Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 24
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 24: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 24. "Assalamu akaikum" muryar Hajjaty ce ta ratsa…
3,347 words
"Assalamu akaikum" muryar Hajjaty ce ta ratsa kunnuwan su, atare suka amsa mata da wa'alaikum salam shigo daga Ciki, Tura ƙofar tayi kamar kullum fararen Kayane a jikinta, Tasha uban ado kamar amarya, sam bata gaji da ca6a ado, Hannayenta sun sha ƙunshi na jan lalle. Hajiya saratu dake a tsaye tana kallonta, Haushin Matar take ji, ta tsani taga ƴar aiki tana ɗaukar wanka kamar yar masu gida, zuciya da saƙe saƙe, sai ta dinga ganin kamar obinna bin jikinta yake yi da kallo, fargabanta kada wata rana dattijonsu ya ƙyasa, Ƙarasawa Hajjaty tayi cikin ɗakin Asaman Carpet ta ɗaura tray ɗin, sai faman sakar mashi murmushi take yi shima ɗin mayar mata da martanin murmushin yake yi, Hankalin Hajiya saratu yaƙi kwanciya Tana a tsaye ta ruke qugunta "Yalla6ai fatan ka wuni lafiya, tun ɗazu nake jiran shigowarka gidan bansan kun dawo daga masallaci ba, ae da tuni na jima da kawo maka abinci" Yanayin yadda take magana muryarta tamkar ana busa sarewa, ƙamshin turarenta Ya addabi hancin hajiya saratu Lumshe ido yai kafin ya amsa mata da"lafiyalou Alhamdulillah, nagode da kulawarki agareni, Kina ji da dattijon nan naki sosai nima na yaba da hakan"
Fuskar Hajiya saratu a ɗaure ta furta"ke! Tashi kibar ɗakin nan tunda kin kawo mashi abincin,ya gode sai anjima" miƙewa Hajjaty tayi tare da jiyawa ta kalleta"Ina wuni hajiya" "Da ban wuni ba kin ganni, Ƴar rainin wayau sai yanzu kikasan dani aɗakin, dallah ni zo ki fuce waje" jikin Hajjaty yai sanyi duk sai ta ji ba daɗi
"Inaso zan zuba mashi abincin...." tunkan ta ƙarasa Hajiya saratu ta daka mata tsawa"Nace ki fita ko"? Matsawa tayi tare da fusgo hannun Hajjaty taja ta waje, Obinna dake a kishingiɗe saman gadon ƙayataccen murmushine akan fuskarshi, lamarin saratu sai addu'a ya fahimci kishin mahaifin nata takeyi.
Bayan fitarsu daga ɗakin, a bakin ƙofar suka tsaya da tafiya, Hajiya saratu na faman ciccije le6e ta furta"Ni ban yadda dake ba, akan me zaki dinga zuwa ɗakin Ubanmu, balallaga dake Ina laifin Ki turo matasan ƴan matan masu aikin su dinga yi mashi hidima"? Idanuwan hajjaty tuni sun cicciko tab da ƙwalla, ta tsani faɗan hajiya saratu, a shekaru kusan tsaran junane amma ta tasata gaba tanayi mata faɗa kamar wata ƙanwarta "Ai shine ya za6eni bani nake kawo kaina ba, Yafi so ina yi mashi hidima, kuma ki tambaye shi zai fada maki hakan" Harara Hajiya saratu ta watsa mata"ae dole ya za6e ki, tun da kin riga kin asirce shi da wannan munafukin turaren naki, mace sai kace karuwa, Kin bi jiki duk kin feshe da turare Bakisan haramin bane mace ta fesa turare mai ƙarfi ba? Ina laifin wanda zaki ɗan matsa a hammata!" yawu hajjaty ta haɗiya batare da tace mata komai ba "Idiot, daga yau karki kuskura In ƙara ganin Kin a ɗaki babanmu, tun fil azal ni baki kwanta min araina ba, Ina raga maki ne saboda mijina ba dan haka ba wlh da tuni na jima da korarki can ƙauyanku na can india, A tsawace takai ƙarshen maganar tare da ingiza hajjaty, tai taga taga zata faɗi daƙyar ta samu ta dafe bango, dogon tsoki Hajiya saratu ta buga kafin Ta juya ta koma ɗakin obinna.
