Kwai cikin kaya book 2 complete - Chapter 20
Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 20: Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 20. ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻by BilynAbdull Page 26 BARKA DA…
4,081 words
.................Daga can akace “goro yaron alkairi”. Ya cigaba da faɗin, “Da alamafa damunar bana zatai ɓarna, dan na hangi ɗakunan mutane da yawa sun buɗe ta sama batare da sun fargaba, kuma lallai bular zata zubda yoyon ruwan da zai iya haifar da ambaliya”. dariya ta tuntsure dashi daga can, tace, “Ɗan alkairi kana nufin dai dara zataci gida kenan, ɗan zaki yafara buɗe idanunsa ga rundunar kuraye masu gudun tseren neman abinci koda bai kasance halalinsu ba?”. “Ƙwaraima kuwa mamana, bana sanar miki wani ƙwai dake cikin ƙaya ya bayyana ba kwanakin baya, kuma duk haɗarin maciji ya gama shawaginsa ya barsa dan ya gagara haɗiya”. “ƙwaraima kuwa ka sanar min da wannan, a farautar zaki yaci karo dashi kenan matsayin abinci?”. “Hhhhh mamana kina birgeni da saurin ramfo zance, to wlhy ina mai tabbatar miki da hakaɗinne ta kasance, tsagerun dawa na tunanin Zaki yafi ƙarfin ruwan ƙwai sai gashi harma yana ƙoƙarin damƙosa cikin ƙayoyi”. “Kai ɗan alheri karka sa farin ciki ya karni yau ɗinan ban kalmashe bakin buhun dana farama ɗureba, yanzu dai ina fatan kana hanyar gidane?”. “Hasashenki baya zama kuskure mamana, mu haɗu acan na baki sauran bayani, dan kuwa garin bita da ƙullin ƴaƴan kura sun rufta damisa da ƴaƴan fadarta a ramin ɗan zaki, shiko ya afka musu ƙasa yasa ƙafa yatake harma da share wajen kwanciya domin buƙatar hutu”. Wata irin dariya ta shigayi mai cike da nuna tsantsar farincikinta data daɗe da mantawa da samunsa, yau ɗan nata ya biyata da daddaɗan labari. tace, “Ɗan albarka wannan zinaran kalamai naka sunfi ƙarfin saurare a salula, garzaya gida nima ina gab da iskoka, dan tun safe na nema alfarma ga Uwargida sarautar mata akan zuwa na duba mai babban suna”. “Babu damuwa mamana ina tsumayenki acan, alkairin ALLAH ya cigaba da baibayeki tare da nasarar cigaba dayin haƙo a ramin azzalumai batare dasun fargaba har sai kinkai musu wuya lokacin sungama shiga tarko”. Murmushi tayi daga can tana faɗin “Amin ɗan albarka” kafin ta yanke wayar, shima ya tura tasa a aljihun yana murmushi. Cigaba yay da tafiya harya fito titi, napep ya tara takaisa inda motocin ƙauyensu ke tsayawa, duk da garinsu ba ƙauye bane sosai dole muce dashi ƙauye, dan kuwa a ƙarƙashin wata ƙaramar hukuma yake, saidai yamafi l.g ɗin dukkan abubuwan cigaba, gashi a bakin titi kuma babu nisa da babban birin jiharsu. A mamakinsa ana saukesa falletsetsiyar mota na cin birki a gabansa, baiyi mamakin hakanba, dan kasancewarsa drivern boss yanada alaƙa da sanin mutane manya sosai ta fannoni da dama, lokaci-lokaci kuma yakanci karo da wasunsu koda ace shi ya mantasu dan dama dalilin shige da ficin boss na aiki yake sanin nasu. Wanda ke ciki ya sauke gilashi yana murmushi, sosai gimba ya zaro ido irin na bazatar ganin wanda bai zatoba, “Lah Ɓaleru! Dama rai kanga rai? wane mai gangancine yay kasadar baka idanunsa kaketa haska hanya dasu cike da ɗaukar faɗi?”. Dariya na cikin motar yay har yana bugun sitiyari, yace, “Gimba kaidai baka rabo da shaƙiyanci, kasan ɓalerun naka da shige-shige, ko iska ta shafamin lafiya. Daga ina haka zuwa ina?”. Gimba yace, “Wlhy gida nai, zamuje hutun ƙarshen mako domin ganawa da iyali”. Ɓaleru yay ƴar dariya da faɗin, “Mutumina baka wasa da gona, shiyyasa kullum gatanan cikin yabanya take, banga laifinkaba, yi birgimarka ka more mata sune jin daɗin duniyar ai dama. Shigo mu haura dan nima dai can na nufa ɗin”. Babu musu Gimba ya shiga yana maida masa murtanin shaƙiyancinsa, saida suka ɗauki hanya ɓaleru yace, “Nifa mamaki oganka ke bani, gashi jinin manya, ɗan tsohon shugaban ƙasa mai tarin dukiya, shi kansa ƙwaron kansane dan ya tara bayan wanda aka tara masa, amma abin mamaki kamar shima baya mora balleku ƴan muna jira ALLAH ya baka mu samu”. Murmushi gimba yayi, cikin son kare boss ɗinsa yace, “Ai abin nagartace, sai dai irinku ƴan ƙwanta ka mutu mu haye basa ganewa, komai boss yake da tsari a cikinsa, shi bai ɗauki wannan dukiyar da ta tsolema kowa idanu wata tsiyaba, marasa nasaba da itama amfanuwa suke da tagomashinta amma ta ƙyaƙyƙyawar hanya, bai yarda da almubazzaranci ba, amma shi kogine maiba na kus
Chapter notes and social links
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻by BilynAbdull Page 26 BARKA DA JUMA'A ..............Jawaad da yay ɗan jim fuskarsa ɗauke da murmushi yana juya maganar gimbiya ta ƙarshe a ransa, koba komai ya sakejin kimarta, domin ta nuna tanada ƙyaƙyƙyawan tsari da tausayi akan talakawa. yace, “Shikenan ranki ya daɗe, ke uwace, kinada damar yanke duk hukunci daya dace a kanmu koda babu saninmu, sai dai ina neman alfarmar zuwa na sanarma kakana da kuma ƙannen mahaifiyata, zuwa gobe insha ALLAH zan dawo na sanar miki yanda mukayi”. “Wannan tunanin naka shine ƙyaƙyƙyawan tunani da yakamata ya fito daga bakin jajirtaccen ɗa mai riƙo da tarbiyyar magabatansa, kaje ka sanar musu ɗin babu damuwa, sai dai zan baka shawarar koda likita yace zai sallami bilkisu kace ya jinkirta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, dan nafison da an sallameta kawai nan za'a wuto da ita”. Kansa ya jinjina mata. Ta ɗauki ɗaya daga cikin wayoyinta masu azabar ƙyau ta miƙa masa, “Kasaka Number ka anan, saika ɗauki tawa yanda idan sun amince ɗin zakai kirana ka sanarmin basai kayi wahalar zuwa ka koma kawomin bilkisu ba kuma”. Tasowa jay yay ya amshi wayar, Number sa ta musamman da wanda ya yarda kawai kuma yakeda kusanci dashi matuƙa kawaine ke da ita ya saka mata, sanan yay kira yaga tata, saving yay mata da Jawaad A yusif ya maida mata yana godiya. ___________________________________ Tare Jawaad suka dawo da dattijon nan dan zai juya dasu Amaturrahman masarauta. Shi kaɗai ya shigo ɗakin da sallama ciki-ciki kamar yanda ɗabi'arsa take ta rashin son hayaniya, babu kowa a ɗakin, Safah kaɗaice kwance tana barci a gadon da Bilkisu ke jiyya, mamaki ya kamashi da tunanin ina suke har ita Bilyn?. kafin yay yunƙurin yin wani abu aka buɗe ƙofar toilet, Bilkisu ce ta fito ɗaure da zani, ta yafa ƙaramin towel a kafaɗarta da alama wanka tayo saboda yanda ruwa ke jiƙe da fuskarta, duk tsefaffen gashinta ya kwanto goshinta da gefen kumatu. Wani faɗuwa gabana yayi dan banyi tunanin iske kowaba tunda su Nabeelah sunce zasuje sallah, Mama kuma tunda ta gasamin jiki ta fita akan zata ɗauraye kwankikan da akaci abinci, bawani ƙwarin jikin nakejiba dama, dan dukan da sukaimin yasa jikina yin tsami ko ina ciwo yakemin, wai danma Doctor ya bani maganin ciwon jiki nasha. Nakasa koda ɗaga ƙafata da sunan juyawa baya, sai kawai na duƙe a wajen inaji tamkar ƙasa ta tsage na shiga ciki dan matsananciyar kunyar data riskeni, nice yau tsaye gaban boss babu riga? Dagani sai zani da ƙaramin towel ɗin dana yafo a kafaɗa, kaina sanye da hular wanka, dukda nasan fuskata kawai zai iya gani da hannayena zuwa gwiwa, sai ƙafafuna suma iya rabin ƙwairi dan zanin ya sauka min ƙasa sosai duk da ɗaurin ƙirji nai dashi, hakan ba ƙaramin abun kunya bane a gareni. Ɗauke kai Jawaad yay daga kallon daya kafeta dashi yana mai lumshe idanu a hankali da furzar da sassanyar iska daga bakinsa, baice da ita komaiba ya juya ya fita zuciyarsa na gudu da sauri-sauri. Hawaye nake kashirɓan da bansan dalilinsuba sam, dukda naji ƙarar buɗe ƙofa da rufewa alamar ya fita na kasa miƙewa tsaye bare na tashi. “Bilkisu lafiya kuwa? Ko jiri kike ganine?”. Muryar mama ta dawo dani hankalina. Saurin ɗago kaina nai ina share hawayen da suka jiƙen fuska, ganin dagani sai ita a ɗakin yasani sauke numfashi ina mai ɗaga mata kai alamar juwarce. Kwanikan hannunta ta ajiye tazo ta taimakamin na tashi tsaye, da taimakonta muka ƙarisa bakin hadon dan a gaske yanzun saima nakejin tamkar juwarce tazomin, ita ta taimakamin na shirya, ina kammala shiryawa su Nabeelah da Amaturrahman da Marwah na shigowa. Sannu suka yimin kafin Amaturrahman ta shiga tada Safah tana faɗin Su zasu wuce gida, jinai kamar nace su zauna, amma banda wannan ikon, ga Safah ta sanya kukan shagwaɓa akan itafa anan zata zauna tare dani. Ina mamakin wannan irin ƙauna da Safah ke nunamin. Kafin kowa yace wani Abu boss ya shigo ɗakin da sallama. Nidai ƙasa nai da kaina ban yarda nako saci kallonsaba, tambayar da yakema Safah akan mitakema kuka kawai naji, Nabeelah ce ta bashi amsa da cewar tace bazata tafiba anan zata zauna wajena. Banji ya bata amsaba, sai saukar hannunsa naji akan nawa dake riƙe dana Safah, a take tsigar jikina ta tashi, gashi har yanzu akwai damshin ruwa jikina dama, ya cire hannunta batare da yace uffan ba, binsu da kallo nai ta ƙasan ido har sukaje gab da ƙofa. Ranƙwafawa yay yaymata maganar da duk bamujiba a cikin kunne, ta ƙyalƙyale da dariya tana tsalle, shima wani shegen murmushi ya saki maiban mamaki, Safah tace, “Amma Yayanmu (Yanda taji Nabeelah na faɗa) kafin goben zaka rama mata dukanta ko? Inba hakaba saina saka Abbu ya turo sarkin tsabga na masarauta ya musu dukan mutuwa da dorinarsa”. Janyeta yay daga jikinsa da take neman shigewa yana lumshe idanu, a hankali yace, “Karki damu zan rama mata da kaina”. Sosai ta shiga daka tsallen murna Nabeelah da Mama na dariya harma da Amaturrahman, Marwah ce dai tai murmushi kawai tana rakuɓewa a jikina, juyowa yay muka haɗa ido nai saurin janye nawa, da hannu ya yafito Marwah alamar taje itama. Da sauri kam ta nufesa cike da ɗoki harda murmushin daya bama kowa mamaki, dan tunda tazo taƙi sakin jiki da kowa. Hannunsu ya kam suka fita, Amaturrahman taimin sallama tabi bayansu tare da Nabeelah da zatai musu rakkiya, mama kuma ta bisu da kalaman godiya dana addu'a. Nima haka godiyar nake musu har suka fice.Bayan wucewar su Amaturrahman Jawaad bai koma cikiba, mota ya shiga yabar asibitin. Kai tsaye gidan Alhaji baba ya nufa, harya zauna kusa da Alhaji baba baisan ya shigoba, saida Jawaad ya kwanta tare da ɗora kansa a cinyar kakan nasa sannan ya kawo numfashi. Cike da mamaki jay yace, “Tunanin mikake haka da zurfi sofo?.” Shafa kan Jawaad yay cikin ƙoƙarin danne damuwarsa yace, “Kaima zaka tsufan wataran ai, ango mai rinton mata, yaya kukayi dasu a masarautan?”. Dariya Jay ya ƙyalƙyale da ita yana faɗin, “Ashe dai ni jarumine tunda gashi na ƙwace kuma dole a barmin. Ka fara gayamin damuwarka Baba sai na faɗa maka nima”. Jay yay maganar cike da kulawa ga kakan nasa abin ƙaunarsa. Sosai Alhaji babba ya sake danne halin da yake ciki ya nunama Jawaad bashi da wata damuwa, badan Jawaad ya aminceba ya haƙura, sannan ya zayyane masa duk yanda sukai da gimbiya Munaya. Alhaji babba yace, “Banƙi ta tataba, sai dai kuma kai kana ganin babu damuwa?”. Zaune Jawaad ya tashi sosai, yace, “Amincewarka ni itace kawai tawa baba, dan kaine zaka hangomin abinda ya dace da wanda yake kuskure saboda kana gaba dani, dalilan data kawo na komawarta gidan Dad abin dubawane, nikuma gashima ban shiryama maganar tarewar tataba saboda akwai ayyukan da gidan da zan ajiyeta yake buƙata, tunanin da nake dai bai wuce dama ta koma gidan Ummah babba ba, dan dama ni ban tsara zata koma can gidanba saboda haɗarin dake tattare da hakan koda Qaseem da Hudah da Momynsu. Alhaji baba yace, “Lallai kayi tunani mai ƙyau, yanzu dai ka bata dama, dan kowa yanama Uwargidan sarki ƙyaƙyƙyawan sheda akan adalci da shiga matsalar talakawa da ƙarfinta da dukiyarta, to akanku wannan ba sabon abu bane, bakuma yauta faraba, shiyyasa banajin wani ɗar balle tunanin akwai wani manufa a lamarinata” Jawaad yace, “Shikenan Alhajin ALLAH zanyi yanda kace”. Daga haka hira sukaɗan taɓa zuwa sallar la'asar, daga nan Jawaad yay masa sallama ya wuce gida, dan a matuƙar gajiye yake, rabonsa daya huta tun daren alhamis ranar laraba kenan, gabaɗaya bai hutaba, a hankali ya furta, ‘Dukta cinyemin lokaci ta gajiyar dani’ ya ƙare maganar daɗan lumshe idanu ya buɗe akan titi. iske gidan nasu yay kaca-kaca anata hayaniya, dai-dai sashensa yay fakin inda ya saba, ya fito fuska ɗaure batare da ya kalli kowaba a cikinsu ya shige abinsa, dan ya fahimci cecekucen maganar aurence suke har yanzu, shikam a tsarinsa duk abinda ya gama da matsalarsa to yagama kenan baya sake waiwayensa sai dai kuma sabo idan ya taso. Yanda suka ganshi a tsume yasa aka rasa mai tunkararsa da magana dukda kuwa shigowar tasa suke jira dama, Hatta da Momy da Shahudah duk suna gidan sunzo saboda mama Atika data buƙaci ganin Momy, ga kukan da Shahudah keta dirja tunda Jawaad ya baro gidan. (Kaike musu yanda kaso ace ɓarnar motace, inba kaiba saiwa ɗan Abdul'aziz😂, kaikeyi kayi kuma kamar bakaiba dole a ganka a ƙyale🤣🤣). Yana shiga falonsa ya dannama ƙofar key yana jan wani wawan tsaki, a kwanakinnan ko shara sashen baya samu saboda yaraba hankalinsa biyu, ga matsalar aiki ga matsalar cikin gida, duk ƙura ta kwanta bisa kayayyakin falon, haka ya tsallake yanzunma ya haye sama, canɗinma dai yay ƙurar sosai, bai kulaba ya ƙarasa bedroom, shi daɗan sauƙi saboda ana zama, gadonma a gyare yake, ga mayen ƙamshinsa daya kama ɗakin na nan, kayan jikinsa kawai ya rage, dagashi sai boxer ya haye gadonsa yana lullumshe idanu. Cikin ƙanƙanin lokaci barci mai nauyi yay awon gaba dashi (Barcin bayan la'asar baida ƙyau Jay🤦🏻). A hankali numfashin Jawaad ya ƙara nauyi alamar barcinsa yayi nisa, mafarki mai sarƙaƙiya, wanda a cikinsa aka sake maimaita masa kalmar “(Ƙaddarar haɗuwar Jini a cikin jini da zai zama jini a yanzu ta zama tabbatacciyar alaƙa da zata zama sanadin buɗe ma'anar jini a cikin jini, takuma warware sirrin ɓoye, Kuzama masu addu'a, dan lokacin da ƙullalliyar sarƙaƙiya mai cike dacin amana zai bayyana yayi, dolene maciya amana, amana tacisu suma, dolene waɗanda sukai shuka su girbe abarsu dai-dai da abinda suka shukaɗin tun a duniya kafin aje babbar kotu kowa ya amshi sakamakonsa, dolene gorar da azzalumai suka fafe dan tafiya ta buɗe a yanzun da suke gab da kaiwa ƙarshen tafiyar tasu, ɗan zaki ya girma, kaine jagoran fidda ƘWAI CIKIN ƘAYA, karkuyi wasa da addu'a!! dan itace babban takobinku na yaƙar wata riundina ta azzalumai masu son zuciya, gaggawarku zaizama sanadin tonuwar wasu jinane da aka kwarayar. wannan itace ƙaddararku, ƙaddara mai sarƙaƙiyar data saƙa jini a cikin jini, karku manta! Addu'a!! Karku manta!! Karku manta!!)”. Cike da firgici Jawaad ya farka, ya jiƙe sharkaf da gumi dukda kasancewar yammace mai cike da ni'ima canjawar iskar farkon damuna, ɗan zafi-zafin dake garin bashida gallazawar da zatakai mutum da irin wannan zufar da yakeyi, gaba ɗaya jiyay ɗakin na juya masa tamkar hajijiya, ya dafe kansa da hannu yana karanto addu'oin da duk sukazo masa kan harshe. Ya ɗauki tsahon mintuna zaune kafin yaji ɗakin ya tsaya dai-dai, ya sauke hannunsa yana furzar da iska zazzafa, idanunsa sunyi wani irin kaɗawa sunyi jazur, wannan wane irin mafarkine haka? miyasa yaketa maimaita kansa garesa? Akan wa ake masa wannan nunin?; ‘Ya ALLAH ka warwaremin abinda banida ilimin saninsa, ka haskamin abinda ya kasance duhu a gareni, ka jagoranci tunanina akan abinda kakemin ishara dashi acikin barcina’. Idanunsa ya sauke akan wayarsa dake haske, kamar zai share sai kuma dai ya ɗauka, ashe yayi barci mai tsaho, ga magrib harta gabatoma, saƙon da'aka turo masa ya buɗe, sanin muhimmancin wanda ya turo masa saƙonne yasashi nutsuwa ya karanta abida ya rubuto. “Oga na shirya faɗa maka komai a yanda yake, ina kuma buƙatar a bani matata itama, amma akan farashin kuɗaɗe, kabani address ɗin inda zamu haɗu, sannan kazo da naira miliyan hamsin, nikuma zan baka labari mai matuƙar tsada akan kai kanka bayan nata itama”. Naka ɗan fir'auna. Ƙaramin tsaki Jawaad yaja yana mai dafe goshinsa da hannun damarsa tare da murzashi da ƙarfi, da ace ya iya kuka akan komai da a yau zama zai kawai yayta kuka har sai ya ƙoshi dan kansa yay shiru, to amma a tsarin wannan harƙallar kuka a garesa kasawace. Miyasa ɗan fir'auna yace yanada labari a kansa? Kenan shima su.... Ya haɗiye abunda ke neman toshe masa numfashi da sauri yana girgiza kai da faɗim, ‘No...’ bazai kasance hakaba. Komawa yay baya ya sake zubewa a gadon, ƴar ƙarar da agogon ɗakin yayce ta sakashi miƙewa kuma zumbur. Toilet ya nufa, ya sakarma kansa ruwa na tsahon lokaci kafin yay wanka ya fito ɗaure da alwala yay gaggawar shiryawa ya fita.Ganin mutane sun sassauta zuwa dagani sai Mama a ɗakin da Ummie yasa nai dauriyar tattaro dukkan abinda ke raina ina mai kallonsu, “Mama!”. “Na'am Bilkisu ya akai?”. Tafaɗa tana ɗago kanta ta kalleni, Ummie ma daina latsa wayar tai ta maido hankali kanmu. Cikin bama kaina ƙwarin gwiwa nace, “Mama dan ALLAH mi yake faruwa? Gaba ɗaya tunanina ya kulle bana fahimtar komai daga kalaman mutane wanzu daga safiyar yau har kawo yanzun?”. Murmushi maman Amina tayi, sai kuma ta taso zuwa inda nake ta zauna a bakin gadon, hannunta ta saka ta kamo nawa, har yanzu fuskarta da murmushi, “Bilkisu ya kamata dama kisan miya farun kodan kiyaye girman nauyin dake kanki a halin yanzun, danke ɗin matar aurece da haƙƙinta ya koma kan wani”. Banji komai dangane da kalamantaba face wani mummunan faɗuwar gaba da harbawar zuciya, ta cigaba da faɗin................... Wani irin mazarin rawa jikina ya shigayi hawaye na rige-rigen sakkowa akan kumatuna, cikin matuƙar rawar leɓe dana harshe nace, “Mama! Ki..k...kina nu..fin ni aka ɗaurama aure da BOSSS!!!?”. Mama tace, “Bafa bos nace mikiba, Jawaad! Nace”. “Innalillahi....” Na shiga ambata, yayinda Ummie ke ma mama ƙarin bayanin cewar Boss ɗin ai Jawaad nake nufi nima, haka muke cemasa a wajen aiki. Mama tace, “Ayyo, aiban fahimta bane ƴannan”. Komai nama daina fahimta, wani irin zazzafan zazzaɓi nakeji yana saukarmin, cikin lokaci ƙanƙani nafara rawar sanyi, tunani kalma ɗaya acikin abinda mama taimin bayani na kasa nutsuwar yi, ni Bilkisu Adam makaho ce aka ɗaurama aure da Boss ɗinmu, JAWAAD ABDUL-AZIZ YUSIF!!? dama na jima zuciyata na kokwanto akan rashin damuwar da bangani a tattare da Momy ba akan aurena da Yah Qaseem, miyasa Momy ta zaɓi rabani da masoyina wanda na ɗauka dukkan yardata na bashi? Bazan ɓoyeba ina ƙaunar Yah Qaseem sosai, sannan ban tsani Boss ba dan yanada nagartar da dukkan macen ƙwarai zataso mallakarsa matsayin mijin aurenta, to amma yaya zanyi da aunty Shahudah da dukkanma ahalina? Wannan kuwa bai zama cin amanaba ga Dad da halaccinsa a gareni?. ‘To ai bake kika ce a ɗaura miki aure da boss ɗinba ko’ wata zuciya ta ayyana min daga can gefe kuma wata tace, ‘Bakuma kowa zai fahimci bakida hannu a cikiba kamar yanda mama ta faɗa miki dangin Momy na ambata hatta da Yah Qaseem dayasha gargaɗinki akan mu'amularki da Boss ɗin’. Sharr na matso wasu hawaye masu zafi da suka cikan ido. A fili na furta, ‘Innata miyasa rayuwa takemin hakane? Miyasa duk yanda naso ƙoƙarin raɓar duniya saita goce mani? Tunda na rasaki keda Abba ban sake hawa dokin da yay daidai da cikar dukkan burukanaba, dana hau matakin nasara sai ƙaddara ta sake zuwa ta datse zaren da nake tafiya da ƙwarin gwiwata a kansa, kune kuka sanarmin duniya ba komai bace face wani filin gwagwarmaya na ƙwanji da zuciya, kune kuka tabbatarmin jajircewa na iya zama babban ƙawance da duniya koda duniyar bata buƙatar hakan, miyasa ni tawa jajircwwar a kullum nisantani take da tawa duniyar, shin gaggawa nake a cikin al'amarina shiyyasa nake durƙushewa kafin nakai kokuwa tawa ƙaddarar kenan kullum a curkuɗe?....” “Wannan ai itace tabbatarciyar nasara kuwa Bilkisu, duk ɗan adam ɗin dakeji a zuciyarsa shine kaɗai wane, shine kaɗai za'aita kira wane daga farkon ƙarni har ƙarshensa to ya tabbata akwai ganganci da tarin wauta a al'amuransa, nasarar mai nasara itace ƙalubale, kadingaji kamar baka kaiba, baka cancanci kaiwaba, bazaka ka kaiba, sai kaga watarana ka kai harma ka wuce, lokacin da wani yake ganin ya rigaka ɗauka baka da damar ƙwata babu zato saiya suɓuce masa wajen hura hanci da gadara kai ka tsinta a ƙasa amatsayin shara kaci kai nagartar da har abadan bashi da damar hangokama, wannan rubutacciyar ƙaddarace ga mafi yawan mutane marasa gata, duk wanda ake ganin bai kaiba ko bazai kaiba shike wucewa wataran bilkisu, Jawaad shine mijin da yafi cancanta da nasararki, UBANGIJI kuma yafiki sanin miyasa ya zaɓa miki shiɗin, karki damu da adawa ko tunin kinci amana, a sannu duhun da kike ganin yana binki zai yaye yazama haske, a sannu waɗanda suke ganin keɗin baki cancantaba zaki zame musu hasken da zai mamaye rayukansu, ba'a cika baki da nasara, ba'a cika baki da farawa, ba'a cika baki da iyawa, ba'a cika baki da cancanta, ba'a gadara da abinda baka da ikon dawwamar dashi a hanunka tunda kaima a wajen wani aka amsa aka baka, dagaske duniya rigar aro ce bilkisu, duk taƙamarka da ita da alfahari wataran saika tuɓeta da mutunci koda ƙasƙanci, duk abinda kaga kayi a duniya koka tsinci kanka kafin kai anyi dubunka masu ninkin banikin ɗinsa, bayanka kuma wasune zasu amsa su dama ko kaƙi ko kaso. Dan haka ki godema ALLAH da ni'imar da yay miki na mallakar miji mutumin kirki da bai ɗau duniya komaiba matsayin, dukda tarin dukiya da ALLAH ya bashi tun yana ƙanƙaninsa, shiba duniyar bace a gabansa, dan da itace bazai taɓa rabuwa da ƙyaƙyƙyawa irin Shahudah ba data haɗa komai na gata da nasaba ya ɗaukeki a matsayin ƴar riƙo a gidansu, wadda suke kallo ƙasƙantacciya a cikinsu. Akwai hikima mai yawa a al'amuran UBANGIJI bilkisu da jahili baya ganinsu ta fuskar data dace kinji”. Kaina na gyaɗa mata a hankali, dan kalamanta sun sakani jin sanyi a raina, sai dai ina jinjina yanda zan rayu da mutum murɗaɗɗe mai wulaƙanci da ƙasaita irin Boss, aɗan zaman danai dashi na fahimci abinda ba'a sakashiba sam baya burgesa balle ya tsoma kansa. To miya kawosa cikin nawa lamarin ni kuma?. Wannan itace tambayar data tsayamin a rai har dare. ___________________________________ Zaune yake a ɗaɗɗaure, an ɗaure masa idanu da jan ƙyalle, bakinsa ma a liƙe yake, shi kansa baisan a ina yakeba, abinda kawai ya sani da zai iya tunawa shine. Ranar juma'ar da aka ɗaura auren su boss, lokacin da ake tsaka da wannan dambarwa ta neman sanin wanda ya rikita tsarin auren, yabi sahun masu gani da ido babu damar tofa albarkacin baki, har aka gama rikicin massallaci aka nufi gida, baiga boss ɗinsaba, dama baisa ran ganin nasanba a wannan lokacin, ganin su dad sun ɗunguma gida shima saiya hau napep domin komawa gidan ya ɗau jikkarsa ta tafiya gida weekend kamar yanda ya saba, dama sunyi sallama da boss tun a daren jiya, hakan yasa bai damu daya kirasaba koya jirasa. Shiru gidansu boss yake babu wata hayaniya, dan duk suna gidansu Shahudah, Mama Atika da mama badiyya dake fama da jiyyane kawai a gidan sai hadimai da samari waɗanda baza'a rasaba da suka dawo daga wajen ɗaurin aure. Jikkar kayansa ya ɗauka ya fito bayan sunyi sallama da baba mai gadi, cike yake da nishaɗi akan yanda auren ya kasance, Boss ya samu wadda yake masa fata tun sanda ya fara ganinsa tare da ita, yana gab da barin layin wayarsa tai ring, cirowa yay ya duba, gani mamansace yay murmushi tare da ɗagawa yana waige-waige, saida ya tabbatar babu kowa ama kusa dashi balle yay tunanin za'a jisa kafin ya fara maganarsa kai tsaye cikin zaurence kamar yanda suka sabayi. “Mamana albishirinki?”..............✍ Karku rikice, muje zuwa page 27, danjin ina aka dosa, nasan dai dayanku sun fahimci kowanene ma kafin akai ƙarshen zance😉🤫👌🏼. ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa. SAFIYYA HUGUMA tazo muku da; ƊAURIN ƁOYE ALƘAWARIN ALLAH. HAFSAT RANO tazo muku da; SAUYIN ƘADDARA ƊAURIN GORO MAMU GEE tazo muku da; BURI ƊAYA ƘAUNAR MU. MISS XOXO tazo muku da; KAIMIN HALACCI IGIYAR ZATO. BILYN ABDULL tazo muku da; WUTSIYAR RAƘUMI... GUDU DA WAIWAYE.... abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu. 09032345899 sai kunzo😍😍😍😘. masu buƙatar link ɗin telegram kuyi haƙuri baya nunawa anan, amma insha ALLAH a page ɗin dazaiyi yawo a watsap da facebook zan saka saiku ɗauka acan. Musha weekend lafiya, maybe kuma ku ganni lahadi koma gobe idan ALLAH ya kaimu.😍😍😍😍. ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭Bilyn Abdull 📚: Page 27