Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo - Chapter 34
Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 34: Mar’adam’s book 2 by aysha a bagudo Chapter 34. nana hauwa'u ta qaraso inda yake cikin rud’ewa da rawar…
3,355 words
nana hauwa'u ta qaraso inda yake cikin rud’ewa da rawar jiki ta riko hannunsa ya fixge "har ke ban cireki acikinsu ba kuyi rayuwarku nayi tawa tunda bakwa sona nima na hakura daku har abada zabiba ta bud'e baki ta soma magana cike da in ina "ni ..ni dai yaya wallahi banda ni dan ba dani aka shirya komai ba hasalima yau din nan nasan komai aunty kahdija ta ta'bata alamun tayi shiru amman ta zame jikinta "dan allah yaya karka mana haka wallahi muna tsananin sonka muna qaunarka ta durkushe kasa tana jan gwiwowinta zuwa garesa ya tsaidaita ya juya ya haye sama a matukar fusace yake taka step ."wani irin naunayen ajiyar zuciya suka sauke atare "mami ta kallesu daya bayan tace "garin yaya kuka yi wannan kuskuren ?yaakayi kuka bari yasan komai ? tayi masu tambayar ajere cikin tsananin tashin hankali,gbdynsu sukai shiru dan basu da bakin magana ta sake sauke ajiyar zuciya "ina maryam take ? tana waje ! nana hauwa’u ta bata amsa cikin kuka kai tsaye kofar mami ta nufa ta bude inda taci karo da maryam durkushe tana zubar da hawayen mami ta kai hannunta ta d'ago ta ta rungumeta ajikinta tana shafa bayanta .”
jinta ajikin mami yasa ta sake fashe da wani sabon kuka mai ta’ba zuciya " dan allah mami ki fad’awa yaya bani da masaniya akan komai ,kuma allah danasan shiri ne ciwonki da bazan ta'ba amincewa ba gara na cigaba da rayuwata haka dashi "kukan ya isa haka abinda ya faru ya wuce ba kuma zai gogu ba ta zareta ajikinta suka koma parlour'n ta zaunar daita akan kujera sannna ta zauna a gefenta tana rarrashinta "yanzu mami ya zaayi kenan ? "ku da kuka tona asirin komai sai kusan yadda zakuyi dan babu ruwana ,ban da son jawa mutane tashin hankali meye abun baje hira a gidansa alhalin kusan halinsa? Kiyi hakuri mami ki yafe mana inji cewar aunty shahida "mami dan allah kije ki shawo kansa ya janye sakin ya maidashi d’aya Ke kadai ce zaki iya shawo Kan yaya nana hauwa’u ta fad'a tana share hawayenta "da sauri maryam ta kalli inda take zaune “sister saki ukun yayi min kenan ?nana hauwa’u ta gyad’a mata kai alamun “eh!ahankali ta runtse idanunta gam tana jin wani irin rad’ad’i da ciwo acikin zuciyarta wallahi tayi wa kanta alkawari muddin ba ita ce acikin gidansa ba babu wacce zata zauna cikinsa cikin jin dadi, duk inda ake zuwa dan biyan buqata zata domin ta hanashi jin dadin rayuwa kuma duk runtsi sai ta dawo gidan zaman lafiyarsa ya janye sakin kamar yadda sister ta bada shawara bata gama fita daga wannan tashin hankalin ba taji muryar aunty zabiba ta karad’e parlour’n “.
“gsky mami ya kamata mu ajiye son rai a tsaya a duba lamarin yaya shima tunda ya nuna baya son aurenta kar a wani maidashi a hakura kawai allah ya hada kowa da abinda yafi zama alkhairi .” da sauri maryam ta bud’e idanunta ta kalli inda take zaune qirjinta na wani irin bugawa "bayan ya gama maidaita qaramar bazawara zaki fad'i haka ? aunty khadija ta fad'a a fusace "to meye amfanin wannna auren tun kafin ayisa yace bai so ?tunda akayi auren nan ku fad'a min rana daya wanda muke da kwanciyar hankali ?”kullum zuciyarmu cikin fargaba take, yin aure halal ne haka barinsa halal ne idan ma zai gare rayuwarsa haka abarshi mana matsawar bazai dinga biye biyan mata ba ,”tunda suka fara magana a tsakaninsu mami bata ce uffan ba har Qarfe uku ATA bai sauko ba gabdaya cikin damuwa da tashin hankali suke most especially maryam wacce har wani rama tayi nana hauwa’u dake kusa da maryam ta dinga kwantar mata da hankali “sister karki d’aga hankalinki yaya zai janye sakin da yayi miki yanzu fa kin rigada kin zama jinin jikinsa jininsa gauraye yake da naki wata killa ma akwai ajiyarsa ajikinki shiru kawai tayi dan bakinta bazai iya furta komai ba dan hatta miyon bakinta ya qafe idan tayi qoqarin had’iye wa jinsa take tmkr mad’aci ."
Da misalin karfe biyar ne mami ta mike ta haura sama ta shiga dakin ATA ta iske shi zaune akan kujera kwaya d'aya dake dakin yayi baya da kujerar yana kallon saman d’akin ganin shigowarta ya runtse idanunshi gam .da sanyin jiki mami take qarasowa inda yake stood ta janyo ta zauna gabansa ta zuba masa ido tana kallonsa tana nazarinsa dakin yayi shiru tamkar babu kowa aciki har tsawon minti goma mami na zaune agabansa yadda batayi magana ba haka bai bud’e idanunshi ba ta kira sunansa "adamcy nah! shiru ne ya sake biyowa baya ta kai hannunta ta kamo hannunsa ta kai bakinta tana sheshekan kuka saukar hawayenta yaji a hannunsa ya d’an bud'e idanunshi akanta tabbas hawaye ya gani yana sharara akan kuncin mahaifiyarsa abinda ya tsani gani kenan naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske sannan ya kai dayan hannunsa yana d’auke mata hawayen fuskarta dake kwarara sannan ya motsa lips dinsa da kyar "why sweetheart?Bata ce masa komai ba illa cigaba da zubar da hawaye "da fatan ba Adam bane yayi sanadiyar zubar hawayen nan ?ahankali ta gyada masa kanta alamun shine.”
numfashi ya sauke yana son sanin dalilin kukanta "adamcy kana son saka sweetheart dinka kuka,baka jin damuwa yadda kake saka sarauiyar dad dinka kuka ?mami ta furta tana dago da idanuwanta ta zuba masa da matuqar damuwa "ina cikin damuwa adamcy !"nima acikin damuwar nake” jin sautin muryarsa cikin tsanani bacin rai ya qara d’aga mata hankali ya zame hannunsa ya mike ya qarasa qarahen dakin ya tsaya rike da kugunsa yana jin zafi da ciwon abinda mahaifiyarsa da yan'uwansa suka masa "."Adamcy na !ta sake kiran sunansa a karo na biyu yana jinta yaki juyawa mami ta cigaba da magana "ka sake min wani alfarma a karo na biyu adamcy .” ya d’an juyo a natse ya kalleta "kayi hakuri ka janye sakin da kawa maryam ka maidashi d’aya sannan ka maida maryam d’akinta saboda allah da girman mahaifinka da darajan haihuwarka da nayi "ya bud'e baki yi zai magana "karka ce aa adamcy ta katse shi ta hanyar fad’ar haka “kayi dan allah da mahaifinka da kuma ni da nayi silar zuwanka duniya domin muddin ka rabu da maryam zata shiga damuwa mai tattare da tashin hankali idan ta kasance cikin damuwa nima zan shiga domin nice silar komai .”
ya juyo sosai ya fuskanci mami "abu na farko tana rayuwarta batare da kai ba na shigo daita cikin rayuwarka, abu na biyu yanzu kun zama abu daya wayasani ma ko rabo ya shiga tsakaninku "gaksy ni sweetheart bana son abinda kike min akan yarinyar nan ban gama fita cikin matsala ba zaki sake shigo min da wata damuwa "ba zancen shigo da damuwa bane adamcy naji hakan ajikina akwai rabo a tsakaninka da maryam .”yayi shiru kawai yana mamakinta a ransa yace “ai kuwa badani ba dan bazan sake gigin kusantarta ba kuma ni bana jin haka ajikina domin spam din daya fitar ba d’a bane dan duk spam din da zai zama d’a fitarsa nada matuqar wahala daga jikin d’an adam mami ta d'an yi gyaran murya "ni mahaifiyarka ce zan iya sakaka kayi min abu dole koda kuwa ranka bai so amman a wannan karon banason na maka dole alfarma nake sake neman da baka hakuri saboda dalilai masu yawa dan allah ka janye ka kuma maida maryam iska ya fesar mai zafi daga bakinsa sannan yace "shikenan naji na janye na maida ita ."iyakar abinda ya fad'a kenan ya fice daga dakin domin idan ya cigaba da tsayuwa zata nemawar yanuwnasa afuwa abinda bazai so ba kenan shi dasu har abada .”
“Alhamdulillah! mami ta dinga furtawa tana nemammansa afuwa da sauki a wajen Allah suna zaune jugun jugun ya sauko ya nufi kofa "zabiba ta zabura ta mike zata bishi aunty shahida ta dakatar daita tana cewa "da alamun kin fara manta waye adam arayuwarki wallahi zamanki matar aure da ya’ya bazai hanashi yi miki mugun bugu ba mu barshi har ya sauko da kanshi "ni dai zan wuce gida dan bazan bari wannan fuskar ta sake shigowa muyi ido hudu ba inji aunty khadija gabdaya suka kwashe da dariya ban da maryam wacce idanunta sukayi jajur tsabar kuka” nima tashi zanyi na wuce nasan mami zata shawo kansa suna shirin mikewa mami ta sauko "mami ni zan wuce gida inji cewar aunty khadija itama zabiba ta gyara zaman mayafinta nima zan gudu dan yau sai wani ikon allah ,allah yasa dai ya sauko "kun gama hadasa mana tashin hankali shine zaku gudu daya bayan daya ?"dan allah mami Kiyi hakuri bamu san zai dawo ba tunainmu fitarsa yayi nisa "ai shikenan tunda ya janye sakin .""
Wani irin ihu nana hauwa ta saka tare da zuwa inda maryam take ta rungumeta "sister yaya ya maidake ai na fad'a miki yanzu kin zama wani bangare na rayuwarsa "kunga kuzo ku wuce sai qarshen wata kenan "in sha allahu mami suka hada baki gabdayansu sukai mata sallama gidan ya saura daga mami sai maryam nasiha da kwnatar da hankali mami tayi tawa maryam muryata a dashe tace “mami na gode “har karfe goma suna zaune a parlour'n sallah ne kawai Ke tashinsu amman babu ATA babu alamunsa har shabiyu ta buga suka rufe kofar parlour'n batare da sun murd’a key ba koda zai shigo suka hau sama daga maryam har mami babu wanda ya runtsa sai faman juyi suke bayan sunyi sallar asuba ne suka kwanta inda wani naunayen bacci ya d’aukesu sai karfe shadaya suka tashi da sanyi jiki maryam ta sauko domin samawar mami abinda zata ci kawai ta gansa kwance akan kujera ya daura tafin hannunsa d’aya a daidai mararsa yayinda d’ayan hannunsa ke saman goshinsa idonsa biyu sai dai tunaninsa yayi nisa domin likitansa bai dade da wucewa ba abinda sakamakonsa ya nuna ne yake yawo acikin brain dinsa “wai anyi masa amafani da wasu kwayoyin jima’i ne wanda shine ya haddasa masa azababben ciwon kai da bai jin magani “ how come ?ya tambayi kanshi Idanunta na kanshi ta shige kitchen ta fara aikinta .”
Kwana bakwai kenan da ATA ya maida maryam sai dai bbu wani saukin al'amura dan babu abinda ya canja daga yanayin zamansu duk da mami dake tsakaninsu dan bai kallon duk inda mrym take idan yana gida hatta mami baya wani hira daita harkar gabansa kawai yake .addu'a dai mami take qara yi kan Allah ya canza masa rayuwa ya kuma daidaita tsakaninsu yasa zaman lfy ya shigo cikin rayuwar aurensu .yau tunda safe maryam ta tashi da aikace aikace gyaran cikin gidan, aiki kawai take kmr wacce tasha kwaya domin koina yayi kura dan ta kwana biyu bata kakkabe gidan ba tun kafin zuwan mami duk mami na zaune tana kallonta shirun da mami tayi ne yasata kallon inda mami take mami tace “anya kuwa mrym bazaa kawo miki masu aiki ba dan naga aiki yayi miki yawa kuma ko babu komai zasu dinga d’auke miki kewa idan na wuce .?tayi murmushi kawai batare da tace komai ba “ki bar aikin nan haka mrym ki huta gobe zansa a kawo miki masu aiki sai suyi ,yanzu zanyiwa cristi magana tasa akawo mutun biyu nasan sun isheki ?”
Maryam ta girgiza kai alamun “a’a ! “mami karki wani damu da masu aiki dan ni bana ra’ayi masu aikin. bbu abinda na fi tsana a rayuwata sama dasu dan wallahi wasu masu aikin ba aiki yake kawo su ba , mami tayi murmushi dan ko bata fad’a mata ba ta fahimceta “ to ai shikennan Allah ya bada sa'a Amman dai yanzu ki bari ki dan hutu haka. naga ko karyawa bakiyi ba ,ai yanzu nan zankarasa nama kusan gamawa.mamaki ya cika zuciyar mami ganin irin aikin da take wanda bata yinsa a lokacin da take gidanta komai masu aiki suke yi mami ta gyara zamanta tare da kunna TV tana kallo daga nan inda take zaune suke hira da mrym din ,kafin wani lokaci mrym ta gama komai har abinci .”koda yamma tayi ma zagaye mami tayi ta shiga kitchen ta shirya masu lafiyayen abinci , farar shikafa ce da miyar pepesoup din kayan ciki ,sannan da miyar pepesoup din freshe fish dataji kayan hadi da ganye ugu aciki sai kamshin ke tashi .”sannan taje ta shirya komai tsaf tsaf a dinning ta bude kulolin abinci ta dinga d’aukar girkin hotuna da vedio byn ta gama ta rufe komai taje ta sheka wanka ta hade cikin daguwar rigar atamfa wacce ta sha stone work sai kalli take zubawa ga wani kamshi na musamman dake tashi ajikinta. karku manta mrym akwai son kwalliya da posting a social media tana gama kwaliyar ta fara zubawa kanta hotuna kala dabam dabam kamar yadda ta yiwa girkin sai datayi posting sannan ta soma qoqarin fitowa ”
ahankali take saukowa zuwa parlour kasa tayi maseefar kyau sai kyali take abu ga farar mace kusa da mami ta samu guri ta zauna sai dai idanunta na kallon tsaitin kofar shigowa mami ta kalleta tana murmushi tace “ kai Kai maryam kinyi kyau ,yau adamcy bazai ganeki ba “mrym ta saki wani murmushin jin dadi tana cewa “kai mami har wani kyau nayi . ?”wallahi kinyi kyau sosai kuma naji dadin ganin wannan kwaliyar daman inata son nayi miki magana akan kin rage kwalliya ba kamr sanda kike gida ba, marym ta sake yin murmushi “gsky kinyi fine sosai allah yasa adamcy yaga kyan kwaliyar nan “Ameen ta amsa a cikin ranta .”bayan kamar mintuna goma suka jiyo sallamarshi a ciki suka amsa alokacin da yake taku cikin parlour, kunnenshi makale da waya yana magana da saurinta ta mike ta tarbeshi zata karba briefcase din hannunsa ya hanata batare da ya kalleta ba ya nufi hanyar sama yana jan tsaki dan baqaramin jin haushin nacinta yake ba“.
jiki a sanyaye maryam ta shige kitchen ta zauna tana runtse idanunta yayinda zuciyarta ke mata wani irin zugi mami sarai ta fahimci damuwace tasa yin haka nan da nan itama taji damuwa zuciyarta ta sosu ta mike ta shiga kitchen din ta iske mrym zaune har lokacin idanunta a runtse suke ta kai hannunta ta riko hannunta ba tace daita komai ba suka fito kai tsaye dining area suka nufa ta zaunar daita itama ta zauna tana ta’ba qirjinta alamun ta kwantar da hankalinta .”byn kmr minti talatin ATA ya sauko jikinsa sanye da riga white t shirt da wando jeans three quater sai kamshin turarensa Red ne yake tashi ajikinsa , kai tsaye dinning area ya nufa inda ya hangi su mami zaune da alamun zaman jiran fitowarsa suke .'ahankali ya karaso gurin tare da samu guri ya zauna kusa da mami yana gaisheta “ai na d’auka bazaka gaisheni bane ?dan ka wani shigo ko kallon inda mutane suke bakayi ba ta fad’a cikin rashin sakin fuskar numfashi ya sauke yace “barka da dare sweetheart ?barka ya aikin ?alhamdulilllahi ya fad’a atakaice sannan ya ciro wayarsa yana operating .”
ahankali mami tayi wa mrym alamar ta koma kusa dashi ta tashi ta koma kusa dashi ji yayi kamar ya tashi ya canza guri amman ya share ya cigaba da dandana wayarsa “maryam bismillah kiyi serving dinmu wani irin mikewa tayi wanda yasa gabadaya santsar jikinta girgiza most especial qirjinta d’agowa yayi da niyar sauke mata ruwan bala'i idanunshi yaci karo da girjinta kallo daya yayiwa Rabin nonuwanta ta saman rigarta ya d’auke idanunshi amman duk da haka say da yanayinsa ya d’an canza nan da nan kwalkwaluwarsa ta shiga circulating ya dinga jin wani iri a sansar jikinsa abinda bai ta’ba ji akanta ba kenan sai yau .”cike da natsuwa tayi serving dinsa. bawani abinci kirki ya ci ba ,ya ture plate din gefe 'ahankali ya maida bayansa ya jingina da kujerar da yake zaune akai Tare da dan zamowa kadan yana duban mami itama mami shi take kallo tana tabe baki “ba dai har ka koshi ba ?”
ya dage mata girarsa daya alamun haka ne ,”yanzu duk yadda girkin nan yayi dadi ? ya yatsina face dinsa kawai batare da ya cewa mami komai ba dan bai ji wani dadin da yayi ba murya a sanyaye mrym tace” to ko na hado maka coffee ne?bai ce uhm ba bare um uhm parlour ya dauki shr har kusan tsawon minti goma batare da ko tari yayi ba , sai da mrym din ta km maimaitawa tmbyrta tukun muryarsa a dake yace “ please banason damuwa dan Allah“ “maryam je ki had’o masa zai sha tsabar jin kai ke damunsa jin haka yasa mrym din mikewa 'ahankali tana jujjuya mazaunanta har ta nufi kitchen mami tace “adamcy kalli can ya kai idanunshi inda ta muna masa bayan maryam ya hango ya waigo ya kalli mami”sweetheart me hakan yake nufi kuma ?me nayi ?na nuna maka ne kaga irin halitta dirin da allah yayi wa matarka ,mrym nada daidai nata kyau adamcy “takaicin da ya tsaya masa a makwashi ne ya samu ya hadiye da kyar yana hango tahowarta da yadda take motsa qirjinta saurin d’auke idanunshi yayi ya kamo lip's dinshi na kasa yana cizawa da karfi har ta karaso ta’aje masa coffee a gabansa bai dana cizan lip's dinshi ba,yana son shan coffe din amman yaki d’auka ya sha .”
Mami ta zuba masa ido tana kallonsa kafin ahankali ta d’auki cup din coffe ta mika masa babu musu ya kar’ba ya fara sha yana lumshe ido mami ta cigaba da kallon yadda yake shan coffe sak mahaifinsa kusan har ya so ya zarta tariq abdallah da komai ya d’an dubi mami yace “ ya’akayi sweetheart ?ta hararesa tana cewa “ban sani ba nan kafi kauri ga abinci ka zauna kaci yadda ya kamata aa sai ruwa “tsam ya mike tsaye ya soma taku rike da cup “sweetheart ni zanje na kwanta bacci nake ji tabi bayansa da kallo ,”to Allah ya tashemu lfy “daren ranar sam ATA kasa runtsawa yayi kwana yayi yana juyi yana watsa jikinsa ruwa hannuwanshi yasa duka ya dafe jijiyarsa dashi yana juyi da kyar ya samu ya runtsa sakamakon wani irin feeling da ya dinga tasoma masa sai wuraren asuba bacci mai nauyi yayi nasarar daukar shi.”washegari da sassafe ya bar gidan ya wuce office .”
zaune yake a office dinshi aiki yayi masa yayinda kanshi ke duke yana fama da aiki rubuce rubuce dake gabansa yaji Knocking din kofa , kansa na duke ya bada izinin shigowa batare daya dago kansa ba yaga ko waye ba ammar ne ya shigo cikin office din da sallamarsa ATA ya amsa batare da ya dago kansa ba ya cigaba da abinda yake" ganin haka Yasa ammar ya tsaya abakin window , yana kallon haraban ma’akatan wanda ma’aikata ke kai kawo dan yasan tunda ya iske ATA kan aiki bazai taba sauraransa ba matsawar bagamawa yayi ba dan sanin da yayi masa kenan na maida hankalinsa matuka akan aiki idan yana yi .Kusan minti shabiyar yayi tsaye , sannan ya soma takowa ahankali izuwa bakin makeken tablet din da ATA ke zaune ,yaja kujera daya ya zauna yana dubansa, Sai lokacin ATA ya d’ago tsumammun idanunsa ya dubeshi har ka gaji da tsayuwar kennan ?
“Ba dole nagaji ba dan naga alamun sai nakai ga zama tukun zakiyi lokacina ya fad’a hk yana mikowa ATA hannu suka gaisa ,yaushe ka dawo qasar ? Dariya ammar yayi yana cewa “shekaranjiya na dawo yau km nace nazo naganka ,ko bai yi bane ? Wani irin farinciki ya lullube zuciyar ATA ya danyi murmushi har dimple dinsa ya lotsa tsantsar kyawunsa ya sake bayyana ,yana son a dinga nuna masa kulawa da soyayya ,ammar yace aboki lfy kuwa irin wannan farinciki haka ?”babu komai nima haka na tsinci kaina ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune yana jujjuyawa dashi , ammar yace “ya mami da dolen dolalo ?sai da ATA ya yamutsa fuska sannan yace “sweetheart tana lfy ita dayar ce dai gsky bansani ba ammar ya sake yin dariya kace zaka qara aure har yanzu shiru ko ka canza shawara né zaka cigaba da zama da dolen dolalo?