Jiki asanyaye hajjaty ke tafiya yayin da hawaye ke bin fuskarta, Da mayafin hannunta take share ƙwallar dake sintiri saman kuncinta, Kalaman Hajiya saratu sun ƙona mata rai.
Tun fitar Hajiya saratu daga ɗakinta, Pravin Yana zaune gefen gadon shi, Shi da Tagwayensa zayn da zayn, suna zaune saman sofa, ransu ya 6aci matuƙa babu annuri akan fuskokinsu
"Yanzu me kuke so ayi"! ya jefa masu tambaya yana mai kallon fuskokinsu "Ka sama mana hanyar da zamu bar ƙasar nan, saboda mun gaji da zaman gidan nan, a takure muke kowa baya son mu kusan kullum ne sai anyi mana Gori" murmushin gefen fuska Pravin ya ɗan saki Yana duban ya'yan nashi cikin so da ƙauna "Kun bani Kunya wlh, Why maganar mutane zata dame ku? Har wani ya isa yasa kubar Danginku? Kenan wata rana zaku Iya kashe kanku saboda wani ya 6ata maku rai eye"! ɗaure mashi fuska suka yi don sun fahimci uban nasu babu zuciya a ƙirjinsa, shiyasa bai ganin illar abunda ake yi masu, yafi so su zama masu matattar zuciya irin shi "Daddy pls, ka fahimce mu, bama jin daɗin zama gidan nan, america muke son komawa da zama" girgiza kai pravin yai"bazaiyiwu ba, ai baku keda kanku ba, Nima ina buƙatar ku atare dani, Ku faɗi wani abun na daban da kuke so zan iya yi maku shi" magiya suka dinga yi mashi akan ya amince masu su koma america, "Daddy bafa da kuɗinka xaka ɗauki ɗawainiyarmu ba, munsan komai kakeso mommy zata yi maka taimakonmu kawai zakayi mu samu ta amince mana" Ɗaure fuskarshi yai"saboda ni bani da arziƙin da zan Iya ɗaukar nauyinku"? Girgiza kai sukayi atare Ta6e la66ansa yai"bansan me kuka ɗauke ni ba, Ita kanta mahaifiyar taku A yanzu bata kama ƙafata wurin arziƙi ba," kallon Juna su ka yi da mamaki akan fuskokinsu Miƙewa yai daga gefen gadon Ya nufi gaban drawer chest, Ya buɗe ya zaro atm card, dawowa yai ya zauna yana fuskantarsu "Banyi maku Iyaka da kuɗin dake acikin acct bank ɗina ba, don nasan har abada bazaku Iya ƙarar da su ba, a duk lokacin da kukeso zaku Iya cirar kuɗi ku biya buƙatunku, sannan kuje ƙasar da kuke so, Farin Cikinku shine nawa" Kallon da suke yi mashi kamar basu yarda da maganarshi ba, saboda sun raina arziƙinsa, Still murmushine akan fuskarshi yace"baku yadda da mahaifinku ba ko"? Shiru basu tanka mashi ba, Aransu suna ayyana may be babu ko sisi a atm ɗin, idan ma akwai kudi to Na mommynsu ne tunda ita ke da kuɗi.
Miƙa hannu pravin yai tare da ruƙo wayarshi dake a gefenshi, kamar sakarkaru haka suka tsare shi da ido suna kallon shi, Daddana wayar yayi kafin Ya miƙa masu da sauri Zayn ya kar6i wayar Suka haɗa ido suna kallon screen ɗin wayar, Total balance ne na kudin dake a acct bank dinsa, tsabar firgita har saida suka ɗan zabura ganin millions of dollars, wanda a kuɗin nigeria Billions ne. Aruɗe suka haɗa baki wurin furta"Daddy Numbobi ne waɗannan ko kuwa kuɗin ne dagaske" dariya ya sakar masu "Abunda idanuwanku suka nuna maku, Just ku ɗauki atm ɗin zan tura maku pin ɗinsa ta text message," lamarin yai mugun ɗaure masu kai, Girgiza kai Zayn yai"a'a daddy kuɗin sunyi mana yawa, ni tsorona ma kada ace Na mommy ne" Miƙa mashi wayar yai "Idan har kuka bari na kar6i atm ɗin nan kada ku ta6a tsammanin zan taimaka maku!" Kallon Juna sukayi zuciya na azalzalarsu akan su kar6i atm din suyi sharholiyarsu "Zayn mu kar6a ko"? Girgiza kai zayn yai"A'a zaid kuɗin mommyne fa, idan muka ta6a zata gane ni dai ban goyi bayan hakan ba" "Pls zayn tun da daddy ne ya bamu just mu kar6a kawai" "No zaid, kuɗin sunyi yawa zasu sa mu shagala mu daina yin sallah ne" Pravin dake kallonsu ba ƙaramin dariya suka bashi ba. "Har yanzu akwai ƙuruciya atattare daku, kuɗin kuke gudu? Ai nayi tunanin idan na baku jiki na rawa zaku kar6a, ban ta6a tunanin kuna da zuciyar Imani akan kuɗi ba, Sam baku da haɗama, Ga dama ta samu amma kuna ƙoƙarin yin watsi da ita"! Muryar zayn na rawa ya furta"Daddy zamuyi shawara tsakaninmu, ka ajiye mana atm ɗin zamu kar6a" jiki na rawa ya ruƙo hannun Zaid suka fuce daga ɗakin. Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa Ya maida atm ɗin inda ya ɗaukosa, komawa yai gefen gadon ya zauna yana cin abincin Da abla ta kawoma Hajiya saratu
*Dr.Jazz*
Tun zuwa shi gidan Mommynsa ta ke ta faman tarairayarsa tamkar ƙaramin yaro, Yana daga kishingiɗine saman doguwar sofa ya ɗaura kanshi saman laps ɗinsa, Sai zuba mata shagwa6a yake yi, yatsun Hannayenta na acikin sumar kanshi Tana yi mashi susa Mahaifiyar Dr.Jazz Baturiyar ƙasar England ce, sunanta na asali Harriet, Silar zuwanta aikatau gidan ta musulunta suka canza mata suna zuwa khadija amma sunfi kiranta da Turai, Farace jawur tana da jiki bata da tsayi launin idonta green ne, sumar kanta launin blonde, A yanzu ba matsayin mai aiki take ba, Matace awurin Sir mubarak, Ya daɗe da auranta tun Bayan rasuwar matarshi Hajiya naja'at, Ƴa'ƴan shi biyu da uwar gidansa gaba ɗayansu ba mazauna Nigeria bane, Suna a ƙasar canada suna kula da Babban companynsu tare da sauran ƴan uwansu dake zaune agidan Hateem. Turkish dress ne a jikinta, Riga da wando launin red colour, Ta ɗaura satin scarve asaman wuyanta, ta zubo da gashin kanta har gadon baya, Allah yayita da ruwan kyau. "Jazz sai nake ganin kamar baka yi kewata ba, Meyasa bakasan zuwa ganina? kullum Sai in ni na shiga gida nake samun damar ganinka idan naci sa'a baka tafi aiki ba. Fararen idanuwanshi ya daura akan fuskarta, "Mommy ba haka bane, Ni just banason haɗuwa da daddyne, ya cika faɗa, kuma sharri yake yi min yana cewa wai ni mata maza ne, Fisabilillah" "Ya faɗi hakanne donka Gyara rayuwarka, ni kaina ina mamakin shagwa6arka sai kace wani yaron goye, komai naka irin na mata"
Ɗaure mata fuska yai"mommy kina goyan bayansa kenan, yaci gaba da kira na mata maza"? Girgiza mashi kai tai"A'a, Ai nafi kowa jin haushin inji ya kiraka da hakan, Yana ta6a min zuciyana, donni nasan namiji na haifa ba maca ba" murmushi Jazz Ya saki"to kice mashi ya daina" "Zan buga mashi warning, kada ka damuwa" maƙe mata kafadai yai"Allah mommy ni nasani wasa kikeyi, saboda ke kanki shakkarshi kike ji ba zaki Iya buɗe baki ki yi mashi magana akan ya daina ba" Jan kumatunshi tayi da hannunta In jiwa ya faɗa maka! Ni bana jin tsoronshi awaja ne mutane ke jin shakkarshi, da zarar ya shigo nake juya shi son raina, Har girki yana yi min" Baki asake Jazz ke kallonta "Uncle mubarak ɗin"! Jinjina masa kai ta yi"ƙwarai kuwa, ae dukkan Namiji bawan matane, Har ya buɗe baki zai ƙara magana, Wayar Aljihun wandonshi ta soma ruri, miƙewa yai da sauri ya curo wayar, bayan ya duba sunan mai kiran nashi ya ɗago tare da kallon mommynsa, Wanene ya kira"?
Bai amsa mata ba sai dai ya sakar mata murmushi, da sauri Ya fito daga falon gidan, Kamar wani munafuki duk faɗin gidan bai isheshi ba sai da ya shiga garden tukunna ya dakata da yin tafiyar, Yai picking call ɗin jiki na rawa ya kara ta akan kunnansa, Kirari ya soma yiwa wanda ya kira shi wayar tamkar maroƙi, "Yalla6ai Kajin nan suna nan cikin ƙoshin Lafiya, Suna samun kyakkyawar kulawa yadda ya dace," dakatawa ya ɗanyi da yin maganar, yana sauraron muryar mai magana, "Ana basu hatsi yalla6ai mai rai da lafiya, Yanzu haka idan nagama magana da mama zan tafi gidan gona domin duba lafiyarsu," sai faman sakin murmushi yake yi, aladabce yake yin maganar 'kasan kajin turawa saida hatsi mai kyau, Gaskiya basu da matsala yalla6ai, biyu daga cikinsu ne kaɗai suke neman gazawa, shi zakaran ciwon nashi Ya lafa, sauran Kajin muna nan muna basu kyakkyawar kulawa, in sha Allah zasu samu lafiya harma asamu nayin farfesun sallah"
Tuntsirewa dr Jazz yai da dariya hada dafe ciki. duk wannan surutun da ya ke yi acikin waya baisan Sir Mubarak na tsaye abayanshi ba, daga shi sai gajeran wando, Da singlet fara, hannunshi ɗaya ruƙe da Cup na coffee
Mamaki ne ƙarara akan fuskarshi Jin dr jazz na Zancan kajin turawa awaya
"Okey toh, Zuwa anjima idan nashiga gidan Gonar zan Kiraka Awaya" Daga haka sukayi sallama, Juyawar da zaiyi karaf suka haɗa ido da sir mubarak, tuni yasha jinin jikinsa, Duƙar da kai ƙasa yai ido ya raina fata "Jazz! Dawa kake magana a waya? Kajin menene naji ana magana akai? Ni dai A iya sanina likitan mutane ne kai bana dabbobi ba" sosa ƙeya jazz yai, mirya dabarbarce yake faɗin"am...umm..dama " Ya rasa ta ina zai taro zancen, Kallon tuhuma Sir mubarak ke jafa mashi hakan yasashi yin saurin fauzewa "daddy, Ni da abokina ne dr fawan muka buɗe gidan gona, kajin turawa ne muke kiwo, wasu ne babu lafiya shine ya kira muna tattaunawa game da yadda zamu shawo kan matsalar" Ajiyar zuciya Sir Mubarak Ya sauke"Okey, mu shiga gidan" yai maganar tare da miƙa mashi Cup din hannunsa, da sauri jazz Ya kar6a Yana sha atare suka nufi gidan sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi.
*GIDAN ƊAN IYA*
Mahboob ne ke ta faman zuba sauri Yana tunkarar harabar ajiye motocin su, ya ɗauki wankan shadda, tunkan Ya ƙarasa idonshi ya sauka akan motar Uncle abdallah, ƙura ido yai yana kallon bayan motar sunanta Ya karanta, Aranshi Ya ayyana lallai mutanan nan ba ƙananun shaggu bane wannan mota haka mai tsada! saboda almubazzaranci da rashin sanin ciwon kuɗi, Ina laifin ko ƴar ƙaramar honda mutun ya saya ya wadatar, mutane sun ɗaurewa ƙaryar arziƙi wurin zama, Allah dai ya shirya mu, ae ni wlh ko nayi arziƙi ban Iya fidda kuɗina in sayi mota, na ƙwammace duk inda zanje in taka da ƙafata, idan ma da nisa ne ƙwara in biya kuɗi In hau motar Haya, Ita ma wannan motar da nake amfani da ita ba don babansu abokina ne ya bani kyautarta ba kuma ina ganin mutuncin shi saboda ya ji tausayina ya siyamin ganin ina hawa motar haya yasin da tuni na jima da siyar da ita' Shi kaɗai ya ke yin sambatunsa, Har ya ƙarasa gaban motarshi Ya buɗe front seat Ya shiga Ciki Yana ƴan dube dube, da alama wani abu yake nema, saƙo da lungu na motar yake ta bincikawa, har ƙarkashin seat, tuni ya haɗa uban gumi.
"Ina na ajiye zoben nan Jiya? Ko dai ban shigo da shi mota bane? fuskarshi a hautsine Ya jefawa kanshi tambayar, zurfin tunani ya shiga yi still bai tunano inda ya ajiye shi ba, A ƙarshe Ya soma tunanin kodai Ya shigar da shi ɗaki ne,
Fitowa yai daga cikin motar Ya datse murfin, Jiki na 6ari ya nufi cikin gidan.
Abie da Uncle ɗan Iya ne zaune a saman sofas na palourn tare da Uncle abdallah, Sun nutsa suna tattaunawa dangane da 6acewarsu tajuddeen, Mahboob Ya faɗo falon Ko kallo basu ishe shi ba hankalin shi na akan zoben shi da bai gani ba.
"Wancan ba mahboob bane? Kamar naso na wayi fuskarshi" Uncle abdalla ne yai maganar,
Girgiza kai uncle ɗan Iya yayi Yayin da yake bin bayan mahboob dake ƙoƙarin karya kwana zai nufi sashen ɗakinsa "Shine, halan bai gaishe ka ba"?
Murmushi ɗauke akan fuskar Uncle Abdalla yace"Tun da muka zo ban yi tozali da shi ba, sai dai naji labarin shi awurin junaid"
Cikin nuna 6acin rai Ɗan Iya yace"baida wayau ne ai ni bansan baizo ya gaishe ka ba, bari ya fito daga ɗakin ɗan rainin wayau, Zahra tafi shi hankali"
Abie yace"Ƙuruciyace ke damunshi, Zahra kuma ae tafi shi shekaru baza a haɗata da shi ba" Ɗan Iya yace"babu wata ƙuruciya atare da shi, Sarai yasan me yake yi sai girman jiki ba wayau" da alama Ranshi ya 6aci da rashin gaishe da uncle abdallah da baiyi ba.
Kafin wani daga cikinsu ya ƙara yin magana Hajiya adama ta fito daga ɗaki hannunta ɗauke da baby junaid, tun da ya dawo daga school a wurinta ya wuni ya hanata sakat duk inda za ta je ƙafarta kafarshi toilet ne kaɗai yake bari ta shiga, Ta canza Kayan jikinta zuwa atampa riga da skirt, Ta yafa mayafi akanta, kafin ta ƙarasa shiga palourn Mamie ta fito daga ɗakin Ummi su biyu ganinta yasa suka nufi wurinta fuskokin kowannansu da fara'a suka soma gaisawa da junansu
Atare suka ƙarasa shiga palourn, Kowa ya samu wuri ya zauna, Kafin suka fara gaishe da Mazajensu, miƙa ma junaid hannu uncle abdallah yai"zonan kyakkyawan Jikana mu gaisa," da sauri Junaid ya sauko daga saman laps din Hajiya adama ya nufi sofa ɗin da uncle abdalla yake azaune Ya haye saman jikinshi yana faman sakar mashi murmushi, shafa fuskarshi yai da tafin hannunshi"Masha Allah mutumina, Ka tashi lafiya? Fadamin meyasa baka je school ba yau? Sannan baka bi mu zuwa masallacin Juma'a ba" Zaro ido Junaid yai haɗi da ɗan girgiza kanshi muryarshi da shagwa6e yace"nafa je, ae yau da wuri ake tada mu duk ranar juma'a, kuma ni ai ban isa zuwa masallaci ba inji mommy" maganarshi ba ƙaramin ƙayatar da su take yi ba, musamman In ya haɗa da shagwa6a,
"Junaid kaji tsoron Allah, Aneelerh ce ta faɗa maka haka? Faɗamin gaskiya ka dai san me ƙarya ɗan wuta ne" jin haka yasa shi saurin sanya tafukan hannayenshi biyu ya toshe fuskarshi Yana tiƙar dariya" muryarshi ƙasa ƙasa ya furta"ba ita bane, ae malaminmu ne yace mu ƙananu ne bamu isa ɗaukar zunubi ba" gaba ɗaya suka saki dariya, bayan sun tsagaita da yin dariyar ne, Uncle ɗan Iya yai masu gyaran murya hakan yasa suka dawo da dubansu gare shi.
"Dama yanzu nake shirin aikawa a kira mun ku, don mu haɗu duka muyi magana, Kafin mu shiga cikin zancen Ina ƙara yiwa baƙinmu barka da zuwa fatan kun wayi gari lafiya" da fara'a Hajiya adama ta amsa mashi a mutunce
Mami tace"tun ɗazu da safe take son yin magana mun fara sai nace ta bari idan kuka dawo daga masallacin juma'a zaifi mu haɗu mu duka mu tattauna tunda abune daya shafi kowannanmu da buƙatar aji shawara daga bakin kowa"
Jinjina kai Abie yai"hakane, Yanzu Ina aneelerhn take"?
"Tana a ɗakin zahra, Bari na shiga na kirata" kafin ta mike muryar junaid ta katse mata hanzarinta. "Ni zan Kirata" Bai jira amsarta ba, Ya sauko da gudu Ya nufi Ɗakinsu, uncle abdallah ne ya ɗan ɗaga murya yana yi mashi faɗan ya daina gudu kada ya faɗi yaji ciwo, Jin haka yasa shi dakatawa da yin gudun ya soma yin tafiya a tsanake
A lokacin Aneelerh da Zahra suna zaune saman gado kowa ya dafi waya suna fira suna chatting, sun ɗauki wankan dogayen riguna "Ba zaki leƙa wurin surukar taki ba? Kin barta a ɗaki ita kaɗai" acewar zahra "Ɗazu da safe na shiga na gaishe ta, har ma na tarar da mami zaune suna tattaunawa shiyasa ban tsaya ba," "Gaskiya aneelerh ki godewa Allah, surukarki tana da mutunci ta iya magana ga faran faran da jama'a, Ni wlh ba ƙaramin burgeni take yi ba, Inasonta sosai, da ace tana da wani ɗan Bayan Yaya uzair Allah dana aure shi" har cikin zuciyarta take yin maganar, Aneelerh na murmushi tace"Chief Owais din fa? Ko kin fasa"! farfari Zahra Tayi mata da ido "shi wannan na dabanne, idan ana maganar ƙarauƙarau ba a maganar Zinari, My dream man inaji araina ma ya kusa dawowa ƙasar jiya har mafarkinsa nayi" Murmushin gefen fuska Aneelerh ta saki "Allah Ya cika maki burinki zahra, Ni na ƙosa inga fuskar Owais ɗin nan, har tambayarki nayi hotonsa kinƙi ki nuna min, bansani ba ko rowa kike yi min" dariya Zahra tayi"Ina jin fargabar zuciyarki ta buga silar ganin kyakkyawar fuskarshi, kuma kinga ke matar aure ce bana son ki kalli haramun" Sakin baki aneelerh tayi yayin da take kallonta, tama rasa bakin magana "Fuskarshi tsadane da ita, idan har zaki Iya biyan farashi sai muyi ciniki in nuna maki" fashewa da dariya aneeleeh tayi jin wani zancen abakin zahra. Faɗowa Ɗakin Junaid yai tun abakin ƙofa yake faman ƙwala mata kira"Mommy!mommy!" a hanzarce ta kai idonta ga ƙofar "Babyn mommy lafiya kake ta ƙwalamun kira" tai maganar tare da sakowa daga saman gadon ta nufe shi, hannu biyi tasa ta ɗauke shi tana kallon fuskarshi "Mommy ana kiranki, ki zo inji su abie" "Sune sukace ka kira ni"? Ɗaga mta kai yai alamar eh ya ƙara da cewa"ke kaɗai banda Zahra" Harara zahra Ta wurga mashi"aiko sai naje ɗan baƙin ciki, so kake kayi mun buƙulu wata'ƙil ƙudi ne za'a raba mana, Saukowa tai daga saman gadon ta ɗauko masu mayafi a closet ita da Aneelerh ta yafa mata akanta, atare suka fuce daga ɗakin zuwa palour