Kenza eBookz

Kwai cikin kaya book 2 complete - Chapter 9

Kwai cikin kaya book 2 complete - Chapter 9

Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 9: Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 9. kamar yanda Mom suke da Abban Boss, nima da Abbansu Aunty Shahudah da…

4,120 words

kamar yanda Mom suke da Abban Boss, nima da Abbansu Aunty Shahudah da Mamana babansu ɗaya”. Kai Jabeer ya shiga kaɗawa yana faɗin, “Tab cakwakiya kenan, kice shiyyasa Qaseem beson kowa ya raɓu dake? Kodai ƴar gida zamuyi?”. Murmushin yaƙe kawai nai masa bance komaiba, danni gaba ɗaya kaina ya toshe, koda wasa ban taɓa kawo cewar boss mijin aunty Shahudah bane ba, to yama akai na kasa fahimta? Koda yake bai taɓa zuwa gidanba ina nan, bankuma taɓa ganin koda hotonsa ba a gidan, amma kuma inban mantaba nasha jin sunan Jawaad a bakin ƴan gidan, ‘ya salam, miya toshe min kaina haka?’. Har mukaje station wannan tunani ne keta kaikawo tsakanin ƙwanyata da zuciyata batare da nasan ma'anar hakanba, shima kuma oga Jabeer bai sake cemin komaiba saima redio daya kunna. Koda muka iso office nabi oga Jabeer kamar yanda ya umarceni, ya bani ƙaramar takarda ta address ɗin wajen da boss yace sannan na fito. Na iske su ummie sunata shirin tashi, dan biyar tayi, ALLAH ma ya soni nayi sallar la'asar yanzu da muka koma gidansu boss, nima ɗaukar tarkacena nai muka fito tare, dan Ummie zanbi, na leƙa office ɗin yah Qaseem bayan na fito daga wajen oga Jabeer na iske bayanan ya fita wai. Daurewa nai na cire alaƙar Aunty Shahudah da boss data tsayan a rai ba gaira ba sabar na biyema Ummie mukaita hirarmu, har gida ta kaini, sai dai bata shigaba iyakarta gate na sauka ita kuma ta juya. Na iske su a falo aunty Shahudah kwance Doctor na saka mata ƙarin ruwa, ba hurumina bane tambayar abinda ya sameta, na gaishesu tare da mata sannu cikin jimami sannan na wuce ɗaki abina. Bansan miyasa na tsinci kaina cikin rashin jin daɗin komaiba, nai wanka na canja kaya, ganinma magrib tayi saina bari nai salla sannan nai zaman yin azkar har aka kira sallar isha'i, itama tashi nai nayi sannan na fito falon dan sake duba Aunty Shahudah, dan banajin yunwa, tun abincin da naci a gidan boss bai sauka ba, duk da saida Nabeelah ma tai fushi sannan naci bayan ummah ta saka baki. Na iske aunty Shahudah ta koma ɗaki, sai yah Qaseem kawai a dining yana cin abinci, sannu da dawowa nai masa, yay murmushi yana min alamar nazo. Ban musaba naje garesa, naja kujera nima na zauna, “Kinyi ƙyau” ya faɗa yana kashemin ido ɗaya, murmushi kawai nayi bance komaiba. Haka yayta ɗan jana da hira harya kammala, ya miƙe domin zuwa yay wanka, nima miƙewar nai nace bara na sake duba aunty Shahudah naje na kwanta na gaji. Zaune na isketa Aunty Aamilah na bata magani, na sake mata sannu da ALLAH ya ƙara sauƙi na fito, ɗaki na koma nai kwanciyata duk da nasan gobe idan ALLAH ya kaimu babu aiki, amma inason na kira Dad da safe idan ya bari sai naje gidan Inna Zainabu na gaishesu, da wannan tunanin barci ya kwasheni.

A ɗakin Shahudah kam bayan fitowar Bilkisu Aamilah ce ta sauke ajiyar zuciya tana mai fuskantar ƴar uwar tata da ƙyau. “Sister ga shawara mana” Shahudah da duk tazama kalar tausayi ta jinjina mata kai alamar tana saurarenta. Aamilah ta sake jan numfashi kafin tace, “Ina ganin yarinyar nan Bilkisu zamu iya sakata tai mana wani abu” murya a dasashe Shahudah tace, “Ban ganeba Aamilah ”. “Sister ina magana ne akan Brother Jawaad, da nayi tunanin Broth ne a farko, sai dai daga baya nasan bamai yuwuwa bane, musamman idan mukai dubi da yanda basama shiri tun suna yara, sam jinin Qaseem da Jawaad bai haɗuba, bankuma san lokacin dazai haɗunba, so idan mukace zamu ɗorasa akan ya taimaka mana sai dai ya ɓata komai tunda dama can bason aurenku yakeba, yanzu da yarinyar nan ta shigo, sai naga mizai hana mu amfanu da ita, dan kinsan bata da yawan hayaniya da surutu, sannan mutumin dake da irinki bazai kalletaba da sigar birgewa balle akai ga so, ballantana zuciyarmu tayi tunanin ko zata iya cin amanarmu, ko shi yaji wani abu a kanta”. Shahudah datai shiru tana kallon Aamilah tace, “Maganganunki kawai naji Aamilah, amma ban gane ina suka dosaba sam, wane taimko zamu nema akan Bb?”. “Yauwa, yanzu kikai tambaya mai ƙyau Sisi na, inaji a raina Yarinyar zata taimakemu, sai dai bani da tabbacin wajen aikinsu ɗaya, duk da dai naga kullum tare take fita da Broth, ku

ma Broth da Brother Jawaad wajen aikinsu ɗaya ne, amma wannan ba wani abu bane, zamu iya tambayarta”. Kai kawai Shahudah ta jinjina alamar gamsuwa, Aamilah tace, “ki kwanta ki huta zamu tattauna zuwa da safe, tunda weekend ne tana gida babu inda take zuwa”. Nanma da kai Shahudah ta amsa mata..

★★★★★

Washe gari da safe na tashi nai ƴan ayyukan dazan iya harda kayana da sukai datti, na gyara ɗakina tsaf nai wanka sannan na fito, babu kowa falon dan har lokacin ma bana tunanin wani ya tashi a jama'ar gidan, kicin na nufa na samawa cikina abinci naci, kafin na sake komawa ɗaki na shiga neman Number dad da ya kirani kwanaki uku da suka shige, kusan duk Numbers nashi na ƙetare inada ita, dan yakan kirani lokaci-lokaci idan yay tafiya tamkar yanda yakema sauran ƴaƴansa, bata shigaba, na sake gwadawa har sau uku saina haƙura, bazan iya zuwa ko inaba bayan wajen aiki saida umarninsa, dan banida wani jagora sama da shi a halin yanzu a duniya, sai ko yaya Qaseem da nake fatan ya zama na biyu a matsayin miji. Na aje maganar zuwa gidan Inna zainabu akan sai idan ALLAH ya kaimu gobe, idan naje inda boss yace na gama abinda nakeyi sai na shiga wajen wanke kai daga nan na wuce can koda ban jimaba sai na gaishesu na taho gida, da wannan tunanin na miƙe da nufin zuwa gidansu Amina. Harna fice babu motsin kowa, muka gaisa da baba mai-gadi na fice abina. Da sallama na shiga gidan, Amina dake a tsakar gida tana wanke-wanke ta amsa tana kumbura fuska, dariya nayi ganin yanda tayi, dan nasan dalili, ta ɗauke kanta da faɗin, “Munyi fushi, ki koma a binki”. Kafin nace wani abu mama tace, “Kwarai kuwa Amina ina bayanki”. Kunnuwana na kama duka biyu na kneeling alamar dai na tuba, dariya suka sanya daga mama har Amina da yayan Amina daya fito da ga bayi, shine yace, “A ni dai na yafe ma ƴar ƙanuwata, nasan aikine ke mata yawa”. Nace, “Yauwa Yayanmu, shiyyasa nake yayinka a koda yaushe”. yay dariya da haɗe yatsun sa babba da manuniya alamar dai-dai👌🏼 kenan. “Oh, mu baƙya yayinmu kenan? To kin ƙarama kanki laifi har tsallon ƙwaɗo sai kinyi” Amina ta faɗa tana miƙewa ɗauke da kwandon data saka kwanikan. Mama tace, “A'a auta nimafa na huce, ama mai-gadon lu'u-lu'u haƙuri”. Dariya muka saka gaba ɗayanmu saboda furicin mama, Amina tace, “Shikenan na haƙura tunda mama ta saka baki, amma da yau ɗinan saina tsamar da ƙafafunki”. Harararta nai kafin na zauna a inda ta tashi na gaida Mama da Yaya Sule, daga nan muka hau hirarmu.

Wajen sha biyu Amina na tayani tsifar kai muna hira, mama kuma nata ƙoƙarin ɗaura awara da muka tace da Amina bayan munje munkai markaɗe, nace, “Amina!”. “Na'am” ta amsamin tana leƙo fuskata. Ɗalli namata a fuska da ɗan yatsa, ta matsar da fuskarta tana ɓata fiska saboda zafi, niko na kwashe da dariya, “Ke ɗince kin wani kawomin fuska saikace maison leƙa ramin gwal”. Dariya itama tayi tana ranƙwashina a kai, “Ai bazakici bulusba kuwa”. “ALLAH da zafi” na faɗa ina harararta” tace, “Nima ai naji zafin shiyyasa na rama”. “Ba komai zaki gane shayi ruwane. Maganarnance dai zamu sake”. Shiru tayi kamar bazatace komaiba, tsifar da takemin ma ta koma min ita a hankali, na zungureta da hannu dan nasan ta faɗa kogin tunanin nata. Numfashi ta kawo a hankali, tace, ”Ina saurarenki”. “Amina, a zaman da kikai gidanmu na tsahon wasu shekaru, nasan zakisan halayyar kowa dake cikin gidan nan”. Tace, “Hakane” “Alhmdllh, mizan iya sani akan Qaseem da Salman?”. Shiru tai na wasu sakanni kafin ta sauke numfashi, “Duk abinda kikeson sani zan iya faɗa miki Bilkisu inhar na sanshi, wanda kuma ban sanshiba zance miki ban saniba, kimin tambaya zanfi fahimtar mikike son sani game dasu?”. Cike da gamsuwar maganarta nace, “Hakane, Qaseem da Salman suna neman mata?”................✍

Asha weekend lafiya🤫🤭😉😍👌🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

Yau ƴan wattpad sai haƙuri yaƙiyi wlhy, da ƙyarma nai copy ɗin wannan a can ɗin, amma zan cigaba da gwada muga in za'a dace😔 Bilyn Abdull 📚: Page 13

.................Shiru tai na wasu mintuna kafin tace, “Ban taɓa ganinsu da idanunaba a gado ɗaya da mace, amma tabbas Salman yakansha zuwa da ƴammata gidan idan kamar basa nan, ko kuma suna barcinsu na ƙaddara, dan akwai lokacin farkon dawowarsu da yataɓa zuwa da wata yarinyar ƙabila suka kwana a gidan, da safe ta fito zata tafi ALLAH ya haɗasu da Alhaji a bazata, koda ya tambayeta daga ina? Saita faɗa masa Salman ne ya kawota, wlhy a lokacin nazata Alhaji zaiyi kiran Salman yaymasa tatas a gaban yarinyar, ya kuma gargaɗesa sake kawo wata sai kawai naga ya sallami yarinyar ta tafi, shikuma ya shiga mota abinsa ya fita rai a ɓace, dan ko driver hanawa yay ya tuƙasa da kansa yaja mota ranar. Bilkisu bansan miyasa Alhaji keda sakaci wajen tsawatarma yaransa akan abinda ba daidaiba, ya gwammaci ya shanye ɓacin ran a ransa komin zafin da abun yay masa da kuma illarsa garesu da yazauna ya nuna musu kuskurensu, gaskiya ban taɓa ganin wanda yayma boko da rayuwar yahudu ƙazamin ruƙo irin Uncle ɗinkiba, sai dai ina tausaya masa, dan banyi tunanin waɗannan ƴaƴan nasa zasu masa addu'a ba a lokacin da ƙasa ta rufe idanunsa, sai dai dayake UBANGIJI gafurunne kuma rahimun ba'a shigar masa al'amari, ikonsane ya canjasu kosu ƙare rayuwarsu a haguggunce kamar yanda suka tashi. Qaseem kam dai bazance na taɓa ganin ya kawo mace gidan nanba, sai dai nakanji yana waya, dan kusan sau uku ko biyu inajin yana waya da ambatar sunan hotel, ba sunan hotel daya shigo ciki bane kawai yasa nai tunanin hakan, sunan mata dakan shigo a zancen nasa da salon yanda yake wayarne kawai dai ya ɗarsa mani haka. Sai kuma faɗa da naji wataran Hajiya na masa akan batun aure, take cewa ya zauna yanata shashanci a waje sai ya gama tsufa baiyi aureba, idan soyake wata ta haifa mata jika a waje sai ya bada himma. Kinga a zancenta yana nuna kenan yana yin abinda bai daceba ta kamashi ko aka kawo mata labari. Sai dai shima babu tabbas, tunda ba ido da ido nidai na gansaba. Abu na biyu kuma Qaseem baya shaye-shaye, baida wulaƙanci tamkar Hajiya, dan baya shiga huruminka sai idan kaine ka saka kanka a ciki ko wani dalili ya haɗaku, da wahala kiga yana hantarar masu aiki sai idan sun ƙuresa gaskiya, shiyyasa lokacin da kikazo gidan naga yanata biyema su Hajiya akan abinda suke miki nata mamaki, dan nasan ba halinsa bane, sai daga baya na fahimci soyayyace yake miki batare da shima ya saniba, shiyyasa baya iya yin shiru akan al'amarinki. Salman yana shaye-shaye, dan ɗakinsa ma zaki gansu zube baya shakka balle shayin kowa, sannan ɗan wulaƙancine dason yanƙwana mutum, sai dai shi kuma akwai ƙyauta, dan bashi da rowa, akwai kuma tausayi idan ƴan mutuncin na kansa bai cake ba, dan wani rashin mutuncin nasa abinda yake sha ne ke azashi bisa hanyar aikatawa. Haka rayuwa take, duk inda kika samu mutum da mugun hali zaki samesa da ƙyaƙyƙyawa kuma”. “Hakane kam Amina” na faɗa ina sake juya maganganunta a cikin raina.

Tunda na dawo gida maganganun Amina ne kawai keta kai kawo a raina, na idar da sallar la'asar ina cikin naɗe abin sallar Aunty Shahudah ta shigo, sosai nayi mamakin ganinta harma fuskata ta kasa ɓoyewa, dan tunda aka bani ɗakinta bata sake shigowaba, hasalima a wancan lokacin catai ƙyanƙyami kayan ciki take tunda na taɓasu. Sai da ta gama ƙarema ɗakin kallo sannan ta zauna a bakin gado, fuskarta wasai babu alamin turɓune wa kamar yanda takeyi da, sannan babu kallon banza balle hantara. “Oh, sai kallona kike tamkar kin samu tv Bilkisu”. Murmushin da ban shiryaba nayi, dan inaga yaune karan farko dana fara jin sunana a bakinta, nace, “Aunty Shahudah ai mamakin shigowarki nan nake, nasan dai.....” sai kuma nai shiru ban ƙarisa ba. Batace komaiba sai gefenta data nunamin da hannu alamar na zauna. Nima ban musaba na zauna ɗin inata ƙara mamakinta dai. Cikin katsemin tunani tace, “Bilkisu aiki nazo kimin, konawa kike buƙata zan biyaki”. Kallonta nai da mamaki, sai kuma na girgiza kaina, “Aunty Shahudah ni yanzu dan zaki sakani abu har sai kin biyani? Bana buƙatar ki dinga kallon haka tsakanina dake, ki sakani kominene kike da buƙ

ata a matsayinki na wacce take sama dani kuma nake ƙanwarki, nikuma nai miki alƙawarin inhar baifi ƙarfin himmata ba zan yimiki shi”. Tai guntun murmushin da ke ƙarama ƙyaƙyƙyawar fuskarta ƙyau tana jinjina kai, Tace, “Bansan haka kike da kirkiba ai, amma duk da haka zan biyaki, domin aikin ya cancanci hakan”. “Humm” kawai nace mata. Ta sake muskuta zamanta da cewar, “Waje ɗaya kuke aiki da Broth ko?”. Nasan Yah Qaseem suke cema haka, dan haka nace mata “Eh”. Tace, “Yauwa, a Station ɗinku, akwai wanda nakeson kimin aikin a kansa, sunansa Jawaad, bai zama lallai ki sanshiba, dan shi mutumne da baya shiga kowane tarkace, yanzu ɗinma sai munyi shawara da dogon nazarin da har zaki iya samun kusancin taimakon nawa a wajenshi, dan nasan bazai kulaki ba kai tsaye”. Ta ɗanso bani dariya a maganganunta, amma sai na danne banyiba, dan nima nasan gaskiya dukta faɗa akan halayyar Boss, to amma yanda take faɗan magana a habaice kuma tanason na mata aikine ya saka abin son bani dariya. Tace, “Abinda yasa na zaɓeki a aikin nan saboda, baki da surutu, sannan kin iya hausa sosai, zaki fimu sanin hanyoyin da zaki fahimtar dashi ya fahimta saboda shi mayen son yaren hausane”. Yanzunkam kasa daurewa nai sai da na murmusa, banda shirme irin nata dasu da suka ɗauki yaren wani wata tsiya, ai sai sakarai ke ƙin yarensa. “Tom aunty Shahudah, yanzu mikikeso nayi ni?”. Jim tayi alamar tunani akan abinda ke'a ranta, sai kuma zuwa can ta sauke numfashi, “Zan ringa baki saƙo kina kai masa kulum, wannan shine kawai aikinki, idan kuma ya tambayi wani abu game dani, sai kisan yanda zaki tsarashi da manya-manyan hausarnan naku. Amma dai Aamilah zata sake miki bayani yanda zaki fahimta, danni harma narasa yanda zaki sake ƙara fahimtata”. “Karki damu Aunty, ko a yanzunma na fahimceki, matsalar kawai shine yanda zan samu kusancin dashi, da har zan sako masa babbar magana data shafi rayuwarsa ne, dan kinga wannan babbar maganace data kasance sirrinsa da ya shafesa ba zancen aikiba, amma namiki alƙawarin zan gwada ta wasu hanyoyi, saiki dage da addu'a kuma”. “Okey, zuwa anjima zamu fita ni da Aamilah, zamu sayo abinda zakije masa dashi ranar Monday”. Na jinjina mata kaina kawai, dan bansan miyasa take bani tausayiba yanzu, na kula tana sonshi sosai, to ai Boss ya cancanci a soshi, sannan ita kanta ina mamakin yanda ya iya sakaci da wannan ƙyaƙyƙyawar halittar, ba namiji irinsaba hatta dani mace aunty Shahudah na birgeni, tana cikin mata ƙyawawa ajin farko da ba cikin baƙaƙeba kosu kansu fararen ta shiga cikinsu saisun yabata, sun dace sosai matsayin ma'aurata ita da Boss, ‘sai dai nikam ta yaya zan tunkaresa da maganar nan?’.

JAWAAD

Tun sanda yasha maganin sai ya dinga samun nutsuwa a hankali harya farajin ɗan ƙarfi bayan tafiyarsu bilkisu, sai kuma yaƙi da zuciya, sosai maganin na masa aiki, amma yasan wataran zai daina tamkar yanda na bayama sukai yayi suka shuɗe, ko abokinsa Doctor Sooraj ɗin da ya bashi shawarar amfani da wannan maganin ya tabbatar masa na wani ɗan lokacine kawai, babbar mafita shine yay aure, inba hakaba ƙwayoyin da yakesha domin kare kansa daga faɗawa halakar da yake gudu to lallai zasu iya masa illa ma wataran, tunda har ALLAH ya bashi lafiya da muhalli, dukiyar aure mi yakema zaman jira? Idan matarsa yakeso ya dawo da ita mana yabar cutar kansa. A lokacin da Dr Sooraj kema Jay wannan maganar ƙin ce masa uffan yay, daga ƙarshema sai yay masa sallama ya baro office ɗin.

Da daddare bayan tafiyar su Ummah gida ya samu kira daga Uncle Nasir, duk da bayajin ƙwarin jikinsa haka ya tashi ya fita bayan ya saka dogon wando a jikinsa, dan harma ya riga yay shirin barci shi. Kansa tsaye falon Uncle Nasir ya nufa, bayan yay sallama aka bashi izinin shiga sannan ya shiga, Uncle Nasir na zaune shida matarsa suna hira da kallon labarai, ya gaishesu da girmamawa. Duk fuskokinsu ɗauke da fara'a suka amsa masa, Uncle Nasir yace ya taso susha Fruit salad ɗin da yake sha, Jawaad ya amsa da, “Alhmdllh Uncle na ƙoshi”. “Aiko saika shashi” cewar Hajiya Sumayya matar Uncle Nasir, ta cigaba da faɗin,

“kai yanzu Jawaad kenan ka girmi cin abincin kowa a gidan nan?, tunda kai aure shikenan, da ai ba haka kakeyiba, mu yanzu ka yayemu daga iyayenka kenan?, inaga ko shayin wajenan rabon daka shashi tun daren ɗaurin aurenka da Shahudah, to ni dai yanzu kamar yanda na saba a baya kullum zan zubo abinci na aiko dashi sashenka, idan kaso kaita jerenshi kamar ɗakin amarya”. Murmushi yayi tare da kai hannu ya shafi kansa, yace, “Nayi laifi Ammi, amma ayi haƙuri, kinsan yanayin aikinmune yasa, wani lokacin bana shigowa da wuri, kuma ina fita da wuri, amma daga yanzun indai na dawo da wuri zanyi magana a kawo mani”. “To yanzu naji magana, bara na zuba maka fruit salad ɗin”. Uncle Nasir dake saurarensu yace, “ Ke nama lura sake ɗaure masa ƙugun zama babu aure kikeyi, yanzu ba zancen adinga kai masa abinci nai zamanyi ba, zancen wadda zata dinga dafa masa kamar kowane magidanci zanyi”. Tace, “Ah Alhaji indai nan ne aini ina bayanka, ga ƙannensa nan su Abdur-rahman za'ai musu haihuwa ta bibbiyu, shiko ya zauna ruwan ido kamar wanda bai ɗanɗana auren yajiba”. “Barsa, ai na shirya maganinsa wannan karon, idan har bai shiryaba ni a shirye nake na zaɓi ɗaya daga yaran gidanan na aura masa”. Da sauri Jay ya kalli kawun nasa harda waro idanu. “Kalleni da ƙyau fa, ALLAH inhar baka yunƙuro a cikin shekararnan ba, a yaran gidanan zan aura maka, karkuma ka ɗauka maganar wasa nake maka, gobema insha ALLAH zanje na sami Alhaji babah muyi magana (Kakansa mahaifin Mamansa), idan kuma matarka kakeso ka dawo da ita”. Shiru Jawaad yayi baice komaiba har Uncle Nasir ya gama masa faɗa sannan ya bashi haƙuri akan insha ALLAH zaiyi abinda sukeso, amma su ƙara masa lokaci. Uncle Nasir yace, “Ba damuwa, ALLAH ya kawo mafita, amma ranar lahadi idan ALLAH ya kaimu akwai meeting da za'ai ƙarfe huɗu, sai kai ƙoƙari ka halarta, karka bari ayi kuka da kai kamar ko yaushe dan ALLAH”. “Insha ALLAHU Uncle zan kiyaye”. Ya daɗe a sashen suna hira dan sai kusan ƙarfe ɗaya ya koma sashensa, kasancewar yasha barcin rana sai bai iya yin na darenba da wuri, lap-top ya buɗe ya shiga wasu ayyukan, sai wajen biyu da rabi ya rufe ya tashi, alwala yayo yay nafilfili tare da jero doguwar addu'a akan mahaifinsa da mahaifiyarsa, dama sauran al'umma baki ɗaya.

Sakamakon rashin kwanciya da wuri ya sashi makara sallar asuba, ya tashi a gaggauce ya nufi toilet ya ɗauro alwala, bayan ya gabatar da salla yay wanka ya gyara gadonsa sanan yay shirin fita, Gimba ya tafi gida weekend, dan haka shi da kansa yaja motarsa sai ƙaton gidan gonarsa da ya gada wajen mahaifinsa dake can asalin ƙauyen kakansa Alhaji Yusif, inda sukai rayuwa da kakarsa mama maryam, garin kuma da mahaifinsa yay rayuwar ƙuruciya harma data girma. Sosai an samu cigaba da abubuwa masu dama a cikin ƙauyen wanda duk sanadin mahaifinsane, an musu titi, an kuma kai musu wuta, ga dam ɗinsu da har yanzu suke noman rani, dan garin yana ɗaya daga cikin manyan garuruwan da ake amfanuwa da nomansu da kiwo a jihar tasu dama maƙwaftanta baki ɗaya. Alkairin mahaifinsa da shi kansa wanda yakeyi yasa a kullum yake mai daraja a wajensu, idan yaje ji suke tamkar su haɗiyeshi, saika rantse wani sarakine. Kamar yanda ya saba gidan mai gari ya sauka, dan haka ya keyi a duk lokacin da yaje ƙauyen, hakan na ƙara masa daraja da kwarjini, kamar yanda shima yakejin daɗin abinda suke masa ɗin, dan maigari yana masa abu tamkar uba, kasancewarsa abokine ga mahaifinsa Abdul-aziz tunna ƙuruciya. Ya samu tarba kuwa ta mutuntawa, inda akaita haba-haba dashi da abincin gargajiya masu tsafta kamar yaune aka fara ganinsa matsayin baƙo. Sam Jawaad bashi da girman kan zaɓar cima ko raina cimar ƙauye, hasalima suna masa saɗi fiye dana zamani, idan har yaje ƙauyen nan komi suka bashi cin abinsa yake, saboda yanada yaƙini akan tsaftar iyalan baba maigari, tun yana ƙanƙanin yaro mahaifinsa ke zuwa dashi, hakama mama maryam na kawosa kafin ta rasu, hankalinsa kwance yaci ya ƙoshi, dan dama da yunwarsa yazo, bayan sun gaisa da baba maigari da jama'ar dake fada suka nufi gidan gona shi da Abbati ɗan b

aba maigarin da zasuyi sa'anni da Jawaad, dan abokinsane na amana, dukkan sirrin gidan gonarsa yana hannun Abbati, shike kula da komai, Abbati dukda yayi karatu har matakin degree na biyu yana zaune ne anan ƙauyen tare da iyayensa, iyakarsa yaje birni wajen aiki ya dawo garinsu ya kwanta, matarsa ɗaya da ƴaƴa huɗu, yayi ɗan gininsa na zamani saboda ƙauyen yanzu yanada dukkan cigaban da ake hangensa a birnin, kuma mafi yawansu sunada aƙidar son zaman gida sai dai waɗanda aiki ya tilastama komawa birnin akan dole, dan a dalilin Abdul-aziz mahaifin Jawaad ƙauyen yanada manyan ƴan boko matasa masu jini a jika dake taka rawar gani sosai a sassan ƙasar. Suna tafe suna hirarsu cikin nishaɗi, inda Abbati keta kiran sauran abokansu dake gida ta waya yana sanar musu Jawaad yazo. Jawaad ya fige wayar yana hararar Abbati, “Malam ya isheka haka, sai gayyatomin ƴan iskannan kake salon kuzo ku addabeni da surutu mara ma'ana”. Abbati ya kwashe da dariya, “Oh ashe kana tsoron surutun namu? Ai indai kaga munbar maka surutu kuwa sai kayi abinda mukeso, ka dubemu daga mai yara uku sai masu huɗu amma kai ka zauna ruwan ido Jay, ai kosu Jabeer da kuke tare a birni sunada iyalansu, wai kodai da kurwanka Shahudah ta tafine bani labari kafin su Isa su zo”. Kafin Jay yay magana sukaji ance, “Ai gamu mun iso”. Daƙƙuwa Jay ya watsama abokan nasa huɗu da suka iso wajen yanzu-yanzu, waɗanda suma duk sunyi karatu kowa da abin yinsa, kuma suna bada gudunmawa a gidan gonarsa suma. “Duk kunci ƙaniyarku zomayen banza, uwarwa ya gayyatoku nan?”. Dariya suka sanya baki ɗaya, Labaran ya dunƙule hannu ya bigi damtsen hannun Jawaad yana faɗin, “Bar wani mazurai gaye, munfika ƙarfi fa inma hayaƙin kakeji, dan mu kullum matanmu ƙara mana sukeyi” duka shima Jawaad ya kai masa, Labaran yay saurin duƙewa. “Ɗan iska da ka tsaya naima fuskarka damage sai naga ƙarfin da Asiyan ke baka, mara mutunci”. Dariya suka sanya su dukansu, Aminu yace, “Mudai mun gaji da ganinka haka ALLAH kuwa”. “Gaskiyane Aminu, ya kamata ka duba Jay” cewar isa. “Hakane kam lokaci baya jira fa, kullum girma muke ƙarawa ƙuruciyarmu na guduwa” cewar Salisu dake dafe da kafaɗar Jawaad. Murmushi kawai Jawaad yayi, yasan halin abokan nasa, tunkan yay auren farkoma haka sukaita addabarsa, sai da akai bikinsa da shahudane suka sama masa lafiya, yanzunma ko waya yake dasu faɗansu kenan, shi kansa ba auren bane bayaso, gidan jiya yake tsoron komawa........ Adam ya katse masa tunani da cewar, “Idan kuma a birnin babu wadda tai maka ka duba a garin nan mana, auren nan shine cikar martabar mutum”. Abbati yace, “Maganarku nakan hanya ƴan uwa, ko ɓato maka rai akai daga waje kana shigowa gida kaga iyalanka sai kaji ka huce, musamman idan kayi dace da macen datasan yanda zata tattali dukkanin farin cikinka, koda gajiyarka ka kwaso kanada inda za'a nuna tausayinka a sauke maka ita da kulawa”. Jawaad ya shafa kansa yana sauke numfashi da girgiza kai, “Kudai baku da magana saita aure dai jarababbu, ko hutawa bakwayi, karku damu zanyi, kumin addu'a kudai. a tare suka shiga masa addu'ar kuwa kafin su fara bashi hannu suna gaisuwa. Jawaad nason abokansa na ƙauyensu, dan suna bashi nishaɗi da faɗa masa gaskiya komai ɗacinta, shiyyasa ko kansa ɗaukar zafi yay a wajen aiki tuni yake ƙoƙarin ware weekend ɗin da zai shigo, dan yasan zai samu nutsuwa sosai..............✍

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull