Mijin malamah by nimcy luv - Chapter 45
Mijin malamah by nimcy luv Chapter 45: Mijin malamah by nimcy luv Chapter 45. Allahamdulillah! A nan na kawo ƙarshen BOOK1 wanda suka labari ne, akan yadda…
3,330 words
Allahamdulillah! A nan na kawo ƙarshen BOOK1 wanda suka labari ne, akan yadda aka samu cikin Khalil da kowa ke cewa ɗan shi. I hope yanzu zaku fahimci labarin daidai idan mun ɗora... Da yawa za kuga kamar Malama Majeederh ba ta yi achieving komai a rayuwarta ba sai baƙin da ƙaddarori da suke ta rige-rigen faɗa mata. Ba zan iya cewa kun ji daɗin BOOK1 ko aka asin hakan ba... Abu ɗaya na tsani tsagwaron labarin yana BOOK2. Akwai wasu ƙalubalen tunda mutum a karan kansa bai taɓa dauwama da farin ciki ba, to rayuwa haka take yau fari gobe baƙi, yau zuma gobe maɗaci. Duk macen da zata buɗe baki ta ce tunda tayi aure da mijinta zaman daɗi suke basu taɓa samun matsala ko saɓani ba, tuni na bugi ƙirji na ce ƘARYA TAKE. Allah ya taɓa zuciyata na fahimci komai na gane komai kuma ina fatan zaku biyoni domin kuma ku fahimta...
1. Wacce rayuwa Majeederh za ta yi a gidan Abuturab?
2. His Excellency zai yarda ya saketa ko ya ya? Zata haihu da shi ko ya ya?
3. Abraham zai dawo kamar yadda ya yi al'ƙawari? Idan ya dawo ya samu labarin Majeederh na gidan mijinta me zai faru? Zai haƙura ya barta tayi rayuwa da mijinta ko ya?
4. Ina fatan baku manta da General Alpha Bello khan ba? Shin bayan ya gudu sbd baya son auren haɗi tsakaninsa da Majeederh ina yaje? Yana raye ko ya mutu ne? Yana cikin hankalinsa ko hauka yake? Zai bar Majeederh ko ya?
5. Aliyu ya ce idan har bai auri Majeederh ba to mutuwa ya yi, shin ya zata kaya? Zai haɗa su kishi da Latifa ne?
6. Kuna ganin Abbu zai yi aman shi ya lashe? Wacce magana Fulani zata faɗawa Majeederh amma bata samu dama ba sai Abbu ta faɗawa.
7. EHEM🤓 WAYE AJLAAL SULTAAN Mr ji dakai masu taƙama da rawani, kuna ganin zai dawo Nigeria a karo na biyu? Waye zai yi SACRIFICE a cikin zataran mazan? Su waye zasu haƙura da Majeederh wa kuma kuke ganin ya dace da ita matsayin miji na gari?.
WANNE IRIN ZAMA ZA A YI TSAKANIN MAMI DA ƊAN RAINONTA?🤣 BILLAHI DRAMA CE BABBA WANDA BAI BIYONI A BOOK2 BA BABU RUWANA... KUN TAƁA GANIN INDA MATA TAKE GUDUN MIJINTA?😂DUK MAI SON SHIGA GROUP 2 ZAI BIYA #500 BABU YAWA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616 ayi maza a cika group wanda bashi da 500 kada ya karanta na sata yazo na yi masa Discount sbd Allah shi ya taɓa zuciyata ba ruwana. Ina ƙaunar masoyana na amana da gaskiya da duk mai karanta littafina. Ubangiji yabar zumunci da ƙauna Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira ya sadaku da dukkan alheri yayi muku albarka🥰Ya hure muku kuɗin siyan MIJIN MALAMA 2 thanks for the love and cares thanks for patronize me 🤞🏽kune ni da bazarku nake taƙama kune kuke sawa asan da zamana 😘😘😘😘 Nimcyluv sarauta's love you👑💋❣️ [8/5, 11:56 AM] _KHADSALT_🌹💞: _*Arewabooks@Nimcyluv*_
*MIJIN MALAMA* BOOK 2 PAGE 51
Kukan ta ya shiga ratsa dukkan wata jijiya dake kan His Excellency Abu-turab zuwa tsakiyar ƙwaƙwalwar shi, me ya sa ta kuka har haka? Bata son shi ne ko yaya? Ko kuma kukan farin ciki ne ta same shi a matsayin mijinta? He couldn't understand why she was crying, deep down na zuciyarsa yana jin faɗuwar gaba. A hankali ya nemi waje ya zauna saman kujerar dake parlourn ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa, ya jima nan zaune He was thinking about where to start?? Ya miƙe yana gyara zaman babbar rigarsa ya nufi Main parlour ya samu Uncle Isma'il zaune shi da Jawaad ya zauna yana rusinawa ya ce "Sannu Uncle" Uncle I ya ce "Yawwa Ur Excellency, har ka fito? Fatan lafiya? Ta dai fito ko?" Ya jinjina kai cikin nutsuwa ya ce "Eh, daman nace yanzu zamu ta fi ne?" Uncle I ya girgiza kai ya ce "To ni dai san samu ka tafi da matarka, tunda babu amfanin wani zaman tana ƙarƙashin ikonka a yanzu, to amma kasan bidia'a irin ta mata yanzu sai ka ji wannan surutu, kuma ni ma a karan kai na ina son sai mun zuba mata furnitures ɗin ta da komai ai ba a kai ta haka ba" His Excellency ya ɗan kalli Uncle I can ya ce "No need Uncle,I have fixed the part where she will sit, added new furniture's that was ordered from Turkey" Uncle Isma'il ya yi jim sai kuma ya girgiza kai ya ce "I don't think that would be possible, gwara dai ka bari akai mata na iyayenta wanda za mu yi, daman ai responsibility ɗin mu ne" His Excellency kallon Uncle I kawai yake bai san yadda zai masa bayani ya fahimta ba. Ganin hakan yasa Anti data fito daga bedroom ta nemi waje ta zauna tana ɗan murmushi ta ce "Ba aikin lada zamu hanaka ba, kasan mu mata muna da gutsiri tsoma, ina tsoran watarana a goranta mata rashin kayan ɗakin ace kai ka yi mata komai" A hankali Abuturab ya ce "Haba Anti, ko ban auri Majeederh ba zan mata komai, plx na yi niyya" Ta girgiza kai ta ce "Baka san mata ba ne Ur Excellency, musamman dangin miji kaɗan daga cikin halinmu ne gori" Ya lumshe idanunsa ya buɗe calmly ya ce "Oh, a bari na tafi da ita, after that sai ku kawo mata tunda kun matsa" Uncle Isma'il ya ce "Better, hankalina sai ya fi kwanciya da hakan" Anti ta ce "Amma kayi mana alfarma, ko zuwa Magriba ne sai ka dawo ku tafi not now" Abuturab ya ce "if you are more comfortable with that, Allah ya kaimu" Ya miƙe tsaye Uncle Isma'il ma ya miƙe suna haɗa hannu ya ce "Thank you, Uncle" Daga nan ya fita yana rufe Idanu, sbd daman bai gama warkewa ba ya matsa dole sai ya zo. Tun kafin ya ƙarasu P.a Hammad dake tsaye shi da Jawaad suna hira zaka ɗauka abokai ne, sbd Hammad he's so funny and nice person friendly to everyone. Driver ya buɗewa His Excellency Abu-turab back seat ya shiga ya zauna, Hammad ya ce "Jawaad see you soon" Ya ce "Ok Dear bye" driver yaja motar bayan Hamma ya shiga gaba, slowly suke tafiya bisa umarnin Abuturab ɗin. Majeederh har yanzu tana zaune bakin ƙofa, tana jin kamar bata kyautawa Abuturab ba na rufe ƙofar da ta yi amma gabaɗaya she's Uncomfortable da shi, zuciyarta ta kasa ganinsa matsayin mijinta na sunna, what should I do?“ Think, Majeederh” Zuciyarta ta bata amsa, ta ƙara sunkuyar da kanta kamar ƙaramar yarinyar, her heart broke, she hugged her knees even righter. Nothing hurts like they words, maganganun mutane da surutun su akanta suke damunta, taya zata ya fewa Abraham? Duk duniya ta tsane shi wallahi bata ko ƙaunar jin sunan shi balle sake ganin mai kama da shi. Kukan Baby Khalil ya sanya ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi inda yake tana zuwa ta ɗauke shi, haka kurum ta samu kanta da ƙura masa idanu, wani kyakkyawan bugu zuciyarta tayi sbd wani mahaukacin kama da yake sake yi da Abraham, ya juye sak Abraham komai da komai musamman yadda yake tsotsar lip's ɗinsa da saurin kwaɓe fuska, tayi saurin rufe Idanunta,tare da rungume Baby Khalil a hankali ta ce "Allah ya isa, ba zaka taɓa ganin daidai ba a rayuwarka, Ubangiji ya rusa maka farin cikinka kamar yadda ka rusa nawa, Allah ya hanaka kwanciyar hankalin kamar ka hana nawa kwanciya Ubangiji ya raba ka da iyayen...," Anti data murɗa ƙofa ta shigowa da spare key ɗin dake hannunta tayi saurin cewa "Subuhanallah! Ya isa haka" Kalmar da ta tsayar da Majeederh daga mummunar addu'ar da take akan Abraham. Ta nemi waje ta zauna idanunta akan Baby Khalil tana ƙara ganin kammminsa da Abraham ɗin kafin ta ce "Why? Wannan muguwar addu'ar ta mece Majeederh?" A hankali ta ce "Ya rusa mini rayuwa Anti" Anti ta girgiza kai kawai kafin ta sauke numfashi ta ce "Idan Abraham ya lalace still ke ya lalacewa tunda uban ɗan ki ne khalil, kina ganin yadda suke muguwar kama" Majeederh ta haɗe fuska tare da yin ƙasa da kanta. Anti ta ɗora da cewa "Bai kyauta, bai kyauta, bai kyauta amma hakan baya nufin ki yi mummunan alkaba'i akan shi, idan ki ka ce kin barsa da Allah kaɗai ya wadatar, wlh duk wanda ya buɗe baki ya ce ya barka da Allah to mutum ya shiga uku, no need ki yi wannan addu'ar ko dan Khalil ɗan ki plx, Majeederh ke malama ce kin fi kowa sanin me ya dace da wanda bai dace ba, Majeederh Ubangiji ne ya amshi addu'armu ya dubi halin da kike ciki ya haɗaki da miji na kece raini, kaf familyn Khan! Babu wanda ya yi dace da miji irin naki" Ta ɗan yi shiru tana ƙara girgiza ƙafa ta ce "Wlh yanzu baki da wanda ya shige Abuturab, yana son ki sosai Majeederh ki yi ƙoƙarin kyautata mu'amalar ki da mijinki, ki duba yadda idanun duniya ke kan ki ko? Kada ki yarda ki bada wata ƙofa da zaku samu matsala da mai gidanki yanzu shi yake da iko akan ki, yi na yi bari na bari, ki riƙe uwar mijinki hannu bibbiyu da sauran dangin miji, babu ruwanki da kowa balle a ƙara saka mini wani tension ɗin kizo jininki yana mugun hawa zuciyarki ta buga a iska, ƙaddarar data same ki ita take ta trending a duniya kiji na faɗa miki bawai iya Kano ko Nigeria ba, da kin shiga Google ki Twitter za kiga shi ne the most trending news" Gaban Majeederh ya faɗi ta runtse Idanunta, ita kam taya zata daina tsinewa Abraham? Babban takaicinta wai ɗan cikinta shi ne yaga tsaraicinta? Ya yi mata Fyaɗe ya tuzarta ta a idanun duniya shikenan yaga komai da komai nata duk irin killace jikinta da take, takaici ya sanya ta ƙara runtse Idanunta ta nemi hawaye ta rasa. Anti ta ce "Kuma da kike ta tsinewa Abraham akan me? Sbd baki yadda ƙaddara ba? Kada ki tsawaita ƙiyayyarki akan shi domin abin da ka tsana watarana shi kakewa mugun son da ba zaka iya controlling kanka ba,I am advising you as a mother and not your uncle's wife, ko da wasa kada ki faɗawa kowa matsalarki sai wanda kika yarda da shi, Abuturab ɗin nan ya fi Abbu a wajanki, Abbu ya kureki shi ya amsheki hannu bibbiyu da ƙaddara data faɗa miki yanzu ne lokacin daya dace ki kwantar da hankali ki samu nutsuwa da mijinki Majeederh" Ita dai Majeederh was speckless ta kasa cewa komai. A hankali ta ce "Anti Abbu ya tsine mini, kada na lalace" Anti ta girgiza kai ta ce "A'a in sha Allah ba zamu ga wannan rana ba, zai sakko ne, naso Abuturab ɗin ya bari an ɗan gyaraki amma ina, ko arba'in ma kiyi sai ki tare" Da wani irin sauri ta ce "Kamar bani da gata Anti? Yau ɗin nan zan wani bisa" Anti ta ce "Hakan ma ce Allahamdulillah, gata kowa kina da shi gaba da baya" Tana faɗin hakan ta miƙe bayan ta amshi Khalil daya koma bacci tana cewa "a sauya masa suna, uba Khalil ɗa Khalil?" Majeederh ta haɗe rai ta ce "Uwa kawai yake dashi" Anti bata sake cewa komai ba ta fice daga bedroom ɗin. Grandpa na zaune a parlour shi da wasu manyan mutane, ya ɗaga kai a hankali idanunsa ya sauka akan Abraham dake tsaye kamar kurarre ya zubawa gefe ɗaya jirkitattun idanunsa wanda sukai wani kala. Grandpa ya kalli mutanen ya ce "This discussion has come to an end. We will meet tomorrow morning at the office" Suka miƙe tare da kwasar ducoments sukai waje, Grandpa ya miƙe yana isa inda Abraham ke tsaye frm head to toe yake kallonsa ganin gabaɗaya ya sauya kamar bashi ba, ya yi sanyi ba zafin ran nan, shi ya ɗauka da gaske ya samu matsala a ƙwaƙwalwar shi, shi ya sa bada shawarar kai shi can asibitin mahaukata ashe depression ne kawai. Zai kama hannunsa ya ji ya ce "I want a plane that leaves in an hour to Germany" Grandpa ya yi murmushi, so Finally ya haƙura da Majeederh kenan? Ya haƙura da auren Mamin tasa? Ya ce "Right now my grandson" Wayarsa ya ɗauka ya yi danne-danne na wasu daƙiƙo kafin ya ce "Done, nan da 30 minutes jirgin zai tashi daman" Abraham bai kula Grandpa ɗin nasa ba ya nufi upstairs kai tsaye, Grandpa na zaune ya ganshi ya fito cikin sabuwar shiga nrml shiga ya yi ba wacce ya saba ba, Camouflage-print cargo trousers da Gymashark sports t.shirt kansa na nan a hargitse har gefen goshinsa duk ya cukurkuɗe amma hakan bai hana wani irin ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious fita daga jikinsa ba, ya shiga sakkowa daga upstairs ɗin fuska kamar ya ce ya shiga uku, hannunsa zube cikin Aljihu sai ka ɗauka wani babban mutum ne he just 20yrs ko gama rufata bai ba. "Ka shirya tafiya wajan Denial kenan?" Ya yi masa banza, murmushi Grandpa ya yi tare da miƙewa yabi bayansa, back seat suka shiga bakiɗaya driver ya jasu zuwa airport sai da sukai nisa ya ce "Grandpa" Ya ce "Yes dear" Ya ɗan yatsuna fuska sosai ya ɗauki seconds bai ce komai ba sai da sukai nisa sosai ya ce "About the Gang team, Where's Taj?" Grandpa ya yi shiru sai kuma ya watsa hannu yana ɗaga shoulder's ya ce "I don't know where he is, after you left the country, the Gang team was gone" Abraham ya yi shiru yana buƙatar ganin Taj, ya ji ina yakai al'ƙawarin da ya yi masa na wasiƙa? Ina yakai envelope ɗin? Har suka isa airport Abraham bai sake ko buɗe ido ba balle magana, suna isa jirgin na shirin rufe ƙofa bai tsaya jin me Grandpa zai faɗa ba, da sauri sauri ya shiga taka steps ɗin benen har ya shiga yana shiga ƙofa ya rufe, Grandpa ya yi murmushi yasan Abraham fushi yake da shi, yana kuma fatan this time around ya samu daidaito da mahaifinsa Denial. Yana tsaye har jirgin ya tashi kana ya shiga mota yabar wajan shi ma... Maman Alpha ce zaune ita da Anti sai Yaya Bilkisu a hankali ta ce "Daman komai ya yi farko yana da ƙarshe, gwara Majeederh muna ganinta munga Irin ƙaddarar daya faɗa mata,amma ɗan uwanta ba? Babu wanda yasan duniyar da Alpha ya shiga" Ta faɗa cike da damuwa. Yaya Bilkisu ta ce "Allah ba azzalumin bawansa bane, sai dai bawan daya zalunci kansa da kansa, Allah kuma baya ɗorawa bawa abinda ba zai iya da shi ba, sai dai bawa ya ribaci ƙaddarar daya jawa kansa, mu duka muna addu'ar Ubangiji ya dawo da hankalin Alpha zuwa gida kullum da shi nake kwana nake tashi ki duba shekara nawa yanzu?" Maman Alpha ta yi shiru tana wani irin murmushin takaici Anti ta ce "Haka ne, In sha Allah yana nan lafiya ma" Kafin su yi magana suka ji sallama da mamaki Anti ke kallon Latifa Omar wacce ta shigo ɗauke da damuwa bayan sun gaisa ta ce "Anti don Allah ku yi haƙuri dan gane da reported ɗin da na yi a gidan jarida, raina ne ya ɓaci duk yadda na yarda da Majeederh nake kareta a gaban jama'a da iyayenmu amma hakan bai hana taci amanata ba, na ɗauka Majeederh tana sane da cikin jikinta ta rufe ni shi yasa raina ya ɓaci, Apparently I a made misunderstanding, without stopping to research the matter, ku yi haƙuri plx" Yaya Bilkisu ta ce "Allahamdulillah, tunda kin gane kuskure ne, kuma ke ɗin aminiyya ce ta gari ga Majeederh" Ta ƙara basu haƙuri kafin ta shige bedroom ɗin da Majeederh take ciki. Ta sameta zaune riƙe da Baby Khalil da idanunsa yake buɗe ta ƙura masa idanu, tayi murmushi ta ce "Mai jego" Majeederd dai bata ce komai, Latifa ta shiga bawa Majeederh haƙura Exlty yadda ta bawa su Anti hadda kukanta, ganin Majeederh bata ce komai ba ta ce "Plxx Bestie let by gones be by gones sharrin shaiɗan ne" A hankali tana rufe ido ta ce "No bad" Tana jin a ranta tabbas sharrin shaiɗan ɗin ne, tunda ta yarda da Latifa ita ɗin ƙawar arziƙi ce wacce samun kamarta zai wahala musamman idan ta tuna har mijinta ta bata opportunity na aura, ta ƙara lumshe idanunta damuwarta biyu ce a yanzu yadda abu ya tsine nata ya kureta kuma ya cireta daga cikin yaran daya haifa ya sadaukarwa da duniya ita yafi komai ɗaga mata hankali, idan ta tuna wai little ɗan data raina da hannunta shi ne ya yaga rigar mutuncinta sai ta ji zuciyarta ta mata nauyi bata jin daɗin komai a duniyar, tana fatan mutuwarta ta risketa amma da alama kamar yanzu ta saka hannu a fata na rayuwa, suna ɗaki su Anti kuma na parlour suna jiran har dare ya yi Abuturab ya zo tafiya da matarsa.... Zaune take tayi wani irin zama kamar zatai sujjada ta yafa wani jan mayafi akanta, mutumin dake gabanta ya ce "Ke la'ananniyya ce, ke muguwa ce, yake azzaluma me kuma ya kawo ki yanzu bayan sharaɗin da nayi miki?" Ta ƙara sunkuyar da kai tana shakkar haɗa idanu da mutumin sbd muninsa bakinsa har wani hayaƙi yake ta ce "Kamar yadda ka sani tun farkon zuwana wajanka akan Aminiyyata ne, ta hannun damana, bana buƙatar duk wani cigaban ta tunda na fahimci ta fini komai na rayuwar duniya, tana da kyau tun muna raya ta tashi da farin jini duk da baa ganin fuskarta, wannan dalilin yasa na da ƙushe wannan farin jinin nata, danginta na sonta tana kare mutuncinta, ta fini ilimi nesa ba kusa ba, har tazo taci gasar Kur'ani ta duniya, na mayar da ita mujiya a wajan maza, ban san tana da ciki ba kai ne ka fara ankarar dani, a sanda na koma gida bayan na bar nan sai dana kashe dubu ɗari biyu na maganin da zai zubu mata da jinin al'ada duk dan kada ta gane, sannan ka ƙara yin aiki da jinin zai dinga fita duk wata, kai ne ka sanya Aljanu kwantar da jiki, kuma kai ne kasa Aljanu suka tashi cikin kuma suka haɗa ɗan cikin motsi duk da yana cikin ƙoshin lafiya, kai ne ka hana likita ganin cikin Majeederh, kullum results zai nuna she's good...." Da sauri mutumin ya ce "Tsinanniyya la'ananniyya dai na yi mana turanci a nan ko na turɓuɗeki ki zama toka ko ɗan akuya" Jikinta na rawa ta kwaso wata ashar ta maka alamar ban haƙuri ta ce "Kuma ni na ƙara rura wutar son da takewa Abraham har take sake masa jikinta, kada ka manta kafin aikin yanan ya ci sai dana zubar da ɗan cikina babu adadi, kai ne ka sanya na fara bin mata ƴan uwana sbd duk aikin da kake mini akan rusa rayuwar Majeederh, kai ne kace na sanya mijina ya aureta yadda zan fi jin daɗin durƙosar da rayuwarta kai ne....," Ya yi saurin dakatar da ita da faɗin "To cikakkiyar azzaluma Ubangiji ba zai barki ba, lallai zaki girmi abinda kika shuka yanzu na haka wani cikin ne dake gashi nan ina Kallonsa a ƙasan mararki kuma ya zama dole ki zubar da shi" Gaban Latifa ya faɗi ta sha cikinta tana lumshe idanu ta ce "Zan zubar idan zaka mini abinda nake so" Ya ce "Bayan mugwayen abubuwan da kikai mata me kike buƙata yanzu?" Ta ce "Kada ka taɓa bari Abuturab ya kusance ta balle ta haihuwa har ɗan ya samu gadu, kada ma su haɗa gado har abada sannan ina son sanin waye MIJIN MALAMA na gaske??
Littafin mijin malama na kuɗi ne. Ka biya ka karanta hankali kwance rubuta zan yi a nutse ba skipping yadda za ku ji daɗi har a fara zuba love soon☺️☺️☺️08119237616
*Aunty Zee MOM MUJAHID KATSINA* *08162859027*