Kenza eBookz

Mijin qwaila cmplete - Chapter 9

Mijin qwaila cmplete - Chapter 9

Mijin qwaila cmplete Chapter 9: Mijin qwaila cmplete Chapter 9. Ya yi shiru ransa ya na dan baci, sai dai bai ce mata komai ba.

4,487 words

Ya yi shiru ransa ya na dan baci, sai dai bai ce mata komai ba.

Taci gaba da magana "Akwai wata yarinya da kake nutsuwa a tare da ita kamar ni? Na sani ba ka taba son wata mace sama da ni ba Ali, amma ina mamakin yadda kake son karyata zuciyarka Ali."

Ya gyara mata kwanciyar kanta a kirjinsa, a nutse ya ce da ita.

"Duk wadannan da kika lissafa ba su kadai ne farin ciki ba Basma, aure da kike jinsa ya wuce duk yadda kike tsammani, wannan farin cikin da kika lissafo sai ki ga ya kasa samuwa idan ba a yi taka tsan-tsan ba, shi yasa tun farko ba na yaudarar mace na ce zan aure ta. Dai dai gwargwado ina gudarwa aurena kuskure, kamar kwayar zarra na ganin idona."

Jikinta a sanyaye ta ce. "Ali ina da matsala kenan ko....?

Ya tare ta cikin tausasawa. "No, ni ne nake da matsalar, saboda dukkan tsarina da tsantsenina na nauyaya shi akan matar aurena, ciki har da cika zuciyata taf da kaunarta fiye da yadda nake da tasiri a tata zuciyar.

Wannan shi zai ba ni damar da zan Kore mata dukkan aibuna, wanda hakan zai alkhairantu rayuwar 'ya'yana, wadanda na sha fada miki tun yanzu nake share musu fagen rayuwa mai kyau, dan ina jin ba ni da abin alkhairin da ya wuce su...."

Basma ta gaji da toshe kunnenta daga jin maganganun da suke neman fasa mata zuciya. Ta tare shi da neman yin kuka.

"Takaita min manufarka Ali, na gaza ne dan na cika sonka, na gaza ne dan bazan iya cike guraben da ka hakawa matar aurenka ba, ko kuma na gaza ne dan akwai wadda ka fi so a kaina...? Buds bakinka dan Allah ka fada min gaskiyar magana."

Ya yi shiru ya na shafar kanta a hankali ya na nazarin maimaita amsoshin da ta riga ta amsa, ta ke son goga masa bakin jinin ya fada da nasa harshen ta ga bakinsa. Can da ya fahimci jiran amsarsa ta ke, sai yace.

"Ni ban san abin da zan ce miki ba Basma, ba mu taba alkawarin aure da ke ba, bai kamata yanzu ki daga min hankali a kansa ba. Ba na so nayi ta yi miki laifin cewa ba zan aure ki ba, sannan ke ma bai kamata ki damu ba idan na fadi hakan, wanda kamar rashin auren nawa gareki ma ya fi..."

Ta kwace kanta cikin bacin rai da fita hankali.

Ta janyo bargo tana rufe jikinta, muryarta a kausashe ta ce.

"Ka ga malam! Na gaji da wannan yaudarar da kwane-kwanen, ka fito fill ka fada min wata ta hure maka kunne. Yaya kake neman mayar da ni karamar yarinya, ko kuma an fada maka dai dai nake da mutan kauyen da ka baro....

Ya tsura mata ido ya na daga kwance, ya yi fuska, ya ce.

" To Basma na sami matar aure, shi kenan! Na fada miki bana son bata miki rai."

Kamar tashin hankalin fuskarta ya ragu, amma na zuciyarta ya ninninku matuka, shi ne kuma ya tunzura wuce gona da iri a kalamanta.

"Na rantse ba ka isa ba Ali, an fada maka an haifi shegiyar da zata Shiga tsakanina da kai..."

Fuuu! Ta mike ta fada bandaki kamar mintina sha Biyar, ta fito cikin fushi sai faman kumburi ta ke tana munfarfashi, shi kuma ya na daga kwance ya na binta da kallo.

Ta na tsaye gaban madubi tana daure gashinta, ya jefa mata tambaya, hankali kwance.

"Dams munyi da ke zaki damu rayuwar aurena ko kuma ni zan damu da taking?"

Ta table baki ba tare da ta juyo ta dube shi ba. Tace

"Idan ka ga dama ka damu tawa rayuwar amma na rantse maka ni zan damu taka da son ranka ko babu..."

Ya yi karamar dariya ya na kokarin tashi zaune.

"Da zaki shawartu da na shawarce ki katse bata lokaci a kaina. Ba zaki wani iya damuna ba, domin dukkan kawaicina da hakurina bai shafi lamarin iyalina ba."

Wannan karon kamar ta fara sabawa da takaicinsa, dan ko juyowa ba ta yi ba ta ce.

"Duk mun fadu, sauranmu aikatuwa."

Ta day wayarta sannan ta dube shi da kyau, ta ce.

"Bari na dawo maka da tambayar da ta bata maka rai rannan, tunda yanzu neman bacin ran naka nake, wacce jakar ka bi da gudu rannan?"

Kuncinsa cike da murmushin da ya ke dadewa bai yi kamarsa ba. Ya ce

_She is my fianceee_

Ta dafe baki tana zaro ido, kawai kuma sai ta tsuntsure da dariya har da kwanciya a sofa. Ta yi dariyarta ta isheta, sannan ta mike zaune da ragowar dariyar tana nuna shi da hannu.

Mum Abdoul [2:54PM, 2/24/2018] ‪+234 703 300 1537‬: ♦🔸♦🔸♦🔸♦🔸 *NA SAN DA BAMBANCIN* Page 29

*KAINUWA WRITERS ASS* ®

*Na* *Shopiee* *Ummu shukran*

*Ban manta da ke ba Rahinat saboda irin kwarin gwiwar da kike ba ni Allah ya saka da mafificin alherinsa ameen*

"Ali, daga yau na dauke maka shaida biyu da na yi maka, zamowarka mai cikakken tsari, da kuma kasancewarka mutum mara karya dan a so shi..."

Ta ci gaba da dariya sannan ta dora.

"Bafulatanar kauye, Empty brain a ilimin boko da na addini, balle na ce sahabbai kake son kwaikwayo.... Hahahaha! Ali !! Bukatunka ga mace ka ke tsammanin jaka ce zata iya dauka? Ali, qwallinka da tsantseninka kake tsammanin matar daji zata iya dauka...? Na rantse Ali ka fadi babu nauyi, kuma ka rage digo da yawa na kason kallon kimar da nake maka."

Har yanzu yana dariya. "Kalma daya ce ba ta yi min dadi ba cikin maganganunki. Da zaki janje ta ni sai na kara miki digo a taki kimar kiran matata JAKA, duk runtsi ko muzuru ba zan iya kiran mijinki haka ba."

Ta kara tuntsurewa da dariya, tana tafa hannaye ta ce. "Ka kira shi mana! Ai babu wani mijin bayan kai, jaka kuwa mafarkin ido biyu ce, yanzu ne kuma nasan ba da gaske ka ke ba. Ta idan gundurarka na yi bari na baka hutu, ko shi yasa ka ce na rage sonka ba na cire sonka gaba daya ba?"

Ya tare ta cikin raha. "Ni kuwa ba na so ki yawaita cika baki Basma, kamar kin manta ban cika zolayarki ba, ko ina yiwa kowa karya ke dai banayi miki, saboda haka ki dauki maganata da muhimmanci."

Ta zabga tsaki ta yi gaba tana cewa. "Na barka lafia, sai na ga goron auren." *******************

Ya kwana ya wuni da farin cikin ya sabule Basma daga rayuwarsa, saboda haka da yamma ya shirya ya nufi gidansu, dan tuntsurar da ta maryam ma wadda ta dami mahaifiyarsa da zancen.

Abin da bai so ba, tare da maryam din akayi masa oyoyo, ita da zainab suka riki hannunsa suka isa har gaban kyakkyawar innarsa wadda ta ke zaune sanye da farin gilashi a idanunta.

Ya fada kan kujerar kusa da ita yana fadin. "Hii mum."

Ta kara fadada fara'arta tana dubansa. "Ali, mun yi kewa fa, sati biyu ba mu saka a idanu ba, amma ka kwana biyu ba ka leko na ganka ba, sannan ka kashe wayoyi...wai mene ne hikimar kashe wayoyin da kake kwana biyu."

Ya saci kallon maryam da ke hidimar zuba masa lemo, sannan ya maida hankali ga innarsa cikin sakewa ya ce.

"Momi zuciyata ce ta bude kofarta, wasu abubuwa masu tauri da korar sauran lissafi suka cikata, su suka da min son kadaici."

"Ko" inji momin fuskarta na bayyana farin ciki idonta a Kansa. Ta ce.

"To sha lemon ka ba ni labari, a kawo abinci?"

Ya girgiza kai lokacin da ya karbi lemon a hannun maryam, sannan ta zauna kusa da shi kamar 'yar uwarta mace, sai kallonsa ta ke sai ka ce wata tsohuwar mayya. Ya ajiye tambulan, sannan ya mokada kafada.

_"Surprise mum_watan aurena ya tsaya."

Momi ta zare gilas cike da farin ciki da mamaki, ta ce da shi.

"Ka shirya karrama mu kenan? Gaskiya na yi farin ciki, maryam din ce ko Basma, ko wata daban?"

Ya kara satar kallon maryam ya ce.

"Wata 'ya marainiyar yarinya ce mai tsada na ga ana yiwa kokawa, shi ne nima na shiga aka yi da ni. To na sami sa'ar tsigo furen soyayyarta, yanzu kokawar da ta rage min ta yadda zan kwaci kaina daga mafiyancin masoyanta..."

Momi sai dariya ta ke tana kallonsa da kayen yadda yake bata labarin. Ta ce

"Wacce tsadaddiyar yarinya ce haka? Gaskiya ina tayaka murna da sonta. A ina ta ke?"

Cike da karsashi ya ce . "Sunanta Rahma, kuma a kauyen da na kai ziyara ta ke...."

"Ita ma ziyarar ta kai?" Inji momi da ta tare shi cikin doki. Ya girgiza kai.

"Haifaffiyar can ce, a can din kuma ta girma."

Momi ta rage walwalar fuskarta zuwa hade girar rashin fahimta, ta kada kai ta ce.

"Ali ban fahimce ka ba, 'yar kauye mai tallan fura da nono, ko kayan Gina zaka auro...?"

Kai tsaye ya amsa. "Ba ta tallar nono, sai dai kiwon shanu."

Fuskarta momi na cika da jimami, amma maryam sai ta debo dariya irin wadda Basma ta yi masa, ita had da kwanciya a kasa tana faman nuna shi da yatsa, sai dai ita ba ta tanka ba.

Momi ba ta iya hasala komai ba, illa juya hannu kawai ta ke, ta ce.

"Ban ga hikima a wannan azancin naka ba Ali, me yasa ba zaka yi auren dazaka yi farin ciki ba kamar mutane masu daraja irinka? Me zaka tsinta a karamar yarinya yar shekara sha bakwai, kuma 'yar kauye wadda ko aji kila ba ta taba gani ba, Ali zaka rusa farin cikin 'ya'yanka."

"A'a momi." Ya fada yana duban agogo ba tare da damuwa ba, yace.

"So ya hanani ganin aibun da ke kika gani, farin cikin 'ya'yana kuma ba zai sha ruwa ba, zan shirya masa ta duk hanyar da karfi na zai iya, ki yiwa daddy maganar, shi ma zan same shi gone."

Sai ta kasa tanka masa, ta ni shi da kallo kawai tana ficewa, kuma da gayya ya take kafar maryam da ke kwance tana dariya, ta na kara ko waiwayowa ya dubeta bai yi ba. *******************

Washe gari ya dauki yammaci ya koma gidansu. Daga can filin wasan gidan ya hango mahaifinsa tsakiyar karnukansa uku yana wasa da su, sanye yake da farin wando _three quater_ da farar singileti. Cike da farin ciki ya nufi shi, da farin cikin suka rungume juna, sannan Aliyu ya sunkuya yana wasa da wani kare, mahaifinsa na binsa da kallo cike da kauna. Ali ya dago cikin sangarta yace.

"Daddy ka sami labarin na sami matar aure ko?"

Daddy ya rungumo kafadar Aliyu ya ja shi suka nufi kujerun hutawa. Ya zaunar da shi, shi kuma ya dora kafa kan tasa kujerar da ya ja, ya sunkuya yana dafe da kafadarsa ya ce.

"Na ji Ali, kuma na kwana da shakkar kai da kanka ka tsarawa kanka ganganci irin wannan."

Aliyu ya dan yi fuska, sai dai bai ce komai ba, ya ci gaba da shafar kan wani kare da ya dafe masa.

Mahaifinsa ya ci gaba da kallonsa cikin murmushin yake, sannan a tausashe ya ce.

"Ka gane gangancin da ka ke shiryawa kuwa Ali, wanne farin cikin kake tsammatarwa kanka ga matar da ba ta da ilimin boko da na addini, kila ko mota ma ba ta taba hawa ba, duk ci gaban zamani da wayewar da ka yi da ita ko yarda akwai su ba ta yi ba, bare ka ji dadin ka gama da matakin farko na matsalarta...."

Aliyu ya kara yin fuska, ya ce. "Haba Daddy, wannan ai mugun data ne..." Mahaifinsa nasa ya tare shi cikin dan bugun kafadarsa, na alamar rarrashi.

"A'a ba mugun fata ba ne Ali, bambancin da ke tsakaninku nake son nuna maka. A matsayina na mai son farin cikinka sama da kowa, kuma mai kauna da fatan matarka ta samar da gagarumar gudunmowa a nishadinka da farin cikinka.

Ali wanne farin ciki ka yiwa kanka tanadi a yarinya mai shekaru goma sha bakwai, sannan ga duhun kan kauyanci da jahilci?"

Aliyu ya sauke ajiyar zuciya, amma ya kasa cewa komai. Mahaifin nasa ya kara tausasa murya.

"Ina son ka fahimce ni da kyau Ali, ai ba ka kawo Abu m na tankwabe wannan ma dan na ga da tsabar ganganci a ciki ne ya sa zan kasa goyon bayanka, kai da kanka ya kamata ka zauna ka yi tunanin *BAMBANCIN*da ke tsakaninku, wanda zai iya hana muku zaman lafiya idan kunyi sure.

Tazarorin da ke tsakaninku kamar sama ce da kasa, kana da kudi ita 'yar talakawa, kai boko mai digiri uku, kila mota ba ta taba hawa ba bare ayi maganar ta taba ganin alli. Abincin da kake ci daban, Wanda ta ke ci daban. Duk maganar da zakayi cikin ilimi zaka yi ta, ita kuwa zata fadi abin da ya zo bakinta ne kawai, yadda ake shirya gida da yi masa kwalliya bata sansu ba, dan ta saba rayuwa karkashin rufin bunu....ta ko ina _life style_ din Ku ya bambanta Ali, bambancin kuma shi ne haske a gidan aurenku ba wai dan ba kwason juna ba, kuma na fi tausaya maka don zata tawaye ka da yawa."

Ali ya dafe kai cikin runtse ido da girgiza kai, ya sauke numfashi ya dubi mahaifinsa da kyau.

*"NA SAN DA BAMBANCIN*Dad, na kuma yi duk lissafin da ka yi, sai dai na kasa rinjayar da nauyinsa akan nauyin son Rahma da nake ji a zuciyata. Ina son yarinyar kwarai fiye da duk wani so da ka taba samun labari daddy."

Daddy ya kawar da kai da dan kyabe baki.

"Amma ka yi asarar wannan so mai daraja tunda ka aza shi a muhallin da ba zaka sami raddi ba, ko da a fatar baki yarinyar nan ta taba cewa tana sonka?"

Aliyu ya dago a sanyaye ya dubi mahaifinsa ya na girgiza kai.

"Ba ta taba ba dad, duk da haka na kasa da zuciyata ta ga laifinta."

Daddy ya fara dariya cikin ka da kai. "To ina tabbatar maka _I love you_shi ne mafi karancin gatan da zaka rasa daga gareta, ka ke kayi nazari, dan ba zan matsa maka ba."

Aliyu ya yi shiru tamkar mai son zurfafa tunani, sai dai Rahma ce kawai ke yawo a zuciyarsa cikin watsar da aibunta.. [2:54PM, 2/24/2018] ‪+234 703 300 1537‬: ♦🔸♦🔸♦🔸♦🔸 *NA SAN DA BAMBANCIN* Page 30

*KAINUWA WRITERS ASS* ®

*NA* *Shopiee* *Ummu Shukran*

*Shafin na yau naki ne Ameeratu ummyn Nihlah Allahu ya saukar mana da ke lafiya alfarmar fiyayyen halitta Annabin rahama(S.A.W)*

Rashin amincewar daddy ya nuna bai rage komai a cikin son Rahma da shiryawa kai aurenta ba.

Yana ji a ransa kawai kauyacin Rahma da jahilcinta kawai kowa ya sani, amma ba su San amfaninta gare shi da zai iya danne jahilcinta da kauyancin nata ba, ko da kuwa zata dauwama cikin kauyanci da jahilcinta.

Ranar juma'a ya gama komai na shirin kai kansa ga neman auren Rahma ba tare da ya sanar da kowa ba. Tun yammacin juma'ar ya yi tanadin, komai ya adana cikin motarsa _jeep_kamar kudade, tsarabar Rahman, su Musa da Dagaci, sai kuma zuciyarsa da ya korar mata dukkan tsoro da fargabar yadda zata iya rutsawa da shi.

Da sanyin safiya ya cusa bindiga a aljihu ya shige mota yana bata wuta, direbansa da ke masa bangaren ya cimmasa a guje daga shi sai singileti da dogon wando. Ya rusuna cikin haki yana gaishe da shi, ya ce.

"A yi hakuri oga, ban san da wuri zaka fita ba.... Shi ne... Oh naga sai tara kake fita ranar asabar."

"Ai komai daurowa ta ke." Ya fada lokacin da ya ke shirin ta ke giya, ba tare da ya dubi direban ba a ladabce direban ya ce.

"Mai gida ina zuwa? Idan...." Ya tare shi da kallonsa fuska a bace.

"Ko ina zauna akwai aikin da zan yi maka?"

A ladabce Balarabe ya girgiza kai. "A'a, ina nufin idan na yi wanka sai na biyo ka."

Aliyu ya yi murmushi ya fara Jan motar yana cewa. "Idan ka yi wankan sai ka tafi biyan bashin zancen da ba ka je jiya ba, ko kana nufin ban fahimci yadda kake yamutse min fuska jiya ba? Da na rike ka har dare na hana ka zuwa hira."

Balarabe ya bige da bin motar da kallo yana murmushi cike da kaunar ogansa tunda bai bashi damar raddi ba, maigida na da sakin fuska da daukar mutum da daraja, ko ya yi fushi bai cika tsawaita shi ba, in yaso kuma yana wasa da su tamkar abokansa.

A bakin _get_ ma haka suka yi da maigadi yana daura _belt_ yake cewa maikudi maigadi.

"Ranka ya Dade ayi mana addu'a." Maikudi ya rusuna da fara'a ya na cewa.

"Allah ya taimake ka, Allah ya dawo mana da kai lafiya, Allah ya ba ka dukkan abin da kake nema."

Aliyu ya ja mota yana dariya, ransa na yi masa haske game da fatan maikudi. _Allah ya baka abin da ka ke nema_

Kamar dama ya San zai je neman muhimmin abu a duniyarsa.

Ya dagawa maikudi hannu yana cewa. "A kula da kyau, kar a bar kowa ya shigo min gida, duk yadda na ke da shi."

Maikudi na masa Allah ya kiyaye yana tuna Basma a zuciyarsa, yasan da ita maigida yake. Haba yarinya kamar ta hada dangi da mayu, ya fada a ransa yayin da a fili ya dora.

"Allah idan ta zo yau zan nuna mata kalar rashin kirkina."

Lafiyar mota da kwarewar gudu da mota ya sanya Aliyu isa Rugar Gulu cikin awa uku daga Kaduna. Ya tsayar da mota dab da bigiren da aka tashi tantinsa satin da ya wuce yana bin wajen da kallo. Wata sabuwar kaunar Rahma na kara cika kirjinsa, dan babu abin da Rugar da duk wani abu a cikinta ya ke tuna masa sai soyayyarsa da Rahma.

Dai-dai sannan lokacin Rahma na kwance kan bishiyar kanyar da ta hango Basma a kirjin Aliyu ranar da zai tafi, a yau tana cikin damuwar da ta zarce ta wancan ranar. Dan kuka ta ke sosai, amma zuciyarta ta kasa sanyi kamar mai shirin babbakewa. Duk fadin duniyar nan ita sai ta yi mata kunci tamkar wadda aka saka cikin kura tandu.

Kamar almara ta hango silalowar bakar motar Aliyu, kukanta ya dauke, hawayenta kuma suka tsaya cak! Ta kurawa motar ido cikin bugun zuciya da fargabar ta ga sannan matar ta fito tare da Aliyu, ko Aliyu tare da wani, sai ga kyakkyawa Aliyu mai kamshi ya fito. Nan take ya kamshinsa ya karade wurin iskar ta dinga ratsa zuciya har kwakwalwa tana rikida zuwa halittar son sa, har sai da halittar son nasa ta cika zuciyar ta ta fal! Sannan ta fara sauyata wasu hange hange masu tsauri.

Rasuwar Halliru, aurenta da ake shirin daurawa ga mai rabo nan da bayan sallar azahar, yadda zata rasa Aliyu da yadda zata dauki rashin, sai kuma yadda zata iya nasarar samunsa duk cikin wadannan dakiku da ba su fi cikin luddai ba.

Wannan ya sanya kukanta dawowa sabo fil! Mai ciwo fiye ma da na dazu, tunda yanzu tana kallon kyakkyawar fuskar Aliyu da ke son zame mata kila wa kala duk da zuwan nasa a yanzu ya shayar da ita mamaki kwarai, don kafin wannan lokacin ta fitar da rai da zuwansa.

Fitarwa da ya yi awon gaba da saka ran farin ciki a rayuwa iyakar zamanta a duniya.

Aliyu ya gama da kallon muhallin tantinsa da zagayensa, zuwa turbar da yake bi zuwa wajen motsa jiki da kiwon rahma. Ya bi ganinsa nisan wajen gadarsu Rahma da hakan ya sa shi matsanancin jin kishin ganinta. Da sauri ya kai ganinsa ga bishiyar hanyar da ya hangeta rannar da zai tafi, kamar almara sai gata a bishiyar.

Cike da wani irin nishadi ya karasa gare ta har da hadawa da gudu. Jiki a sanyaye ta diro daga bishiyar tana kokarin goge hawayenta Wanda tun kafin ta sauko ya kula da su.

Ya dubi ta run daga sama har kasa, ta na sanye da kodaddiyar atamfa zani daban, rigar daban, dankwali daban, daurin kan ma ta wani tamke shi, ga urban murjani da dankara a wuya, kunnenta kuma da wanj yararin yari.....wannan shigar tata ta ishe kawar mata da kai ya tsartar da yawu, amma sai sam ba su Dada shi da kasa ba, sai ya fi damuwa da tarin hawayen da ya gani a idonta. Bai kuma yarda idonsa ke gizo ba, ta rame matuka! Cikin Barin jiki ya dafa kafadarta yana dubanta a rikice.

"Rahma me ke faruwa?"

Ta ja da baya a hankali dafe da gurin da ya rike a kafadarta tana kallonsa kai tsaye. Hawayenta na kara gudu. Hakan ya sa ya kuma shan gabanta ya rike kafadunta duk biyun, kuma ya rike da kyau yadda da ta yi yunkurin kwacewa sai ta kasa. Da murya kasa-kasa ya ce.

"Fada min Rahma, mene ne ya faru?"

Tana kokarin tsayar da hawayen ta ke kokarin bambare hannunsa daga kafadarta, fatar jikinsa kamar auduga, amma nata hannun da ta ke kokarin hukunta shi da shi wani tattaura har da kaya-kaya, hakan ne yasa da ya saki kafadarta sai ya riko tafukan hannayenta yana kallo, sannan a hankali ya dago ya nacewa kallon fuskarta, zuciyarsa cike da wani irin rauni dalilin so da kaunarta. Da wannan damar kuma ta yi amfani ta kwace hannayenta ta ja baya tana kuka da girgiza kai har ta furta."

"Ni na fasa sonka wallahi." Shi ma ya ja baya yana tuntsura dariya dan yasan laifin da ya yi ta fasa son nasa. Ya sha gabanta yana ci gaban da dariyarsa, yace mata.

"Wai me yasa daga na yi Dan karamin laifi kike cewa kin fasa aurena? Idan kuma mun ji auren idan na yi laifin me zaki dinga fasawa?"

Ta fara kokarin goge hawayenta tana kau da fuska. Ya kuma kasa kai yana dariya ya ce.

"Rahma kar ki bari na saba da kukanki har ya zame min jiki, ki daina cutar min da kanki ta hanyar damuwa da abinda bai kamata ya same ki ba. Ina muka kwana, ya ya Halliru?"

A nan ne ta kara fashewa da kuka cikinsa ta ce.

"Yau kwanan sa biyu da rasuwa!" Aliyu ya yi mutuwar tsaye, amma zuciyarsa ta tsayar da aiki ne bayan ta rasa abin da zata yi, KUKA KO DARIYA?

Dariya zai yi domin Halliru ya mutu ya saukaka masa dawainiya da fafutuka, ko zai iya kuka ne dan sabo da Halliru da kirkinsa, ko kuma kukan kishin kukan mutuwar Halliru da Rahma ta ke zai yi? Ko kuma tasa mutuwar zai wa kuka kafin ta zo.

Da ya yi dabara duk sai ya kori kuka da dariyar da fuskar jimami ya ce.

"Ayya! Allah ya yi masa Rahma, me ya kashe shi?"

Furtawa kawai sai ta kuma fashewa da kuka. Takaici duk ya cika zuciyarsa, amma haka ya zura ido yana kallonta har sai da sonta ya raunana zuciyarsa da tausayi sannan ya katseta a sanyaye. [2:54PM, 2/24/2018] ‪+234 703 300 1537‬: ♦🔸♦🔸♦🔸♦🔸 *NA SAN DA BAMBANCIN* Page 31

*KAINUWA ®

*Na* *Shopiee* *Ummu Shukran*

*Ya zama dole na gaishe ku muta ne na kainuwa writers Allah yabar kauna har karshen abada muna tare for ever🤝*

"Ya isa, wannan kukan ya isa, kuma nasan ba zai dawo miki da halliru ba."

Ta kokarta cikin kukan tace. "Shi tasa ta kare, kaina kawai nake tausayi, ina jin a raina da wuya idan rayuwata ba ta kare cikin kunar rai da bakin ciki ba."

Ya yi dira-dira a rikice kamar zai rungumeta, sai kuma ya nutsu cike da tausayi ya ce.

"Tsayin rayuwatazan kare duk wani abu da zai kona ranki Rahma, kar ki yanke kauna, idan dai kina tare da ni, iyakar karfina ba zan barki ki yi bakin ciki ba."

Ta fara girgiza kai da murmushin yake.

"Ban San da yadda zata kasance har na sami farin cikin da kake tanadar min ba, Wanda yake-kashen mutane a kaina ya bayyana,dan sarkin dorin rugar sama da mu ne, shi kuma ya kashe halliru ya danna shi ruwa a kogi, har sai da ya mutu.

Asali shi ne Wanda ya fara fitowa ya na sona tun ina karamata, ya yi ta min toshi har tsawon shekaru, amma rashin tarbiyyar gidansu ya sa Baffanmu ya hana shi aurena, kowa ya yi zaton zai yi tawaye a wannan lokacin amma sai aka ga salin alim ya janye jikinsa ko duriyarsa ma ba a cika ji ba a rugarmu.

Ashe shi ya dinga bin dare ya kashe sale, da Tanimu, babu wanda ya ko zarge shi sai da layin kisan sa ya zo kan Halliru suka yi a gaban mutane cikin bacin rai da cika baki kuma ya fadi abinda ya yi.

A washe garin ranar ne kuma aka tsinto gawar Halliru a kogi."

Aliyu ya jima cikin nazari, sannan ya ce.

"Me yasa ba za'a mika shi ga hukuma ta hukunta shi ba?"

Ta karkada kai tana tabe baki. "A yanzu ya bar garin, na tabbatar kuma sati daya ya yi yawa zai dawo, kuma idan ya dawo sai ka ga an rasa wanda zai yi masa ko mugun kallo. Ai sun saba ko musu ba ayi da yan gidansu sai su illata mutum da mugun asiri..."

Aliyu ya debo wani dogon tsaki, ya katse ta. "Dan Allah bari yi min maganar banza, duk jarumtarku ku dinga shakkar mutun daya......"

Ta yi sakare tana kallonsa, ta ce. "Sihiri gaskiya ne..."

Ya tare ta da fadin. "Allah ma gaskiya ne, ina tabbatar miki mutum na karshe ya kashe a masu son aurenki, ko ya sha giyar wake ba zai iya zuwa muhallina ya kashe ni ba, ke ko muhallinsa naje na rantse miki ba zai iya kashe ni ba, kuma ko da shaidan yake bautawa ba Allah ba akan tsafi, kar ki kara yi min maganarsa.

Yanzu me ake ciki?" Ta kalli gidan Dagaci da hawaye, tana nunowa da hannu.

"Jiya na ji rade-radi a gidan Dagaci ya yi kiran baffanmu ya tabbatar masa zasu hukuntashi idan aka kuma rasa rai a kaina, saboda haka lallai zuwa yau ya aurar da ni ga wani.

Dazu kuwa Dagaci ya aiko har gidan aka kira shi, nan da nan kuma naga an tashi harkar biki a gidanmu, ba zan yaudari kaina ba, na sani ana fitowa masallaci sallar azahar za a daura min aure da duk wanda ran mahaifina ya kawata masa."

Yana saurarenta sannan zuciyarsa na shirya masa mafita,dan haka tana direwa ya bi turbar gidan Dagaci da kallo, sannan ya kama kafadarta yace.

"A can ke nan kike tunanin za a daura auren?" Ta janye jiki.

"Ina tsammanin haka, musamman idan an yi gudun rigima tunda shi Dagaci ana ganin kimarsa ba za a tashi hayaniya a gidansa ba."

"Ok, yanzu maza ki koma gida, in Allah yaso zaki sami labarin da ni aka daura."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull