Kyawuna jarabta ta complete - Chapter 8
Kyawuna jarabta ta complete Chapter 8: Kyawuna jarabta ta complete Chapter 8. Ana Magrib suka shigo gidan, dinning direct sukayi, zama sukayi Ammi na…
4,452 words
Ana Magrib suka shigo gidan, dinning direct sukayi, zama sukayi Ammi na fitowa, Sharif yace "Ammi ina yaran nan wai nisukema dariya" dan hararanshi Ammi tayi tace "toba dole suyimaka ba nan nan yaran nan suka rokeka kudi kahanasu, anyway suntafi wajen Hajiya, kasan jikan Hajiya tazo shine ita sukaje gani nace musu nai musu kawa age mate dinsu ce wai zasu cemata ta shirya suje shopping tareda ita gobe" tsaki Sharif yayi yace "Ammi bani abinci na naci nima naje naga jikan Hajiyan muga ko za'ayi ta gida ne, Ammi tanada kyau"? Hararanshi Ammi tayi tace "inkaje ka gano da idanunka" tai maganan tana bashi plate na biryani rice, karba yayi yafara ci sanan ta zubama Asad dake daddanna wayanshi kaman bashi awurin. Biryani ta zubamai sanan ta turamai gabanshi tace "ina kaje dazu Asad" dagokai yayi yakalleta spoon yadauka zai faracin abincin yace "naje nasha iska ne kawai Ammi" ture abincin Sharif yayi yamike yace "Ammi natafi" wanan karan dariya Ammi tayi tabishi da kallo fita yayi abinshi, tashi itama Ammi tayi tai sama bata wani dade ba tafito rikeda drawing book din Du'a samin shi tayi zaune inda tabarshi yanacin abinci, kujeran kusada shi taja tazauna sanan ta ijiyemai drawing book din agabanshi, Ammi yabi da kallo saikuma ya ijiye spoon din dayakecin abinci dashi yadauki drawing book din yabude yana dubawa, ahankali yakalli Ammi yace "Ammi who drew this"? murmushi Ammi tayi tace "zanen yayi kyau" dasauri yana kallon drawing din yace "this is classic, I mean the hands behind this drawings is a genius, Ammi wow, idan yanzu nabada wayan nan zanen akai bringing this shoe to life my company zai zama number show brand company in the whole Africa" murmushi sosai Ammi tayi tace "zaka bama mai zanen aiki kenan"? sai alokacin ya kalli Ammi yace "who drew it Ammi" ahankali Ammi tace "zan gayamaka, but my zanen is very dear to me nai alkawari zaka bama mai zanen aiki dudda batai makaranta ba" dasauri yace "Ammi u mean mace ce tai zanen!" gyadamai kai tayi tace "yes mace ce, but batai school ba sabida some matsaloli irin na rayuwa, but she's talented, inason kabata aiki sanan kabiyata tsakani ga Allah yanda kake biyan illustrators dinka" yatsine fuska yayi yace "Ammi kinsan qualifications din illustrators dina kuwa, how can I pay wacce bada da credentials haka is not possible ma" fizge drawing book din Ammi tayi tace "then forget it" dasauri yace "okay naji Ammi kawo" ya karbi drawing book din yana kara dubawa, Ammi tace "yanzu yaushe zata fara aiki" ahankali yace "gobe Monday, for now Sharif will handle everything dan sai next week zan koma"
wa.me/+2347012181461
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️M SHAKUR
Free page EPISODE 1️⃣ 9️⃣ Gyadamai kai Ammi tayi cikeda jin dadi tace "Allah maka albarka Asad dina" murmushi yayi yace "Ameen Ammi, but who is the girl"? kaman bazata fadamai ba tace "jikan Hajiya ce, she's 21" yatsine fuska yayi yace "Ammi ni all those children banson raini fa" hararanshi Ammi tayi tace "to Uncle Asad, ya za'ayi ma tamaka raini, jikan Hajiya ai she's just like ur sister su Mariya idan tayi badaidai ba ka gyaramata, kuma batada raini ko kadan that I know" yatsine fuska yayi irin baimasan maganan nan ahankali yace "Ammi I want coffee" tashi Ammi tayi tace "bari nahado ma tunda yaran nan duka sun gudu gidan Hajiya sun barni nikadai" kitchen tawuce tashiga....
Yau idan kaga bakin Du'a har kunne, har Rahima dake feeling tagirme su bazata iya zama friend din Du'a ba jitayi tanason Du'a sabida yarinyar akwai kyau dudda sun lura duk sun fita wayewa basu wani damuba kafin kice me cika falon Hajiya sukayi da hayaniya, suka tasa Hajiya agaba sai tabama Du'a itama kudin shopping gobe duk suka tafi tare, itama 200k tadauko tabata daman tanason takai yarinyar shopping but bata sami lokaci ba waya ma tace "gobe idan zata dawo zata taho mata da waya" duk suna cikin uban hanayinan Sharif yay sallama, dasauri Rahima tace "kinga Du'a we have two brothers, wicked and harsh, yanzu zakiga weekend one din shike mana murmushi da wasa amman shine ba'acin kwandalan shi" Hajiya dake kallonsu tace "Au haka kikace Sharif shigo kaji yanda kannenka kebata maka suna" turo kofan yayi yashigo hakan yasa Du'a itama tadaga kanta dantaga wanda ake batawa, wani kyakkyawan gayene dogo mai tsayi gashinan fari fat kaman su Rahima, tana ganinshi taga kamanninshi da Rahima da Mariya, baida kiba ko kadan, sai uban kyau ga sajenshi baki sidik dasuke nan akwance, gashin baida tarin gashi irin na Asad amman akwai gashi kadan da lowcut yakeyi ko kadan bata ganeshi ba hakan yasa kawai ta tsaya tana kallonshi daga inda take zaune kusada Hajiya dasu Rahima.
Dauke kai yayi daga kallon Du'a ganin kannenshi da kowa na wajen yace "Hajiya yanzu har gidanki suka tattaro sukazo suna gulmana yaran nan, aiko wlh zan baku kashi" yay maganan yana dunfaro su, ihu sukayi duk suka tashi suka kankame Hajiya Du'a ko sai dariya dasauri Hajiya tace "jama'a na shiga uku, wani yamikomin wayata yaga wlh Ammin ku zan kira tazo ta kwashi yaranta kutafi gida tunda neman kasheni kuke kai kuma wlh bazaka taba yaran nan agidan nan na ko kazo kazauna kokuma kawice katafi idan mugunta kazo yi nagayamaka kukuma ku dagani" Da sauri suka dagata shikuma yazo gefenta yazauna kusa da ita yay folding hannu yace "Hajiya jikanki batada kunya ita batasan yayanta yazo tagaidani ba wlh idan tace zata biyema marasa kunyan yaran nan nida ita bazamu shirya ba" yay maganan yana hararan Du'a, sosai Du'a ke murmushi ganin yanda Sharif keda ban dariya, ahankali cikin yar muryanta tace "Ya Sharif ina yini" hararanta yayi yace "lpy lau" Mariya dake gefenta tace "Ya Sharif kaga harda ita zamuje shopping din gobe tunda Ya Asad yabamu namu kai kabata nata ai itama kanwarka ne yanzu" dasauri Hajiya tace "ohh ni yasu Mari ke Mariya yaushe kika dawo scammer eh, Sharif yaran nan damfaran ka zasuyi ba yanzun nan nabama Du'a nata 200k dinba" dan sosakai Sharif yayi yace "Hajiya ni bansan ko yaran nan basuso nai aure bane, kudin aure fa nake tarawa" saikuma ya kalli Du'a yace "nasan sun riga sunce miki banda kirki I will prove them wrong, kinga ban shigo da kudi ba, but zanbama Mari gobe tabaki okay" gyadamai kai tayi tana kallonshi irin kaman bata yarda ba dinan dan ita Grandma tariga tabata kudin ta, kaman Hajiya ta lurada hakan ne yasa tace "baki cema Yayanki kingode ba" murmushi tayi ahankali tace "nagode Ya Sharif" nan fa dakin ya kachame da hira, shi Sharif baida girman kai yana shiga kannenshi yayi hira dasu sosai iyayensu dasuka rasu yasa yafara haka dan he is all dasuke dashi couple with the fact Asad baida wasa, saisa yake hira dasu yasasu dariya yasasu bakin ciki komi ba, daga karshema zamewa Du'a tayi tai bacci shoulder ta nakan jikin Rahima, sai wuraren 11 Sharif ya tarkatasu sukama Hajiya sallama suka tafi kaman karsu tafi, itakuma ta tada Du'a tawuce taje ta kwanta.
Flat dinsu ya shiga yana maida kofa yarufe sanan yashigo ciki Asad yagani zaune afalo yana kallon wani horror movie a smart TV dake falonsu, tsaki Sharif yayi danya tsani horror movie zama yayi yace "kafara kallon film din aljannun nan naka ko" dagamai gira daya Asad yayi sanan yadauki drawing book din da Ammi tabashi ya jefama Sharif din, dasauri ya chapke yace "what is this" yay maganan yana budewa, ganin wasu hadaddun zanen takalma yasa yamike tsaye yacigaba da kallon su one by one. "woooooo Asad who drew this??? Wow Wow, waye yay zanen nan eh, we need this talent a company mu wlh, who drew this Asad" dan batarai yayi yace "Ammi takawomin wai I should hire wacce tai zanen a company mu" dasauri Sharif yace "of course Asad you should hire this talent karfi all those competing companies su gano mai zanen su rigaka hiring nashi, but waye mai zanen a ina Ammi tasamo maka" tabe baki yayi yace "tace wai jikan Ammi ce mai zanen, she's a small girl 21, kuma karatun ta a JSS2 ta tsaya due to some reasons best known to them, how can someone dabaida qualification zaimin aiki eh" dasauri Sharif yace "in this case don't look at qualification look at the talent, Asad ko bature illustrator dinka baitaba zana takalma masu kalan kyau dinan ba, this is masterpiece wlh, mukai takalman nan trust me all celebrities across the globe will be rocking ur brand, yarinyar nan tun wuri without second thought kadauketa" yatsine fuska yayi yace "Ammi tariga tasa nadauketa gobe zata fara aiki" dasauri Sharif yace "gobe" dan yasan gobe zasuje shopping, gyadamai kai Asad yayi yace "yes, inaso you should handle everything, interview her kasata a office na illustrator din let her get to work, guide her, before nagama this TV program in yaso once am back sai afara work on production" gyadamai kai Sharif yayi yace "okay Asad, bari naje na kwanta, kaine night owl" yay maganan yana stairs yana murmushi da gangan yaki fadamai wacece jikan Ammi yanaso yaga reaction dinshi ranan dazaiga wacce yace to daga rijiya ce jikan Hajiya ita yabama aiki.
Wuraren 5:30 Hajiya tashigo dakinta, tadata tayi ahankali tabude idanunta tashi tayi ahankali tazauna Hajiya dake kallonta tace "guess what" bude idanunta tayi tarr tana kallon Hajiya, murmushi Hajiya tayi tace "kinsami aikin" wani irin murmushi tayi tawashe fararen hakoranta, Hajiya tace "amma ance yau zaki fara aiki, danhaka tashi kiyi salla kiyi wanka ki shirya yarinya na is now a working class young lady, my lucky jika" murmushi sosai tayi ahankali cikin muryan baccinta tace "Grandma shopping dinmu dasu Rahima fa" murmushi tayi tashafa gefen fuskanta tace "don't worry about that karfe 4 zaki tashi daga office idan kindawo sai kuje, yanzu tashi kije kiyi salla" gyadamata kai tayi ta tashi dasauri tai bayi alwala tayi tafito tai salla saida tai karatun Al Qur'ani tai addu'a Allah ya sanyama aikinta albarka sannan takoma bayi tayo wanka tafito mata shafa ta shirya cikin riga da skirt na atampa sanan tafito falo, tunda take saukowa Hajiya ke kallonta ganin yanda mahaukacin shape dinta yafito akayan yasa taji bata natsu ba, ko aikin ma data bari tayi sabida tasan Ammi da yaranta ne tasan yanda sukeda natsuwa kuma tasan zasu sa ido akan Du'a, saisa ta natsu da bata bartaba, sanan kuma tanason yarinyar takara girma tai wayau tasan ya rayuwa take outside home, kujeran dinning Hajiya taja mata hakan yasa ta zauna tace "grandma cikina namin wani iri idan natuna zani aiki" dan dariya Hajiya tayi tana zuba mata tea da Irish tace "kina feeling butterflies a ciki, it's normal, yanzu ci abinci karki latti fa, 8 ake zuwa aiki" dasauri tashiga cin bata wani ci sosai ba dan bata iyacin abinci sanan ta tashi, Hajiya tace "anya bazan sayo miki Vitamin B complex ba kuwa Du'a baki iyacin abinci, oya tashi muje sama kiga" tashi tayi sukai sama, dakinta suka shiga Hajiya tabude wardrobe dinta, wani sabon abaya taciro mata black mai mahaukacin kyau ta ijiye kan gado tace "inaso ki zama very wise girl, kinga kalan jikin da Allah yabaki dan haka bazaki dinga saka atampa haka kina zuwa aiki ba, zan karo miki hadaddun abaya masu kyau su zaki dinga sawa kina zuwa office okay, inaso idan kikaje ki natsu ba ruwanki da gulma ko surutun office respect ur senior idan kikai laifi aka miki fada take ur correction, karkiga sabida kinga Sharif ko Asad sabida kin sansu suna kaman matsayin yarana ne kidinga musu magana anyhow ko rashin kunya no, a office is strictly work and formal communication okay, ki natsu kafin ki zauna akan kujeran aikin ki da za'a baki kiyi addu'a, kullum idan kika shiga office dinki kafin kifara aiki kiyi addu'a hakan zaisa kidinga samin cigaba Allah na Buda miki, ki zama mace mai kamunkai, abinda yasa nama barki kiyi aiki sabida inaso ki sami experience ne kisan menene rayuwa dan bakisan komi kan rayuwa ba Du'a, be very smart okay, karki damu yau zan sau miki wata" gyadama Hajiya kai tayi tace "thank u Grandma" ajiye mata kayan tayi tace "oya shirya nima bari naje na shirya zan shiga office yau saina saukeki a company ku" wucewa tayi tafice, shiryawa tayi cikin doguwan rigan ita kanta saida ta kallo kanta saboda yanda tai wani kalan kyau, parking kalabanta tayi sanan tazauna kan kujeran tadau gyalen abayan tana kokarin rolling bata iyaba aka turo dakin aka shigo, Hajiya ce ta shirya cikin ubansun gown din lace rikeda waya tamikama Du'a tace "ga Mamin Ki" karba tayi takai kunnenta ahankali tace "ina kwana Mami" ajiyan zuciya taji Mamin ta tasauke tace "Du'a ya kike" murya chan kasa tace "lpy lau" murmushi Mami tayi tace "ance kinsami aiki Allah ya sanya alheri ki kulada kanki kinji" murya chan kasa tace "to" "OK bye" bye tace Mami ta katse wayan karban wayan Hajiya tayi tace "bani gyalen kiga namiki rolling" rolling Hajiya tamata tsaf, saita juya tana kallon gaban mirror hannu tasa tadauko wani pink janbaki da kwallin saka mata kwallin tayi sanan ta shafa mata Jan bakin kadan daya saje da lips dinta, kafin tadau turaruka ta fesa mata sanan tadauko wata jaka tace "idan mace zata fita most especially office haka makesure kinada pad kwata daya aciki incase of period yazo miki, sai wipes, sai lip balm, sai dan karamin turare haka dayar hoda ko madubi, pen da dankaramin jotter haka" tai maganan tana daukan komi tana samata ajakan sanan tabata jakan, karba tayi tana murmushi Hajiya tawuce tafita tace "sa takalmi ki sako" takalmi tasaka sanan tajuya takalli kanta a mirror wlh kaganta bazaka iya tantanceta da balarabiyaba tai wani irin kyau akayan, hakanan saitaga tama kanta girma tadawo wata babba kaman yar mai kudi jin Grandma ta kwalama ta kira yasa tajuya da gudu tafice.
don magana dani M Shakur chat me up by clicking on this link wa.me/+2347012181461
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
Free page EPISODE 2️⃣0️⃣ Razika da Shemau tagani a falo tsaye duk suna kallonta suna murmushi sabida tsabagen yanda tai kyau, sake washe musu baki tayi tace "natafi office" kwashe wa sa dariya sukayi sukace "adawo lpy Du'a, Allah yabada sa'a" Ameen ta amsa sanan tawuce tafita waje tana musu bye, tsakar gida tayi tana tafiya ahankali ita kanta Hajiya tsayawa tayi tana kallon Du'a to some extend bata wani cika blaming Kaka ba data dage cewa Du'a ba jikan ta bane dan wlh Du'a bata da banbanci da balarabiya ga kyau ga diri ance mutum tara yake baicika goma ba Du'a tamafi ashirin, fararen kafafunta Hajiya tabi da kallo dake kara haske bakin abayan data saka karasowa wajen tayi tace "muje grandma" murmushi tamata ta rungumo kafadan ta tace "kinyi kyau jikalle, yau kukaje shopping ki zabo takalma masu kyau da hills ba chan chan ba kinji, good shoes takes a woman to good places, takalman Du'a dina should be epic kaman cendarella koba hakaba" "hakane Grandma" tai maganan tana shiga mad jeep din Grandma, Grandma ma tashiga driver ta yajasu, hira Hajiya keta mata ganin she's a bit nervous daurewa kawai take wayaga sabon shiga, cikin wani ubansu glass building taga sun shiga mai tsawo wanda daga gani kasan akwai elevator dan sabida yanayin tsayinshi sunan company EPIC & COs LTD, parking direban Grandma yayi takalleta ganin yanda take kalle kalle tace "this is company dazaki dinga aiki aciki wuce kitafi" kallon Hajiya tayi idanunta sukai zuru zuru kaman zatai kuka tace "Grandma mezance" dariyan da Grandmaa keji ta hadiye tace "just go this is beginning of new phase, anriga an baki aikin so amsan da zuwanki idan kikaje akwai receptionist awajen ki gayamata sunanki she will tell u what to do, come here" Hajiya tama goshinta peck tace "Allah bada sa'a don't forget abubuwan dana fadamiki" gyadamata kai tayi gabanta nafaduwa sanan tabude kofan ta fita, direban grandma yajata suka wuce suka tafi suka barta tsaye awajen, haduwan ginin kadai yasa taji she's having change of mind ita daketa murna zatai aiki ita ko kadan batai picturing something like this ba irin wanan big organization dinne Ammi zata saman mata aiki ba, takai kusan 5min tsaye awajen sanan ta dage tafara tafiya towards the entrance door da kofan yay kala da kofan bank, taga yanda mutanen dake wucewa ke shiga hakan yasa itama taje, security dake wajen ne dake bada hand sanitizer ne yabita da kallo sanan yace "ur hand Miss" muka hannunta tayi aka zuba mata ta shafa yace "u can go in" shiga kofan tayi nan kawai taga glass yarufe ta ihu tayi tashiga buga glass din. "wayyooo Allah na innailaihi Grandm......" bata karasa kiranta ba taga kofan ya budu ga mutane dayawa awajen kowa na harkan gabanshi bama a lurada ita ba yasa tashare hawayen daya zubomata da sauri tashiga tana kalle kalle still ganin desk da counter da aka rubuta reception yasa tai wajen, wata hadaddiyar chic ce awajen kafinma Du'a ta isa wajen yarinyar ke kallon Du'a kaman zata hadiyeta tace "how can I help u Miss" ahankali Du'a tace "my name is Du'a Muhammad" dasauri receptionist din tace "the new illustrator, please come with me Miss Du'a" Receptionist din ta tashi tai hanyar elevator Du'a biyeda ita suka shiga, 4th floor ta danna da elevator yafara tafiya runtse ido tayi danji tayi hanjinta na neman fitowa, wani complete new section tagansu aciki saiga wata secretary dake zaune gaban system ga kujeru zaman mutane awajen, nunama Du'a kujera tayi tace "have a sir Miss Du'a" sanan takalli secretary dake kallon Du'a tace "she's the new illustrator, u take it from here" gyadamata kai tayi tawuce itakuma Du'a ta zauna tana kallon office din dake gabanta dakenan arufe jikin kofan anrubuta M.D Mr Sharif Alameen Kitse, takai kusan 1hr azaune awajen sanan aka bude kofan wasu manyan baki dake sanye da suit turawa suka fito tareda Sharif dake sanye da suit yayi wani irin kyau, binta yayi da kallo sai baice komiba yawuce yataka bakin har zuwa wajen elevator sanan suka shiga yadawo ya tsaya gaban secretary din cikeda fushi yace "tun yaushe Miss Du'a ke zaune anan Miss Amal"? dasauri matan tace "about an hour ago" "and u couldn't take her to her office" yafadi ranshi abace, tashi Miss Amal tayi tace "sorry sir I thought zaka fara ganinta ne tukunna saisa na bartaka sallami baki tukunna" cikeda takai takaici yawuce gaban Du'a yace "I apologize for that Miss Du'a, shall we" tashi tayi tana gyadamai kai yabude office dinshi yashiga tana biyeda shi sai kallon office din take yanda office din yahadu kujera yanuna mata ta zauna sanan shima yawuce ya zauna yakalleta da murmushi a fuskanshi yace "you want coffee kona kaiki cafeteria kici abinci"? Gizgizamai kai tayi ahankali cikin muryan nan nata mai bala'in dadi tace "I had breakfast thank you" cikeda gamsuwa yana kallonta yace "it's fine, anyway welcome to EPIC & COs LTD, company ne that is into creating and inventing all kind of shoes dakika sani da different materials, starting from animal skins har zuwa leather shoes, munada lots of investors da abubuwa da yawa which I believe since kina nan yanzu u will understand everything, Today is all about introduction babu abinda zakiyi gobe ne zaki fara aiki officially, that aside. My name is Sharif Al Ameen Kitse, nine MD wato managing director of this company, sorry bazaki sami daman ganin CEO dinmu ba dan he's officially on leave sai next week zai dawo, I will give u a tour around the company har zuwa warehouse dinmu dake kasa inda ake hada takalman da ire irenki ke zana mana, zan kaiki HR department zaki miki small abu za'a dauki hotonshi da some biometric dan za'a miki ID card na aiki, we have mosque we have church, rest room cafeteria duk acikin nan, and if u are having any difficulty with anything feel free to give me a call okay I'm ur brother banda haka Hajiya tace nakulan mata da jikan ta inba hakaba saitaci kaniyana" yay maganan cikeda wasa yana kallonta dan murmushi tayi itama dan sosai yanada kirki, ahankali yace "are you ready for ur tour ko kina bukatan wani abu, water juice ko cingum ko sweet kinsan mata da kwadayi remember I have sister nasanku, nabaki sweet"? yay maganan yana jawo wata yar locker shi yanuna mata, uban sweet ne na chocolate da sauransu aciki yana kallonta, kasa cemishi a'a tayi ahankali yasa ahankali tace "eh" ciko chocolate da sweet yayi a hannunshi yamika mata hannu tasa takarba ahankali tace "thank you" jakanta tabude ta zuba sanan tadauki daya tabude tasa abaki, murmushi yamata yace "let's go" gyadamai kai tayi tabishi suka fito tana biyedashi suka shiga elevator, ya danna 5th floor yace "let's start with 5th floor nanne floor na Oganmu duka, CEO anan kuma office din illustrator company yake dan haka anan office dinki yake" jin shiru yasa yajuyo yakalleta gani yayi ta kankame idanunta lips dinta na motsi, dan murmushi yayi yace "scared of elevator"? Gyadamai kai tayi ahankali daidai kofan nabudewa yafice ahankali tafito itama idanunta har sunyi ja sabida tsoro, tazaci 4th floor nada kyau dasukazo fifth floor dinnan saitaga wane 4th, ga mutane sai aikinsu suke sai gaida Sharif ake ana bin Du'a da kallo dashi kanshi Sharif saida ya lura, gaban wani office yaje dake kusada CEO dan tazaran ba yawa taga an rubuta illustration, bude kofan yay ya shiga yajuyo ya kalleta yace "come in" shigowa tayi tana bin office din dakallo table ne hadadden gaske da laptop ke kai ga kujera dake juyawa, ga dogon couch, sai frames a bango na zanen takalma masu kyau, sa shelf dawasu irin hadadden drawing book dabata taba ganinsu arayuwanta ba suke ganin su take kallo yasa, Sharif yadauko daya yace "anan zaki dinga zanen it's digital drawing book, kome kike zanawa is connection to this MacBook" yanuna mata laptop din dake kan kujeranta, yace "we can't wait for xanenki, you can keep ur bag dan nanne official office dinki" gyadamai kai tayi ahankali ta ijiye jakanta kan table sanan yakalleta yace "mucigaba kokin gaji" murmushi tamai ahankali tace "mucigaba" fita yayi tabishi wanan karan saitaga baibida ita elevator ba sun dauki stairs hakan bakaramin dadi yamata ba harsaida ya lura dansai murmushi takemai, suka tafi kowani floor yana nuna mata komi, sukaje Cafeteria company babban gaske all employees dinsu are entitle to lunch kaje za'a baka free lunch, dasafe kuma kowa is entitle to either coffee ko lip tea saisa kowa nan yake fara tsayawa dasafe ya karbi tea sanan kowa yawuce office, yakaita mosque incase tanaso tazo tai salla, yakaita warehouse, yakaita HR yana tsaye akai taking biometrics dinta aka mata passports saida tagama komi sanan suka taho abin har mamaki yadinga basu wanan tour din dayake bata ba aikinshi bane, sake komar da ita Cafeteria yayi yakalleta yace "tea or coffee"? murmushi tayi kaman mai tsoro tace "tea" sawa yayi aka hada tea a coffee aka kawo musu a disposable cup mai marfi yabata nata yana rikeda nah I yace "muje" sakebin bene yayi da ita suka tafi har 5th floor, office dinta yakaita yace "now sit round relax do anything dakikeso, if u want anything just dial my number awanan landline Din" yanuna mata telephone din wajen yace "dial 444 zaiyi connecting naki to me" gyadamai kai tayi, waving mata hannu yayi yace "bye" ahankali tace "bye" harya wuce saikuma yaleko yace "drink our tea kiji da dadi kafin yahuce" gyadamai kai tasake yi tana murmushi, wucewa yayi yatafi abinshi, zama tayi kan kujeran ta da tuntuni yake shigan mata idanu tahau wasa akai tana juye juye saikuma tamika hannu tadauki cup din tashiga shan tea aiko dadi hakan yasa tacigaba dasha tana murmushi ita kadai.
wa.me/+2347012181461
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
free page EPISODE 2️⃣1️⃣
Sosai takebin office din da kallo kaman wacce bata taba ganin office ba arayuwanta, ga katoton TV dake makale a bangon office din, gawani camera Ata sama amakalle shima dabata san koname ba, ahaka tana zaune ita kadai har lokacin azahar tayi, knocking office dinta akayi saikuma aka budo kofan, Sharif ne murmushi lullube kan fuskanshi yana kallonta batare daya shigo cikin office dinba, dan murmushi tasakinmai itama dan wani irin kunyanshi takeji ganin yanada kirki sosai, ahankali yace "is time for zuhur u wanna join me?" Gyadamai kai tayi da sauri dan tuntuni takejin fitsari dama amman kunyan tafita ita kadai takeji taje, tashi tayi ahankali tafito duk yana kallon ta sanan taja kofan office din suka wuce tare har mosque yanuna mata side din mata ta tafi, wucewa tayi bayinsu sai kallonta matan dake wajen suke itadai babu wanda take cema uppan besides ma kanta akasa dan kunyan yanda suke kallonta takeji, fitsari tayi tayo alwala sanan tashigo masallacin ganin cupboard dake cike da hijabai yasa tadauki hijabi tasaka tai salla abinta, tana idarwa ta zauna tana kokarin rolling gyalenta babu yanda batayiba takasa hakan yasa takama gyalen ta wajen wuyanta gamgam tamike tafito, jigine da bango masallacin taga Sharif yay folding hannunshi akirji da alamu ita yake jira, ganinta yasa ya yunkura yataho inda take yana kallonta yace "maiya sami gyalen"? Ahankali tace "ban iya yanda Grandma tamini ba" Dan murmushi yayi yace "then u have to learn dagayau, let's go have lunch" yay maganan yana hawa stairs yay hanyar canteen dinsu tana biyeda shi, shiga sukayi ga few employees dinsu dake wajen suna cin abinci cikeda girmamawa suka shiga gaidashi amsasu yayi batare daya kallesu ba sanan yaja kujera yanuna mata alamun ta zauna zama tayi ahankali tana kallonshi ganin yanda yake wani kulada ita kaman yar kanwarshi, shima zama yayi yakalli yarinyar datazo cikeda girmamawa tace "mezan kawo muku sir" batare daya kalleta ba yace "I want pasta da salad, mezakici Du'a" yay maganan ahankali yana kallonta, kallon yarinyar tayi sanan tace "jallof rice" juyawa yarinyar tayi ta tafi itakuma tasauke kanta kasa tana wasa da yatsunta Sharif sai kallonta yake kaman yamata magana saikuma yay shiru shima ahaka har aka kawo musu abincin, cin abincin shi yafara hakan yasa yace "bazaki ci ba" Dan dagokai tayi ta kalleshi ahankali tadau spoon tafara cin abincin, bini bini yake satan kallonta, ta bala'in yima kyau, komi nata daban ne, harya gamacin abincin shi batai rabin nata ba hakan yasa yacigaba da jiranta, kadan takara akai ta ture hakan yasa yace "u okay" gyadamai kai tayi tasha ruwa sanan ta tashi alamun su tafi tafiya sukayi har office yasake rakata sanan yawuce nashi office din, wuraren 4 tana zaune a office dinta telephone din wajen yahau kara dasauri ta dauka, muryan wani security taji.