Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 15
Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 15: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 15. "Babu ruwanki da kallonsa kiyi abinda ya kaiki maza tashi…
3,171 words
"Babu ruwanki da kallonsa kiyi abinda ya kaiki maza tashi ki tafi dan ki samu ki dawo da wuri “numfashi ta sauke” gsky aunty bazanje yanzu ba “ya fad’a tana wasa da yatsun hannunta “sai yaushe zaki?maryama tayi shiru ta kasa mgn “da dai kin daure tunda kinga baki da lokaci sai asabar da ladidi tsaki maryama taja kana tace “wallahi ban san dalili ba hakan nan najin fad’uwar gaba kuma dai yau bana son zuwa koina “aunty ta numfasa tace “to shikenan Kiyi zamanki muje kiyi wanka ki karya ki sha maganin ciwon kai ta mike ta fito wanka tayi ta shirya ta karya aunty ta bata magani ta sha tayi kwanciyarta akan kujera .”
Ahankali ta rufe idanunta lokaci d’aya kwakwalu warta ta bud’e tunani ya kusantota yaki barinta ta huta duk da bata son tayi tunani akan matsalarta amman haka tunani ya mamayeta , ahankali ta dinga tunanin maganganun yusif ,me yasa zaki damu kanki maryama already kin rigada kin yarda kin rasa yusif har abada kamata yayi kin haka rami ki binne komai ya zama tahiri arayuwarki” zanyi haka zan cire komai araina kuma zan dage da addua har na samu nasara arayuwata ahankali tabi shawarar zuciyarta ta haka rami mai zurfi aciki zuciyarta ta binne duk wata matsalarta .”
tun daga wannan ranar maryama ta cire tunani da damuwar komai acikin ranta ta toshe kunnenta duk abinda ke faruwa aciki gidan tana ji kuma tana gani amman ta share sannna taki bari mahaifiyarta tasan halin da’ake ciki yayinda kullum sai aunty ta sheida mata sakon kiran aunty fati har sanda sati ta cika aunty ta matsa mata lallai taje taji dalilin kiran da take mata “Allah aunty bana son zuwa duk sanda kika fad’a min sakonta gabana faduwa yake “kiyi hakuri ki daure kije bana son tazo gidan nan “ta fad’a muryarta a raunane ganin yanayin aunty yasa ta riko hannunta “shikenan aunty zani bari na sauya kaya naje yanzu na dawo .”
“Yauwa princess maza tashi kije Allah ya tsare min Ke “Ameen !ta furta a tsanake ta fito ahankali take taku har fito titin unguwarsu ta mike zuwa captor road tana gama garasawa bakin titi ta samu adaidai mai zuwa unguwarsu aunty fati tafiya kad'an suka yi ta sauka pencilima ta mikawa mai adaidaita kudi ta ta tsallako hannunta na hagu inda zai shigar daita amawo ."a natse ta shiga gidan kai tsaye bangaren aunty fati ta nufa bakinta dauke da sallama ta shiga parlour'n inda ta iske muktar da aunty fati zaune ." Rike da remut tana qoqarin canza tasha a tare suka kallo kofar tare da amsa sallama .”
tun daga kasa muktar ya dauki kallon maryama ransa nayi masa dadi wani irin yanayi ya tsinci kanshi ciki mai wuyar misaltuwa yana jin yadda soyayyarta ke fixgarsa yayinda maryama ta had'e fuska sosai tmkr taga wani mugun abu ta qarasa ta tsugunna har kasa ta gaishe da aunty fati ,aunty fati ta amsa mata fuskarta a d'an sake wanda hakan ya dan bawa maryama mamaki domin tunda suke daita kyara da hantara tattare da zagi né a tsakaninsu ."
Maryama ta dauke kanta tare da mikewa tsaye ta zauna tana jiran taji dalilin nemanta da aunty fati take "ke maryama baki ga muktar bane da bazaki iya bud'e ki gaishesa ba ko shi kike jira ya gaisheki ? "murmushi ya saki yana cewa"Kinsan ‘yan boko ba dai girman kai ba " wani kallon takaici maryama tayi masa daga sama har kasa wanda yasa ma kasa cigaba da magana illa ya zuba mata kwala kwalan idanusnhi masu firgitarwa ."sama da awa daya tana zaune tana wasa da yatsun hannunta sannan aunty fati ta gyara zama ta kira sunanta .”
"maryama !
muryarta a raunane ta amsa da “na’am !"na kiraki né domin na samu labari wannan yaron yusif ya canzaki da shukura yanzu ita zai aura shine muktar yace abashi ke tunda kowa gudnki yake kinga kenan shi zai taimaka ya aureki sai yanzu na na gane dashi kika dace ba da sauran mazan da suke zuwa neman aurenki suna guduwa , d'ago idanunta tayi ta zubawa aunty fati tana kallonta gabanta na dukan tara tara sannan ta waiga ta kalli inda muktar din yake yana kallonta kamar tsohon maye ."
"Karki dauka ya rasa wacce zai aura ne yasa zai aureki aa tausayi kika bashi domin yaji babu dadi aransa , yanzu me kika gani zaki auresa ko kuwa zaki tsaya jiran masu kudin da basamu zakiyi ba ?ta tambayeta tana gyara zamanta tare da tsareta da idanunta "parlour'n ya dauki shiru na kusan mintuna goma batare da maryama tace uhm ba bare uhmm illa nazari maganar aunty fati da take da kuma tunani amsar da zata bata domin dai a halin yanzu wannan shine labari mafi muni daya kusanto rayuwarta muktar fa ? "ke nake sauraro !?"
Murayarta can kasa ta soma magana a tsanake "a zahirin gasky ni ina da wanda nake só kuma wanda a shirye yake da aurena idan da hali zaa iya bashi kaulat ko Islam ,ko kuma sakina amman ni dai gsky ayi min hakuri akwai wanda muka tsaida magana dashi ."ta tsinci kanta da fad’ar haka ba dan akwai din ba sai dan tsiratar da rayuwata daga shiga maseefa”waye shi kuma a ina yake ?"maryama tayi shiru ta kasa magana hankalinta idan yayi dubu tô a tashe yake tayi datasani zuwa gidan amman tasan ko bata zo wannna maseefar sai ta biyota har gida "
“ke banson iskanci banza bayan nasan babu kowa a kasa shine zaki ce kina da wanda zaki aura tô ke nake son ya aura ,oh a zuwan kinfi karfin aurensa shine kika lissafo min daidai shi ko ?"ko d'aya aunty a dai bashi cikinsu shine zai samar da kwanciyar hankali "bata son wata fitina ta kuma lura kamar fitinar ce take bibiyarta arayuwarta, ran a aunty fati a matukar bace tace "d'an ma Kinsamu zai taimaka miki maza tashi ki bani waje na sallameki sannan ki fara shirin aurensa dan dolenki ki auresa"
Jiki a sanyaye maryama ta mike hankalinta a matukar tashe bazata ki dan shaye shaye ba dan mahaifinta ma har ya bar duniya yana sha babu komai acikin rayuwarsu sai matsala ita me kai ta saka rayuwarta cikin ha'ula'i ?kuma tasan idan ba tsanarta da aunty fati tayi ba babu yadda zaa yi tace ta auri d’anta domin ko ita take da diya kamarta tayi imani bazata dauketa ta bawa muktar aure ba mutumin da idan yayi shaye shayensa har kwata yake fadawa haka maryama ta koma gida tana cika tana batsewa duk ranta a dagule ."
Aunty ce ta fito daga kitchen tace "lafiya kuwa naga har kin dawo yanzu ?hawaye maryama ta share tace" aunty laifin me nayi da allah ya qaddaroni cikin wannan dangin ?basa sona basa qaunar cigabanna idan akwai wacce suka tsana a duniya tô nice suna jin kamr su kasheni wallahi suzo su kasheni su huta da muguwar tsanar da suka min na rasa me nayi masu arayuwar nan da suka tsane ni."aunty ta zauna kusa daita jikinta na rawa tace "me ya faru maryama ?"na gaji da wannan rayuwar aunty fati so take ta kasheni dan Allah ku barta ta kasheni ni yanzu nafi bukatar mutuwa da rayuwata akan dai ta hadani da muktar .”ta qarasa maganar tana kuka .”
“kwantar da hankalinki kiyi min bayani da kyau ban fahimceki ba ta hadaki da muktar kamar ya ?" "Wai ya aureni !"numafashi aunty ta sauke cikin rarrashi tace "haba maryama ki daina daga hankalinki tunda ga maganar yusif nasan baba gali zai yi mata bayanin komai maryama ta fashe da wani sabon kuka dan ta ta’bo mata wani ciwo ne data binne "babu wannna auren bilkisu .”muryar umma suka jiyo daga bakin kofa aunty ta juya da sauri qirjinta na bugawa fiyye da kaida ummah ta gyada mata kai "haka né abinda kikaji na fada shima an canza masa tunani har ma dana iyayensa ahankali ta tako ta dafa kafandan aunty dake kallonta a tsorace cikin tsananin tashin hankali ."
“Ummah ban gane ba me kike qoqarin fad’a min ?“abinda kika ji shi na fad’a miki balkisu yusif ya koma wajen shukura “inna lillahi wa inna ilahi rajiun shi kawai tayita fad’a tana maimatawa nan da nan yanayinta ya sauya ta zauna shiru taji duk wani kuzari na jikinta yayi kasa tsawon mintuna talatin sannan ta bud’e bakinta da kyar tace “shima yusif din ya koma wajensu "Ki kwantar da hankalinki babu abinda allah bazai iya ba kuma in sha allahu allah zai kai maryama matakin da ba'a só allah yasa hakan shine mafi zama alkhairi arayuwarta ummah ta zauna ta dinga tausar aunty da maryama tana bata baki har aunty ta saki ranta sai dai hawaye yaki tsayawa umma ta qara da tabbatar masu duk runtse maryama bazata auri muktar ba “
Maryama ta rungume ummah ajiknta “na gode umma dan allah karki bari a aura min shi wallahi na hakura da auren ma har abada “bazaki hakura da aure ba akan wani dalili domin duk dan sunah baya gudun aure yadda akayi aure aka haifeki in sha allahu kema zakiyi aure har ma da ya’ya da jikoki ummah ta fad’a tana shafa bayanta suna cikin wannan hali habib ya shigo aunty tayi sauri ta goge hawayenta tana daidaita natsuwarta ganinsu haka ya fahimci akwai damuwa dan haka da hanzari ya qaraso ya riko hannun aunty cikin nashi yana tmbyarta “lafiya na ganku haka ?babu komai aunty ta basu amsa “ya babu komai ?ya kalli ummah fuskasa dauke da tambaya .”
“Me yasa zaku boye masa yana da kyau ya sani ko babu komai zai taya yaruwarsa addua nan ummah ta fad’a masa komai “shiyasa nace ta hakura da batun wani aure ,bafa dole sai mutun yayi aure zai shiga aljanna ba “kul kar na sake jin ka fad’a haka zatayi aure musa aranmu dukkaninsu babu mijin aurenta acikinsu mu godewa allah da yasa har tana masu sonta baa barta haka ba babu abinda zai zo da bazai wuce ba wata sai labari ahankali ummah ta shawo kansu suka shiga wata hirar ,”
******
Kwanakin dari kenan da auren su maryam wanda yayi daidai da kwanakin sabain da tarewar maryam a gidan ata acikin lokacin babu wani abu da yayi sauki acikin zaman auren mai dadi a tsakanin maryam da ata duk abinda maryam zatayi domin ta cire kiyayyarta a zuciyar ata tayi amman ko a jikinsa domin dai yaki sakewa daita ."shiyasa damuwarta ta qaru zamansu babu wani shaawa dan ata yaki rungumar marym sai ma kyma da nuna ko in kula ."
Sosai motocin jami'an tsaro guda hud'u dake gaba da bayan motar da ata ke zaune aciki ke falfala gudu akan titi kamar suna gasar tsare baka jin komai sai jiniya mai tsanani domin a kauce abasu hanya sosai motocin dake Kan titi suka dinga komawa gefe suna basu hanya wanda adaidai wannan lokacin maryam na can tsaye acikin kitchen tana kwashe abinci tana zubawa a kuloli ."
Bayan ta gama ta jerasu akan table duk abinda take cikin hanzari take yi kar oga ata ya shigo bata gama ba duk da ba abincinta yake ci ba sai maakatan gidan ke ciki kuma idan tayi lattin ganawa yaci ubanta ,qarar jiniya taji alamar dawowarsa dan zaro ido tayi tare da daga kai ta kalli agogon dake manne a parlour'n karfe takwas da minti ashirin cikin sauri ta haye sama ta shiga dakinta wanda ya sha gyara gwanin burgewa. ta cire kayan jikinta ta daura towel sannan ta nufi bayi ."
Cikin jin isa ya turo kofar parlour'n tare da shigowa babu kowa a parlour'n jakar dake hannunsa ya ajiye akan kujera da wayoyinsa sannan ya nufi sama yayinda zuwa wannan lokacin maryam ta fito tana tsaye a gaban madubi tana shafa lip's dinta byn ta gama ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka can zuciyarta ta bata umarnin ta saka marasa nauyi tun sanda ta tare a gidan tsawon sati tara kenan atamfa da dogayen riguna take sakawa ta sanya kaya marasa nauyi masu yanayi dana bacci yana tsaye a dakin yaji an turo kofa bai juyo ba ."
cike da faraa ta tsaya a gabansa tana cewa "oyoyo baby sannu da zuwa "wani kallo yayi mata a dage yana sake tamke fuska tmkr yaga wani mugun abu cike da sanyin jiki ta kallesa ganin yadda yayi mata kallon kaskanci "leave my side “ya fad'a yana nuna mata kofar fita yayi maganr cikin bacin rai bata wani damu ba tunda idan da sabo ta saba da halinsa "ga abinci "bana ci kina tunanin zanci abinncikin ne ko me ?”kayi hakuri please kaci ko kadan ne na sha wahala sosai kafin na gama bai ce mata komai ba ya juya ya bar parlour'n.”
Wani bakinciki ta dinga ji acikin ranta "oh ni maryam me zan yiwa wannan bawa naka na canzashi?gani bata da abinda zatayi yasa taja kafafunta ta koma dakinta ."ta fad'a kan katifa wasu hawayen bakinciki na zuraro mata nasihar sister ce ta fado mata "maryam kinsan yadda akayi auren nan hakuri zakiyi da Adam idan kina son kici riba ,auren da kayi dan soyayya ma hakuri kake yi bare wanda iyaye suka had'a zaman aure dan hakuri ,gidan aure makaranta ce mai girma ba zaka gane hakan ba sai ka shiga, akwai darussa kala dabam dabam sai kin zauna acikinsa zaki fahimta."wasu hawaye suka qara tsiyayo mata yanzu haka zata qare rayuwarta cikin hakuri "tunda kina son shi dole zakiyi hakuri dashi ."zuciyarta ta bata amsa da hakan .”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 10
Ahankali ta yunkura ta mike tsaye kamar wata mahaukaciya ta soma zariya acikin d'akin tana sambatu "yanzu me zan masa na kawowa kaina kwanciya hankalin acikin gidan nan ?tayiwa kanta tambayar tana mai qara shiga tashin hankali "babu abinda zaki iyawa wannan mai shegen taurin kan da zaki burgesa ,komai zaki masa a banza ne a wajensa "tayi shiru na minti biyar tana tunani kafin ahankali ta qarasa inda wayarta take ajiye, ta kai hannu ta d'auka tana tunanin kiran d'aya daga cikin yan'uwansa wani tunani tayi sai kuma ta fasa kiran domin dai tasan kowa a cikinsu abu d'aya yake fad'a mata shine hakuri hakuri !! kuma yanzu da zata kirasu hakurin dai zasu bata ."
"bana son wannan hakurin gashi kuma hakurin dole zanyi tausayin kanta ya kamata tana mai jin kamar duk ita ta jefa rayuwarta cikin matsala a dalilin zunzuruntun qaunar da take masa da taki auren tun farko data zauna da rayuwarta lafiya ."yanzu me zanyi ?ta sake tambayar kanta tana cure hannuwanta waje d'aya "idan da hali ki sake zuwa wajensa ki kwantar da kai tunda kece a kasansa "da sauri ta girgiza kai alamun shawarar bata yi mata ba "wallahi da zan cire kulafucinsa nayi hakuri na bar rayuwarshi da komai zai zo min da sauki "ta sake bawa kanta wannan shawara "amman ina bazata iya ba dan tana da kulafucinsa tana mutuwar son shi kamar yadda yake mugun kinta murmushin takaici maryam tayi tana cewa "Allah kasani ina wa adam wani irin so mai girma, allah ka nuna min ranar da zai soni kamar yadda nake sonshi dan zan só faruwar haka."
"burina a koda yaushe mu kasance a matsayin miji da mata kamar sauran ma'aurata dan haka maryam karki gaji da halin mijinki kije ga mijinki baki san abinda allah zai yi ba wata rana sai labari ga kuma alqawarin da kika d'aukarwa mahaifiyarsa kuma mami ta yarda dake shiyasa ma ta baki amanarsa da wannan shawar ta fito daga cikin d'akin cike da sanyi jiki ."bayansa ta hango yana taka step ahankali yayinda hannuwansa duka ke cikin aljihun wandonsa kunnensa manne iPod ."kai tsaye bayansa tabi yo tana kallon yadda yake taka step yana wani rangaji." alamun taku yaji abayansa ya waiwaya ya kalleta sannan ya juya ya cigaba da taku ,yana gama sauka ya samu waje ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun parlour'n ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya yana cigaba da wayarsa "karka qara min damuwa ammar akan wanda nake ciki, ina ruwa da wata yarinya ta gama bautar qasanta mana ina ruwana ."
"idan zanyi aure dole sai ita zan aura ?" kaga dan allah malam mu bar maganar nan ta isheni haka yes of course ni na furta zan qara aure amman ba lallai sai wannan yarinyar ba .""Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun maryam ta furta a kasan zuciyarta qirjinta na dukan uku uku sakamakon jin maganarsa ,ta tsaya nesa kad'an dashi tana kallon yadda yake motsa bakinsa tare da sauraron maganarsa .shiru ATA yayi can yace "ammar ba lallai tayi min ba ka dai san halina ba duk abinda yayiwa mutane yake min ba ina da test "maryam ta runtse idanunta qirjinta ya cigaba da beating very fast amman kuma ta d'an ji sausauci jin abinda ya fad'a dan haka ta taka ta shige kitchen tana mamakin yaya ammar ."
"In da wani ne ya fad'a mata zai kasance cikin masu bawa mijinta goyon bayan ya qara aure zata musa sai gashi taji da kunnenta sosai taji ciwon abun aranta ta had'o masa shayi irin wanda tasan yana so ta qaraso inda yake zaune jikinta a sanyaye ta mika "ga shayi !".ya d'ago tsumammun idanunshi ya zuba mata batare daya kar'ba ba ya cigaba da wayarsa "kasan Allah da nayi niyyar naga yarinyar nan ko sau d'aya ne amman jin yadda kake wani zuzutata naji bazan iya ganinta ba ." wani naunayen ajiyar zuciya maryam ta sauke najin dadin abinda ya fad'a dadinta dashi akwai ra'ayi kuma ra'ayinsa nayi mata dan ba duk abinda mutane ke so yake masa ba "ga shayi ka sha " ta sake furtawa a raunane kwayar idanunsa ya sake d'agowa ya zuba mata wanda yasa ta sake shiga tashin hankali "nasan kana da d'abiar shan shayi a duk lokacin da ka dawo daga aiki ".
wani dogon tsaki yaja yana d'auke kwayar idanunshi akanta "abinda ya kamata tayi tun a farko shine dan shirme irin nata ya dawo karshe" ya sake jan tsaki ." Daga can bangaren ammar kuwa cewa yayi "haba ATA kaji da madam mana ,dan allah kayi qoqarin kabi mahaifiyarka shine kawai zai samar maka kwanciyar hankali da natsuwa "na sani ammar ina iyakacin qoqarina the girl always doing nonsense wai abinda ya kamata ayi da farko dan hauka irin nata shine ya dawo karshe "haka zaka d'aure kayi hakuri kuma da zaka d'aure ka .."enough ammar ! ya fad'a tare da amsar qaramin cup din hanunta ya ajiye akan table ya mike ya nufi kofar fita ya barta a wajen tsaye bayanshi tabi da kallo tana furta "oh ni maryam naga takaina."