Kenza eBookz
Cover art for Lu'u Lu'u Book 3 page 3

Post

Lu'u Lu'u Book 3 page 3

.....remember ten or twenty. She accepted it and drank it, then it went down as she wished, she went in to take a bath, then she asked for food which she sat down and ate very much without distinguishing between its flavors. She is fighting because she needs a lot of energy around her. She knows... where the achievement has already been achieved..... she knows, her body is missing, there are many black faces living in the house... there are a lot of shadows that have entered the dark walls of the house, they live their lives and hunt her without knowing it, but who is it..... but why does she assure herself where this olive tree is.... where is the tree, then she puts regret in the heart of everyone who laughs at her in her plan... her life is long gone her dream. SHIEKH MUHAMMAD HAISAM is the name that is lying in her mind... one name is like a test for her. She sleeps with him.....she wakes up with him.......with all the plans of how she will deal with him, so that no other teacher will enter the kingdom of AGADEZ and say he will live.....

Standalone post2,037 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 03*

"Na gode" Ya furta yana kuma qoqarin shutting down system din.

"Salaana ya fito da mota" Haisam ya fadi yana qarashe kasheta ba tare daya dubi omar da yakeson yayi tambayoyi wa haisam din ba.

*M A M M I N A*

_"Kwanciya ba taki bace zaituna........ki tashi zaituna.......ki tashi ki nuna ma koma waye da yake wasa da rayuwarsa cewa yana kutsawa sansanin mutuwa ne yana yin wasa da ajalinsa......ki tashi zaituna kada ginin nan na shekaru masu yawa da kika jima kina yi ya fado ya danneki.....ki tashi zaituna!!!.....kada ki bari akhnan ta fahimci komai.....kada ki bata qofar da zatayi nisa dake da burikanki ba tare da sun kammala cika ba"_

Ire iren wadannan maganganun sune abinda taji zuciyarta na rad'a mata har cikin kunnenta a sanda take kwance da tarin zazzabin da ya dinga kadata kamar zata datse harshenta da haqoranta.

Wani irin wuf tayi ta tashi.......ta kuma buqaci maganin da zai warkar mata da zafin zazzabin cikin mintuna goma ko ashirin. Ta karba ta kuma sha,sannan kuma ya sauka kamar yadda tayi buri,ta shiga tayi wanka,sannan ta buqaci abinci wanda ta zauna ta cishi sosai ba tare da tana banbance d'and'anonsa ba. Tana cine kawai saboda tana buqatar energy sosai a tattare da ita,tana cine saboda tana buqatar aga confidence da cikakken karsashin nan da aka santa dashi,tanaso ta fito a giwarta sak,batasan komai nata ya nuna karaya ko rauni.

Ta sani......indai cimmawa ne an riga da an cimmata.....ta sani,jikinta kuma yana bata akwai tarin baqin fuskar dake rayuwa cikin gidan.....akwai tarin inuwoyin da suka saje da duhun katangun gidan,suke rayuwarsu suna kuma farautarta ba tare data san hakan ba,saidai koma waye.....koma meye tana bawa kanta tabbacin indai itace wannan zaituna din.......indai itace zeenatu to sai ta sanya nadama a zuciyar dukkan wanda yayi gigin ketawa ta cikin shirin ta......rayuwarta dama dadadden burinta.

SHIEKH MUHAMMAD HAISAM sunan da yake kwance a ranta......sunan daya zame mata tamkar wani jarrabawa. Dashi take kwana.....dashi take tashi.......tare da dukka tsare tsaren yadda zatayi dashi,ta yadda ba wani malami da zai sake mararin shigowar masarautar AGADEZ yace zai rayu ba tare da amincewarta da samun dama da dukkanin goyon baya daga gareta ba.

"Ki aika saima....ta duba cikin bangaren suturu mafi zama alfarma ta bani daya" Tayi maganar da d'aya daga cikin hadiman da ita ke biyewa yalwa a matsayi a gurinta. Har hadimar ta fice idanunta yana kallon sashe daya,lissafinta akan toshewar kowacce qofa da zata bada makama akan batan yalwa takeyi. Ba yalwa ba dalilinta,saidai ba wani abu da zai alamtawa kowa b'ata yalwan tayi,b'atan nata yabar tarin hujjojin da duk wanda ya kalla zaice yalwa ta zabi ta tafi da qafafunta bawai da sunan b'ata ba.

Ta sani......ta kuma tabbatar da cewa. Bata yadda za'ayi yalwa ta zabi tafiya daga gareta,bata yadda za'a yi yalwa ta zabi tafiya daga masarautar agadez. Tafiyar yalwa din wani SHIRYAYYEN ABU NE da mutane irinta ne kadai zasu gane hakan.

Tsaf ta shirya cikin ire iren shigar dake nuna zallar alfarma alfahari da kuma izzar da takejin tana da ita. Ba kwanaki ko shekaru qalilan ba........a dukka tsahon shekarun data kwashe qasar agadez ta samu wani irin girma da ba wata halittar diya mace data sameta. Girmamawa da tarin darajtawar da ita ta nemeta.......ita ta siyeta.......ita kuma take tattalinta har kawo yanzun da takejin ba wani.....ba kuma wani abu daya isa ya rabata da wannan izzar tata,izzar da itace MAKAMINTA izzar da takejin zatayi dukkanin me yuwuwa gurin adanata da kyau har zuwa sanda numfashinta zaibar gangar jikinta.

"Ina fatan akhnan na cikin gida?". Kai ta gyada mata cikin maqurar ban girman nan da suka saba bata.

" Eh tabbas.......ance ta fita zuwa dakin karatun me martaba"

"Dakin karatu kuma?" Mammina tayi tambayar tana zubewa hadimar tata idanu.

"Eh Allah ya baki yawan rai" Shuru ya ratsa kadan,mammina din tana juya zoben dake yatsar hannunta. Wani abu ne yake harbawa cikin kanta da saurin gaske yana sake nauyayawa da kuma zurfafa tunaninta.

Zuwa dakin karatu baya cikin dabi'a ko al'adar akhnan din kaf tsahon rayuwar data raineta a kai,idan dan zamanta dashi ne fa?......idan dan kebancewar da tayi dashi ne wanda duka duka idan aka lissafesu guri daya ba zasu haura kwanaki biyar ba fa?. Hakan na nufin zai zamemata wani sabon aikin kenan wajen kawo qarshen alaqarsu da aurensu?. Ya kamata ta bari irin hakan yaci gaba da wanzuwa?,har takai sun fara musayar wasu dabi'u a tsakaninsu ita dashi?.

"Inason magana da ita.....zan isa zuwa dakin karatun inaso kuma kowa ya sani"

"An gama" Ta fada cikin girmamawa ta juya ta ficewa.

A yau fitar tata ta zama cikin salon da takanyi amfani dashi lokuta da dama. Wata irin tafiya tsakanin sassanta zuwa dakin karatun sultane din. A kowanne taku da zata gamu da bayi ko hadiman gidan kyauta ce take yinta. Kyautar kudade ga duk wanda suka hadu a hanya dashi. Wannan salon yana daya daga cikin wani hanya data bata daman mallakar zuciyar mutane da yawa dake rayuwa cikin masarautar,alkhairinta kuma ya danne na kowa........sai d'ai d'aikun da har a lokacin alkhairin nata ya gaza saya mata matsugunni a ransu ba tare da suma sunsan dalili ba.

*_SHEIKH MUHAMMAD HAISAM_*

Cikin lafiyayyar motar Mercedes Maybach S_class suke tafiya zuwa killataccen gidan dake cike da tarin tsaro. Killataccen gidan da almaz ya dade a cikinsa.......JINJIRI da har yanzu baida cikakken suna kuma D'A ga ajani ya zama cikon na biyun.

Yana zaune d'ai d'ai saman lausassar kujerun alfarmar da motar ta mallaka,yayi relaxing sosai cikin kujerar,dukkanin idanunsa a lumshe suke qasa qasa,zaka iya dauka bacci ne yake shirin saceshi. Sau uku omar yana daga idanu yana dubansa,sai ya bari ba tare da yace dashi komai ba. Iya yanayinsa kadai ya gaya masa 'yan miskilancinne suka motsa,dukkan alamu sun nuna bayason magana me zurfi....kaman yadda yake ganin alamun akwai wani kwantaccen fushi qasan ranshi.

Tafiyar kusan awa daya ce cif ta kaisu unguwar,unguwar dake a wani muhalli da ba kowa yake samun sukunin zama a gurin ba. Unguwa ce ta masu hannu da shuni dake cikin garin agadez qwarai da gaske,wannan ya sanya unguwar keda wani irin security sosai.

A hankali omar ya dafe Bluetooth din dake kunnensa sanda suke fitowa daga cikin motar suna dosar ainihin cikin gidan.

"Ina captain?,na gaza samunsa a waya" Maleek ya fada cikin yaren oromo. Saida omar ya saci kallon haisam kadan,yadda yake takawa d'ai da wannan ginshirar tasa sannan ya maida dubansa

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Kabi captain a hankali,abubuwanne yau suka motsa......da alama kaman a kusa yake,na kasa gane meye haka me girma da nauyi daya taba ransa".

"Please omar.......ka fada masa"

"Nooo maleek......ba'a irin wannan lokacin ba"

"When?" Maleek ya tambaya cikin sarewa. Kaman omar zai saki dariya sai ya daure.

"Inde falaak ce na tabbatar haisam bazai bari ka rasata ba,tunda ya tabbatar kana sonta"

"I trust you......"

"Kaman yadda nayi trusting Captain namu....." Omar ya amsawa maleek yana yanke kiran da dan hanzari ganin suna dab da shiga ainihin qofar farko da zata sadaka da sassannin gidan

Gaba kadan omar ya qara yana daidaita tafiyarsa data haisam din,sannan ya sanya key din hannunsa ya murza ya bude qofar.

Qawataccen parlor ne da aka yiwa wani sassanyan tsari me daukan hankali. Daga cikin parlor din ba kowa sai mutum uku,sheikh Ousmane ahmad(almaz),sai jinjiri dake zaune saman daya daga cikin lausasan darduman dake shimfide a qasan gurin.

Idanun haisam a kansu su dukkaninsu,yayi sallama da muryarnan tasa ma'abociyar kwarjini,sallamar data ratsasu dukkaninsu suka kuma daga kai suna kallonsa.

Da murmushinsa ya taso,Ahmad almaz,wanda dukkanin kamanninsa suka juye zuwa na wani kamilin matashi wanda ainihin kamanninsa na ba'abzine mallakin qasar agadez ta fara tsatsowa. Wani irin kamala da bata da alaqa kota kusa kota nesa da wancan ALMAZ din,wancan almaz din da zaituna ta sassaqashi da kalar tunaninta da cutatarwarta.

Yana sanye cikin ainihin kayan gargajiya na agadez,wanda hakan ya taimaka qwarai wajen sake bayyana kamanninsa da mahaifin sultane wato kakansa. Wata irin boyayyar kama da me nazari zai saurin daukota daga fuskar almaz din.

Cikin girmamawa da nutsuwa ya rusuna yakewa sheikh haisam barka da zuwa. Haisam din ya amsa yana duban fuskar almaz din. Ba abinda yake dawo masa sai wahalar da sukaci kafin su maida almaz din cikin hayyacinsa. Ba abinda yake tunawa sai ranar da sakamakon gwajin DNA na almaz ya fito,wanda ya sake wanke masa kokwanton da yayi saura a ransa na kasancewarsa jinin SULTANE MUHAMMAD HAMMUD. Ba abinda yake sake tunawa sai yadda almaz din ya birkice a sannan,kuka wiwi.....yana iya tuna kalaman daya gaya masa a sannan.

"Ba ragontaka sam a tattare da d'a namiji......d'a namijin ma daya amsa sunan YARIMA kuma sarkin gobe.......idan wannan yariman yayi kuka yau.....a gobe mai zai gayawa mutanensa game da JARUMTA?" Yanayin yadda maganan tayi tasiri nan da nan a zuciyar ahmad ya sanya haisam lumshe idanunsa a hankali,ba shakka akwai wani burbushi ko kuma ace jinin sarauta sosai dake zagayawa cikin jikinsa.

Idanunsa ya daga yana dorawa akan JINJIRI da yaketa tunanin bashi suna. Ba nasabarsa kawai suka datse ba......ba rabashi da mahaifiyarsa kawai sukayi ba......ba nonon dake kasancewa abinci ga kowacce sabuwar haihuwa suka haramta masa ba. Aah......daidai da SUNA sun kasa bashi.....RAI kawai suka bar masa,amma sun kashe dukkanin rayuwarsa gaba daya.

Murmushi kadan ya saki,Shima ya taso a nutse zuwa gurin haisam din. Cikin nutsuwar da yake gani tun ranar farko tattare dashi ya soma gaidashi. Shi din SAK jinin AJANI.....yana diban kamanni qwarai da wasu daga cikin 'yan uwansa wadanda kamannin ajani suka dauko. Baida shakka tantama ko kokwanto akan sahihancin zamansa halastaccen dan ajani saboda komai nasa ya nuna hakan.

Hannu ya miqa masa kai tsaye,miqa hannun daya lura cewa ya yiwa jinjiri nauyi har sai daya kalli tattausan farin tafin hannun haisam sannan ya maida dubansa ga idanunsa.

"Karbi mu gaisa......muhammad......daga yau zaka amsa sunan muhammad" Wani abu ya gani sosai cikin idanunsa,wani irin rauni da laushi,kaman ma hawaye ne kwance cikin idanun nasa. Sanda tafukan hannunsa suka hadu dana haisam sai ya kasa boye abinda ke cikin ransa.

"Tunda na tashi a jikina nakejin wannan rayuwar ba tawa bace,tunda na tashi na tabbatar akwai wani boyayyen abu cikin rayuwata,a jikina nakejin ni dinnan bani bane,ina dadewa cikin tunani,ina jimawa cikin nazarin da bansan wanda zai fahimtar dani ba,bansan fuskar kowa ba sai ta matar da tamim dana kwashe shekaru ina ganinsu tare tun tasowata......tun daga ranar dana fada hannunka na fara jin kamar sabon ruhi dama gangar jiki ka bani.....muhammad.....sunan yayimin dadi.....kaman wani suna ne me girma ko?" Ya qarasa maganan yana danyin murmushin da yafi kama da yaqe,idanunsa akan fuskar haisam.

Har cikin jininsa yaji wani abu ya zarta masa,sunan annabi guda......annabin da sunansa......jarumtarsa......shahararsa da mu'ujizarsa ta zagaya ko ina,amma yau sai ga wani diyan da aka Haifa cikin musulunci da sunnar annabin baida koda labarin sunan annabinsa?.

Sai da yaja iska sosai yakaita har hunhunsa sannan ya fesar,yayi qoqarin daidaita nutsuwarsa yana dafa jinjiri da ya zama muhammad ajani a yanzu.

"Ba rayuwarka bace wannan.......ka kuma fita kenan a cikinta" Yayi maganan yana jin shima tasa zuciyar tana wani irin tsagewa. Wato har gwara ahmad almaz kenan?,wato har gwara gwara shi?. Shi sun barshi yaci gaba da shaqar iskar rayuwa da cakuda da mutane,duk kuwa da cewa iskar gurbatacciya ce......gurbayacciyar iska ce dake cutarwa gami da naqasa dukkanin wani gaba ta dan adam......amma muhammad fa?,sun kasheshi ne ba tare da sun zare numfashinsa daga ruhinsa ba,amma dukkanin wani kisa na ma'ana sunyi masa shi. Sun watsar dashi ne kawai yana rayuwa irin rayuwar dabba,wadda batasan komai ba sai abincinta. Ba asali......ba suna.....ba makomar rayuwa......ibada da addini duka babu ko daya.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