Mijin malamah by nimcy luv - Chapter 13
Mijin malamah by nimcy luv Chapter 13: Mijin malamah by nimcy luv Chapter 13. MIJIN MALAMA Paid book ne. Book 1 and 2 1kne 08119237616 [8/4, 5:30 PM]…
3,945 words
MIJIN MALAMA Paid book ne. Book 1 and 2 1kne 08119237616 [8/4, 5:30 PM] _KHADSALT_🌹💞: 16 Maganganun Imran su ka yi wa Majeederh dirar mikiya a kunne. Duk yadda take so tayi shiru ta kuma daure amma har zuciyarta ta kasa yin hakan gani take da zarar Imran ya fasa aurenta babu wanda ya yi saura zatai ta tabbata a gida. Majeederh ta runtse Idanunta a hankali cikin muryar dake nuna zallar abin da zuciyarta ke buƙata ta ce "Imran ba tsofa na yi ba, am just 20, na fi kowa kyau a gidanmu" ta ƙare maganar tana sanya duka hannunta tare da dafe kanta dake juya mata tana ganin komai bibbiyu. Imran ya miƙe ƙafafuwan a saman office ɗin shi idanunsa buɗe cikin isgili ya cewa Majeederh. "Tsari na ne haka, ina son auren macen da bata haura sha bakwai zuwa takwas ba, lokacin da na zo neman aurenki wanne irin rashin mutumci ne ba a nuna mini ba? Ko an faɗa miki ke kaɗai ce mace Majeederh, ki je kici karatu daman ni wayewar ki tsoro take bani karatunki ya yi yawa" ya juya kaɗan sbd ya ƙara sanyawa zuciyarta dafi, dafi irin wanda ta sanya masa, domin har ranshi yana ƙaunar Majeederh a shekaru biyun da suke shige "Ki roƙi Allah kada ki tsofa a gida, domin darajar mace gidan mijinta gadai ƙannenki....," “....Stop it, ya isa..” Ta kashe wayar da sauri tana zubewa a gefen gado, ta kasa tantance wanne kalar yanayi zuciyarta ke ciki, da gaske ta tsofa ko kawai faɗar Imran ce? mene abun iliminta na addinin? Ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta tana ambaton sunan Allah. Aure take so da gaske yanzu ta fahimta kuma shi ne dalilin da yake sawa tayi azumi domin riƙe kanta. Tana jin wayarta na ƙara ta shareta domin babu wanda zai kirata idan ba Latifa ba, mai kiran nata al'amuran bikin Widad ya sha kanta. Sai da ta kwashe adadin mintina kusan goma kafin ta ji sauƙin zuciyarta, ta miƙe a hankali tana cire kayan jikinta kai tsaye bathroom ta nufa ta yi wanka tana fitowa ta goge jikinta tare da zura night wear masu ɗan kauri sbd sanyin hadarin dake fusawa, ciwon Limoniyarta yana ƙoƙarin tashi, bata jin daɗin komai rayuwar tayi mata juyin wainar tan da wannan shi ake kira da gwara na yi bara a bulayi yin bara a kofai. Jikinta sai fitar da ƙamshin Nivea men active clean shower Gel yake. Ta juya kaɗan tana jan pillow ƙarar ƙofar da ta ji ya sa ta yi saurin rufe Idanunta tana jiran ta ji wannan karan kuma mene? Waye kuma?. Mami ta dubi Majeederh tana sakin murmushi ta ce "Hawwa'u shiru ke ɗaya? Sau zan faɗa miki ki daina zama haka, bakya gudun abin da zai taɓa lafiyarki 24hrs kowa na shira banda ke rayuwa za tayi haka?" Majeederh ta lumshasshun Idanunta kamar tana jin bacci so romantic domin gabaɗaya idan bata yanayi na jin daɗin zuciya shagwaɓewa take kamar ba ita ce babba ba, bata taɓa riƙe da nuna shagwaɓarta ga abin da take so. "Ina magana ki na ji? Oh! Ni Asabe Allah ya ye miki wannan miskilanci maza tashi ki kwashe kayan dinner ɗin can" da tsananin mamaki wanda Majeederh ta kasa shanyewa ganin ita ko hannu bata saka cikin abinci ba. A hankali cikin jan idanunta tana lumshewa ta ce "Kaya? Dinner?" Ta furta cikin sanyin murya wacce take always cool and so romantically. "Eh, abincin da su Rumana da Raihana suka ci, naga gabaɗaya suna wajan fira sun yi baƙi ke kuma babu abinda ki ke sai zaman banza, to tunda suna wajan mazajen da za su aura ai ke sai ki yi aikin gidan" Tunda Mami take magana Majeederh ta zuba Idanunta wanda suke farare tas kamar madara. Rayuwa kenan! Zamani riga duk shekaru data bawa su Ruma amma yau ita ake cewa ta kwashe kayan abincin da suka ci sbd suna wajan samari duk sanda su kai aure bata san mene zai iya faruwa da ita ba. Bata ce komai ba ta miƙe tare da ɗaukan hijabi ta saka Mami ta ce "Allah dai ya yanke kazar wahalar nan, ya kawo ƙarshen zamaninki bana iya bacci sbd tausayinki yanzu ke babu wani daya taɓa cewa yana son ki da aure?" Ba tare data kalli Mami ba tayi gaba tana cewa "Babu" Washegari da wuri Majeederh ta tashi sbd daman tun Subhi idanunta biyu dalilin azumin data ɗauka ta gyara gidan bakiɗaya, tana cikin haɗa breakfast Aaliyyah ta fito tana murza Idanunta ta ce "Good morning Anti Jeederh" bata kalleta ba sai data gama haɗa kunun gyaɗar ta juya tana harɗe hannu a ƙirji tana juya idanunta da suke ɗauke da ruwa kamar mai shirin kuka. Sai kawai ta girgiza kai tare da juyawa tana faɗin "Ki haɗa a parlour" she said. "Ok Maah" A parlour Majeederh ta samu Ruma na waya tana ganin Majeederh ta ce "My Imran ga Anti Jeederh ku gaisa" "Antynmu, ok give her the phone" Imran said. Ruma ta miƙe tana bawa Anti Jeederh wayar ta ce "My Imran zai magana da babbar yaya, yama ce mini wai zai haɗaku aure da ƙanninsa idan Muzayyid ya amince" Majeederh tayi jim she was so speechless. Sai kawai tabar parlourn Idanunta rufe zuciya babu daɗi. Kaya ta sauya cikin Nidha abaya dark blue tayi rolling da babban vail kafin ta ɗauki kyakkyawan liƙab ɗinta ta sanya, gabaɗaya yau ta kasa jurewa dole ta isa gare shi, shi ke ɗauke mata kewa. Ta samu Abbu a parlourn shi ta tsuguna har ƙasa ya amsa yana cewa. "Ya maganarmu dake?" Ta yi shiru ta kasa cewa komai. "Zan iya ɗaukar shirunki matsayin amsa" "Abbu ka zaɓa mini ko waye, na amince zan aure shi" “…. Karatu na zaɓa miki, ki je nan da shekaru uku zuwa huɗu sai ki aure kafin nan kin kammala karatu" Ta runtse Idanunta bata san amsar data bawa Abbu ba sai tsintar kunnenta tayi ta jin yana cewa "Allah ya yi miki Albarka, su dai bar su suyi auren tunda shi suka zaɓa" Fitowa tayi bayan tayi sallama da mutanen gidan kanta a ƙasa tana rungume da ƙirjinta tafiya take a hankali mai cike da nutsuwa da kamala, ilhamarta ta gama bayyana gidan karamcin data fito, tare da tarbiyyar da take da shi. Napep ta tsayar ta shaida masa inda zata, tunda suka shiga kanta ke sunkuye lokaci zuwa lokaci mai napep ɗin ke kallonta ta cikin madubi har ya isa bakin gate ɗin data shaida masa. "Mun iso" ya ce yana karkaɗe kujerar da yake kai da dosta. Shirun da ya ji yasa ya juya mamakin yadsuta zuba tagumi Idanunta rufe yake yatsun hannunta kawai ya kalla yasan za a zuba kyau kuma Ubangiji ya gama tsara halittar shi a jikinta. Ya ce "Malama mun iso" Majeederh ta yi saurin buɗe Idanu, domin sunan da ɗalibanta na makarantar Ahlul Madar suke faɗa mata kenan Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Ya saki murmushi ta cikin liƙab tare da fitowa tana ɗaukar jakarta ta bawa mai napep ɗin guda ɗari biyu. Ya ɗauki hamsin ya bata ta kalli hamsin ɗin ta ce "100 ne" "Tab,Yoo maganar da kike wazai kawo ki nan a ɗari inda aka ƙarawa litar mai kuɗi" bata iya musu ba ta juya tare da nufar gate ɗin da aka rubuta. *"An orphanage for young children"* Ta faɗaɗa murmushinta tare da ɗan ƙarawa tafiyarta sauri zuciyarta sai janta take Idanunta ya kwaɗaitu ta son ganin abin da su kayi kewa. Kewarta ya yi mata jagora har zuwa office ɗin Akeeth. Yana ganinta ya miƙe tsaye with so much respect na tarin iliminta bawai don ta girme shi ba ya ce "Your wlcm Majeederh-khan" ta jinjina kai tare da zama kan kujera tana rarraba Idanunta dake cikin liƙab, Akeeth ya ce. "Bar gaigaye za kici tumu ne" "Uhm" ta furta ta ɗauki Wayarsa ringing ɗin farko aka ɗauka Akeeth ya ce "Come with him" Ya kashe kiran yana kallon Majeederh yadda take kallonsa yasa ya fahimci me take nufi ya ce "She's goode, but she's trouble Maker very stubborn boy" "....Am very sorry for that" Majeederh said. Tana haɗe hannu waje guda alamar ban haƙuri. Akeeth ya watsa hannu baya ya ce "Is there nothing serious, kawai har yanzu bai sauya ba" Ya gyara zama sosai cikin fahimta ya ce "Baya jin magana, ya yi ƙanƙanta da irin trouble ɗin da yake haɗa mana, he just Five years amma fitar shi ne sai shi, baya ɗaukan karatu da muhimmaci" Majeederh tayi shiru kawai domin bata san me zata ce ba, bawai don ta rasa ba, sai don bakinta ya yi mata nauyi harshenta ya harɗe bakiɗaya. Tun kafin ya shigo jikinta ya bata yana tsaye a ƙofa ta juya da ɗan sauri ganinsa tayi tsaye daga shi sai gajeren wando na Adidas sai wata ƴar shirt mai photon lion a gaba wacce ka yaga masa ita ta baya, jikinsa futu-futu. Kan nan na shi gabaɗaya a cure fatar shi haƙa ƙarin, ta dube shi suka haɗa idanu da gudu ya ƙarasa wajanta cikin farin ciki da murn ya faɗa jikinta yana cewa "Mamina, ƴar madara" Faɗa zata yi masa amma jin yadda yake sauke ajjiyar zuciya a jikinta ya yi lamo tare da ƙanƙameta ya sa rauni ya bayyana a tare da ita, rauni irin na uwa da ɗanta ta lumshe idanu tana shafa sumar kan shi "Little" "Ƴar Madara" Ya ce yana rufe Idanu tasan tunda ya ce Ƴar madara bai ce Mamina ba to fushi yake da ita. Akeeth ya ce "Majeederh ni banga cancantar riƙe shi a wajanki ba, duba da cewa ke ba aure gareki ba, kuma idan kika duba yanayin society ɗinmu akwai wasu abubuwan da idan mutum mara aure ya yi shi musamman ɗiya mace za a fara yi mata wani irin kallo nada ban, tunda mutane basa buƙatar bincike kafin making decisions zuwa zatar da shi, kawai the only thing da suka iya yaɗa jita-jita da ƙanzon kurege, You have to be very careful" "I'll, but" ta yi shiru daga maganar. "But what? Open your heart Mrs Khan" Majeederh ta ce "About his family?" Akeeth ya ce "Oh Yes! Babu wata amsa gamshasshiya wacce bincikenmu ya nuna, na faɗa miki a bakin masallaci aka tsince shi a shekaru uku da suka gabata,zan ci-gaba da bincike komai ake ciki I'll let you know" ta jinjina kai Akeeth yana ta son ko sau ɗaya ne yaga fuskar Majeederh amma ina. Ta miƙe tsaye tana riƙe da hannun Little. "Thank you!" "Always Wlcm" fita su ka yi har bakin gate tana kallon yadda Little yaƙi ce mata komai, alamun ya yi fushi sosai ta duba hamsin ɗin da tayi saura a hannunta sai kawai ta bawa mai ice-cream na kan hanya ya bata na hamsin ɗin ta kalli kyakkyawar fuskar shi wacce ta kasa bayyanar da asalin yare ko ƙabilar daya fito ta ce "Take Little, Mami ce am sorry muje gida na baka chocolate" ya buɗe idanunsa ya ce "Ƴar madara" ta dungure masa kai, ganin daga gidan marayun zuwa gidansu akwai tafiya ya sa ta durƙosa tare da cewa "Hau baya, sweetheart" da sauri ya haye bayanta ya maƙale hannunsa a ƙasan ƙirjinta....
MIJIN MALAMA Paid book ne Book 1 and 2 1kne Pay....08119237616 [8/4, 5:30 PM] _KHADSALT_🌹💞: 17 Tafiya suke a nutse duk da ya yi mata nauyi a baya shekarun shi biyar a duniya amma yana da girma jiki ga shegen wayo. Ya ƙara shigewa bayanta ya ce "Mamina" "Little babe" ya leƙo ta gefen fuskarta ya ce "Mamina ke baki da mota? Me ya sa baki zo wajena ba, me ya sa kike mini faɗa ai nayi ƙarfi duka nakewa yara, I will fight, and I will win" Murmushi kawai ta yi masa a zuciyarta tana mamakin yadda da yawan lokaci turanci ke zama a bakin shi, bai ci ace daga fara karatun shi ya fara turanci har haka ba. Jin ta yi shiru ya ce "Get me down, Mami" "No, little ba zaka iya tafiya ba" ya fara buga ƙafa a bayanta tare da ƙoƙarin sakin kuka. A hankali ta tsaya tana mai da numfashi kana ta sauke shi a ƙasa ya yi mata murmushi yana rufe Idanu tare da suɗe baki na daɗin ice-cream. Gani tayi ya durƙosa a gabanta ya ce "Ni ma zan rama muki, haka muke a school" "What! wa zaka goya?' Ya tura baki gaba ya ce "Ke Ƴar madara, ai duk wanda ya goyaka kai ma kai masa haka ko Mami?" Ta tsora masa idanu surutun shi na bata mamaki ƙwarai ta sunkuya daidai tsayin shi ta shiga kaɗe masa gasar jikinsa tana shata samar kan shi daya hana a aske ta ce "To ai uwa duk abin da ta yi wa ɗanta daidai ne" "Kyautatawa nada daɗi kin ce Mami?" Ta jinjina masa kai cike da jin daɗi tana faɗin "Shikenan ka bari idan ka sake girma ka goyani" ya dinga tsalle da murna zai goya Maminsa ƴar madara. "Promise?" Ta miƙa masa hannu ta ce "Promise" ta kama hannunsa suka cigaba da tafiya tana jin zuciyarta daɗi ga wani farin ciki yau zata kwana da Little daman sabgar shagalin musabaƙa ya sanya ta kai shi can tunda ba kowa yake kula da shi a gidan nasu ba. Tun daga can har gida suka ƙarasu a ƙafa suna tafe yana mata surutu wasu ta gane wasu kuma kamar wani yare nada ban haka yake. A daidai ƙofa Majeederh taci karo da Latifa taja baya tana ƙara riƙe hannun Little dake ƙoƙarin tafiya wajan daya hango yara age mate ɗin shi suna faɗa. "Yanzu na shiga ake ce mini bakya nan" cewar Latifa. Ta lumshe Idanu cike da gajiya ga azumi don ma rana ta fara sanyi a gajarce ta ce "haka ne" Latifa ta ce "Ki ce ɗan rigima kika ɗakko daman tun da mu ka yi waya nake son tambayarki shi sai kuma naga you're not on the mood na share" Majeederh ta ce "Ayya, muje" suka shiga cikin gidan a tare tana shiga ta jiyo muryar Uncle Isma'il ta faɗaɗa murmushinta tana sakin hannun Little ta shiga parlourn Abbu. Uncle Isma'il ne da Uncle Bello suna zaune suna tattaunawa akan maganar Widad da kuma kuɗin Ruma da za a kawo. Ya Uncle Bello ya dubi Majeederh ya ce "Hawwa'u an dawo? Yanzu ake ce mana bakya nan" ta sunkuyar da kanta ƙasa cike da ladabi ta ce "Eh Uncle, an yini lafiya" "Allahamdu lillahi" ya bata amsa yana mai jin tausayinta har ranshi sbd zurfin ciki da take da shi ga yadda duk al'amarin rayuwa yake jirkice mata. "Uncle..," Uncle Isma'il ya yi saurin ɗaga mata hannu cike da ɓacin rai da damuwa ya ce "Kin kyauta tunda tsarin da ki kaiwa kanki kenan, ba bu abin da zamu iya ikon ki ne ke kike da kanki Hawwa'u" zuciyarta ta buga tsoro da fargaba suka risketa a wannan lokacin idan aka tsaga jikinta ba lallai a samu jini ba sbd tsabar fargaba. Amma sam fuskarka ko yanayinta bai nuna hakan ba. Cikin sanyin murya ta ce "Me nayi Uncle?" A hassale kamar zai daketa ya ce "Ni kike tambaya me kika yi ko Hawwa'u? Yanzu yaron nan Imran kwanaki yazo yana son ki har iyayensa ya fara yunƙurin turawa, ban san mene ya faru ba naji maganar shiru, yanzu kuma na samu labarin zai kawo kuɗin Rumana na tambayi Abdul'aziz ya ce da kanki kika cewa Imran bakya son shi kada ki sake ganin ƙafar shi?" Duk da sanyin shigewar hadari bai hana Majeederh jin wata zufa ta yanko mata ba, daga ina wannan al'amarin ya bayyana waye ya shirya mata maganar da bata san da ita ba, waye yake shirin wargatsa burinta?. Ta kasa cewa komai yawun bakinta ya maƙale ga ƙishin azumi ganta ya shiga juyawa. Uncle Isma'il ya gyara zama domin ya fi kowa zafi akaf familyn Khan. "Duk abin da ya faru ki kuka da kanki, ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka, itikafi rayuwa kaɗai zai sanya ki kai kanki tubalin tundun mun tsira, idan ba sukike rayuwar duniya ta baki naki kason ba, ina cewa akan idanunki aka haifi Widad? Sa'ar Aaliyyah ce amma aurenta za ayi, akan idanunki aka haifi Du'a Yaronta ɗaya ciki ne da ita yanzu, shi ne kin samu mijin aure zaki wasa da damarki akan wani karatu? Anya lissafi da burin zuciyarki da kwaɗayin ganin kin samu wadatacce ilimi ya miki adalci? Hawwa'u aure da haihuwa da arziƙi na Allah ne, kuma lokaci ke wanzar da samuwar su kada ki rufe idanunki akan wani abu wanda bashi da wani muhimmaci, ke ba a bin kunya bane ace saurayin da yake son ki ya koma wajan ƙanwarki, baban abin takaici ma wai ke ce da kanki kika lamumce masa auren Rumana, Goodness what noises? Meke damunki ne?" Majeederh ta fara shiga ruɗani da fara kokwanto anya ana sonta a gidan? Me ya sa ake shirya mata abin da bata sani ba? Ta ɗago kai a hankali tare da zare liƙab ɗin kanta, fuskarta ta yi jajur cikin muryarta mai sanyi kamar wacce take shirin yi musu shagwaɓa ta ce "Uncle ka yi haƙuri, ka zaɓa mini mijin ko a gobe ne" Rashin sani ya fi dare duhu, rashin sani baƙo ya sha ruwa wanka, sun kasa fahimtar ita kanta a ɓukace take da yin aure, babu abin da take sha'awa irin ta ganta gidan mijin babu abinda ke birgeta irin ta juya taga nata mijin a gefenta. Uncle Bello ya numfasa a lokacin ya ce "A'a ba ayi haka ba, ai darajarki da kimarki ta shige a nema miki mijin aure, kaf yaranmu ba wanda muka sadakar ko zaɓawa miji ba zamu fara a akanki ba, kin yi kuskure tun farko sai ki gyara ki je Allah ya zaɓa mafi alheri" Uncle Isma'il ya ce "Wallahi kin ɓata rawarki da tsalle Majeederh iliminki bai amfana miki da komai ba....." "Uncle Mami na kakewa faɗa?" Siririyar Muryar yaron ta tsayar da Uncle Isma'il daga yin magana. Sai a lokacin Abbu ya ɗaga kai ya ce "To rasai yanzu za a san ka dawo, ko zaka rama mata?" Little ya dinga kallon Uncle Isma'il yana huci idanunsa suka kaɗa tare da yin jaa wata kalar zuciya ce da yaron kamar kuturu ya shiga surutu a ranshi bakinsa kawai ke motsawa. Cikin sauri Majeederh ta kama hannun shi ta ce "Say sorry to him" ya yi shiru idanunsa ƙuri akan Uncle Isma'il ganin yadda ya sanya Maminsa a gaba yana mata faɗa gashi har fuskarta tayi jaa daman ta haka yake gane kukan zuci take. Majeederh ta finciko Little ta ce "Ka bawa Uncle haƙuri" ba tare daya kalleta ba ya ce "He is shouting at you" "He's my Father, am i your mother, na ce ka bashi haƙuri, say sorry to him" ya kafe yaƙi cewa hannu Majeederh ta ɗaga hannu ta zabga masa mari nan take yatsun hannunta ya bayyana a fuskar shi duk da kasancewar fatar shi baƙa. Cikin ɓacin rai ta jawo shi har gaban Uncle domin gani take idan bata hukunta shi ba a haka zai tashi da rashin kunya da shiga sabgar da babu ruwan shi. “....Say sorry to him..” "Uhm, Allah ya shirya ya kyauta, tun baki haifi naki ba kin fara dakon wahala Majeederh?" Cewar Uncle Bello Abbu ya ce "Hankaka mai da ɗan wani naka kenan, kin kyauta kina riƙe wanda yake zagine yayyina" Idanunta ya kaɗa sosai ta ce "Don Allah Uncle ka yi haƙuri ba zai sake ba" Ta miƙe tana kama hannunsa lokacin Latifa ta gaji da jiranta har ta tafi gida. Ta samu Aaliyyah ta dawo daga makaranta tana shirya abincin rana lunch. Raihana na zaune ana waya da saurayi. Babu wanda ta kula sai Aaliyyah dake cewa "Sannu da dawowa Anti Jeederh" ta shige ɗaki tana jinjina kanta alamar "Yawwa" suna shiga ta saki hannun Little tare da ɗakko bulala ta waya ta kama hannunsa ta zirara masa guda ɗaya "As form today na ƙara jin kayi magana da babba sai jikinka ya faɗa maka" ta ƙara zirara masa hannun ya taro jini amma bai motsa ba sai cewa ya yi "Faɗa ya miki ƴar madara" Majeederh ta ware Idanu tama rasa me za tayi sai kawai ta miƙe tare da shigewa Bathroom tayi wanka da Alwala ta wanke fuskarta sosai har jan fuskar ya daidaita domin ta fahimci sauyin fuskarta yake sawa Little ya fahimci halin da take ciki, bata taɓa ganin yaro mai fikira da shegen wayo kamar shi ba ga ɗan banzan wasa da shiga faɗan da bana shi ba. Duguwar riga ta sanya ash ta saka hijabi a kan idanunsa tayi sallah har sallar Asr tayi Asstagafirullah na lattin da tayi kana ta fara azkar na yamma ta dube shi fuska a haɗe ta ce "Sallah" da sauri kamar zai kifa ya shige bathroom. Babban abin da yake bata mamaki kafin ya yi sallah sai ya duba ko'ina yaga ita kaɗai ce a ɗakin yake yi jikinsa har rawa yake sbd tsoro ta rasa dalilin haka. Yana idarwa ta dawo kusa da ita a hankali ya ce "Sorry Mami" Tayi shiru fuska haɗe sosai ya marairaice ya ƙara cewa "Sorry" Sai a lokacin ta ce "Uncle zaka bawa" ya maƙale ka faɗa ya ce "I hate him, faɗa yake miki" wata kalar tsawa ta daka masa tare da nuna masa waje ta ce "Out" Dai-dai lokacin Aaliyyah na shigowa ta ce "Mun shiga wannan tsaiwar ai ta sa na kusa sakin fitsari a wando, wai little kikewa tsawa haka?" Idan Majeederh ta gini ya motsa Majeederh ta motsa. Aaliyyah ta ja hannunsa suka fita yana tirjewa shi a wajan Majeederh zai zauna duk da tsawar da tayi masa. Har akai sallar Magriba Majeederh ta sha ruwa tai sallah Idanunta bai ƙara ganin Little ba, a wajan Mami take ji wai ko abinci yaƙi ci ya fito waje sun yi faɗa an fasa masa kai. Sosai tai mamaki babu yadda za a yi aci galaba akan Little a kullum ita take bada haƙuri ta tabbatar hakan baya rasa nasaba da faɗan da tayi masa. Tana son ta tambayi yana isa amma girman kai da nauyin baki irin na Majeederh sai kawai tayi shiru. Cikin dare wajan ƙarfe ɗaya taji saukar numfashi a jikinta, Numfashin mai ɗauke da zafi da buɗe Idanunta da suke ciki da bacci ganinta ya sauka akan Little dake rawar sanyi kayan safe ne a jikinsa har yanzu ta buɗe ido da kyau tare da taɓa wuyansa jikinsa zafi zau bakinta har ɓari yake ta ce "Little, little" ya buɗe ido yana ganinta ya ce "Sorry Jee Mami" bata kula shi ba ta ɗauki paracetamol na ruwa tare da ɗora shi a cinyarta zata bashi maganin ya girgiza kai ya ce "Ba zan sake ba ƴar madara, na daina Jee" jin ana ce mata Anti Jeederh shi kuma ba zai iya faɗa bakiɗaya ba ya sa yake cewa Jee, sai watarana data bashi alawar madara ya ce da Maminsa da alawar madarar suna kama tun daga nan yake cewa ƴar madara. Ta ɗauke kai ya ƙara sakin jiki yana kwaɓe fuska ya ce "Zan sake ba Mami, zan sake ba" ta saki fuska tana murmushi ta ce "Ok good boy I forgive you" da sauri ya shige jikinta ya rungumeta jikin nan nasa zafi sosai ta shafa kansa taji ya saki ajjiyar zuciya da sauri ta taɓa cikin shafal ba komai da alamar yadda yunwa ke damunsa ta ɗago shi za tayi magana taga har bacci ya ɗauke shi a hankali ta ɗauke ajjiyar zuciya tare da jansa jikinta ta rungume shi wani irin son shi na ƙara ratsa zuciyarta...