Mar'adams book 3 - Chapter 12
Mar'adams book 3 Chapter 12: Mar'adams book 3 Chapter 12. bayan kamar minti goma ya mike tsaye maryama taga tahowarsa amman bata d’ago kanta ba dan kwata…
3,263 words
bayan kamar minti goma ya mike tsaye maryama taga tahowarsa amman bata d’ago kanta ba dan kwata kwata bata son ko kallonsa a yanzu dan kallonsa zai haddasa mata jin mummunar tsanarsa acikin ranta ,har ya iso inda take zaune ya tsaya akanta yayinda ta tattara dukkanin natsuwarta kan zane da take bata d’ago ba ,har sanda ya janyo kujera gabanta ya zauna tare da ware qafafunsa still bata bar abinda take yi ba .ahankali ya gyara zamansa ya duko da kanshi daidai kanta yana kallon zanen. numfashi ta sauke ta bar abinda take tana jin yadda qirjinta Ke bugawa da karfin gaske sakamakon dab da junan da sukai wanda da zai matso da kujerar kad’an zasu iya had’ewa da juna “ki cigaba da aikinki kada ki ‘bata min lokaci kisa nayi asara .”ya furta cikin wani irin salo da sautin murya hucin bakinsa da numfashinsa na shiga hancinta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa “.
“sir ko zaka ..” bata kai ga yin magana suka ji an turo kofar glass din office din an shigo .”sautin muryar ammar dake d’auke da sallama yasa mr ata ya waigo bayansa ido cikin ido suke kallon juna da ammar . ganin ammar bai sa mr ata ya mike ko gyara zamansa a gaban maryama ba illa ma ya cigaba da mata bayanin yadda yake son tayi masa zane da kallo ammar ya bisu yayinda maryama bata masa ba sai gyad’a masa kai tayi tana jin kamar ta fashe da kuka amman ta danne dan muddin ya gane hawayenta shine rauninta ta kad’e a hannunsa “so take ta d’ago su gaisa da oga ammar amman ta kasa dan wata irin faduwar gaba take ji saka makon kusancinta da mr ata gashi yaki mikewa bare ya barta ta samu natsuwa .”
ammar ya koma jikin window office din ya d’an zuge labule kad’an yana hango haraban ma’aikatan dan yasan ko yayiwa ata magana ba lallai ya sauraresa ba .sai da mr ata yayi raayin tashi dan kashi sannan ya mike ya tura hannuwansa duka cikin aljihunsa ya qaraso inda ammar yake tsaye batare da yace masa komai ba “mutumina kana shaa’aninka har kun fara soyayyar ne ?“oh my god sai ka bari taji? ya furta a can qasan makoshi ta yadda idan ba bakinsa ka kalla da kyau ba bazaka fahimci abinda yace ba .” murmushi ya kwace a saman fuskar ammar “kar dai ka tsaya ‘bata lokaci ?ammar kayi kasa da muryarka mana “okay amman mutumina kayi zafi zafi fa karkaje garin neman gira ka rasa ido kar wani yayi maka shigar sauri a ma’aikatar nan “babu wannan mahalukin a yanzu idan ka ganta da wani to ni ne idan zata só wani to ni ne .”ammar yayi murmushi yana kallon inda maryama take kamar tasan kallonta yake ta d’ago idanunta da suke ta tara hawaye tana dannesu ta saukesu akanshi tana qoqarin motsa bakinta domin gaishe da ammar yayinda ammar din tuni har yayi taku d’aya ya jiyo muryar ata cikin rad’a yana cewa “karkaje !ammar ya tsaya cak yana fuskatarshi “ko me yasa ?”gaisawa kawai zamuyi daita “bana bukata dan nasan halinka byn gaisawa har da rayuwata zaka shiga .”
sanyayyar murmushi ya subuce masa sanda yake hango kishinsa a fili “me kake tunani akaina ?amman dai tunaninka kar yaudareka kasan bazan sota ba ?”ata yayi shiru adaidai lokacin da wayar mr ata ta soma ringing yaja qaramin tsaki yana jin haushi “mutanen nan suna son d’aga min hankali wani tsakin ya sake ja sannan ya kalli inda maryama take yace “Ke ..”tana jinsa tayi masa banza tamkar bataji shi ba “am talking to you ina magana kina jina “.a sheke ta d’ago ta kallesa kwayar idanunta cike da rauni da ‘bacin rai “karki ‘bata min lokaci kin gama “?kamar tayi masa banza sai kuma ta tsinci kanta da ce masa “sauran kad’an na gama ,oga ammar ina kwana ?kina lafiya maryama ya fama da wannan abokin nawa ?numfashi kawai ta fesar “.tana ta’be bakinta ina ruwanta dashi bare tayi fama dashi ta maida kanta ta cigaba da aikinta.”
Ammar ya juya kan ata wanda ya koma mazauninsa shima kujerar dake fuskarsa yaja ya zauna “kai mutumina kabi yarinyar nan ahankali fa “wani abu kaga nayi mata ne da zaka zo min da wata magna ?” ji yadda kake mata magana, kana kallonta kasan bata jin dadin aiki da kai “kar Allah yasa taji ,kana ganin yarinyar nan muguwar yar rainin sense ce kai kaga rashin mutuncin da ta min jiya ace ba ita bace wata ce dabam da yanzu na koreta “me ye tayi maka ?amman bana tunanin maryama tana da matsala nayi aiki daita “nan mr ata ya shiga magana kasa kasa yana koro masa abinda ya faru ai kuwa ammar yayi dariya kamar me “wallahi tayi min daidai haba ai kai din ne baka da kyau shine ka wani tasa diyar mutane gaba kana son firgita masu yarinyar Allah zan fad’a mata ta cigaba da jajurcewa “tashi mu bar office din nan karka ballo min ruwa .”tare suka mike ata ya zagayo suka fita wanda hakan ya bawa maryama damar aiwatar da aikinta a tsanake .”
Bayan minti goma ya dawo shi kad’ai ya zauna a mazauninsa ya tsarke hannuwansa duka cikin juna ya rike ha’barsa dashi yana kallon zara zaran yatsun hannunta dake kwance tana zane, komai nata dabam ne bai ta’ba ganin halittar data shiga zuciyarsa kamarta ba “kin sace zuciyata ya Allah ka shigar dani zuciyarta da rayuwarta domin na zama abokin rayuwarta na har abada ita dai maryama bata san halin da yake ciki ba ta dukufa kan aikinta.”bayan kamar minti shabiyar ta gama ahankali ta d’ago kanta karaf idanunshi ya tsarke cikin juna wani irin bugawa da karfi qirjinsu yayi take yayi saurin wayancewa “kin gama ne ?”jikinta a sanyaye gabanta na faduwa tayi saurin gyad’a masa kai .”ya mike tsam ya d’auki zanen data fara zanawa ya tako har inda take.”
tana ganin tahowarsa tai saurin mikewa tsaye ta mika masa takardar cike da girmamawa ya kar’ba ya soma dubawa yana taku ahankali ahankali acikin office din yana duba dayan zanen da tayi .gani tayi ya ajiye zanen farko da tayi a daren jiya sannan ya kai d’ayan hannusa ga zanen da tayi yanzu yayi kuci kuci da takardar ya watsa mata “shima wannan bai min ba har gara na farkon zaki iya tafiya sannan ki godewa allah zuwanki ma’aikatan nan ya gyara rayuwata yayi sanadiyyar sauyawata da wani labarin akeyi ba wannan ba akan iskancin da kike min jiya .”ya qarasa fad’a yana tsareta da tsumammun idanunshi ,bata bari ya qara magana ba ta ra’ba ta gefensa har jikinta na gogan nashi sbd kusanci ta wuce zuciyarta tamkar zata kama da wuta kuka ne ke qoqarin kufce mata amman ta danne saboda ganin idanun mutane gabad’aya taji aiki akarkashinsa ya fita ranta tana shiga office dinsu ta zauna tana sauke numfashi.”
maganganunsa suka soma dawo mata wanda ta kasa fahimtar inda suka dosa me yake nufi tana bukatar tasan me yake nufi “ki godewa allah zuwanki ma’aikatan nan ya gyara rayuwata yayi sanadiyyar sauyawata da wani labarin akeyi ba wannan ba akan iskanci da kika min jiya “kamar yaya kenan yake nufi ?wani mummunar abu yake yi mara kyau wanda zuwanta yayi sanadiyyar sauyawarsa ko me ?” to ita a wa kenan data sauyasa ganin kwakwaluwarta na neman daurewa yasa ta kad’a kai tare da yin watsi da maganarsa maimakon cigaba da tunani sai ta janyo jakarta ta fito da kayan aikinta ta fara wani aikin wanda some ta ajiye mata .”
****** Washegari
11:00 dot a office dinsa tayi masa gbdy ma’aikatansa suka dinga shiga office dinsa domin gaishesa a dakike ya dinga amsa masu kwayar idanunshi maryama kawai take son ganin sai dai har lokacin da karfe shabiyu ta buga babu maryama babu alamunta a office dinsa kamar yadda sauran ma’akatansa suka saba shigowa byn sun yi gaisuwa idan akwai aikin da yake bukata ayi masa sai yasa some ta basu mikewa yayi rike da wasu file guda biyu ya fita ya ajiyewa some sannan ya shiga office din da take aiki .”hangota yayi zaune tana aiki ahankali ya zarce inda take yace ta biyosa sannan ya juya ya fice daga office din ya koma office dinsa .”kamar maryama bazata tashi ba amman sai fahimci idanun sultana suna kanta dan haka tá mike ta shiga office dinsa ta samu waje ta tsaya a gabansa fuskarta a had’e tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa .”
gabansa ne yayi wata mummunar fad’uwar ya tsura mata ido ta bala’i qara shiga ranshi haka yake son mace jajitacciya mai natsuwa da kamewa “manyan ma’aikatana sun shigo domin gaisheni ke me yasa baki shigo ba ko kinfi karfin kizo ki gaishe dani ne ?”ta tsura masa ido kamar tace masa siyanta yayi ko ita bawarsa ce amman sai tace “shigowa gaisheka yana cikin kaidodin aiki a karkashinka ne ?”baya ciki ikona ne yasa hk “okay !ta fad’a tana gyara tsayu warta tana ciza gefen lips dinta alamun bazatayi ba .” yaji kamar ya fixgota yayi mata muguwar matsar da zai sa ta shiga hankalinta ,ya tsura mata ido kawai har kusan mintuna talatin sannan yace ta dauki file din gabansa “ta kai hannunta ta dauka ta soma dubawa “ kije ki duba page 9 da 10 irin zanen da nake bukatar ne ki natsu Kiyi min aiki mai kyau “amman sir da ka kira wadan da suka fini kwarewa zaka fi samun abinda kake bukata kar nazo nayi maka kace bai maka ba .”ta qarasa fad’a tare da maida file din inda ta d’auka yayi murmushi aciki ranshi yarinyar nan tana son na koya mata hankali tana son nayi mata abinda banyi niyya ba “ki dauka kije kiyi abinda nake so taki d’auka ta cigaba da tsayuwa.”
a tsawace yace “take it and leave me my office”numfashi ta sauke tana yatsunsa fuska ta juya har ta kai bakin kofa yace “ke!” ta tsya batare data juyu ba “awa uku kawai na baki “ta qarasa ficew tana cewa “aikin banza ai dakasani ka bawa wasu sun maka kaga aikin shirme duk wannan abun akan idon some ya faru ta cika da mamaki karo na biyu kenan maryama ke sainsa da mr ata .”Ahankali sultana ta mike zata bar office din sai ga some ta shigo tace “ ina zuwa ?”tayi mata banza “at least ki zauna ki d’an yi wani aiki mana tunda kika zo yau bakiyi aikin komai ba.” sultana ta kalleta a wulakance sannan ta soma magana cikin tsananin fushi “kina hauka ne ? “aiki sai naga dama zanyi dan bama fama da yunwa da tallauci aikin nan ra’ayi ne ko nayi aiki ko kar nayi dole kuma abiyani saboda mahaifiyata tanada karfin iko acikin wannna kamfanin dan haka daga yau ido ne naki akaina dan ko mr ATA bai isa ya koreni daga wannan ma’aikatanr ba dan banyi aiki ba okay.”
Some bata ce mata komai ba har sultana ta qarasa inda maryama take zaune ”uhm Ke dai bagajiya da aiki kamar ba d’azu kikayi wani aikin yanzu kuma kin dukufa yin wani “me ya kawo ni ?”ai aikin ya kawoni kinga dole nayi”sultana tayi shiru can ta cigaba da mgn “duk aikin da mr ATA ya kawo bakya sallakewa ?”taya zan tsallake me ya kawoni idan ba aiki ba kuma dai ai shi din mai gidana ne dole nayi masa duk aiki daya sakani sultana ta cigaba da surutu mara ma’ana “maryama tace “kinga sultana kin dameni ni fa ina son aikina “ ko ma dai menen bazaki ta’ba burge mr ATA ba “banzo dan na burge kowa ba nazo dan nayi aiki ne oky sultana taja tsaki da numfashi sannan ta fita “.
Some ta tsaya akan maryama !tana kiran sunanta “yes ma ta tsaya kusa daita rungume da file “duk cikin masu aiki a kamfanin nan daga manya har kana babu wanda Ke iya maidawa sir magana saboda tsoro amman naga ko kad’an bakijin tsoron komai kina iya mutsu dashi kina iya magana dashi kai tsaye tun shekaranjiya hankalina a tashe yake sai gashi naga sir yayi shiru bai ce komai ba “Eh ! nima nayi tunanin zai ce wani abu sai naga bai ce ba sai abu na gaba nima ina jin tsoronsa kamar kowa “really!?” yes ma !ta fad’a tana sakar mata murmushi “na danne nawa tsoron ko nace so nake na cire tsoronsa dan naga alamar kowa najin tsoronsa shine nake son na cire kaina ya zamo ban dani sannan kuma na rufe damar da zai fad’a min abinda ya ga dama, no chance for him “shiru some tayi tana sauke numfash.”sannan tace “ki dai bi ahankali “okay ma .”
Cikin yanayin na tashin hankali sultan ya shigo office din mr ata yana huci tmkr zaki ya soma magana “yana cewa wai me ka d’auki kanka ne komai kai sai ka nuna wa mutane isa da mallaka , kayi iko akan kowa ,kayi iko akan komai, Ka dinga abu da d’agawa naga alamun so kake ka mallakemu gbdy da kamfanin “mr ata bai ce masa uffan ba illa ya fesar da numfashi mai zafi kana ya mai da jikinsa sosai akan kujera tare da lumshe idanunsa inda sultan ya cigaba da fadar magana son ransa idanunshi ya bude a hankali cikin yanayin tashin hankali ya ci gaba sauraronsa “kamfanin IGA mu suke bawa aiki amman dan rashin godiyar allah irin naka sai da kayi munafurcin da suka kawo maka aiki “ me muka tsare maka me ala dole so kake ka malleke kamfani .”
“Mallakar kamfani kuma na nwa ?ai tun tuni na mallake ,kuma babu wanda ya isa yayi abinda yaga dama matsawar ina cikinsa ,kai kanka kasan nafi karfin na tallata sanaata ga kowa bare IGA “ abu na farko bansan ku kuke masu aiki ba sun bukaci aiki daga gareni kuma nayi masu abinda suke so amman kawai saboda burika kullum ka ci min mutunci ko kayi abinda zan bar kafanin nan ka maye gurbina ka zama MD na wannan ma’aikatar shine zaka zo kana fad’a min mgn kana son matsayina sai dai baka da wannan kokarin sannan baka da talent din sannan daga yau idan kana son ka zo wurina ka dinga amfani da common sense din kafin kazo okay yayi maganar a tsawace .”
“Adam kana wuce gona da iri acikin kamfaninmu ka tattara kwararu masu aiki a wurinka ka hana kowa ya dinga sakasu aiki sai kai kad’ai “mr ata ya kallesa a kaskance jin ya shigo da wata maganar bai kai ga cewa komai ba yaji ana neman izini “ko zan iya shigowa ? aka fad’a daga bakin kofa”kullum kana jin dadin ganinmu cikin damuwa kullum burinka kaga komai namu ya tsaya .” shi dai mr ATA bai ce uffan ba dan daman tuni ya maida idanuwanshi kan system.“daga yanzu zan fad’awa gabadayan family’s dake aiki acikin kafanin nan kada wanda ya sake bin umarninka ko bin wata dokarka acikinmu dan baaajiyemu kayi ba “ maryama taji shiru ba’a bata izini shiga ba tace “sorry sir ! ta juya da sauri ta koma kasancewar taji kamar alamun fad’a “sultan kana damuna alhalin kasan bana son damuwa dan Allah zaka iya tafiya please .”
“Bazan tafi ba sai lokacin dana ga dama dan ba kai kad’ai kake son yin abinda ka dama ba wai har kamar ni zan sa akira min yara zan sakasu aiki suki bin umarnina wai suna maka aiki “rashin tunaninka bazai bari ka fahimci komai ba kai kasani babu wanda zan hana yayi maka aiki sai dai idan suna min aiki amman tunda idanunka yanzu sun dawo Kan ma’aikatan dake karka shina saboda a tunaninka sune nasarata muje ka zabi duk wacce kake son tayi aiki da kai .”wani farinciki ya kama sultan saka makon burinsa ya cika sai dai yaki bayyana hakan dan kar mr ATA ya fahimta ya canza ra’ayinsa dan yasan halinsa .”
Mr ata ya mike ya fito sultan ya biyo bayansa cike da farinciki kai tsaye office din su maryama ya shiga akayi saa duk kusan wadan da yake aiki dasu suna gurin har maryama tunda ya shigo gaban maryama ke fad’uwa sakamakon idanunshi dake kanta “ya numfasa sannan ya soma magana “acikinku wa yake son yayi aiki akarkashin sultan ?gabadaya office din yayi shiru babu wanda yayi magana wanda hakan ya nuna basa bukata ,maryam kam taso tace zatai aiki dashi tunda shi wannan balainsa yayi yawa amman har sanda mr ATA ya gama maganarsa ya shiga wata bata iya cewa komai ba “duk wanda yake bukatar yayi aiki akarkashinsa ya daga hannu? nan ma shiru maryama ta kalli gabadayansu ma’aikatan wurin taga babu alamun akwai wanda Ke bukata dan haka tayi qoqarin daga nata hannun wanda hakan yasa cikin hanzari mr ATA ya cigaba da magana wanda kuma yasan zai kasance akarkashina ya daga hannu ?gabadaya suka daga hannu banda maryama alamun bata tare dashi .”
sultan yaji zafi sosai kenan duk matanka iko da kaidodin da yake masu da balain da hantararsa sun fi bukatar kasance akarkashinsa akan shi lallai sai ya tashi tsaye akan ATA .”wani kallo mr ATA yayi wa maryama ganin har lokacin taki daga hannunta yayinda kowa hannunsa Ke sama d’auke idanunta tayi cikin nashi tana hura hanci “ka gani sultan babu ruwana kawai ni business dina ne agabana bani da burin shiga hakin kowa idan kamfani ne kasan ina dashi masu tarin yawa anan ma ku nake taimakawa da rayuwarku domin idan na barshi barayin cikinku zasu karyar da kamfani qarshe ku dawo kuna bara a wurina which’s very bad .”ya fad’a yana kallonsa a dage ,yanzu ko zaka iya tafiya kasa a nemo maka wasu maaikatan da zasuyi aiki da kai dan wadan nan nawa ne ?”
Tun bai kai ga rufe baki ba maryama tace “sir ko zan iya cewa wani abu ?yayi shiru yana dubanta cikin tsananin fad’uwar gaba yana fargaban bata damar yin mgn d’an bai san me zatace ba hakan nan ya tsinci kanshi cikin tashin hankali da fargaba dan dai shi din miskilin kanshi ne da gabadayansu zasu iya fahimtar yanayin daya shiga “kayi shiru sir ko zan iya cewa wani abu ?ta sake maimaitawa sai daya sauke naunayen ajiyar zuciya a boye sannan yace “yes!.ta rausayar da kwayar idanunta cikin nashi sannan ta bude baki a natse ta soma mgn “sir dayawa daga cikinmu suna jin tsoron su amince da wannan da bansan ko waye shi ba sbd da kai koda kuwa suna só , haka zalika suna jin tsoron suki amincewa da zama kusa da kai duk dai saboda tsananin tsoronka .”sultan ya gyada alamun ya gamsu da maganarta domin daí gsky magana ta tsage ta fad’a kuma ta burgesa sosai kawai ka barshi ya zabi wadan yake so acikinmu .”
gabansa ne yayi wani mummunar faduwa nan take fargaba da tashin hankali da yake ciki ya qaru ya tsura mata tsumammun idanunshi sosai yana jin wani iri a ilahirin jikinsa shi da yake burin matso daita kusa dashi sosai idan ya kasance sultan ya zabeta fa ya zai yi ?muryarsa a kasalance yace “me kika ce ?karka yi kamar baka jita ba alhalin kaji abinda ta fad’a,wannan yarinyar gsky ta fad’a domin ta kawo mana masalaha dan haka zan zabi wadan da nake son suyi aiki akarkashina cewar sultan ,mr ATA bai ce uffan ba illa ya runtse idanunshi qirjinsa na wani irin luguden bugu dan dai itace ta kawo wannan tsarin da wani ne da shi kad’ai yasan irin azabar da zai yi masa amman ko yanzu bazai barta haka ba sai ya hukuntata .”