Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 8
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 8: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 8. ƙurmin Daji ne mai nau'ikan tsirrai da dabbobi…
3,302 words
ƙurmin Daji ne mai nau'ikan tsirrai da dabbobi iri-iri. Manya manyan bishiyoyi masu tsayi da faɗi suna da Dogayen rassa, Faɗaɗan Ganyayyakinsu Sun toshe hasken Farin watan da ke a sararin samaniya kaɗan ne ke samun damar haskowa ta tsakankanin Ganyayyakin, yau shekara Uku da watanni rabon da ta tsinci kanta A waje, Ina ga sauran ƴan uwanta Prisoners waɗanda tun da uwar su Ta haife su basu ta6a tozali da haske rana ba, Ɗaya bayan ɗaya Danish ya dinga janyo su kamar basu son fitowa, Kaf ɗin su Ya fiddo da su, kafin Ya maida ƙofar kogon tamkar ba'a ta6a ratsa cikinta ba.
Sai faman zazzare idanuwansu suke yi suna bin Dajin da kallo duhu Ya hana su ga komai da kyau, Tsananin tsoro ne ya kamasu, Ga wani irin bala'intaccen san yi kamar Jaura ta gifta, Haƙoran su sai kakarwa su ke yi, muryoyinsu Na rawa suka soma ambaton sunan Danish Suna faɗin sanyi su ke Ji.
Da sauri Ya buɗe akwatin kayan su dama shi ne ya ɗauko shi Tare da back pack ɗin Unaiza, Ya zaro masu bargunan su, A saman bayan su Ya lullu6a ma kowannansu bargo, Tunani ya shiga yi ya zaiyi dasu? Ga dukkan alamu sun gaji basu Iya motsawa gashi yana fargabar kada akawo masu hari yasan dole abiyo bayansu. Babu mai ƙoshin lafiya acikinsu kowa takan shi ya ke yi shiyasa ko farin cikin fitowar ba su yi ba duk da irin ɗaukin da suka dinga yi, su fa har yanzu basu yarda cewa sun fito daga kurkukun ƙaddara ba, gani su ke yi kamar har yanzu suna aciki, saboda duhun daya mamaye idanuwansu basu Iya gani dakyau hada ƙarin nauyin da idonsu yai masu sakamakon kukan da suka sha, wasu ma daga cikin su ciwon ido suke fama dashi, Danish ne kaɗai yake Iya ganin su da kyau.
Yanke shawarar ya yi da zuciyarshi nan take ya haifar masu da jin matsanancin bacci, Asaman dogayen ciyayin da ke shimfiɗe masu cukowa, Kowan nan su Ya kwanta hada masu goyan cikin su, Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa, Ya ɗauki bargo ɗaya daga Cikin wanda Ya lullu6a masu Kamar walƙiya ya 6ace Bai dura a ko'ina ba Sai acikin kogon dutse mai girman gaske, da sihirin shi ya kawar da duk wani abun cutarwa Ya gyara wurin tsaf babu ko ƙura balle aje ga batun halittun da ke rayuwa a cikinshi, Bayan ya tabbatar da babu abun cutarwa Ya shimfiɗa bargon dake a hannun shi, Kafin Ya juya tare da 6acewa ya dawo wurin da yabarsu kakkwance suna bacci, Cikin mintuna Biyar Yai aikin da acikin awa biyu mutun zai iya yin shi, Bai da banbanci da Jinni, kamar walƙiya ya dinga ɗaukarsu ɗaya bayan ɗaya yana kaisu saman shimfidar da yayi masu a cikin kogon dutse bai bar kowa ba, Bayan ya kammala kwashe su ya ɗauke masu akwatin kayansu da jakar ya shigo dasu Cikin kogon ya ajiye shi. Komawa yai cikin dajin Ya haɗo itace dayawa ya shiga dasu ruƙe a hannun shi Cikin kogon dutsen, Ya jera su a ƙasa nesa da inda su Angel su ke akwance, Ya tsinto duwatsu guda Biyu ya gurzasu jikin juna nan take wuta takama Ya cinna ta a jikin itace sosai Wutar ta ruru, a ƙalla ya sauke ajiyar zuciya yafi sau a ƙirga, ya hada uban gumi shi kaɗai, jiki bai saba da wahala ba, fuskarshi sai naso ta ke yi kamar an watsa mashi ruwa, Ya jima zuƙunne abakin wutar Yayin da idanuwanshi ke akan ƴan uwanshi dake lullu6e cikin bargo suna bacci, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi kamar an kora ruwan san yi, haƙika yayi danasanin duk wani abu da ya faru dasu, Ya ji ƙunci sosai A cikin ran shi, miƙewa ya yi a hankali ya ke tafiya yana tunkararsu a gaban shimfiɗar su Ya zuƙunna tare da miƙa yatsun hannayenshi Ya ruƙo bakin bargon dake lullu6e dasu Ya yaye shi, Hasken wutar da ke cini ne Ya haskaka mashi fuskokinsu, Idanuwanshi na akan Marasa ran cikin su, idan ka kalle su a yadda suke kwance baka ta6a cewa gawawwaki ne, Tuni idanuwanshi sun kaɗa jawur, Zuciyarshi ta ƙara karaya tsananin tausayin rayuwar ƴan uwanshi ne ya kama shi, Ya rasa ya akai duk waɗannan abubun su ka faru ba tare da sanin shi ba? Shin me ya faru da su bayan An ɗauke shi daga Cikin su? tambayoyi ya shiga jefa ma kanshi. Ataƙaice Daren Ranar Danish bai runtsa ba, Kwana yai a zaune yana gadin su.
*MIDDLE STEP THE PRISONERS BOOK TWO🔥💫*
*BIRNIN ABUJA🏙*
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E5🔥💫_
*Daga alƙalamin Hafsat Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._
*ANEELERH*
Kwance ta ke asaman katafaren gadon ta da ke acikin haɗaɗɗen bedroom ɗinta da ke a sabon gidan su na Abuja mallakin Uncle ɗan Iya ɗaya daga Cikin ƙannan Abie ɗinta mazaunin garin Abuja, Attajirin mai kuɗi ne mai yiwa ƴan siyasa hidima, Tun bayan da Abie ya samu ƙarin matsayi a wurin aikin shi aka yi mashi transfer zuwa ministry of finance da ke anan Abuja, a ƙalla yau watan su bakwai da barin jihar jos, ba ƙaramin canjin rayuwa su ka samu ba a gidan ɗan Iya, mutunne mai son jama'a ga iya mu'amala da kyautatawa mutane, kusan halin shi ɗaya da matar shi Aishatu wadda ake da Aunty Ummi.
"Aunty Aneelerh! Auntyna! Where are u? i'm back" can cikin bacci ta dinga jin ana ƙwala mata kira, Sautin muryar matashiyar budurwa.
Nauyin bacci ya hana ta buɗe idanuwanta sai ma ƙara ƙudundune kanta da ta ke yi acikin lallausar bargonta, faɗowa cikin ɗakin ta yi Tabarakallahu Zankaɗeɗiyar budurwa jawur da ita, Jikinta na sanye da egyptian gown launin shuɗi, Ta yi rolling veil akanta, Light make up ne akan fuskarta daga ganinta ba ƙaramar wayayyi bace a jin farko, Takalman ƙafarta high hills ne launi ɗaya da Mayafinta white colour, hannunta na dama na asanya da Tsadadden agogo silver colour. Ƙamshin turaren Jikin ta mai matuƙar sanyaya zuciya, wayar da ke a ruƙe a hannunta ƙirar i phone 15 pro ce.
Agogon bangon da ke a ɗakin ta kalla ƙarfe 9 Na safe, Da sauri ta wurga ƙwayar idanuwanta kan Aneelerh dake kwance saman gado, girgiza kai ta ɗanyi fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi tace"Auntyna kenan bakya gajiya da bacci, sam kin canza mini ba kamar yarda na sanki ba, Gaskiya zanyi magana da Daddy ya hanzarta sama maki aiki ki fara Ni bana son inga mutun yana zaman kashe buje" da zolaya ta yi maganar a yayin da take ƙarasa shigewa Cikin bedroom ɗin, Cikin sanɗa take tafiya tana tunkarar A.c remote da ke ajiye saman bedside drawer, ɗaukar shi ta yi saboda mugunta ta ƙure mata sanyin A.c, Jikin Aneelerh tuni ya fara kakarwa Sosai ta ke ƙara nannaɗe kanta Cikin bargo, Dariya sosai *FATIMA ZAHRA* ta sa ki a yayin da ta ke kallonta, Kasa jurewa Aneelerh saboda sanyin ya addabe ta, A gigice ta sanya hannu ta yaye bargon ta jefar dashi kafin ta yi yunƙurin buɗe ido da sauri Zahra ta rage sanyin a.c ta ajiye remove ɗin saman drawer, ta ruƙe qugu tana binta da kallo.
Sleeping dress ne a jikinta Riga da wando Milk colour, Gashin kanta a hargitse, Tunkan ta buɗe ido ta soma surfa masifa tana faɗin"junaid bana hana ka ƙara min sanyin a.c ba? Saboda ka raina min wayau ko?wlh idan ka bari na damƙi hannun ka sai ka gane ba ka da wayau, Sullu6iyo kawai......" Bata ƙarasa maganar ba ta soma Jin sautin dariyar Zahra, hakan yasa ta yi saurin ware idanuwanta tare da wurga su kan fuskarta.
Gwalo ta yi mata tare da ɗaga mata gira tace"Ba junaid bane yayar shi ce mai irin halin shi, " Harara Aneelerh ta shiga watsa mata kamar ƙwayar idon zata faɗo kasa.
Zahra tana dariya tace"Iya hararar ne kawai idan mutun ya isa ya sanya hannu ya dake ni, kai da ka zo baƙunta gidan mutane ka ishe su da baccin lalaci....." bata samu damar ƙarasa maganarta ba, Aneelerh ta rarumi pillow a zafafe da duro daga saman gadonta, zaro ido zahra ta yi kafin ta juya da gudu ta nufi ƙofa cikin rashin sa'a ƙafarta ta jirkice ta fasa ƙara zata kife ƙasa da sauri Aneelerh ta janyota zuwa jikinta, sosai ta ƙanƙameta sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi ta firgita sosai.
"Rasa kunya 6eran tanka, Yanzu ga ki a hannuna, mai ƙwatarki yau sai Allah" Kokoyi su ka soma Yi kamar ƙananun yara, Zahra sai ƙwalawa Umminta kira ta ke yi tana faɗin tazo ta cece ta daga hannun Aunty aneelerh zata kashe mata ƴarta, Aneeleh na dariya tace"Nima ai ina da uwar sai in kirata tazo taga idon mara kunya" ta ambaci hakan tare da ƙwalawa Maminta kira.
Sun shaƙe junansu sai nishi su ke yi gyalen Zahta tuni ya jima da zamewa saman tiles, gashin kanta baƙi wulik anyi mata kitson kalaba ya sauko har kafaɗarta.
"Aunty Aneelerh Am sorry wlh na miƙa wuya, zan maki biyayya na tufa bazan ƙara ba" Azabar zafin da taji ne yasa ta furta mata hakan donta ƙyale ta.
Sakinta Aneelerh ta yi don itama ta gaji da kokawar Sai haki ta ke yi, A nan ƙasa suka zauna saman floor suna kallon juna.
"Ɗauko mun ruwa mai sanyi in sha" harara zahra ta ɗan jefa mata"Baki da hannu ne"? Zaro ido Aneelerh ta yi tare da cewa"bugun da nayi maki bai ishe ki ba" Jin haka yasa zahra yin saurin miƙewa hannunta ɗaya dafe da qugunta, Binta da kallo Aneelerh tayi fuskarta ɗauke da murmushi fucewa tayi daga Cikin ɗakin, after some minutes ta dawo hannunta ɗauke da glass ɗin ruwa me sanyi, ta miƙa ma Aneelerh hannu tasa ta kar6a tare da kafa ruwan abakinta Kur6a uku tayi mashi ya ƙare, Janye shi tayi daga bakinta tadan kalli zahra da ke tsaye tana gatsina mata hanci.
"Ki gama yi mini rashin kunyar ina nan ina jiran ki, in dai ni ce za ki zo roƙona in faɗa maki ƙiyamil lailin da za ki yi don ki mallaki Zuciyar matashin saurayin nan da ki ka ƙwallafa rai akan shi, meye ma sunan shi? tai tambayar tana kallon Zahra, Dariya ta saki tare da kai hannu ta kar6i glass cup din hannun aneelerh, Cikin kwarkwasa ta Juya ta nufi ƙofar fita daga ɗakin tana faɗin"Heart beat of Obinna" Murmushi Aneelerh tasaki tare da cewa"Ehem shi nake nufi, zakiyi bayani ne" bayan fitar zahra miƙewa Aneelerh ta yi tare da juyawa har ta kusa shiga toilet Muryar zahra ta katse ta"Bafa tafiya nayi ba, taimakon nan dai da aka saba aunty Aneelerh, " Juyawa aneelerh ta yi tare da kallonta, Fuskarta ɗauke da murmushi.
Harara ta jefa mata"ƴar wahala wanka zan shiga idan na fito zamu tattauna" Zahra tace"idan ma shekara za ki yi zan zauna in jira ki" ta6e mata baki Aneelerh ta yi a yayin da ta ke shigewa cikin toilet taja ƙofa ta datse.
Daga gefen gadonta Zahra ta zauna tana jiran fitowarta, almost 15 mins Aneelerh ta buɗe ƙofar toilet ta fito jikinta sanye da rigar wanka fara ƙyal, ganin yadda zahra ta tsare ta da ido yasa ta murguɗa mata baki "Tubarkallah" Dariya Zahra ta sa ki kafin ta tsagaita da yin dariyar tace"Masha Allah Iyayen mu sun Iya haihuwa" girgiza kai Aneelerh ta ɗanyi"Allah ya shiryeki Zahra, Yanzu dai ta shi ki fuce zan sanya sutura, Ki jira Ni a palour " maƙe mata kafaɗa zarah tayi"Nifa ba ƙaramar yarinya bace da zaki kore ni, Menene aciki don kin sanya kaya agabana, sai kace wani gardin ƙato Nima fa macace kamar ke komai ki ke dashi ina da....." Kafin ta ƙarasa maganar Aneelerh ta nufeta da gudu Zarah ta bar Cikin ɗakin tana dariya.
Kaitsaye ta nufi Cikin Hadadden palourn gidan mai girman gaske. Tun kan ta ƙarasa ta hango mami da ummi zaune saman sofa suna fira, kowaccen su na sanye da atampha riga da zane ba ƙaramin kyau su ka yi ba.
"Gani nan tafe" kamar daga sama suka ji miryarta.
Atare suka ɗago suna kallonta, mami tace"yaushe kika dawo gidan"?
"Ban jima da shigowa ba, Na shiga ɗakin Aunty Aneelerh ne, Na same ta kwance Tana bacci," Tai maganar a yayin da ta ke zama saman sofa mai mazaunin mutun ɗaya.
"Nasan kin kwaso gajiya, Tun asuba sai yanzu aka kammala aikin decoration ɗin, Kin ci abinci kuwa"? cikin Kulawa mami ta yi mata maganar, Fuskarta ɗauke da murmushi tace"mun aikatu Mami, Uban aiki kamar zamu shekara muna Yi, kinsan hidima idan akace maki ta Hamshaƙan attajiran masu kuɗine komai dagaske ake yin shi basu ƙaramar harka, Mami zanso Kije Gidan nan zaki sha mamaki wlh, Haɗaɗɗiyar Daular arziƙi ce...." tun kan Zahra ta rufe baki Ummi tace"Ae Obie estate Aljannar Duniya ce Mai zaman kanta, Idan fa ki ka shiga gidan Sai ki rasa gane Awace ƙasa kike, tsabar kayan alatun da ke a cikinsa, Yasin in mutun mai ƙaramin Imani na rayuwa acikin tuni zai daina Sallah....." Dariya mami ta saki Yayin da take sauraron su, daga uwar har ɗiyar gwanaye ne wurin Iya bada Labari.
"Aunty duk yadda zan kwatanta maki Haɗuwar Kayan alatun dake acikin Estate ɗinsu Ba zaki Fahimta ba, Gani da ido yafi abaka Labari, Obinna family duniyace mai zaman Kanta, Ranar dana ta6a zura ƙafa ta cikin gidan wlh Sai da gabana ya faɗi, nace Anya ko Mutane suna tunanin duniya? Yo abu kamar baza a mutu ba, wannan ae sai mutun ya manta cewa da tur6aya aka halicce shi" Dariya sosai Mami ta ke yi tana kallon Aunty Ummi da ke kora mata jawabi, Zahra ta ɗaura da cewa"Ni wlh Naso Daddy ya sama mun Ko aikatau ne agidan su, tun ranar da naji Salary din masu aikin gidan da dollar ake biyan su, Ci da sha da suturarsu duka A kyauta ake yi masu, ai duk wanda Ya haɗa alaƙa Da ɗan familyn Obinna kakar shi ta yanke saƙa, Shi da talauci sun raba Jaha...." in serious matter za'a ta ke magana, Ummi taci gaba da cewa"Shiyasa naso mahaifin ki ya kutsa ki cikin danginsu tun da dama ɗan bangar siyasa ne, Ni ko wannan Yaron ne *DR JAZZ* kisamu ki aure shi, ko mun samu muma mu dangawali arziƙi" ta ƙarasa maganar tana dariya, tur6une fuska zahra tayi Jin abunda Ummi tace"haba ummi, dr Jazz fa meye haka, Ni da na ke harin bugun zuciyar Family ɗin gaba ɗaya, Taya zaki haɗa ni da yaron da har yau ba'asan waye ubanshi ba acikin family ɗin" da mamaki akan fuskar Mami tace"kamar ya ba'asan Ubanshi ba"? Zahra tace"ɗaya daga Cikin ma'aikatan gidan su ce tazo dashi aikatau, Matar ma farar fata ce, ba ki ga yaron ba kyakkyawa ga son mutane, ni bazan Iya auran mara asali ba, Ta ya Ummi zatai min fatan auranshi? Ga gwarazan samari a family din kyawawan gaske masu kama da kakansu Obinna...." tana magana tana turo baki.
Ummi tace"Saboda nasan baza ki Iya samun wanda kike so ba, Haukan banza ki ke yi a kan shi, ke kin sani Ruwa ba sa'an kwando bane, Babban Goro sai magogin ƙarfe, Wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa, In banda haɗama irin ta zahra taya zaki nace wa mutumin da yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba? Shiyasa nace ƙwara Dr Jazz ɗin shine dai dai da ke," ɗaure fuska Zahra tayi jin abunda Umminta take faɗi, ta haɗe rai sosai, Muryarta a ƙule tace"Mami kinga ni ko? Ita fa mahaifiyata ce amma bata min fatan naci ka burina, Kullum sai dai tayi discouraging ɗina, meyasa ta ke yi min haka ne"? a bun ka ga me saurin kuka tuni idonta sun ciko tab da ƙwalla.
Fuskar mami ɗauke da matashin murmushi ta soma magana a tsanake"kwantar da hankalin ki zahra, Ai duk kyan takalmi ƙafa ce ke taka shi, kuma idan Allah ya ƙaddara cewa shi Yaron wanda kikeso Mijin ki ne duk min muƙamin shi duk mun izzar shi da kyanshi wlh da kanshi zai nemo ki a duk inda ki ke, Ai shi so bashi a matsayin mutun, mai kuɗi ko talaka Zahra kuma ta haɗa komai da duk wani ɗa namiji zaiso zama da ita a matsayin matarshi,..." Tunda mamin Aneelerh ta soma magana zahra ta washe baki tana zabga uban murmushi kamar wadda akayiwa albishir da gidan Aljanna, Tsabar murna batasan sa'adda ta sauko daga saman sofa ɗin da ta ke zaune ba, ta dawo ƙasa saman carpet, Ta kafe mami ido tana kallonta kamar wadda ta samu Tashar Bolly wood, Hakan ba ƙaramin dariya yaso ba Ummi ba, Ganin yadda zarah ta ke sakin murmushi jin ana yabanta.
"Mami ni ba ina kushe Zahra bane, Just bana so ta ƙwallafa rai akan abunda ita kanta tasan bazata ta6a mallakarshi ba, Yakamata ta runƙa tuna matsayinta, Mahaifinta fa ɗan bangar siyasa ne ba wani shege ba, Ta ya ya ta ke tunanin zata Mallakin Hamshaƙin mutun kamar *OWAIS SHARAFUDEEN OBINNA*!? Bazan iya lissafi ma matan da su ka yi hauka akanshi ba, Daga cikin hada Ɗiyar Chancellor na ƙasar Germany bayan ita akwai Ƴar sarkin saudi arab, Ga ɗiyar shugaban ƙasar America....." Lamarin ya ɗaure wa mami kai, Baki asake ta ke kallon Ummi sai da ta kai ƙarshen maganar tukunna tace"Ni ko zanso In ga wanene wannan Namijin hurul ainin, Farin Jini sai kace ɗan gwal yo wannan koda lu'u lu'u aka ƙera fatar Jikin shi sai haka," Dariya su ka saki gaba ɗayan su.
"Saboda Farin Jinin da Allah ya yi mashi kakan shi Ya toshe duk wata ƙofa da za'a Iya ganin shi, Zaiyi wuya ki samu hoton shi a social media, shahararre ne sosai babu inda ba asan shi ba, Da zarar kin ambaci sunan shi awuri sai an girgiza" Ummi ce ta kora mata jawabi, Al'ajabi Ya kama Mami"Na ƙosa Inji tarihin Family ɗinsu, Najima Ina jin zancensu abakin mutune da kuma labaransu a gidan radio, Nasan fuskokin Ya'yanshi a tv sai dai bansan Komai dangane da su ba"
Gyara zama Ummi ta yi"Jinin Nasara shi ne sunan da akeyiwa family ɗinsu laƙabi da shi saboda wadatar Arziƙin da Allah yayi masu, Suna ɗaya daga cikin Most richest family in the world, shahararru ne na bugawa A jarida, shi Obinna da ki ka ji ana faɗi Kakan su ne tsohon ɗan siyasa ne wanda yai gwagwarmaya ya ruƙe muƙamai da dama tun daga ƙasa Nigeria har zuwa ƙasashen waje, Allah ya yi su da farin Jini, matan shi biyu a yadda naji labari, amma dukansu basa araye yanzu, shi kaɗai ne ya rage, ƴa'ƴan shi bakwai kaf ɗinsu suna ruƙe da manyan muƙamai, su ke ruƙe da ƙasar nan, Manyan ƴa'ƴan shi ƴan Uku ne sune first born ɗin shi" numsafawa Ummi tayi kafin ta soma zayyana mata sunayen su kamar haka.
"SENATE PRESIDENT LATEEF OBINNA, bayan shi akwai CHIEF OF ARMY STAFF SIR MUBARAK OBINNA, cikon Na ukun su shine HIS EXCELLENCY ABDUL RAZAK Obinna Gomnan Jihar Lagos, waɗannan sune yan ukun shi, bayan su akwai ƙannan su maza HIS EXCELLENCY DEEN OBINNA Gomnan Jihar kaduna state, mai bi mashi PRIME MINISTER HATEEM OBINNA Shugaban ƙasar Canada Shi ne ya ke auran Gimbiya mujeedat ƴar Sarkin Dubai....." Tun da Ummi ta soma bata labarin Mami ta baza kunne tana sauraronta, ga dukkan alamu al'ajabi ya kamata duba da yadda ta saki baki tana kallonta