Mar'adams book 3 - Chapter 14
Mar'adams book 3 Chapter 14: Mar'adams book 3 Chapter 14. “Har mr ata ya fito haraban ma’aikatan zuciyarsa tafasa take . da wannan d’acin rai ya qaraso…
3,322 words
“Har mr ata ya fito haraban ma’aikatan zuciyarsa tafasa take . da wannan d’acin rai ya qaraso gida duk wani d’aga hannu da securities suke masa bai kalli inda suke ba ,hakan yasa duk suka shiga hankalinsu alokacin da jerin motoncinsa suka paka babu wanda yayi kaud’in isa inda yake dan duk lokacin da yanayinsa yayi haka to gagarumin bala’i ne zai biyo baya.haushinsa ba’a iya kan wanda ya ta’bosa yake tsayawa ba har akan wanda bai da ruwa da tsaki yake saukewa , dan a irin wannan lokacin yake korar mutun daga aiki ko kuma ya bawa mutun hutun satittika.” tun kafin yasa kai cikin babban parlour’n gidan ya soma jiyo hayaniyar mutane sai lokacin ya tuna ashe gobe ne zaayi sunan auta.” a dake ya sanyo kai cikin parlour’n fuskarsa babu digon annuri bai tsaya ba kai tsaye samansa ya nufa batare daya kalli tarin matane dake zaune a parlour’n mami ba, ita kanta mami bai nemita ba sakamakon kansa dake masa mugun sara .
“Ahankali ya zauna akan daya daga cikin kujerun cushions din parlour’n sa kanshi na cigaba da sara gabadaya ya kasa samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali.”ji yayi muddin bai kira maryama ya mata bala’i ba bazai ji dadi aransa ba sannan zuciyarsa bazata samu kwanciyar hankali ba dan haka ya soma neman layinta. shigowar maryama kenan tana yiwa umma sannu da gida inda umma Ke tako wa zuwa inda take tsaye tana tambayarta “yau kin dade a wajen aiki .muryarta a gajiye tace “wallahi wannna boss din namu ne sai ahankali nan ta shiga korowa umma abinda ya faru da yadda suka rabu dashi “ikon allah shi kuma haka nashi tsarin yake ?” “ke dai bari umma mutane na mugun shan wahala a hannunsa amman fa duk da wannan takurawar tasa wai haka suke son aiki akarkashinsa nifa ina ganin zan soma neman wani aikin dan bazan jura ba“Allah ya zaba miki abinda yafi zama alkhairi ko cigaba da aiki akarkashinsa ko samun wani aiki “amen umma “! maryama ta fad’a tana cire jakarta tana qoqarin ajiye jakarta kenan wayarta ta d’auki qara ta d’auka tana duba screan din wayar suann “sir ! ta gani wato sunan mr ATA ne yake yawo a screen din wayar tayi shiru tana jin kamr ta d’auka sai kuma tayi tunanin kar ta d’auaka dan batasan me kiran nashi zai haifar mata ba gara ta sharesa dan haka ta kashe wayar gabad’aya gaban ta na fad’awa ta shige d’akinta .”
Yayinda adaidai wannan lokacin mami na zaune agefen gadonta kusa da maryam tana cewa"haba maryam banason ina ganinki shiru , yawan tunani ko saka damuwa a zuciyarki shin zai miki maganin halin da kike ciki ne? "Jin haka yasa maryama fashe mata da kuka dan daman danne kukan take tana yinsa a cikin ranta “subhallah !”mami ta furta tana riko hannunta cikin nata “haba maryam daga magana meye kuma abun kuka ?”tunanin ne banaso bare ganinki cikin damuwa “akwai abinda aka miki ne kika dawo nan ke kad’ai ki baro yan’uwanki ?cikin muryar kuka maryam ta girgiza mata kai tana saka hanu ta rufe bakinta saboda wani kukan da yake kuma tahu mata suna cikin wannan halin sai ga nana hauwa’u ta shigo bayanta aunty khadija ce rungume da baby da sauri suka qaraso suna tambayar mami “lafiya mami me kuma faru maryam take kuka ? .”
“nan mami ta fad’a masu tsaki aunty khadija tayi sannan ta soma yi mata fada cikin zafin rai “ki zauna kashe kanki abanza ki cuci abinda zaki haifa dan wanda kike damuwa akanshi bai san kina yi ba wai shin dole ne da bazaki rabu dashi da tunaninsa ba ?”a’a khadija banaso haka dame kike son taji ?ke daya kamata ki rarrasheta ki kwantar mata da hankali tunda Kinsan ba'a son tana yawan shiga damuwa da tunani saboda cikin jikinta “.Allah mami maryam din ce da kayan haushi mutumin ko kallon inda take ba yayi bare ya duba situation din da take ciki amman ita kullum cikin damuwa take ,yanzu ki duba kiga kowa tsabgar gabansa yake cikin walwala amman ita ta dawo nan tana damun kanta da tunanin banza da wofi ta qarasa maganar tana jan tsaki sannan ta juya ta fice .”
nana hauwa’u zama tayi kusa daita suka saka maryam a tsakiyarsu .ita kam maryam kuka kawai take dan bata da abinda ya wuce kuka most especially idan ta tuna abubuwan da tayi duk akan adam amman babu abinda yayi tasiri akanshi da kyar suka samu tayi shiru ta share hawayenta tare da zabga tagumi still dai tunanin da basa son tayi shi ta sake lulawa ahankali mami ta dinga mata nasiha .” yayinda mr ata yake can bangarensa bai fito ba sai dai zuwa lokacin yayi wanka ya sauya kaya zuwa na shan iska .”wayarsa ya d’auko ya sake kiran number maryama sai dai amsa daya ake bashi wayar is switch off…..Oh my godness god wai me yake faruwa dani ne? komai ya zama worst a gareni? me ma yarinyar nan ta take nufi dani ?“anya kuwa yarinyar nan bazata haukata ni ba ? wannan shine tambayoyin da ya cigaba dayi a zuciyarsa yana jin zafi mai quna a ransa .”
Zaune yake shiru a parlour’nsa rike da waya layin maryama yake nema amman still a kashe ya duba agogon wayarsa karfe goma ta wuce tsaki yaja “may be tayi baccinta ya furta a fili yana rufe bakinsa aka turo kofar parlour’n aka shigo saurin waiwayowa mr ata yayi,ahankali kuma ya d’auke kanshi yana fesar da iska ganin yaya hisham ne ahankali yaya hisham ya dinga takowa har ya qaraso inda yake ya tsaya gaban Mr ata yana kallonsa kawai, rasa abun cewa yaya hisham yayi saboda yadda yaga fuskar mr ata alokacin tana cikin wani yanayi daya kasa fassarawa ko da ganin haka sai ya samu waje ya zauna ya zuba masa ido kamar yadda yayi masa, a hankali yaya hisham ya saki fuskarsa zuwa yanayin mur mushi, yace” ATA nazo maka da wani albishiri mai dadi mr ata yayi shiru yana kallonsa yana jiran yaji wani irin albishiri ne duk da baya tunanin akwai abinda zai wanke masa zuciya ahalin da yake ciki .”
“babynmu yaci sunan abbanku muhammed tariq ga mamakin yaya hisham murmushin ata ya fara daga yanayinsa sai daya bashi wasu mintuna sannan ya bud'e baki ya cigaba da magana ! Mr ata what this smile ?" wani sabon murmushin ya sake yi cike da tsananin farinciki mara misaltuwa cike da murya Ata Ya furta "ya Allah.! Amman gskiya naji dadin wannan alamarin allah kuma ya raya min ya kuma shirya ma mai sunan babana albarka “Ameen yaya hisham ya furta a fili fuskarsa cike da tsananin murna. yayi mamaki Kwarai da gaske domin bai dauka zai ji dadi har haka ba shikenan fad’a ya qare atsakaninsu a natse ata ya mike ya nufi hanyar fita waje fuskarsa dauke da murmushi yaya hisham ma ya biyosa kai tsaye dakin mami ya shiga anan ya iske mami da yaranta kaf har da maryam zaune .”
Kai tsaye gadon baby ya zarce ya tsaya shiru yana kallon baby kwance cikin showel haka zalika maryam shiru tayi tana kallonsa yana ta’ba qirjinsa yana murmushi kafin yaya hisham ya kai hannu ya d’auki babyn ya kai masa sumbata a goshi ya mika masa ya karbi baby ya nufo wajen mami ya zauna kusa daita “sweetheart!”ya kira sunanta “naam adamcy nah ran my prince ya dade yayi murmushi jin dadi har dimples dinsa ya lotsa “an dade baa min abinda ya faranta raina ba “haka ne kasan baby da shiga rai ai na lura tunda aka haifi yaron nan kake son shi kai ma allah ya baka naka masu albarka shafa fuskar babyn ya cigaba dayi yana murmushi “babana ,my prince ,my averything cikin murmushi ya kalli mami “sunan babana hisham yasa bansan yadda zan misalta farincikina ba.”
nan take fuskar nana hauwa’u data sauran yanuwata ta bayyana tsantsar farinciki daman burinta kenan sunan babanta amman duba ga shi kad’ai iyayensa suka haifa yasa tayi tunanin sunan abbansa zai sa allah sarki ashe ita zai wa suprise ta kalli yaya hisham tana masa kallo mai dauke da murna da godiya“maryam kuwa ji tayi jikinta yayi mugu mugun sanyi sai taji inama ace nmj zata haifa ba mace ba kai wannnan mutumin ko me zata haifar masa bazai nuna farincikinsa haka ba “ta fad’a a kasan rabata “hisham ya tsallake sunan kowa a dangi yasa na babana bansan yadda zan kwatata murnata ba yau “. hankalin mami gabadaya ta maido kan ata dake zaune rike da baby “lallai wannan abu yayi kyau Allah yayiwa rayuwar ishaq albarka koni naji dadi sosai kuma nasan hajiya zulfa’u ma zataji dadin wannna alamarin kai kowa ma nasan zai ji dadi yaya hisham ya mike ya fita yana dariya byn Kmr second biyar nana hauwa’u ta kwashe kayan baby daaka kawo wa mami tabiyo mijinta d’akin da take jego suka shiga tare ta nufi wordrobe din baby ta bude ta soma qoqarin ajiye kaya .”
Ahankali ya tako zuwa inda take ji tayi kawai ya hadeta da jikinsa ta baya ta juyo a tsorace suka hada ido fuskarsa a sake “meye na wani tsorata bayan kinsan mu kadai ne a dakin “ ?a ganinka bai dace naji tsoro ba?ya daga mata girasa daya lumshe masa idanunta tayi tace “yau ne fa na cika kwana shida da haihuwa “matsota ya sake yi sosai ya hadeta jikinsa “an só !? sai akace kar naji dumin jikin matata ?numfashi ta sauke alokacin da taji ya zame hular kanta ya fara shafa sabon kitson daaka mata kamar wata sokuwa haka ta dawo yayi kamar zai warware mata zani tayi saurin rikewa tana kallonsa ganin yadda ta tsorata ya saki murmushi yana cewa “malama babu abinda zan miki wani naunayen ajiyar zuciya ta sauke “nayi missing dumin jikinki da lip’s dinki bari na rungumeki na rage zafi yana gama fad’ar hk ya hadeta da jikinsa ya kai hannusa ya taro byn kanta ya hade bakinsu waje daya .”
*** Da misalin karfe shad’aya na daren ranar bayan maryamta taga ma komai nata ta dawo parlour’n ta zauna akan kujera hannuta rike da littafin zane tana aikin mr ata duk da tace bazataje aiki gobe ba saboda wulakancisa amman zatayi iyakar qoqarinta taga ta zana masa abinda yake so sai ta mikawa yusura gobe da sassafe ta mika masa ta jima tana zane sai dai bata gama ba acikin biyar uku kawai ta samu damar yi masa a qarshe ta tattara taje ta kwanta washegari karfe bakwai a gidan su yusura tayi mata alokacin yusura na qoqarin futa zuwa aiki bayan maryama sun gaisa da iyayen yusura ta maida hankalinta kanta “ya naga kin biyo ta nan kuma cikin wata irin shiga “?bazani aiki bane yau nazo ne na kawo miki wadan nan zane ki kaiwa mr ata “what ?haba maryama so kike ya tasheni aiki kawai kije ki shirya ki kai masa da kanki ?ai ban gama bane shiyasa nake jin tsoron zuwa ,shine ni zaki tura ni dai gsky Kiyi hakuri gara kije da kanki “yanzu dai bazaki kai masa ba?” gsky ba wai bazan kai masa bane tsoro nake ji maryama ta dauki lokaci tana fama da yusura as ending dai da kyar ta karba da zumar zata bawa madam some sukai sallama
Taron suna akayi a gidan mami mai cike da tsantsar farinciki dan tsabar murna ma mr ata bai je koina ba yayinda duk wanda ya kalli fuskarsa zai san yana cikin farinciki da annashuwa sannan duk wanda yaji sunan da baby yaci sai yayi murna tare da yiwa marigayi alhaji ishaq addua kowa ka kalli fuskarsa farinciki yake banda maryam da gabad’aya tayi wani iri kallo daya zaka mata kasan akwai damuwa atattare da ita duk da mami tana cikin hidima amman hankalinta na kan maryam bini bini zata nemota taga yanayinta ,baby ishaq wanda aka masa lakabi da ashraf ya samu kyaututtuka ta bangaren dabam dabam ta bangaren yan’uwa da kaninsa da kuma bangaren qawayen hajiya zulfa’u dana mami ata ma kyauta yayi masa ta mussaman inda ya bashi takardun gidajensa biyu dake acikin runin gidajensa dake banana estate .”
Zaune maryam take akan kujera a parlour’n umma ta rungume pillow hannuta rike da littafi wanda ya kasance english novel ne tana karantawa domin so take ta cire damuwar mr ata aranta dan tun safe take cikin tashin hankali da fargaba shiyasa ma ta kasa qarasa masa aikinsa dan batasan wainar daake toyawa ba jira take biyar tayi ta kira layin yusura taji ko ta bawa madam some .”knowking din kofa taji ta ajiye littafin hannunta akan kujera da pillow ta mike ta garasa bakin kofa ta bude wata kyakkyawar budurwa ta gani tsaye abakin kofar lokaci daya taji wani mummunar faduwar gaba from know where ya diram mata “ko zan iya shigowa ? budurwar ta tambaya “sunana anifa friend din sadam ko nace tare mukayi karatu dashi haka ma wurin aikinmu daya dashi bana nan nayi tafiya na dawo naji abinda ya samesa”jin haka yasa maryama ta qara sakin fuska sosai tace sannu da zuwa ki shigo daga ciki budurwar ta shigo ta tsaya tana qarewa falon kallo” ya kika tsaya ki zauna mana babu mutsu ta samu waje ta zauna tana cigaba da qarewa falon kallo .”
“Kece matar daya aura “?maryama ta gyda mata kai alamun “eh!allah sarki wai ya wannan alamarin ya kasance ance anemi sadam an rasa amman kuma ke kina raye ?kuma kin cigaba da rayuwa batare da kin cigaba da nemansa ba ko yana raye ko ya mutu?” ya zakice hk ?kin kuwa san irin nemanshi da mukayi ?” munyi iya qaqarinmu ni alokacin bana cikin haiyacina ni dai nasan an binnesa da ransa daga nan kuma bansan komai daya faru ba “okay budurwa ta gyada kanta tana cewa “allah bayyana shi idan yana raye idan kuma ya mutu allah ya jikinsa dan sadam mutumin kirki ne kowa nashi ne sam bashi da matsala banji dadin abinda ya faru dashi ba allah dai yayi masa rahma.”ameen !maryama ta fad’a .”muryarta cike da runi.”
“Amman dai ya kamata kiyi aure zuwa yanzu tunda baya raye .”maryama tayi shiru tana dubanta hakan yasa budurwar tace “am really sorry shawara ce na baki dan naga ke yarinya ce bai dace kice zaki tsaya batawa kanki lokaci ba saboda rayuwa babu tabbas ko yana raye bare baasan a hali da yake ciki ba a mace ne ko a raye “haka ne banji zafin mgnrki ba amman dai na barwa allah komai .”gsky ne kinyi rashin miji mai hakuri da son mutane kai baqarmin sabo mukai dashi ba alokacin muna karatu koda yaushe muna tare har ma mutane suka fara tunanin ko akwai soyayya a tsakaninmu .”
Maryama tayi murmushi kana tace “Amman kuma bai ta’ba bani labari ki ba ?duk wasu abokan karatusa nasani ,haka dayawa abokan aikinsa nasani kece dai gsky ko sunanki ban ta’ba ji ba sai yau shiru budurwar tayi sannan maryama ta cigaba “bari na kira mahaifiyarmu idan zata dawo yanzu ku hadu watakilla ya taba bata labarinki ?” Oh ! bata nan ne ?eh ta dan fita amman bazata jima ba zata dawo zan so naganta dan hasalima akwai abinda ya kawoni saboda akwai aikin project din da muka fara dashi kafin nayi tafiya in fact maryam document din gabadaya suna hannunsa inda zan samu document din gaskiya da zanji dadi sai na qarasa komai idan aka biyani sai nã kawo masa nashi kason tunda tare muka fara .”
“Okay wannan ba matsala bane wani suna ne ajiki sai naje dakinsa na duba miki uhm zakiga sunana da sunanshi maryama ta mike itama budurwar ta mike da sauri “ammm ko zan iya biyoki dan ba lallai ki gane document din ba maryam ta tsaya jim tana mata kallon mamaki kafin tace “tunda akwai suna ai komai zai zo da sauki amman dai muje tayi mata alamar ta biyota da hannunta “maryama tana gaba budurwar data kira kanta da anifa ta biyota basu tsaya akoina ba sai a bakin kofarsa .”
Tsayawa tayi cak qirjinta na bugawa a hankali ta tura kofar dakin ta sanya kafarta daya tana mai jin faduwar gaba tunda aka nemesa aka rasa bata qara shigowa dakin ba ta shigo sosai haka ma anifa abubuwa dayawa sun dawo mata yadda a farko kamar bazai karbi soyayyarta ba daga baya ta juye soyayyar gaskiyar daya dawo yana mata sadaukar wa da yayi a gareta aranar daurin aurensu murmushinsa tabbas matar tayi gsky shi din mutumin kirki ne .”a hankali ta sauke naunayen ajiyar zuciya tana kallon koina a dakin komai nashi yana nan kamar lokacin da yake nan dakin babu dotti da alamun umma na kula da dakin sosai .”
Ahankali suka fara duba wuraren da takardu suke sai dai duk document din da maryama ta nuna mata sai anifa tace bashi bane can ta kalleta “ammmm ko akwai key din wordrobe dinsa a hannunki ?maryama daukowa tayi ta mika mata tare suka bude wani jaka suka gani dan haka suka fito dashi tare suka bude suka fito da takardun ciki gbdy sai dai basu gani ba tarasa yadda zatai can tayi wani tunani dan haka ta kalli maryama “ko zan iya samun ruwa ?ta dafe kanta maryama tayi tana cewa “sorry wallahi na manta ban baki ruwa ba akawo miki juice ko ruwan Kika fi bukata ?kawo min ruwan ma ya isa ok bari naje na kawo miki ta mike ta fita wanda hakan ya bawa budurwa damar kira a waya .”
byn an dauka ta soma magan kasa kasa “na fa duba inda kace amman banga komai ba sai wasu takardun dabam can bangaren data kira akace “ki dai duba da kyau zaki gani anan suke ,wa kika samu a gidan?” “ wannna sakariyar yarinyar , okay shinkenan naji na daina ta fad’a tana ajiye wayar akan gado ta cigaba da dubawa har tagani naunayen ajiyar zuciya ta sauke da karfi ta dauki abinda ya kawota tana mgnr a fili “ya allah na gode maka da baka bari na sha wahala ba “kin gani ne taji sautin murayar ta cikin waya ?eh ! nagani bari nayi masa kyaywan ajiya ajikina kafin ta dawo ta daga rigarta daman akwai bodyhug data saka domin aiwatar da shirita ta nade takardun ta saka acikin rigarta ta maida rigarta ta sauke da sauri sannan ta cigaba dadduba sauran takardun zuwa sanda maryama ta dawo dakin tana qaqarin mika mata cup din ruwa taji sautin magana “me kik jira ne ?ga ruwa taji muryar maryama a gigice ta dago da sauri ta mike tana duban wayarta da mgn ta fito “kina jina Kiyi sauri mana ina kiranki please “budurwa tayi sauri ta dauki wayar tana rage volume ta gefe “wannan muryar fa ? Maryama ta furta a matukar rikice .”
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 13
Jikin budurwar na kyarma tace “wani abokin aikina ne wallahi”ta fad’a a rikice tana maida hankalinta ga wayar “kana jina?” okay gani nan zuwa yanzu “daga haka ta kashe wayar gbdy, maryama tayi shiru tare da zuba mata shayayyun idanunta tana kallonta qirjinta na dokowa da qarfi “tabbas wannna muryar da taji yanzu daga cikin wayarta tasanta kuma ba muryar kowa bace face muryar ya sadam dinta ,jikinta a matukar sanyaye ta mika mata cup din ruwa data kawo mata tana cewa”wanan murya kamar ta sadam ?”da sauri budurwar tace “no! d’an dai kina cikin alhinin rashinsa ne kikaji kamar irin nashi ne amman sam sam bashi bane wannna ,tayi maganar a rud’e zufa na karyo mata .”