Kenza eBookz

Kwai cikin kaya book 2 complete - Chapter 58

Kwai cikin kaya book 2 complete - Chapter 58

Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 58: Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 58. “Da haɗin bakinki kenan mijinki ke aikata komai!!” Qaseem ya faɗa…

4,212 words

“Da haɗin bakinki kenan mijinki ke aikata komai!!” Qaseem ya faɗa cikin matsanancin fushi tamkar zai haɗiye Mom, baya tai da sauri jikinta na rawa, cikin rawar murya tace, “Qaseem anya kana cikin hankalinka kuwa? Miya samu kanka? Ko an sauya mana kai ne?”. “Komai ma ya sameni fiye da yanda tunaninki ke baki ke da shi. Tun bansan kaina ba ke da shi kuketa nunamin banida wani maƙiyi a duniya sama da Jawaad, Why?. Mom! Nace Why? Shiɗin baɗan ɗan uwanki bane?, shi ɗin ba mijin ƴarku bane? Miya aikata mai zafine wai a gareku da har yau ban taɓa saninsa ba ni?......” “Qaseem!!” Mom ta faɗa cikin tsawa tana fashewa da kuka. Cikin ficewar hayyaci Qaseem yace, “Eh ki kira sunana koma sau dubune, gaskiyace bazan taɓa fasa faɗaba, to idanma baki saniba yanzu zan sanar miki, idan kuma kin sani bara na maimaita miki. Ita wannan tsintsiyar magen da kike magana MIJIN naki ya tsintota daga ranar ne dan ya jefata cikin abinda yafi ranar zafi, cikin wuta yay niyyar jefa mata rayuwa saboda cimma burinsa, mahaifinane shi amma nasha zarginsa da aikata abubuwa marasa ƙyau a cikin gidan nan, amma da naso ɗaukar mataki saina gaza hakan, na tabbata dukkan ƴan aikin da akai raping a gidannan shine yay musu.....” Tsawa Mom ta daka ma Qaseem jikinta na matuƙar rawa, “Qaseem!! Mahaifinka zaka ƙullana sharri irin wannan saboda Jawaad da Bilkisu?”. Da ƙarfi Qaseem ya daki tebir ɗinsa, kayan sama suka tarwatse, ya matsa gab da Mom yana nunata da ɗan yatsa ƙirjinsa na sama da ƙasa na kumburar zuciya. Ya cigaba da faɗin, “Tun kin nuna bakisan komaiba bara na faɗa miki to, tun lokacin da akaima ƴar matarnan Amina fyaɗe a cikin gidanmu na gaskata hakan a cikin raina, domin kuwa lemon da aka ajiye ta sha lemo ne da kaf gidan nan shi kaɗaine ke shansa, hakanma yasa ba'a ajiyesa a fridge ɗin kitchen sai na falonsa kawai, ko a falon ƙasa inhar baya ƙasar kwashewa kike ki maida masa sama, to tayaya akai ranar yaje kitchen har yarinyar ta gani ta ɗauka ta sha bayan shi mai shan ma baya nan? Abu na biyu sai da na ɗauki kwalin lemon a bola naje nai bincike akan ɗan sauran cikinsa na gane magani ne mai ƙarfi aka saka a ciki kuma a ƙalla ya kai kwanaki biyar da zubawa, abu na uku na zauna nayi dogon nazari da tunani harna gano ainahin maganain da akai amfani da shi, sai kuma kwatsam na tunano na taɓa ganin maganin a wajen Dad amma a wancan lokacin sai ya gayamin na ciwon bayane dan na gansa da shine a bazata, da yake kuma ban kawo komai a rainaba sai ban amsa na karanta ba a