace"Bana so ku nuna mun shirya agaban tsohuwa, Ku cigaba da pretending cewa Kuna goyan bayanta baku atare dani, ta hakanne zan samu damar bayyanar maku da gaskiya,'

Atare suka haɗa baki wurin amsa mata da toh, Kallon azeeza ta yi wadda ke atsaye tana jinsu amma bata iya ganinsu,

"Mu koma Ciki mu kwanta, Azeeza ta gaji da tsayuwa" ta ruƙo hannun azeeza, Batool da javed su ka yi gaba a cikin ɗakin suka yi ma juna sallama, Kowa ya wuce gadonshi, sai da tafara kai azeeza saman gadonta ta kwanta ta lullu6eta da bargo, kafin Ta koma nata gadon, daga ƙasa ta ajiye fitilar hannunta, ta haye saman mattress ɗin taja bargo ta lullu6e jikinta zuwa saitin neck ɗinta, kasa runtsawa tayi, ɗan juyawa ta ɗanyi tare dakai idanuwanta saman shimfiɗar Danish, why Har yanzu ba a dawo da shi ba? Allah yasa dai ba jikin nashi bane yayi tsauri sosai ba, duk da babu sabo a tsakanin mu, naji na yi kewarsa sosai, inaso na sake ganin danish, Fatana Allah yasa adawo dashi, kada maganar batool ta tabbata na cewa duk wanda aka ɗauka ba'a dawowa da shi ya tafi kenan har abada! To wai ina ake kai su? Idan suna araye meyasa ba a ta6a dawo da su ba? Ni dai a iya sanina mutuwa ce kaɗai idan akayi ta ba'a dawowa!!!!!

Ɗaura hannunta na dama tayi asaman goshin ta zagoyo da shi, idanuwanta na fuskantar ceilling,

"Menene ma'anar Gidan Kurkukun ƙaddara? A iya sanina Gidan Kurkuku Yana nufin Gidan Gyara hali, Amma wannan kurkukun meyasa last name ɗinshi Ya ƙare da ƙaddara! Dole ya kasance ɗaya Cikin biyu, Kodai kyakkyawar ƙaddara ko kuma mummuna, ' lumshe idanuwanta ta yi a hankali ta ware su, Zuciyarta Cike fal da tunani, Tun lokacin da daddynta ya gudo da ita daga Gidansu, Take lissafin kwanaki, bata ta6a bari lissafi ya kwace mata ba, ko babu calender tana iya hasashen Yau nawa ga wata, ku ma ta canka dai dai,

Tana Cikin Yin tufka da warwara, Tajiyo Takun Tafiyar Mutun, Tunkafin ma takai idonta kan wanda ya shigo ɗakin nasu, Ta yi hasashen tsohuwa ce, daga kwance ta wurga eye balls dinta kan tsohuwa dake shigowa Cikin ɗakin, Sanye cikin shigarta, ta gado jar doguwar riga me hula, hannunta ruƙe da kaskon turaren wuta, zagaye ɗakin ta soma Yi tana kora hayaƙin ta ko'ina, murmushin takaici angel ta saki, yau ta ƙudiri aniyar sai tayi mata magana ga da ga, batare da jin tsoro ba, ta mike tare da saukowa daga saman gadonta, Cikin sanɗa take tafiya har ta ƙaraso bayan tsohuwa ta Cigaba da binta suna tafiya atare, batare da tsohuwa ta ankara ba, kasa kunne angel tayi tana sauraran ɗalasiman da take karantawa, kai daga jin yadda take Karanto su zaka shaida cewa ba abun arziƙi bane, wani mugun abunne take ƙulla masu,

"ƴar nan Kina tunanin bansan Kina bin bayana bane"? Tsohuwace tayi maganar, batare da ta juyo ta kalli bayanta,

Koda angel taji maganarta, bata ji wani fargaba ba, saima ƙwarin gwiwa da ta samu na cewa" nasan kinsan ina bin bayanki mana, Taya ki aiki nake yi, naga kina ta wahala ke kaɗai, Me zai hana yau Ki bani Kaskon turaren wutar In rage maki aiki"? juyowa tsohuwa tayi suka fuskanci juna ita da angel, Wani irin balagaggen murmushi ne ɗauke akan fuskarta tsohuwa,

Ɗaure fuska angel tayi tamau ba fara'a ko misƙala zarratin,

"Bibiyata kike Yi kenan? Da alama har yanzu baki daddara ba, Ina mai baki shawarar Ki ajiye makaman yaƙin ki, Ki yi rayuwarki tamkar salihar dabba, ki ajiye wannan Girman kan naki, da taurin kan nan da kafiya, Muyi rayuwa Cikin salama,' takai ƙarshen maganar tana washe wawulan bakinta,

Still angel bata tanka mata ba, Jira take ta kammala Suratan nata marasa kan gado,

"Ƴata faɗa da aljani ba riba, Ko har yanzu Kina tunanin zaki Ci galaba akaina ne eye? Tsabar takaici Ji take kamar ta shaƙo wuyan matar, mummunar banxa kawai, ta ambaci hakan acikim zuciyarta, a fili kuma tace"tun yaushe kuma? Cin galaba akanki tuni na fara, bari na faɗa maki abunda kike tunanin bansani ba,' ƙura mata kwarkwararrun idanuwanta tsohuwa tayi tana jiran jin me zata ce, "Kafin na faɗa maki irin nasarar dana fara samu akanki, zan fara faɗa maki babban kuskuran da kuka tabka," fuskarta ɗauke da murmushi takai ƙarshen maganar, Tsohuwa dai tayi kasaƙe tana kallonta,

A tsanake angel taci gaba da cewa"Kuskuren kuwa shine, ɗauko ni da ku kayi zuwa Cikin gidan Kurkukun nan, ganganci ne mutun ya ɗauko ajalinsa ya raine shi da hannunsa, ada ina tunanin meyasa na kasance acikin gidan kurkukun ƙaddara? Amma yanzu na samu amsar tambayata, inaji araina Ba hakanan Allah ya ƙaddara mun rayuwa acikin gidan kurkukun nan ba, babu shakka Nice zanyi silar tarwatsewar........" bata kai ƙarshen maganar ba, Sakamakon wata ƴar iskar dariya da tsohuwa ta fashe da ita, Ta wage wawake bakinta, Haƙoran nan jawur dasu, kasancewar angel na a kusa da ita, Da sauri ta kawar da kanta gefe Jin ƙarnin Jini na fita daga cikin bakin tsohuwa, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai zuciyarta ta shiga ruɗani, gaba ɗaya ta rikice tana zare ido, fuskarta ɗauke da tsantsar mamaki da aljabi ta ɗago tana kallon tsohuwa a lokacin ta dakata da yin dariyar,

Da shaƙaƙƙiyar Miryarta ta tsoffi tace"Your dream will neva come true angel, Wasiƙar jaki ce kike saƙawa aranki, wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, har yanzu akwai sauran kuruciya atattare dake, shiyasa nake yi maki uziri, bakisan komai game da gidan kurkukun ƙaddara ba, ki kalli ginin da kyau, Tsohon ginine wanda tun kafin zuwana duniya aka ƙirƙire shi,"

Angel fa ta shiga ruɗani, Idanuwanta azazzare take kallon tsohuwa, sama sama take fahimtar zancenta, wata irin narkakkiyar zufa ce ta shiga tsastsafo mata ta ko'ina ajikinta, saman goshinta duk ya jiƙe da zufa, bakomai ya tsara mata arai ba, face wannan ƙarnin Jinin da taji abakin tsohuwa,

"Gidan Kurkukun ƙaddara, Baida ƙopa a lokacin da aka Ginasa, Kurman ginine, Ke Ko mutuwa bata isa ta fidda gawar mutun daga Cikinsa ba idan har ya shiga Cikinsa, Duk wanda muka ƙaddara ma rayuwa acikinsa, Anan zai rayu Anan kuma zai mutu, Ƴar nan ta ina kike tunanin zaki iya tarwatsa Gidan kurkukun ƙaddara? Ta yi mata tambayar tana sakin shu'umin murmushi,

Tuntsirewa Angel tayi da dariyar yaƙe, tana girgiza kai, hada dafe Ciki, tsohuwa ta zuba mata ido Itama da murmushi akan fuskarta,

"Halan wani shaƙiyancin ne zaki yi mun shine kike dariya" ? Tayi tambayar tana kallon angel,

Dakatawa tayi da yin dariyar, Tare da sanya hannu tana kore hayaƙin kaskon turaren wutar dake a hannun tsohuwa daya takura mata,

Sai da ta daidaita natsuwarta tukunna tace"Ubangijin mu Allah subhanahu wata'ala, mamallakin Komai da kowa, mahaliccin Maginin gidan kurkukun ƙaddara da kuma tsohuwa ita kanta dake agabana, da iznin shi komai ke wakana, wanda idan yaso a yanzu haka da muke atsaye sai ki fadi ki mace shikenan, An shafe babinki rayuwarki, duk wani ƙarfin iko da kike taƙama dashi kinga ya qare, Zaki je ki fuskanci reality, Allah kenan da shi na dogara, Kuma shi zai bani Ikon tarwatsa ku, wai ke har kina da bakin cewa duk wanda kuka kaddara ma rayuwa acikinsa Bai isa ya fita ba? Anan zaiyi rayuwa anan zai mutu? Ke wacece? Kin manta ta ƙofar da kika bi kika zo duniya? Kin manta yadda aka halicce ki tun daga ɗigon maniya har zuwa gudan jini? Ke kanki fa baiwace ta Allah ƙasƙantacciya butulu, waɗanda ma suka fiki hatsabibanci irinsu fir'auna Yanzu suna Ina?

Jin wannan tambayar ta angel yasa Walwalar dake akan fuskar tsohuwa ta gushe zuwa tsananin fushi da 6acin rai,

"Dama nasan bazaki bani amsa ba, ƙarya ta ƙare, Idan Allah yaso arana ɗaya dake da kurkukun duka zai shafe babinku, Shi kaɗai yake da iko akan komai, Bansan A ina kika samu kwarin gwiwar Yin magana a gadarance ba, akwai fa ranar da wannan sihirin naki bazai ta6a taimakon ki ba,

Zaro ido tsohuwa ta yi tana kallonta, Cike da mamakin Jin ta ambaci cewa tana da sihiri taya akai tasan hakan? Bata kai karshen zancen zucin nata ba Angel tace"Kina mamaki ne? Ta yi tambayar fuskarta ɗauke da murmushi, Kafin taci gaba da cewa"Ɗaya daga Cikin nasarorin da na fara samu kenan, Kina amfani da sihiri wurin sarrafa Tunanin waɗannan bayin Allah, Kun Hana ayi ibada acikin gidan kurkukun ƙaddara saboda Itace Lagwanku, wannan dalilin yasa Duk wani prisoner dake rayuwa acikinsa, kuka hana shi yin addini, Hakan na nufin ku kanku Kuna tsoron Allah saboda kunsan cewa shi kaɗaine zai Iya kawo ƙarshen ku, shiyasa kuke gudun dun wani abu daya shafi addini musulunci, sai dai kunyi abanza, domin kuwa kome kuke Yi Allah yana kallonku, dama ce na ɗan lokaci ƙanƙani, "

Ajiyar zuciya ta sauke kafin taci gaba da cewa"Ke kanki kin fara Jin shakkata, dalilin dayasa kuwa nace haka, Saboda kinga addu'ar da nake Yi masu tafara tasiri ajikinsu, Har sun fara gaddama dake, Wannan dalilin ne yasa Kika Koma Yi masu hayaƙin sihiri domin juye tunaninsu, sai dai kash aduk Lokacin da ki ka turara masu hayaƙin sihiri ni kuma ina bin kowani gado In tottofe su da addu'a, wannan yasa kike jin haushina saboda ina ruguza maki shiri, sabo tsabar makirci kikayi ƙokarin cusa masu tsanata acikin zuciyoyinsu, duk don saboda kisa in karaya, shima kinyi abanza,"

yadda take magana babu tsoro tamkar zata shaƙo wuyan tsohuwa, daurewa kawai take yi tana yin magana da ita, saboda munin fuskar matar, Ƙyamarta take Ji, fuska duk ta lalace ta ta6ar6are,

"I ave alot to say, Amma bazan Iya jure Yin magana mai tsayi dake ba, saboda 6ata lokacine yin magana da matacciyar zuciya," fuskar tsohuwa babu annuri take kallon angel, Kaskon turaren wutar dake a hannunta tuni garwashin ya mutu, hayaƙin ya daina wanzuwa

Dogon tsoki Angel taja, tare da juyawa zata je ta kwanta, har ta kusa kaiwa bakin gadonta, ta ɗan dakata da yin tafiyar ta waiwayo ta kalli tsohuwa dake a tsaye ƙiƙam uwa saƙago, ta kafe ta da waɗannan kwartayen idanuwan nata,

"A'uzubillahi minasshaiɗanirra'jim, Aniyarki ta biki, Kuma ina nan ina zuba ido, Gobe adawo mana da ɗan uwan mu danish, idan ba haka ba komai zan iya aikatawa wlh, zan nuna maki hatsabibanci na, zan addabi rayuwarki,

