Mar'adams book 3 - Chapter 37
Mar'adams book 3 Chapter 37: Mar'adams book 3 Chapter 37. Ranta a 'bace ta juya masa baya tana magana da kanta "aikin banza kawai ko ina ruwan mutun dani…
3,259 words
Ranta a 'bace ta juya masa baya tana magana da kanta "aikin banza kawai ko ina ruwan mutun dani ko.."again ? taji sautin muryarsa a bayanta "no sir zanyi magana a fili fili ."ya girgiza mata kai kawai ya koma ya zauna akan kujera yana juyi yana tunanin "taya zai aureta ma da wannan dottin tunanin damuwarta ?”ai dole ya wanke mata kwakwaluwarta fes kafin komai."maryama ta cigaba da tunani tana cigaba da duba kofar shigowa ko zata hango bullowar nadiya amman shiru lokaci nata tafiya har karfe uku ta wuce amman shiru babu ita babu alamunta ya taso daga kan kujerar da yake ya tsaya kusa daita ya tura hannuwansa cikin aljihun wondonsa batare daya ce mata komai ba "ina tunanin nadiya bazata zo yau ba "why do you said that ?"Ka duba lokaci ka gani sir , har karfe uku ta wuce wani mutun ne zai zo by this time akan aikinsa ?"kina ganin abu mai sauki ne mutun ya samu aiki a ATA company yaki zuwa?ni zuciyata ta tabbatar min da zata zo kuma nasan zata zo" allah yasa maryama ta fad'a muryarta a raunane ."
cikin haka wayarta ta d'auki ringing ta duba shima ya dan mika wuyansa yana duba screen din wayar sunan umma ya gani dan haka ya sauke numfashi ya juya ya koma cikin office dinsa "hello umma eh har yanzu ina office tukun akwai abinda muke yi ,aa karki damu in sha allahu zan dawo gida akan lokaci Eh komai yana tafiya daidai babu wata matsala sai na dawo tana gama wayar ta juya zuwa cikin office dinsa "sir !ya bar abinda yake ya tattara hankalinsa akanta tun kafin tace wani abu ya soma motsa lip's dinsa "is almost four :30 pm now har yanzu bata zo ba abinda zaa yi kije office din hisham ki jirani ."tayi shiru tana tunanin wani office kenan "office din karshe kafin muzo nan "okay sir har ta juya ta sake juyowa ta fuskancesa "kana ganin nadiya zatazo yau kuwa gashi ina ganin lokaci na Kure min banason naje gida bakwai ta wuce sir na gode sosai ni ban ta'ba tunanin zaka bata lokacinka akaina haka ba dan naji zuciyata ta yarda cewar dan i kayi haka ba dan wani kasuwancinka ba ,a halin yanzu babu wanda nake jin ya sake samun yarda da amincewa aciki zuciyata kamarka dan allah ka bari na cigaba da jin haka acikin zuciyata saboda naji dadin kulawarka sosai dan kana da kirki matuka , na gode maka sosai Allah ya jikan iyaye aransa yace “ameen! yayinda a zahiri "uhm!" ya fad'a yana tsareta da tsumammun idanunshi yana jin tamkar ya fixgota zuwa garesa . Maryama ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta juya ta fita daga cikin office din zuwa wanda yace ta shiga ta jirasa ,tafiyarta dake rikitashi yabi da kallo tare da yin tagumi yana bin every step of her nan take yaji jijiyarsa ta harba ."
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 35
Ahankali mr ata ya kai hannunsa kan jijiyarsa dake harbawa still yana sake tsurawa tafiyar maryma ido har sai daya ga alamun ta tura kofar office din hisham ta shiga sannan ya runtse tsumammun idanunshi ,gabad'aya yanayinsa ya sauya ,wani irin ajiyar zuciya mr ata ya dinga saukewa da qarfi kana ya bud'e idanunshi yana jin wani irin yanayi a sansar jikina. yayinda gabad'aya tsigar jikinsa suka mike ."ji yayi kamar ya tashi yabi bayanta ya janyota tare da sanyata ajikinsa ya rungumeta tsam ya d'an tsotsi bakinta ko ya d'an samu sausauci abinda yake ji akanta."akaro na biyu ya sake kai hannunsa yana shafa jijiyarsa da take mike sambal ,yana shafawa yana lumshe tsumammun idanunshi at the same time yana sauke numfashi "wayyo allah ina cutar da kaina over akan yarinyar nan ahalin nasan irin matsanancin qaunar da nake mata "I love you so much maryama ,sonki da qaunarki sun mamayeni ina matukar shan wahala akanki yayi maganar fili ."wani wahalallen numfashi ya sake saukewa tare da gyara zamansa yana tura gabad'aya lip's dinsa na qasa cikin bakinsa tare da rikesu da hakorinsa." Ahankali mr ata ya soma qoqarin kawar da abinda yake ji akan maryama dan yayi imani idan bai yi haka ba komai zai iya faruwa a tsakaninsu ya janyo laptop gabansa ya soma duba sakonin da'akayita turo masa ."
maryama kuwa tana gama shiga office din hisham tabi office din da kallon tsanake komai tsaf tsaf gwanin burgewa ga wani qamshin turare mai sanyin dadi dake tashi acikin office din ,sosai office din ya had'u sai dai bai kai wanda mr ata yake zaune ciki ba .ta sauke numfashi da qarfi kana ta qarasa gaban makeken table din ta tsaya tare da rungume hannuwanta duka a qirjinta kafin ahankali ta maida shayayyun idanunta zuwa gefen makeken tabel din inda nan kwayar idanunta suka sauka akan wani qaramin madaidaicin fream mai azababben kyau tayi taku biyu tare da kai hannunta ta d'auki fream din tana dubawa, mace da nmj ne cikin shiga ta alfarma da wani kyakkywan baby, inda gabad'aya hannuwansu ke jikin baby sun bashi kyakkywan runguma ,sunyi kyau sosai kowannensu fuskarsa d'auke da murmushi wanda babu tantama na farin ciki ne .acikin kallon kurullar da takewa hoton ne ta gano irin tsananin kamar da matar dake cikin fream din tayi da mr ata ."tayi shiru kawai tana kallonsu gabanta na fad'uwa kafin ahankali ta ajiye fream din a inda ta dauka ta cigaba da tsayuwa tare da zance zuci"ya Allah kasa nadiya tazo"dan muddin ban yi mata tarin tambayoyin dake cunkushe da zuciyata ba bazan samu salama ba ,matsawar ban ganta ba kuwa zuciyarta zata qare ne acikin wasi wasi ."
mr ata cigaba da duba sakonin mutane ,bayan kamar mintuna talatin da barin maryamah office dinsa ya gama duba sakonin mutane tare da kashe laptop din gabansa ya rufe ya yunkura zai mike tsaye domin dai shima zuwa yanzu zuciyarsa ta aminta da nadia bazata zoba ,sai dai bai kai ga qarasa mikewa ba yaji ana knowking din kofa glass din office dinsa tare da neman izinin shigowa." a natse ya kai kallonsa ga kofar sannan ya koma a hankali ya zauna Inda tsumammun idanunshi na kallon glass din kofar shigowa ,nan take ya fahimce nadiya ce kuma daman yayi wannan tunanin duk da bashi da tabbaci kasancewarsa tare da maryama ne ya hanata zuwa ,sai dai ko wani dalili ne na dabam ."cike da jin isa ya motsa lip's dinsa ahankali yana cewa "coming!tare da yin juyi akan kujerar da yake zaune ta turo kofar ahankali ta shigo tare da maida kofar ta rufe ahankali ta tsaya batare data qaraso gabansa ba ."daga inda take tsaye ta soma magana cike da matsanancin fargaba "ammm so..."am so sorry sir nayi lattin zuwa sakamakon wani dalili na samu sakonku ta hanyar e-mail daga office dinku that's why I came "coming !"ya fad'a yana hade hannuwansa duka ya dafe ha'barsa yana qare mata kallon tsab ."
Jikinta a matukar sanyaye ta qaraso taja kujerar dake fuskantarsa baya kad'an ta zauna a hankali ,a natse ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa dake ajiye akan table ,fuskarsa da zuciyarsa a dake ya soma neman number maryama yana manna wayar a kunnensa,ringin d'aya ta d'aga.yayi magana a can kasan makoshi sannan yayi disconnecting din kiran ya ajiye yace "ko kinzo da takardunki?yes sir! ta fad'a tana sauke numfashi "let me see!" ta mika masa wata jaka baka wanda takardunta ke ciki ,sai daya furzar da numfashi kana ya miko zafafan yatsun hannunsa farare sol ya kar'ba ya bude a natse ya fara duba takardunta yana cewa "kin tabbatar da komai na ciki ? yes sir komai na ciki ta fad'a tana faman kyalle kyalle acikin office din yayinda shi kuma ya cigaba da duba takardunta daya byn daya yana satar kallonta ,gabadaya ba'a natse take ba dan kallo daya mai hankali zai mata ya fahimci bata da gaskiya "sir zuwa yaushe ne zan fara aiki ?"very soon zai iya kasancewa ma next week "ya fad'a yana mika mata takardun tasa hannunta ta kar'ba shi kuwa sai faman kallon kofar shigowa yake yana mamakin yadda maryama ta 'bata lokaci gurin shigowa ."
"Sir na dade rabona da aiki da ATA company ko zan iya samun takardun tsaretsaren ayyukanku na yanzu?"me zai hana zaki samu mana ya fad'a adaidai lokacin da maryaamah ta turo kofar ,ahankali ta shigo ta maida kofar ta rufe ta had'e hannuwanta duka a qirjinta ta rungume fuskarta babu alamun wasa ko tsoro atattare daita ,jin motsin shigowa yasa nadiya ta d'an juya bayanta sai ganin maryamah tayi tsaye tana kallonta, kallo mai tattare da tunhu ma, da sauri nadiya ta mike tsaye jikinta na karkar wa tana kallon maryamah, ido cikin ido suke kallon juna dan sam bata yi expecting zata ganta ba duba da ba'a wannan company take aiki ba , maryama ta soma taku ahankali har ta qaraso kusa daita ta tsaya still kwayar idanun nadiya na cikin nata babu abinda maryamah ke gani alokacin sai tunanin ganinta na farko da taí lokacin da tazo gidansu amatsayin abokiyar aikin sadam yadda komai ke zuwa maryamah haka yake zuwa ma nadiya tunanin maganarta da sadam ne ya shiga dawo mata daki daki alokacin da take bashi labari samun aikinta a ATA company ."
"My heart na samu aiki a ATA company gsky naji dadin samun wannan aikin "ba dadi ya kamata kiji ba ,abun ki tsaya kiyi tunani ne ," me yasa suka kiraki adaidai wannan lokacin cewarsa "idan zaka tuna ai na ta'ba aiki dasu lokacin baya kafin naje kasar Índia kuma naji dadin aiki dasu haka zalika suma sun ji dadin aiki dani ,daman kuma ni bani da wani babban burin da wuce nayi aiki da ATA company yanzu ga dama ta samu sai yanzu nasan na samu aiki mai kyau "babu wani aiki mai kyau da kika samu dan baza kiyi aiki da wannan campany ba". ya fad'a tare da mikewa tsaye ya juya mata baya ,ta kallesa a matukar firgice tana cewa "me kake nufi da bazan yi aiki da wannan kamfanin ba ?ta tambayesa tana dawowa gabansa ta tsaya tana kallonsa ranta a bace "saboda maryama na aiki a d'aya daga cikin kamfanin su " to sai me idan maryaamah na aiki a AGC ? maryama na aiki a AGC ni kuma zanyi aiki a ATA ta ina zan hadu daita ."?
" kaga my heart banason wani rigima yanzu ." kai yanzu ba kamata yayi kayi murna ba zan samu aiki da zamu ji dadin rayuwarmu kafin ka samu naka aikin ba ?"ya matsota sosai tamkar zai shige jikinta dan har masoyan suna iya shakar numfashin juna sannan ya kai hannuwansa duka ya riko kafad'unta tare da kwantar da murya "ina son ki samu aiki mana amman me yasa bazaki fahimceni ba idan ya kasance plan aka had'a miki fa taya zaki kubutar da kanki ?lokacin data kawo nan qirjinta ya dinga bugawa fiyye da kaida ."kafafuwanta suka kama rawa "tabbas zargin sadam ya tabbata plan akan shirya mata gashi kuma tana tsakiyarsa tsundum . ta sake tuna maganar sadam ta karshe " ban amince kije ba amman idan kince lallai sai kinje duk abinda ya biyo baya babu ruwana kuma bazan saka kaina cikin rigimar ba sannan zaki nemini ki rasa rashi na har abada ".duk wannan sharad'in daya gindaya mata da zata fito sai da yayi qoqarin hanata hasalima shine dalilin da yasa bata zo akan lokaci ba dan rigima sukai sosai da kyar ta samu ta fito ."
"I hope that you recognize my face ?" maryamah ta tambayeta tana tsareta da kwayar idanunta masu matukar haske ." muryar nadiya na rawa da zuciyar ta tace "uhmm .." eh na gane ki sosai amman ban yi tunanin zanganki anan ba ." eh dole kiyi mamaki ganina tunda Kinsan abinda kikayi ,amman ni duk wannan bai dameni ba ,akwai tamabayoyin da nake son zan miki a halin yanzu,tambaya ta farko "me yasa kikazo gidanmu amatsayin abokiyar aikin sadam ? nan take gaban nadiya yayi wani irin mummunar fad'uwar kafin daga bisani ya shiga dukan tara tara, zuciyarta banda tsinkewa babu abinda take wani irin tsoro da matsanancin firgice suka mamayeta alakaci d'aya ta nemi dukkanin wata natsuwarta ta rasa kallo d'aya zaka mata kasan bata cikin kwanciyar hankali da natsuwarta ."
"sai tambaya ta gaba me yasa kika bawa wani number wayata ya kirani a tsakar dare nazo aiki da wuri ?"nan ma gabanta ya ba da dammm hantar cikinta ta kad'a "bayan kin rasa wayarki na samu wayarki a hannun wani bayan haka kika kirani domin kiji wayar tana hannun waye da kika ji muryata kikayi discounting din kira me kike nema atare dani ?duk me yasa kika min wad'an abubuwan da kika min ?nadiya tayi shiru ta kasa kwakwaran motsi yayinda jikinta ya cigaba da rawa "ta rasa wace amsa zata bata domin gamsar daita yadda nadiya ke kallon maryama cikin rashin sanin me za tace mata haka mr ata yake binsu da kallo yana mamakin qarfin halin maryama ,yar yarinya daita amman akwai kwarewa da qarfin hali da rashin jin tsoron fuskantar duk wanda zatai magana dashi sai a yanzu ya sake gasgata qarfin halinta ba iya akanshi kad'ai take yi ba ,kuma yayi imani bashi ba duk wanda yayi mata ba daidai ba sai ta saisaitashi tare da yi masa karan tsaye arayuwarsa kamar yadda take qoqarin yiwa nadiya a yanzu "
gabad'aya nadiya ta rasa abun yi domin tana cikin wani irin gigita da tashin hankali wanda bata ta'ba shiga irinsa ba ,ahankali mr ata ya maida kwayar idanunshi sosai ya zubawa maryama kamar yadda nadiya tayi kafin ya juye fuskarsa ya sake had'eta tamau kamar yadda ya saba zuwa yanayi na kamewa da rashin d'aukar raini sannan ya kalli inda nadiya take tsaye cikin tsananin gigita ya bud'e baki ya fara magana "ke... ya kikayi shiru ki bud'e baki ki bata amsar tambayoyinta, dan matsawar baki ba bata amsar tambayoyinta ba lallai bazaki bar office din nan ba idan kuma ya zama lallai sai kin barsa to ki tabbatar a hannun hukuma zaki kasance ."ya qarasa maganar yana kallonta à kaskance "ta waigo da sauri inda yake tana kallonsa a matukar tsorace "yes me yasa kike bibiyar rayuwarta tare da caza mata kwakwaluwa?.bana bibiyar rayuwarta amman a wasu lukuta yana da kyau mu bar wasu abu saboda sirrin dake ciki dan ..."sai kuma tayi shiru ta kasa qarasa maganarta "ko babu komai bazata fad'a masu abinda zai yi sanadiyyar rasa sadam arayuwarta ba domin shi din muradin ranta ne da soyayyarsa aka halicci zuciyarta kuma tayi imani sadam na matsanancin sonta ."
"me kike kokarin kice nadiya ?kinga karya bata da wani mahimanci arayuwar d'an adam bana bukatar kiyi min karya dan girman allah idan Kinsan wani abu akan yaya sadam ki fad'a min bare ma ni jikina yana bani kina tare dashi "what !"yes abinda kika ji shine abinda na fad'a "sadam fa kika ce ?"!nadiya ta furta sunansa tana duban maryama ?shifa fa ?"inji cewar maryamah "idan har sadam yana tare dani ai da tun tuni na kawo muku shi koda kuwa acikin halin hauka yake ko wani abu makanmanci haka idan kuma akan muryar da kika ji ne a waya kisani wannan muryar ba muryar sadam bane muryar sabon saurayina ne da zan aura ne ta fad'a tana saisaita natsuwarta tare da hura mata hanci amman dai zan fad'a miki wani abu domin nasan sadam bazai ta'ba fad'a miki tsakaninmu dashi ba ."nida sadam mun kasance masoyan juna ne mun had'u dashi a shekarun baya a makaranta ."
"abubuwa dayawa sun shiga tsakanina dashi tare da alqawarin aure byn nayi tafiya zuwa kasar india na samu labarin aurensa da mutuwarsa nayi matukar gigita da jin aurensa kuma naso da zarar na dawo kasar na maka shi a kotu .nan take maryam ta shiga wani sabon tashin hankali mai tsanani ta koma ta jingina jikinta da glas wanda shine madadin bango acikin office din tana cigaba da kallon nadiya cike da tsananin tashin hankali "."Ina ta qoqarin shirya yadda zan maka shi a kotu domin kwatarwa kaina hakina kwatsam sai kuma naji labarin mutuwarsa tsayawa fad'a miki irin tashin hankalin dana shiga maryama bata lokacin ne saboda ina mutuwar son sadam son da bazan iya bar ma wata halitta ba"
"actually akwai wasu hotunan da mukayi dashi kafin na bar kasar nan ,idanun maryamah ya cika da ruwan hawaye shi kuwa mr ATA jira yake nadiya ta gama maganarta ."nayi imani wadan nan hotunan suna cikin dakinsa kuma duk da baya raye zaa iya ganosu cikin sauki shine ma dalilin da yasa na dawo saboda banason kuga munin hotunan da mukayi dashi dan ya sha bani labarin yadda kuka yarda dashi kuka aminta dashi muddin kuka ga hotunan mu tare cikin wani yanayi kwarin gwiwarku akanshi zatai sanyi."hawaye masu zafi suka zubo akan kuncin maryama lokaci data ta tuna ranar data kamasa yana amsa wayar mace "banyi niyyar fad'a miki ba saboda nasan zakiji ciwo sosai acikin ranki amman wallahi wannan shine dalilin zuwana gidanku har na bukaci nabiki dakinsa sai dai a ranar ban samu naga hotunanmu ba shiyasa nayi tunanin sake dawo da daddare . lura da nayi idanunki biyu kina aiki yasa na kiraki tare da canza murya ni kaina lokacin zuciyata a tsorace take saboda banason kiga private pictures dinmu shiyasa nayi duk abinda nayi na kwashesu dan allah kiyi kokarin ki fahimceni amman fa kisani mijinki sadam ya yaudareni matukar yaudara ."
"maryamah sadam yaci amanata na yarda dashi na mika masa ragamar rayuwata amman ya watsar da yardar da nayi masa saboda bai fad'a min cewar zai yi aure ya barni ba ."na tafi kasar india da zumar idan na dawo zamuyi aure dashi amman sai labarin aurensa kawai naji yayi aure intakaice miki ana gobe zaa daura aurenku munyi waya dashi daace zaa ga wayarsa to da kin tabbatar da duk abinda na fad'a miki wata killa da zuciyarki ta buga sakamakon abinda zaki gani domin abubuwan dake tsakanina dashi ko Ke da kike matsayin matarsa bana tunanin kunyi irinsa dashi ."Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun maryama ta dinga furtawa acikin ranta hawaye na zuba akan kuncinta masu radadi da ciwo."
Yayinda zuciyarta ta dinga mamakin maganganun nadiya akan halittar data yi imani bazai ta'ba aikata hakan ba domin itama ta yarda dashi "maryama ki daina mamakin ,bazan ta'ba daina mamaki ba nadiya har sai naga sheida akan hakan yanzu ga wayarki a hannunki nayi imani idan har zaa samu hotunanku a wayarsa ko katin hotunanku to lallai zaa iya samu a wayarki tunda kuna tsananin son juna bai zama lallai ku iya rabuwa da hotunan juna ba "wannan haka ne maryama nadiya ta fad'a tana goge nata hawayen sannan tana qoqarin bude wayarta domin tabbatar mata da gaskiyar data bukata hotuna guda biyar ta nuna mata kuma duk suna tare da sadam babu kayan kirki ajikinsu cikin yanayi na tsananin soyayya "kadan ne wannan maryama ,kinga bazai yuwu na bar wayata a hannunki ba duk da nasan ganin wadan hotuna zasu miki wuya allah dai ya jikan sadam kawai ni zan wuce ta d'auki jakarta ta rataya ta fice daga office din ."