lokacin. Tun daga wannan ranar na fara bibiyar al'amuransa, sai dai abin mamaki bana iya cewa komai akan dukan abinda zan gani. to bara nama faɗa miki abinda baki saniba, a dukkan tafiye-tafiyensa cikin kashi uku biyu bayinsu yake ba, idan yace yabar ƙasarnan tafiyar sati biyu to kwana huɗu ko sati guda ya keyi ya dawo, da wannan makircin nasa yake amfani wajen aikata laifi a rasa wanene keyi a gidan, Mom ya kamata kiyi tunani da hankalinki, a dukka masu aikinmu uku da akai Raping a gidanmu duk sai baƙya nan ake aikatawa, kuma da anyi washe gari ko kwana biyu dayi Dad yake dawowa.......” Ƙasa Mom ta zube tana kallon Jawaad dake tsaye kawai yana kallon tamkar wani gunki, tun fara maganarsu baice komaiba bai kuma motsa ba. hawayene ke kwarara a idanun Mom tamkar an buɗe fanfo. Qaseem ya nuna Jay da faɗin, “Kayi haƙuri Jay ka gafarceni, zan faɗi wani abu a kan matarka duk da bata a wajen nan, tunda Bilkisu tazo gidanmu ban taɓa jinta a zuciyata da sunan soyayya ba, sai dai ina sonta matsayin ƴar uwata kawai. Amma tun randa na farka a barci naga Dad tsaye kaina a cikin ɗakina naji duk duniya babu wadda nakeso sama da yarinyar nan, ga wata sha'awarta mai tsanani inaji wadda inhar zata kasance kusa dani sai naji inason taɓa mata jiki, abin mamaki duk wannan sha'awar tata da nakeji ban taɓa jin zan iya lalata mata rayuwaba, ni dai kawai burina na taɓa jikinta ko nayi kissing ɗinta na rungumeta shike nan. Da ya ke kuma yarinyace mai tarbiya ko hannunta bata yarda na taɓa sai ta nunamin ɓacin ranta. Kuma saifa ina a kusa da itane nakejin hakan, amma da zarar bama tare da juna ni mantawama nake da ita gaba ɗaya. A daren da Dad ya fara shigo mata ɗaki har aka tsoratamu da ƙara a gidannan nine na fara fitowa, ni duk zatona mai gadine wani abu ya sama, shiyyasa nai gate kai tsaye, ina isowa maigadi na buɗema Dad ƙofa ya fita a gidan....” Dafe kai Jawaad yayi da sauri zuciyarsa na wani irin matsanancin harbawa da sauri-sauri, duk da Dad yake zargi dama hakan bai hanashi jin maganar tai masa nauyiba a ƙwaƙwalwa da zuciya.... “Ƙwarai kuwa Dad” Qaseem ya bama ya sake maimaitawa yana kallon Mom cikin ido, “A tunaninki mai aƙidar kar ƴan uwansa su raɓesa ne zai ɗakko budurwa kamar bilkisu ya ajeta gidansa dan ya ƙyautata mata rayuwa kawai? Aini tun washe garin da aka kawota gidannan na ganta kuma akai min bayanin zuwanta nasan akwai manufa a zuciyarsa game da ita, sai dai narasa ta wace hanya zan kuɓutar da ita? Wannan mijin naki da kike ji da gani ramin bushiyane daga shi sai ƴaƴansa, ke kuma matarsa kura ce kema daga ke sai ƴaƴanki. Bara na sake maimaita miki shine keta bibiyar rayuwar marainiyar ALLAH akan fyaɗe har cikin gidan aurenta, da yaga bazai cimma burinsa cikin sauƙiba shine ya tafka mana asirin da har nai maganar shirya aurenta duk da a zuciyata sam ba haka bane ba. A gaban duniya ya nuna cewa ya ƙyautata mata rayuwa, zai kuma aurama ɗansa jininsa ita, amma sai ya zagaye ta bayan fage shi da ɗan uwanki Uncle Nasir suka zurmaki a ciki da ɗauraki a dukkan hanyoyin da suka gama tsarawa, ke kuma kika hau saboda baƙya son aurenmu bisa naki gurɓataccen tunanin na jahilci da son zuciya. Kuka ɗakko hayar ɗan fir'auna akan ranar ɗaurin aure za'a aura mishi ita, ni kuma zaɓinku, daga baya sai ace mistake aka samu, shi kuma dama kunbiyasa akan karya sake ya saketa duk bala'in da za'ayi har sai ƙura ta lafa an kaita gidansa. sai shi Dad yaje ya cika burinsa a kanta kawai batare da kowa yasan hakanba har ke kanki. Sai dai UBANGIJI ba azzalumin sarki bane, sannan shi yana dubi da ƙyawawan zuciyoyi masu tsoronsa da biyayya a garesa, ashe Jay ya saka ana bibiyar dukkan al'amarinsu basu sani ba..........” Zubewa Mom tai ƙasa kawai tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai tare da riƙe kanta da ke juya mata. Jawaad yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa da mai dawa kan Qassem. Murmushi mai ciwo da ƙunar zuciya Jay yay yana tura ɗayan hannunsa cikin aljihu, ɗayan kuma ya dafa kafaɗar Qaseem sukaima juna murmushi. Takawa ya sakeyi gaban Mom ya tsaya har lokacin fuskar tasa da murmushin, ya durƙusa a gabanta yana haɗiye ɗacin daya tokare masa maƙoshi, “Har yanzu ke uwace a gareni Mom, yayar mahaifina, duk da ina zargin kina cikin waɗanda suka tarwatsa masa ahali”. Da sauri Mom ta ɗago tana kallon Jay, ta shiga girgiza kanta tana hawaye, “Jawaad dan ALLAH kar kaimin wannan mummunar zargin, mi Abdul-aziz zaimin niko a duniyarnan da har zan tarwatsa masa a hali?......” Miƙewa Jawaad yayi yana ɗage kafaɗa da taɓe baki, “Wannan amsar a gaban alƙali zaki badata Mom ba ananba”. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni Aysha wannan wace irin ranace”. Mom ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka. Qaseem da yakejin kamar ace yau ɗin ranar barinsa duniya ce yace, “Momy wannan ranace ta tonon silili, ranace mafi muni da a garemu bisa ga son zuciyar mijinki, rana ce da duniya suka san wanene shi? Mom Dad ya cutar da rayuwarmu, kaicon dukiyar da zata kasance haramtacciya ga mai ita, ki kalla yanda ake nunasu cikin ƙasƙanci dan ALLAH, wace riba sukaci? Wane alfahari suka barmana muyi? Wane tunƙaho da taƙama ya rage mana kuma?”. Mom da batasanma wainar da ake toyawaba game dasu Dad sai yanzu da Qaseem ya nuna mata a tvn office ɗinsa a take ta ƙwalla ƙara ta zube yaraf a sume. Jay daya fice ƙofar office ɗin ya tsaya dansu Sir Ahmad tuni suka bar wajen ganin maganace data shafi family ya dafe kansa da rumtse idanunsa da masifar ƙarfi, dan yaji dukkan abinda Qaseem ɗin ke faɗama Mom, ya kuma tabbatar ƙarar tata nada nasaba da ganin abinda ya farun.

___________________________ Dr Tayyeb hospital _______________________

Kamar yanda ƙarar kai kawon jirage ta ɗauki mafi yawan mutanen dake cikin asibitin haka ta ɗauki tasu Anuwar dake zaune jigum-jigum suna jiran farkawar Umm-Anum, dan Dr Tayyeb ya sake shiga ya dubata, ya kuma musu bayani akan su kwantar da hankalinsu da ruwan da aka saka mata ya ƙare zata farka normal insha ALLAH. Aunty Batool ce ta fara miƙewa ta leƙa ta Window'n da suke a kusa da shi, da ɗan mamaki ta juyi tana kallonsu Ummah da faɗin, “Anya kuwa yau garin nan lafiya yake? Helicopters nefa na sojoji keta yawo wannan ƙarar da mukeji”. “Helicopters kuma? To miya faru kuma?”. Ummah ƙarama ta faɗa tana miƙewa itama ta leƙa. Tabbas kuwa zancen Batool gaskiyane, dan har wasuma dake cikin asibitin sun fara fita waje. “Gaskiya garin nan babu lafiya kam”. Ummah ƙarama ta sake faɗa tana nufar ƙofa. Da sauri su Anum sukabi bayanta harda Batoul da Anuwar ma daya bisu a ƙarshe shi da Ummah babba, sai dai Ummah babba na gabansa. “Ya salam”. Anuwar ya faɗa da sauri saboda karo da sukaci da wani bawan ALLAH dake ƙoƙarin shigowa shi kuma Anuwar ɗin yana yunƙurin fita. A kusan tare suka buɗe baku zasu bama juna haƙuri sai hakan ya gagara kowa ya cak a tsaye baki buɗe jiki na tsuma. Idanun Uncle Sulaiman tamkar zasu faɗo ƙasa dan ruɗani da al'ajabi, cikin sarƙewar harshe yace, “Ja...waa...” sai kuma ya gaza ƙarasawa ya girgiza kansa yana haɗiye yawu da ƙyar. Shiko Anuwar wani irin yamutsawa jininsa keyi da kansa, ya kafe Uncle Sulaiman da kallo tamkar ya samu television ɗin kallo. A haka Shahudah da sauran ƴammatan family ɗin sa'anninta suka iso wajen suma zasu koma ciki. A take duk sukaja wani wawan birki suna kallon Anuwar. “Kai!!” Shahudah ta faɗa daɗan ƙarfi tana matsawa gab da Anuwar da binsa da kallo daga sama har ƙasa tana zagayashi. Nannauyan numfashi Anuwar ya sauke da ɗan lumshe idanu ya kalato busashen yawun daya rage masa ya hadiye da ƙyar da raɓawa ta gefen Uncle Sulaiman zai wuce. Caraf Shahudah ta riƙo hannunsa jikinta na rawa. “Kai dan ALLAH wanene kai?”. “Muhammad Anuwar Abdul-aziz yusif tafida”. Wata murya dake a bayansu ta basu amsa saɓanin shi Anuwar ɗin da sukaima tambayar. Juyawa sukai da azabar sauri har Uncle Yusif na neman zubewa ƙasa wajen rawar jiki. “Hajiya Mariya, kinsan mi kika faɗa kuwa?”. Uncle Sulaiman ya faɗa yana ware idanunsa akan Ummah babba data basu amsar. Murmushi mai ciwo Ummah babba tayi tana kamo hannun Anuwar ɗin cikin nata, “Alhaji Sulaiman ai ko baku sami wannan amsarba ya kamata kuyi tunanin hakan direct tunda wanda ya mutu baya dawowa ai ko? Kuma koda ace yaya nada rai ai bazai zauna a wannan ƙuruciyarba tunda har Jawaad daya bari matsayin ɗa ya wuceta”. “Haj....h...ha..hajiya mariya kin sake sakani a ruɗani wlhy, a ina Abdul-aziz ya samu ɗa bayan Jawaad kuma?”. “Biyoni da zakayi shine kaɗai zai baka amsar dukkanin tambayoyinka”. Ummah ta faɗa tana murmushi da kama hannun Anuwar suka nufi corridor ɗin da ɗakin da aka kwantar da Umm-Anum yake. Ba Uncle Sulaiman kawai ba, hatta su Shahudah bin bayansu sukai, yayinda wasu a cikinsu kuma suka nufu kaima iyayensu rahoto.

Dr Tayyeb na ƙoƙarin fitowa daga ɗakin da Umm-Anum take dan ya sanarma su Ummah su shiga an cire mata drip yaci karo da Ummahn dake riƙe da Anuwar. Murmushi ya ɗanyi yana ja baya ya koma cikin ɗakin da juyawa ya kalli Umm-Anum dake kallonsu da murmushi yace, “Yauwa hajiya, dama zan sanar muku ku shigo ta tashi normal Alhmdllh, dan zama mu iya sallamarku kamar”. Kafin Ummah tace wani abu Uncle Sulaiman dake a bayansu cikin tsananin kiɗima yace, “Bilkisu!”. Da sauri Umm-Anum ta maida dubanta gareshi, sai kuma taɗan waro idanu waje itama tace, “Yayah Sulaiman!”. Cikin matuƙar rawar jiki ya afka cikin ɗakin, babbar rigarsa har tana neman taɗesa Dr Tayyeb yay azamar tarosa yana faɗin, “Subahanalillhi, Alhaji yi a hankali”. Duk da Umm-Anum batajin ƙwarin jikinta hakan bai hanata sakkowa daga saman gadon ba. Sakkowar tata kuma tayi dai-dai da faɗowar Uncle Uwaisu da sauran ƴan gidan su Jawaad ɗakin. “Wlhy itace da gaske!!” Uncle Uwaisu ya faɗa yana jan birki da ɗaga hannaye sama tamkar wani zararre.... Kafin wani a cikinsu ya samu damar sake tofa tashi Nabeelah ta kutso tsakkiyarsu jikinta na rawa, “Ummah! Ummah!! Ummah!! Ku kalla television, ku kalli abinda ya faru dasu Yayanmu a wajen ƙwato Alhaji babba, m....m..matsafa Ummah, wlhy matsafa suka gano acan.....” Uncle Sadiq ne yay azamar rarumar remote ɗin television ɗin ɗakin ya kulla, anko haske dai-dai inada ake fiddo su Uncle Nasir daga cikin gidan daga su sai jajayen ƙyallaye, Jawaad na rungume da Alhaji babba yana shafa masa ruwa a fuska za'a sakashi cikin helicopter shi da wasu a cikin waɗanda aka ceto. A take ɗakin ya ruguntsume da tsananin tashin hankali da ruɗani, Umm-Anum ta fashewa da kuka tana dariya kuma, cikin wani ƙarfin zuciya ta ɗaga murya wajen faɗin, “Rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya”. A take ɗakin yay tsit, suka juya gaba ɗaya suna kallonta a wani irin yanayi mai wahalar fassara a fuskokinsu................✍

Nima dai kam na tsinci kaina a yanayin har takai alƙalamina da faɗuwa a ƙasa batare da na shirya hakanba😳🚶.

Kuyi manegi babu editing yau🤒🚴🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻*_ƘWAI CIKIN ƘAYA!!_*

Bilyn Abdull ce

Page 60

_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR... 🙋🏿‍♀️🙋🏿‍♀️INA KUKE NE? 🔊🔊KU MARMATSO, DOMIN ZAMAN JIRA YA KARE, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKA HADA HAZAKA DA KAIFIN TUNANI SUN SAKE ZAGE DAMTSE SUN ZO MU DA WASU SABBIN SALON RUBUTUN SU, WADANDA ZASUWA’AZANTAR, SU NISHADANTAR, KANA SY DILMIYA KU A KOGIN KAUNA, BASU TSAYA ANAN BA SALON RUBUTUN SU YA SAKE ZUWA DA SABBIN TSARE TSARE NA DARUSSA DABAN DABAN, DA KUMA HANYOYIN GYARIN JIKI DA WAJE._

_KADA KU MANTA MARUBUTAN ZAFAFAN DAI SUNE WADANDA SUKA YO MUKU HAR KASHI BIYU A SHEKARAR 2020 DATA GABATA,: WUTSIYAR RAKUMI DA GUDU DA WAIWAYE NA BILYN ABDULL. 2-DAURIN BOYE DA ALKAWARIN ALLAH NA SAFIYYAH HUGUMA.3-BURI DAYA DA QAUNAR MU NA MAMUH GEE-4- SAUYIN KADDARA DA DAURIN GORO NA HAFSAT RANO. SAI 5-KAI MIN HALACCI DA IGIYAR ZATO NA MISS XOXO.._

_A WANNAN SABUWAR SHEKARAR TA 2021 MA HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE DAWOWA DA WASU SABBIN DA’DADAN LITTATTAFAN NASU:_

_1_

_* SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA DA ABADAN TAZO MUKU DA SABON LITTAFIN TA MAI SUNA: *(SIRADIN RAYUWA)💜*_

_2_

_*HAFSAT RANO* MARUBUCIYAR GUGUWAR SO DA RUHI DAYA, TA ZO DA SALON NATA LITTAFIN MAI SUNA: *(ABINDA KE CIKIN ZUCIYA..*)💘_

_3_

_* MAMUH GEE* MARUBUCIYAR TARAYYAH DA EZNAH, TAZO DA SABON ZUWA MAI SUNA: *(MIN QALB)❤️.*_

_4_

_*MISS XOXO* MARUBUCIYAR NAUFAL DA SAIFUL-ISLAM, TA YUNKURO DA WANI MAI SUNA: *(KIBIYAR AJALI)*💜_

_5_

_SAI MARUBUCIYA *BILLYN ABDUL* WADDA TAYO MUKU KWAI CIKIN KAYA, DA CIKI DA GASKIYA TA YINKURO DA WANI MAI TAKEN: *(YANKAN BAYA)*💝_

_RIGIJI GABJI DUKKAN WADANNAN LAGWADAR DADADAN LITTAFAN BIYAR ZASU ZO MUKU NE INSHA ALLAHU AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA;_

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Page 60

...............Umm-Anum na kuka tana dariya duk a lokaci ɗaya ta nuna tv'n da yatsanta manuniya, cikin wani ƙarfin zuciya ta ɗaga murya wajen faɗin, “Rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya”. A take ɗakin yay tsit, suka juya gaba ɗaya suna kallonta a wani irin yanayi mai wahalar fassara a fuskokinsu. Kowa ya gagara cewa komai sai kallonta kawai da suke. Ta share hawayen da suka gama wanke mata fuska tana kallon Ummah babba. “Mariya a kaini wajen baba”. Da ƙyar Ummah babba ta iya gyaɗa mata kai a hankali. Bata ƙara cewa komaiba ta gyara mayafin jallabiyar ta data naɗa tamkar yanda larabawan Saudia keyi, Batool ta ɗakko mata takalmanta zuwa gabanta, dafa Batool ɗin tayi ta saka dan ƙafarta ciwo take mata kaɗan-kaɗan, tun jiya bata gama saki ba har yanzun. ta maida dubanta ga su Uncle Sulaiman dake tsaye tamkar sojoji, har yanzu babu wanda ya iya gaskata ruɗani da al'ajabin da idanunsu ke gani a zahiri da magiji. Hannayenta🙏🏻 ta haɗe waje guda tana ɗan murmushi, “Ku gafarceni, ganin Mahaifina a yanzu gareni yanada matuƙar muhimmanci”. Bata jira amsarsu ba ta raɓasu ta wuce abinta Batool da Anum da Nabeelah sukabi bayanta.

Da kallo suka bita tamkar wasu wawaye harta fice ita da zugarta. Ummah ƙarama da babba suma sukai yunƙurin bin bayansu. Uncle Sulaiman ne ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin jiki da rawar murya yace, “Hajiya Mariya a ina kuka samu Bilkisu? Tun tsahon wane lokaci kuma?”. Kanta ta girgiza masa tana share guntun hawayenta itama, “Bani da ikon amsa waɗan nan tambayoyin Alhaji Sulaiman, inaga mu bari har sai lokacin da Yayah taso hakan da kanta, na tabbata zatazo ta sameku har gida insha ALLAHU. Mun barku lafiya”. Ta ƙare maganar da kama hannun Ummah ƙarama suka fice suma. “Uncle wacece ita ɗin wai?”. Shahudah da idanunta ke lullumshewa saboda hajijiyar da take gani ta tsananin tashin hankali ta faɗa tana dafe bango. Saurin ruƙota matar Uncle Sadiq tayi jikinta na rawa itama. “Shahudah!!” ta faɗa daɗan ƙarfi ganin jikin Shahudah ya fara saki alamar neman suma takeyi itama. Ruɗewa ɗakin ya ƙarayi, masu share hawaye suka ƙara ƙarfafa kukansu da sauti, yayinda wasu suke zubewa ƙasa daɓar tsabar shiga ruɗani da abinda ake nunawa har yanzu daga gidan tv.

__________________ STATION _____________

Da taimakon Jawaad da Qaseem aka fita da Mom zuwa mota, Qaseem ya shiga baya ya riƙeta yana kuka da kiran sunanta da roƙon karta tafi ta barsu, “Mom Please ki tashi, dan ALLAH karki tafi ki barmu muna sonki, idan kika tafi abin zai mana yawa Mom, idan kika tafi wa zamu kalla muji daɗi”. Ya ƙare maganar da kife kansa bisa fuskarta yana cigaba da kuka, shi kansa bai taɓa sanin shi rago bane mai rauni irin haka ba sai a yau, gani yake kaf duniya babu wanda ya kaisa shiga ruɗani da tsananin tashin hankali. Har Jawaad daya ja motar ya fice daga station ɗin Qaseem nata kuka rungume da Mom. A haka suka isa General hospital, inda suka tadda ƴan jarida da jama'ar gari cike anan ma, har takai da ƙyar ƴan sandan da aka zuba ke control ɗinsu. Burin kowa yaga gawarwaki da mutanen da aka ƙwato wajen su Dad. A haka dai aka samu shiga da Mom ciki da ƙyar. Darajar waɗanda suka kawotan yasa akai mata amsar gaggawa da miƙata wani ɗaki.

Motar su Umm-Anum na shigowa asibitin ana shiga da Mom ciki, gurin a cinkushe yake da mutane, hakan yasa suka rasa hanyar da zasubi su shiga balle susan ta inda zasu fara. Aunty Batool ce tai tunanin kiran Jawaad, dan haka ta ciro wayarta daga bag ta fara nemansa, harta tsinke bai ɗaga ba, bata gajiba ta sake kira, nan ɗinma dai harta tsinken bai ɗagan ba. Kanta taɗan dafe zatai magana sai idanunta suka sauka akan Jawaad dake magana da wasu police su uku da alama suna masa bayani ne akan yanayin da asibitin yake ciki na cikar mutane da ƴan jarida. “Alhmdllhi ga yayanmu ɗin canma ai”. Dukansu inda take kallo suka kalla, kafin wani ya samu yin magana Anum da Nabeelah suka nufi inda yake, sai dai kafin su ƙarasa aka dakatar dasu a tsawace. Bayani Nabeelah keson ma police ɗin daya tsaidasun amma yaƙi saurarenta, hakan yasa ta fara masa magana da tsiwa dan sun roƙesa amma yana neman cin zarafinsu ma. Hayaniyarsu ta jawo hankalin Jay ya juyo. A bazata yaga ƙannensa, ya ɗan ɗaura hannunsa na dama saman goshinsa da keyi tamkar zai tsage saboda azabar ciwon kai. Da sauri ya kalli police ɗin da suke tare yana nunasu Anum ganin wancan ɗan sandan da suke tare ya ɗaga hannu zai mari Nabeelah amma ta duƙe. “Kaga, cemasa ya barsu suzo”. Amsa masa yay da to, yana nufar inda su Nabeelah suke, yay saurin riƙe hanun ɗan sandan daya sake ɗaga hannu zai mari Nabeelah dan bakinta yaƙi mutuwa saboda haushin baƙar maganar daya faɗa musu dan sunce su ƙannen Jay ne wajensa zasuje. A harzuƙe ɗan sandan ya juya zaiyi magana sai yaga ogansu, saurin gyara yanayinsa yay zai masa bayanin abinda ya faru tsakaninsa da yaran sai yaji ogan nasa yacema su Nabeelah suje wajen Jay ɗin. “Oga kasan mi sukayimin kuwa?”. Murmushi yay masa da ɗan buga kafaɗarsa, “Komi sukai maka kayi haƙuri. ƙanen yallaɓai Jay ne”.

Da kaushin murya Jawaad daya tsare su Nabeelah da rikitattun idanunsa yace, “Miya kawoku nan?”. “Uh...Uhm Yayanmu bamu kaɗai bane, Ummu ce tace a kawota wajen Alhaji babba”. Nabeelah ta bashi amsa tana laɓewa bayan Anum idanunta cike da tsoro. Da sauri Jay ya hau waige-waige, saiko idanunsa suka sauka akan Batool da su Ummah da suma kallonsu sukeyi. Batare da ya sake cewa komaiba yabar wajen zuwa inda su Batool ɗin suke.

Umm-Anum data rage a mota bata fitoba hango Jay ya nufosu ta fito da ƙyar dan jikinta duk babu daɗi, kallo ɗaya zakaima idanunta kuma kasan tayi kuka sosai, dan sun kumburi sun kumayi jaa. Sauri riƙeta Jawaad daya ƙaraso yayi, ya taimaka mata ta tsaya akan ƙafafunta sosai tana sauke ajiyar zuciya, “Ummuna miyasa kuka fito? Kallafa ƙafarki ta kumbura?”. Maimakon ta bashi amsa sai tambaya ta jefa masa, “Ina Bilkisu?”. “Amma Umm......” “Ni dai ina yarinyata nace maka?”. Numfashi ya sauke da ɗan ƙarfi yana lumshe idanu sai kuma ya buɗe lokaci ɗaya, “Tana ciki Ummuna, sun saka mata drip ne saboda ta suma acan, amma inama ganin ƙila ta farka yanzun dan tun ɗazun Dr Bello ya sanarmin ta farfaɗo”. “Alhmdllh, babana fa”. Yanzu kam ɗan murmushi ya mata da sumbatar hannunta, “Shiyyasa naga idanunki sun kumbura ko Ummuna, kinyi kuka?”. Kansa ta dungure tana ƴar hararsa, yay murmushi da kama kunnuwansa alamar na tuba.

★★★★

Sun fara shiga ɗakin da aka kwantar da Bilkisu, kamar yanda Jawaad yay hasashe sun iske ta farka, tana zaune jingine da filo wata Nurse na bata abinci da takeci da ƙyar dan warin asibitin yay masifar addabarta, farkawarta amanta biyu saboda warin asibitin, yanzu ma Dr Bello ne da kansa yasa aka kawo mata abincin dan taci tasha magani kafin Jay yazo ya ɗauketa kamar yanda ya sanar masa. Gaba ɗaya tayi wani zuru-zuru, idanunta sunyi masifar kumbura da ƙanƙancewa, sannan sunyi jajur a ciki. shigowar su Jay yayi dai-dai da zaburarta ta sakko a gadon saboda tahowar amai, Nurse ɗin ta ajiye tray'n abincin da sauri tana ƙoƙarin kamota amma tuni takai toilet. Duk rufa mata baya sukai cikin tashin hankali, sai dai duk a ƙofar bayin sukaja birki, Jay da Nurse ɗin ce kawai suka sami damar shiga. Sosai hankalin Jay ya tashi ganin yanda bily ke yunƙurin amai tamkar zata amayo hanjin cikinta, Nurse ɗin na riƙe da ita tana jera mata sannu da shafa bayanta. Matsowa yay kusa da ita shima ya ruƙo hannunta. Da ƙyar aman ya tsagaita, ya taimaka mata da kansa ta wanke bakinta, sai numfashi take saukewa a wahale, kwantar da ita yay a ƙirjinsa tausayinta mai tsanani yana ratsashi, a ƙasan ransa kuma tunani yake ‘mi taci haka?’. “Ka kaini gida, banason warin asibitin nan”. Ta faɗa murya can ƙasan maƙoshi tana sake lafewa a jikinsa da shaƙar ƙamshin turarensa da yake ɗan dawo mata da nutsuwarta. Ɗago kanta yay ya saka fuskarta cikin tafukan hannunsa suna kallon juna, “Mi kikaci haka?”. Ya faɗa cikin tashi daskararriyar muryar yana raba idanu akan fuskarta tamkar zai gano abinda ke damunta anan ɗin. Matsawa tai zata sake kwanciya a jikinta tana faɗin, “Banci komaiba, warin asibitinne banaso nidai”. “Jawaad yaya dai?”. Ummah ƙarama ta faɗa kafin ya samu damar sake tambayar bily.

Da sauri naja baya daga jikinsa dan na manta bafa mu kaɗai bane, bango na dafe saboda jikina babu ƙarfi. Ban iya fahimtar amsar daya bataba dan hankalina baya a garesu, tadai riƙe hannuna ta kamani muka fita sunata jeramin sannu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull