Mijin malamah by nimcy luv - Chapter 37
Mijin malamah by nimcy luv Chapter 37: Mijin malamah by nimcy luv Chapter 37. Have a nice weekend👑 [8/4, 5:30 PM] _KHADSALT_🌹💞: Rawa jikin Jee ya fara…
1,479 words
Have a nice weekend👑 [8/4, 5:30 PM] _KHADSALT_🌹💞: Rawa jikin Jee ya fara da wani irin ɓari naman jikinta na wani irin ƙyarma, tsoro da fargaba ya wanzu a zuciyarta, tana jin ƙirjinta na wani kalar ɗagawa da ƙarfi, sosai hankalinta ya tashi jin an sanya hannu tare da rufe mata baki, duk da kasancewar duhu bai hanata fahimtar waye ba, domin ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious ya riga daya fallasa waye. Majeederh na ƙoƙarin zame hannunsa ta ji ya cire nasa da sauri yana ɗan ja baya, cikin sauri ta miƙe jikinta na rawa ta nufi wajan socket ta kunna hasken bedroom ɗin, riƙe kanta tayi da kyau tana kai dubanta zuwa direction ɗin inda yake ta ganshi durƙoshe a kusa da kujera ya kifa kansa a armchair hannunsa duk biyun tsakanin cinyoyinsa, rawar da jikinsa yake da karkarwa ya sanya gabanta ya faɗi tare da tunanin ko bashi da lafiya ne? Me yasa mesa? Me ya kawo shi gidansu, har cikin bedroom ɗinta? Ko yau ɗin ma ta katanga ya shigo? Sake ware idanunta ta yi a kansa taga har lokacin jikinsa rawa yake ga jijiyoyin kansa da suka fito sosai. Da sauri ta ƙarasa kusa da shi ta ce "Khalil" Shiru bai bata amsa ba, duk da yana jin muryarta a tsakiyar kansa, Majeederh ta rikice domin daman tun yana ƙarami bata jure ciwonsa balle yanzu da take ganin ya yi ɗan wayo idan ya yi ciwo zai iya mutuwa, a yanzu kuma Abraham ya mutu zata iya zaucewa Ubangiji ne shaidar irin son da take masa, tuna hakan yasa ta ƙara yin ƙasa da murya ta ce "Khalil are you okay?" Ya yi mata shiru, ganin rawar jikinsa ka ƙaruwa fiye da kima har wata miƙa yake faffaɗan ƙirjinsa na buɗewa yana matse ƙafa ya sanya a ruɗe cikin tashin hankali Majeederh ta kai hannu zata taɓa kafaɗarta cikin sauri muryarsa bata fita sosai ya ce "Don't torch me" Ya faɗa a rarrabe murya can ƙasa abubuwan da suke masa yawo a jiki ya sanya baya fahimtar taƙa maimai abinda gangara jikinsa ke buƙata. Majeederh ta cire hannunta a hankali kuma ta juya idanunta ya sauka akan wayarsa dake yashe har ta fashe ma, cikin sauri ta ɗauki wayar da mamakinta tana shafa saman screen ɗin iphone din idanunta ya sauka akan photonta wanda take zaune a office ɗin ta na B.u.k idanunta lumshe a photon kamar mai bacci sai ɗan murmushi da ta yi wanda ya sanya dimples ɗinta lomawa ta yi wani irin kyau sosai. A hankali ta lumshe idanunta tana wani irin son Abraham na ƙara yawa a zuciyarta, hasken da wayar ya kawo da sunan Taj a saman screen ya sanya Majeederh kallon wayar tana mamakin me ya sa ake kiran shi by this time? Kiran ya katse wani ya ƙara shigowa a sanyaye ta saka hannu ta ɗaga kiran tana mannawa a kunnenta tare da yin shiru tana son ji Who's on the line? Daga cikin wayar Taj ya yi dariya ya ce "Bad boy gani a hanya ina following naka, amma banga motarka ba, ka nutsu wallahi ba zaka iya driving a halin da kake ciki ba, kuma duk masifar taurin kan ka yau ƙaryar alawa ƙasa dole sai ka nemi mace ka kwanta da ita kamar yadda na yi maka al'ƙawari, idan kowa ba haka ba You won't sleep a wannan daren, shi ya nace Joshua ya zuba maka ƙwayar kaɗan a cikin Cork ɗin amma ya juye" Taj ya ƙara fashewa da dariya sosai ya ce "Zan yi dropping Debeka a gidanka sai ku kwanta tare kasan yadda take mahaukacin sonka, yarinyar classic beb ce yanzu zata gigitaka ka faɗa mini inda kake idan na yi dropping ɗinta a gidanka sai na zo na ɗauke ka, ni zan koma club ne Now the party has started, the classic babies are coming into the club, wallah ka yi missing Bad boy.....," Cikin tsawa Majeederh ta katse Taj idanunta har wani rufewa yake a karo na farko na rayuwarta ta ce "Uwar Debeka da uban Debeka, wato kune kuke bashi kayan Shaye-shaye ko? Ko ke son haɗa shi da wata figaggiyar yarinya mara tsafta wacce take fama da Datti a jiki" Takaici ya sanya Majeederh yin shiru. Taj ya ce "Au wai wajanki ya zo?" Ya faɗa yana zare idanu, yana kuma danne dariyar dake ransa. Majeederh ta ce "Meye Sunanka?" Ya ce "Taj" Ta jinjina kai ta ce "Baka da hankali ko? Kana forcing na shi ya aikata abinda Muslunci ya hana?" Taj ya ce "A'a Mami, Debeka fa budurwar shi ce, kuma a gidansa take zaune, bayan itama akwai wasu ƴan matan da suke zuwa wajansa,kuma duk mu'amala yake da su kenan dai a lalace yake, kuma mene haramcin daga kwanciya da mace Mami?" Wani irin rikitaccen tashin hankali ne ya rufarwa Majeederh ta runtse Idanunta da kyau, tana son hana kansa gasgata abinda Taj yake ƙoƙarin faɗa mata. Ta cikin wayar Taj ya ce "Good night Mami, ki lura dashi please cikin dare yana yawon firgita" Yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da kifawa a jikin kujera ya dinga wata mahaukaciyar dariya kamar zautacce. John ya ce "Taj why?" Taj ya ɗaga kafaɗa hannunsa riƙe da pen Shisha ya ce "What?" Da turanci John ya ce "Me ya sa zaka sakawa Bad boy ƙwaya a Cork? Muma da muka saba harka idan muka sha kusan haukacewa muke, balle shi da ko sakin fuska bayayi ko Debeka da yake ɗagawa ƙafa ta baro ƙasar su ta biyo su bai taɓa maganar 5 minutes da ita ba, even small hug bai taɓa yi mata ba, ka manta sanda tayi masa allurar bacci sbd buƙatarta kusan kasheta ya yi fa, amma all this ka ɗauki abu ka bashi yanzu kasan ba zai iya riƙe kansa ba idan ya aikatawa Mamin tasa wani abu fa? Jesus mummunar labari zai faru" Taj ya haɗe fuska irin ko a jininsa ɗin nan ya ce "Ni fa Am happy for him, ita Mamin tasa zata gane shi ba yaro bane" Sai a lokacin wani da zuwansa country ɗin kenan kuma sun fi good time shi da Bad boy tsare girar su ɗaya ya ce "This is not fair, how can you imagine yaje wajan Maminsa a haka? Kasan mugun son da yake mata? Ko fa president baya so kamar....." Sai kuma ya yi shiru da bakinsa. Taj ya ce "C'mon ka ƙarasa faɗar maganarka, wanne president? Meye haɗin President da Abraham?" Salamon bai ce komai ba ya ɗauki kwalbar giyarsa ya ratsa ta cikin mata ya shiga rawa hankali kwance. Taj, John, Joshua suka kalli juna John ya ce "Who's Abraham?" Taj ya ce "President's son" Joshua ya ce "Dream, idan shi ɗan gidan shugaban ƙasa ne meyasa yake zaune shi ɗaya tal sai Grandpa yana rayuwa kamar mara gata, sai kuɗi da yake da shi kamar hauka, wallahi idan shi ɗan President ne bamu isa ya shigo cikinmu ba, kawai Salamon yana raina mana hankali ne" Taj ya ce "Something is fishy, Farkon haɗuwata da Abraham a University of Oxford, a lokacin na duba card ɗinsa naga alrdy ya yi nisa a karatu, naga tambarin Germany da kuma National I.d card na germany bai bari na gama gani ba ya karɓe ya ce, asali Grandpa University of Munich dake Germany ya sashi shi kuma bai so yama tsani ƙasar bakiɗaya, muna level ɗin ƙarshe a University of Oxford wasu manyan mutane suka zo tafiya dashi ya kafe babu inda za shi nayi mamakin yadda suka kasa kama shi sbd at the end ma ɗaya ya harba shi ne muka tattara mukabar ƙasar, daga ƙarshe dai ban ina yaje ba domin ya barmu for good 1yr" John ya ce "Baka tunanin laifi ya yi wa mutanen?" Taj ya ce "Maybe, he's smart and stubborn boy to be honest ban taɓa ganin mutum bai iliminsa ba, baya taɓa zama lectures amma bugu ɗaya ya kewa exam, tun yana secondary haka record ɗin yake shi yasa aka dinga yi masa promotion da wur wuri ya gama secondary school sanda ya fara University zaka raina shi sosai, amma dake yana da jiki sosai ba a ganin shekarun nasa, kuma Grandpa ɗin nan nasa kuɗi ne dashi kamar su kashe shi wallahi, waye zai ce Bad boy ya karanci Likitanci? Kusan me ya sa?" Suka girgizawa Taj kai ya ce "Cos he's not his dream, Abraham's doesn't like it, Business kawai yake so bayan nan sai ɓangaren tsaro yana son sama sojan ƙasa, yanzu haka idan ya yi zanen gida miliyoyi yake samu, gabaɗaya shi ke siya mana suttura sometimes" Gang team ɗin sukai shiru kenan dole akwai abinda Abraham yake ɓoye musu na daga rayuwarsa. Taj ya ce "Excuse me" Wayarsa ya ɗauka ya ƙara danna number Abraham yana ji tana ringing ba a ɗauka ba, ya miƙe ya ce "Bari nayi dropping Debeka"