Kurkukun kaddara book 1 - Chapter 45
Kurkukun kaddara book 1 Chapter 45: Kurkukun kaddara book 1 Chapter 45. "Koda gigin wasa kada ku kuskura kuce zaku Hana giants tafiya da deeja!! ina…
519 words
"Koda gigin wasa kada ku kuskura kuce zaku Hana giants tafiya da deeja!! ina gargaɗinku idan har kuna son zaman lafiya to ku daina yunƙurin shiga huruminsu....." Haris ne ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa yace"Wai ina ruwanki da rayuwarmu ne? Bakin nuna baki damu da mu ba? To ki fita sabgarmu mana? Idan ke bazaki Iya hana su tafi da ita ba, to mu ki barmu muyi da kanmu" rai a6ace yai maganar,
Muryar danish ce ta ratsa kunnuwansu, a yayin da yake saukowa daga saman gadonshi yace"Haris ka sassauta kalamanka, Abunda tsohuwa ta faɗi gaskiya ne, Baza ku Iya ja da giants ba, Kuna Yunƙurin jefa rayuwarku cikin hatsari ne, Na rasa ya zanyi in fahimtar daku," wani irin mugun kallo haris ya jefa mashi,
"Danish kana goyan bayanta ne? Bayan duk irin ƙarairakin da take yi mana, da kuma Nuna rashin damuwarta akanmu , Sannan da ita fa ake haɗa baki ana cutar da rayuwar ƴan uwanmu amma duk ahaka kake binta"? Zuciyarshi a hasale yayi maganar, sam baiyi tsammanin danish zai mara mata baya ba,
"Haris u ave to understand me, Bazamu iya yin komai ba, saboda mu ba komai bane, Ni bana so na rasa wani acikin ku......." Kasa karasa maganar yayi ganin irin kallon hararar da angel ke jefa mashi, shiru yayi tare da duƙar da kanshi ƙasa,
Tsohuwa ta dasa da cewa"Bawai bana son taimakon ku bane, kawai ba yadda zanyi ne, Ni kaina giants sunfi ƙarfi na, matsayinsu da nawa ba ɗaya bane, sunfi ni ƙarfin iko, Idan nace zan hanasu tafiya da wani daga Cikin ku zan rasa raina ne......" Angel tace"Oh ashe ta ranki kike Yi? Su baki damu da rayuwarsu ba, Ae ni nayi tsammanin har rayuwarki zaki iya sadaukarwa akansu ashe ba haka bane, ƙaunar da kike yi musu ta bogi ce, Ni na tabbata da ace ƴa'ƴan da kika zuƙunna kika haifa ne da baki faɗa musu wannan maganar ba"
Girgiza kai tsohuwa tayi wannan karan idanuwanta hada farin ruwa kwance acikinsu tace"Bazaki ta6a fahimtata ba, Koda ace na sadaukar da rayuwata akansu nayi abanza, saboda yin hakan bazai canza komai ba, Ae ƙwarama Ni dana 6ata tsawon shekaru ina rainansu, Iyayensu fa da suka sadaukar dasu? Suna can suna sharholiyarsu sun ma manta da suna da wasu ƴa'ƴa da suka sadaukar, Nifa kaɗaice na damu daku, Ni da ban haɗa alaƙar komai daku ba, ae na cancanci a jinjina mini"
Maganar tsohuwa ta yi matuƙar girgizasu, Kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu, batare da wani ya kuma Yin magana ba,
"zan Koma ɗakina, Amma kafin nan zan ƙara ja maku kunne, Kada Ku kuskura ku shiga hurumin giants, Idan Kunne Yaji Jiki ya tsira" tsohuwa na kammala maganarta, Ta juya tana dogara sanda ta shige Cikin ɗakinta, Idanuwansu akan abayanta har saida ta 6ace ma ganinsu....
*Domin neman ƙarin bayani 08103884440 ko 08169856268 Text on whatsapp only banda phone calls, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, Ga wanda ya shirya yin payment, zai iya yi mini magana, Cikin next month Takun farko zai ƙare in sha Allah, zamu nutsa Cikin labari*
share fisabilillah❤👌