Kenza eBookz

Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 36

Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 36

Kurkukun kaddara book 1 Chapter 36: Kurkukun kaddara book 1 Chapter 36. Juyawa tayi da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar ɗakinta, tana ƙoƙarin kai…

3,348 words

Juyawa tayi da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar ɗakinta, tana ƙoƙarin kai hannu ta buɗe ƙopar muryar angel ta katse mata hanzarinta "Ba zaki ce komai ba? Saboda rashin gaskiya? Zuciyarki ta bushe baki ji baki gani zalunci kaɗai kika sa agaba, wlh rantsuwar ɗan musulmi idan har ba'a dawo mana da ƴan uwanmu ba, SAI NA KASSARA RAYUWAKI, koda kuwa zan rasa raina ne'

Girgiza kai tsohuwa tayi batare data waiwayo ta kalleta ba ta soma magana

"Zaki Iya zagina ki ci mutuncina son ranki, saboda a yanzu ni kike ganin laifina, Unaisah ga shawara...." a ruɗe angel ke kallon bayan tsohuwa, Jin yau ta ambaci asalin sunanta,

Cigaba da magana tsohuwa tayi"ME ZAI HANA KIYI TUNANI AKAN WAƊANƊA SUKA SADAUKAR DAKU A GIDAN KURKUKIN ƘADDARA? mutun baya ta6a kasancewa acikin gidan kurkukun ƙaddara dole sai in Na JININSA NE YA SADAUKAR DASHI!!, nifa ba kowa bace agidan kurkukun nan face Ƴar Aiki me rainon Yara," tsohuwa nakai karshen maganarta, ta yi saurin tura ƙofar ɗakinta ta shige taja ƙopa ta garƙame, ta tafi tabar angel da tunani, Zuciyarta ta shiga ruɗani, Kenan dama Tsohuwa bakowa bace Agidan kurkukun ƙaddara? Su kuma prisoners dake rayuwa acikinshi na Jininsu ne suka sadaukar dasu?tayaya kenan? Wata irin sadaukarwace wannan? Meyasa aka sadaukar dasu? Me za'ayi dasu? danginsu basa ƙaunarsu ne shiyasa suka sadaukar dasu ko kuwa?

Wani irin matsanancin ciwon kai ne Ya taso mata, me raɗaɗin gaske, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta, Ɗaƙyar ta iya ɗaga kafarta ta juya tana kallonsu Batul, waɗanda ke zazzaune Cikin jimamin rashin ƴan uwansu, da alama Basu ji komai ba game da abunda tsohuwa ta tattauna da angel,

"Wa suke dashi A duniyar nan? Zuciyarta ce ta bata amsa da cewa "ALLAH"

biji biji take gani acikin idanuwanta, daƙyar ta samu ta iya zuƙunna agabansu, Muryarta a disashe tace"kuyi haƙuri dare yayi sosai, Ku zo muje mu kwanta, " miƙewa kowannansu Yayi, Suna jan ƙafa suka Nufi gadajensu Kowa Ya haye ya kwanta, sai da tabi su ɗaya bayan ɗaya tayi masu addu'a, taja masu bargunansu ta lullu6e masu Jikinsu, koda tazo saitin gadon Parveen sai da ta matse kwalla, bakomai take tunawa ba face kukan parveen da kuma kalamanta na karshe da take cewa Tayi mata addu'a kuma idan an kawo abinci su ajiye mata, angel tasha kuka kamar ba gobe, lokacin data zo kan gadon Deeja, tuni jikinta yayi sanyi tunawa da irin muguntar da tayi mata ɗazu da suna wasa, ta sanya gwiwar hannu ta daki bayanta harta kife ƙasa, cikin shessheƙar kuka angel ta furta "NAYI DANA SANI" Wuce wa tayi zuwa bakin gadon Rubina, Ta jima tana kallon shimfiɗarta, Kafin ta nufi gadonta ta hau sama ta zauna daga tsakiya, Hannayenta ta ɗaga sama Ta soma yi masu addu'o'i, Yayin da hawaye ke fita acikin idanuwanta, wasu na bin wasu,

A daren Ranar Kowa Ya runtsa banda Angel, Ta dage sai addu'a take yi masu ta hana idonta bacci duk don saboda su Parveen,

A washe garin ranar, dayawansu basu farka daga bacci ba, har lokacin tana a zaune tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, fuskarta ta kumbura sumtun, tayi ja sosai, ga jirwayen hawaye,

Mutsu mutsun da taji ne yasa ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta Sun kumbura ga raɗadi da suke yi mata, daƙyar ta samu ta ware idanuwan sosai, gefenta ta ɗan kalla don ganin wanene ya motsa, Danish ne ta gani zaune saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi fuskarshi babu alamun damuwa atattare da ita,

Zuro da ƙafafuwanta ƙasan gadon ta yi tare da gyara zama daga gefen gadon tana fuskantar danish,

Cikin sanyin murya ta ambaci sunan shi"Danish" a hankali ya buɗe idanuwanshi ya juyo yana fuskantarta,

"Ka tashi lafiya"? Jinjina mata kai yayi alamar eh, ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin tace" Inaso na tambaye ka wani abu idan ba damuwa" ya amsa mata da toh,

Saukowa tayi daga saman gadon, taje bakin gadonshi ta ɗan zuƙunna daga ƙasa, ta ɗago tana kallonshi idonsu acikin na juna tace

"Shekaran jiya da daddare, lokacin da na shiga cikin toilet ka biyo ni, Taya akai ka shigo bayan na datse ƙopa ta ciki na sanya jam lock"? ta tsare shi da ido tana jiran jin amsar da zai bata, ɗan tahalikin nan yayi shiru yana binta da ido batare daya motsa lips ɗinsa ba balle ma tayi tunanin zai bata amsa,

"Ba ka yi mini kama da maƙaryaci ba, duk da bana yarda da mutun ta yanayinsa, pls tell me the truth kawai inaso na sani ne, saboda kafin na shiga toilet ɗin sai da na tabbatar na barka a kwance kana bacci kafin na shiga ciki, Kuma ko bayan dana shiga saida na Haska ko'ina babu mutun, amma wani abun mamaki sai gaka acikin toilet ɗin, wanda nayi Imanin bata ainihin ƙopar ka shigo ba, Kuma baka Biyoni abaya ba" Cikin tuhuma take yi mashi maganar,

muryar shi a sanyaye yace" Bazan iya baki amsa ba, saboda ni kaina bansan ta ina na shiga ba, abunda na sani shine Na sanyawa raina inason nabi bayanki ne, kuma na samu kaina Acikin toilet ɗin shine kaɗai abunda zan Iya tunawa amma bayan wannan bansan komai ba"

Zuba mashi ido tayi tana kallonshi, har cikin ranta ta yarda da maganarshi, domin kuwa babu alamun wasa a fuskarshi ya bata amsar, kwara tabi komai asannu wurin yin bincike, Idan ba haka ba, zata iya tarwatsa lissafin kwakwalwarta ne,

Ƙaƙaro murmushi ta yi akan fuskarta, yayin da take kallon shi,

Mayar mata da martanin murmushin yayi Calmly yace" kin sanya damuwa aranki, Jiya kinyi kuka kuma baki yi bacci ba Why? Akan su Parveen ne"?

Jinjina mashi kai tayi alamar eh, ta ƙara da cewa"na damu dasu sosai, Ina ji araina kamar baza a dawo mana dasu ba, shiyasa zuciyata ta karaya har nagaza runtsawa"

Duƙowa taga ya yi saitin fuskarta, har saida ta ɗan tsorata, Zuciya da saƙe saƙe sai tayi tunanin ko kiss zaiyi mata, ƙiris ya rage tsinin hancinshi ya gogi nata, runtse ido tayi tana jin me zai mata

"Ki kwantar da hankalin ki, Zasu dawo na yi maki alƙwarin hakan," ɗagowa tayi tare da kallon shi, "Taya akai kasan cewa zasu dawo"? Tayi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi,

Murmushin gefen fuska ya ɗanyi, Can kuma yace"Kin manta anzo an ɗauke ni, Kuma an dawo dani, Suma zasu dawo ne"

Girgiza kai angel tayi"amma koda aka dawo dakai, baka Acikin hayyacin ka, kamar an ƙara maka Ciwon Ajikin ka, danish zaka Iya tuna ina aka kai ka bayan an ɗauke ka daga Cikin mu"? ta jefa mashi tambayar,

"Angel, ba zan iya tuna komai ba, tun bayan da giants suka ɗauke ni bansan meya faru ba, har sai ranar da suka dawo dani cikinku tukunna na iya tuna wanene,"

Shiru angel ta yi bata kuma cewa komai ba, Lamarin ne yafi ƙarfin tunaninta, Wata irin Murɗaɗɗiyar sarƙaƙiyace Acikin Kurkukun mai wuyar fassaruwa,

Miƙa hannu danish yayi tare da ruƙo nata hannun acikin na shi, Magana ya soma yi idonshi acikin nata"angel, ina neman yafiyarki, for everything that happened because of our misunderstanding, I hate you for no reason, but now I can say that I love you more than anyone........" kalaman shi ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, sai taji tamkar an yaye mata damuwarta na ɗan wani lokaci,

ƙayataccen murmushi ta saki tana motsa lips ɗinta, alamar tana so tace wani abu amma ta kasa furtawa, sam batayi tsammanin jin hakan daga gare shi ba, ta yi farin Ciki saboda yana ɗaya daga Cikin nasarar da take so ta samu na Jituwa atsakaninta da kowannan su, tana so ta shiga cikin zuciyoyinsu sosai ta yarda zata samu damar janyo ra'ayinsu, yanzu saura mutun biyu ya rage mata haris da deeja, taci alwashin Idan aka dawo da deeja bazata ƙara bari faɗa ya haɗa su ba, Shi ma haris ɗin bazata biye mashi ba, xata jasu ajikinta,

"What are u thinking about"? Jin voice ɗin danish yasa ta ɗanyi firgit ta kalle shi, still idanuwanshi na akan fuskarta,

" baki bani amsa ba," ya tambaya yana sauraranta,

"Dama ni ban ruƙe ka azuciyata ba, Ni baka yi mini laifin komai ba, dani dakai tamkar ƴan uwana ne jini," ba ƙaramin daɗin kalamanta yaji ba, har cikin zuciyarshi yaji sanyi, zame hannunshi yayi daga Cikin nata, ganin ya lumshe eyes ɗinshi yasa tayi tunanin ko bacci zai koma ne,

Yunƙurawa tayi tare da miƙewa daga gaban gadon shi, A dai dai Lokacin Batool ta fito daga sashen makewayinsu, itama fuskarta a kumbure, suna haɗa ido da angel ta nufeta, rungume juna su kayi kowa yayi shiru, batare da sunyi magana ba,

Azeeza dake zaune saman gadonta, farkawarta kenan idanuwanta na akansu,

Sun ɗauki lokaci kafin suka raba Jikinsu daga na Juna,"

"Idanuwanki sun nuna alamun baki yi bacci ba jiya, meyasa"? Batool ce tayi mata tambayar,

"Taya xan iya runtsawa, alhalin ƴan uwana suna Acikin mawuyacin hali, anzo an raba ni dasu, an kaisu wani wurin, dole na damu, Nayi kewarsu sosai, Na gaza jurewa ne....." kukane ya ciyota, da sauri ta duƙar da kanta ƙasa, sam bataso ta nuna rauninta agabansu, saboda zata ƙara karya masu zuciya ne, sai dai duk ƙoƙarinta na hana kanta yin kukan hakann ya faskara, ita dai sam hankalinta bai kwanta da ɗaukar su parveen da akayi ba,

Dafa kafaɗunta Batool ta yi da hannayenta biyu, Cikin sigar lallashi tace"pls angel, u should stop shedding your tears, kina ƙara sanya mana damuwa ne, ke da kike ƙarfafa mana gwiwa yau ke ce da kanki ki ke zubar da hawaye to mu me zamu yi kenan"? Idon batul cike tab da kwalla tayi maganar,

Ta wutsiyar idonta ta hangi azeeza dake a zaune ta kasa kunne tana sauraronsu, da alama baccin bai sake ta ba, bata fahimtar me suke tattaunawa,

Sanin raunin azeeza yasa tayi saurin sanya tafukan hannayenta, ta share hawayen da suka wanke fuskarta, murmushi tayi wanda kai zuci ba takalli batool dake kallonta tace "Nadaina batool, bazan ƙara ba, kema kada kiyi kuka" jinjina kai batool tayi"Nima bazan bari hawaye na su zuba ba, Angel inaso mu haɗa hannu wurin taimaka ma sauran ƴan uwanmu, mu dinga lallashinsu muna basu baki har Allah yasa adawo dasu Parveen, Inaso mu sama ma junan mu farin ciki koda kuwa babu wani acikin mu, kamar ke da kika jure rayuwa batare da Mahaifinki ba, haka nakeso muma mu ƙarfafa zuciyoyin mu, mu yi rayuwa da sanin cewa wata rana samu iya rasa wani,

Tun da batool ta soma magana angel ta natsu tana kallonta, acikin zuciyarta tana Jinjina Ma batool, Yarinyar akwai tawakalli, Tana da hankali da tunani, Allah yayi mata baiwar iya sarrafa harshe wurin tsara kalamai masu kwantar da hankali, Haƙiƙa Iyayensu sunyi babbar asara Na rashin ya'ya kamar su,

"Angel kinyi shiru baki ce Komai ba, Ina ta surutu Ni kaɗai," ajiyar zuciya angel ta sauke tare da kallon Batool tace"Am sorry Sister, naji maganganunki, sunyi mini daɗi sosai kuma in sha Allahu, zamu yi hakan, Zamu haɗa hannu wurin sama ma kanmu farin ciki,"

Muryar azeeza ce ta katse su da cewa"Wai har yanzu ba'a dawo mana dasu parveen ba? Jiya har mafarkinsu nayi," saukowa tayi daga saman gadon ta nufi su angel dake a tsaye ta ruƙe qugu tana kallonsu,

"Ba'a dawo dasu ba Azeeza, Mu ƙara haƙuri zuwa anjima may be Giants su kawo mana su" Batool ce ta bata amsar tambayarta,

Ta6e baki azeeza tayi tare da cewa"Ni dai indai ba'a dawo mana dasu ba, Bazan ƙara Cin abinci ba" maganartace ta basu dariya,

Sauran ƴan uwansu dake bacci ɗaya bayan ɗaya suka dinga farkawa, duk wanda ya buɗe ido saiya tambayi su deeja, Angel da batool ne ke kwantar masu Da hankalinsu akan su ƙara haƙuri zuwa anjima, lokacin da kowa Yayi wanka, Suna a zazzaune saman gadajensu, Sai ga giants sun shigo kawo masu abinci, Bayin Allah duk sunyi tsammani za'a zo masu da ƴan uwansu amma sai suka ga akasin,

Koda suka koma saman dining carpet domin Cin abinci, saboda damuwa, kaɗan suke tsakura suna ci ba don suna jin daɗin abincin ba, Angel hada ƙoƙarin mikewa taje karkashin gadon batool ta ɗauko kwando, tazo tana kwashe kingin abincinta, Yasmin tace"meyasa ba zaki ci ba? Bafa Ki ci dayawa ba'? Angel tace"su parveen zan ajiye mawa, kada su dawo da yunwa anjima, Jin abunda tace ne yasa suma suka rage sauran nasu abincin don a ajiye ma su parveen, angel ta kwashe duka cikin kwandon, Taje ta 6oye a karkashin gadon batool,

Bayan tafiyarsu Giants, Hanna ta basu shawarar su motsa Jiki Ko sun samu Lokaci yayi saurin wuce wa duk don saboda tsammanin za'a dawo masu da ƴan uwansu yau, bayan sun kammala motsa Jikin nasu Kowa Ya gaji sai uwar xufa ke tsastsafo masu, A dole suka je toilet kowa ya watsa ruwa a jikin shi, ba ƙaramin ɗaɗi suka Ji ba, saman gadajensu suka koma kowa Ya hau ya zauna fira suka soma yi atsakanin su, wani irin bacci ne yazo ma angel batare data shirya mashi ba, dama jiya ana binta bashin baccin da batayi ba, gyara kwanciyarta tayi asaman gadonta, tare da jan bargo ta lullu6e kanta, Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita,

*ANEELERH*

Almajirai ne daddabe a gaban motarta, sunyi dandazo suna jiran Ta basu sadakar kuɗi kamar yadda ta saba basu a duk lokacin da tazo zata wuce ta wurin makarantar allonsu, Sai faman zumuɗu almajiran suke Yi, Kayan Jikinsu duk sun yayyage, kowannan su na aruƙe da kokwan bararsa,

Zuge glass ɗin motar ta yi, almajiran sai kallonta suke yi, tana a zaune saman driver seat, Jikinta na asanye da atampa, riga da skirt sunbi shape ɗin jikinta, Ta yafa mayafi akanta, ba ƙaramin kyau ta yi ba, Yayin da baby junaid ke akwance saman passenger front seat, Kayan sanyi ne ajikinshi sunyi matuƙar yi mashi kyau, baccin shi yake yi hankali kwance, ga wani irin ƙamshi dake fita ajikin shi,

Ƙoƙarin Zaro kuɗi take Yi acikin ƴar purse ɗinta Bendir guda ta ciro na ƴan ɗari biyar biyar, zarowa ta dinga yi tana miƙa ma almajiran, Sai murna suke yi, suna kai hannu suna karba tare da yi mata addu'o'e Sai da ta kammala raba masu, tana yunƙurin Zuge glass ɗin motar, taga an zuro mata hannu, ras taji gabanta ya faɗi ganin hannun babban mutun sanye cikin baƙar safa,

Da sauri ta kalli fuskar mutumin, ya sanya Mask a fuskarshi, Baƙaƙen kaya ne ajikinshi, bakomai ya faɗo mata araiba face mutumin da ya Ɗauke mata baby junaid ɗinta lokacin da taje gidanta, nan take gabanta yyi mugun bugu, A tsananin tsorace ta shiga kiciniyar zuge glass ɗin motar, ganin zata datse mashi hannu yasashi yin saurin zame hannunshi

Key tayi ma motan hannunta na kerma ta ruƙe steering da wani irin speed ta fusgi motar da gudu ta haura saman titi tana ambaton"La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" tarasa ina zata dosa, saboda tsabar ruɗi, Gani take kamar mutumin yana abiye da ita, ashe dama bibiyar rayuwarta yake yi? Tayi tambayar acikin zuciyarta, Marece ne sosai Tana kokarin shan kwana, muryarshi ta ratsa kunnata"Baki bani sadakar ba" a gigice taja burki ta tsayar da motar, idanuwanta azazzare ta ɗago tana kallon shi ta cikin Rear view mirror ɗin motar,

Mutumin Yana a zaune Cikin back seat na motar, a hakimce,

Tayi matuƙar razana ganin shi acikin motarta, taya akai ya shigo bayan ta rufe motar, Anya kuwa mutunne ba aljani ba? muryarta na rawa tace"dan..dan Allah na roƙe ka, kada ka cutar damu, bansan wanene kai ba, ban kuma san laifin da nayi maka ba, ka faɗi kome kake so zanyi maka shi" idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,

"Kome nake so zaki yi mini"? Ya yi tambayar yana kallonta, a tsorace tace"Eh, wlh zanyi"

Ya amsa da "Okey, " hannu taga ya zura cikin aljihun wandon Jikin shi ya lalubo wayarshi, Ya ɗan daddana ta kafin ya miƙa mata wayar"Location ɗin nan zaki bi, " batare da musu ba ta kar6i wayar tashi, idonta akan google map ɗin daya buɗo mata, daga gefenta ta ɗaura wayar, Ta ci gaba da driving tana bin location ɗin, yayin da zufa ke tsastsafo mata, zuciyarta a firgice take da tsoron inda zai kai su, Wayar shi kanta abun tsoro ce saboda ta banbanta da sauran wayoyin da ta saba gani, Babu sunan Company ajikin wayar,

Dogon titi suka Miƙa sham6al har zuwa cikin wata area, Ta jigunannun masu kuɗi, Manya manyan gine gine, Unguwar shiru babu yawaitar mutane acikinta, a bakin wani katafaren Gida ta ƙaraso da motar, yace tayi horn ta danna horn nan take Wagegen gate ɗin gidan Ya zuge awani slow, kutsa motar tayi acikin gidan, har saida ya bata umarnin ta tsayar da motar tukunna ta tsaidata,

Buɗe murfin motar yayi tare da fitowa ya zagaya other side ɗin da junaid yake a kwance, Ya buɗe motar ya zura hannu ya ɗauke shi, Aruɗe aneelerh take kallon shi, ganin ya ɗaukar mata yaro,

"Let's go in" yayi maganar yana nuna mata hanyar zuwa cikin gidan, Jiki asanyaye ta buɗe motar ta fito tabi bayanshi, Wa'iya zubilla Ta yi matuƙar girgiza da ganin kyawun gidan ya tsaru iya tsaruwa kai kace ba'a 9ja yake ba, Duk da a tsorace take hakan bai hanata bin ko'ina da kallo ba, suna ƙarasowa bakin glass door ta falon gidan, Muryar na'ura ta karaɗe kunnuwansu, wani abun mamaki daya ɗaure mata kai, na'urar da ta soma magana tana sanar da zuwan su, sai da ta faɗi Cikakken sunan aneelerh, wato Aneelerh muhammad falgore, Ras taji gabanta ya faɗi, a karshe na'urar tace"you're permitted to come in" nan take ƙopar glass ɗin ta zuge,

Mutumin yace mata su shiga Ciki, ta zura kafarta acikin katafaren falon, Tsayawa faɗar irin kyawunshi 6ata baki ne sai wanda ya gani, wani irin sanyin a.c ne ta ko'ina, Komai na Cikin falon White Colour ne atsaftace yadda kasan ba'a ta6a amfani dashi ba, saboda kyawunshi da sabuntakar furniture ɗin dake acikin shi,

Miƙa mata Junaid Ya yi, da sauri ta sanya hannu ta kar6eshi, ta rungume shi ajikinta, A saman Sofa 3 seater Ya bata Umarnin ta zauna, xama tayi tana faman baza ido, Jira take taga me za ayi mata, Acikin zuciyarta sai addu'o'in neman tsari take karantowa,

Takun takalma ta soma ji daga can saman twin stairs ɗin dake a falon, a hanzarce takai idanuwanta wurin tana kallonsu, waro ido waje tayi Jikinta ya shiga 6ari ganin Gabza gabzan Mazan dake saukowa saman benan, kowannansu na asanye Cikin shiga ta baƙaƙen kaya, A ƙalla sunkai su takwas, bakwai Suna a left hand na benan, Yayin da mutun ɗaya ke tafiya atsanake ta right hand ɗin stairs ɗin

Kusan atare suka sauko daga saman benan, Aneelerh bata Iya ganin komai na Jikinsu ba, Gaba ɗaya sun rufe kansu daga ƙasa har sama Cikin black dress, Dogayen riguna na maza masu haɗe da huluna kamar alkebba, Guda bakwai ɗin suka Ƙame a tsaye tare da goya hannayensu saman ƙirjinsu, shima wanda ya kawota gidan Yana a tsaye gefen hand sofa ɗin da take a zaune Ya ƙame kamar yadda sauran su ka yi

Mutum ɗayan nan daya rage, shine Ya zauna saman sofa 2 seater, Ya ɗaura ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya, aneelerh fa tasha jinin jikinta, sai faman ƙanƙame junaid ta ke yi ajikinta, Yaro sai bacci yake yi baisan halin da Mommynsa ke ciki ba,

"Ki natsu Ki saurari maganganun da zamu tattauna dake, mintina ƙalilan zamu salleme ki ki tafi" Na gefenta ne yayi maganar, wanda suka zo tare da shi,

Jin haka yasa ta daidaita natsuwarta, ta kasa kunne tana jiran Jin me zasu Ce, wanda take tunanin shine team leader ɗinsu, wanda ke zaune saman Sofa 2 seater akanshi ta tsayar da idanuwanta, wata irin ƙirar ƙarfi ce gare shi, taban al'ajabi, mai matuƙar jan hankali da tsoratarwa, kai daga ganin wannan babu wasa acikin lamuranshi, baƙaƙen kayan sun zauna mashi sosai, sun bayyanar da zazzafar surarshi, tayi tunanin shi zai yi mata magana amma sai taji yayi shiru,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull