Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 63

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 63

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 63: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 63. Lumshe ido owais yai, A hankali ya furta sunan…

3,324 words

Lumshe ido owais yai, A hankali ya furta sunan big guy, on the other hand big guy ya amsa mashi da na'am yalla6ai"

"Sako ya shigo min daga Uncle Hateem, Zuwa gobe da safe Sheikh Imam zaizo Nigeria, yayi tafiya ne zuwa sudan, ka yi ma brother din yaron nan magana ya tambaye shi idan yana jin yunwa ya fadi me zai iya ci akawo mashi" amsa mashi yai da toh. Ya mayar da dubanshi ga su salsabeel"tun da yana jin maganarka ka tambayar mana shi me zai Iya ci akawo mashi, sannan pls kace mashi ya kwantar da hankalinshi zuwa gobe insha Allah sheik imam zai shigo Nigeria, shahararran malamin addinine muna da tabbacin zai Iya taimaka mashi"

Gyaɗa kai salsabeel yai"ay yana sauraronka, Yanzu haka magana yake yi min.

"Meyasa kuka harbe shi? Duk da harsashin bai fasa jikinshi ba yayi mashi illah saboda babu kakin giant a jikinshi"

Hankalin Unaisah dana Big guy ya tashi matuƙar, muryarta na rawa ta furta"meya faru dashi? Yaji ciwo ajikin shi" "Bazan Iya sani ba, sai ya dawo suffarshi ta mutane tukunna zamu ga illar da yayi mashi, sannan ya fadamin yana son kayan marmari su kadai yake sha'awar sha"

Damuwace ƙarara akan fuskar Angel"meyasa bazai Iya cin abinci ba"? Ta fada tana duban salsabeel.

"A halin yanzu Danish dinki, ba mutun bane Giant snake nake, bazai Iya cin kalar abincin mu ba, har sai ya dawo cikakken mutun.

Kwa6e fuska tayi tana duban kan macijin, har yanzu bai dagoba tunda ya kwantar da kanshi saman jikinshi daya nannaɗe.

Miƙewa tsaye big guy yai"ka zauna atare dasu, zan je na kawo mashi kayan marmarin" amsa mashi salsabeel yayi da toh.

Bayan fitar big guy, ta ƙura ma salsabeel ido, har yanzu mamakin ganinshi take yi, abubuwa dayawa sun cunkushe mata brain dinta, tana son jin ya akai ya tsira daga kurkukun ƙaddara? Shin ya sauran ƴan uwansu suka ƙare sun mutu ko sun rayu? Tayaya Akai Ya haɗu da jami'an da suke kula dasu? Ko dai dama shima jami'insu ne!? ta ɗaura mashi alamar tambaya, tadai haƙura ne har zuwa time din da danish zai rikiɗa ya dawo mutun donjin amsar tambayoyinta, kamar yadda take kallon Salsabeel haka shima yake kallonta, yayi kewarsu sosai, kuma yaji dadin ganinsu, da ransu da lafiyarsu, bakomai yake tunawa ba face ranar daya fara haduwa da ita har yakaita dakin da suka tattauna, da kuma ranar da ya ceci rayuwarta lokacin da matsafa sukayi mata wanka da jini, ranar da ta azabtu ta galabaita, Allah kenan mai yadda yaso mai jujjuya al'amurra, yanzu tamkar ba'ayi ba, tayi haske abunta gwanin kyau har girma ta ƙara mashi akan yadda suka yi rabuwar ƙarshe a kurkuku.

Murmushi yasakar mata, itama ta mayar mashi da martanin murmushin, ya fahimci aƙagare take da son jin labarin ƴan uwanta daga gare shi.

*PRISONERS💔✍️*

Tun bayan fitowar Batul daga ɗakin Ummin america, a tsakar dare ta nufi down stair, baiwar Allah tana tafiya jikinta na kakarwa, hatta haƙoranta kerma sukeyi suna hadewa jikin juna, tsoro take ji ita kaɗai kamar aljana, sai faman firgita take yi gani take yi kamar macijin zai kawo mata hari.

Daƙyar take iya taka ƙafarta saman floor din falo, ga wani azababban tari daya farmata.

Sam ba ta ji takun tafiyar mutum ba, saboda hankalinta ba akwance yake ba, sai ƴan waige waige take yi tana faman hadiyar yawu.

Yayi mamakin ganin ɗaya daga cikin yaran tana yawo a tsakar dare, babu mayafi a jikinta, ƙura mata ido yai a ƙoƙarinshi naya gano wacece acikinsu, ya rasa gane batul ce ko Unaisah, saboda launin gashinsu kala ɗaya ne ga kuma nannaɗewar sumar kan nasu daya kasance iri ɗaya, zuciyarshi ce ta raya mashi cewa Unaisah tana adaki fa ya barota tare da salsabeel wannan ba ita bace sai dai ko ƴar uwarta ce Batul.

Da ƙarfi ya ambaci sunanta"Batul" rass taji gabanta Ya faɗi, a firgice ta waiwayo don ganin wanene, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar big guy dake sanye cikin face mask,l.

Tsabar tsoro da ruɗu yasa ta zabura zata watsa da gudu, sai dai kafin tayi hakan yai saurin haura ƙafa ya damƙo damtsen hannunta ya janyota zuwa jikin shi, ƙanƙame shi tayi atsorace ga tari da take yi.

Lamarin ya ɗaure mashi kai, ɗago da kanta yai daga saman ƙirjinshi ya furta"ke! Daga ina kike? Ya akai kika fito daga ɗaki"? Daƙyar ta Iya buɗe baki tace"sanyi nake ji babu bargo shine na fito zani ɗaki in ɗauko" "Awani ɗaki kike"? "Ɗakin aunty ummi, boss man ne yace muje can mu kwana, saboda munajin tsoron kwana ana mu dakin"

"Meyasa baki tambayeta ta baki bargo ba"? A tsoroce take yi mashi magana"tayi bacci ne, kafin ta kwanta ma saida nace ta taimaka ma parveen da kaya ta sanya saboda tayi ma nata fitsari sunjiƙe sharkaf amma taƙi bata sai dai ni na cire nawa muka yi musanya ta bani nata, kuma ɗakinta sanyi sosai" Tunda tafara magana Big guy yake jinjina kanshi, ga dukkan alamu ya fusata matuƙa, bashi ba hatta chief owais dake acan room dinsa yana sauraron maganganunsu.

Ruƙo hannun Batul yayi acikin nashi ya juya da ita suka nufi ɗakin.

A lokacin Ummin america tana ƙoƙarin fitowa daga cikin toilet, ta gama sheƙe ayarta da gardin daya kirata awaya, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, zura ƙafarta keda wuya hasken ɗakinta Ya kama, a firgice takai idanuwanta kan masu shigowa ciki, tunda tayi arba da big guy tare da batul gabanta yai mugun faɗuwa.

Wani irin kallon tuhuma yake jefa mata, ranshi amatuƙar 6ace ya soma magana.

"Ke baki da hankaline? Kin ajiye yara aɗaki kin kure masu sanyin A.c ? Idan ƴa'ƴankine na cikinki zaki Iya yi masu haka"?

Muryarta adabarbarce tace"am..ba haka bane ni ai bansan basu iya jure sanyin A.c din ba, na saba kwana....." bata ƙare maganar ba, Ya daka mata tsawar data firgitar da ita, sakin hannun batul yai ya matsa kusa da ita, abunda wani ɗa namiji bai ta6a gigin yi mata ba, da yatsan hannunshi ya nuna ta"ki shiga taitayinki, This is the last time I'll warn you. Don't be reckless in your work. We don't accept mistakes, koda gigin wasa kada ki kuskura ki ƙara maimaita laifin nan" yana huci ya faɗa "Yarinya harta fara mura tana tari! Ke ko ajikinki ai nayi tunanin zanzo na sameki kina bacci ashe idonki biyu hakan na nufin da gangan kika kure sanyin A.c din dakinki, Ke bari kiji bana so gobe da safe inji yarinyar nan tana yin mura, ki san yadda zakiyi ta dawo daidai, bama itaba hatta sauran ƴan uwanta kada ki bari ɗaya daga cikinsu ya tashi da mura, idan ba haka ba zaki fuskanci hukunci mai tsanani daga hannun chief.. " hankalin ummin america ba ƙaramin tashi yai ba, duk tabi ta susuce musamman daya ambaci sunan owais, muryarta na rawa take fadin"na kar6i laifina bazan ƙaraba, kuma aini bansan sanyin zaiyi masu illa ba..." bai bari ta ƙare maganar ba ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu"bana sonji, kawai kiyi abunda ya dace don ki ceci kanki, nabarki lafiya" afusace ya juya zai bar dakin har ya kusa fita karaf idanuwanshi suka sauka akan parveen dake kwance saman carpet tana yin bacci, Arude ummi ta furta"yanzu zan maida ta saman gado, bansan ya akai ta faɗo ƙasa ba" wani ɗan iskan kallo big guy ya watsa mata.

Kafin ya maida dubanshi ga batul"ke ina yar uwarku take? ya akai naga ku huɗune? Where's hannah"!

Sai daya ambaci hakan batul ta tuna da babu hanna acikinsu, waige waige ta soma yi jikinta na rawa tace"bansan a ina take ba, tare da ita muka nufo dakin aunty ummi, ni na ruƙo hannunsu ita da Parveen bansan ta kufce min ba, dama aruɗe take"

Gyaɗa kanshi yai"okey, wuce kije ki kwanta, zanje na nemota" ya faɗa tare da juyawa ya kalli ummi dake ta rawar jiki"ina ƙara jaddada maki kada ki bari yaran nan su wayi gari babu lafiya, idan kunne yaji jiki ya tsira" yana fadin hakan ya haura ƙafa yabar ɗakin. Fitar shi keda wuya, Ummi ta ɗaure fuskarta tamau babu annuri, ranta ya 6aci matuƙa, hankalin batul ba ƙaramin tashi yai ba ganin tana tunkarota, girgiza kai tadinga yi tana nufar bango harta kure mashi, "Dan Allah kada ki ta6ani, bani da lafiya..."daƙyar ta furta maganar, "Ni ki ka kai ƙarana a wurinsu? Yaushe kika fita daga dakin munafukar banza, harni zakija ma bala'i ina zaman zaman lafiyana? Kinsan wacece ni? Don ubanki!

Girgiza kai batul tayi tuni hawaye sun wankan fuskarta"aunty ummi kiyi hakuri bazan ƙaraba, dan Allah kada ki ta6ani" Tsawa ta daka mata"kashe ki zanyi, kinyi kuskura batul da kika gaya mashi abunda ya faru tsakanina daku, wallahi sai kinyi danasanin sanina da kikayi, don kuwa daga rana irinta yau bazaki ƙara dariya ba zan ƙuntata maki har sai kinji kin tsani kanki"

Fashewa batul tayi da kuka mai tsuma zuciya, saboda rashin imani ummi ta sanya hannu ta shaƙi wuyanta tamkar zata kashe ta, "Jibarki dallah, jahila dake, bakisan komai ba sai cin abinci da bacci, ni ban ta6a ganin daƙiƙiya ba irinki"

"Batul ! Batul! Meyasa kike kuka"? Jin muryar Parveen yasa ummi yin saurin sakin wuyan batul, jiki ba ƙwari ta sulale ƙasa tana cigaba da yin kuka

"Kiyi min shiru idan kika bari wani yaji wallahi saina naƙasa ki wawuya" da sauri batul ta haɗiye kukanta, baiwar Allah hada sanya hannu ta share hawayen fuskarta. Shu'umin murmushi tasaki kafin ta juya tana kallon parveen data farka tana faman mutsustsuke idanuwanta "Ke tashi ki koma saman gado ki kwanta" muryar ummi ce ta fargar da Parveen ta ware idanuwanta sosai akan fuskokinsu Muryarta da kasalar bacci tace"batul make faruwa? Meyasa kika zauna a ƙasa"? Tai maganar tana kokarin miƙewa da niyar taje wurin Batul, ummi ta dakatar da ita"cewa nayi kije ki kwanta saman gado, babu abunda ya sameta, kaya zan bata ta sanya ajikinta" jiki asanyaye parveen ta nufi gadon donta kwanta sai dai hankalinta bai kwanta ba da yanayin data riski batul "Parveen ki kwanta kiyi bacci, lafiyata ƙalau, yanzu aunty ummi zata bani kaya in canza na jikina sai inzo mu kwanta a gadon" ajiyar zuciya parveen ta sauke jin batul tayi mata magana, hayewa tayi saman gadon ta kwanta batare data rufe idanuwantaba. Ta6e baki ummi tayi tare da mayar da dubanta kan Batul, badan taso ba tace"shashasha, Ki jirani in dauko miki kayan" cikin sanyin murya batul tace"toh" Wuce wa tayi cikin ɗakin can inda katafaren closet dinta yake, ta bude ta dauko jibgegiyar sweater tare da dogon wando, ta haɗo da duvet, ta nannaɗosu ta dawo inda batul take a zaune ta wurga mata su saman jikinta "Salon kuma kiyi min ƙazanta, ni bana sharing kaya da wani don yazamarnin dolene" ta faɗa tare da juyawa ta nufi gaban mirror inda ta daura A.c remote ta kashe ta gaba daya, ta kunna masu room heater, duk don saboda gudun kada gobe aji basu lafiya, shiyasa tayi hakan. Miƙewa batul tayi hannunta ruke da sweater din, ta zame hannun doguwar rigar jikinta, da dabara ta zura sweater din, tayi mata girma, haka wandonma yayi mata faɗi, ahaka ta sanya su, kafin ta cire rigar jikinta, anan ƙasa tabarta, ta nufi saman gadon ta haye gefen parveen ta kwanta, ta lullu6e masu bargon su dukansu, kafin ta rungume parveen a jikinta, duk don ta samu sauƙin raɗaɗin da take ji, ta tsorata da ummi kalaman da tayi mata sun tsaya mata arai, fargabanta kada ta kashe ta, tuni idanuwanta sun cicciko da ƙwalla Cikin muryar raɗa parveen take yi mata magaba"batul tayi maki wani abu ko? Ni naji ajikina" daƙyar ta iya furta"kiyi shiru parveen kada tajimu, ni batayi min komai ba, bana jin daɗin jikinane" Sautin kuskus din da suke yi ne yaja hankalin ummi ga kallon bargon da suka lullu6a dashi atsawa tace"kada in kuskura in ƙarajin maganarki! Ko tari bana sonji" tsit sukayi shiru suna faman ƙanƙame junansu .........

*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✍️*

Idan muka koma 6angaren Hajiya saratu data garƙame kanta acikin toilet, tsoro da fargaba sun hana ta sukuni, ta haɗa uban gumi zufa ta ko'ina take tsastsafo mata, ga wani takurarran bacci daya addabi idanuwanta, ta rasa ya za ta yi, ta kasa tsaye takasa zaune, sai zarya take yi acikin toilet, jin shiru tsit babu sautin komai daga waje hakan yasa tayi tsammanin ko dai jami'an sun kashe macijin ne, cikin sanɗa take yin tafiya tana tunkarar toilet door, ta ruƙo handle din ƙofar ta buɗeta, shigowa ɗaki tayi ta nufi wayarta dake ajiye saman bedside drawer takai hannu ta ɗauke ta tana ƴa waige waige duk tabi ta ruɗe.

Layin pravin ta danna ma kira, kusan sau uku bai ɗaga ba, hankalinta ashe take fadin"pravin ka ɗaga kirana mana"

Sake kiran layin tayi, a lokacin da kiran ya shigo mashi yana a kwance saman shimfiɗeɗɗan gadon hajjaty, sleeping dress ne ajikinta, shi kuma shorts ne babu riga, ya rungumeta a kirjinshi, sun manne ma juna, duvet din daya lullu6a masu iya saitin kafaɗunsu ya tsaya.

Bacci ya ƙaura ce ma idanuwan hajjaty, tun da tayi tozali da narkekan macijin nan, lallashinta yake yi duk don ya samu ta kwantar da hankalinta.

"Pravin wayarka fa tana ringing yakamata ka duba me kiranka"

"Nasan wa ke kira na, bai wuci hajiya saratu bace, ta gama ci min mutunci shine yanzu take kirana saboda ta tsorata da ganin maciji, wallahi ba zan je ba, nafi so taji a jikin ta"

Muryar hajjaty ƙasa ƙasa tamkar me yi mashi raɗa ta furta"please, matarka ce, yakamata kana darajata"

"Ni ma ai batasan darajata ba, saratu bata girmamani, tayi min gori ta gaya min maganganun da suka ƙona min rai, sauƙin ma ba ita ka ɗai bace Ina dake"

Lumshe mashi ido hajjaty tayi, Yaci gaba da cewa"kina ƙaunata tsakani da Allah, baki ta6a guduna ba, kin rabu da kowa naki kin biyoni Nigeria, a zaman da mukayi dake ni baki ta6a yi min laifi ba..." ƙayataccen murmushi tasakar mashi.

"Ina fata kai ma ba zaka ta6a guduna ba, Kuma ba zaka ta6a yi min laifi ba, pravin bani da kowa a halin yanzu Allah ne gatana sai kuma kai, dan Allah ka ruƙe min amana kada ka aikata abun da zaiyi silar rabuwar mu, ka ji tsoron Allah a dukkan lamuranka na rayuwa, idan kana tunawa da mutuwa zaka ƙara jin tsoron Allah, bana so wata rana muyi abun da zamu yi danasani arayuwarmu..."

Bai bari ta ƙare maganar ba yai hanzarin katse ta"my woman, bansan yaushe kika fara yin wa'azi ba, idan ban manta ba, Ni ne na koya maki alwala ko"

Dariya ta saki jin abunda pravin yace, kafin ta ƙara cewa wani abu ya rigata fadin"muyi bacci please dare yana ƙara nutsawa" da shagwa6a hajjaty tace"ni dai ka tafi ɗakin matar ka, ita yakamata ace kana atare da ita bani ba"

"Bana so in bar ki ne saboda na lura haryanzu jikin ki bai daina kerma ba"

"Amma itama saratun ai tsoron take ji, tana buƙatarka agefenta, pls ka tafi wajenta, Ni nafiso kana kamanta adalci a tsakanin..." bai bari ta ƙare maganar ba, yai saurin haɗe bakinsu, ya zura hannayenshi biyu cikin rigar baccin jikinta, sarrafata ya soma yi cikin ƙanƙanin lokaci ya fara caza mata kai, yayi mata hakanne don ya mantar da ita zancen tafiyar da take yi mashi, kuma yaci galaba akanta, bai rabu da ita ba har saida yaji ta fara yin bacci tukunna ya ƙanƙameta.

Phone dinsa sai ringing take yi, tana daga can gefe daya saman mattress din, a hankali ya raba jikinsa daga nata.

Ya laluba hannu ya damƙo wayar, murmushin mugunta ya saki kafin ya ɗaga kiran.

Ko sallama babu hajiya saratu tace"pravin ina ka shiga? Ina ta kira baka picking! Ba zaka dawo daki ka kwanta ba ne"?

Tun daga kan muryarta ya fahimci babu natsuwa atare da ita "Me zan dawo nayi maki? Ni da bani da amfani awajenki"? Muryarta tamkar zata fashe mashi da kuka tace'kaga ni ba wannan na tambayeka ba, ina son ganinka ka, pravin, hankalina ba akwance yake ba, nasan kaga abunda ya faru ɗazu"

Tuntsirewa yayi da dariyar mugunta, ran hajiya saratu ya 6aci matuƙar masifa ta soma zazzaga mashi sai da tayi mai isarta tukunna ya katse ta da cewa"saratu kenan, kefa da kanki kikace nine ɗan kwali ke ce hula, hakan na nufin kece namiji ko? To meyasa kike neman mace donta baki kariya? A tunanina ni yakamata inji tsoro bake ba, shi namiji da jarumta aka san shi bada ragwantaka ba"!

Takaicin duniya ya ishi hajiya saratu, cikin lalama tace"pravin dan Allah ka dawo ɗaki, idan saboda abun da na fada maka ne ya 6ata maka rai, zan baka haƙuri"

"Bana buƙatar haƙurin ki saratu, lokacin daya dace ki lallasheni ki tarairayeni ki bani hakuri bakiyi ba till now da buƙatar kan ki ce ko? An gaya maki ni shashashane bansan ciwon kaina ba"?

Shiru bata tanka mashi ba, kuma tana sauraronshi.

"Ko gobe kada kiyi tunanin zan dawo gida, ni yanzu haka ma gani akwance tare da wadda tafi ki iya tarairayar miji....."tsawar da ta daka mashi ce ta sanya shi yin shiru, tamkar zata fasa mashi screen din wayarshi"ya isa haka! Ya isa! Kada ka ƙara maimaita min maganar da kayi idan ba so kake ranka ya 6aci ba......" bata ƙare maganar ba, yai rejecting kiran, Ya jefar da wayar saman mattress, Ya janyo hajjaty a jikinshi, ya daura hannunshi saman sumar kanta, har cikin ranshi yana ƙara jin ƙaunarta, bai da tamkarta a duniyar nan, saboda kyautata mashin da take Yi, yana matuƙar ƙaunarta, kiss ya manna mata saman forehead nata, kafin ya cusa kanshi gefen wuyanta, ƙamshin turarenta ya daki hancinsa ahaka bacci yai awon gaba da shi.

Jefar da wayar hannunta tayi saman gado, ranta ya 6aci matuƙa pravin ya ƙona mata rai, kishine da ita, gani take kamar dagaske ne abun da ya faɗa mata yana can shida wata suna sheƙe ayarsu, kokwanton maganarshi take Yi, ta riga ta yarda da pravin tasan bazai Iya cin amanarta ba, wata'kil ya faɗa mata hakanne don ya huce raɗaɗin abunda tayi mashi.

Damuwace ƙarara akan fuskar hajiya saratu, adaddafe ta nufi gado ta haye ta kwanta idanuwanta suna fuskantar ceilling, babu alamun zata runtsa adaren Yau.

*Hajiya Turai💔*

Safa da marwa take Yi acikin ɗakinta, Hannunta ruƙe da wayarta, night gown ce a jikinta.

Fuskarta tayi jawur tamkar wadda tasha kuka, musamman kumatuntu, green eyes dinta kuwa sun ciza launinsu, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, since wuraren ƙarfe goma take kiran layin dr.jazz babu alamun zai ɗaga, gashi har dare ya nutsa bai dawo gida ba, ta kira layin Sir mubarak kusan sau talatin shima Bai daga ba tamkar ta fasa ihu haka take ji.

"Mom" kamar daga sama taji an ambaci sunanta, tsabar ruɗi sai taji kamar muryar jazz ne.

A firgice ta juyo don ganin wanene, Yana daga tsaye bakin ƙofar ɗaki, cikin shiga ta kayan bacci ya zura hannayenshi cikin aljihun wandonshi, matashin saurayi ne kamanninshi sak dana Sir mubarak.

"Ibad kai ma baka yi bacci ba"? Muryarshi da kalasa ya furta" How can I sleep, Mom? Jazz hasn't come home yet. na jaraba kiran layukan wayarsu duk akashe, bansani ba shi jazz ko aikin kwana yake yi a asibiti, nazo ne naji ko sun faɗa maki meya hana su dawowa gida"?

Ta lura da yanayin shi tsantsar damuwace akan face dinsa, batayi mamaki ba saboda ƙaunar da suke yi ma Jazz, sun dauke shi tamkar shaƙiƙinsu

"Ibad, I don't know why they haven't come home yet, I've been trying their phones since 10 o'clock, and nobody is picking up. I'm really worried, inajin fargabar ace wani abun ne ya faru da su" tuni idanuwanta sun ciko tab da ƙwalla.

Ruƙo hannunta Ibad yai"haba mommy, kada ki zubda hawayenki please, ki kwantar da hankalin ki, Everything is going to be okay. They'll come home safely."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull