Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 2

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 2

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 2: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 2. "Ba zaki rasa ba biftu.....sultane yayi wata irin kafewa…

3,375 words

"Ba zaki rasa ba biftu.....sultane yayi wata irin kafewa da saukeshi sai anbi a hankali,ba babban dalili ne zai sakashi sauka,ko janyewa daga bangaren hakeem takai tsaye,tunda har ya karbi dukiyar aurensu,dole sai munbi a hankali......wannan karon koda ta kama mu sanya morsa safiyya cikin lallashinsa......zan duqa mata zan kuma saukar da kaina na roqa miki haka".

"Indai alfarma ta bangarenta ce mammina banaso......" Ta fada a zafafe da tarin qiyayyar da ko sunanta bata qaunar ji.

"Biftu!" Mammina ta kira Akhnan da wani irin yanayi daya sanyata dole tayi shuru.

"Ki sauka ki nema wani abun kici,idan kin gama kizo ki sameni,akwai shawaran da zamuyi".

"Okay" Kawai ta fadi tana sauke wayar gami da katseta.

Cikin izzar nan tata take saukowa daga stairs din. Duka gidan shuru ba motsin kowa,kuma tasan hakan baya rasa nasaba da umarnin data bayar.

Ba komai saman dining kamar yadda ta buqata,bata damu ba,don dama bata jin zata iya cin komai,saita juya tana shiga kitchen da kanta,abinda ta shafe a qalla shekara biyar zuwa bakwai rabonta da yi.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Komai yana killace a kuma tsaftace cikin tsari da sanin makamar aiki. Tea kawai take da buqatar sha,amma batasan yadda zata hada ba,don haka tasan ya zame mata dole ta kira wani cikinsu birra ya hada mata,saita daga wayarta tayi kiran da duka duka na sakanni ne ta kuma yanke kiran kai tsaye ba tare data jira an daga ba.

Cikin qasa da minti biyar birra ta shigo kitchen din. Duk saita rude ganin Akhnan din tsaye cikin kitchen din. Ta qaraso da matuqar girmamawa ta rusuna tana fadin.

"Allah ya taimakeki me kike buqata?,dadai kin koma kin zauna,kome kike buqata saina kira cook din ta hada miki". Hannu tadan daga mata.

" Basai kin kirasu ba......hadamin tea kawai".

"An gama" Ta furta tana yin gaba da hanzari.

Cikin mintuna ta kammala hada mata,sannan kuma ta wuce mata dashi saman dining,ta taka a hankali ta bita a baya,ta zauna sosai birran na qoqarin saka saka mata kyakkyawan yadin da ake shimfida mata saman jikinta. Hannu ta daga mata kawai,sai birran ta maida hankalinta gurin raba mata tea din gida biyu yadda zai mata dadin sha.

Rusunawa tayi bayan ta gama tana ja da baya.

"Akwai wani abu?". Kai ta girgiza mata.

"Kina iya tafiya" Ta amsa mata tana daukan cup din tea din takai bakinta.

Wani taste da qamshi daban taji ya mata a baki,saidai taste din bawai ya canza bane sosai,don haka sai ta aza daga bakinta wanda yake da alaqa da rashin jin dadin da zuciyarta take ciki.

"Alhamdulillah" Ya furta a nutse sanda ya kammala shiryawa cikin kaftan pyjamas da ya dace da amam din kanshi daya zauna masa sosai ire iren na malaman qasar Indonesia. Sak irin shigar mazan da Indonesia,saidai kaman yadda ya saba a wasu lokutan yakan zagayo da jelar amam din kanshi ya lullube hancinsa zuwa habarsa,ba zaka iya ganin komai ba banda kyawawan zagayayyun idanunsa da kuma cikakkiyar girarshi.

Yau din ya wareta ne kawai do nufin kewayawa cikin gidan. Ya sanarwa da me wada,kuma yace ya zabi duk wanda yakeso ya tayashi tattakin cikin gidan,kai tsaye kuma yace MAHER don shine zai dace sosai da tsarin aikinsa,tunda kusan maher din yasan gurare da yawa na cikin gidan.

A nutse ya sauko,ya sani zuwa yanzu Maher bai iso gidan ba,sai ya tako a nutse yana ratsa parlor din nasa,daidai sanda muryar jibrilla hadimin da aka sake bashi yayi magana wanda baima lura dashi ba yana goge dining area.

"Ranka ya dade......me martaba ya aiko da saqo a baka idan ka sauko" Ya fadi yana duban wata farar takarda a hannunsa. Baice komai ba ya miqawa jibrilla hannu,shi kuma ya tako a hankali yana rusunawa gami da miqa masa takardar.

A nutse yaci gaba da takawa a hankali,sannan ya bude takardar yana dubawa. Minti daya kacal ya gama karantawa,sai ya nannadeta yana azata saman conceal mirror din dake daura da gurin.

Buqatar ganinsa yakeyi a kebantaccen library dinsa. Haka kawai yake ganin girman dattijon,yayin da a wasu lokuta kuma yake kallonsa kamar motii dinsa ta bangaren wasu dabi'u nasa da sukayi kamanceceniya.

Ya riga yasan kusan map na gidan gaba daya,yasan location na gurare da yawa cikin gidan. Bai taba nuna hakan ba,saboda sirranta aikinsa da kuma sirranta matsayinsa,don haka ko a yanzun daya fito a nutse,sai daya tambayi me wada direction din library din sannan ya wuce kanshi tsaye.

Sosai hanyar da zata sadaka da library din keda wani irin yanayi me daukan hankali. Guri ne dake da tarin bishiyu da suka qarawa gurin qarancin haske suka kuma sanyashi ya zama da wata irin weather ta musamman data dace da daminar dake sanyo kai da jiran umarnin rabbu don soma zubar da ruwa ga doron duniya.

Sosai yanayin gurin yayi masa,yaci gaba da takawa a hankali yana sake karanta gurin,har zuwa sanda ya isa makekiyar qofar library din.

Tun daga bakin qofar zakasan cewa lallai an tsara gurin sosai da wani irin yanayi da zai baka nutsuwar yin karatu

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 03* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________

Hadimai hudu ne ke kula da bakin qofar,wasu irin tsayyayun mutane da yanayin jikinsu kawai zai gaya maka alamun qarfi me yawa a tattare dasu,suna tsaye kyam,tahowarsa kuma ya sanya biyu daga cikinsu matsawa suka buda masa qofar suna rusunar da kawunansu qasa gami da buda masa hanya sosai.

Cikin nutsuwar shin nan yayi sallama a nutse cikin tsarrarren library din. Tun a ranar farko da bincikensa ya fada ga library din yaga tsarinta ya masa,zai kuma dace da yanayin nutsatstsen karatu.

"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Sultane dake zaune saman daya daga cikin lafiyayyun tausasan kujerun zama da aka zuba a gurin ya amsa,fuskarsa yana gauraya da murmushi.

"Maraba da sheikh muhammad" Sultane ya sake fadi yana gyara zamansa sosai,ya dubi nannie dake zaune daura dashi.

Ta jima cikin library din suna tattaunawa da sultane din,wanda duka akan abinda ya shafi auren akhnan ne. Tun daga wancan ranar daya gaya mata kada ta sake tuntubar akhnan din,sai bata sake neman nata ba,bata kuma sake magana akan komai ba. Ta sani tunda har sultane yayi magana akai akwai wani dalilin nasa. Mahaifinta ne,ya fita sanin d'iyarshi,tasan tabbas akwai dalilin da ya sanya yace kada ta sake bari maganan ya shiga tsakaninta da alkhnan.

"Ga yaro na Fatimatou" Sultane ya furta yana murmushi gami da miqa hannuwa haisam dake takowa gurin.

Murmushi nannie ta saki tana duban haisam din. Ba ranar da zama zai hadata da sultane bai bata labarin haisam ba,mamaki take kullum na yadda ya shiga ranshi haka farat daya,to amma itama a yau nata mamakin ya ragu duba daya data masa. Akwai wani irin cikakken nutsuwa da kamun kai tattare da shi,uwa uba tana hangen kwarjini me yawa a tare dashi da wani irin haske da ita kanta batasan na meye ba.

"Ba shakka,yau naga muhammad haisam" Ta fadi tana girgiza kai har yanzu idanunta a kansa sanda yake zama daura sultane din.

Cikin girmamawa suka gaisa da sultane,ya juya akalar gaisuwar tasa ga nannie wadda shekarunta suka kusa na nanay dinsa.

Cikin kulawa sa wata qaunar haisam din ta amsa masa. Godiya ta masa me yawa game da kula da karatunsu falaak da kuma amincewa ya zama mashawarci ga sultane din,sannan ta miqe.

"Bari na bawa uba da d'ansa guri ko?" Tayi maganan tan dariya gami da gyara lullubinta.

Murmushi sultane yayi,yakanji kamar duk wani matsala na rashin samun magajin d'a namiji ta yaye masa a duk sanda ya tuna da haisam,a duk sanda haisam yake gefansa.

"A fito lafiya" Ta sake fadi tana rusunawa sultane din cikin nuna girmamawar data saba gareshi tun daga quruciya kawo yanzu.

"Allah yasa" Ya amsa mata shima cikin kulawa.

Shuru gurin ya danyi bayan ficewar nannie,sai ya gyara zamansa sultane din yana matso da farantin dake cike da kayan marmari gaban haisam din.

"Allah yasa ba ayyukanka na katse maka ba......baka kwana da sanin zan nemeka ba ka tashi da hakan" Kai ya girgiza a nutse,fuskarsa adan sake ba yadda ta saba kasancewa ba.

"Ba wani damuwa a cikin hakan".

"Bismillah mana" Sultane ya fada yana masa nuni da fruit din. Baice masa komai ba,ya miqa hannu ya dauki fruit din,ya riqe a hannunsa ba tare da yaci ba.

Ya lura kaman akwai maganar da sultane din yakeso yayi dashi,amma kuma kamar tana masa nauyin fadi,wannan ya sanyashi ya gyara zamansa kadan yana fadin.

"Ina fatan ba wani matsala ko damuwa bace?". Murmushi ya kuma saki yana girgiza kai.

"Ko daya......shawara ce nake da buqatarta" Sai ya miqe ya zauna sosai.

"Gami da bayi maza da mata dake cikin gidan nan.......akwai hade haden auren da nake buqata nayi.....inason shawara kan zamansu a cikin gidan,dukkaninsu sun balaga sunkai munzali,morsa safiyya tana aiwatar da wannan tsarin ga hadiman bangarenta". Kai haisam ya jinjina,kima da darajar sultane tana qaruwa a idanunsa. Gefe guda matar daya ambata din,ya yabawa girman hasashenta da hankalinta. Mace kamar ita har tayi wannan tunanin,ta kuma dinga aiwatarwa da dukka qwarin gwiwarta da qoqarinta?. Sunan nata sai ya maida tunaninsa baya,kamar dai itace wadda ta sanya oustaze Ousmane kawoshi a madadinsa......sannan kamar itace mace ta biyu a gurin sultane din indai bai manta ba,indai kuma lissafinsa ya bashi daidai.

Tunaninsa da fatansa dukka masu kyau ne,yana da tsananin hangen nasa da kuma qoqarin kare haqqin musulunci,sai ya maida apple din inda ya daukota ya hade tafukan hannunsa guri guda.

"Akwai tarin kuskure da sabawa addini akan ajiye bayi ko hadimai ko 'yan aiki maza da mata cikin gida ba tare da aurar dasu ba ko kuma duba buqatunsu na dan adam ba.......akwai tarin tuhumar cikar nagartar dukkan wanda ya aikata wannan....." Kai sosai sultane ya girgiza cikin gamsuwa.

"Abu mafi kyau shine......a basu dama kowa ya zabi wanda yakeso,a kuma aurar dasu kaman yadda musulunci ya tanada"

"In sha Allah" Sultane ya fadi yana jinjina kai,zuciyarsa girman haisam da qaunarsa suna sake samun gurin zama.

Yana yiwa mutanensa da yawa kwarjini,kwarjinin da ya sanya malaman dake tare dashi ba kowanne lokaci suke bashi shawarar da zata dace da shinda ya kamata ayi ba. Yafi buqatar jin gaskiya a bakunansu fiye da su gaya masa abinda rai da zuciyarsa sukeson ji,amma ba kasafai suke iyayin hakan ba,saidai ya hango wannan qualities din tattare da haisam din.

Shuru ya sake wanzuwa a tsakani,har yanzu haisam yana ganin akwai wani magana ta daban da sultane yakeso yayi cikin idanu da bakinsa......sai ya sauke idanunsa yana maidawa ga littattafan dake gefansa cikin nazarin wadanne iri ne.

★A hankali ta hadiye tea na qarshe data kurba,ta kuma dire cup din saman table din tana jin yadda wata kasala da mutuwar jiki take saukar mata lokaci guda. Idonta ta lumshe sannan ta budesu lokaci guda,a hankali ta dafa table din ta miqe ta fara sauka daga gurin tana jin yadda kasalar take bin jikinta.

Ta alaqanta hakan da yunwar data tarawa cikinta na kwana da kwanaki,yanzun kuma ruwan zafin da tasha ne qila yake sauka a jikinta yana sake mata gabobinta. Wayar hannunta ta daga tana duban lokaci,bata manta ba mammina nason ganinta,kuma kiran mammina din abune me matuqar muhimmanci a gareta. Tana buqatar taje,don tana neman duk wani hanya da dabara da zai sanya sultane ya janye daga qudurinsa,banda haka a yanayin kasalar da takeji ba abinda take buqata irin ta koma samanta ta kwanta ta huta,ta kuma qara bacci,ta tabbatar awa daya zuwa biyu zata tashi fresh.

Saman takeso ta koma,amma sai taji ba zata iya hawa stairs din ba,don haka ta matsa na'urar dake kusa da ita,ba jimawa birra ta qaraso a gaggauce.

"Zan fita gurin mammina.......shiga ki samomin abu mafi kusa dake da zan lullube kaina" Ta qarasa maganan a kasalance. Cikin girmamawa ta amsa ta kuma haura saman da azama,ba jimawa ta sauko da wata Riga.

Gabanta a hude yake,tana zubi da alkyabba don hade take da hular da zaka saye kanka dama fuskarta gaba daya,tana da dogon hannu bata da nauyi kwata kwata,saidai ita tsahonta gaba dayanshi bai qarasa har qasa ba.

Baya kawai ta juyawa birra din,ita kuma ta qaraso cikin girmamawa da kulawa ta zira mata,akhnan din ta sanya hannu ta rufa hular a kanta sannna ta fara tattaki don ficewa daga sassan.

"Zan iya yi miki rakiya?" Birra ya fada tana sadda kanta qasa,kai kawai akhnan din ta kada mata alamun bata buqata sannan taci gaba da takawa tana ficewa.

Iska sosai ta zuqa sanda ta fara takawa a farfajiyar da zata zame mata kamar ragin hanya,yadda zata bulle sassan mammina ta hanyar mahadar data hada library din sultane da kuma shiyyar mammina din.

Tanason hanyar,saboda tafiya a hanyar yana tuna mata abubuwa masu yawan gaske,tafiya a hanyar yana tuna mata rayuwarta a France,lokacin karatunta da wasu lokuta takejin kewar da takan sanyata siyan ticket ta koma qasan tasha iska na satittika sannan ta dawo. Hanya ce da ba wani zirga zirgar mutane,duk wanda ka gani a area din amitacce ne,sannan kuma akwai abinda ya kaishi ta gurin. Library din sultane ne kawai a gurin,sai dakunan ajiyar kayayyaki na musamman na sultane mammina da morsa safiyya,sai akayi masa gurin hutawa kebantaccce,da kuma hanyoyin da zasu iya sadashi da hanyar da zata bulla dashi sassan kowacce cikin matan nasa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A hankali take takawa da salon tafiyar nan tana me matuqar jan hankali,saidai a yau din tafiyar ta kasance da wani irin yauqi saboda kasalar dake ci gaba da saukar mata,har tana jin kamar qafafunta ma sundan fara nauyi,hakanan wayar hannunta taji dama ta barta a sassanta bata fito da ita ba. Ba kowa kuma ta gurin ballantana ta bashi wayar ya maida mata,hakanan dai tayi ta maza taci gaba da riqon wayar a hannunta tana kuma ratsa guri..

"Idan ba damuwa ina iya tafiya?" Haisam ya buqata yana duban sultane cikin girmamawa,ganin bai sake cewa komai ba,ga kuma saqon da abdii ya aiko masa kan maher yana jiransa.

Murmushi ya saki yana jinjina kai.

"Kana iya tafiyarka muhammad,ina fatan kuma ba zaka gajiya ba a duk sanda na sake kiranka".

"In sha Allah" Ya amsa masa a nutse sannan ya miqe,cikin girmamawa sultane shima ya miqe,a jikinsa yakejin haisam din abun girmamawa ne.

"Na gode qwarai da gaske da sadaukarmin da lokacinka da kayi" Sultane ya fadi. Sosai haisam yakejin godiyar sultane din tayi girma a gareshi,saidai kuma baice komai ba ya fara takawa sultane din yana masa tattaki har bakin library din.

A nutse yasa hannu ya sauke yankin daya lullube bakinsa zuwa hancinsa yana sheqar iska sosai yana aikata hunhunsa gami da ci gaba da takwa da qasaitaccen takun nan nashi. Har yanzu idanunsa na hango masa magana kwance a idanun sultane......to wacce magana ce?,wacce damuwa ce haka data masa nauyin daya gaza fadi.

Bai kammala aje zaren wannan tunanin ba yaji kamar an wafci hankalinsa da kalaman.

"Bakka kana bane eenyuuf hin hayyaminaa........Sanduuqa sana irraa fagaachuu hin dagatinaa........Sun lubbuu kee balaaf saaxiluu dagachuu.....Ajaja Mammina ti" Wata irin jarumta yayi gurin riqe kansa,y kuma kame hankalinsa da nutsuwarsa da barin waiwayawa zuwa ga inda maganar take fitowa.

Dukkan wani reaction da zaiyi zai nuna cewa eh yaji yaren oromo......yaji kuma wani abu da yaja hankalinsa,wanda baya fatan hakan ya faru.

Yarensa sirrinsa ne......reaction dinsa akan komai makaminsa ne. Yaren oromo cikakke yakeji......da wasu nauyayan saqo daga bakin bayin nan guda biyu. Dayan ya fahimci fuskarsa TAMIM na farko daya fara gani maqale jikin window din sultane......saidai bai samu nasarar ganin fuskar mutum na biyu ba,don ya bada baya yana kuma bada umarni da zafi zafi da alaman bacin rai akan bude gurin daya fahimci wani store dinne.

"Kada kabar kowa ya sake bude gurinnan......kada ka manta,kayi qoqarin nesanta kanka da akwatinnan.......manta hakan yana daidai da sanya rayuwarka cikin hatsari......umarnin mammina ne wannan" Ya maimaita maganganun cikin kansa yana kuma sake tisasu yadda zasu zauna a gurbin da yake buqatar su zauna din,har yanzu kuma idanunsa suna kallon qasa,saidai idanun hankali dana zuciyarsa suna tare dasu sanda ya sanya hannu yana rufe gurin suka kuma taka suna barin gurin da sautin magana qasa qasa da baya iya jin abinda suke fadi.

Lallai bai shakka gidan sarautar agadez itace TA DAYA da zarginsu zai fada a kai......kuma itace ta farko daya kamata hankalinsu ya koma kai. A yau yaji yaren oromo gaba daya da irin karin harshen da yake tabbatar masa OROMIA ne koma waye yayi wannan maganan,dashi din dame sauraronsa.

Cikin mamaki ta damqe hannuwanta da taji yatsunta sun fara rawa kamar wadanda aka kama ake sarqesu cikin na juna,tadan sunkuyar da kanta tana duban yadda yatsun nata sukaci gaba da motsawa da hanzari hanzari. Mamaki ya kamata tana jin yadda idanunta suka soma mata nauyi,kamar sunkuyar da kan nata data yine bai musu daidai ba suke yunqurin fadowa daga gurbinsu zuwa qasa,wannan ya sanya daga kanta da sauri,a wannan karon kuma ba inda idanun nata suka sauka sai a kanshi.

Bibbiyu bibbiyu idanunta suke gani kafin su fara nuna mata blurry (dishi dishi). Amma duk da hakan idanunta basu gaza sauka sosai kuma fes cikin fuskarsa ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 04* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________

Zagayen idanunsa take ta qoqarin tsaida idanunta tare da kwatantasu da wadannan idanuwan.....wannan idanun da suka zame mata barazana a hippodrome......wadannan idanun da suka zama barazana ga zaman lafiyar baccinta.......wadannan idanun da babu wani dare da zai mamaye sararin subhana......ta kwanta da zummar bacci ba tare da sun farmaki baccin nata ba.

Wannan qamshin.......wannan turaren shine abu na biyu daya dinga tasowa tun daga tazarar dake tsakaninsu yana yin kyakkyawar ajiya cikin hancinta. Kaman zata shide saboda yadda takejin qofofin iskarta suna rufewa suna raguwa daya bayan daya,amma hakan bai hanata shaqo qamshin da kyau ba,abinda ya sake dawo mata da hoton hippodrome cikin idanuwanta kenan fes.

Nutsuwarsa dake bayyane muraran saman fuskarsa,da takunsa dake cike da wata ajiyayyar qasaita ne taji yana qona zuciyarta dake wani irin matsewa a qirjinta,kamar ana saka hannu ana barazanar takureta guri daya. A yau gangar jikinta dama zuciyarta gaba daya suna sake bata tabbacin shine.......daidai sanda yake ci gaba da takowa cikin kame ganinsa da kuma shagala da al'amuran da suka shafeshi kadai,da zare kai daga cikin al'amuran da basu kasance damuwarsa bane. Wani irin sanyi taji yana ratsa kowanne sashe na jikinta,amma taqi baiwa hakan hankalinta,tafi tattara hankalinta a kansa. Har yanzu bai dago idanunsa ko sau daya ba ballantana ya kalleta,har yanxu bai dubi sashen da take ba ballanta ta samu nasarar aika masa da saqon data binne cikin idanunta.

Wani irin ninkuwa gudun zuciyarta yayi,abinda ya fara barazanar daukewar numfashinta sanda haisam din yake dab da ita,abinda ya bata daman sake kallon qwayoyin idanunsa......irin kallon da ake kira na tsaf da tsaf......kallon daya tabbatar mata SHINE ABOKIN KARAWARTA NA WANCAN RANA.

Readers Also Read

More by Huguma