Kenza eBookz
Cover art for Lu'u Lu'u Book 3 page 5

Post

Lu'u Lu'u Book 3 page 5

..... I can't answer your question..... because everything came from the hands of Sheikh Muhammad, why was everything taken away and put into his, I don't know the name of the coffee". Shuru was quiet and reading the situation of Birra. Birra slowly opened the book, and every paragraph that came to her was full of points His grandfather asked him to marry Falaak, but since he had finished his lunch, everything was heavy for him and he raised his head and his face was lying in surprise, he did not want to come.

Standalone post1,681 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 05*

Lokaci na farko mahaukaciyar tsanar da takewa yarinyar ta taso mata. Karom farko da wannan tsumammiyar tsanar ta yunquro daga muhallin da taketa ajiyarta ta kafa sabbin rassa da sansani......saidai wani qaqqarfan sashe na zuciyarta yana sake jaddada mata.

"BA YANZU BA......DA SAURAN LOKACI" Da gaske ne......ta yadda da sauran lokaci......don ba zata taba yadda yarinyar taci bulus ba.......FANSAR SAFEENA da kuma rainon data yiwa MAQIYIYA na wadannan shekaru dukka saita fanshe......komai runtsi,komai tsanani......kuma komai wahala.

"Basai kin biyo ni ba" Tace da tafisu kai tsaye tana juyawa zuwa hanyar da zata sadata da sassan sultane.

A nutse ta shanye tea din da takejin d'an d'anonsa ya canza sama da wanda ta saba sha. Ya mata wani irin dadi da har sai datace da birra dake shirin juyawa ta bata guri.

"Wanne irin kaya kukayi amfani dashi a coffee dinnan?" Murmushi kadan birra ta sauke,sannan ta rusunar da idanunta.

"Yaukam bazan iya amsa tambayarki ba.....saboda komai ya fito daga hannun sheikh muhammad ne,yasa an kwashe komai an zuba nasa,bansan sunan coffee din ba". Shuru ta danyi kadan tana kuma karantar yanayin birra qasa qasa.

"Shugaba ne.....me kulawa da dukka wani nauyin dake kansa" Wata zuciyar ta rada mata maganar.

"Amma hakan shine tabbacin ya cancanci samun kusanci da zuciyarki da rayuwarki?" Ta yiwa kanta tambayar da amsarta ta tsaya cak cikin iska tana lilo.

Tana jin ficewa birra,a hankali ta bude littafin tana ci gaba da karantawa,wanda dukkan wani sakin layi da zatazo sai ya aje mata points da abubuwa masu tarin yawa.

*_S U L T A N E_*

Cikin kasala ya sauke numfashi cikin qawataccen dakin hutawar tasa,ya lumshe idanunsa sannan ya budesu duka lokaci guda. Ya rasa dalilin daya sanya yakejin irin wannan kasalar me qarfin gaske haka a jikinsa cikin satin gaba daya. Kamar dai yanzu,fita yakeso yayi,yana da zaman fada da kuma tattaunawa da wazeer dama yayan kakan morsa safiyya akan auren falaak da yace masa anje nema ta hannunsa,amma tunda ya kammala cin abincin rana komai yayi masa nauyi.

A nutse ya daga kansa da fuskarsa dake kwance da mamakin wanda ya fado masa daki haka,ba neman iso ko izini,mamakinsa ya sake fadada sanda idanunsa suka sauka akan fuskar zaituna.

Cikin qarfin hali ya tashi daga kashingidar da yayi ya zauna sosai yana dubanta,kallon da yake matan ya sanya gargadi me qarfin gaske qwacewa zuwa gareta.

Kuka kawai ta saki,kukan da take da tabbacin yana da tasiri matuqa ga sultane din,kukan data tabbatar yana daya daga cikin abinda ke saurin karya mata shi.

"Subhanallah......zaituna....ke da kanki?" Ya fadi yana daga mata hannu yana kiranta cike da mamakin abinda ya sanyata kuka.

Batayi qasa a gwiwa ba ta qaraso gabansa tana zubewa,hannunta saman fuskarta kaman qaramar yarinyar tana danne hawayen dake zuba mata.

Wannan hawayen ba fake bane......wannan hawayen bana qarya bane,hawaye ne na gaske,baqinciki da d'acin da taji a sanda ake shaida mata Akhnan bata da lokacin ganinta da saurararta da kuma ganawa da ita......shi ya cushe mata mafitar numfashinta.

"Bansan bani da kima daraja ko martaba ba sai yanxu......bansan cewa bankai naci darajar kasancewata matarka ba......bansan wanne tozarci aka shiryayimin ba ba tare da kunya da kuma tuna cewa ni dimma UWA ce ba koda ban haifa ba.....ni din MATARKA ce ba sai a yau" Ta fada tana sake narkewa da kuka. Ba bakinsa kawai ba,shi idanunsa ma a yanzu nauyinsu yakeji,baida wani sauran energy da zai dogon jayayya ko magana da zaituna. Ya sani wasu lokutan tana da rigimar da bata da tushe,don haka ko a yanzu sai yayi saving energy dinsa ya zuba mata idanu yana jiran ta bashi cikakken bayanin abinda ya faru daya sanyata zubda hawaye haka kamar qaramar yarinya.

"Yanzu lalacewata da tozartar da aka shirya yimin har takai ni da kaina saina nemi izinin ganin biftu?,har takai bani da ikon ganinta?" Ta fada tana nuna kanta da yatsarta wasu sabbin hawayen suna zuba mata.

Da zaki daina kukan da nafi fahimtarki zaituna" Sultane ya fadi yana jin yadda qafafunsa da hannayensa suke sake yin sanyi.

Ta fahimci da gaske fuskantarta yakeson yi din,kuma tana fatan fahimtar tasa ta zame.mata tsani da zata soma girgiza iko da isar da sheikh muhammad yake hangen ya samu. Gyara zama tayi sosai gabansa,saidai har yanzu bata har hawaye ba,duk da yadda takejin zazzabin dake jikinta yana shirin dawo mata.

"Naje da zummae duba lafiyar akhnan cikin dakin karatunka......amma hadiman da aka sauya dake kula da muhimman sashe dama biftu suka gayamin sheikh haisam bai bada wannan damar ga kowa ba sai mutum biyu......ashe bana cikin mutane masu muhimmancin da sune zasu fadi wadanda ke da ikon ganin biftu ma bawai iya kadai ganinta ba?" Ta fadi muryarta tana rawa sosai.

Idanu sosai sultane ya zuba mata,yana kallon yadda take hawaye daya bayan daya. Baice da ita komai ba,sai daya bata tazarar lokaci sannan ya sake daidaita zamansa.

"Zaituna" Ya kirata dakasalalliyar murya da kasalar da yake jinta har jininsa.

"A yau a kuma yanzu haisam ya fimu iko da biftu.......a musulunce haisam yana da ikon iyakance adadin mutanen da yakeso biftu tayi hulda dasu suma suyi hulda da ita.....bai sabawa addini ba......"

"Hardani uwarta?.yatsa ni uwarta dana raineta?" Tayi tambayar cike da zallar mamaki tana nuna kanta da yatsa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Koda ni da nake mahaifinta a yanzu ya fini iko da ita" Sultane ya fada cikin nutsatsen muryar nan tasa mai cike da kamala. Saidai maimakon kamalar ta sanyata fahimtar ainihin gaskiyar maganar sultane......sai maganan ya zame mata tamkar wani baqar magana ce daban sultane yake gaya mata.

"Kanason gayamin ni ba mahaifiyarta bace ta asali?,kanaso ka tunamin abinda na riga dana sanshi?.......burin morsa safiyya na dab da cika kenan?" Ta fada cikin yanayin son tada hankali,domin kuwa dama take nema....qofa take nema da zata ja hankalin sultane ya rusa wannan tsarin,ta kuma samu daman isa ga akhnan kaman yadda ta saba don ida ginin tsari da manufarta. Shuru sultane din yayi yana dubanta jikinsa na sake mutuwa da kasala,shurun da yayi ya bata daman gama fadin abinda take da niyyar fada sannan ya soma magana a nutse

"Jahiltar maganata bazai qareki da komai ba zaituna sai bacin rai.....da kyakkyawar niyya da manufa me kyau ya kamata ki kalli maganata.......ina miki bayanin nan ne badon na amintar dake ba,sai don na baki haske. A irin abinda akhnan ta fuskanta..........farmaki daga mutum mafi kusanci da aminci daga cikin masarautar mahaifinta......bazai zama abun mamaki ba don mijinta ya killaceta daga kowa ciki harda ke,ba kuma da manufar yana tuhumarki bane ko zarginki.......aah.....qilan yayi hakanne don ya sama mata nutsuwa da dawowa hayyacinta daga firgicin data fada" Ya qarasa maganar yana nazarinta. Shuru tayi,shurun kuma da bai masa kama da shurun wanda ya gamsu da maganar da aka gaya masa ba.

"Me ya tashi hankalinki haka zaituna?" Sultane ya samu kansa da qare mata kallo gami da jefa mata tambayar,tambayar data zowa mammina da wani irin bazata,bazatar data sanyata daga kanta da sauri ta kalleshi,sai kuma ta buge da sharar qwalla.

"Abubuwa da yawa sultane,ina tsoron kada a gina qauracewa juna tsakanin ni da ita.....diyatace......ina jinta a matsayin diyar da ni Allah bai bani ba,sai ya wanken zuciya.......ya kuma bani madadi da biftu din". Kai ya gyada a hankali.

"Inde hakanne ki kwantar da hankalinki,akhnan zata cimmaki har sassanki ba tare da kin daga hankalinki ba"

Kai take kadawa a hankali,yadda take kada kan a zahiri zaka dauka ta gamsu ne,zaka sauka fahimta tayi,saidai abinda yake zuciyarta......abinda ke cikin SAQAR RANTA daban yake da abinda kai kake hangowa.

"Na fahimta,Allah ya saka da alkhairi" Kawai ta fadi,ta kuma zabi ta miqe.

Idanunsa ya lumshe yana furta.

"Madalla" Ba tare daya iya dubanta da kyau ba saboda yadda jikinsa yake sakeyin rauni.

"Lokaci yayi......abubuwa sunata tabarbarewa.......abubuwa suna sake lalacewa........lokaci yayi sultane..........ya kamata na samu sarari......ya kamata komai ya qare" Abinda take fada kenan cikin ranta. Tana jin zuwa yanzu ya kamata yasan makomarsa shima.......tana jin zuwa yanzu tayi shekarun da ba wani d'a namiji data taba yi dashi.....komai izzarsa.....komai kudinsa.....kuma komai sarautarsa.......tana jin an kawo gaba.....an kuma kawo gargarar da shima ya kamata ya soma fuskantar makomarsa.

"Me kika yanke?,wane mataki kike nufin dauka akan wannan abun?" Tafisu dake biye da ita a baya ta fadi qasa qasa hankalinta gaba daya yana kan mammina.

Wani murmushi tayi,bawai don ta daina jin dacin abun a bakinta da zuciyarta ba.....bawai don abun ya bata farinciki ba,aah......saidon ta tabbatar ita zaituna tafi qarfin kasancewa cikin qasqantaccen yanayi irin wannan jar abada.

"Lokaci yayi tafisu da sultane shima zai d'an d'ani WACE ZAITUNA kamar yadda sauran na baya wuka dandana......ya isa haka,na masa kara da yawa tafisu,lokacina ne yanzun tunda har ya fara aza matsayi da isar wasu gaba da tawa". Wani irin shuru me kaifi ya gifta kafin tafisu tace.

"Me kenan ranki ya dade....?"

"Ya kamata sultane ya kwanta.....ya kwanta ya huta,ya kwanta kwanciyar da zata zarce dashi har makwancin nasa na gaskiya". Maganar saita qare da wani irin shuru me wani irin kaifin gaske,tafisu ta motsa bakinta zatayi magana,amma sautin muryar hadiman dake zaune cikin wata rumfar da aka katange da bamboo wood ya ratso har inda suke.

"A villa road ne.......nima dana taho daga kasuwa tun daga nesa na hangi hayaqi"

"Kai kaga wutar da takeci kuwa?......me martaba bai sani ba,an jima ba'ayi mummunar gobara irin wannan ba a agadez,kuma abun mamakin gida daya ne yakeci da wutar"

"Wutar nan anya haka kawai ta sauka?,lokaci guda gidan ya koma kamar burbusashen biscuit?" Dayan ya sake fadi.

*Akhnasaim tales*🤍

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