"takai ƙarshen maganar tare da jefa mata harara ta murguɗa mata baki, gyaɗa kai tsohuwa tayi Batare da ta furta wata kalma ba, ta dogara sandarta zuwa kopar ɗakinta, ta buɗe ta shige tare da jan ƙopa, tafiyarta keda wuya angel tabi kowani sashe na ɗakin ta tottofe shi da addu'o'in neman tsari kamar yadda ta saba, ta kuma bi kowani gado tun daga kan gadon su Hanna duk ta wanke su da addu'a, bayan ta kammata ta koma saman gadonta, A tsakiyar gadon ta zauna tare da ɗaga hannayenta tana addu'a, akan Allah yabata Ikon yin nasara akan miyagun mutanan nan, Allah kuma Ya tsare mata daddynta aduk inda yake, idan kuma Ya mutu Allah ya kai rahama ƙabarinshi, Hatta danish sai da ta yi ma shi addu'a, Ta kuma roƙi Allah daya kawo masu ɗaukin fita daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara, Ta jima tana yin addu'o'i kafin daga ƙarshen ta janyo bargonta, ta lullu6a ma Jikinta,

Cikin ƙanƙanin Lokaci Bacci Yayi awon gaba da ita, can cikin dare wata irin zufa ta soma wanke fuskarta, wani irin matsanancin zafi ta ko'ina ajikinta, mutsu mutsu ta dinga yi tana matse idanuwanta, yayin da ta dunƙule hannayenta, tamkar ƴar dabbe, duk ta hargitsa shimfiɗarta, da alama mafarki take yi, ciccije la66anta tayi har sai da ta fasa su, ƙasa ƙasa take karanta duk wata addu'a da tazo mata a cikin kanta, a daren ranar bata yi bacci mai daɗi ba,

Tun daga saman gado Ta mirgino ta ƙundumo ƙasa ta daki floor ɗin sosai, har cikin kanta taji zafin buguwar da ta yi, Lokaci ɗaya ta farka kamar wadda Aka tsakura ta ware manyan gray eyes ɗinta tana kallon ceilling, Sai faman haki take yi kamar wadda ta yi gudun famfalaƙi,

Ƙoƙarin tariyo abunda tayi mafarki akanshi tayi, A cikin mafarkinta wasu baƙaƙen Maguna Guda uku sun farmake ta asaman gadonta, Faɗa ya kaure a tsakaninsu, Ta dinga yakushinsu tana kai masu cizo suma suna kokarin yakushinta sai dai Allah bai basu nasara ba, a ƙarshen itace taci galaba akansu ta yi masu jina jina sukai ta kuka, har suka sauko daga saman gadonta suka watsa aguje,

Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, lokaci ɗaya ta saki murmushi har dimples ɗinta suka lotsa, da alama taji daɗin damben da tayi acikin mafarkinta, bata motsa daga kwancen da take a ƙasa ba, hada bargonta da pillow ɗinta duka suna rungume a hannuwanta, Suma hadasu akayi artabun,

"Gidan kurkukun ƙaddara Ba gidan marayu bane Gidan Matsafa ne" yanzu ta ƙara tabbatar da zarginta akan cewa Gidan Mallakin Matsafa ne, Sai dai batasan wasu kalar matsafa bane, masu shan Jini, ko kuwa masu Cin naman mutun, akwai sauran rina akaba, dole sai ta bi asannu tukunna zata gano ainihin me waɗannan matsafan suke aiwatarwa da mutane ,

Ta yi zurfin acikin tunaninta muryar batool ta katse ta"Sister lafiya? Me kike yi a ƙasa"? Wurga idonta tayi akan batool dake A zuƙunne gabanta, ba tasan Lokacin da tazo wurinta ba,

"Sai faman sakin murmushi kike Yi kamar wadda akayiwa albishir da mukullin fita daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara" fashewa angel tayi da dariya Jin abunda batool tace, haƙiƙa maganarta ba ƙaramin daɗi tayi mata ba, wannan babban albishiri ne kuwa mutun ya mallaki mukullin fita daga kurkukun ƙaddara, Har tafara ayyana irin shagalin da zatayi aranar da tabar gidan kurkukun nan, zatayi farin Cikin da bazata Iya misalta shi ba,

"Faɗamun me kike ma dariya? Wata'ƙil nima ya sanya ni farin Ciki"acewar batool fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull