Kyawuna jarabta ta complete - Chapter 6
Kyawuna jarabta ta complete Chapter 6: Kyawuna jarabta ta complete Chapter 6. "oyoyo oyoyo, su maigida an iso" jin muryanta yasa dasauri Hamad yajuya washe…
4,461 words
"oyoyo oyoyo, su maigida an iso" jin muryanta yasa dasauri Hamad yajuya washe baki yayi yace "Hajiya wanan kwalliya haka, bazaki barma yara ba" dakuwa tamai tace "kaci gidanku, yanzu dani dasu idan akaje gasan kyau basai akwasheni sau dari baza'a kwashe suba" karasawa yayi har inda take sanan cikeda girmamawa yadan runtsuna yace "ina yini Hajiya" hannu tasa tashafa kanshi tace "kasha hanya Soja na maigida, jekai wanka kahuta kaida komawa kano sai gobe" tai maganan tana kallon Du'a dake bayan Hamad kanta akasa tana wasa da hijabinta kunya yahanata dago kai. "Du'a" matar takirata ahankali, ahankali Du'a kaman wacce ke tsoro tadago kanta takalli kakanta fess tagane ta danga kamanninta da Mami nan, black beauty abinta yar gayu, ganin takasa magana yasa dasauri tabude mata hannu tace "zonan zoki rungumeni, taho taho" ahankali Du'a taje dasauri tashige jikinta takankameta kankameta Hajiya tayi tace "Alhamdulillah Alhamdulillah, Du'a sannu, sannu kinji, akwai abinda ke miki ciwo"?girgizamai kakan nata kai tayi, dagota Hajiya tayi tasa hannu tai cupping face nata tana kallonta kaman yanda Du'a me kallonta ahankali rasama mezatama yarinyar tayi hakan yasa ta manna mata kiss a goshi sanan takama hannunta tarike tace "muje nakaiki dakinki kiyi wanka"
Ciki tashiga da Du'a falon wani irin hadadden gaske gashinan Duplex sai yan aiki guda biyu dataga suna gyara dinning suna ganin Du'a duk suka bitada kallo suna gaidata. "welcome Du'a" murmushi Hajiya tayi tace "kingan su suke tayani aikace aikacen gida, wanan sunanta Shema'u, dayan kuma sunanta Razika, duk sun sanki, jeki musu sallama" gabansu taje ahankali sai kallonta suke kaman basu taba ganin mutum ba, hannu tamika musu cikin muryanta mai dadi tace "Assalamu Alaykum, nice to meet you" dasauri suka karbi hannunta suna murmushi Razika tace "you are so beautiful" tsayawa tayi turus tana kallonsu Hajiya dake kallonsu tace "tell them thank u sunce kinada kyau" ahankali tace "thank u" sakinta sukayi itakuma Hajiya tasauke ijiyan zuciya sanan tace "taho mutafi" dasauri tajuyo kaman jira take dama stairs sukayi sukai sama saitaga ashema kasan baida kyau wani daki tabude dakin mai kyau sosai saiga hoton ta datana yarinya tana rarrafe kusada Hajiyan dasauri tashiga dakin tana kallon hoton, murmushi Hajiya tayi tace "lokacin kina yar tatsitsiya keda Mamanki kunzl ganin gida, little Du'a, jeki yi wanka kizo kici abinci zan baki labarin anjima" gyadamata kai tayi sanan tacire hijabi ahankali tawuce zuwa kofan datagani wanda ta tabbata bathroom ne saida tashiga sanan Hajiya tafita daga dakin.
Saida tayi wanka sanan tafito daure da towel, akwatin ta dataga anshigo dashi tabude tadauki wata doguwan riga wanda yawanci kayanta dogayen riguna ne daidaikune riga da skirt, saka rigan tayi sky blue ce mai kyau sanan tasaka hijabi salla tayi sanan tazauna tana tunanin maganan Hajiya datace tasauko, tashi tayi ahankali tacire hijabinta ta ijiye sanan tabude kofa tafito, ahankali take sauka daga stairs tana karabin gidan da kallo, daga sama sama takejin maganan Hajiya da Hamad saikuma takarasa suna ganinta sukai shiru. "kin idar tahonan" tauna mata kusada ita akan dinning hakan yasa ta taho zama tayi wajen Hajiya tace "debi abincin ki kici" dasauri Hamad yace "kafin namanta banfada mikiba kuran nama tazo gidan nan ba" turo baki tayi Hajiya ta harareshi tace "karkaga kana maigida kanemi samin jika kuka sama zamu hau nidakai, ci abinci ki kinji kome kikeso" gyadama Hajiya kai tayi sanan tadebi rice da stew da plantain da fish tanaci, bini bini Hajiya ke kallonta hartaci rabin abincin sanan tasha ruwa haka
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️M SHAKUR
EPISODE 1️⃣3️⃣ Har dare hira suke Hajiya da Hamad, kagansu zaka dauka Hamad jikan ta ne, Hajiya wata irin mace da idan kana tareda ita you have no reason or what so ever to hate her ne, kodan sabida yaranta biyu kachal aduniya saisa takeda son mutane haka oho, danta na farko yaranshi uku dukansu Maza kuma kanana dan Mami tariga shi aure yana UK achan yake aiki sai Mami dakeda yara hudu tana aure a kano, Bayan Mami ta haifi wata tarasu, Hajiya is very very educated, lawyer ce babban gaske amman yanzu tai retire saidai she's still an advocate na Human right, batun yauba taso tadauki Du'a, akwai lokacin data kusan kulle Maman Abba wato Kaka, sabida kukan da Mami tamata ne tana rokonta yasa tahakura daga lokacin tai fushi da Mami ta shareta, saisa koda wasa bata taba taka kafarta agidan Abba ba dan batada daukan nonsense and zasuga yanda zata maida yarinyar nan, Du'a tariga tabar gidan nan kenan har abada saidai in bata raye.
Ganin Du'a na gyangyadi akan kujera yasa ta tadata. "Du'a Du'a tashi kije ki kwanta adaki" ahankali ta tashi murya chan kasa tace "saida safe Grandma" murmushi tamata tace "kiyi alwala sanan kiyi addu'a kafin ki kwanta kinji" gyadamata kai tayi sanan tawuce, dakinta tabude tashiga tamaida kofan tarufe, bayi tashiga tadauro alwala kaman yanda aka umurceta sanan tafito, fadawa kan gadon tayi tana karanto addu'an bacci sanan taja bargo ta lulluba tana rufe ido fuskan mutumin nan tagani yay flashing a idanunta dasauri tabude idanunta tana yaye bargon tafito da kanta waje tanabin dakin da kallo, mutumin daya ciro ta daga rijiya she just saw fuskanshi, lumshe ido tayi ahankali still tana ganinshi saikuma ta girgixa kanta kaman tana kokarin koran abin dan bataso tana ganinshi, ahaka bacci yay awon gaba da ita......
Hajiya tashigo dakin da asuba ganin wutan dakin A kunne, karasawa gaban gadon tayi, zama tayi atabaki bakin gadon tana kallon fuskanta, Du'a is just different! ahankali takai hannunta ta kwashe gashin daya sauka a gefen fuskanta, shafa gefen fuskanta tayi tana kiranta ahankali. "Du'a, Du'a atashi daga bacci asuba tayi" bude idanunta tayi ganin kakanta yasa taji kunya murmushi tayi dasauri Hajiya tace "na tabbata yau zata yalwatu da ni'ima a gareni, wanan kayataccen murmushi dakika gaisheni dashi Du'a, Masha Allah jikata is very beautiful, barakallahu fiki, tashi kiyi alwala kizo kiyi salla kifito kuyi sallama da Hamad yashirya zai tafi" gyadamata kai tayi Sanna tasauka daga gadon ahankali bathroom tashiga itakuma Hajiya tawuce tafita.
Saida tai salla sanan tafito sanye da hijabi, a falo tagansu suna zaune Hamad na rike da mug yanashan coffee, karasowa tayi ta tsugunna ahankali tace "ina kwana Grandma" "kintashi lpy Du'a ya kwanan Abuja" murmushi tayi tace "I love here Grandma, Ya Hamad good morning" "morning dama ke nake jira zantafi" yatashi bayan ya ijiye cup dinshi, Hajiya tace "sa takalmin ki kiraka yayanki" tashi tayi tasaka slippers din da Hajiya ke nuna mata sanan tabi bayan Hamad suka fita daga falon sauka suke daga matattakala kaman daga sama yace "ya akayi kika fada rijiya Du'a" dawani irin sauri takalleshi ta tsaya batare data cigaba da tafiya ba hakan yasa shima ya tsaya yana kallonta yace "answer me" murya chan kasa tace "Muhsin din Ya Nana ne yazo" dawani irin sauri cikeda mamaki yace "Muhsin"gyadamai kai tayi tabashi labarin komi iya wanda tasani, shiru yayi saikawai yay kwafa yace "muje" binshi tayi harwajen mota, sanan ya tsaya yace "be a good girl kinji, kinga yanda rayuwanki take kasancewa awajena maza so be careful kinji" gyadamai kai tayi shafa gefen fuskanta yayi yace "wuce ki koma ciki bye" waving hannu tamai tawuce shikuma yashiga mota yatada yabar gidan bayan security yabudemai gate.
Ahankali da sallama tabude falonsu tashiga, Hajiya na zaune kan kujera tanacin fruits dake cikin bowl akan cinyanta, ganin Du'a ta shigo yasa tanuna mata gefenta tace "zoki zauna anan Du'a" murmushi tayi takaraso wajen tazauna, bowl din tanuna mata tace "zaki sha fruits"? gizgiza mata kai tayi tace "na koshi" murmushi tamata tace "karki damu nariga namiki friends sunje kano ne but maybe tsakanin yau ko gobe zasu dawo zaki gansu yanmata kaman ke zadan su girma miki but I'm sure u will like them" murmushi tayi tace "thank you Grandma" murmushi tamata sanan tace "yanzu abinda ke mind dina is school, banso kishiga secondary school dan kinyi girma saidai lessons, koda wasa bazakiyi rayuwan kullen nan dakikayi agidan ubanki ba, don't worry I will think of what to do akanki, yanzu dai zansa driver na yadauke ki Razika zata biki kije saloon ama gashin nan lafiyayyen gyara ko amiki kalba ko kitso duk wanda kikeso, sanan amiki gyaran farce right" gyadamai mata kai tayi tana murmushi, Murmushi itama Hajiya tayi tace "answer da naki stop nodding head be acting like a big girl okay" murmushi tayi sosai wanan karan tace "okay Grandma" "good girl, jeki shirya kiduba wardrobe dinki akwai kaya awajen kisa daga nan" harzata gyadamata kai saida sauri tace "Tom" wuce wa sama tayi Grandma tabita da kallo harta bace mata.
Wardrobe din dakin tabude hadaddun karyane wanda mostly abaya ne, dogayen riguna kala kala daban daban, ahankali tadaura hannunta kan wani baki fitodashi tayi daga leda tana kallon rigan kaman Grandma ta aunata shiryawa tayi cikin rigan saikuma dagudu tai wajen madubi tana kallon kanta yanda taga tayi kyau ko Nana su bata taba ganin tasaka doguwan riga mai tsada nan ba, murmushi tayi tadaura dan kwalin saman tadauki hijabinta akai tasaka tafito tasauko kasa Hajiya na ganinta tace "ina gyalen abayan Du'a" dasauri tace "nadaura akai Grandma" dan dariya Hajiya tayi saikuma ta mike tace "zokiga" karasowa gabanta tayi Hajiya ta yaye hijabin dan kwalin ta warware sanan ta gyaramata parking gashin, takalli Razika dake wajen tace "he daukomata handbag a dakinta Razika" da sauri tai sama, taimata rolling gyalen saitai kaman wata balarabiya, saukowa Razika tayi da jaka mai kyau, Hajiya ya karba tabata tace "perfect oya kutafi to driver na waje yana jiranku" takalli Razika tace "stay by her side, saikun dawo, bye Du'a" juyowa Du'a tayi tamata waving hannu alamun bye sanan suka wuce suka fita sai murna take basabamba, mota suka shiga direban yajasu.
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
Free page EPISODE 1️⃣4️⃣ Bini bini direban Hajiya dake sanye da uniform ke kallonta tamadubi, hakan yasa Razika takalleta, ganin yanda take kalle kallen hanya tana murmushin nan dake karamata wani kalan kyau nadaban yasa Razika tace "is this ur first time a Abuja Du'a?" juyowa tayi tazubama Razika mayun idanunta dakesa mutum yaji wani kwanciyan hankali harzata gyadamata kai ta tuna maganan Hajiya hakan yasa tace "eh" murmushi sosai Razika tayi tace "Abuja ai nada kyau, nima Hajiya tadaukoni daga kauyen mu takawo ni nan, sanan akwai lesson teacher dake zuwa mana karatu duk asabar da lahadi, Hajiya nason yara, kinga tunda nake a Abuja bantaba ganin yarinya mai kyau kaman keba" dan murmushi tayi saikuma tadauke kanta tamaidashi kan titi tana kallon motoci dan kunya takeji taji ance tanada kyau bamataso adinga cemata haka, ahankali tace "thank you" "yauwa munkawo" Razika tafadi ganin driver yay kwana yashiga wani babban Plaza, parking yayi hakan yasa Razika tace "sauka muje" bude kofa tayi ahankali tafito tana kallon wajen yanda akwai mutane kowa na shiga da fita abinshi, ko yanda takebin mutanen datake gani da kallo ne yasa taga suna kallonta itama oho dasauri tarike hannun Razika gam data fito tace "muje" tana rikeda hannun Razika suka wuce suka shiga wani hadadden saloon dake nan first floor, ma'aikatan suka taso suna gaidasu kafin Razika tamusu bayanin me za'amata nan aka shiga yi mata gyaran gashin.
"inje insiyomana ice cream a wanchan shagon Du'a" ta tambayi Du'a da ake wankema gashi, murya chan kasa tace "eh" tashi Razika tayi tafice daga saloon din daidai angama wanke ma Du'a tulin gashin aka nannade mata gashin da towel matar tace "tashi muje dryer" tashi tsaye tayi tawuce taje tazauna ana sliding kofan saloon din aka shigo, juyowa tayida sauri tazaci Razika ce, wani Alhaji tagani yaci babban riga milk na shadda dake kyalli da akalla zaikai 60yrs baki dashi mai kyau ga gemu kadan tareda wata mata kana ganinta kaga yar duniya ga hujin hanci akan hancinta guda uku tana rikeda jaka tana taunan cingum tana sanye dawasu kaya dabasu da maraba da babu ajikinta, suna shigowa masu aikin suka taresu. "welcome Alhaji, welcome Hajiya" gyadamusu kai yayi yanabin matan saloon din da kallo one by one, zama matar dake taredashi tayi kan kujera tawani kamo hannunshi ganin ba ita yake kalloba da sauri yajuyo yakalleta jinta kamamai hannu, kashemaai idanu tayi tace "Baby kagaya musu style din da za'a min" washe baki yayi yace "kai wlh mata kun iya rigima yanzu style ne sai an tambayani, ninasan kan style ne" kallon yar aikin dake gabansu yayi wacce ke jiran bayanin su kafin sufara aiki yadan lashe baki sanan yace "okay bari muga" juyawa yayi yacigaba da kallon yan shagon, Du'a yanuna da akema rolling gashinta a roller za'a sata a dryer yace "how about that fine baby style, Zinariya kinason style din"? yamata tambayan still yana kallon Du'a da akema gyaran gashi wacce ko kallonsu ma batayiba madubi take kallo tana kallon abinda ake mata akai wanda is new to her tabama kofa baya, ganin inda yake kallo yasa Zinariya tace "katafi meeting din dakake dashi Sweet, idan kagama saika biyo kadaukeni" tai maganan tana shafamai hannunshi still datake rikedashi, dan juyowa yayi yakalleta kaman wanda ya manta da abinda ke gabanshi yace "ohh meeting dinan, to,to bari inje, saina dawo" yay maganan yana juyawa bude kofan yayi harzai fita saikuma yadawo dasauri yawuce wajen kujeran Du'a ya tsaya tagaban wajen yana facing nata directly yakare madubin datake kallo yana murmushi yana kallonta kaman yanda takedan kallonshi atsorace yace "nace nawane kudin gyaran kan Zinariya"? Ya tambayi mai gyaran kan Du'a yana kallon Du'a kaman wani tsohon maye wanda baitaba ganin mace ba sai akan Du'a, Mai gyaran gashin Du'a dake kallonshi ne itama cikeda girmamawa tace "all payments are done to Christy Alhaji gatachan the cashier" tanunamai wacce ketare da Zinariyan shi data daure fuska tana kallonshi, yana kallon Du'a still yace "in that case ba matsala, by the way young lady ur hair is beautiful" yama Du'a magana yana wani kalan kallonta, sai alokacin Du'a tadago kanta ta kallai da kyau wanan sa''an Abban tabe hakan yasa tamai shiru, wani irin hadiye yawu yayi yana lashe baki murya chan kasa yace "bala'i Allah yayi mace anan" rasa yanda zaiyi yasa yawuce yawayance yana kallon Zinariya yace "natafi Baby" yawuce yafita ya shiga hadaddiyar jeep din da aka kawosu ciki daidai lokacin Razika na shigowa rikeda ice cream guda biyu tazo inda Du'a take tamika mata tace "gashi" hannu tasa takarba tana murmushi tace "thank u" gajeren tsaki Zinariya tasaki tadauke idanunta dagakan Du'a kishi nawani irin turnuketa kaman taje tashake yarinyar takeji tadai daure dantafi karfin karaman yarinya haka. *********
Kano! Tundaga nesa yake hango yanayin Ammin shi dake tsaye achan baya, jiyayi ranshi yabaci sosai, ahankali yakalli Sharif dake tsaye gaban kantar Max Airline yace "collect the ticket" sanan yawuce yana tafiya daidai kaman dan Sarki, yau yana sanye da native kaya dasukamai kyau ba kadan ba, farin yadi yasaka anmai dinki jumper daya zauna ajikinshi chass, kafanshi yasa wani takalmin Dior mai kyau black dakeda igiya, gashin kanshi dinan as usual looking so coily and black, idanunshi yasaka bakin shade dan baison kallo sosai sai kamshi yake zubawa, wucesu Aneesa yayi batare daya kallesu ba yakarasa inda Ammi ke tsaye tana daddanna wayanta tasanya wani hadadden abaya mai tsadan gaske, dayake tabashi baya ko kadan bataji zuwan shi ba dan hankalinta ma yayi nisa dan tunani take, zuba hannunshi yayi a aljihun wandonshi yana kallon screen din wayanta dan yafita tsawo ganin number datake kira da akai saving da Maigidana yasa murya chan kasa yace "Ammi" firgigit tadan waigo ta kalleshi saukar da wayan tayi dasauri gudun kar yaga number datake kira tace "is it time for boarding already son" shiru yayi yana kallonta, saikuma ahankali yakai hannunshi yacire glasses din idanunshi yace "Ammi baki gaji da kiran mutumin nan ba eh?" dan murmushi tayi dakana ganin murmushin kasan na damuwa ne tace "inaso na sanar dashi zamu dawo Abuja ne dama, kaga yakamata yazo yaduba mahaifinshi baida lafiya fa" cikin dan bacin rai yace " Ammi yafiki sanin mahaifinshi baida lafiya idan baizoba ki shareshi shiya sani, Ammi kidena sa kanki a damuwa, what if u fall sick eh? ina zansa kaina" tunda take maganan take kallonshi, ganin ranshi yabaci na damuwa yasa tai murmushi tace "wayagaya maka ina cikin damuwa eh, I'm fine kawai dama sabida Dadda kane nadamu, oya maida glasses dinka kafo kyau ahaka, mata sukaga this ur no nonsense eyes bazasuyi approaching dana sunce suna sonshi ba" dan murmushi yamata daya karamai wani irin kyau saka glasses din tayi tace "oya muje to, come here lemme hold ur hand asan nine maman this handsome boy" turobaki yayi yace "Ammi kindaiga akwai yara anan ko karkisa su rainani" yay maganan yawuce dasauri kafin tarikeshi zuwa wajen Sharif dakechan, binshi da kallo tayi saikuma takarasa inda su Aneesa suke tace "let's go girls gobe sai makaranta" duk dariya sukayi, Aneesa tace "Ammi kince zakicema Ya Asad ya chanza min waya in munkai" gyadamata kai Mami tayi tace "eh dukanku zansa ya chanza muku" ganin Sharif namusu waving hannu yasa Ammi tace "kumuje" wucewa sukayi saba ko 3min basuyiba sukai boarding jirginsu zuwa Abuja.
Suna sauka airport motoci biyu sukazo dukansu, shiga sukayi yayi Ammi takalli Asad dake kusada ita tace "gobe zaka fara shirye shiryen aiki ko" gyadamata kai yayi yace "eh gobe ne, illustrator dinmu Ammi yasami accident a hannunshi I don't know how am gonna start looking for new one, gawanan TV program dinan dazan fara dukshi yabatamin schedule" ahankali tace "don't worry komi zai daidaita I trust my son" harsuka karasa anguwansu, wani hadadden gida aka bude musu shiga sukayi gidan ya bala'in hadu, sassakowa sukayi Security gidan nashiga da kayansu ciki shikuma yay hanyar flat dinsu, binshi da kallo Aneesa data fito daga motansu tayi, fitowa Mariya tayi tace "yarinya kin debo ruwan dafa kanki" juyowa tayi takalli Mariyan cikeda tsiwa tace "mekike nufi?" Ammi dahartai gaba tajuyo ta kallesu tace "to bismillah tsiya zata fara ne" dasauri Aneesa tace "Ammi Mariya ke tsokana na fa" murmushi Ammi tayi tace "barta kinji Aneesa zomuje" dasauri Aneesa tabita tanama Mariyan gwalo itakuma tai dariya zata mata gwalo Rahima ta ture mata meya tace "dalla wuce mutafi" wucewa tayi tana turo mata baki sukai flat dinsu.
Hadadden Babban falo ne dayaji komi na duniya, stairs sukayi, sukai dakinsu daya hadu sosai irin dakin mata Ammi tashiga dakinta, ahankali ta ijiye handbag dinta tazauna kan gado tai shiru saikuma tamika hannunta tadauko wayanta dake cikin handbag din tai dialing number datai saving da my husband, har wayan tai ringing ta katse ba'a dagaba, sake dialing number tayi wayan na gabda tsinkewa aka dauka dasauri tace "Alhaji wanan wani kalan haline kakeyi? children are all at home, Asad is back yau kusan 5days kenan ina kiranka baka dauka what is all this Alhaji bazaka zo kaduba iyalanka ba? Eh?" muryan mace taji tawanija tsaki mtswwww..... cikin muryanta dayakedan shake da alamu bacci suke tace "dalla Malama karki sake kiran number nan kinwani hana mutane bacci, yabaki kudi yasaki gida mai kyau, aikinki shine zaman gida u are a house wife, ki kulada gidanshi da yaran kanninshi daya mutu that's ur work and leave him alone, yana nan ina kula dashi, ki ganshi nan ma bakinshi kan tsayayyun nonuwana yana tsotsa yana bacci ba irin naki ba daya koma kaman silipas" wani irin tari Ammi tashigayi batasan lokacin data yarda wayan akasa ba yafadi kuka taji tanaji but batason yaranta suji tana kuka ko su ganta jitayi duniyan tamata zafi dasauri ta tashi bude kofan dakin tayi tafita sauka kasa tayi tafice compound security na ganinta yabude mata kofa murmushi dole tamai tace "idan yarana na nemana tell them nashiga wajen Hajiya, Mamana" Gyadamata kai yayi yace "yes ma" fita daga Gate din tayi, ko tafiyan kafa goma batayiba ta tsaya gaban gate din gidan dake gaban nasu, knocking tayi security gidan yabude kofa yana ganinta yace "welcome back Ma" murmushi tayi tace "is Hajiya around" "yes she is" dasauri tashiga gidan direct kofa tabude tashiga Hajiya na zaune kan kujera tana duba wani magazine idanunta da glass sai yar aikinta dake goge TV stand, jin sallama yasa tadago kanta takalli Ammi datai sallaman, fadada murmushin fuskanta tace "Walida" ahankali muryanta narawa sosai tace "Haj.....iya" tashi Hajiya tayi dasauri ahankali takaraso gaban kofan tana kallon fuskan Ammi ganin yanda idanunta suka cicciko da hawaye yasa takama hannunta tace "muje sama" tana rikeda ita sukai sama har zuwa dakin Hajiya, shigarda ita ciki tayi sanan tamaida kofan tarufe kafin ahankali takama hannunta ta zaunar da ita kan gadonta tace "ya isa Walida ya isa" wani irin rungume Hajiya tayi gam, duk duniyan nan batada wacce tarike amatsayin uwa sai Hajiya, saisa babu abinda take boyemata, Hajiya bata hanata kukan ba saidai bubbuga mata batada takeyi ahankali tace "it's okay ya isa" tadade ahaka sanan tadago kanta, tissue Hajiya tabata fuskanta tashiga sharewa tace "Hajiya babu narasa Yaya zanyi da Baban Asad, gabaki daya baida lokacin iyalinshi, har muje kano munyi sati mudawo mutumin nan baizo yaduba mahaifinshi ba, yana nan Abuja fa amman yakauracewa gidanshi, kullum ina cikin yima yara karyane yay tafiya wanan kasan yay tafiya wanchan kasan, Hajiya Asad danshi ya tsani mahaifinshi sama da komi, kinsan bakin halin Asad koyaya naso nawanke mahaifinshi bayama yarda bama ya saurarena, nasan Asad kadai na haifa wlh Hajiya ke shaida ce anan falon ki ranan nace na yarda ya karo aure ba hanashi kara aure ba, Hajiya yaki sai bin matan banza, kince idan naje kano nabada sanarwa masallatai asashi a addu'a wlh duk nayi, baya daukan wayana yanzun nan nakirashi wata karuwanshi ce tadauka, I don't know what to do Hajiya, ina zansa raina inji dadi eh? Baban Asad yana girma yanakara tambarewa shekaranshi 60 fa yanzu".
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️M SHAKUR
Free Page EPISODE 1️⃣5️⃣ Hannu Hajiya tasa cikeda tausayinta tace "stop crying, dena kuka, ya isa" tasata ajikinta tana bubbuga bayanta tana gayamata kalamai masu sa natsuwa hartai shiru, saida ta natsu sanan Hajiya tace "bari nakawo miki abinci kici nasan is being long bakisa abinci acikin nan naki ba" batama tsaya sauraronta ba tawuce tafita, lafiyayyen tuwo takawo mata da miyan kubewa busassa da kifi da man shanu, bude kofa tayi tashigo dakin tana kallonta, maida kofan tayi tarufe takaraso ijiye tray tayi akan carpet tace "wayyo jikin tsufa, sako kici kinga kinsani aiki" murmushi tayi ahankali sanan tasauko tasan halin Hajiya hakan yasa batai gaddama ba tashiga cin tuwon sosai taci tuwon ta koshi sanan taje tawanko hannunta anayi tafito carpet din Hajiya tanuna mata hakan yasa tazo tazauna kusada ita, ahankali Hajiya tace "Walida, ke yanzu ba yarinya bace, inda ace Asad yayi aure da yanzu kinada jikoki dozen ma halan" dan murmushi tayi Hajiya tace "my point is indai rayuwan zaman aure ne you've come a long way saidai kibama wasu shawara, kunada yaro dakeda shekaru 33 aduniya aiko littafi aka baki zaki iya rubutawa kan zaman aure, Baban Asad wanan halin nashi bayau ko jiya yafara ba, kinyi kuka kinyi kuka Walida, kukan jini ne kawai yarage bakiyiba, kinsan yanayin lafiyanki, amatasayina na mahaifiya agareki dudda bani na haifeki ba abinda nafadi miki kafin kutafi kano shizan kara gayamiki ki manta da batun mijinki and concentrate akan yaranki, fi fawwalama Allah lamarin Baban Asad kidinga mishi addu'a idan yanada rabon shiriya wlh zai shiryu, kinsan yanda Asad ke sonki sama da rayuwanshi ko ciwon kai yaron nan yaga kinayi lamarin shi saiya tabarbare yaron dayakeda TV show dazai fara nan da kwana biyu, I think, kinason ya susuce ne"? Dasauri Ammi tace "a'a Hajiya" "then dole ki jajirce ki kauda komi, Alhamdulillah baihanaki ci ba baihanaki shaba, ke kodama yahanaki danki Allah ya horemai mezai dameki, ki share batun shi yanda yasa kafafunshi yafita dakanshi zaisasu kuma yadawo gidan kinji" harcikin ranta taji wani sanyi wani zubin takance inama ita yar Hajiya ce, dan Hajiya tayi arayuwa, tadauketa tamkar yar cikinta, haka tadauki yaranta tundaga su Asad da Sharif harzuwa kansu Aneesa kaman jikokinta, babu abinda abinda take iyayi bata sanar da itaba, murmushi tayi ahankali tace "Hajiya nagode, Dadda da Turai sunce na gaisheki" haba Hajiya takama tace "wanan rigimammen tsohon yanzu bai biyoku yadawo nan Abuja yadinga ganin specialist bako" dariya tayi kaman ba itane tasha kuka ba tace "ai yace shi kano yakeso, Turai natare dashi dakuma Nurse dinshi, ya samu lafiya sosai kafin mudawo ma" Hajiya tace "Masha Allah".
"Grandmaaa" Du'a data shigo falon takira Hajiya ganin bata falo, shigowa Razika dake biyeda ita tayi tace "tana sama, muje kinuna mata kalban da aka miki" dasauri Du'a tai stairs tana murmushi sosai dan kitson da aka mata yamata kyau dan ba'a taba yimata kalanshi ba, tana kaiwa falon sama takara kiranta. "Grandma" dasauri Hajiya take tareda Ammi tace "jikata tazo bangayamiki ba, Du'a gani nan adaki shigo" bude kofan dakin Grandma ahankali tayi tashigo Razika biyeda ita, ganin wata babbar mace baka tareda Grandma yasa ta tsaya batare data karaso ba, saukar da kanta tayi kasa ahankali ta gaida matar tace "ina yini" murmushi Hajiya tayi takalli Ammi tace "ana gaidake" wani kayataccen murmushi Ammi tayi tace "Masha Allah, sabida kin ganni kikaki karasowa ciki wajen Grandma dinki" dan murmushi Du'a tayi cikeda kunya ta girgixa kai saikuma tajuya dasauri tace "bye Grandma" sanan tabi ta gefen Razika tafice dasauri, dan dariya Hajiya tayi tace "kinganta haka take akwai kunya" takalli Razika tace "anmata kitson" gyadamata kai tayi tace "anyi kalba akayi, yayi kyau sosai" "haka nakeso, jeki bata abinci taci" ficewa Razika tayi, Ammi tace "Hajiya yar Muktar din UK ne" dariyan manya Hajiya tayi tace "yar Zainab din kano ce, Du'a, wacce nake baki labarinta" murmushi Ammi tayi tace "Allah sarki Yarinyar ga kyau ga natsuwa"
Saida tai wanka sanan ta chanza kaya zuwa wani gown data dauka daga wardrobe red iya guiwa ya tsaya mata yamata kyau, bata daura dankwali ba tasaki kalaban dayake nan har waist dinta kaman ansaka mata attachment tabude kofa tafito da saurinta ta sauko dan itada Razika sun biya wani super market tadauki drawing book babba da HB Pencils da eraser da colors, dakin kasa wanda shine dakin Razika da Amina ta shiga suna zaune sunacin abinci duk suka bitada kallo ganinta adakinsu, Razika ta kalla tace "ina drawing book dina"? Dan ware ido Razika tayi sanan tace "inama nasa ohh natuna suna dinning" dasaurinta harda dan gudunta tawuce tafita a dinning ta tsaya ganin komi yasa tasaki wani murmushi she's so happy and excited bayan reading novels wanda technically Ya Hamad ne yakoya mata the only thing datasan ta iya shine zane, babu abinda bata iya zanawa ba saida yawanci abinda tafi zanawa yanzu shine takalma tana bala'in son zama takalma sabida batada takalma agida dayawa dan bata fita saisa hakanan idan tazauna saita dinga zama dream shoes dinta.