Kenza eBookz

Mar'adams book 3 - Chapter 35

Mar'adams book 3 - Chapter 35

Mar'adams book 3 Chapter 35: Mar'adams book 3 Chapter 35. wani irin zafin yaji ya ratsa nashi tafin hannun ita kam ji tayi kamar ya jona mata wutar…

3,201 words

wani irin zafin yaji ya ratsa nashi tafin hannun ita kam ji tayi kamar ya jona mata wutar lantarki ne tayi saurin bude idanunta sai dai ta kasa d'agowa ta kallesa .mr ata yayi shiru yana cigaba da kallon hannunta daya d'an kumbura kafin ahankali yace "kinyi aiki da hannu ne "?uhm amm "nayi amman ba wani mai yawa bane ".ta bashi amsa a diririce tana sauke numfashi, bai tsaya iya hannunta ba ya kai hannusa daidai saitin wuyanta yadda yaji wani abu ya tsalga masa a gabad’aya ilahirin jikinsa itama hk taji dan haka da sauri ta d'ago idanunta da suke a shanye ta tsura masa oly eyes dinta shima kallonta yake sosai ya tsura mata idanunshi masu firgitar da mutum “bayan wannan ciwon akwai abinda ke damunki."?yayi mgnr kamar bashi yayi maganar ba Ikc daya tayi saurin kawar da kanta gefe kmr tayi kuka tace "babu komai ."kinci abinci?"tai shiru yayinda shi kuma ya cigaba da shafa hannunta mai ciwo ,wani iri ta dinga ji ajikinta har tsigar jikinta na tashi wanda a zahiri yake kallon haka "shima wani irin yaji a jikinsa tamkar an jona masa wutar electric yayinda sha"awarta ta soma motsa masa .”

Zazzafan numfashi ya sauke kana yayi kasa da muryarsa sosai “kinga abinda ke had’ani dake bazan ta'ba tmbyrki abu ki bani amsa alokacin ba har sai nã maimata kanta " ya qarasa maganar yana furza mata iskan bakinsa muryarta a raunane tace “kayi hakuri banci ba ."wani zazzafan kallo yayi mata mai dauke da nau'ikan soyayya "ko zan iya sanin dalilin da yasa zaki kai har by this time baki ci abinci ba ?” "bana jin ci ne amman da zarar na koma gida zanci bai sake cewa komai ba ya mike ya fita wanda hakan ya bata damar sauke lafiyayyen numfashi dan muddin ya ta sata gaba irin haka bata samun tayi wadataccen numfashi ,bayan second goma sai gashi ya dawo hannunsa rike da cup fari sol da kwalin biscuit super two ya zauna tare da mika mata cup din tea ya rike mata biscuit din a natse tasa hannunta mara ciwo ta kar’ba tana cewa “na gode !”

ahankali ta kai cup din bakinta shi kuma yayi shiru zaune yana dubanta yana mika mata biscuits cike da tausayawa sannan yana tunanin hanyar da zai fito mata da maganar da take ransa sai dai har ta gama shan tea ta ajiye cup bai samu damar cewa komai ba tace "sir lokaci na tafiya idan akwai aikin da zan maka ka bani sai nayi maka a gida ?"babu sai dai ina son na yi miki wata tambaya idan babu damuwa?” da sauri tace "no babu wata damuwa zaka iya .”ta fad’a haka ne saboda tunaninta ko akan nadiya ne "mahaifiyarki tana zaune acikin gidanku ne ?"taji ya jeho mata tambayar da batayi tsamanin ita zai mata ba ta d’an saci kallonsa kafin ahankali ta gyad'a masa kai alamun “Eh! "shi wancan mutumin gali mai aiki a gidan borodi ." maryama tayi tsam da ranta gaban ta na faduwa da sauri sauri ,sosai ta natsu tana jiran taji mai zai fad'a akanshi "wani irin zama kukeyi dashi ?"muryarta a sanyaye tace “normal muna zaman lafiya da kowa ma "kin tabbatar da abinda kika fad’a ?"ta sake gyada masa kai ya sani ko zaa mutu zurfin cikinta bazai barta ta fad'a masa akwai damuwa ba .”ya sake janyo hannunta yana shafawa yace "me kika fuskanta atattare dani .”?

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 33

Jikin maryama na rawa tace "ban .."ban fahimci komai ba ya d'an yin sama da hannun rigarta kad'an yace "ki natsu sosai maryama ki kalleni ki fad'a min abinda kika gani "jikinta ya sake d'aukar rawa "ni wallahi ban fahimci komai ba sir "uhm !"ya fad'a yana sauke numfashi tare da tsurawa pink lip's dinta idanunsa yana cigaba da shafa saman hannun ta, muryarta na rawa tace "stop sir !"stop what !"? ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi "abinda kake yi ne bana so , “please stop touching my body". ta fad’a tana danne kwalla dake kokarin zubo mata "ya kwantar da muryarsa sosai yace "bakya son ina ta'ba jikin ki? ya tambayarta yana ‘kara bin jikinta da wani shu'umin kallo mai gigita zuciya da sauri tace "eh wallahi bana so "ta fad’a tana qoqarin zame hannunta amman ta kasa dan yayiwa hannun kyakkywan rikon da bazata iya zamewa ba "dan Allah ka sakar min hannu sir bana son kana ta'ba min jiki "ni kuma ina so"ya fad'a kmr bashi yayi mgnr ba, Ikc ma ya sake riko hannunta sosai cikin nashi yana furza mata hucin numafshin sa , "shiyasa kikaji nace mai kika fahimta atattare dani kikace babu komai bayan ni nasan kin fahimci komai "ni allah ban fahimci komai ba wIh “ta fada tana fashe masa da kuka dan zuwa yanzu ta fahimci abinda yake nufi daita so yake ya lalata mata rayuwa ya cuceta ."

mamakin saurin kukanta yake , yayi notice dinta kwatakwata kuka baya yi mata wuya"lumshe tsumammun idanunshi yayi yana saisaita nunfashinsa ,dan buguwar da zuciyarsa take akanta ya wuce kaida ,shi kad’ai yasan me yake ji a daidai Ikc nan, dan ji yake kamar ya fito mata da zuciyarsa taga halin da take ciki akanta ,jin taki daina kukan yasa ya bud'e idanunshi da kyar ya tsura mata kafin ahankali ya motsa lip's dinsa "me ye hk ? ya fad'a yana sake tsareta da tsumammun idanunsa "mai yasa kwatakwata baki jin kunyar kuka?"dole ne nayi kuka nidai dan allah ka daina ta'ba min jiki dan wani iri nake ji " ta qarasa mgn tana turo masa qaramin bakinta gaba, yaji kamar ya kai bakinsa kansu ya fara tsotsa a zahiri ,amman sai ya share yayi murmushin aciki dan shi yasan me take ji ajikinta kuma abinda yake bukata kenan, ta soma jin wani abu akansa shine hanya mafi sauki da zai mallaketa gabad'aya, ya sake shafa skin dinta yana sauke boyayyen ajiyar zuciya ,duk da ya san jikinsa nada tsananin taushi amma sai yaji nata kmr yafi nashi soft kai everything ma ko dan akwai banbancin halitta ne?akwai abubawa ajikinta dake mugun d’aukar hklsa a tare daita wanda a duk Ikc da yayi arba dashi ya kan gusar masa da hklnsa ."

Bai san sanda yayi kusa daita sosai ba yace "fad'a min me kike ji ajikinki "wannan iskanci da kake min wallahi ji nake Kmr kana shafa min wu..."kafin ta qarasa maganarta taga ya tsareta da kwayar idanunshi yana jefanta da wani shi'umin kallo mai rikitarwa ,wanda yasa tayi gaugauwar yanke maganarta qirjinta na bugawa da sauri sauri .ba zato ba tsammanin zai doke mata baki sai jin saukar hannusa tai a saman lip dinta ya bata bal....wanda yasa tai saurin saka hannuta a daidai gurin saboda zafin da taji ya ratsata ta tsura masa idanunta tana kallonsa hawayenta na cigaba da zuba "wallahi mr ata mugu ne na bugawa a jarida ga azabar da take ji gashi yaki sakar mata hannu "dan Allah ka rabu dani nace bana so bana so kana ta'ba ni " ta fada tana bubbuga kafafuwanta a kasa hade da sakin gunjin kuka"kallo ta kawai yake without saying a word to her lallai ma yarinyar nan kurciya na mugun cinta.” Inda mata ke nemansa ruwa a jallo idan akwai abinda yafi wanda yake mata ma suna só da zasu samu dama amman ita dan iskanci ta samun damar har kuka take tana danganta hakan da iskanci ." hannunta ya saki sannan ya mike tsaye yayi taku kamar zai fita don ita a tunaninta fitar zaiyi sai ganin tayi ya kashe light din office din nan take duhu ya mamaye office din ,nan da nan kukan da take yi ya tsaya cak. tsoro ya ziyarceta Ikc daya hankalinta ya tashi shayayyun idanun ta zaro sosai cike da storo sakamakon ganin yadda yake tattaki zuwa inda take zaune ."

da sauri ta mike tsaye tana cewa "sir ni zan wuce gida "karki damu yanzu zamu wuce ."yanzu zamu wuce kuma ?"ta maimaita a fili zuciyarta na luguden bugu "eh zamu kai ki gida ne ko bakya so?" tayi shiru tana tunanin tare da nazarinsa "kin yi shiru ya fad'a yana dawowa gabanta ya tsaya yana kallonta ta d'an d'ago ahankali idanunta sukaci karo da sarkan zinarin wuyansa dake kwance a qirjinsa wani sabon tsoro ya kara dirar mata a zuciya wadda yasa tai saurin sunkuyar da kanta tana runtse idanunta gam "ko kin fi so ki shiga motar hanya kuna gogayya da maza ?"numfashi kawai ta sauke batare da tace masa komai ba ."ahankali ya juya yana maida maballin rigarsa ya kwashe wayoyinsa ya nufi kofar fita tana tsaye kawai taji alamun baya gabanta dan haka tayi qoqarin bud'e idanunta taga har ya kusan ficewa daga cikin office din, tabi bayansa da kallo tana maida numfashi bata san me take ji adaidai wannan nan lokacin akansa ba .”idan tace tasan abinda take ji ko tasan abinda shi yake tattare dashi tayiwa kanta karya ta dai tasan a duk lokacin da tayi arba dashi ya kan gusar mata da hankalinta bazata ce so bane dan bazata jefa rayuwarta cikin matseefa ba dan ko soyayya ne sai tayi duk yadda tayi takicesa aranta bare ma bashi bane .”

Bazata ta’ba wannan ganganci ba shi kuma tasan yafi qarfin ya sota sai dai idan wata manufa garesa akanta idan ba haka ba ina ita ina shi hanyar jirgi dabam ta mota dabam ta sake numfasawa tana tunanin binsa ,ta bishi ne ko kuwa ta kama gaban ta ?" abu daya ne zai sa ta bishi saboda taimakon da zai mata akan nadiya if not bazata sake ganganci binsa ba kuma tasan halinsa muddin taki baqaramin aikinsa bane yace ya fasa taimakonta ."ta kusan mintuna a haka bata motsa daga inda take ba kafin ahankali ta soma taku ta fito ta shiga office dinsu inda kusan kowa ya watse ,wasu tsirarrun maakatan sultan ne suke kai kawo ,ta kai hannunta ta d'auki jakarta dake ajiye akan table ta rataya a kafad'anta tana qoqarin fitowa daga office din wayarta ta shiga qara mara sauti,nan take ta tsaya ta ciro wayar daga cikin jakarta tana duba screen din wayar suannsa ta gani yana yawo ahankali ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta d’aga "hello sir !"dan Allah malama ki fito karki ‘bata min lokaci .""O.."okay sir.."kafin ta rufe bakinta har ya katse kiran.”

jiki a sanyaye ta qarasa fitowa daga office din tana d'aga qafafuwanta da kyar, a tsaye ta ganshi ajikin had’addiyar motarsa bmw fara sol hannayensa duka suna cikin aljuhun won dashi , ganinta yasa ya bud'e mata murfin kofar baya sannan yayi mata alama ta shiga da kwayar idanuwansa,wani yrrr taji a gaba d'aya ilahirin jikinta ahankali zuciyarta ya dinga bugawa da sauri sauri "wannan shine karo na biyu da yayi mata haka ,kuma a gaban masu tsaronsa da direbansa ,ba ita ba hatta masu tsaronsa da direban sa a ruwa sun dasa ayar tambaya akanshi dan duk tsawon lokacin da suka d’auka tare dashi suna masa aiki babu wanda ya samu wannan matsayin bayan mahaifiyarsa gashi karo na biyu kenan yana bud’e mata murfin mota .”ahankali maryama tayi kasa da kanta tana d’ora hannunta d’aya akan d’aya tana d’an jujjuya jikinta alokacin da yake sake mata alamar ta shiga, tai tsam da zuciyarta dake tsinkewa tana sake nazarinsa da kyau."

alamunsa da abubuwan da yake mata suna nuna mata kamar só ne saboda duk yadda mutun yake sonta tana ganewa amman kuma shi nashi salon ne yazo dabam shi yasa ta kasa fahimtarsa da kyau Idan yayi wani abu kamar só sai kuma yayi wani abu kamar sha'wa ,za dai tafi ajiye abun a matsayin shaawa dan ina mutun kamar shi zai sota ?" "me mutun kamarsa zai yi daita ?"wace ce ita ?"waye ubanta a duk fadin kasar nan da har zai sota ita data kasance jinin talakawa ,me yasa zai sota?"kai wanan ma ba abune mai yuwu ba, akwai dai abinda yake nema a wajenta wanda ba sai ta tsaya wahalar da kanta ba tuni tasan me yake so atare daita gara ta kama mutuncin kanta zai fiyye mata alkhairi kuma har abada bazata yarda ta banzatar da budurcinta ba duk wuya duk runtsi tana tare da abunta .”cike da natsuwa ta shiga ta zauna bangaren daya bud’e mata tana mai ra'be jikinta tare da kamkame kayan jiknta tana kallon bangaren da take zaune tana jinsa ya shigo ya zauna a kusa daita bai ra’beta ba sai dai taji idanunshi ajikinta suna yawo wanda ke qara saka zuciyarta tsinkewa tare da mummunar bugu .”

ahkl mota biyu suka fara fita sai motar da suke ciki tabi bayansu sai kuma mota biyu dake biye dasu a natse direba ke jansu, motar tayi shiru yadda bai ce mata qalla ba itama bata waigo inda yake ba bare ma ita bata da abinda zata ce masa ,dan kusan shi ke takalota da magana har suka isa titin Liverpool bai ce uffan ba , anan taga motocin gabansu sun d’auki wata hanya haka ma motocin bayansu yayinda motarsu ta sauka zuwa kasan bridge din Liverpool ahankali direban ke jansu ,tukinsa bai yi slow ba hakazalika ba mugun gudu yake shararawa ba a haka har suka shigo unguwarsu still babu wanda ya cewa danuwansa wani abu ,a ruwa yayi parking a inda yayi jiya yana cewa “ranka ya dade mun qaraso mr ata bai ce masa qala ba illa ya rankwafo zuwa jikinta yana qoqarin bud'e mata murfin motar daga cikin “ya rabbi ta furta tana saisaita numfashinta sakamakon abinda taji ya tsarga mata ai yana barin jikinta tayi wuf ta fito daga mota adaidai lokacin daake kiran sallahr isha'i kafin tayi tattaki ta tsallaka ta karya kwanar da zata shigar daita dogon layinsu taga ya fito bata tsaya ba ta soma tafiya.”

ahankali ya biyo bayanta, idanuwanshi na kanta haka ya dinga binta yana bin duk wani takunta da kwayar idanunshi tamkar wacce ke rangaji haka take ajiye takunta a nutse duk ilahirin jikinta na juyawa ,duk jin kan maryam daya sani da nuna ita wa tace wajen iya gayu da sanyin murya tare da iya tafiya bai ta'ba ganin tayi irin salon maryama ba kai bai ma san mata nada irin wannan salon ba ko don bai kallon mata ne sai maryam din data zame masa dole kuma da ita kad’ai ya zauna bai sani ba , dan shi bai san komai da ya shafi shirgin mata ba tsakaninshi dasu a wajen aiki ne kuma tsakani da Allah shi baya kallon tafiyarsu ." "Wait" ! Kunnuwanta suka jiyo mata muryarsa mafi soyuwar sauti domin dai ko tana so ko bata só zuciyarta ta aminta yana da sanyin murya mai dadi da shiga jiki ,ta tsaya cak ta kasa juyowa zuwa garesa sakamakon abinda ke nukurkusan zuciyarta da ganganr jikinta a natse ya qaraso zuwa gareta ya tsaya a gefenta yana had'a kafad'anta danashi "ta d'an matsa kad’an aranta tace "matsalarsa kenan son jikin matseefa”.

ya motsa lip's dinsa ahankali "karki mata tambayar da nayi miki d'azu a office ,tana jinsa amman tayi shiru "zan baki lokacin nan da qarshen watan nan ina son ki natsu kiyi tunani akaina, bana son idan na tambayeki ki tsaya min inda inda ko kice baki fahimci komai ba ,ko kuma kizo min da wannan banzar kukan naki I can't take it "yana gama fad'ar haka yace zaki iya wucewa zuciyarta na bugawa da matsanancin qarfi ta soma d'aga qafafuwanta wanda take jin sun mata nauyi kamar yadda maganarsa suka mata nauyi acikin kwakwaluwarta ,tana tafiya amman still tana jin idanunshi na biye daita a duk inda tasa qafarta sai dai ta kasa juyowa taga halin da yake ciki a haka ta shige gidansu bazata iya cewa ga adadin lokacin daya d'auka a kofar gidansu ba ."kai tsaye bangaren umma ta shiga kamar koda yaushe Sai dai duk jikinta yayi wani iri umma ta hango zaune ita kad’ai a parlour’n hannunta rike da casbaha da alamun idar da sallarta kenan .” assalamu alaikum “ta furta tana mai qoqarin qarasawa inda take, umma ta amsa mata tana kallonta da kulawa “maryama kin dawo ?”na dawo umma sannu da gida .”yauwa !”ta amsa tana dubanta maryama tayi shiru tana jingina bayanta ajikin kujera har lokacin zuciyarta taki daina bugawa inda ita kuma so take ta saisaita ta dawo normal .”

“Lafiya kuwa maryama naga duk kinyi wani iri “?hawaye ya d’an gangaro a gefen idanunta amman tayi dabarar gogesa “haka fa jiya kika shigo min nayita tambayarki abinda ya samu hannunki kika yi ta wasa da hankalina batare da kin fad’a min ba yau ma gashi kin shigo min wani iri anya kuwa maryama kina son kwanciyar hankalina “?nafi kowa son kwanciyar hankalinki ,babu komai ne yasa yau na gaji ne sannan jiya yankewa nayi yasa kika ganni wani iri “naji kin gaji ne yau shi yanka garin yaya ne ta faru ?”maryama taso sheida mata komai amman dai tayi tunanin ta bari har mr ata yagama mata binciken da yace zai yi mata ta gyara zamanta tana duban umma “ki kwantar da hankalinki babu komai kawai dai sausayi ne numfashi umma ta sauke tace “naji sausauyi ne amman fa kisan bayanshi akwai abinda ke damunki menene shi ?”maryama tayi shiru suna kallon juna da umma tasani dole umma zata damu sakamakon jiya bata runtsa ba zariyar data dinga yi daga dakin zuwa parlour ma kad’ai ya isa ta gane tana da damuwa wacce baa akan kowa bane sai akan mr ata .”

”ina jinki fad’a kinji maryamata baki da wacce tafini nima kuma haka damuwarki damuwata ce haka kuma farinciki farincikina ne .”maryama kam data rasa me zatace wa umma kawai ta fashe mata da kuka “subhallah maryama me ye abun kuka ?”ta fad’a tana riko hannunta maryama ta share hawayeta haka nan ta tsinci kanta da cewa “gaskiya umma na gaji da wannan shegen aikin akwai abinda nake jira da zarar na gama zan daina zuwa wannan dan iskan aikin na huta “nunfashi umma Ta sauke cikin rarrashi tace “haba maryama ki dena iskanta aikin da muke cin abinci dashi kiyi hakuri wata rana sai labari yanzu fad’a me ya faru ?”Umma dan kana cin abunci a k'ark'ashin mutum sai ya dinga wulak'antaka, shima fa Allah ne ya bashi ba wayansa ko dabarar sa ba."hakane maryama amma wasu basa fahimtar hakan, yanzu fad’a min mai kuma mai kamfanin creation yayi miki dan nasan shi ne kawai yake baki matsala ?”shiru maryama tai dan bazata iya fad’awa umma cewar mr ata yana ta’ba mata jiki ba “kawai dai wulakancinsa ne yayi yawa “in dai akan wannan ne ke meye damuwarki in sha Allah wata rana zaizo ya daina “babu rana kullum abubuwansa gaba suke ta fad’a tare da mikewa ta nufi dakinta umma tai murmushi kawai tana cewa “Allah ya kyauta shi kuma Allah yayaye masa .”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull